Showing 24001 words to 27000 words out of 48040 words
Chapter 9 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
Har kwana biyar ya ga Ma’am ba ta da niyyar shiga kitchen, sai dai ta nade
hannu ya gama ta side tana santi, tare da mamakin yadda aka yi ya iya girki haka.
Ya je ya yo musu cefane mai dumbin yawa ya cika musu fridge da freezer, ga nama da
kifi nau’i-nau’I babu wanda bai sayo ba. Sai girkin Ma’am yake jira ya dandana.
Amma har kwana bakwai Halimah ko ruwan shayi ba ta taba dafa musu ba. Yau dai ya nade
hannu a kirji ya ce, “Sweetheart, yau fa girkinki za mu ci, na gaji da cin girkin kato. I want to
taste my wife's cook”.
Halimah ta sunkuyar da kanta feeling embarrased, ta ina za ta fara fada wa Hashim ko
indomie ba ta iya dafawa ba? Hatta ruwan zafi cook ce ta ke dafa musu, ita ba za ta iya tuna
shekara nawa ta yi rabonta da kicin din gidansu ba. Ba ta taba kawo wa ranta wata rana irin
wannan na zuwa ba, da za ta yi aure har ta yi girki tunda abu ne da suka riga suka cire rai da
shi.
Mu karasa a littafi na biyu, tare suke.
-Takori
AURE KO BOKO?
(Littafi Ga Matasa Maza da Mata)
2
SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
GABATARWA
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai.
Duba da halin da matasa ke shiga a kasarmu Nijeriya a yau, daga mazan har matan, akan
rashin aikin yi ga wadanda suka samu damar yin ilmin zamani mai zurfi da matsalolin da hakan
yake haifarwa, sannan da halin wasu daga cikin manyan 'yan bokon wannan zamani na baiwa
boko fifiko akan addini, yasa na yanke shawarar rubuta littafin AURE KO BOKO? Ba don komai
ba sai domin ya zamo hannun ka mai sanda ga irin wadannan 'yan boko da matasa masu zurfin
ilmi marasa aikin yi. Tasirin furucin iyaye akan 'ya'yan su mai kyau ko maras kyau, hakika shi
bakin iyaye kaifin sa da tasirin sa yafi na reza. Sannan 'ya'ya amana ne a hannun mu,
kasancewar Ubangiji yayi musu umarnin su yi wa iyaye biyayya sai da yayi tagociya ga cewa
banda akan umarnin Ubangiji.
Ina fatan wannan dan littafi ya zamo mai amfani ga al'umma, matasa maza da mata, ya zamo
sadaqatul jariya ga iyaye na ya yafe min kurakuran da ke cikinsa.
- Sumayyah Abdulkadir (Takori)
3rd June, 2021
GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowanne gidan radiyo ko kafafen yada labarai ba tare da
izni na ba, ko copying dinsa a kafafen sada zumunta, yin hakan karya doka ne kuma abin
tuhuma daga Lauya na Barr. Sadiq Rufai Wali.
GODIYA
Ga dukkan members na Takori's online Forum, na gode da kaunar ku da goyon bayan ku.
FATAN ALKHAIRI
Ga duk makaranta littatafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, ina godiya da
yabo da fatan alkhairin da kuke yi mun, Allah ya barmu tare cikin alherin sa, har zuwa ranar da
muka daina numfashi.
AURE KO BOKO?
Amma tsakaninta da Hashim soyayya ce da amana babu boye-boye ko ha’inci, don haka ta
rausayar da kai tana mai kautar da idanunta daga kallon sexy eyes din shi, ta ce,
“Wallahi Cherie ban iya ba, ban san yadda ake yi ba”.
Ko daman ya tsammaci hakan, yana so ya tabbatar ne. Ganin irin tsananin damuwar da
fuskarta ta nuna sai ya sunkuya ya sumbaci wuyanta ya sakalo ta cikin jikinsa.
“Halimah, kada ki damu, in dai kina da niyya za ki zama expert a girki watarana, just say kina
son koya, kuma kina da passion a kai”.
Da sauri ta ce, “Wallahi ina so na koya ko don kada ka yi min kishiya”.
Dariya ta ba shi sosai, ya ce, “Don’t ever think of this between us. Idona ba zai iya kllon wata
diya mace ba bayan Ma’am dina, my Boss, my Oga on top, my uwargida, my amarya, my
Sweetheart, mother of my children, apple of my eyes… Halimatus-Sa’adiyyah Hashim
Yakasai…” Dole ya sanya ta murmshi daga damuwar da ta shiga. Hakan yake so da ma shi ya sa ya
kawo rahar. Ya kwantar da ita a kirjinsa kanta na bisa kafadunsa. Gashin kanta yake shafawa a
hankali zuwa gadon bayan ta, yana rada mata wasu kalamai wadanda suka zamanto sirri ne a
tsakanin su. Birona ba zai iya rubuta su ba. Tun daga wannan rana Hashim ya zage yana koya wa Halima girki iyakar wadanda ya iya, ya
kuma sayo mata littattafan koyon girki na Hadiza Umar Dogon Daji da na Chef Azizah Idris
Gombe. Wadanda ke koyar da girki a saukake na gargajiya da na zamani, My Essential Kitchen
(Aziza), from my kitchen (Hadiza Dogon Daji). Ga kuma online class da ta yi joining na Mami Gabdo (manti’s kitchen). Kasancewar ba ta
komai sai ta maida hankali, kuma da yake ta sa damuwar abin a ranta cikin sati uku abubuwa
da yawa suka zauna mata. Ta fara girka musu saukakan abubuwa.
Hashim bai tsaya a nan ba ya shiga cikin ibadar Halimah, sallah, wanka, tsarki, alwala da
sauransu duk sai da ya tsaya ya yi correcting dinta. Sannan ya fara yi mata dorin karatun
Alkur’ani mai girma duk bayan sallar asuba kafin su koma barci, da ya lura bai fi hizfi biyu ta iya
ba, shi ma a wajen Zarah ta koya. Tana missing Zarah, amma tunda ta yi aure a Misissipi ba ta kara samun contact da ita ba.
Rayuwar Halimah ta samu kyakkyawan cigaba cikin watanni uku. Addini ya kara ratsa ta, ta
daukar wa kanta duk wasu responsibilities na macen aure. Sosai ta ke kula da mijinta wanda ke
yin komai iya karfinsa don inganta rayuwarta da kasancewarta cikin walwala da kwanciyar
hankali. Ya gama karantar Halimah tsaf! ‘yar love ce, ita dai a yi love, idan hakan ta samu babu
irin biyayyar da ita kuma ba za ta yi mishi ba. Sai ta samu Hashim ya zarta tunaninta ya dame ta
ya shanye a fannin nuna soyayya da iya making love din, babu gazawa he is always available
at her service a duk lokacin da ta ke bukatarsa.
Wannan satin ya ce ta shirya za su je Kano wajen su Inna, don ya ki kai ta ne har sai
hankalinta ya kwanta. Kullum ya gaisa da Inna ko Yaya Rabi’a sai ya ba ta wayar sun gaisa, har
sun dan saba suna hira sama-sama.
Jikin Inna da Rabi’a ya yi sanyi da suka ji sacrifice din da Halimah ta yi a kan soyayyarsa, da
kuma ko wace ce Haliman da ko wane ne ubanta gare shi. Da yadda ta dauke shi aiki cikin
mutunci da karramawa.
Sun yarda in ban da soyayyah ta hakika, shi din da bai isa ya samu Halimah ba. Duk da haka
sun so a ce ya dauko musu daidai su, don samun nutsuwa da kwanciyar hankalinsu, amm
tunda komai ya riga ya faru, ba su da ja da yin Allah.
Sosai Halimah ta ke shiri don tafiya Kano, ta ware wasu manyan atamfofinta da ba ta dinka
ba da niyyar kai wa Inna Hajara da Dr. Rabi’a, sannan ta ware kayan kwalliyarta masu tsada
don kai wa Sa’adatu.
Ana i-gobe za su tafi, Hashim ya shigo dakinta ya same ta tana hada kaya. Tunda ta ke a
rayuwarta ba ta taba zuwa Kano ba, daga Adamawa sai Maiduguri wajen dangin iyayenta, su
din ma ba sosai ba, kasancewar Daddy ba wani damuwa ya yi da su ba, saboda talakawa ne,
shi kuma ba ya son su zame masa liability sai tasa ta taso shi yake nemansu in za su yi masa
amfani. Saboda haka ne babu wata shakuwa tsakaninsu da danginsa na uwa ko uba.
Zama ya yi gefenta bisa carpet, ya dauko wayarsa ya yi danne-danne ya mika mata, ya ce ta
sa mishi account number dinta, amma kada ta tambaye shi komai.
Ta yi hakan cikin dari-dari ta mika masa.
Ya karba ya yi ‘yan danne-danne sai ga alert ta samu, kudi ne masu dama, ya ce, “Ki yi
hakuri auren mu ya zo at a smart pace (afujajan) ban samu damar yi miki lefe ba. Mun yi
shawara da Yaya Rabi’a ta ce kawai in ba ki kudin, kin fi ta sanin abin da ki ke so”.
“Haba Cherie? Ni wallahi na yafe, duba tulin suturar da nake da ita wadda za su yi min
shekaru biyar nan gaba, ba su mutu ba ban daina saka su ba sabida kaya ne masu nagarta.
Don Allah ka maida kudin nan ka ji da hidimar yau da gobe, kada ka manta daga ni har kai
unemployed ne (marasa aikin yi) yanzu. Bar ganin ka tara ‘yan kudade gaba ta fi baya yawa”. Ya ji dadin maganganunta sosai, ya kuma kara yaba hankalinta.
“Na sani sweetheart, amma wannan hakkinki ne na al’ada, insha Allahu Allah zai rufa mana
asiri. Ina ginin gida a Kano, za a gama zuwa next year mu koma mu daina zaman gidan haya,
don haka nauyin zai ragu. Alhamdu lillahi kun biya ni sosai a NCC na samu na tara na gina
gidan kaina, ga mota na mallaka alhamdu lillah. Things will be alright da yardar Ubangiji. So ki
karba kawai”.
“Na gode, Allah ya kara budi na alkhairi”.
Ya janyo ta jikinsa yana fadin, “Tun safe ki ke hada kaya, kwana uku fa kawai za mu yi”.
Ta girgiza kai, ta ce, “Ka bar ni in yi sati tare da Inna. In ba haka ba ba za mu saba ba”.
“Abin da Kanon gaba daya za mu koma sweetheart?”
“Duk da haka. Ban taba zuwa ba tun aurenmu sai yanzu. Ka yi hakuri ka bar ni mu yi sati”.
“Your wish is my command Ma’am, I have missed calling you Ma’am… from the time I know
how sweet you are sweetheart ya mamaye bakina”.
Ya fada yana kokarin hade bakinsu wuri guda, ita kuma tana sinne kai a jikinshi. Har gobe in
ya kusance ta ba ta fasa jin kunyarshi kamar a lokacin ta fara zama matarshi. Tana son Hashim,
yadda harshenta ba zai iya bayyanawa ba.
****
BABI NA TAKWAS
Tunda suka kamo hanyar Kano suke hira abinsu kasa-kasa, hirar da daga jinta za ka san
masoya ne na hakika, kuma sabon aure. A lokacin ne ta kara sanin abubuwa da yawa da suka
shafe shi da ba ta sani ba a baya. Ita ma ya kara sanin nata, a kan asalin mahaifiyarta. Ya yi
mata alkawari watarana zai kai ta har Maiduguri ta ziyarci dangin mahaifiyarta. Sun shigo Kano yamma lis, ta shiyyar Na’ibawa suka shigo, kafin a hankali su gangaro cikin
gari. Ya dauke kan motar suka shiga unguwar Yakasai.
Kowa ya san Inna Hajara, ya san ma’abociyar tsafta ce. Gidanta ko ruwanka ne ya zube za
ka iya tsugunnawa ka kurbe abinka. Kullum a share tas-tas a kintse, don ma dai ganyen
bishiyar umbrella kan bata gidan wasu lokuta, amma a take ta ke kwashewa, da yake bishiyar
ba ta zubda ganyen da yawa. To yau ma hakan ta gama sharar yamma ta yi wanka ta zauna tana sauraron Aminci radio,
Sa’adatu ta zo hutu daga makarantar kwana da ta ke yi a GGC Kano, ta aike ta ta debo mata
kwai a kangon da suke gidan gonarsu, wanda like yake da katangar gidan.
Sallamar Hashim da santaleliyar matarsa ya dauki hankalinta. Ta mika hannu ta rage sautin
radiyon tare da amsa sallamarsu tana murmushi. Halima sai sunkuyar da kai ta ke, ta mika
mata hannu tana fadim, ta zo gabanta ta zauna. Yara suka soma shigo da jakar kayansu da
tsarabar doya da potatoes da Hashim ya yi wa Inna a kan hanya. “Masha Allah, masha Allah”. Kawai Inna ke fadi, domin ta ga Haliman ba yadda ta tsammace
ta ba. An ce mataimakiyar shugaban ma’aikata sukutum, ta dauka za ta ga uwar mata irin
matan Abuja da ke like wa kananan yara, sai ta ga yarinyar da a fuska ba ta fi Sa’adatu mai
shekaru ashirin ba, wannan ya kara sanyaya zuciyarta da auren hankalinta ya kara kwanciya da
auren.
Har kasa Halimah ta durkusa tana gayar da Inna, ita kuma sai saka musu albarka ta ke. Ta
mike zuwa firjinta da ke kicin ta debo musu kunun aya mai sanyi da gardi. Tana fadin, “Kin sha
hanya Halimatu, maraba da Sa’adiyyah”.
A lokacin Sa’adatu ta shigo, niki-niki da crets din kwai. Saura kadan ta saki kwan a kasa don
murna. Cewa ta ke,
“Welcome Aunty Halimah”.
Ta zo gaban Halima ta kama hannunta, sai kallonta ta ke tana mamakin kyawun halittarta. Ba
ta san sanda ta ce,
“Brother you are among the luckiest”.
Murmushi ya yi idanunsa na satar kallon Halimar ya ce, “Koh?”
Inna ta ce, “Tashi sarkin magana ki kai musu abinci su samu su huta gajiya, ina ce dai kin
gyara dakin nasa da na ce ki gyara suna hanya?”
Sa’adatu ta ce, “Ai tun safe na kalkale shi Inna, na sa turare na san brother da son turaren
wuta”.
Inna ta ce, “To dauki jakar kayansu ki shigar musu da ita. Halimatu tashi ku je ki huta, ina
fatan kinyi sallar la’asar?”
Halimah cikin jin dadin tarbar da ta samu daga family din Hashim, ta ce, “Mun tsaya a hanya
mun yi Inna”.
“To madallah, Allah ya huta gajiya”.
Halima ta bi bayan Sa’adatu wadda ta dauki trolley dinsu da handbag dinta zuwa dakin
Hashim da ke gidan.
Babu komai a dakin, daga shimfidadden carpet mai taushi blue, sai dirkekiyar sabuwar katifa
da aka jefa a kasa, aka kalailaye ta da kyakkyawan bedsheet, sai sababbin filulluka guda biyu.
Halima ba ta fahimci Hashim ma a dakin zai kwana ba sai can bayan isha da ya shigo daga
masallaci ya zare rigarsa ya bar farar singlet da dogon wandon jeans din da ke jikinsa ya fada
gefenta a kan katifar yana fadin,
“Na gaji, yau sai kin kwana kina min tausa tunda ba ki karbe ni tuki ba har muka zo Kano”.
Halimah ta zaro ido, “Don Allah ka tashi ka fita, kada Inna ko Sa’adatu su shigo, ka yi wa
Allah ka fita ko ni in fita”.
Wani kallon so ya jefe ta da shi, sannan ya yi dariya.
“Ai nan dakina ne tun na samartaka, kuma kina ji ita Innar da kanta ta ce a nan za ki sauka.
Gara ma ki saki jikinki yarinya ba alfahari ba, Innata is very simple and easy going. Sannan tana
da wayewar kai daidai misali…”
Halima ba sauraronsa ta ke ba, mikewa ta yi jikinta har rawa yake ta yayibi mayafinta ta fice
dakin Inna.
Inna da Sa’adatu na kallon talabijin, Halima ta fado dakin duk suka dube ta, sai duk kunya ta
kamata, ta ce, “Inna… am… na ce ko ina ne dakin Sa’adatu? Ina so zan kwanta”.
Inna Haajar ta dube ta with concern cikin yaba nutsuwarta a ranta ta ce,
“Dakin mijinki za ki zauna, daga yau har ku koma. Sai in ba ya nan ne za ki kwana tare da
Sa’adatu. Ki saki jikinki da mu mun zama uwa daya uba daya. Ni uwarki ce ba suruka ba”.
Hawaye ne ya cicciko idanun Halimah, ta ji dadin kalaman Inna Haajara, something she
missed from a mother, wato kulawa. Za ta iya cewa ta ji kaunar dattijuwar har cikin ranta. Ta yi
musu sallama cikin jin kunya ta juya ta koma.
Hashim na waya lokacin da ta shiga, da turanci yake magana ba ta san ko shi da waye ba, ta
zauna gefen katifar tana zumburo baki, ya rufe wayar da murmushi ya ce, “Kin