Showing 3001 words to 6000 words out of 48040 words

Chapter 2 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

“Mun fahimta Daddy,
kuma insha Allahu za mu kiyaye. Allah na tuba ni Daddy ko a Mexico ban taba haduwa da
namijin da ya yi min ba balle a Nigeria, ba'a haifi wanda zai ishe ni kallo ba, ka kwantar da
hankalinka, ‘ya’yanka are safe at this side (‘ya’yanka a kebe suke a wannan bangaren)”. Prof. ya ce, “Da kyau my daughter. Halimah kin yi shiru kina jin mu, tunanin me kike?”.
Murmushi Halima ta kakalo wanda iyakarsa fatar bakin ta, ta ce, “Daddy me zan ce to? Sai
dai in ce Allah ya taimaka mana wajen sauke nauyin da a rataya a wuyan mu. I will work harder
yadda ma’aikatan NCC duka za su amince da zabin ka, su ga cewa ko da gata da kananan
shekaru to da cancanta cikin zabin da ka yi musu”. Hanan ta yi dariya, “Wai ke Sis Leemah, me ye damuwarki da ma’aikata ne? Cewa nake
duka karkashin Daddy suke? Ko basu amince da zabin Daddy din ba sai me? Sun isa su cire ki
ne?”
Daddy ya ce, “Is okey Hanan, kin santa akwai concern, ni kuma na san za ta iya shi yasa na
bata, and that is good nuna damuwa ga damuwar wasu, balle ma duka ba su da matsala. Your
P.A will assist you also, sannan tsohon mataimaki na zai nuna miki yadda komai yake, ba za ki
samu matsala ba insha Allah, as sharp as this brain of yours”. Halima ta yi murmushi, “Allah ya taimaka mana Daddy, mun gode, Allah ya ba mu ikon
faranta maka yadda ka ke faranta mana”.
Su duka biyun ya dora hannu a kafadunsu dama da hagu yana fadin,
“These are my daughters”.

Ko da Halima ta koma dakinta a wannan daren kasa barci ta yi. Tunani kala-kala ya yi wa
zuciyarta kawanya. Shekarunta ashirin da hudu, amma Babanta ya fito fili ya ce, bai so ta yi
aure a bisa wasu hujjojin sa wadanda addini ba zai taba karba ba. Ga shi ita tana son yin auren,
don duk wadanda suka yi karatu tare har babbar kawarta Zarah sun yi aure sun barta, sai ta
tsufa ta tsofe a gida? Ko sai ta kai shekarun da maza za su daina sha’awarta? Daddy dai so
yake su rayu ba aure, kamar yadda yake rayuwar sa!

To kuma what about the call of nature? Na kowanne lafiyayyen dan adam?
A yanzu haka ma ba wani saurayi ko manemi tare da ita, duk sun gudu sun kama gaban su.
Ba irin maneman da ba ta yi ba a Mexico, don Ubangiji ya kyautata halittar ta, amma barazanar
Daddy na kullum cewa, muddin suka saurari saurayi zai dakatar da karatunsu, ya sa duk ta kore
su. To sai yaushe Daddy yake nufi zai musu aure? Ko ko irin rayuwarsa yake so su ma su yi har
tsufan su? Da yawon daren da yake zuwa basu san inda yake zuwa ba?
Tunani ne da ba ta da amsoshinsa, kuma ba za ta iya yi wa kowa maganar ba, ta bar wa
Allah komai. Shine masanin gaibu. Ya yi mata zabin abin da ya fi zama alkhairi ga rayuwar ta.
****














BABI NA BIYU
La’asar sakaliya, a wani madaidaicin gida ckin wata unguwa mai tsohon tarihi a jihar Kano,
wadda aka fi sani da 'Yakasai'.
Gidan wadatacce ne sosai, mai dakuna biyar ciki da falo. Madafi da bandaki biyu. A
tsakiyar gidan bishiyar umbrella ce mai yawan ganyayyaki da nunannun ‘ya’ya yalaye sharr,
amma ga dukkan alamu masu gidan ba sa tsinkar su. Watakila don ba su da yara ne. Ko basu
iya cin 'ya'yan umbrella ba. Inna Hajara ce zaune ta shimfida tabarma a karkashin bishiyar tana tankaden garin masara.
A gefe ta kunna rediyonta tana sauraron shirye-shiryen gidan radiyon Freedom. Sallamar
babban dan nata ta sa ta mika hannu ta rage sautin rediyon. Ya shigo cikin takunsa na
nutsuwada haiba, ya ja kujera ‘yar tsugunne ya zauna yana fuskantar mahaifiyar sa.
Dogo ne sosai, baki mai dogon hanci. Kalarsa ta fi kama da ta mazan kasar Addis-Ababa,
musamman lallausar sumar kansa da ta nuna shi ruwa biyu ne. Innar sa Hajara basudaniya ce
ta usul, daga garin Jazeera, Sudan, mahaifinsa ne Bahaushe, wanda karatu ya kai shi Sudan
ya auro Haajara, shekararsu goma tare Allah ya yi masa rasuwa, tun daga lokacin kuma ba ta
koma kasarsu ba, sannan bata kara aure ba, ta maida hankali ga tarbiyyar ‘ya’yanta uku da
uban su ya mutu ya bar mata.
A lokacin da maigidanta ke raye, sun yi rayuwa ta sukuni da yalwa, domin shi din Dr. ne a
jami’ar Bayero, suna zaune a unguwar Janbulo tun kafin a yi gidaje da yawa a cikin ta. Bayan

rasuwarsa rayuwa ta yi tsananin da dole ta sayar da gidan ta sayi karami a cikin gari wanda
suke ciki a halin yanzu don ta tallafi rayuwa da karatun ‘ya’yanta. Ta kuma kama sana’ar gidan
gona har yau, inda ake kiwon kaji da raguna har da shanu, inda ake fidda madarar shanu a
sayar da kwai da kaji, in shekara ta zagayo lokacin babbar sallah ta sayar da ragunan da ta
kiwata ta zuba wasu.
Da wannan sana’a Inna Hajara ke tallafe da marayunta. Suka kuma zame mata abin alfahari
domin sun bada himma a karatu na addini da na zamani. Babbar ‘yarta Rabi’a ita ta gaji
mahaifinta. A kasar sudan ta yi karatun shari’ar addinin musulunci a yanzu haka babbar lecturer
ce a (Aminu Kano School of Legal and Islamic Studies), shi da ya biyo bayanta a wannan
shekarar ya gama masters dinsa daga jami’ar Ahmadu Bello, inda ya karanci injiniyan sadarwa
(Telecommunication Engineering) da kwalayen digiri da masta masu daraja ta farko.
Kanwarshi mai binshi Sa’adatu tana jami’ar Bayero tana karantar harshen Larabci (B.A
Arabic) duk a kokari da jajircewar uwa irin Inna Hajara wadda ba ta hada komai da ilmin
‘ya’yanta ba, domin kuwa a cewarta babansu ya sha yi mata wasiyya a kan hakan.
Ba su cikin arziki, basu cikin daula, amma suna cikin rufin asirin Ubangiji wanda shi ya fi
komai kwanciyar hankali. Sun fi karfin abinda zasu ci, da sutturar da zasu daura. Yayarsa Dr.
Rabi’ah na nata kokarin wajen ganin ba su rasa komai ba tunda shi har yanzu bai fara aiki ba.
Yana dai aikin koyarwa a wata makaranta mai zaman kanta wai ita ‘yan Dutse a Kano, bai jima
da farawa ba.
Inna Hajara ta dube shi kamanninsa kullum da mahaifinsa marigayi Dr. Ismael Yakasai har
razana ta yake. Wani lokacin ko kallonta ya yi sai gabanta ya fadi don hatta kwayar idanunsu iri
daya ne. Gashin kansa da launin fatarsa shi ne irin nata na Sudanese. Saurayi ne ajin farko,
wanda ya dama ya kutsa cikin ilmummuka daban-daban. Babban sirrin kyawunsa shi ne dogon karan-hancinsa wanda har wani lankwashewa ya yi a
karshe, ko maza ‘yan uwansa ba za su bar fatan ina ma a ce su ne shi be, balle kuma mata.
Shi kam zai ce ya sha wuya a hannun mata lokacin karatu a jami’a, musamman ‘ya’yan masu
da shi, wadanda suke ganin kudin iyayensu zai iya jawo ra’ayinsa gare su. A hankali suka
fahimci nagarta da kamewa, sannan uwa-uba rikon addini irin nasa daban ne dana sauran
maza. Ba kowa Allah ke yiwa irin baiwarwakin da yayi masa ba. A daddafe ya kammala karatu
ya huta, ya zauna a gida yana ta neman aiki lungu da sako. Shekarunsa talatin da daya cif, in
har lissafin da yake yi daidai ne. Duk inda ya ji wani online vacant dake bukatar profession din
sa sai ya shige cike ya aika.
Inna Hajara ta dube shi da murmushi, “Yau ina ka shiga ne? tun dazu ban ji dawowarka ba,
bana jin ko abinci ka ci”.
Ya ce, “Inna, abincin nan yau ba zai shiga cikina ba, zuwa na yi in gaya miki gobe zan yi
sammako zuwa Abuja ma’aikatar da suka yi mana aptitude watannin baya, sun kira ni da
gaggawa. Sai a sanya mu cikin addu’a”.
Inna Haajara ta washe baki cikin murna, ta ce, “Addu’a ai duk bayan sallar farilla kuna cikinta,
Allah ya shige gaba Ya bada sa’a, Ya kuma karawa rayuwa albarka”.
A daren ranar ya kulle kayansa kala biyu da duk abin da zai bukata, da ma jiya makarantar
da yake koyarwa wato ‘YAN DUTSE suka biya shi albashin wata. Don haka ba shi da matsalar
kudin mota har wajen kwana zai iya kamawa.
Ya kira Yayarsa Dr. Rabi’a ya gaya mata batun tafiyarsa Abuja, ta yi masa addu’a sosai, ko

ita tana so kanin nata ya samu kwakkwaran aiki ya yi settling down ba aikin private school ba
wanda babu fansho ba garatuti. Ga karatun shi mai matukar kyau ga kyawun sakamako, don
dai yanayin kasar tamu ne sai alhamdulillahi.
Washegari tun asubahi ya bi motar farko zuwa birnin tarayyah.

****

Su biyar ne a kan luntsuma-luntsuman kujerun da aka tanada don baki maziyarta masu son
ganin shugabar bangaren daukar ma’aikata. Tun safe suke kan layi har yanzu da azahar ta
gabato, ya ga cewa komai runtsi dole ya je ya yi sallah, aiki dai na duniya ba na lahira ba. Don
haka ya mike tare da gaya wa abokan zamansa zai je ya yi sallah ya dawo. Kallon mahaukaci suka hau yi masa, bai kula ba ya yi wucewarsa. Su kam ai ko za su
kwana wurin nan ba su matsawa ko nan da can.
Minti biyar bayan fitarsa sakatariya ta fito da takardu a hannunta ta kira sunan sa, duk cikin
wadanda ke zaune babu mai wannan sunan. Don haka ta tsallake shi ta kira na gaba. Ya
rungumi file din da credentials dinsa ke ciki tamkar ya rungume zuciyar sa, ya shigo ofishin da
sallama. Bayan ya idar da sallah ya dawo, nan suke gaya masa an kira shi ba ya nan. Ya mike zuwa
ga tebirin sakatariyar, calmly ya ce,
“Excuse me Ma’am, I went to pray for some minutes”.

Wani kallon banza ta yi masa da ma gata kirista ce. Nan ta ke gaya masa, gara ma ya kama
gabansa don layi ya riga ya wuce shi.
Kyale ta ya yi ya koma wajen zamansa ya zauna yana kallo daya bayan daya suka shiga
suka fito, amma matar nan ta hana shi shiga. Wayar da ke kan tebirin ta ce ta yi kara ta daga da
sauri, yana tsaye a kanta rungume da hannayensa a kirjinsa. Daga ido ta yi ta dube shi, sannan
ta ce,
“Ok Ma!” Tare da kife wayar,
“Allah ya so ka, ta ce ka shiga”.
Murmushi ya yi wa kansa, ya dauki jakar goyonsa ya saba a baya, wadda ke dauke da
dukkan takardunsa. Ya sanya kai a katafaren ofishin.

Yana shirin ganin dattijo ko magidanci, sai ya ga wata kyakkyawar budurwa son kowa na juyi
a kan kujera, kwata-kwata shekarunta ba su fice na Sa’adatu kanwarsa ba.
Mamaki ne ko al’ajabi ya hana shi yin abin da ya kamata, wato gaisuwa, sai ya tsaya kikam
yana kallon ta. Kyawunta kam zai iya cewa bai taba ganin mace mai irinsa ba. Ba wannan ne
abin da ya tafi da hankalinsa ba, kankantar shekarunta ne da wannan mukamin.
Hanan ta kufula da kallon da ya tsaya yana yi mata, babu gaisuwa babu nuna girmamawa sai
kallo. Ga ta da son girma kamar gyambo. Ta ga kuma kamar kallon raini yake yi mata. A fusace
ta ce,
“Please get out, idan ka zo ne don ka kare min kallo”.
Ya sauke idanunsa kasa, “I’m sorry Ma”. Sannan ya samu kujerar da ta dace da shi ya zauna.

Amma sai Hanan ta maida kai ga files din da ke gabanta, ta ce,
“In ka gama zama ka san inda dare ya yi maka. Ba zan duba takardunka ba, domin ba zan
dauki mayun kallon mata ba”.
Ya yi ‘yan mintuna a zaune ya kasa cewa komai. Zai so ya gaigaya mata magana cewa, ba ta
isa ya tsaya kallonta ba, bata da abinda zai kalla; rather mamakin mahaukacin da ya ba ta
ofishin yake.
Cikin bacin rai ya mike ya juya ya fita, yana fadi cikin ransa; ashe NCC ta mahaukata ce, in
ba haka ba ya za a yi a dauki babban mukami irin wannan a bawa wannan shashashar yarinyar
da ba ta ko kai shekaru ashirin ba?
Shi ma in dai irinta ne za su shugabance shi suna ba shi order ya fasa aikin, ba ya so.
Ta bi shi da kallo baki bude don ta dauka zai yi apologizing.

Tafiya yake yana zancen zuci ba tare da lura da cewa a kan titin motocin ma’aikatar yake
tafiya ba. Daidai lokacin da wata sullubebiyar mota ta taho kan titin da gudu, direban motar
yana ta yi masa horn amma bai ji ba tsabar bacin ran da wannan yarinyar ta kunsa masa. Yana
tuno wahalar da ya sha na zuwa Abuja da albashinsa da ya karar wajen kudin mota, da kama
daki da yayi a hotel, ga layin da ya hau tun karfe bakwai na safe, har zuwa yanzu bai sanya
komai a cikinsa ba.
Sannan yarinya kanwar bayansa ta zo ta yi masa wannan wulakancin? Tun fil’azal kowa da
ya sanshi a duniya ya san abu daya da ba ya dauka a rayuwarsa shi ne raini, musamman daga
wanda ya girma.
Duk kokarin da Halima ta yi na sarrafa sitiyarin motarta sai da ta dauke shi ta yi cilli da shi a
gefe. Ta take totur din motar tana kiran sunan Allah. Securities da tsilli-tsillin mutanen da ke
wajen suka yo kansa don ba shi taimako. Halima ta bude kofar motar ta fito sanye cikin
doguwar riga fitted gown ta wani sassalkan yadi ruwan madara, ta yane kanta da wani karamin
mayafi baki, idanunta rufe cikin prada dinta kamar kullum.
Sabanin Hanan, Halima ba ta so a tuka ta a mota, ko a hada ta da mai tsaron lafiya a
matsayinta na EVC/CEO, tafi so tayi driving kanta in dai ofis za ta je, sauran wurare ne ta ke
shiga karkashin kulawar masu tsaron lafiya for security reason.
Suna kokarin sanya shi a wata mota ta ma’aikatar NCC don kai shi asibiti sakamakon jinin da
yake zubarwa, Halima ta ce,
“Ku sanya shi a motata, mutum biyu ku shigo mu je tare”.
Jikinta sai rawa yake don ba ta taba kade ko zakara ba balle dan mutum. Wani asibiti mai
zaman kansa suka nufa kusa da ma’aikatar inda aka karbe shi da gaggawa sabida matsayin
Halima.
Duk wani taimako da ya kamata sun ba shi, sun masa dinki a goshinsa da gyara gocewar
kashi, sauran kananan ciwuwwukan duk sun manne su da plasta. Likita ya ce, za su rike shi
tsawon kwana biyu don tabbatar da cewa babu internal injury. Halima ta kama daki V.I.P aka
shigar da shi can bayan likitoci sun gama duba shi sun ba shi kwanciya ta kwanaki biyu. Gida ta koma don ya samu barci sakamakon allurar barcin da aka yi masa. Aikin da ta je
domin ta yi mai muhimmanci dole ta fasa shi. Wanka ta yi tare da sallar la’asar, sai a lokacin ta
samu nutsuwa. Ta kira mai girkin abincinsu Helen ta ce ta shirya mata lunch a basket ta sanya
mata a mota za ta fita nan da twenty minutes (mintina ashirin).

Tana shiga mota domin ta tuka, sai jakarsa da ke gefe wadda wani security ya sako a motarta
ta dauki hankalinta. Ta san babu kyau yi wa mutum bincike, amma haka kawai ta ji tana son ta
duba ba don tsoro ba sai don tsaro, ta san wane mutum ta ke dawainiya da shi.
Babu komai cikin jakar sai takardun shaidar karatu (qualifications) tun daga firame har jami’a.
sai kuma CV wanda ke dauke da dukkan bayanan da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login