Showing 45001 words to 48000 words out of 48040 words

Chapter 16 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

a kan BOKO!
Yau ya tabbata sai Ubangiji Ya tsayar da shi hisabi tsakaninsa da Haleemah, idan har bata yafe
masa ba!
*****








BABI NA GOMA SHA UKU
Karfe goma na safe Hashim ya iso café (business center) dinsa. Abin da ya ba shi mamaki
dirkeken kwadon da ya rufe kofar shagon ya tarar a gefe a yanke. Kofar shagon kuma a
sakaye, wato an sakaye ta.
Cikin wata irin mummunar faduwar gaba ya finciki kofar iya karfinsa ya shiga. Fetal! Sunan
wani fili. Duka computers, printers, scanners, photocopying machines, lamination machine da
duk wani abu mai daraja da ke cikin shagon babu shi. Kwashewa aka yi? Tashi sama suka yi?
Allahu A’alam, amma da ya tuna da yankakken padlock da ya baro a kofa sai ya gane shigowa
aka yi ta karfin tsiya aka yashe shi.
Daga tsayen da yake ya sulale a kan kafafunsa. Yanayin da yake ciki ya fi dacewa da a kira
shi suman ido biyu. Ya fi karfin awanni biyu a haka, kafin nutsuwa ta zo masa sakamakon
kalmar innalillahi wa’inna ilaihi raji’un da ta samu muhalli a kan harshensa.
Sai kawai ya mike ya sabi hanya, tafiya yake tun daga filin tsohuwar jami’ar Bayero ba tare
da ya san inda yake jefa kafarsa ba. Ya wuce Kofar Famfo, ya wuce Kofar Duka-Wuya, ya wuce
Kofar Gadon Kaya, ya wuce Hauren Shanu, ya wuce Kofar Na’isa, ya wuce Kofar Dan’agundi,
ya wuce ta cikin Sabuwar Kofa ya bulla Yakasai. Tun karfe sha biyu na rana har karfe biyar na
yamma kafin kafafunsa su kawo shi gida.
Halimah na yi wa Safiyyah wankan yamma yadda ta ke yi kafin babanta ya dawo, ya same ta
tsaf tana kamshi. Tsuke cikin kyakkyawar suttura, sai ga shi ya fado gidan kafafunsa futu-futu
kamar an kwato shi daga bakin kura.
“Baban Safiyyah, lafiya?”
Ta fada hankali tashe.
Ya ja kujera ‘yar tsugunne wadda sun gaje ta ne daga Inna ya zauna yana maida numfashi.
Kawai Halimah sai gani ta yi hawaye sun zubo masa.
“Ba ni wayarki zan yi reporting wa police, wayata babu kudi”.
Halima ta kara shiga tashin hankali.
“Police Baban Maama? Fara gaya min mene ne don Allah?”
Ya mike tsaye, “Ki bari in je police station in dawo”.
Sai da ya je ya dawo ne yake gaya mata komai. Halima ta runtse idonta, ta ce,
“Ya Salamu sallim!”

‘Yan sanda sun yi iya kokarinsu, amma kullum abu daya suke gaya musu, “Ana kan bincike”.
Ba shagonsa kadai aka yashe ba, har na kusa da shi da na gabansu. Tun suna jelen ofishin
‘yan sanda har sun gaji sun bar wa Allah komai.
Kasar Najeriya da shuwagabanninta suka kara sire wa Hashim. A kullum sai ya zauna yana
kiyasce-kiyascen abin da zai yi idan Allah ya ba shi shugabanci komai kankantarsa. Wani irin
determination ya shige shi a kan leadership (kwadayin shugabanci) da kuma kwadayin siyasa
(political inclination). Har zama yake ya yi ta rubutun abubuwan da zai yi idan da a ce shi ne ke
da shugabancin Nigeria, da kuma matsalolin masu ilmi irinsa da matasa ke fuskanta.
Rannan Halimah ta dauki daya daga cikin rubuce-rubucensa tana karantawa. Taken rubutun
shi ne babban abin da ya dau hankalinta; NIGERIA’S TRAUMA IS POLITICAL DICHOTOMY…
there is always a dichotomy between what our politicians say and what they do… insecurity
overwhelmed us… thugging, insurgency, robbery, kidnapping, unemployment are the major
problems of our youths......
Haka ya yi ta jero matsalolin matasa wadanda suka addabi al’umma, wanda unemployment
shi ne silar mayar da su heartless suke cutar al’umma. Abubuwan da zai yi wa matasa idan ya
samu damar shugabanci komai kankantarsa.
Ya koma shiru-shiru ya rage walwala, kullum cewa yake,
“Halima ba ni da sa’a!”.
Ita kuma sai ta ce, “Bar fadin haka Baban Maama, haka rayuwa ta ke, WATARANA ZUMA,
WATARANA MADACI, ko kai ne beran masallaci saboda talauci, haka nake sonka. BA ZAN
DAINA SONKA BA!” (Sunan littafin Watarana Zuma....na canza shi zuwa AURE KO BOKO?)
Hatta wasan da yake yawan yi wa Maama (Safiyyah) ya rage shi, ya rage fita, daga sana’ar
kajin Halima suke ci suke sha. Halimah ta fahimci he is a bit depressed don haka ta dage wajen
counselling dinsa, yi masa nasiha a kan muhimmancin yarda da kaddara, kunna masa wa’azin
malamai masu tuni da cikar imanin bawa bai yiwuwa har sai ya yarda da kaddara mai dadi ce
ko mara dadi. Ta kara dagewa wajen kyautata masa tare da faranta masa a shimfida.
Hashim ya yarda da fadar Manzon Rahma cewa, rabin addinin mutum shi ne dace da samun
mace ta gari. Halima ba ta gaza ba har sai da ta samu Hashim ya saki ransa, ya koma cikin
nutsuwarsa, ya fara fita ‘yar buga-bugarsa yana samo musu dan abin da ba za a rasa ba. Wani
abu sai kasata Najeriya. Mutum mai kwalin digiri na uku kenan, babu irin cike neman aikin da ba
ya yi online amma in magana ta fara kankama a karshe wanda ke da kafa (wanda ya san wani)
shi za a ba wa aikin ko da kuwa kasa yake da shi a qualification.
Tuni Hashim ya daina neman aiki, aikin gwamnati ya fita ransa, ko aikin koyarwa a makarantu
ya daina nema. Zuciyarsa ta kekashe ba abin da yake so yake mafarki irin SIYASA.
A daidai wanan lokacin Maama (Safiyyah) ta cika shekara guda, sabanin wasu makafin da
idanunsu ke a bude garau gani ne ba sa yi, Safiyyah idanunta a rufe suke ruf! Tun a wannan
lokacin Safiyyah ta san muryar uwarta ta san ta ubanta. Ta san ta lalubi fuskokinsu ta gane su.
Ta san in ta ji muryar babanta ya dawo ta fito da gudu ta yi masa oyoyo! Ko da kuwa za ta ci
karo da wani abun ta fadi ta buge ko ta ji ciwo ba ta fasawa.
Wata irin soyayyah suke yi wa Maama, ko sauro ba sa bari ya cije ta. Kullum tas-tas da ita
cikin wanka da kyakkyawar suttura. Yadda Halima ke kula da ita ba ta kula da kanta haka.

******

“Duk inda za ki nemo min lambar wayar uban yaron nan ki nemo min yanzu-yanzu”. Prof. ya
fada yana duban Hanan da rinannun idanunsa.
Wayarta ta dauko daga jakarta ta budo lambar Baban Salim ta mika masa.
A take ya dau lambar a wayarsa ya kira, sakatare ne ya dauka ba bata lokaci ya fada masa
ko shi waye, kuma so yake ya ganshi, in zai yiwu a gida don family matter ne.
Minista ya san ko waye Zubair Numan, amma bai taba sanin yana da alaka da matar dansa
ba. Sabida ba shi ya karbawa Salim auren ba kaninsa ne, kuma ba mazauni bane sannan irin
mutanen nan ne ba masu kwakkwafi ba. Nan ya bada appointment karfe takwas na daren ranar.
Karfe takwas din kuwa a harabar gidan Ministan ta yi musu, shi da Hanan tana dauke da
babynta.
Fargabar duniya ta ishe ta, don Daddy bai gaya mata inda za su zo kenan ba, da ta fara kiran
Salim ta gaya masa.
Minista ya sa aka yi musu jagora zuwa falon saukar bakinsa na musamman. Ya sa aka cike
gabansu da abin tarbar baki, amma sai ya lura chairman a masifar fusace yake.
A hakan suka gaisa, Daddy ya ce ya yi masa alfarma uwargidansa ta kasance a wajen don
abin da ya kawo shi ya shafe ta.
“No problem”. In ji Minista, nan ya kira Hajiya Mubina. Ba jimawa ta shigo tana taku daidaya.
Ganin Hanan zaune rungume da jaririya ya ba ta mamaki.
Daddy ya nuna Hanan, ‘Kun gane wannan?”
Hajiya Mubina ce ta ce, “Kwarai na gane ta mana, ba Hanan ba ce?”
Prof. ya ce, “Da kyau, ‘ya ta kenan ta biyu cikin ‘ya’ya biyu kacal da Allah ya ba ni, wadda
dan ku ya aura ya saki babu dalili. Now, kun ga wannan…”
Ya nuna ‘yar hannun Hanan, “Ke ba ni ita nan”.
Jiki na rawa Hanan ta ba shi ita, ya dauka ya kai wa Minista har wajen zamansa. Da sauri ya
karbi ‘yar ganin yana neman kwala ta da kasa.
“Jikarku ce ta gaba da fatiha na kawo muku, kun raba su ta karfi ba su rabu ba, ga
sakamakon abin da suka zaba nan. Na gama nawa kukan, saura ku. Hanan tashi mu tafi, Allah
ya ba mu alkhairi’.
Hanan ta ki tashi kamar an kafe ta, ZUCIYAR UWA! Ko kusa ba ta jin za ta yarda ta bar falon
nan ba tare da ‘yarta ba.
“Daddy, Yusra fa?” Ta fada muryarta na rawa.
“Yusran uwarki? Kanwar uwarki ce ko kanwar ubanki? Za ki tashi mu tafi ko sai na fasa miki
baki da hanci?”
Ya juya ga Minista, “Kai dan siyasa ne, muddin ka dawo min da ‘yar gaba da fatiha gidana sai
na tona wa media ta ji. Wallahi ba ku san ni ba, ba wai bana son ‘yata ba ne, bata min rai kawai
ta yi”.
Ya fizgi hannun Hanan ya tankada keyarta.
Minista ya sassauta murya abin tausayi.
“Amma Prof. kamata ya yi ka zauna mu yi magana ta nutsuwa ko? I never know she is your
daughter, ce min suka yi ba a san salinta ba, ba ta da iyaye balle dangi. Ko ba haka ki ka ce
ba?” Ya jefa tambayar ga maidakinsa.
Ta sunkuyar da kai hawaye na bulbula. Yau ina za ta kai dan shege a cikin jikokinta?
“Ka yi hakuri Prof. ka zauna mu fahimci juna. Na hada ka da girman Allah”.

Jikin Prof. ya yi sanyi, ya saki Hanan ya samu kujera ya zauna.
“Ka bari in kira Salim, ya zo ya tabbatar min ‘yar nan tasa ce, duk da biri ya yi kama da
mutum, kuma ido ba mudu ba amma ya san kima. Ga kamanni sun bayyana kansu”.
Ya dauko waya yana goge hawaye ya kira Salim. Cikin sa’a shigowarsa gidan kenan.
Yana shigowa falon ya ja turus! Ya tsaya yana rarraba idanu. Uwar da uban suka bi shi da
kallon takaici. Sai ya tsugunna yana gaida Prof. ya ki amsawa.
Minista ya ce, “Salim, is this your daughter?”
Ya nuna yarinyar da ke rike a hannunsa.
Kansa a kasa, bai taba jin kunyar iyayensa a duniya irin yau ba, jinsa yake tamkar tsirara a
gabansu. (Kunyar duniya ma ke nan kafin ta lahira. Allah ka yafe mana kura-kuranmu, ka sa
muna daga cikin bayinKa muminai, Ka kare mu daga dattin zina).
Cikin tsawa mahaifinsa ya maimaita masa tambayar. Kansa a kasa ya ce, “Eh, ni na haife ta,
kuskure ne mun tuba mun bi Allah mun tuba”.
Uban ya ce, “Amma ka san you have tarnished the image of this house ko?”
Hawaye suka zubo wa Salim, ya ce, “Wallahi Daddy sau daya ne, Allah ne ya yi nufin
kasancewar hakan. Mun tuba muna rokon Allah gafara, muna rokonku ku gafarta mana ku ma.
Shaidan ne… kuskure ne...…”.
Ya fashe da kuka.

Minista ya maida dubansa ga Prof. cikin lallashi ya ce, “A karkashin sulhun da nake nema,
ina rokon ka maida masa auran matarsa, tunda akwai sauran zama a tsakaninsu, ko nawa ka
yanke sadaki zan biya. Mu taru mu yi ta istigfari, kuskure ne duk mun yi, ga shi garin kokarin
kare martabarmu mun jawo rugujewar martabar gabadaya. Maida aurensu shi ne maganin
komai, kuma rufin asirin yarinyar. Da kwanciyar hankalinmu gabadaya. Ka yi hakuri Prof. ka
amshi wanan sulhun”.
Shiru Prof. ya yi, Minista bai yi kasa a gwiwa ba ya ci gaba da rokonsa, har sai da Hajiya
Mubina ta sa baki ita ma, sannan ya koro musu sharudda na rikon auren diyarsa; za su rike ta
da kulawa, mutunci da kyautatawa.
Za a sake dauro auren a garin Numan cikin danginsa ba a Abuja ba, don su daina zaton ba
ta da dangi. Sannan babu gori tsakaninta da kowa nasu kan wannan yarinyar data haifa, duk
Minista da Hajiya Mubina suka ce sun amince.
Ya yanka sadaki yadda ya ga dama, duk dai sun amince. Sannan ne ya amince za a mayar
da auren jibi a Numan bayan saukowa daga sallar juma’a.
Salim da iyayensa suka yo musu rakiya har jikin motarsu. Hanan ta ki yarda ta kalli inda
Salim yake, shi kuma sai kokarin su hada ido yake amma ta ki, har suka shige mota direbansu
ya ja suka tafi.
Suna shigowa gida Hanan ta shige daki rike da Yusra ta kira Halimah ta labarta mata duk
abin da ya faru. Halimah ta ji dadi, ta kuma taya ‘yar uwarta murnar samun maslahar rayuwarta,
sannan ta ce da Hanan cikin wata irin kakkausar murya.

“In ki ka gaya wa Daddy kin san inda nake, ko kin san wani abu da ya shafe ni; BA ZAN
TABA YAFE MIKI BA! Kamar yadda ba zan taba yafe masa ba har duniya ta nade’.

safiyya ta wayi gari da bakon dauro (kyanda). Wannan ya tada hankalin Halimah da Hashim
ba dan kadan ba. Wadanda ko kuda ba sa so ya sauka a kan miskiniyar ‘yarsu. Ga shi ko kudin
motar da za a kai ta asibitin Malam babu, balle kudin ganin likita, don haka Halimah ta ce, bari
ta kai ta asibitin Murtala, za ta taka a kafa daga Yakasai zuwa can ba tafiya ce mai nisa ba. Ta roki Hashim ya zauna a gida don akwai wadanda suka yi da ita za su sayi kaji biyar
manya, in ya so sai su yi amfani da kudin wajen sayen maganin da aka rubuta musu.
Ba don ya so ba ya amince, don ya yarda ta fi shi gaskiya. Yana da wata kyakkyawar dabi’a
ta kai ‘yarsa ko matarsa asibiti da kansa, sabanin wasu mazan da sai dai su hada mace da
kudin mota amma ba za su kai ta ko ‘ya;yansu asibiti ba su tsaya su yi musu komai da kansu
ba. Halimah ko wanka ba ta tsaya yi ba sabida rashin nutsuwa. ‘Yar lele ba lafiya, ‘ya daya
tamkar dubu, wadda tun a wadannan shekarun nata ta san soyayyar da iyayenta ke mata. Tana
kuma tausaya musu duk da karancin shekarunta.
Duk da cewa atamfar jikinta mai tsada ce, amma ta fara kodewa. Tun cikin kayan haihuwar
Maama ne. mayafin jikinta a cukurkude yake babu guga don ba su da ayon. Fuskarta ko basilin
ba ta gani ba balle a kai fa zancen hoda. Duk da har yanzu kyawunta bai gushe ba, amma skin
elasticity dinta ya kau, shekaru masu yawa sun karu a kan nata na ainihi. Rayuwar cikin wahala
da rufin asirin Allah ake yinta, ta taimakekeniya tsakanin juna, wadda soyayyar da ke cikinta ce
jigon kasancewarta ‘live’ har a yau. In suka fara soyayya kamar sabon saurayi da budurwa. Ga
tausayin juna da karfafawa juna. They are not only husband and wife; su abokan juna ne kuma
sirrin juna.
Halimah ta yi lullubi rike da hannun ‘yarta suna tafiya a gefen titi don zuwa asibitin Murtala.
Wata mota ta danna horn daga bayansu, “Kun san makaho da ji”. Tuni Safiyyah ta gigice ta
kwace hannunta daga hannun uwar ta yi kan titi a guje ba tare da ta san ina ta nufa ba. Halimah
ta saki jakar hannunta ta dora hannayenta biyu a ka ta saki wani gigitaccen ihu a lokacin da ta
hango wata mota Peageout 504 ta taho da mugun gudu ta yi kan Safiyyah.





Mu karasa a littafi na 3.
Yana tafe insha Allahu bada jimawa ba.




Gundarin labarin AURE KO BOKO yana cikin littafi na 3. Alkawari ne na dauka zai tsuma
zukatan ku insha Allahu.


Taku har abada,
Sumayyah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login