Showing 33001 words to 36000 words out of 48040 words
Chapter 12 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
Janbulo za su dinga karbar kudin haya mai kauri, su samu Hashim ya
sake tada wata kakkarfar sana’ar.
Hashim mamakin Halimah ya hana shi cewa komai. Burin kowacce macen wannan zamani
mai tashen kuruciya shi ne ta zauna a gida mai kyau, a fitacciyar unguwa, ta yi tafiya a mota
dandasheshiya, yau ga tashi matar na fadin ta zabi ta bar gida mai kyau ta koma cikin gari don
ci gabansa. Tabbas Halima halayen ‘yan aljannah gabadaya ta kwashe su. Ba zai gaji da cewa
ya daga mata kafa ya kara dagawa, ta shige aljannah cikin aminci ba.
“Ki bar wannan maganar Halimah, yaya zan fidda ki daga gidanki in maida ke gidan gado don
amfanin kaina? Ki bari don Allah bana so”.
Halimah ta ce, “Ba amfaninka ba ne kai kadai, amfaninmu ne mu duka. Ka ga har sai ka
samu ka koma ka dora PhD dinka a nan B.U.K tunda aiki ya gagara, watarana kwalin zai yi
mana amfani. Don Allah Cherie kada ka ce min a’ah, ina so in na koma Yakasai ni kuma in ci
gaba da poultry din Inna”. Kwana bakwai suna takun saka, ta dage a kan bakanta, shi ma ya dage ba zai yi mata haka
ba, in ya yi hakan ya kware ta. Har sai da Halima ta fiddo masa bacin ranta karara sannan ya
amince bisa sharadin idan sun tara kudin da zai ishe shi gama PhD za su tashi su koma
gidansu. Ai kuwa da kudi masu gwabi aka karbi hayar gidansu, kasancewar ana iya biyan kudin
karatun in parts, babu jimawa ya nemi admission sabida kyawun takardunsa B.U.K suka dauke
shi da sauri, inda zai yi digirinsa na uku a kan fanninsa na Telecommunication Engineering. Bai
kuma fasa zuwa Janbulo yi wa yaran mai kudin nan lesson ba, sannan ga Halima a gida tana
sayar da kwai cret-cret da kajin gidan gona wa tsofaffin customers din Inna, tana da yaro da
yake kula da su ya kuma kwaso kwai kullum da safe. Gadon na Hashim ne shi kadai don Rab’a
da Sa’adatu sun hada nasu wuri guda suna nasu kiwon a gidan Dr. Rabi’a, don haka a wannan
shekarun asirinsu ya rufu. Hashim na ci gaba da karatunsa, ya sayi tsohuwar laptop don
research work, kullum da dare Halima na taimaka masa da rubutu da karin idea, duk rabin
research work din Halima ce ta yi masa.
Rana daya aka wayi gari da annobar mutuwar kajin gidan gona a Najeriya (chicken flu), kaji
suka yi ta zazzabi suna mutuwa. Kafin dan lokaci na Hashim da Halimah ma babu su, domin
gwamnati ta hana cinsu suna ji suna gani kajinsu suka yi ta faduwa suna mutuwa. A lokacin
Halimah na dauke da ciki wata biyar. Sa’adatu kuwa ‘ya’yanta biyu. Rushewar sana’ar poultry dinsu ba karamin shafar tattalin arzikinsu ya yi ba.
A baya Hashim bai san kudin cefane ba, awo kawai ya ke yi, duk wasu kananan bukatunsu
Halimah cira kawai ta ke yi ta yi. Yanzu kuwa sai ya je ya yi buga-buga ya nemo, kudin haya shi
ne kawai madogararsu, sai Ubangiji mahaliccinsu wanda ba ya barci.
Kafin watanni biyar kudin hayar da suka karba yake karewa a bukatun yau da kullum da na
karatun Hashim, cikin mawuyacin hali suke kai wa karshen shekara har Allah ya taimake su
Hashim ya kammala phD cikin shekaru uku cif! Babu jinkiri, sabida yadda suka taru suka maida
hankali shi da Halimah suka kammala research work din cikin lokacin da jami’a ta bukata. Halimah ta daga kwalin PhD din Hashim farin ciki fal ranta, ta ce,
“Ina ma ni ce?”
Duk sai ta bai wa Hashim tausayi, ya rungumo ta ya sumbaci goshinta, ya ce, “My
achievement is yours sweetheart, kuma alkawari ne na dauka insha Allah watarana sai kin
kammala PhD dinki”.
Halimah ta ce, “Kayya! Ta ina hakan zai yiwu alhalin ba ni da shaidar kammala ko sakandire
a hannuna? Ga shekaruna sun tura zan fara hidimar iyali. Kamar yadda ka ce din ne your
achievement is mine, to a barshi a hakan”.
Hashim tausayin Halima ya lullube shi. A take wani tunani ya zo masa, ya ce, “Halima ko in
kai ki ki ga Daddy ne? Just greetings, mahaifi ne in ya bar ku bai kamata ku ku barshi ba, binsa
za ku yi ta yi da neman gafara har sai ya huce”.
Halima ta girgiza kai da sauri, “Cewa zai yi wani abu na je nema a wajensa, ko wahala ce ta
ishe ni na dawo masa. Ni kam alhamdulillahi I’m contented with my life as such. Damuwa ta
daya ce rashin sanin halin da Hanan ke ciki. Haka kawai Hanan ba za ta manta da ni ba”.
Hashim ya ce “Kowacce fassara zai yi mana ki ba shi hakkinsa na haihuwa ki je. Allah shi ne
shaida ba mu je don neman komai ba, sai don sauke hakkin da ya rataya a kanmu. Na hakkin
haihuwa, wanda da shi zai yi hisabi ranar gobe kiyama. It’s almost four years rabon ki da
mahaifin ki, ya kamata mu je din don wani lokacin na kan yi tunanin har da rashin albarkarsa
cikin auren mu cikin abin da ke kara mana matsaloli a rayuwa”.
Halimah ta daga kai a hankali ta dube shi, ya gyada mata kai cikin karfafa zancensa, “Yes,
rashin albarkar iyaye a cikin aure na hana ci gaban rayuwa. Kuma yana kwashe albarka, yana
hana kwanciyar hankali, yana jawo rashin nasara a rayuwa…".
Hawaye ya fito daga idon Halima, ta ce, “Idan kuma ya ce mun zo neman aiki ne fa?”
“Whatever he will say”. In ji Hashim, “Ki tafi da kyakkyawar niyya, ki sa a ranki gafararsa
kawai ki ka je nema”.
Halima ta kwantar da kai a kafadun Hashim ba ta ce komai ba, amma yanayinta ya nuna
amincewa.
****
Allah kadai ya san irin fafutukar da Hashim ya yi tsawon sati guda kafin ya tara musu kudin
motar zuwa Abuja. Lokacin da Halimah ta zo hada kaya kala biyu da za ta tafi da su, rasa
wanne za ta dauka ta yi, duk sun mutu sun kode, amma dai wankakku ne, sun yi mugun jin jiki
dai, don rabon da ta dinka suttura shekaru uku ke nan da suke cikin sukunin cinikin kaji da ta
dinka wasu atamfofi (chiganvy) guda biyu da sallah, sauran kayanta tun na ‘yammatancinta ne.
Da a ce Halima ta san yadda ta koma a fuska, sai ta fi damuwa fiye da damuwar rashin
kyakkyawar suttura.
Tun asubah suka bar gida zuwa tashar Na’ibawa, inda suka hau motar haya zuwa Abuja.
Wajejen azahar suka shiga Jabi Motor park, daga nan suka samu taxi suka nufi Asokoro.
Halima ta daga kai tana kallon garin da ta yi dabdalar kuruciyarta, komai ya sake mata cikin
shekaru hudu. An samu ci gaba sosai a birnin tarayyar Nigeria. Kirjinta ban da balli-balli ba
abinda yake yi. Lokacin da mai taxi ya yi parking kofar katafaren gidansu ji ta yi zuciyarta kamar
za ta tsago allon kirjinta ta fito. Mai taxi ya sauke su, Hashim ya kirgo kudinsa ya ba shi. Halima na barin kafadunsa na dama
suke tafiya zuwa entrance na gidan. Hashim ya kwankwasa kofan, maigadin gidan wanda
tsohon soja ne ya zo ya bude.
Kallon sama da kasa ya yi musu, ko kadan bai gane Halimah ba. Sakamakon shekaru biyar
sun karu a kan ainahin ashirin da hudun ta, kodaddun sutturun jikinsu ya fara kallo, they look
shabby, ba irin mutanen Prof. Bane, don haka a wulakance ya ce,
“Me ku ke nema a nan?”
Halimah ta yi murmushi, ta ce, “Seun, ba ka gane ni ba?”
Kokarin rufe kofarsa ya fara yi don ba shi da lokacin irin su.
Halima idonta cike taf da hawaye ta ce, “ABCDEFG…H for Halimah, H for Hanan…” Karatun
da Seun, yake koya musu suna yara idan Daddy ya fita.
Seun ya zaro ido ya ce, “Halimah ke ne?”
Hawayen da suka cika idonta suka karasa gangarowa. Da sauri ya bude musu kofa yana
fadin, “Oh my dear! My daughter Halima… where have you been?”
Ba ta ba shi amsa ba ta tambaye shi Daddy na nan?
Ya ce, “Ku shigo maza bai dade da shigowa ba, kuma yanzu zai fito ya tafi U.S”.
Kofofin shiga gidan duka a bude suke, don haka suka sa kai cikin dari-dari. Kai tsaye Halima
falon da ta san Daddy ya fi zama ta kankame hannun Hashim suka shiga.
Ilai kuwa a nan suka same shi ya barbaza takardu a gabansa da farin gilashin kara karfin
gani a idanunsa. Babu wani canji da Halima ta gani a tare da shi, yana nan a kyakkyawan
bafillacensa, gani ma ta yi kamar an kara masa kuruciya, ko dayake an ce mai kudi ba ya tsufa.
Su biyu suka yi sallama, ba tare da sun jira ya amsa musu ba suka sanya kai, suka nemi can
gefe suka zauna manne da juna.
Prof. ya cire gilashin idonsa don gani ya yi kamar yana ba shi false vision; ko ta zama
tsohuwa ‘yar shekaru tamanin ba zai kasa gane ta ba. Tunda kuwa a kan hannunsa aka haife
ta, ya kuma raini abarsa da kansa.
Kasa cewa komai ya yi sai kallonsu yake ita da Hashim din, Halimah ta rarrafo daga inda ta
zauna ta zo ta zube a gabansa tana kuka.
“Daddy na zo neman afuwarka da albarkarka. Ka yafe mini, ka sa min albarka’.
Prof. ya yi wani murmushin keta. Ya dube ta a wulakance tare da cikin da ke manne da ita, ya
ce, ‘Har kin dawo haka so soon? Ai kin zo da wuri, har wahalar ta ishe ki ne, ko kuwa talaucin
ya ishe ki? Ko wanda ki ka zaba a kaina din ya sake ki kamar na ‘yar uwarki sabida rashin
dangi?” Makogaron Halimah ya bushe rayas! Yawun bakinta ya kafe. An saki Hanan? Wannan last
sentence shi ya fi tsaya mata a rai ba surutun Daddy na wulakanci ba. A hankali ta girgiza kai,
hawaye na sauka daga idanunta, ta ce,
“Babu ko daya Daddy, I’m here just to ask for forgiveness and your blessing”.
'‘Har abada ba za ki samu ba!” Daddy ya fada in exclamation. Ya dora da cewa, “Har sai
ranar da wuya ta ishe ki kika dawo gidanku, dawowa ta gabadaya, bana hada jini da talaka,
kuma ba zan taba ba insha Allahu… kai kuma… (ya nuna Hashim da dan’alinsa), ka yi ta zama
unemployed kenan muddin ba ka dawo min da ‘yata ba, ka sake ta ko nawa ka ke so zan ba ka
ka auri wata you can marry thausands of Halima not my daughter, zan kuma samar maka aiki
mai babban matsayi a babban bankin Najeriya CBN. In kuma ka ki, to ku tattara ku tafi, kada ku
sake tako min nan. Duk ranar da ku ka sake shigo min gida, kai ba da takardar saki ba, ita ba
da nadamar yin aure ta bar ni ba, sai na sa karnuka sun yagalgala minku. Ku tashi ku ba ni wuri
tun muna iya shaida juna ni da ku”.
Hashim ya tada Halimah wadda ke ta gunza kuka suka mike. Daddy ya kira waya, ga dukkan
alamu da maigadinsa Seun yake magana.
“Idan ka bari suka sake shigo min gida, a bakin aikinka”.
Suna kokarin fita daga falon Halima na waiwayensa, Daddy ya ce,
“Kada Allah ya sa ki haifo abin da ke cikin ki lafiya”.
Wannan magana ta fi kowacce kona ran Hashim. Da sauri ya juya ya ce, “Allah na kowa ne”.
Ya so ya gaggaya masa raddi a kan maganganun da ya yi musu, ya tuna cewa; Baban
Halimah ne, ba zai taba iya cin mutuncin wani da ya shafe ta ba balle iyayen da suka haife ta.
Da sauri ya ja Halimah suka tafi, a bakin get Seun ya faki ido ya jefar da wata farar takarda a
gabansu. Halimah ta sunkuya ta dauka, lambar waya ce a jiki, a kasa ya rubuta ‘HANAN’.
Kallon godiya ta yi wa Seun, don ta san Daddy na kallonsu ta CCTV dinsa.
*****
BABI NA GOMA SHA DAYA
Tunda suka dawo daga Abuja wanda a tashar mota suka kwana ranar, ba ci ba sha don
iyakacin kudin mota ne a aljihun Hashim. Halimah ta kwanta rashin lafiya. A karan-kanta ba ta
san ciwon me ta ke ba, tana dai kwance ne kawai ba ta umh ba ta mh-umh. Amma ta san tana
jin wani iri zafi a zuciyarta. Ya yi-yayi su je asibiti Halimah ta qi, don ya karbi albashin lesson din
yara, ta ce, maimakon ya kashe kudin a asibiti ya je ya sayo mata ‘yan rigunan jarirai da su. Ta
ba shi list din da aka ba ta na abubuwan bukatar haihuwa a Antinatal ta ce ya sayo ko rabinsu
ne, diaper da shawul da rigar sanyi saiti guda biyu.
Ya ce, kudin duka dubu goma ne, kuma ba su da abinci a gidan. Halimah ta ce, bakin da
Allah ya tsaga ba ya hana shi abin da zai ci.
Don haka ya tafi kasuwar Kofar Wambai da tambaya ya samu shagon kayan haihuwa masu
arha ya sayo fiye da rabin list din.
Kamar yadda Halima ta ce, bakin da Allah ya tsaga ba ya hana shi abin da zai ci, hakan ce ta
faru. A daren ranar sai ga Sa’adatu da mijinta Lawan sun kawo musu ziyara. Kallo daya
Sa’adatu ta yi musu ta tabbatar yunwa suke ji, jikin Halimah har rawa yake yi, amma sabida
karfin hali irin nata sai fara’a ta ke tana daga kwance. Mijin Sa’adatu shi ma ba wani karfi gare shi ba, amma dai za a ce ya fi Hashim tunda ba su
rasa abin da za su ci ba don yana hadawa da aikin kafinta, ko yanzu a bayan Vespa dinsa ya
goyo ta.
Sa’adatu juyawa ta yi tana share hawaye, ta san duk rashin Inna ne, duk runtsi Inna ba za ta
bar nata ya tozarta haka ba. Hashim ya dade da yanke alaka da Dr. Rabi’a da ma ita ce mai
taimaka masa, amma tun rasuwar Inna da suka yi baram-baram a kan Halimah ba ta sake ba
shi komai ba. Ta ce ya je ya karata da mai farar kafarsa tunda ya zabe ta a kanta. Shi ma kuma
ko da wasa ko hanyar gidanta bai kara bi ba.
Sa’adatu ta dauko mayafin Halimah ta mikar da ita zaune ta yafa mata, ta ce lallai-lallai asibiti
za ta kai ta da kanta tunda ba ta san muhimmancin lafiyarta ba, shi kuma Hashim din ya biye
mata sabida ba ya son takura mata, duba da halin da zuciyarta ke ciki tun dawowarsu daga
Abuja. Asibitin Malam ta kai ta, ai kuwa nan da nan aka rike ta aka ba ta gado, don sun ce she is
60% dehydrated (ruwan jikinta ya kone kashi sittin cikin dari), sannan ulcer ta kama ta, ga
rashin wadatar jini. Duk abin da aka caza Sa’adatu ta ce mijinta ya ranta mata za ta biya shi
karshen wata in ta dauki dashinta. A wannan ranar Hashim gefe ya koma yana kuka, yana jin kansa useless, yana jin kwalayen
ilminsa useless, tunda duk a sanadin babunsa Halima ta shiga wannan hali, Haliman da ya
daukar wa alkawarin mayarwa tauraruwa a cikin mata. Ya yi kudurin yi mata kyakkyawar
sakayya a kan sacrifice (sadaukarwa)rta gare shi. Ga shi bai samu damar cika ko daya cikin
alwashin da ya dauka ba. Bai taba tsammanin rayuwa za ta yi musu juyin waina kamar wannan
ba.
A lokacin da Prof. ya sallame su ya yi zaton kwalayen ilminsa ba za su barshi ya tozarta ba.
Ga shi dukkan mafarkansa ba su taba zama reality ba.
Ga Haliman kwance rai kwakwai-mutu-kwakwai, ko nauyin asibitinta ya kasa dauka.
Tafiya ya kama yi a gefen titi, bai san inda yake jefa kafarsa ba. Ya san dai zuwa zai yi ya
tashi ‘yan hayar gidansa ya sa gidan a kasuwa don ya kula da Halimah da abin da za ta haifa,
ya ja jari da wani abun cikin kudin, ya sayi ragon suna ya ajiye don