Showing 1 words to 3000 words out of 44977 words

Chapter 1 - MATAR UNCLE BOOK COMPLETE BY MISS HAJO.docx

11 Aug 2025

1441

♠️♣️ *MATAR UNCLE*♣️♠️

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*

(Miss Hajo✍🏾)

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

Marubuciyar*

👇🏾

Auren wata Tara

Ni da yaya arman

Khadijatul sabren

Ribar so

Najmat abiy

Mata ta ce

Komai mukaddari ne

And now

MATAR UNCLE

*GODIYA*

Bismillairrahnanir Raheem dukkan Yabo da godiya su Kara tabbata ga Allah (Swa)Tsira Aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad (S a w)Ina godiya ga Allah s w a da ya sake Bani ikon dawowa duniyar rubutu bayan tsawon lokaci da na shafe Allah ba ni ikon rubuta abunda zai amfani al’ummar musulmi Yayi Hani da hannuna wajen rubuta zunubi kurakuren da ke ciki Allah ya yafe Mun.

*GAISUWA*

Sakon gaisuwa da jinjina gareku daukakin Masoyan miss hajo a duk inda kuke Ina muku fatan alkhairi tare da babban albishir da wannan sabon littafi nawa mai suna *MATAR UNCLE* Wanda nake da tabbacin Insha Allah zai amsu a gareku miss hajon ce dai ba ta sauya ba ta na nan yanda kuka santa🤣kunsan bata da burin da ya wuce ganin ta nishadand’arta da zukatanku dan farincikinku shine nawa kar in cika ku da surutu I love u all Ina kaunarku inajinku chan cikin zuciyata sai mun hade a comment senction🧐

*GARGAD’I*

*Ban lamunta ayi mun amfani da littafi ta kowace siga ba ba tare da izini na ba hakkin mallakar nawa ne ni kadai masu satar mun littafi suna dorawa a youtube ba tare da izinina ba na barku da Allah wannan Karin aka kuma wlh zan dauki mummunan matakin da ban tab’a D’auka ba duk mai bukata ya nemu izinina*

*DEDICATED TO MY SISTER MARYAM L SADEQ*

1:july:2025/Tue

*BOOK ONE*📕👆🏻

🅿️………………………*1*

*QATAR*🇶🇦

(DOHA)

Sanyayyen iska ne mai had’e da lumshewar sararin samaniya ke kad’awa wanda ya k’ara samarwa garin ni’ima mai dad’in gaske,

zaune ya ke cikin k’atoton lambun gidan da ya k’awatu da ababen more rayuwa,

idanunsa sanye yake cikin farin glass yayinda hankalinsa na kan laptop ba ya ko d’agowa saboda yanda hankalinshi ya yi nisa ga dukkan alamu Abu yake mai matukar mahimmanci.

K’aran ringing wayar sa ne ya sanyashi dakatawa daga abunda ya ke ta cikin glass yake kallon wayar kafin ya sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciya ya na Kara wayar a kunnansa,da sallama

Bayan gama sauraren duk maganganun da Abiy ke fada masa kafin cikin nutsuwa mai tattare da lafuzza masu nuni da tarbiya cikin harshen larabci ya mayar masa da ya na zuwa gidan nasa Insha Allah.

Mikewa ya yi tare da nad’e laptop din gabansa wanda sai a sannan na kare masa kallo dogo ne sosai kallo d’aya zaka masa ka ga karfaffen jarumin gwarzon namiji farine kal yana da manyan idanuwa tare da siririn hancinsa da zajensa da ya zagaye kyakyawar fuskar sa kasantuwar gyara da sajen yake sha sosai ya kara baiyayyanar da baiwar kyawun halittar da Allah Yayi masa kallo d’aya zaka masa kaga asalin kyakyawan balarabe kamilallen mutum ne wanda kallo d’aya zaka masa ka tabbatar da ba wasa a tattare dashi ba shi da sakin fuska haka Sam tsarin shekarun haihuwarsa a k’alla bazai gaza 37 ba.

Kai tsaye hanyar da zata sadashi da ainahin part din kasaitaccen gidan da mallakarsa kasan sai mashahurin mai kudi ko kuma mai fad’a Aji a k’asar Sosai na karewa komai na palourn kallo majority off white ne babu Abu d’aya zaka kalla a palourn bai burgeka ba komai ya tsaru kunsan dai yanda daular larabawa take da son k’awa.

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa da ya gama haduwa da komai na more rayuwa Wanda girman d’akin ma kad’ai ya isa ya tsoratar da mai karatu palour na musamman ne a cikin dakin mai dauke da kujeru da plasma sai gefe wajen karatu da ke dauke ababen zaman karatu.

A gaggauce ya yi wanka kasantuwar magrib na karatowa bayaso ya rasa jam’i sosai Yayi kyau cikin farar shaddar Gezna hannunsa sai shek’in tsadaddiyar agogon da ya makala yake yayinda gaba d’aya d’akin ya karad’e da kamshin turarensa mai matukar masifar gigitar kamshi,

tsadaddun wayoyinsa guda biyu ya saka cikin aljihu cikin izza da takama yake taku tamkar jinin sarauta fuskarsa sam ba annuri koda ya fito Kai tsaye tsadaddiyar motarsa kirar lambogini ya tunkara wanda da hanzari mai gadi ya bude masa get tare da barin harabar gidan.

saida ya biya ya yi salla a masallacin kofar gidan kafin ya karasa gidan Abiy gidane na alfarma kallon securityn da ke zagaye da gidanma kadai ya isa ya tabbatar maka da mamallakin gidan jikakkene a mulkin kasar Wanda ko a daular larabawa kasan mallakar wannan gidan sai mashahurin mai kud’i.

Kai tsaye shak’akken palour Abiy ya tunkara Zaune ya tarar da balaraben farin dattijon da a k’alla shekarun haihuwarsa zai Kai 63 cikin gimamawa da tarbiya ya gaisheshi ya amsa tare da shafa kansa cikin harshen larabci ya umarcesa da ya zauna bayan sun zauna ya kallesa cikin Kulawa ya ce”Muhammad Ali na Kira ka ne ba don komai ba sai dan wata alfarma guda da nake nema wajenka?

Cikin sauri ya d’ago tare da kallonsa sai kuma ya b’ata fuska ya na kallon gefe ya ce “Ka wuce neman Alfarma a waje na Abiy umarni kawai za ka ba ni ni kuma na zartar,domin Kai d’in ai uba ne a wajena ”

Murmushi kamilallen dattijon ya yi ya ce”tabbas ina jinka tamkar D’an da na Haifa a cikina Muhammad Ali Baka da banbanci da su Ramadan amma hakan bazaisa na tilasta maka abunda Baka so ba,dole na ce ina neman alfarmarka domin abu ne mai girman gaske nake so ya k’ullu tsakaninmu Ina son Ka Auri y’ata Zahra domin k’ara karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninmu na tabbata ko yaya ya ke raye zaiyi farinciki da hakan!

Lokaci guda wutar kansa ta dauke kafin ya ji wani irin Abu ya soki zuciyarsa wanda saida ya rumtse idanunsa duk yanda ya so saisaita nutsuwarsa kasawa ya yi domin tamkar saukar aradu aka haka ya ji maganganun Abiy bai tab’a tsammanin hakan daga garesa ba dakyal ya iya daidaita nutsuwarsa kafin ya d’ago zaiyi magana Ya dakatar dashi ta hanyar cewa.

“Banyi maka tilas ba Muhammad Ali idan ka na ganin baka son zahra ka fada mun Kai tsaye bazanji komai ba saboda duk ku biyun d’aya kuke a wajena”

Karo na biyu kenan da ya dago tare da zubawa Abiy manyan idanuwansa ba ko kiftawa “Toh da wani ido ma zan iya kallonsa na ce bana kaunar y’arsa bazaiyu ba”Ya fada a cikin zuciyarsa

nauyayyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya dago a karo na biyu ya na kallon abiy da har yanzu shi ya ke kallo ya ce “bansan da wasu kalamai zanyi amfani da su wajen gode maka ba Abiy nagode kwarai da gaske Allah ya biyaka da gidan Aljanna ”

Murmushi Abiy ya yi ya na Sakin ajiyar zuciya ya ce”ni ne zanyi maka godiya Muhammad Ali Allah maka albarka Insha Allah Bazaa’a dauki dogon lokaci ba wajen gudanar da Auren ba”

”Sam saurarensa yake amma hankalinsa ba ya tattare da shi ya tafi wani waje daban “Auren zahra !!!!ya maimaita a cikin ransa kafin ya ce “bazaiyuba!

sam koda ya koma gida gagara bacci ya yi sosai kwalwarsa ta chazu bai tab’a tunanin Al’amura zasu kasance haka ba,

wayarsa ya dauka ya na kafe wani hoto da kallo ba ko k’iftawa ta ya zuciyarsa za ta iya rayuwa da wacce baya so”!bai tab’a son zahra a cikin ransa ba dukda kulawa da soyayyar da take nuna masa matsayin kanwa ya dauketa yasan tabbas ita zata fad’awa Abiy ta na sonsa ta ya zai ma iya rayuwar Aure da zahra bayan Sam tarbiyar yarinyar ma kanta ba ta masa ba wani dogon tsaki ya ja tare da dafe kansa “Tabbas Dole na gujewa Auren nan!”.

*NIGERIA*🇳🇬

(KATSINA)

Sosai ta tsirawa wayar hannunta idanu ba ko kiftawa gaba d’aya hankalinta na ga karanta comment din da ake ta yi mata a posting hotunanta da tayi minti talatin baya amma comment sama da 500 sosai jama’a ke zuzuta baiwar kyawun da Allah Yayi mata kowa na fad’ar albarkacin bakinsa,

wani irin dogon tsaki taja tunowa da duk comment dinnan da take sha dole ta sauke sa kafin ayi mata Chaa kamar wacce ta haifi d’an shege.

Deleted ta danna tana kuma jan dogon tsaki tare da kallon jawahid da ke gefenta ta ce”Wlh y’an gidanmu basuyi ba Ina son social media amma sun tusoni gaba sunki barina na yi rawar gaban hantsina kina gani fa idan nayi posting a take ya ke zuwa viral comment din da nake sha ba na wasa ba ne amma saina sauke”

ta karasa fad’a tamkar zata fashe da kuka saboda tsabar takaici.

Wacce ta kira ta jawahid ta bata amsa da.

“ki hakura da social media dinnan Ayda tunda kowa na gidanku baya so sannan Faruq ma kinga dagun da kuke sha Akan hakan kuma ni kaina bana ganin laifin Faruq ta wannan bangaren saboda ko ni namiji ne haka Zanyi Ayda kina da kyan da ko mace ta kalleki sau d’aya sai ta kuma kallonki Toh me zaisa bazasu killaceki ba “

Tura Baki gaba tayi ta na mikewa ta ce”nasan ai haka sakice saboda ke social media daman bata gabanki “itama mikewar tayi ta na gyara tsayuwar handbag dinta ta ce “gaskiya na ke fad’a maki mace mai mutunci da tarbiya bata tallar kanta a duniya kin kasa gane ba mutuncinki ba ne “

“Ni dai naji dad’in abun baki isa kimun wa’azi ba Boko tare islamiya tare gudun hadda tare yanzu ma gudun lectures tare kinga baki fini ta nan ba”

Dariya mai sauti jawahid tayi tare da cewa “Kinsan dai nafiki jin wa’azi dai ko?Harara ta bi ta dashi tare da maida kallonta ga makekiyar motar da ta faka gaban parking space din restaurant d’in Tana rejecting sabon kiran da ke shigowa wanda sunan waziri ya bayyana ga screen din wayar.

“Toh fa kamar motar waziri nake gani “cewar jawahid “Ayda na tsatsare gira ta ce “Eh jiya ya dawo saura ki sakar masa fuska ki na masa dariyar nan taki da kika saba ya dauki kansa wani shege “

“Sai shegen girman kai wlh ki rage izzar nan tunda kede ba saraki ba ce bare a ce bazata dainu ba “Kin kulata Ayda tayi saboda suna gab da motar da kansa ya fito tare zagayowa ya bude mata daga kallon gayen kaga jinin sarauta saidai akwai nuna karyar kudi a yayinda jawahid ta shiga gidan baya ta na cewa.

“Saraki manya Waziri yau kune a kasar’”Murmushin ya yi ya na bin Ayda da mayataccen kallo mai Cike da so da kauna Wanda ta Kauda Kai ta na yatsina fuska ya ce “saukata kasar jiya na amsa kiran gimbiya kinsan ko daga Chan maracco ta ke son gani na dole na bar kome nake ta taho”

“Haba Babe duba time fa driver na jira na a school salon ya tafi Ummy tayi fad’a “Sorry gimbiya tuba na ke kinsan na dawo ne Cike da kewar ki kinga ko dole na tsaya na karewa kyakyawar fuskar nan kallo “

“tab’e Baki tayi ta na kauda kai a ranta ta ce shegen zuba kamar radio da wani hancinsa kamar na bunsuru”Jan motar Yayi Yayinda ta juya ta kalli jawahid ta ce.

“Don Allah mu wuce gidanmu tare nasan Mamy ba ta dawo ba su aunty hasana kuma hidimar biki suna gyaran jiki na San waccen alhudu-hudun kuma nasan bata missing lectures ko d’aya yau sai an ganta ”

Dariya Jawahid tayi tare da cewa”kin Raina mufedah wlh ba zan biki ba gaskiya Abbana na gida fad’a zaiyi na fada musu yau ai da wuri zan dawo ki Bari next time na je”

“Ta na had’e fuska ta ce “naji zan Rama kema sai ranar da momy bata nan Abba baya nan Kice na rakaki “

”Toh ai babe idan munje ba tafiya zanyi ba zan iya jiranki ma har su ummyn su dawo kinsan nayi kewarki da yawa “”Cewar waziri da ya tsoma musu baki jawahid ta ce”shikenanma waziri ka fansheni”Ayda ta ce “Driver ai zai karasa da ni gida”Ai gidan zan biku “ya fad’a Kai tsaye ta gefe ta Galla mai harara ba tare da ya gani ba.

Alqalam university Kai tsaye suka nufa inda suka saba parking ya tsaya Wanda nan ta hango driver ta sa Yayi parking nesa dashi kafin suyi sallama da niyyar zasuyi waya suka nufi driver suna hira ba tare da ta Bari ya ga an sauke ta ba inda jawahid ke cewa”Nima driver ki zai saukeni gida yau ban fito da mota ba”.

Koda isarsu gida bayan sauke jawahid a gidansu kasantuwar ba nisa tsakaninsu Chan ta samu waziri harabar gidan bata biye masa ya jata da hira ba ta sallamesa don a gajiye ta ke.

Sosai na karewa gidan kallo ya had’u ba k’arya tankamamen gida ne mai matukar girman gaske sai shukoki da ke matukar daukar hankali alamun suna matuk’ar Shan gyara,komai ya yi kama da na manyan masu kud’i domin bene ma kanshi hawa biyu ne sai wani tsararren flat part da ke gefen hagu kusan sai ince ni ya ma fi yimun kyau da d’aukar ido domin wasu irin kawatatun shukokine suke zagaye da gidan ga fentin part din kanshi kamar yau akayi sa decoration din b’angaren ma na musamman ne domin sai a tsirarrun gidajen masu kud’i aka fiya samun irin hakan domin wasu irin glass-glass din da aka kawata part dinma kad’ai abun kallo ne.

ba Wanda ta samu a palour hakan ya sanyata saurin haurawa sama tare da bude bedroom Dinsu ta shige,

rage Kayan jikinta tayi tare da fad’awa toilet ta yi Wanka salla tayi tare da sanya kananun Kaya masu taushi kasantuwar yanayin zafin garin alamun hadari ne dukda sanyin ac da ke ratsata.

hayewa gado tayi tare da janyo wayarta ganin missed call Din yaya Faruq sama da ashirin ne kuma duk kusan tattare saboda ta bar wayar silent ya sanya gabanta fad’uwa idan ka ga ya na mata irin wannan kiran to da dalili ga bacci ne a idonta dukda yamma ta yi sosai,

kashe wayar tayi tare da tashi ta sanyawa dak’inta key ta san zai iya biyota nan d’inma ba tsira tayi ba ga ba kowa a gidan ga shi bata San ta’kamaimai laifin da tayi masa ba don tasan tabbas kirannan idan tayi laifi yake yi mata.

k’ara gudun ac tayi kafin ta koma gado ta kwanta ta na kashe wayarta gaba d’aya don gwara tayi bacci koma me zai mata ya mata bayan ta huta.

Ba jimawa bacci me dadi ya dauk’eta Wanda barcinta har ya fara nisa cikin bacci take jin buga k’ofar da karfi Cike da masifa ta tsinkayi muryarsa da cewa “wallahi Ko ki bude kofar da kanki ko kuma in b’allata da kaina na shigo na ci uwarki second hamsin na Baki………..✍🏾

Toh fa ya kukaji salon🧐mu hade a comment section idan na ji comment din da ya gamsheni gobe zaku jini Insha Allah idan na jiku shiru Nima zaku jini shiru🙅🏾‍♀️

07026166536 domin Neman Karin bayani ko shiga group🪱

Share fisabillah🦇🦅

_*Miss hajo ce*_✍🏾



♠️♣️ *MATAR UNCLE*♣️♠️



```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*

(Miss Hajo✍🏾)

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Marubuciyar*

👇🏾

Auren wata Tara

Ni da yaya arman

Khadijatul sabren

Ribar so

Najmat abiy

Mata tace

Komai mukaddari ne

And now

*MATAR UNCLE*

🅿️……………………….*2*

Cikin Dakiya Ayda ta tashi duk da yanda gabanta ke faduwa hakan bai hanata aro jarumta ba wajen hade fuska tamau ta na mikewa ta nufi kofar tare da budewa saurin ja baya tayi ganin yanda ya fado dak’in kamar wani zaki

“Da uban waye kike waya jiya har karfe d’ayan dare?Daram gabanta ya bada cikin zuciyarta tace “Toh amma waya fada masa bayan jiyan da nake waya Banga missed call dinsa ba wata zuciyar ta bata amsa da cewa “tabbas sauya layi ya yi ya dinga kiranta don lokacin ta ga wata number na kiranta!

“Zan daukeki da Mari Ina miki magana kin tsareni da wannan shaggun idanun naki kamar na mage “ya fad’a a zafafe!

kamar mai Shirin fashewa da kuka ta ce “Yaya faruq Jawahid ce fa ba wani ba”

Kallon Kin Raina mun hankali ya yi tare da nufota gadan gadan da niyyar dauketa da Mari ta yi baya tare da fadawa gado Tana kife kanta da gwuiwa ta sa kuka don tasan yau me rabata da shi sai Allah tunda ummi bata nan ba kowa gidan dole ta lallab’asa su rabu lafiya cikin kuka ta ce “Don Allah yaya faruq karka dakeni ka ga ummi ta hanaka dukana”

Cike da masifa ya ce”bani wayar ki”bata San sanda ta d’ago ba tare da zazzare ido alamun rashin gaskiya ta ce.

“Wayata kuma yay…..”Eh wayarki don ubanki ba ni kafin na sauya maki kamanni cikin kakkarwa ta janyo wayar tare da mik’a masa ya amsa,

ganin hankalinshi na kan wayar ya sanyata saurin rugawa a guje tayi waje da gudu daidai lokacin ummi na shigowa,

Da gudu ta ruga tare da boyewa bayan ummi Tana sauke wahalalliyar ajiyar zuciya”Lafiya Ayda meya faru na ganki haka a firgice?”

Kafin Ayda ta bata amsa ta hango faruq na saukowa daga sama cikin bala’i fuskarsa har ta sauya Kala ya nufosu ummi ta kareta ta na had’e fuska tamau ta ce “me kuma ta maka yau ?Bai ba ummi amsa ba sai mik’a mata wayar ya yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login