Showing 12001 words to 15000 words out of 44977 words
Chapter 5 - MATAR UNCLE BOOK COMPLETE BY MISS HAJO.docx
ban iya ba ai da na soyawa umborn dinmu"harara ta dalla mata ta ce "zaki iya a gidan miji ai uwar son jiki ni daman ba ke na ce ba "dariya Noor ta yi ta ce"Ai kam dole mu tashi muyi aikin d'anmu ko y'armu aunty khadija wata nawa ne"da harara ta bisu tare da cewa "bansani ba nidai don allah kuyimun kafin baby ya zo daukata" Ayda ta ce"baby habu ai ko yazo dole ya jira aikin dansa"Pillow ta buga mata ta ce"marar kunya zamu had'e watanki kusan guda rabonki da gidana"wlh aunty khadija makaranta nima ina son zuwa ita ke hanawa"ta na nufar kofa ta ce"da anyi magana kice makaranta sai kace karatun take"domin itama Alqalam din ta ke Level 4 saura 3months ta gama.
Ana saura kwana hud’u a fara biki Kanwar ummi mai biya mata da ke aure a kaduna wacce suke kiranta da mami ta zo daga ita sai babban D’anta Abdallah mai kusan 30years itama Yaranta hudu ukku maza mace d’aya Halimatu suna ce mata Amna tayi mata aure kasuntuwar ba kasar suke zaune da mijinta ba yasa bata samu zuwa ba D’ayan kuma muhammad yana karatu a london yana da 27 years sai autanta Sadeq mai 16years shi kuma ba na zaiyi candy kasancewar yana zana waec ta Hana sa zuwa tunda ta zo gidan ya Kara rikicewa don Badai kaud’in magana ba idan Tana magana daga nesa ma sai ka jiyota ga wasa da dariya saidai ita akwai fad’a idan ka tabota bata da hakurin ummi Sam Ayda na gefenta faruq ya shigo dawowarshi daga wajen Aiki kenan da sallama a bakinsa saidai fuska hade “Oh ni zulaihatu faruq daman kana k’asar ko nemanmu bakayi ko a waya”yana zama daya daga cikin kujerun palourn ya ce”kinzo zaki fara mitar ai kya tsaya ma mu gaisa tsufa yana Neman ma ya kamaki wlh Ina yini anzo lfy ya hanya”ya fada a jere”A a mutuwa nayi na dawo karewar tsufa marar kunya”Yar dariya ya yi ya ce “Allah huci zuciyar mami”kafin ya mai da kallonsa ga sauran duka ya gaishesu suka amsa Cike da kulawa Tare da tambayarsa wajen aiki ummi ya kalla da ke harararsa ya ce”Ina yini Hajiyarmu maganin kukanmu “ba wani zak’in baki da zakamun ka gama zagayen zagayen yanzu ai mun had’e ai kasan nace maka karkazo bada wayar nan ba”ya na ciro wayar a aljihunsa ya ce”ni na isa na sab’a umarnin uwar manya da yara ga ta Allah huci zuciyarki “ya fada ya na Mika mata nauyayyar ajiyar zuciya a boye Ayda Ta sauke ta tsura masa ido Wanda sai a sannan ya kalleta ya ce”ga wayar nan na yarda kici gaba da rikewa na saka miki sabon sim amma wlh na Kara kamaki da laifi makammancin wancen saina miki karaya hudu na baki ruwan sanyi kin kasa doruwa sannan karki kuma saka security koda yaushe kuma zan amsa wayar nayi duk binciken da ya kamata fatan kinji abunda na fada maki”?!
Jiki sanyaye ta gyada kai momy ta bisa da hararar takaici tare da Jan siririn tsaki Wanda kowa saida yaji faruq ya Taba baki ya ce “oho dai kinji abunda na fada maki”Mami ta katsesa da waye ohon”ni dai ba da kowa nake ba kinga karki jamum”Aunty Laila ta ce”ai shiyasa mukayi shiru ubanta na bata umarni wa zaisa baki”Batare da ya kalleta ba ya ce
”ku kuke jan yara su Raina mutane wlh”aunty Laila ta ce “ka ga ba rashin kunya nace ka mana ba kunfi kusa ya wajen su yaya”ya ce”yana Abuja amma gobe zai dawo ya ce nan zai fara biyowa ma kafin ya kalli Ayda ya ce ki sameni a mota minti biyar sauri nake saura ki batamun lokaci “
“Cikin sauri ta ce”Toh”Momy kamar ta shaketa yana barin palourn ta dalla mata harara ta ce”sakarai da kika rako mata sai ki tashi ki bishi”tura Baki gaba tayi tare da bin bayansa momy ji take kamar ta hadiya zuciya ummi ta ce”ki rage nuna kiyayyar nan a fili Amera ba kyau”
mikewa tayi kamar tasa kuka ta ce”Wallahi ummi bazata tab’a Auren faruq ba muddin kuma Ta auri faruq wlh ba ni ba ita har gaba da abada saidai ta chanza wata uwar amma Tana Auren faruq na sallama masa ita tunda na fada ba sau d’aya ba sau biyu a daina barinta zance ummi kin kasa fahimtata ai shikenan”!
bata jira me ma zasu ce ba tabar palourn ummi ta ce “kiyayyar nan ta amera da Habiba yarinyar nan kafiya ne da ita taki manta abunda ya wuce”mami ta ce”ni fa Banga laifin amera ba wlh duk abunda ta yi ta na gaskiya ai ko ni indai ina mumfashi saidai wani ikon na ubangiji zai sanya ta auri faruq Aunty Laila ta ce”gaskiya kam Allah musu zabi mafi alkhairi”suka amsa da amen”suna jinjina yanda ummi take son nuna kamar komai bai faru ba.
Abdallah da ke farfajiyar gidan idonshi Akan ayda yanda suke zancen gab da gab ya girgiza Kai tare da tab’e baki ya ci gaba Da kiran Noor da yake jira su fito ita da mufedah suyi hira don tunda kiri-kiri Ayda tace bata sonsa faruq take so ya fita sabgarta”Kallon yanda suke zance Mufedah tayi tare da aniyar yau saita mata Tatas ko kuma tace zata fadawa ummi don dukda dan uwanta ne bai dace yanda suke shigewa juna sai anyi magana tace yayantane
Koda ta gama zancenta ta gaban su Abdallah ta wuce ya bita da harara Mufedah ta kallesa ta ce “yaya wai har yanzu baku magana”Fuska hade ya ce “bata da kunya ai ni zan fara gaishe ta ne?Kai ta girgiza ta ce “amma ai yaya ta gaisheka ba tun ranar da kukazo “Noor ta sanya dariya ta ce”Yaya Abdallah kodai duk kishin ne ”ya na watsa mata harara ya ce “zamu b’ata da ke Noor ni sa’ankine “cikin sauri ta girgiza Kai ta ce”yi hakuri”ya ce “muje maganarmu kiramun Fatima “Ta na d’agowa ta kallesa ta ce”Toh yaya ba kuna waya ba”Ya girgiza Kai ya ce “Fad’a nayi mata Ta ji haushi ta yi blocking d’ina”Murmushi noor ta yi ta na lalubo number Fatima ta ce”Yaya Fatima ai ba a mata fad’a ko momy tayi mata sai ta shafe wata ba ta Kira ta ba saidai ita ta kirata”Abdallah ya ce”ikon Allah Ashe haka abun yake “
Ta na dauka noor ta ce “yaya fatima yaya Abdallah ya ce na koraki za ku gaisa”cikin alamun gigin bacci ta ce”Waye haka”Ya na amsar wayar ya ce”Ni ne”Ta ce”ohh sorry Bro ya kake”ya ce”ki cireni a blacklist zamuyi magana “ta ce”okay”mik’awa Noor wayar yayi minti biyu ba ayi na sai ga shi ta kirasa da kanta ya kalli noor da mufeda ya ce”Toh ku tashi zanyi waya “Mufeda ta ce”shikenan Amfaninmu ya gama ko”Noor ta ce”Ai zai nememu watarana ”
Ayda Koda ta shiga bata samu su ummi a palour ba Wanda hakan ke tabbatar mata da kila sun kwanta daman da gajiya a tare da ita ciki ta shige tare kwantawa abinta kafin wani bacci mai nauyi Yayi awo gaba da ita……✍️
*Barka da safiya*🏃🏿♂️
*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️
```MALLAKAR```
*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾
*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE
🅿️……………………….*7*
Washegari da sassafe ta na cikin Shirin tafiya school mufeda ta ce”wannan wani irin zance ne kuke ke da faruq Ayda to wlh ummi zan fad’awa tunda na fada maki bakiji ba “ko kallon ita ta ke Ayda batayi ba bare ta sa ran amsa saima ci gaba da shiryawarta da tayi ta tafi school ko break fast bata yi ba don bata son ta hadu da su momy “
Kallonta jawahid tayi bayan gama lectures ta ce “meya sameki wai duk naga kinyi sanyi”cikin basarwa ta ce “ba komai kaina ke ciwo muje yau gidanku na yi ma bazanje ko Ina ba “
har yamma ta na gidan su Jawahid don ta Kira ummi ta fada mata ta wuce chan mamansu mace mai matukar kirki da Kara ta hado ta da tsarabar turare Wanda duk lokacin da zata je tofa dole ne saita hadota da turare kafin ta ce “ki gaishe da Amera Kice ta kyauta har tazo garin ba ta nemeni ba”Ayda ta yi murmushi kafin ta ce”Insha Allah zan fada mata nasan ma momy zata zo may be Bari ta yi a gama hidimar biki”hakane ai ranar bikin ma munhad’u sai na leko”.
Ko da ta isa gida basu hadu da su momy ba dan sai bayan isha’i ta koma Allah yasa lokacin ma su suna jeren Kayan d’akunan su hasana don dare sukayi
Washegari tunda safe Alhaji Bukar Abban faruq ya bayyana cikin girmamawa k’annen nasa suka gaggaisa dashi kafin ya zayyanawa Ummi abunda ya kawosa na son had’in d’aurin Auren Faruq da Ayda tare da na su hasana Wanda inma tarewarce daga baya sai ayi cikin hikima ummi ta nusar dashi akan kar ayi gaggawa bayan bikin su hasana anyi maganar daga baya Wanda ya amince da hakan Mommy ko wata b’oyayyiyar Ajiyar zuciya ta sauke a b’oye guduawar 1m yayiwa Ummi transfer sukayi godiya yabar gidan ranar kuma dangin mahaifin su hasana sukazo Daga kano aka had’u tare kamar y’an uwa aka cigaba da hidima!.
Washegari a kazo har gida akayi musu lalle da dare kuma suka je saloon,
B’angaren gidan su Faruq sosai Umma ta kasa ta tsare ta Hana su Raudat ko zuwa school saboda karma suje gidan bikin a sace kaf ta ce yaranta ba zasu halarci bikin ba kamar yanda bazatajeba don ta k’ara shaida musu matsayinta a wajen D’an uwan nasu kuma ba abunda aka isa ayi.
Yau alhamis gaba d’aya gidan da shiri na musamman ya tashi sosai momy da ummi suka tsaya tsayin daka wajen ganin anyiwa gidan gyara na musamman don sunyi waya da Adnan jirginsu ya taso awa ukku me kyau zasu sauka
a a gaggauce ake komai ko Ina na gidan saida ummi ta sa aka bi shi da daddadan turaren wutan Fati Ammani uwa uba part dinsa kafin kace me gidan ya kaude da wani irin ni imtaccen kamshi mai matukar Jan hankali an bannata turaren wuta kam don ummi tasan ba abunda Adnan yafi so da kauna kamar kamshi mutum me ma abucin kamshi da tsabta baya shiri da kazanta duk kankantarta saida suka tabbatar an gyara ko Ina na gidan kafin su soma Shirin tafiya tarbarsa don minti talatin ya rage musu”
Ayda da ke chattin ta yi daidai a gado Mufeda ta kalla bayan shigowarta ta ce”wai kina nufin Baki shirya ba driver fa har ya tada mota”Hankalinta na kan waya ta ce”ke ni fa ba inda zanje “
Mufeda ta ce”to saboda me”Saboda a gajiye nake ni karki dameni”tabe baki mufedah tayi ta ce”kinji da bakin halinki Uncle din da ya yi 10 years baya nan munma manta da shi ni da ke kuma zaizo muje tarbarsa Kice bakizuwa “
banza Ayda tayi mata bayan fitarta ta Tabe Baki ta ce”mutumin da ko damuwa baiyi da mutane ba ummi kawai yake waya da ita ko ambaka shi ma ku gaisa ya dinga maka magana kamar bayaso ba inda zanje”
Kallon Mufedah ummi da momy sukayi kusan a tare suka ce “Ina Aydar”mufeda ta ce “ta ce”Bata zuwa ta gaji”
momy ba ta Kara bi ta kansu na ta nufi dakin su Ayda samu tayi ta na waya a kwance ta na ganin momy ta ce”Yaya faruq zan kiraka minti biyu “Karki katsemun waya “Ya fada a zafafe”bata katse kiran ba sai cire wayar da tayi a kunne ta na kasa da kanta ganin irin banzan kallon da momy ke mata kafin ta ce.
”me ya hanaki shiryawa mu tafi taryar Adnan ”cikin rauni ta ce”momy na gaji ne shiyasa da naga duk zaku je ai ya wadatar”bai wadatarba cikakken minti biyar kika Kara ranki sai Yayi mugun b’aci tashi ki shirya mu tafi “kamar zata sa kuka ta ce “Toh”
momy na fita ta mai da wayar rai bace ya ce”Inajin me tace Toh bazakije ba ai tun jiya na fada maki bazakije ba”Hawaye na zuba daga idanunta cikin sanyi ta ce”don Allah yaya faruq ka Bari naje kar momy tayi fushi da ni”Akan bakije ba zatayi fushi da ke?To bazaki ba sai inga umarnin wanda ya Dace ki bi” mahaifiyatace fa”?mahaifiyar taki ai aljannarki ba a karkashin kafarta take ba ni da zaki aura aljannarki take hannuna kuma na fita iko a kanki kuma na ce karkije kuma wlh kije ki ga abunda zan miki tunda baki da kunya”
“Toh shikenan na hakura da zuwa “ta fada gabanta na matukar faduwar tsoron momy k’in kashe wayar yayi minti goma sha biyar momy ta dawo ba karamun baci ranta yayi ba samun Ayda yanda ta barta bata san lokacin da bacin rai ya debeta ba ta wanke ta da mari cikin b’acin rai ta ce .
“tsabar rainin da ke tsakaninmu har yakai haka daman ban sani ba na Baki umarni na dawo na sameki yanda na barki kafin ta kwace wayar ta fasa a take Tana nuna ta da yatsa ta ce”kuma wlh na dawo na sameki Baki shirya ba kiga irin bacin dan da zaki fuskanta “
Ayda bata San sanda ta sanya kuka ba Tana durkushewa a wajen sosai zafin marin ya shige ta tare da zafin fasa wayar cikin kuka ta tashi ta shirya ta na sanya abaya doguwa blue tayi roalling gyalen har lokacin kuka take kamar zata tashi sama ta sauko lokacin duk suna parking space don mota biyu ma har sunyi gaba Wanda ya rage momy da ummi sai Mamy da aunty laila ne zasu shiga ta shiga inda suka shiga Yiwa momy fad’an me yasa zata mata irin wannan marin gashi sawu har ya fito ran ummi sosai ya b’aci ta ce”
“meye kike haka amerah rakiyar dole ce ta ce ta gaji abunda ba dole ba fisabilillahi har kiyi mata irin wannan dukan meyasa kike haka “Momy da har lokacin bata sauko ba ta ce”Dole ce kuwa ummi idan ita bata San mahimmancin muhammad Ali ga rayuwata da Tata ba ke ai kin sani “Daga mata hannu ummi ta yi ta ce”Bai zama dole ba bana son cin zali Sarai kin sani yimun shiru da Allah “
kafin ta koma kallanta ga Ayda da har lokacin kuka take saida suka isa airport kafin ta daina kukan sai shasheka amma kallo d’aya zaka mata kasan ta ci kuka ta gode Allah bata kula kowa ba ko a wajen sosai ta shaku rai bace taja ta tsaya ta na karajin zafin abunda momy tayi mata minti biyar basuyi da zuwa ba jirgi na sauka lumshe ido ummi ta yi ta na Jin wani dadi na ratsa ta ji take tamkar a makafarki haka momy da take Jin kamar ta shiga cikin jirgin ta fito da mutumin mafi daraja da mahimmanci da ya taka huhimmiyar rawa a rayuwarta da ta y’arta.
kallon mutanen da ke saukowa kawai suke Wanda Allah Allah suke su hango sa.
A hankali ya ke taka matattakalar jirgin tare da lumshe ido kafin ya bude a hankali yana shakar daddad’an iskan da ke kadawa ga mahaifar tasa wata natsuwa ce ta dirar masa lokaci guda kafin ya karasa saukowa cikin wani irin fitinannen taku mai matukar Jan hankali “YAH ALLAH” Noor ta furta cin karo da kyakyawar halittar da saida numfashinta ya dauke na y’an dak’ik’u kafin tadawo hayyacinta ”Daman Ana samun namijin novel a zahiri “Cewar noor mufeda da ke gefenta ta ce “ “ga zahiri kingani “Noor ta ce”Daman Uncle Balarabe ne da gaske ashe da momy ta fad’amun”
sanye yake cikin kanunun kaya da sukayi masa masifar kyau ba hula a kansa sai gashinsa da yasha gyara hade da kasumabarsa da itace Abu mafi kallo da ta Kara kawata baiwar kyawun da Allah Yayi masa lumshe ido ya sake a karo na biyu kafin idanunsa ya sauka ga mutane mafi mahimmanci a rayuwarsa bai tab’a Jin yayi kewar mahaifiyarsa da ahalin nasa ba kamar yau karon farko tun bayan shekara goma da yayi murmushi tare da ware hannayensa ganin ummi ta nufo sa wata irin runguma tayi masa kamar zata maidashi ciki a yayinda shima Yayi mata irin natan
wata irin kewa da soyayya da kaunar mahaifiyartasa ce ta bijiro masa baisan lokacin da wasu hawaye masu d’umi suka zubo masa suka sauka Akan fuskar ummi da ta dago domin ta Kara gaskata ba mafarki take ba Muhammad Ali dinta ne yadawo shine rungume jikinta”
girgiza masa Kai tayi itama hawayen take tare da goge masa ta ce”bana son zubar hawayenka Adnan yau ranace ta farinciki a garemu da ahalinmu baki d’aya “
“ummi ki yafe mun”ya fad’a cikin zazzakar muryarsa mai Kama da busawar sarewa
Ayda da har lokacin a Cike take fam ko inda suke bata kalla ba sai sararin samaniya da ta tsurawa ido tana hango yanda duk sauran wanda sukazo tare suka nufesu kowa na masa sannu da zuwa.
Da nuna zallar farincikin dawowarsa momy ma rungumesa tayi Cike da zallar farinciki lurar da nayi kaf wajen yafi shakuwa da momy haka duk ya gaggaisa da yan uwansa.
ganin ya na waige waige ne ya sanya ummi yin murmushi tare da cewa”D’iyarka kake nema ko”shiru Yayi baice komai ba Wanda ummi tasan ita din yake nema maida kallonta ta yi ga Ayda Da ke zaune jikin wani dakali ta ce”Ka ganta chan shalelenka ta girma Adnan“! Kallonsa ya maida ga inda ummi ta nuna masa……………✍🏾
*Domin Neman Karin bayani ko shiga grp 07026166536*
*Idan kin karanta ki daure kiyi sharing sauran grps please*
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
♠️♣️ *MATAR UNCLE*♣️♠️