Showing 3001 words to 6000 words out of 44977 words

Chapter 2 - MATAR UNCLE BOOK COMPLETE BY MISS HAJO.docx

11 Aug 2025

1455

tare da cewa,

“Bud’e securityn munafuka saboda tsabar rashin gaskiya shiyasa kika sauya bud’e Toh kafin wlh na sassauya miki halittu yanda ko naman daji bazasuyi sha’awar cin ki ba”

Kuka ta sanya tare da makalewa bayan ummi ta ce”Don Allah yaya faruq kayi hakuri ni wlh ba da saurayi nake waya ba na fad’a maka jawahid ce “

“Uwar jawahid don uwarki D’an iska zaki maidani ki shafe sama da awa d’aya da rabi kina waya kice mun wata jawahid don kin d’aukeni sakarai ”

“Faruq faruq faruq”Sau nawa na Kira sunanka?

Ummi ta fada da ranta ya soma b’aci don ta gaji da masifar faruq Akan Ayda “ummi don Allah karki shiga maganar nan ki barni da ita’”

Anki a barka da itan nace anki a barka da ita ko haihuwarta kayi”ko ko auren ta ka ke?.

“Ni mijinta ne tunda ba ta da wani miji a duniya bayan ni don haka dole in dinga bibiyar rayuwarta wlh ummi yarinyar nan cin amanata take samari take tarawa kawai ta maidani sakarai tun farko sai da na ce ban yarda Ayda ta shiga university ba amma kuka nace nace a bani matata na sakata karatun bayan munyi aure amma kuka k’iya to bazan yarda ba sai ta bar school dinnnan tunda duk ita ta ke Kara bude mata ido kuma ni kawai na gaji a azo a d’aura mana aure kawai!

Wani banzan kallo ummi ta watsa masa tare da cewa”da Allah wuce ka ba mutane guri marar kunyar gida kawai ai dai ka Bari a d’aura tukwana ta zama matar taka da Baka da aiki kullum sai fad’a da mace Akan saurayi kaji kunya wlh har bakasan yanda zakayi ka janye hankalinta ta daina kule kulen samarin,ko angaya maka wannan hayayagar da zafin ran da kake shi zaisa ta daina abunda ta ke wai ma haka ake soyayya!faruq?

“toh idan Baka sani ba ka sani ita mace tamkar kid’a ce bazata tab’a Baka dad’in sauti ba sai ka San yanda ake buga kid’anta a kwakwalwar zuciyarta mace bata son hantara da kyara daga wajen masoyinta bare har akai ga duka Faruq kar ka fusatani na yi abunda ranka zai b’aci wlh ka k’ara Kai hannunka jikin Ayda da niyyar duka ko kaine Autan maza bazaka aure ta ba tunda kai na lura kullum abunka k’ara gaba yake ba baya ba “

”kamar zai tashi sama ba tare da ya tankawa ummi Kala ba ya nufi kofa kuka Ayda ta sa ta ce”Ummi waya ta”Keda ita har abada”ya fada yana barin gidan gaba d’aya sabon tashin hankali bata San sanda ta durkushe ba tare da sanya kuka Tsaki ummi ta ja ta na mai Kama hannunta ta ce,

“rabu dashi sai ya maido maki wayar da ni yake zancen wannan wace irin soyayya ce ni Maryama “ummi ta fada ta na zama d’aya daga cikin tsadaddun kujerun palourn

”Ayda na ci gaba da kukan tab’ara tare da diddira kafa ta ce”Ummi ni dai wlh ki amso mun wayata “ta na shafa bayanta ta ce “Bar kukan shalelen ummi alkawari nayi maki fa sai ya dawo da wayar bana son kukanki ai kin sani kinci abinci?Tana shashekar kuka ta girgiza Kai”Maid din su ta kwalawa Kira tare da umartarta da ta zubo mata abinci da kanta ummi ta dinga bata abincin don tasan ta barta ba ci zatayi ba saida ta tabbatar ta lallasheta tabar kukan kafin ta ce”ya naji gidan shiru ba kowa “

mufedah na School aunty Hasana da Husaina kuma suna wajen gyaran jiki”Nauyayyar ajiyar zuciya ummi ta sauke sai a sannan Ayda ta ce”ummi ya hanya”Ta na cire hijabin jikinta ta ce “Alhamdulillah suna ta tambayarku”Ai ummi na so in rakaki Daurar school ta Hana”ai za su zo biki duk zaku gaggansu dama ke da Mufedah ce Baku sansu sosai ba “zanje ciki na yi wanka saura ki ci gaba da kukan kanki ya yi ciwo a banza”

Ummi na shiga ciki Mufedah na dawowa daga school sai a sannan Ayda taji sanyi ganin Mufedah tadawo ko zama Mufedah bata gaama ba Ayda da damuwa a fuskarta ta ce “Mufedah yaya Faruq ya amshe wayata don Allah ta ya zaki amsomun”Tabe Baki Mufedah tayi ta ce “Again marar aikinyi ni ai kinsan ba shiga hurumin Marar mutuncin nan nake ba”

b’ata rai Ayda tayi na tura Baki gaba ta ce “Ni dai bance ki aibantamunshi ba a haka nake son Kaya na”Tsaki Mufedah ta ja ta ce”Ai kunfi kusa sai ki bishi ki amso ni kinsan bana shiga sabgarki da yaya faruq tunda kika kunyatani ya nakada miki shegen duka daga na fadawa Abbansa don ya masa fad’a a taimaka maki kar ayi Auren ya kasheki haushin ya masa fad’a ya zazzageki ya daina maki magana kikazo kina Gaba Dani hada kuka ina ruwana duk Kin manta da wannan shi ne yanzu zakizo ki kuma sakani ba ruwana kunfi kusa “‘

“ni dai wannan ya wuce aramun wayarki”mika mata ta yi ba musu tare da tashi tana takaicin wannan sakaryar soyayyar da Ayda keyiwa yaya faruq Wanda ta tabbatar ko Auren akayi a zuciyar faruq kasheta ma yana iya yi tun ta na gidansu ya mai da ita kamar jakarsa donma ummi ta na taka masa burki Ina ga anyi Auren in Banda so so ne me ma Ayda zatayi da faruq shi da ba wani kyau ba sai masifa donma ba laifi ya na da maganai amma yarinyar da tayi fice a kaf zuri’ar familyn su uwa da uba ba me kyanta amma ta tsaya faruq na bata wahala da zancen zucin wannan ta koma ciki a yayinda Ayda ta sanya number faruq don tasan bai da number Mufedah

ringing ukku ya daga Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke a yayinda ta kasa magana sai lumshe ido da tayi ta na sauraron Amon muryarsa da yake cewa”Helo helo “Kasa magana ta yi haka bata katse kiran ba “uban Waye idan ba ayi magana ba zan kashe “

A ranta ta ce”shi komai zagi yayinda a fili cikin narkar da murya kamar zata saka kuka ta ce”Yaya Faruq don Allah ka yi hakuri ka yafemun wlh bazan sake ba na daina sab’a umarnin ka”

Dogon tsaki ya ja jin muryarta ce dan har yanzu bai huce ba ya ce”idan har kina son in huce sai kin ciremun securityn wayarki na ga da wa kike waya da wa kike chatting sa’annan “Daram gabanta ya bada tasan ko giyar wake ta sha bazata fada masa securitynta ba ai Tana daga masa kashinta ya bushe kashe ta ma kawai zaiyi “

“Bakya jina kikayimun shiru “?Uhmm yaya”Ranshi na Kara harzuk’a ya ce”bazaki fad’a ba “nan ma shiru tayi dogon tsaki ya ja tare da cewa”Daga yau karki kara kirana munafuka maciya amana Kuma wlh kinji na rantse dole sai na aure ki kuma dole sai kin rabu da y’an iskan samarin nan tare za ayi bikinmu da na su y’an biyu kuma inga ubanda ya isa ya Hana”

Ya na gama fad’ar haka ya katse wayar”sosai hankalinta ya Kara tashi ta sani ta na kaunar faruq amma Allah ya sani ba ta shirya aure yanzu ba a Karancin shekarunta 19, tasan ma abune da baxaiyu ba kuma ita dai bazata iya kin daina kula samari ba saboda a wajensu take samun kulawar da ya Gaza bata always tsakaninta dashi zagi duka fad’a ba tausayawa ba lafuzza masu dad’i amma dukda hakan tana matukar kaunarsa kuma Insha Allah shi zata aura amma fa ba yanzu ba ita ba ta shiryawa kanta tunkarar rayuwar Aure yanzu da wannan tunanin ta nufi bedroom d’insu ,.

Bangaren faruq kuwa Wani irin kallon banza Umma ta watsa masa bayan gama jero musu bayaninsa na yanason a had’e aurensa da Ayda da su hussaina ta d’aga baki kenan zatayi magana Abbansa ya dakatar da ita ta hanyar kallonsa tare da cewa.

“zanje na samu Maryamar muyi magana idan hakan zaiyu ai ba damuwa ba ce kar kasa komai a ranka Maryam mallakinka ce domin ba ta da wani mad’aurin Aure a duniya bayan ni nikuma bani da wanda zan d’aurawa Aure da ita bayan kai my son “

ya na gama fad’ar haka ya fice daga parlourn yana haurawa sama umma ko har huci take abunka ga manyan matan nan jibga -jibga da dakyal suke tafiya magana ma anayi Ana huci tamkar zata haushi da duka ta ce”

”Sakarai wawa marar sanin ciwon kai ka rasa yarinyar da zakaso sai shegiya marar asali idan ka aureta y’ay’anku sun tambayeka ka nuna musu kakansu da ya haifi uwarsu ka ce me?so kake ka gurb’atamun zuri’a da jinin zina Toh wallahi ka ji na rantse ba ka isa ka watsamun zuri’a ba Idan Aure kake so ga y’ay’an abokai na nan y’ay’an masu kud’i ka zab’a d’aya daga ciki amma Yarinyar nan ko da lu’u-lu’u da zunare da azurfa aka k’erata haramiyarka shege sai shegiya d’an halak sai d’an halak….✍️

*Idan naji comment sama da 300 gobe da safe zakuji bonus*🙇🏼‍♀️

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️



```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*

Miss Hajo✍🏾

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Marubuciyar*

👇🏾

Auren wata Tara

Ni da yaya arman

Khadijatul sabren

Ribar so

Najmat abiy

Mata tace

Komai mukaddari ne

And now

MATAR UNCLE

🅿️……………………….*3*

“Ni fa Umma ba ruwana da wani halascinta ko haramcinta ko ma meye ce nidai Ina son ta kuma Aurenta zanyi “ya na gama fad’ar haka ya wucewarshi ya barta tsaye ta na cigaba da zirfa ruwan bala’i”

Ayda ko da ta koma bedroom dinsu samun Mufedah tayi ta na sallah saida ta gama kafin ta Mika mata wayar ta na zama gefen gado tare da rafka uban tagumi idanunta na zubar da hawaye.

Banza Mufedah ta yi ta kyaleta Wanda hakan sosai ya Kara sanyata damuwa a rayuwa ba abunda ta tsana kamar rashin waya da kuma yaya faruq ya yi fushi da ita Ina zata saka ranta ta Ina zai saurareta “

“mufedah don Allah ki ba ni shawara wata dabara zanyi ya fahimceni wlh nasan yanzu haka Ana ta kirana kuma ya na iya dauka kinga zarginsa zai zama gaskiya”

“Ni fa ba ni da tacewa Ayda kawai tunda ummi ta ce zata amso miki kiyi hakuri “Toh amma ta ya zai fahimceni ya hakura”Ta yanda yake so zakibi ki daina kula kowa tunda shine kawai babban damuwarki dashi “

“ni dai gaskiya bazan iya ba Mufedah idan na rabu da samari na wa zai dinga fitar da ni outing da wa zamu dinga zuwa Shan ice cream da sauransu kinsan yaya faruq duk baya mun wannan Abu kadan yace baida lokaci shi fa ko irin soyayyar nan ma baya nunamun sai nuna iko da isa su ko Wallahi lallabani suke kamar Kwai ke ai kinsani ji bi fa yanda nake juya manyan mutane idan waya na ce a rike mun saina bukata a Miko mun haka ake mun ji bi fa Waziri matsayin mahaifinsa a garinnan amma sai abunda nace yake Toh ta ya kike tunanin zan rabu da su ni dai na San so d’aya ne kuma yaya faruq nake Yiwa shi kawai ki ba ni wata shawarar”

“Toh kinsan da wannan kuma kika nace masa ya ke wahalar da ke wlh Ayda Ina tausaya maki Auren faruq don wlh duk saurayin da bai Kai ga aurenka ba yake yi maka haka Toh gaskiya bayan aure sai abunda Allah ya yi kalli fa yaya faruq ya maidake kamar jakar sa Abu kadan ya hauki da duka ko gaban Waye zagi ko kamar wata Sakarya ke ko kishin kanki bakyaji wlh darajar ki ta wuce hake ki dubi kanki fa a madubi Ayda Doguwa ce ke kyakyawa ta bugawa a jarida Diri ta Ina Allah ya rageki kaf family dinmu ba me kyan ki da haskenki jibi fa kalan fatar da Allah ya miki haskekenki har shuni_shuni yake idanunki tubarakallah masha Allah’ji karan hancinki dubi round face dinki Ayda Kalli dimple dinki uwa uba ga wushirya ta Ina Allah ya rageki tsawo jik’i daidai komai babu ta inda Allah ya rageki Waye zai kalleki ya ce haifaffiyar Nigeria ce amma kin tsaya zaki lalata kanki da kanki akan soyayyar banza da wofi kike fatan Auren mutumin da baisan darajarki ba bayan wlh kinfi k’arfinshi ta ko Ina kin tsaya ana wulakantaki ga mahaifiyarsa ba kaunarki take ba”

Shiru tayi ta na sauraron maganganun Mufedah ba don zatayi aiki da su ba ta ce “uhm”Ai nasan ba saurarata zakiyi ba don haka karki kara kawomun korafi Akan soyayyarku da yaya faruq ba ruwana “Allah Baki hakuri nidai mubar maganar”ta fada ta na kwanciya.

Washegari ko school ba ta je ba koda ummi ta tambayeta lafiya cewa tayi bakomai kallon aunty hasana tayi ta ce”Aunty hasana yau zan rakaku wajen gyaran jikin “To amaryar yaya faruq ko kema gyaran za Asoma maki”Dariya ta yi ta na rufe fuska tare da tashi ta ce”Bari na je na shirya koda ta fito har sun shirya direct wucewa sukayi hadadden wajen gyaran jikin don duk ta rage damuwa amma dukda haka da damuwa a ranta ita ma ko saida aka mata gyaran subhanallah zo kuga irin masifar Kyan da Ayda tayi kamar ka sace ka ruga ita kanta da ta kalli kanta a madubi tasan ta Kara masifar kyau kunsan kyau ya hadu da gyara aiko nan tace itama wlh bata yarda ba sai anyi mata na kwana ukku sanin rigimar Ayda ya sanya hasana da husaina biya mata itama ayi mata yayinda su kuma ake musu na wata guda Angon husaina ya maidasu gida ya na tsokanar Ayda ta na cinye musu abincin gida ta zama katuwa.

A Washegari tunda sassafe ta shirya kamar koda yaushe ta fi son shigar Abaya sosai tayi kyau cikin Egypt abaya dinta mai matukar tsada da kyau kasantuwarka ga Wanda Allah ya Yiwa hasken fata ita tayiwa rigar kyau ba wai rigar tayi mata kyau ba sosai ta haskata Abunka ga bak’in Abu ya had’u da farar halitta

Zaune ta samu ummi tare da kawayenta suna gagganin lefe gaishesu tayi tare da zama ta na daura kanta bisa kafadar ummi tare da cewa”Ummi na Ina kwana”Lfyqlau Autar ummi har anyi Shirin school din da sassafe yau za a fita”Gyada Kai tayi tare da cewa”yau 8 muke da lectures”to kinyi breakfast “?

Gyada Kai tare da tsokanar ummi da cewa”gaskiya ummi kafin biki sai nakaiki an gyara miki gashin nan naki furfura Yayi miki yawa kar ace umminmu ta tsofe “Dariya ummi ta yi ta na Kai mata dankwashin wasa ta ce “za ajimu fa takwara tashi kiban waje ja’ira “Dariya ta yi ta na mikewa tare da nufar hanya ta ce “Tunda kika haifi su Momy ai kingama tsufa “girgiza Kai tayi tare da murmushi “Dattijawan arziki abokan ummi sukayi dariya tare da cewa”ai da gaskiyarta shekara hamsin da biyar ai ba wasa ba donma Allah ya boye shekarunnamu ba acewa ma muntara manyan d’iya da jikoki”murmushi ummi ta yi a ranta ta na zancen zuci.

Kasantuwar ba waya a hannunta Kai tsaye gidan su jawahid ta ce driver ya sauketa a motar jawahid suka wuce school kwata kwata lectures dinma ba fahimtarta take ba 12 suka gama zasu shiga wata 4 daman kawayensu lectures daya suke su bazama yawo gari Ayda jawahid Khairat sai Ubaida su hudu ne dama group din nasu wanda tun daga secondary school suke tare dalilin amintarsu sukaki yarda a raba musu school kowa ta fadawa mahaifinta ga inda suke so kasantuwar abunda suke so iyayen ke so ba wani musu suka bisu da ra’ayinsu Sab’anin jawahid da kawancensu na daban ne don tun yarinta kowace makaranta tare sukayi sai cikon ta biyar d’in nasu Ruky itakuma y’ar zaria ce a nan Alqalam suka had’u karatu ya kawota a Sardauna Estate ta ke da zama sai 6 suka gama yawonsu sun dauki hanyar gida kenan Ayda ta kalli jawahid da ke driving ta na bin wakar Auta waziri tare da langabewa ta ce”Besty ba fa gida za ki sauke ni ba gidan su yaya faruq zaki rakani”

Wani banzan kallo ta watsa mata tare da cewa”Rashin sanin ciwon kan za aje a bazar ko?Tura Baki gaba tayi tare da cewa”Nidai kawai ki rakani don Allah karkice a a “Andaiji kunya wlh wai kamar ke namiji ke bawa wahala mtwswww ni wlh da ni nake da kyanki ai nafi karfin Faruq ya dinga wahalarwa Allah kyauta kilama asiri ya miki”

Ayda na hade fuska ta ce”nidai naji bance ki aibantamun shi ba rakiya kawai nace kimun ”Cike da takaici jawahid ta juya akalar motarta hanyar gidansu faruq Wanda tasan gidan sanadiyar Ayda don itace y’ar rakiyar biko duk lokacin da suka samu matsala haka zata tilastata ba don ta na so ba……..✍️

*Idan kin karanta kiyi sharing sauran grp please*🙏

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️



```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*

Miss Hajo✍🏾

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Marubuciyar*

👇🏾

Auren wata Tara

Ni da yaya arman

Khadijatul sabren

Ribar so

Najmat abiy

Mata tace

Komai mukaddari ne

And now

MATAR UNCLE

*Shafin nan naku ne kyauta Maryam Lolo,Halematuuuu,Maman saddik’a,Ruky Magaji,Asiya sani,Sopy mrs Haru,Alkhairin Allah ya Kai muku har gadon baccinku*

🅿️……………………….*4*

Horn sukayi mai gadi ya bude musu tangammemen get din gidan babban gida ne sosai saidai bai Kai na ummi kyau da girma ba.

Ba a son ran jawahid ba suka shiga cikin ainahin part din gidan don da cewa tayi ita ta jirata a mota ta mata magiya Akan ta rakata ciki da sallama a bakinsu babban palour ne na alfarma y’an mata ne su hud’u zaune kowacce da waya a hannunta karamar cikinsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login