Showing 21001 words to 24000 words out of 44977 words
Chapter 8 - MATAR UNCLE BOOK COMPLETE BY MISS HAJO.docx
zazzakar muryarsa mai matukar dad’in ji da sauraro “Lafiya qlau Adnan ya bak’unta “Bak’unta kuma aunty saikace wani bak’o”A a ai bak’on ne Wanda ya shekara goma baya gari yadawo ai yazama bak’o”
murmushi kawai ya yi da ke Kara bayyanar da kyawun halittar da Allah Yayi masa “Yanzu kuma saura Aure idan ba so kake ka zama Tuzurun karfi da yaji ba ko kuma mu Nemo maka ko a kauye “Haba Aunty har anyi haka Insha Allah za ayi Lokaci ne”
ta ce”Hmmm kullum haka kake cewa Allah kawo lokacin to”ya ce”Ameen”
Momy dai bata sa musu Baki ba tasan har yanzu fushi ya ke da ita Ayda na sauraronsu ta tab’e Baki a ranta ta ce”wannan ai ya wuce tuzuru sa’an momy ai ya zama tsoho amma fa ya fi momy ma Kyan jiki ji fatarsa kamar ba ta shiga rana tsabar hutu “
duk a cikin zuciyarta ta ke maganar nan koda isarsu Airport Ayda na shirin fita ya juyo tare da watsa mata wani irin kallo wanda ba shiri ta zauna Tana tura baki gaba tare da Jan tsoka a cikin ranta ta ce”
”ni fa wlh ba ka takuramun nida ba haihuwata kayi ba”sai kuma sannan ta kalli jikinta ta tuna ba ko gyale ta fito kallabin kanta ne kawai .
Yayi kamar minti goma da raka su momy kafin ta hango sa tamkar baya son ya taka k’asa haka yake taku cikin izza da takama fuskar nan ba alamar wasa kallon wasu y’an mata dake nunasa tayi kamar sunga wani jarumin Indian Film ta tab’e baki ta juya ganin ya na kokarin bud’e motar”
“Dawo gaba”
Ganin yanda ya yi maganar ba wasa ne ya sanyata fitowa kamar wacce kwai ya fashewa tare da yin yanda Ya ce”
Shiru ka ke Jin motar ba ka Jin sautin komai sai na “Al’qur’ani sautin Qiri’ar mahaifin nasa ya ke saurara har wani Lumshe idanu yake yana bi a hankali tamkar muryar da ya ke saurara koma fiye da haka”
Zuba masa idanu sosai Ayda tayi jin yanda ya ke bin karatun Alqur’ani mai girma Cikin nutsuwa ganin ya na nufar hanyar gida ne ya sanyata langabewa tare da cewa”Don Allah Uncle Gidan Aunty Khadija za ka saukeni”
Ba zaki ba”ganin yanda ya yi maganar ne ba wasa a tattare da shi ya sanya taJan bakinta tayi shiru”
SHizif d’inki nawa a Alqur’ani?Ta ji ya jefo mata tambayar”Kamar ba zata bashi amsa ba saboda haushin kin kaita gidan Aunty Khadija ta ce
“60”a tak’aice “zaki kawomun haddar 60 d’in ai don banga alamun hakan tattare da ke ba”
“Sosai cikinta ya kad’u harga Allah karshe karshen nan ba duka zata kawo da ba amma tasan kila fad’a ne ya yi “ta ce”Toh”
Ya na gama parking cikin sauri ta bar Motar ya bita da kallo har ta bacewa ganinsa kafin ya had’e Kansa da settearing mota ya yi minti biyar a haka kafin ya fito,
Kai tsaye part dinsa ya nufa yana zama d’aya daga cikin kujerun palourn tare da fito da wayarsa missed call ya gani barkatai na Abey kawai ya bi kiran bayan sun gama gaisawa yake tambayarsa ranar dawowarsa ya ce “sai lokacin da Ummi ta fad’a”Nusar dashi Yayi game da mahimmanci zaman sa a Qatar ya shaida masa Insha Allah ya gama abubuwan da yake zai dawo “Abey ya ce”Zahra ta ce mun idan ta kiraka ba ka dauka me yasa hakan Adnan “ya ce”ban kula ba ne Abba”ya ce”Toh don Allah ka kirata tunda ka ga maganar aurenku ta na nan jiran dawowarka kawai nake bangarena komai na gama shiryawa Allah muku albarka”ya amsa Ameen “
Kafin suyi sallama daidai kiran zahra na shigowa kyale wayar tayi ta gama ringing dinta kafin ya kashe wayar gaba d’aya ya na d’auko keypad d’insa tare da amsa kiran da ke shigowa”
“Kai yanzu Adnan ka kyauta kenan?Ka shafe kusan sati biyu a k’asar nan amma Baka sanar da ni ba haka matsayina yake a wajenka ko ai ka kyauta sai ka shirya gobe zanzo garin domin ganinka idan Kai Baka bukatata ni Ina bukatar ka”
“Ba haka ba ne Mujahid wlh tafiyarce ta zo mun Kai tsaye amma kaima kasan matsayinka ya wuce haka Allah ya kaimu goben ya kawo mun Kai lafiya”.
Washegari da Kansa ya je Airport tare da dauko Aminin nasa Da iyalansa Kai tsaye gida suka wuce Wanda tun a mota suka fara hirar yaushe gamo mujahid na juyawa ya kalli kyakyawar matarsa ya ce”Cutie nasan bakinsa sa ba ko”?ta ce”eh hero”ya ce “aminina kenan a U.K tare mukayi Degree dinmu na farko mun shak’u da shi sosai lokacin aurenmu ba ya k’asar shekaransa goma rabonsa da Nigeria amma kintuna tafiyarmu honey moon Ina ce maki tare nake da aminina idan kikaga na fita na dad’e lokacin a saudia?ta gyada kai ta ce”Allahsarki Allah barku tare”Adnan ya amsa da amen tare da cewa”amma fa kin wahalar mun da aboki da yawa gaskiya “Ayra dai tayi murmushi batare da ta Kara cewa komai ba inda hirar ta koma tsakanin Adnan da Arman”.(Ayra da Arman na Ni Da Yaya Arman idan Baku manta ba)
Tarba ta musamman Momy tayi musu Domin tun jiya ya fada mata zuwansa murmushi Mujahid ya yi ganin yanda Adnan ke yiwa Amal wasa sai dariya ta ke kafin ya kalli ummi da itama su take kallo gwanin burgewa Arman ya ce”
“Ummi gaskiya mungaji da zuba wa mutumin nan ido gwara ko a ruga ne mu samo masa mata “
ummi tayi murmushi ta na gyara zaman y’an biyun maza da ke jikinta ta ce”Kaima dai ka fad’a Mujahid na rasa me yake Damun Adnan don Allah jibi kaf sa’anninku daga me yara biyar sai hudu sai ukku jibi Kai fa masha Allah gwanin burgewa yara shida me yafi wannan arziki amma shi na rasa me yake damunsa game da batun Aure ba ya ma saka wannan a lissafinsa ya kamata dai ka masa fad’a Kai ma”
Ya na bin Arman da harara ya ce “watau ummi ka zo zugawa ko”?ummi ta ce ba batun zuga Gaskiya ce “idan lokaci ya yi za ayi ai?
Ta ce “Ai Insha allah lokacin ne ya zo shi ma ya maido ka don na gaji da ganinka haka”
Ayda da ke saukowa alamun daga bacci ta tashi Ummi ta kalla tasan Ayda da gigin bacci ta ce”bi a hankali Auta karki fad’i mana na hanaki fitowa bacci bai fita a idonki ba bakyaji sai kin k’ara faduwa irin na rannan””
“Toh ummi yunwa nake ji fa wlh har bana gani sosai “ta fada ta na nufar dining ba tare da ta Lura da kowa da ke wajen ba ummi ta ce”kunkai Har fin d’aya biyun dare bakiyi bacci ba yaya zaku tashi da wuri ina mamakinma idan da makaranta a haka har ku tafi wannan waya dai ta masifa Allah mana maganinta ga breakfast din naki nan”
Zuba mata idanu Ayra tayi “Masha Allah Allah Yayi halitta a nan to ai sak itadai wlh kyakyawar Y’ar india idanunta ya nuna mata a a Indian ma Wanda ya yi kyawun wannan d’aid’aikune wani kishi taji ya taso mata don wlh ko ita da ake fad’ar kyawunta nata nafila ne ashe da taga wanan”
maida kallonta tayi ga Arman ganin hankalinsa ba ya kanta gaba daya ya sanyata sauke ajiyar zuciya dukda ba ta kokonta mijin nata akan kowace irin mace “
Kallon yanda take breakfast din da sauri ya yi hankalinsa gaba d’aya yana kanta ya yi tunanin yunwar da take fada arish din gabanta Yayi mata kadan sai yaga har saura tayi a ransa ya ce”har yanzu Tana nan da rashin son cin abinci da yawa kenan”
tsaki ya ja ganin riga iya gwuiwar da ta fito da ita gashin kanta bakikkirin duk ya bayyana ya sha gyara har gadon bayanta ta tunk’e sai shek’i ya ke don ba ko kallabi kanta“
”maida kallonsa ga Arman da hankalinsa na ga ummi suna cigaba da hirar da baisan me ma suke cewa ba ya yi tare da mikewa ya na Kama hannunsa ya ce”
muje part d’ina Amal da ke hannunsa Ayda idanunta ya fara kaiwa ita dai Tana son kyawawan yara Allah’ya sani
“wow uncle Wannan yarinyar fa don allah ba ni na riketa"ta fada ta na nufar wajen domin amsar ta kallo daya Mujahid yayi mata ya kauda kai a yayinda Adnan ya b'alla mata harara wanda sam bata lura ba hankalinta na ga amsar yarinyar ta mika hannu tare da amsarta wanda jin hannunta ya na gogan fatan nasa ya sanyasa saurin mika mata tare da juyawa ya yi gaba Arman ya bisa yana kumshe dariyar da take cikinsa….✍️
*juma’at Mubarak Allah hadamu da albarkarun ranar Insha Allah yau munshiga hutun weekend sai kuma Monday idan Allah ya kaimu kuyi hakuri posting kullum Bazaiyu ba*🙏🙏🙏
Domin Neman Karin bayani sharhi,or shiga grp 07026166536
*_Miss Hajo ce*_🤙🏿
♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️
```MALLAKAR```
*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE
*CAPACITY CAPACITY CAPACITY NA CE INA MATA MASU CAPACITYN SUKE NA CE INA CAPACITY A WAJEN MACEN DA BA TA K’AMSHI*?📢 NA K’ARA DA CEWA INA AMARE DA UWAYEN GIDAN DA SUKA AMSA SUNANSU SHALELEN MAI HOUSE KAI HAR MA DA Y’AN MATAN DA SUKE KAN CIN LOKACINSU UWA UBA AMARE MASU NIYYAR SHIGA DAGA CIKI TOH GA BABBAN ALBISHIR GAREKU MANYAN MATA NESA TA ZO KUSA DOMIN HAD’ADDIYAR MAI KAYAN K’AMSHIN NAN WATAU *AREEJBYABEER* TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA TURARRUKA KO WANI IRIN LAUNI TUNDAGA KAN *TURAREN WUTA,NA KABBASA,HUMRA,OIL,HALUT OUD,KAJIJI,HUMRA’S GUMELIAN DA SAURANSU* KUNSAN KIMAR MACE DA DARAJARTA BA TA TAB’A CIKA SAI DA K’AMSHI,TURAREN @byabeer YA NA DA MATUK’AR SIRRIKA DA TASIRI GARE KU MASOYA MUSAMMAN WANNAN DA YA KASANCE NA MUSAMMAN DAGA WAJEN Y’AR MUTAN LARABAWA NA TABBATAR KIKA FARA AMFANI DA KAYAN K’AMSHIN arej by Abeer SAU D’AYA TO FA GASKIYA KIN GAMA NEMAN KO WANI IRIN TURARE DON MAI HOUSE DA KANSA ZAI DINGA MAGIYAR A NEMO WANI TA NA NAN A CIKIN GARIN KADUNA *Areej by abeer*
SANANNA CE A HARKAR K’AMSHI TA NA TURA KAYANTA KO WANI STATE CIKIN AMINCI UWA UBA HAR MA DA KASASHEN K’ETARE MUSAMMAN Y’AN UWA MUTANEN NIGER GA KAYANTA DA SAUK’IN KUD’i GA KUMA BIYAR BUK’ATA A ZUCIYAR MASOYI KU TUNTUB’ETA A KAN NUMBER WAYARTA +234 816 492 1522 KO KUMA A SHAFIKANTA NA SADA ZUMUNTA DOMIN GANI DA IDO TIKTOK @areejbyabeer INSTAGRAM @byabeer *SAYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA*
🅿️……………………….*12*
Ya na kumshe dariyar da take cinsa ya ce
“ tsaya mana yallabai saurin me ka ke”
“arman ya fad’a ya na saurin binsa”ai naga kamar waya ka ke ka na dariya shiyasa””
ya fada yana bude parlourn kallonsa Arman ya yi bayan sun zauna har lokacin da dariya a fuskarsa ya ce
”To ai Kai d’inne ka ke bani Dariya wani sa’in kuma haushi kana bukatar Abu na rasa boye boyen me kake”
dogon tsaki ya ja ya na kauda Kai ya ce”kana da matsala Arman “,
“Ai dole na fad’a maka gaskiya wlh idan nine tuni an wuce wajen Kai ni fa idan Ina son Abu kowace hanya zan iya bi don na mallakesa Kai shaida ce domin na gwammace ko zan mutu akan hanyar neman abun amma Kai Ina doraka hanya ka kasa ganewa na rasa girman kan nan naka ma meye ka na cutar da kanka a banza “
“Kai ni fa duk ba wannan ba matsalar da na tunkara ta fi duk wacce nake ciki a baya”
”Cikin kankakanin lokaci Arman ya zama serious tare da zuba masa idanu ba ko kiftawa ya ce”
”me kuma ya faru ko Akan batun Auren zahra ba ka guda ba ka wuce wajen”
ya ce “wannan a wajena duk k’aramar matsala ce akan wacce nake ciki “…………..!
Murmushi Ayra tayi ganin yanda Ayda ke riritar Amal cikin D’an k’ank’anin lokaci sukayi sabo kunsan me d’a,
ummi ciki suka shige da twins din ta sanya musu carton a parlourn ta Ayra da suke ta hira da Ayda kamar daman sun San juna Ayda ta ce”.
“Amma momyn Amal kinyi aure da wuri ne har kika haifi yara har ukku”Murmushi Ayra tayi ta ce.
”Eh da ya ke nayi aure da wuri gsky shiyasa don bakina secondary nayi aure sai bayan haihuwar su twins ne ma na yi degree d’ina kafin a haifi amal Auta Insha Allah sannan ba su Ukku ba ne su shida ne sauran suna wajen kakanninsu Naila da Nihal da Haidar”
wani irin mamaki ya cika Ayda ta ce”tab wlh ko Amal sai ace Baki Haifa ba”
murmushi Ayra ta kuma ta ce “yanzu fa shekarana kusan 27”eh mana wasu ai kamar ku dinma sai ynzu ake musu aure kinji dad’i amma nikam ba na son auren wuri wlh”
Ayra ta ce ai kamawa ta ke ni kaina Allah ne ya zab’amun hakan gidan mu ba wacce ta tab’a aure a haka mun sha wahala sosai *NI DA YAYA ARMAN* kafin muyi Aure “
Ayda ta ce “Allahsrk allah Kara muku zaman lfy da kwanciyar hankali”Ayra ta ce”Ameen kema sis Allah Baki na gari kamar yaya arman ko ma fiye da shi”.
Ta yi murmushi ta ce”Ameeen Toh”Lokacin suka cigaba da hira inda nan su Mufeda suka samesu Noor ta na gidan aunty khadija nan ta ke shaida mata an lik’a time table exams “
Ayda ta ce “Allah kaimu kun had’u da su jawahid kuwa”Ta ce”Eh mun hadu suna ta tambayarki ga basa samunki waya Ina wayar da sugar dady ya saya maki”
ta tab’e baki ta ce”ke fad’a maki ne banyi ba Ashe ba mutunin azziki ba ne da wata manufa ya sayamun wai yaushe zan shirya mu had’u a hotel na fad’a masa maganganu na ce ya aiko a amsar masa wayarsa ya aiko kuma na basa kayansa tun yaushe ko sati batayi hannu na ba”
“Mufedah ta ce”kaji tsohon banza ai gwadama da ya nuna maki manufarsa tun tafiya batayi nisa ba Allah kyauta sai ki dinga kiyayewa”ta ce”Insha Allah ni yanzu kam na ma rufe kofar karbar sabbin samari ma”mufeda ta na daukar amal ta ce”da dai yafi”.
Ayra dai murmushi ta yi sai Yamma suka shirya tafiya ummi ba yanda batayi su kwana ba arman ya ce zasu juya kano ne su gaisa da iyayensu gobe suke son komawa abuja tsarabar turarruka masu kamshi na wajen AREEJBYABEER ummi tayi musu Adnan da Kansa ya maidasu airport saida ya ga saukar tashin jirginsu kafin ya dawo gida.
Bayan kwana biyu ummi na zauna ta na Shan fruit Adnan ya mike bayan gama gaishe ta da Yayi ta ce.
“Dawo ka zauna magana nake so muyi Adnan”dawowar ya yi ya zauna “
Ummi na Jan numfashi ta ce”Adnan Akan maganar da na Saba ce ko da yaushe Akan aure ka na gani manyanta kake abokananka duk da y’ay’ayansu ko hakan ba ya burgeka ya kamata zuwa yanzu ka yiwa kanka fad’a ba sai an maka ba”
shiru ya yi ya na sauraronta cikin ladabi ya ce”Ummi Insha Allah za ayi”Kullum haka kake cewa amma har yau ko sau d’aya Baka tab’a kawomun wata koda wasa da niyyar ka na so ba”Shiru ya yi ba tare da ya ba ummin amsa ba Kansa na kasa”
“Kodai Baka da Lafiya Adnan”da sauri ya d’ago tare da zubawa ummi idanu ba shiri kafin ya janye nasa cikin sauri yana Jin nauyin maganar ummin ya girgiza Kai”Shi kan shi ya na Jin irin ajiyar zuciyar da ta sauke kafin ta ce “
“Allah kyauta daman akwai maganar da nake so muyi game da Ayda””Toh ummi Inajinki “ta ce”
“yaya ya kirani jiya ta inda ya shiga ba nan yake fita ba Faruq ya je ya shirya masa qarya da gaskiya akan wai muna son rabasa da Ayda ne shima yanda nake da iko Akan ta haka ya ke da iko da ita ya ma fini iko da ita ya gama magana tunda ta na sonsa ya na sonta Kiran rana kawai zaiyi a d’aura Auren na Kira Amera na mata bayani ta ce na sameka da maganar duk abunda ka yanke itama shi ta yanke”
Jim ya yi ya na saurarenta kafin cikin nutsuwar da ta zaune masa ya ce”to me take nufi ai duk abunda kuka yanke ya yi”
“ummi ta ce “a a Kai ko kake da ruwa da tsaki da yarinyar nan domin bata da wani uba da ya fika indai da adalci ko ni kaina ka fini iko da Ayda ni Ina mamakin ma yaya da har ya ke zakalkalewa game da lamarin yarinyar nan ko ya manta abubuwan da suka faru abaya shi kan shi gudun Amera da al’amarin nan ya faru ya yi wani irin duka ne baiyi mata ba karshe ya ce ba shi ba ita sannan ba ruwanshi da y’ar ko duk yana mantawa da wannan na Lura kawai saboda D’an sa ya ke wannan abun dukda muma lokacin mun nuna mata b’acin ranmu matsayinmu na y’an uwanta musamman ni da yazamana matsayin uwa a wajenta domin duk wata tarbiya ni na bata ni kaina lokacin nan yaya bai barni ba wani irin rashin mutunci ne bai mini ba suka kasa fahimtar mu amma yanzu ya zo sai zakalkalewa ya ke Akan y’arinyar…!
shi dai Adnan shiru ya yi bai ce komai ba mikewa ya yi ya ce”zaije ya huta”koda ya koma part dinsa kwance ya yi bisa one sitter a yayinda ya zubawa rufin P O P din dakin kallo ba ya ko kiftawa alamun yayi zurfi a tunanin da ya lula kafin ya lumshe ido