Showing 36001 words to 39000 words out of 44977 words

Chapter 13 - MATAR UNCLE BOOK COMPLETE BY MISS HAJO.docx

11 Aug 2025

1454

sai sun ba kansu wahala ba rana ta b’ata musu fuska kowa a waya suka tura masa haka anko tare da fad’ar shagon da zasu sayo duka ankunan guda hud’u na 300k suka fiddo a cewarsu shine pass din su na shiga don sunce sai Wanda ya isa a kawayen nasu ma zai halarta wajen ba sa bukatar kananun yara”(Tofa harkar ta manya ce Ashe 🤣)

Duk Kayan da Ayda zata saka Tundaga kan fara biki har gama wa Ummi ta bada order su daman daga Dubai aka sayo mata komai da zata saka hatta d’inkin a Chan ummi ta umarta ayi mata bayan ta kira kwararriya tela ta auna Aydar aka tura size din Chan kamar yanda tayi a bikin khadija da y’an biyu.

Biki ya rage saura sati biyu ganin da gaske momy ta ke ba zuwa zatayi ba hakan ya sanya ummi yi mata fad’a ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba amma dukda haka momy cewa ta yi.

”kiyi hakuri ummi amma wlh bazanje ba ni umrah ma zamu tafi next week ni da barrister ba na k’asar ma za ayi bikin shi ne daman na Kira na fad’a miki a mana fatan sauka lafiya”

ummi ta ce”hmm Toh Yayi kyau Allah saukeku lfy biki dai tunda Allah ya rubuta ba yanda zamuyi “Momy dai bata Kara cewa komai ba “

Koda suka gama waya ummi aunty Laila ta Kira rai b’ace ta ce”kema wai kina nufin da gaske baki zuwa bikin wayau bakinku d’aya ke da amera na Lura ko”?

“A a Ummi wlh zan zo hatta fatima zata zo don jibi ma muke saka ran zuwan ta sun samu dogon Hutu hada ita zamu taho “Ummi na sauke ajiyar zuciya ta ce”Toh Alhmdulillah Allah kawoku lfy”aunty Laila ta ce “amen”

Komai ummi ta tanada Tundaga kan Kayan d’aki kitchen decoration duk wani Abu da Y’ar gata zata buk’ata ummi ta tanada komai na waje ta saya mata a nan billionaire bride kunsan ku da kanku ba sai am fad’a ba inda aka sai kayan kunsan ummi ta gama wa Ayda gata .

Wani kukan farinciki Ayda ta yi bayan gama sayayyar domin da ita akaje ta zabi komai addua kam ummi ta sha ta tasan momyn nata sunyi dacen Y’ar uwa”.

Hakanan yau ba abunda ya ke fad’o mata a rai sai mahaifinta tsawon shekaru abunda ba ta tab’a ba jiki sanyaye ta kalli ummi da ke waya sai da ta gama wayar kafin ta kalleta da damuwa a fuskarta ta ce.,

”ummi amma dangin babana zasu zo ko?Wani irin faduwa gaban ummi ya yi Wanda har sai da ta so ta yar da apple din da ke hannunta,

kasa saisaita nutsuwarta ta yi zubawa ummin idanu Ayda tayi kafin ummin ta ja dogon numfashi ta ce”

eh zasuzo”Wata Nauyayyar ajiyar zuciya Ayda ta Sauke ta ke ta saki murmushi tare da d’okin ganin dangin mahaifin nata da bata sansu ba”

ta na Shirin yiwa ummi tambayar garinsu ta ga har ta haura sama Tana Kara sakin murmushi ta ce”ko a wani gari suke ko meyasa ba su tab’a zuwa inda nake ba ?”

Yau biki saura sati guda cuf cuf a fara shiri ya kankama ta ko Ina su Ayda sun shiga busy ba kad’an ba kowa sai fad’ar kyawun da ta k’ara ya ke saida ummi ta ce ta dinga yawaita Lahaula domin fa kowa ya kalleta sai ya yaba donma ba ta fita .

yau su noor zasuzo su Ayda sai murna suke Karfe hudu suka zo driver ya je daukosu da gudu mufeda da Ayda suka ruga suka rungume Noor Cike da murna.

yayinda Aunty Laila ta rungume ummi Saida suka saki juna noor kafin Ayda ta Lura da fatima da ke gaishe da ummi “

“omg aunty fatima irin suprised haka kafin ta rungume itama ta na rungumeta ta ce”Oyoyo fav sis I missed you”

”Cike da murnar ganinta Ayda ta ce “ I miss you too aunty fatima yaushe kika dawo ko a whats app ba ki fadamun ba fa”

Ta ce “Fourth day back ”kafin ta Kama hannunta ta ce”Amarya kinyi kyau “koda suka isa ciki saida suka huta sosai kafin a soma ci gaba da tattaunawa”

Misalin Tara na dare faruq ya kirata ya na palournsu “Saida ta k’ara shiryawa sosai ta na Shirin k’ara turare Fatima ta ce “

“karkisa normally kina k’amshi kar yayi yawa tunda fita zakiyi”

“Toh Aunty Fatima ta fada ta na ta fasa sakawa kafin ta fita ta samu faruq din har ga Allah yanzu hirar na su ba dad’i yake mata ba kullum cikin zumud’i ya ke wai lokacin baya masa sauri sai 10:30 ta dawo d’akin inda ta samu su Mufeda da Noor na gwada ankunansu”

“Ina Aunty Fatimah to “Ta yi bacci ta na d’akin su twins “Ayda itama samu tayi ta kwanta don ta gaji Cike da fargabar fad’uwar gaban da yanzu ya zame mata kullum cikinta ta ke”

Washegari Fatima ta ja mufeda ta rakata gidan Khadija best friend dinta ce sosai.kuma sa’anni ne ,

Hugging din juna sosai sukayi Cike da zallar kaunar juna da kewar juna suka hau hirar yaushe gamo”sai isha’i suka nufo gida.

Daidai lokacin suna shigowa Uncle na dawowa gidan Security ya bude masa bayan mota ya fito cikin takun nan nasa mai Jan hankali ya nufi part dinsa cikin D’an d’aga murya Fatima ta ce “Uncle ha da kyaliya?sai lokacin ya juyo da mamakin kallonta ta na murmushi ta karasa kusa da shi ta ce “Uncle yanzu saikace fa ka manta suna na”D’an murmushi ya yi ya ce”rashin kirkin nawa bai Kai haka ba ai Fatima “

Ta na murmushi ta ce “ni dai ban fada haka ba uncle Ina yini ya kwana dubu”ya na katse kiran da ke shigowa wayarsa ya ce”Alhmdulillah ya karatu mutanen America ko”?ta ce”Alhmdulillah “ya ce”ko har kin kammala”?

ta ce”no there is one year left but I want to continue my masters a Chan I won't even return to Nigeria until I'm done ka ga sai na yi zama d’aya”

“ya ce” no talk of marriage ko alhudu-hudu”ta na Y’ar dariya ta ce”Aure kuma uncle now ?no mun barwa su Ayda “

ya girgiza Kai tare da nufar part dinsa ya na cewa”idan Baki fito da shi ba ni zan Nemo maki ko a kauye .

“dariya ta yi bayan ganin ya bace ma ta ta ce”Uncle kenan saikace shi ba tuzurun ba ne ni masu duka-duka 24 years wa ke zancen nan“ kafin ta shige ciki itama.,

Uncle ko da ya koma Wanka ya yi ya na feshe jikinsa da mabanbanta kalalukan tsadaddun dad’ad’an turarukansa bayan ya yi Shirin bacci.,

wani Frame d’in hoton Ayda da ke bed side drawer ya fito dashi lokacin ta na Y’ar shekaru biyar sanye cikin wata tsadaddiyar riga kanta ba hula gashinta ya zubo har baya ta yi dariya hakoranta sun bayyana yayinda dumples d’inta duka sun Lotsa.

Ya Kai mintuna ashirin idanunsa Akan hoton batare da ya motsa ba kafin ya sauke wata irin ajiyar zuciya ya na mayar da hoton inda ya ke kafin ya kishingida ya kwanta bisa tausassan pilon yana maida kallonsa ga frame d’in da ke saitin kansa hotonsa ne shi da ita cikin shigar bak’ak’en Kaya ya rungumota ta gefen sa dukkanninsu cikin dariya hakoransu a bayyane lokacin zatayi 3years idanunsa Akan hoton k’aran ringing wayarsa ne ya katse masa dogon tunanin da ya lula kafin ya dauka da sallama a bakinsa “bangaren Zahra kamar zatayi kuka ta ce “me nayi ma ka Ya Ali You don't always answer my calls”?

ya na had’e fuska ya ce”nothing”ta ce”Don Allah ya Ali ka dawo Qatar wlh Ina son ganinka sosai saboda Kai na dawo Hutu k’asar kuma ance ka na Nigeria ko na biyo ka Nigeria ka ga har na je wajen dangin umma”ya ce “ina aiki yanzu saida safe “kafin ya katse wayarsa”.

Washegarin ranar su Ayda suka je saloon Ana jibi za a fara event dinsu na farko Mami ta iso tare da muhammad da ya gama karatunsa ya dawo kasar domin Abdallah shi yanayin aiki ya ce sai daurin Auren zai zo”Wanda Fatima Sam bata so haka ba ta so suntaho tare da Mamy domin yanzu mutumin ta ne sosai kullum cikin waya suke amma har lokacin bai fad’a mata yana sonta ba itama batakawo hakan a ranta ba.

Da dare wajen karfe Tara Wata madaidaiciyar jaka fatima ta mikawa Ayda ta ce “

rike mun muje ki rakani farfajiya ki rigani fita kinji”Ayda na amsar jakar ta ce”

to kafin ta Kama hannunta su fito Sannu suka yiwa su ummi da ke ta hira Mamy na ta zolayar Ayda tayi sauri ta fice aunty Laila na kallon fatima da ke Shirin fita ta ce”

Ina zaki”?

Ta ceWaje”ana sanyin nan me zakiyi a waje”?

Kai momy wlh kinfiya takura sai kace yarinya fisabilillahi to waya zanyi “

ta na gama fadar haka ta fice ?

Aunty Laila ta kalli ummi ta ce “kinga ko ummi kad’an ma kenan?”

“Yawwa Ayda don Allah inane waje me sirri a nan gidan inda ba me ganinka”

Ayda ta ce saidai bayan part d’in uncle shine ba me zuwa wajen sai dai wajen duk shukoki ne”

Yawwa haka nake son daman ba ni jakar toh”ta amsa ta na fito da karfen shisha”Ayda na zaro ido ta ce,.

”shisha aunty fatima”ta na harararta ta ce”to tonamun asiri nayi tunanin kina da sirri ai Flavour ne to ba wani Abu ba ku har ynzu Baku Waye ba wlh”

A ran Ayda ta ce”ikon Allah wai yau ni ce ake cewa ban Waye ba”

saida ta rakata bayan wajen allah yasa da haske sosai ta na kallo ta fiddo ta harhad’a kayanta Ayda ko ranstuwa tayi ba ta cinta ta San da Kayan shaye-shaye a kayan nan ta na kallo ya hada abun ta dinga sha saida ta gama abunta tsaf kafin ta mayar “

ta na sauke ajiyar zuciya ta ce”Haba tunda na dawo kasar nan sai yau na sha wlh kamar a k’aya nake jina saura inji kinfadawa wani “

Ayda ta tura Baki gaba ta ce “da kinsan zan fad’a ai da Baki ja ni ba”

fatima na Shirin Kai mata duka ta kauce ta na dariya sai kuma ta kamo hannunta itama ta na dariyar ta ce”

“ni na isa na daki amarya guda wasa nake maki “murmushi Ayda tayi ta ce”wai aunty fatima momy da gaske ba ta zuwa”

Fatima ta ce “jiya ta ma wuce saudia ita da mijinta da yaransa ukku kinga da gaske alamun ba ta zuwa”

Hawaye na Shirin zubo mata fatima ta hade rai ta na saurin goge mata ta ce “meye abun damuwar Toh idan ba ta zo ba akwai abunda za a fasa “

Ayda ta girgiza Kai ta ce “a a amma fa aunty fatima ba ta son Auren fa”

da mamaki fatima ta ce”bata so kuma Toh saboda me bayan D’an D’an uwanta ne”

Ayda ta ce”saboda ba sa shiri da mamansa”

Fatima ta ce”ke rabu da su zasu sauko ni bansanma wainar da ake ciki ba kinsan ni koda nake kasar banason k’ananun maganganu sai ayi Abu a gaba na ma na kasa sanin me akayi ai dai kina sonsa ya na sonki ko”?

Ayda ta gyada kai”ta ce”Toh ki kwantar da hankalinki Allah Baku zaman lfy”Ayda na murmushi ta ce.

“amen aunty fatima ke kadaice wlh kika goyo bayan Auren nan gwarama aunty Aisha da twins“

fatima na yin gaba ta ce “ko meyasa basa so oho kaina ya fara juyawa yi sauri muje bacci zanyi”suna shiga ta shige dakinta da ta sauka tare da kwanciya Ayda ma na su ta shige ta na kwanciya.

Yau suka fara event dinsu na farko masha allah Tundaga kan kawayen amaryar da amaryar batun ba a magana kasan y’ay’an banki sunyi kuka sosai Yayi kyau party’n na su ranar Ayda shigar Red ya subhanallah kafin ka ce me hotunansu da video's sun fara yawo a social media.

Washegari sukayi henna Wanda shima ya k’awatu kwarai da gaske duka biyun faruq bai halaarta ba saboda ya ce dinner da kamu kawai zai je Wanda ba ko sisinsa.

Da daddaren ranar laraba sukayi Night party iya su goma kawayensu sai noor da mufeda sosai sukayi kyau shima amaryar ta yi shigar pink dukkaninsu da budaddun ankon riga da wandon kayan bacci iri d’aya su kuma blue da ratsin pink da sukayi order tuntuni a wajen hasfat collection sosai tsarin decoration din nasu da shigarsu yayi matukar burgeni sai karfe biyu suka gama a gidan aunty khadija hakan ya sa Chan sukayi kwanciyarsu.!

Washegari ta Kama Alhamis akayi Mother’s Day Wanda sosai iyayen Ayda sukayi matukar bajinta tundaga kan y’an uwan maman nata da abokanan ummi manya manyan mashahuran mata masu ji da kansu Ayda ta sha lik’i kamar ba asan darajar kud’i ba sosai ya yi kyau Wanda karfe takwas angama komai domin na yamma aka fara.

Daren ranar misalin Tara na dare Ganin yanda Ayda ta ke cire Kayan da sauri noor ta kalla ta ce.

“Ina zakije haka kike sauri”ta ce”Wajen yaya faruq ya na kofar gida ta ce “to sai kibi a hankali saurin me kike “Ayda ta ce “ya ce na yi sauri shiyasa shirya ki rakani”

noor ta ce a shirye nake ai “dakyal suka taimaka mata ta cire gown din kafin ta mayar da doguwar Riga dama ta Riga ta goge make up dinta gyale kawai ta zira ta Kama hannun Noor suka bi ta kofar kitchen don Allah na gani ta tsani zolayar da kakanninsu momy na daura ke mata .

fuskar faruq Cike da tsantsar fara’a ya ke kallonta rabon da Ayda da ga faruq cikin fara a kamar jiya zuwa yau sai tace bata taba ga fara’arsa ba tunda suke a duniya kamar haka Cike da tsantsar doki da murna ya ce.

“babe muyi sauri ummana ta ce na kawo mata ke yau Tana son tayi miki nasiha da ga ita sai ke wai su al’adar gidan su haka ake “

a ran Ayda ta ce “Allah sarki kila ta sauko itama yanzu Tana son Auren kallon noor ya yi ya ce”muje ko “

Ta shiga baya Ayda na gaba Allah ne kadai ya kaisu gidan lfy domin Rabin tuk’in hankalinsa na ga Ayda.

“koda isarsu zaune suka tarar da Umma a palour ita kad’ai gaban Ayda na tsananta faduwa suka karasa palourn ga mamakinta sai taga Umman ta taso tare da kama hannunta ta ce”maraba da zuwa y’ata ta musamman “

Kan Ayda k’asa ta gaisheta bayan sun zauna gefenta umma ta zaunar da ita tare da tambayarta ya hidimar biki ta ce

”Alhmdulillah umma “Ina yini”Noor ta gaishe da Umman daga gefe Chan har lokacin ba ta zauna !ba”umma ta ce.

”lafiya qlau tsayuwar me kike kisamu wuri ki zauna Y’ar wajen laila ce ko?Noor ta gyad’a kai”

Maida kallon ta Umma ga faruq ta yi da har lokacin fuskarsa kamar gonar audiga don farinciki ta ce”

“Toh tsayuwar me kake da Allah ka bani wuri na gama da y’ata sirri nake so muyi ““

Faruq ya ce”Toh umma sirrin ba a gabana ba za ayi”?

ta ce” a a a wannan sirrin na musamman ne wuce ka bamu waje idan na gama na kiraka ka maida su”

Faruq ya nufi kofa da zallar farincikin umma ta amshi Ayda hannu bibbiyu ya na barin wajen umma ta juya saida ta tabbatar da Faruq ya bar wajen kafin sauya fuska ta na had’e rai tamau ta mike tsaye tare da Kama kugu d’aya ta na dakawa ayda tsawa ta ce”

“Bud’e kunnuwanki da kunnan basira kiji me zan fad’a maki”

wani irin fargaba ne suka ziyarci Ayda ba shiri ta mike tare da komawa kusa da noor kamar mai Shirin gudu wa umma ta ce”

“ba bugu ba zagi amma fa na rantse miki da Allah kika kuskura kika auri d’ana kin shirya tarbar bala’i da tashin hankali a wajena domin ba na sonki ba na kaunarki bazan tab’a sonki ba Mayya kin kama mun kurwar d’a yo daman tsintacciyar mage ta na mage ne sunga ba me kwasa shine aka lakabawa d’ana to tun wuri wlh ki sakarwa d’ana kurwa idan ba haka ba sai na b’atar da ke shegiya Y’ar zina”

Cike da zallar rashin kunya Noor ta ce”idan Ayda mayya ce to shima mijin naki maye ne kuma duka y’ay’anki mayu ne “

“Ke karamar Marar kunya banzo ta kanki ba ta bangaren ubanta nake nufi yarinyar da bata da asali ba asan Waye ubanta ba ko Baki da labarin shegiya ce yau na fad’a maki Toh idan Baki sani ba ki sani shegiya ce idan kuma kin isa fad’a mini ubanta ko dangin ubanta d’aya da kika sani”?

“Innalillahi wa inna ilaihirajiun “noor ta maimaita ta na rumtse idanu kafin ta figi hannun Ayda da numfashinta yake kokarin barin jikinta da sauri ta fisgeta sukayi waje .

gaba d’aya Ayda ba ta cikin hayyacinta bin noor ta ke amma bata sanin wata duniya ta ke ciki.,

wata irin bugawa zuciyarta takeyi a yayinda take Jin numfashinta na sama-sama ya na sirk’e mata kafin ta daina fahimtar komai duhu ya mamaye ilahirin ganinta kurumta ta dadashe kunnuwanta daidai suna barin jikin get d’in gidan su faruq ta yanke jiki ta fad’i “

“tashin hankalin da noor ta shiga ba ya musaltuwa kuka ta sanya tare da rungume Ayda dake k’asa ta ce”

“karki mutu Sis wlh karya ta ke sharri ne ki tashi”Ko motsi batayi ba cikin kuka da rud’u noor ta d’ago wayarta tare da danna wayar Ummi.

cikin kuka da tashin hankali ba ta jira me daga ummin zata ce ta ce”ummi ki taimaka yanzu a zo a daukemu muna kofar gidan su Faruq Ayda ta fad’i ba ta numfashi “

“Innalillahi wa inna ilaihirajiun noor yaushe ma kuka fita wai ma me ya kaiku gidansu ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login