Showing 18001 words to 21000 words out of 44977 words
Chapter 7 - MATAR UNCLE BOOK COMPLETE BY MISS HAJO.docx
bugu ihu noor ta sa tare da mikewa ta ruga ta bita da gudu Mufeda ta rik’o Ayda itama Dariyar ta ke hada rik’e ciki da karfi Ayda ta fusge ta na Jan dogon tsaki ta koma ta zauna ta na huci ta ce”wlh sainaci uban yarinyar nan na Lura bata da kunya sam”
Mufeda na dariya ta ce”Sannu aunty babba daga fad’in gaskiya Toh wlh aka ma barku ku kuntar ai ke zaki sha wahala kinsan wlh nanaki da k’asa zatayi ba wani karfi ne da ke ba “Ayda ta ja dogon tsaki ta na janyo wayarta ta ce”munafuka ai duk bakinku d’aya ita d’in banza ta kadani ai ta ruga tasan na jaki zata sha”Mufeda ta ce “to meye a ciki kin Yabi gwaninki itama ta yabi nata ba anyi 1-1 ba”.
Bayan kwana biyu Ayda ta na Shirin tafiya School Ummi ta Aika kiranta ba ta kawo komai a ranta ba ta sauko cikin shirin tafiya school sanye da katuwar hijab dinta har k’asa samun faruq tayi a palour dagashi sai ummi wanda ganinsa ba karamun fad’ar mata da gaba ya yi ba kallo d’aya ya yi mata tare da dalla mata harara daidai shigowar Adnan d’akin sosai ya yi kyau cikin kananun kaya da sukayi masifar masa kyau d’aya daga cikin kujerun palourn da ke kallon ta ummi ya zauna jiki sanyaye ta zauna kusa da kujerar ummi.
“Ummi Ina kwana antashi lfy”Ya fad’a tamkar bashi ya yi maganar ba “Cike da kulawa ummi ta amsa masa tare da tambayarsa ya ya tashi”ya amsa da Alhamdulillah “Ba ka gane sa ba ne faruq ne fa babban D’an Yaya Bukar na ga Baku gaisa ba”
Ummi ta fad’a ta na kallon Faruq”don shi ya Kamata ya fara gaisheshi kasancewarsa karami Adnan ko wayarsa ya fara latsawa tamkar ba shi a wajen”Sannu”Faruq ya fad’a a dak’ile d’aga masa hannu Adnan ya yi ba tare da ya kallesa ba wanda hankalinsa na ga waya hakan ba k’aramun b’atawa Faruq rai ya yi ba yaja tsoki a cikin ransa kafin ya maida kallonsa ga Ummi”
Ummi ta ce”ga ta ta fito Toh wata magana ce ka ke sonka fad’a wacce sai a gabanta “gyara zamansa Yayi ya ce”Daman don kar ta ce karya akayi mata shiyasa na ce a gabanta zan fad’a ummi kinganta nan ba karatu take tafiya makaranta ba kullum sai samari sun d’aukesu a mota yawon banza suke tafiya ta na fakewa da karatu su ne har hotels”
A matukar zabure ba tare da zaton maganar da zata fito daga bakinsa ba Ayda ta d’ago tare da nuna kanta da yatsa lokaci guda hawaye suka fara zarya a idanunta ta ce”ni kuma yaya Faruq yawon banza kuma “a fad’a ce tamkar zai hauta da duka ya ce”Eh ke ko sharri zanyi maki munafuka ko anfada maki duk abunda kuke ban sani ba”kafin ya maida kallonsa ga ummi da ta daskare a wajen ya ce “shiyasa na zo da maganar Aurenta don kar tarihi ya maimaita kansa karo na biyu zan rufa asiri na aureta kar ta d’auko mana abun kunya irin wanda akayi a baya “
Zuba musu idanu Adnan ya yi ba ko kiftawa don tun maganar faruq ta farko ya d’ago ya na saurarensu “
“Wlh ummi sharri ne “?Ayda ta fada cikin kuka
nuna Kansa ya yi a matukar harzuke ya ce”ni nake maki sharrin tsabar raini ya shiga tsakaninmu don ubanki”
Kuka ta sa Cike da takaici ta ce”Wlh sharri kayimun kuma kace Ina tafiya yawon banza me nufinka kenan”
yawon iskanci nake nufi “wlh nidai ba Y’ar iska ba ce saidai idan Kai ne dan iskan don dai kawai kana son b’atamun suna sai ka yi mun sharri Allah ya isana wlh”
ta fada Tana kuma sa kuka fuska had’e ummi ta kalli faruq da ya mike zai hauta da duka ta ce”kar ka fara ma koda wasa kaji na fad’a maka iya maganganun da ka fad’amana ma kad’ai sun isa kuma mungode kwarai ka cika d’a”
idanunsa har sun sauya kala tsabar masifa ya juya ya kalli ummi tafin ya maida kallonsa ga Ayda da ta mik’e Tana Jan baya cikin kuka ta ce”Wlh Allah sai ya sakamun sharrin da kayimun mugu azaalumi kuma ba a son taimakon nawa da zakayi in…..”Saukar marin da taji ne ya sanyata kasa k’arasa maganar da ke ranta
kafin ta Kara d’agowa ta ji saukar wani a d’ayan kuncinta K’ara rumtse idanunta tayi jin wani karan mari da sauri ta bud’e idonta Jin ba a jikinta marin ya sauka ba Wani irin ja baya tayi dukda har lokacin dishi-dishi take gani don bata gama dawowa hayyacinta ba rumtse idanunta tayi jin karin saukar marin a d’ayan kumcin faruq kafin ta bud’e idanuwanta da takejin kanta na matuk’ar juya mata ta sauke su a kan……✍️
*Na sallameku har nayi bacci da saleb’a yau kam*🤣
*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️
```MALLAKAR```
*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾
*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE
🅿️……………………….*10*
Ta sauke a na “Uncle”ya d’aga hannu da niyyar sake marinsa ummi ta dakatar dashi ta hanyar shiga tsakaninsu hankalinta a tashe ta ce”ya isa haka Adnan”Ran Adnan da Yayi kololuwar b’aci ya ce”ki kyaleni ummi na nuna masa hankali
“Waye shi da zaizo ya na fad’a muku magana son ransa kafin ya maida kallonsa ga Ayda ya na nunata da yatsa ya ce
”ji irin dukan da Yayi mata baiwarsa ce?Kafin ya maida kallonsa ga faruq tare da nuna masa kofa a matukar zafuce ya ce
”fita ko wlh a fitar dakai ba hannu ba kafafu” wani irin huci faruq ya ke ya kasa koda furta kalma d’aya sai juyawa Yayi tamkar zai tashi sama ya fice kamar yanda Adnan ya umarta.
ita kanta Ayda ta tsorata da yanayin da ta ga Uncle a ciki da gudu ta ruga sama ta na kuka wani dogon tsaki Adnan ya ja ya na juyawa zai tafi ummi ta kamo hannunsa tare da zaunar da shi tasan halin zuciyar Adnan Sam bashi da fad’a amma aka tab’osa ko ransa ya b’aci ita kanta mahaifiyarsa tsoro yake ba ta zaunawa ya yi Wanda Har lokacin ransa b’ace ya ce”
“meye alak’ar Ayda da Wancen mutumin ummi?ya jefo mata tambayar ”Ta na zama kusa da shi ta ce”Soyayya suke “Soyayya!ya furta ba zato ba tsammani ganin yanda yanayinsa ya k’ara sauyawa ne ya sanya ummi zuba masa idanu kafin ta ja dogon numfashi ta ce.
”Ya naga yanayinka ya sauya”Shi ne daga soyayya har ya samu daman Dukanta?Aunty Laila da ke saukowa ta ce.
”Ai ba yau ne karo na farko ba Duk lokacin da iskancinsa ya tashi a kanta yake saukewa yanzu haka aka duba jikinta ba a rasa tabon dukansa Da tayi masa laifi kad’an sai zagi sai duka amma a haka taji ta gani take sonsa ba sai a kyalesu ba inma kasheta zaiyi ya kasheta tunda bata San ciwon kanta ba a aura mata shi suje Chan su karata amma d’ibar albarkannan baza a Kara yi a gidan ummi ba”
Ta fada ta na zama daya daga cikin kujerun palourn “don ranta itama ya b’aci “Ina Amerah?ya fada ya na kallon Aunty Laila”Ta na gidan Su hasana amma munyi waya da ita yanzu ta taho Tana ma hanya a kowani irin loakaci zata iya isowa”Daga lokacin bai Kara cewa komai ba Sai ummi da Aunty Laila da suka ci gaba da tattaunawa Akan lamarin”ba jimawa momy ta karaso ita kanta yanayin da ta samu Adnan a ciki ta san ba lafiya ba !
“Yawwa ga ma Amirar “Cewar Aunty Lailah”momy na zama kusa da gefen ummi ta ce “Lafiya “Aunty Laila ta bata labarin d’ibar Albarkar da Faruq ya zo ya yi a takaice”
“Ina Alkawarinmu da ke Amerah Amanar da na Baki kenan “?
”ya jefawa momy tambaya ba alamun wasa a tattare da shi momy da hankalinta duk ba a jikinta ya ke ba ta d’ago tamkar zatasa kuka ta ce
“ wlh Ba Laifi na ba ne “
“Idan ba laifi ki ba ne Laifin wa ye “?
ya k’ara jefa mata tambayar ba wasa a fuskarsa ”
“Adnan Don Allah kar kaga laifina a lamarin nan “Momy ta fad’a hawaye na zuba daga fuskarta ta ce”Duk iya yanda zanyi wajen ganin na rik’e maka amanar Ayda kamar yanda ka bani Akan ko k’uda Baka son ya tab’a ta da niyyar cutarwa Na yi iya kokarina Adnan ni ma Abun Fin Karfina ya yi “
d’aga mata hannu Yayi tare da cewa “ da nasan bazaki iya ba tun farko da ban Baki ba da na tafi da ita na tarbiyantar da ita”
“Wannan wace irin magana ce ka ke Adnan kamarya da ka tafi ka tarbiyantar da ita ita mahaifiyarta da ni da na tarbiyantar da ita bamu iya ba sai Kai ne ya kake nuna mata iko da isa Akan y’ar da tayi nakuda ta haifa da cikinta”
” sai a sannan momy ta kalli ummi kafin ta maida kallonta ga adnan da har lokacin ya tsareta da idanu ta na goge hawayen da suke zuba daga idanuwanta ta ce”
“tun bayan tafiyarka Adnan ummi ni ma ta sanyani gaba Akan dole sai na yi aure bayan mutuwar Aure na da Alhaji mudassir tunda kasan komai a kan wancen Auren shekaranka biyu da tafiya Barrister Usman Abokin mijin Aunty Laila da matarsa ta rasu wajen haihuwa ya nuna ya na so na da aure Wanda lokacin banso shi ba ganin yanda ummi ta damu da son ganin na yi aure ya sanyani bin umarninta na auresa to daga lokacin Rik’on Ayda ya koma hannun Ummi amma wlh duk lokacin da zanzo Ina iya bakin kokarina wajen na rike maka alkawarin da na daukar maka abunne ya fi karfina tunda ba na tare da ita a hannun ummi ta ke”
“Wannan duk ba hujja ba ce matsayinki na uwa a duk inda kike kina iya kula da yarinyarki kinsan ko Ina sane da duk….kafin ya yi shiru?momy ta ce “D’aukata ni da ummi duk d’aya ne saboda nima d’in da Kai duka ummin ta rike mu ta kuma tarbiyantar damu har girmanmu”
Amma…!”
“Adnan “Ummi ta katse sa da sauri tare da cewa”wannan wace irin tambayace ka tsareta ka na tuhumarta Akan y’ar cikinta”
“Ummi ba haka ba ne kin kasa ganewa yaran nan wayau garesu fa fiye da yanda ba kya tunani ke yanzu shekarunki sun ja akwai abubuwan da suke faruwa Wanda basu kamata ba ”
Kafin ya ja numfashi don gajiya da doguwar magana da Yayi kafin ya maida kallonsa ga Momy da tayi k’asa da kanta ya ce”akwai waya hannunta?Girgiza Kai tayi tare da cewa”akwai amma na fasata ranar da zaka dawo”Toh idan akwai ma a amshe sannan Daga Yau ba zata k’ara fita Ko nan Da k’ofar gida ba Sannan makarantar da akace an sata na cire ta tunda daman ba ayi shawara da ni da za a sanyata ba kuma ba abunda aka sanyata tayi ta ke ba”!
“
”Kamar mai tsoransa momy ta gyad’a kai Wanda ya na gama fad’ar hakan yabar part din Wanda Aunty Laila suka maida kallonsu ga Momy da har lokacin hawaye ta ke ummi ta ce”ya isa kukan Amera “
“Saida ta ja numfashi kafin ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya Tagumi ummi tayi ta ma rasa wani irin tunani zatayi akan lamarin nan Aunty Laila ta ce”tafiyar tamu akwaita goben kuwa”?
Momy na satar kallon ummi da tayi tagumi ta ce”yanda ummi ta ce”Ummi ta ce”Allah ya kaimu goben umarnin mazajenku zaku bi ko nawa da kuke tambayar yanda na ce”Kafin ta mike ta bar musu palourn ganin fucewar ummi ya sanya Aunty Laila kama hannun momy suka nufi d’akinsu Wanda tun kafin suyi aure suke nan yanzu haka kuma duk sanda zasuzo nan suke zama Wanda nan suka cigaba da tattaunawa Akan lamarin aydar.
B’angaren Ayda kuwa Ta gaji da kukan har bacci ya dauketa saboda irin yanda kanta ke ciwo Noor na kallon mufedah ta ce”Muje ki rakani Ummi ta tayani rokon Dady ya barni tunda ba makaranta nake zuwa ba nan da two weeks saina koma na fada masa ya k’iya”haka ko akayi Ummi na masa magana a take ya yarda sosai Noor ta shiga Farinciki haka mufeda.
Washegari da sassafe momy ta shigo d’akin su Ayda kwance ta sameta idanunta biyu ta na kallon seeling ganin momy ya sanyata tashi zaune tana saurin goge guntun hawayen da ta sha ta kalli momyn da ta zuba mata idanu tamkar yau ta tab’a ganinta ganin irin kallon da momyn ke mata ne ya sanyata k’asa da kanta Ajiyar zuciya momy ta sauke ta na zama gefen gadon ta ce”Kukan
Me kike har idanunki sukayi haka ji yanda kanki ke b’allawa….✍️
♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️
```MALLAKAR```
*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE
🅿️……………………….*11*
“Ji yanda kanki ke b’allawa so kike ki jawa kanki wani ciwon a banza?
Girgiza Kai tayi k’asa-k’asa ta ce”bakomai momy Ina kwana”Tana Kama kanta tare da yi mata addu’ar ciwon Kai ta ce”Lafiya qlau mun shirya zamu tafi”
Momy da sassafen nan”?
Ta ce “Eh jirgin Tara zamu hau gwada mu isa Airport da wuri kina bukatar wani Abu daga waje na”?
Ta girgiza Kai ta ce “nayi tunanin zaku k’ara kwanaki ai”
ta ce “a a “
Shiru duk sukayi na y’an seconds kafin momy ta d’ago ta kalleta da itama itad’in take kallo Allah na gani ta na tsananin kaunar y’arta fiye da komai a duniyar nan amma takaicin Alak’arta da Faruq ya Hana cigaba da nuna mata soyayyar “
“Har yanzu Faruq ya na cikin ranki ko”
Momy ta jefa mata tambayar ?”
”janye idanunta tayi daga na momy kafin ta kalli gefe ta yi shiru”
Momy ta ce”magana zakiyi mun ba shiru ba mungaji ne gwara kawai Idan aurenki zaiyi ya zo a aura masa ke ku karata chan “
“Aure kuma momy?!
ta fada idanuwanta na yin waje kafin ta hade fuska ta na kallon gefe ta ce”Ni wlh bana son wani aure “
Momy ta ce “Toh idan bakya son Auren taren ta mecece kuke Ayda Sannan duk uban samarin wannan da akace kina tarawa wanda banda masaniya sai yanzu na meye wannan rashin kamun kan har Ina?
shiru tayi Tana kallon gefe”Kallona zakiyi kiban amsa ni na ma rasa yaushe idonki ya bude haka Ayda kullum huduba nake maki ki fita sabgar samari ba ruwanki da shiririta Ashe a banza na ke ga kuma wancen D’an iskan da kika nacewa ai dole mu aurar dake tunda kin fito kin gwada abunda kike so”
“ni fa momy gaskiya kibar maganar Auren nan samari kuma Insha Allah na daina kula kowa ai shikenan”?
Wannan kuma ruwanki ai Uncle dinki ya dawo shi zai saita miki zama sannan makarantar ma kinja ya ce ya cireki na barki da shi tunda haka kikeso in kinsan wata ai Baki San wata ba”
“Tab wlh Bazaiyu ba Kamarya an cire ni daga makaranta”?
ta fad’a hankali tashe”Momy na hade fuska ta ce”kamar yanda kikaji na ce Ni kaina uwarki Adnan ya isa ya yi iko da ni bare ke”
Tura Baki gaba ta yi ta ce”yo uba na ne ni wlh saina koma makarantata ”
Aharzuke momy ta ce”ya fi ubanki fitsararriya marar kunya “
Hawaye na zuba daga idanun Ayda ta ce”momy don ubana ya mutu kuma sai Kice ya fi ubana na tabbata da ubana na raye duk abunda kike cewa yayimun ai shi zaimun“
Yanzu dai a takaice rashin kunya kikeso kimun ko Ayda”Tayi saurin girgiza Kai ta na Hawaye ta ce”
“Ni wlh ba rashin kunya na miki ba gaskiya na fad’a momy kiyi hakuri don Allah karki tafi da fushi na”Jikin momy da ya yi sanyi ta mike ta ce”Bakomai Allah shiryeki mun wuce “
“ta yi saurin mikewa tare da kama hannun momy ta na kirkirar murmushi ta ce”To mu je na rakaku”itama momyn murmushin tayi kafin su jera su fito a ran momy ta na hamdalar Da Allah bai tab’asa Ayda ta tambayeta game da dangin mahaifinta ba “.
lokacin su ummi suna haraba fitowa domin rakasu domin Adnan zai kaisu Airport lokacin har ya shiga mota sosai Ummi taji dad’in ganin Momyn tare da Ayda wajen Aunty Laila ta koma tare da hugging dinta ta ce”Aunty Allah tsare hanya ya kaiku lfy “
Ta ce”Ameen daughter idan na isa zamuyi waya a wayar Noor kinji”ta gyada mata kai”Lokacin Mufeda da Noor suna school Noor tayiwa Mufeda rakiya”
Toh ko kuje kiyi musu rakiya airport d’in Ayda tunda y’an uwan naki basanan Uncle d’inki sai ya dawo da ke”Cewar Ummi”
Itama Tana son rakiyar amma jin ance su dawo da uncle ya sanyata cewa”a a ummi kawai ba sai na rakasu ba”Aunty Laila na kama hannunta ta ce “To muje sai kin rakamu “ta warware kallabin da ta daura a kanta Tana sakata mota “
Wani irin Lumshe ido tayi Jin gaba d’aya motar ta dauki wani irin ni’imtaccen kamshi ya hadu da sanyin Ac sai taji ta a wata duniyar ta musamman a ranta ta ce”
“ko Ina yake samun wadannan daddad’an turarukan”jin Karan tashin mota ya dawo da ita hayyacinta ta tuna Ashe har su momy su sunshigo “
momy ke gaban motar “Aunty Laila Ina yini”Cewar Adnan cikin