Showing 36001 words to 39000 words out of 80494 words

Chapter 13 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

mijin ki ne, ba haramun bane, kwarjinin da yayi mata ne yasa hannunta yad'an fara rawa kadan, Ahankali takai dayan hannunta kan lallausan lips dinsa, tabude masa bakin nasa,saita ji laushi saikace bakin Yara, jin hannunta Akan lips dinsa yasa ya lumshe Idonsa babu Shiri =?H?

Saida yaji tana kokarin saka masa spoon din abakinsa ne sannan yabude Idonsa, beyi musu ba kuwa ya qarasa Bude mata bakin tafara bashi abincin, cikin zuciyarsa Yana tunanin dole zai dauki kyakkyawan mataki Akan Minal, yanda take masa d'innan wata Rana Sai Asamu matsala, duk tabi ta maidashi wani Dan jariri cikin mintunan dabasu fi goma ba, zata iya yiyuwa anata bangaren tana ganin hakan ba komai bane, zata iya yiwa kowa, but anasa bangaren akwai matsala gaskiya

Ko cokali biyar beyi ba, yaji wani irin amai yataso masa, kafin yayi yunqurin tashi harya fara yi ajikin hijabinta, duk ya 6ata mata gaban hijab din, lokaci daya ta rude, tafara jera masa sannu, sannan tatashi taja hannunsa tarakashi toilet ya wanke bakinsa, hijabin jikinta tacire, tasake kamoshi suka dawo falon, Akan kujerar ta zaunar dashi tana masa sannu

Kansa kawai ya d'aga mata, Idonsa a lumshe, tace "Bari naje nakawo ma magani awajan mamy"

Cikin sauri yariqe hannunta, dayan hannun nasa Yana dafe da goshinsa yace "karkije, ciwon Kaine kawai, zai daina anjima"


Dawowa tayi tazauna tasaka hannunta duka biyun ta janye nasa hannun daga kan goshinsa tace "to sannu, Allah yasawaqe"

Baisan lokacin da yaji hawaye sun zubo daga idanunsa ba, tunda widad ta mutu har suka kaita makwancinta beyi kukaba Sai yanzu

Amina ta rikice ganin hawaye a'idon babban mutum kamar wannan, tarasa Yaya zatayi masa, duk saita daburce, itama kukan taji Yana kokarin zuwa mata, Bata yi kokarin Hana kanta ba tabar hawayen suka fara sintiri a kumatunta, cikin kuka tace "Dan Allah kayi hakuri kaji...."


Lokaci daya ya fuzgota jikinsa yasaki wani irin kuka, sosai yake kuka kamar mace, baqin ciki sa daya me yayiwa Lubna? Yanzu badon Allah yakawo Minal gidan ba kenan da yanzu shine yamutu, meyasa takeson kashe shi? Dama tanada wata manufa ne akansa?

Cikin sheshshekar kuka yace "thank you Minal..... Nagode... Nagode... ta dalilin ki.... Yauma na rayu...., akaro na biyu"

Kukan yaci gaba dayi sosai, kansa Yana kan Boobs dinta, yayinda hawayen Idonsa suke silalowa zuwa cikin rigarta suna sauka a saman breast dinta

Numfashin tane yake wani irin gudu, gaba daya ya d'aure mata kai, babba dashi Yana kuka, saita ji ta nemi nata hawayen tarasa =??

Ahankali tadora hannunta akansa, tanaso ta janye masa kansa dake kan qirjinta, amma yaqi Bata Damar hakan, domin kuwa sake riqeta yayi Yana kuka kamar Dan qaramin Yaro

Batada zabin daya wuce taqara bashi hakuri kozai daina wannan kukan, Ahankali tace "Dan Allah kayi hakuri"

Saida yasha kukansa, sannan yayi Shiru, amma kansa Yana nan inda yake =?H?
Turo kofar d'akin akayi aka shigo, cikin sauri takai kallonta ga wajan, gabanta ne yafadi ganin Muhsin abokin sa ya shigo, cikin sauri tafara qwace jikinta daga nasa, Saide kuma ta makara, domin kuwa Muhsin yariga ya gansu

Asim kuwa ko a jikinsa, Ahankali ya d'aga, ta cikin sauri kuwa tafice daga d'akin hijabin ta a hannu

Muhsin ne yazauna tare dashi har can dare, sannan yatafi gida, Yana tafiya kuwa Daddy da mamy suka shigo d'akin nasa, alokacin harya sauya kaya zuwa jallabiya zai kwanta, adakin nasa suka zauna gefen gado, shikuma yazauna kansa aqasa, Daddy yace "Asim Iyayen Lubna sunzo sun sameni sunata bani hakuri, meyake faruwa ne kayi mana Bayani"

Be 6oye musu komai ba yafada musu abinda Amina tafada masa, da kuma shawarar da Ishraqa ta bashi, da yanda tasa masa maganin har Widad taci, sannan yaqara da cewa "Daddy saide kuyi hakuri, amma dole zankai Lubna wajan hukuma, dole zatayi musu Bayanin wanda ya sata yin wannan aikin"


Mamy tace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un.... wannan masifa dame tayi kama?bazan hanaka ba Asim, may be ma dasa hannunta acikin mutanan da suke bibiyar rayuwarka, tunda zata iya Sama guba a abinci ai zata hada baki dasu, kakaita koma inane, nayarde maka"

Daddy yace "gaskiya Lubna ta aikata babban kuskure, amma ni a ganina idan aka kaita wajan hukuma ma kamar zubarwa kanmu mutunci ne, ai abun kunya ne ace Asamu irinta acikin zuri'armu, abarta da Allah kawai, zataga yanda makomarta zai kasance, gashi yanzu tayi niyyar kashemin dana, amma al'amarin yajuye yakoma kan 'yarta, kayi hakuri my son, insha Allah zaka samu Yara masu albarka, wanda zasu futo daga tsatson uwa tagari "



Mamy tace"Eto kuma hakane gaskiya, to kayi hakuri Asim"

Shide Asim yarasa gane wanne irin hakuri ne da Daddy, duk lokacin da abu ya sameshi saiyace zai kula da bangaren, kuma daga baya saide abashi hakuri, yanzu wannan dinma gashinan yace yayi hakuri

Daga musu kai yayi kawai, yace "zan kwanta" =??
Basu qara ce masa komai ba,mamy takashe masa wutar d'akin suka futo


Haka gidan sukaci gaba da zama Shiru, har akai sadakar ukun Widad
Alokacin ne kuma masu buqatar takardar nan turawan Singapore sukai waya zasu zo washe Gari, tashin hankalin da Asim ya shiga, yawuce misali, haka Shima Amjad, Amina da Amrah suna d'akin mamy suna gyara mata,Sai lailaye gadon nan suke, mamy tana kan sallaya tana waya da Daddy daya fita unguwa, Amjad ne yashigo, duk ya Rame yayi wani iri, kwanciya yayi agefen gadon, Amrah ta daka masa wata uwar harara, ta tsani tana gyaran gado azo a kwanta wallahi =??

Mamy ta Gama wayar ta kalleshi, "Autan mamy, jeka kiramin yayanka"

"magana kuma mamy?"

"Eh jeka turomin shi"

"mamy, yayafa baya cikin nutsuwar sa yanzu, Nima daga wajansa nake, ko magana ma bayason yi, kibari Hankalinsa yad'an dawo saikuyi maganar cikin nutsuwa, may be danyarabu da matarsa ne shiyasa, kuma taqi dawowa, Aida yanzu andawo da'ita, ni dama nagaji da jarabar kishin ta wallahi =?3?>?#?, Gara daya saketa, idan besaketa Bama wataran saide kiji na saketa "

Amrah tace"to sannu Daddy"

Mamy ta jinjina kanta "meyasameshi yanzun?"

"mamy akwai wata takarda da mukai missed, kuma mutanan da suke buqatar takardar zasuzo su karba ne, bamu San abinda zamu ce musu ba"

Mamy tace "wacce irin takarda ce wannan? To kuyi wata mana, da a'ina kuka Barta harta Fadi?"

"mamy wanda yafara rubutawa baya qasar, kuma da tawadar qasaar Germany akayi rubutun, idan muka sauya da namu zasu gane, takardar yaboyeta tare da sauran document dinsa acikin laptop dinsa, kuma yace computer ta 6ata"

Gaban Amina nane ya yanke yafadi, cikin tashin hankali tace "innalillahi..."

Daga nan tafice daga d'akin cikin sauri, gaba dayansu suka bita da kallo

Afalo ta wuce Asim daya shigo gidan yazauna cikin damuwa
Da gudu tashiga dakinsu, a haukace tabude kayanta ta dauko masa computer sa, innalillah kawai take maimaitawa cikin ranta, da yanzu ta cucesu, bayin Allah ashe neman computer suke Bata sani ba


Tana futowa daga d'akin ta ganshi afalon azaune, cikin sauri ta qarasa wajansa tace "Yaya..."

Yana dago kansa, ta miqa masa laptop din, mamaki, faduwar gaba, tsananin murna suka kama Asim, cikin sauri ya karba dawani irin farin ciki Akan fuskar sa yace "Minal... a'ina kika ganta?"

Itama murmushi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? tayi masa, tace "kayi hakuri Yaya, dama tana wajena, na manta ne ban bakaba, Sai yanzu naji Yaya Amjad yace ita kuke nema"

Shiru yayi Yana kallonta, murmushin yayi mata kyau sosai, zai Iya cewa wannan ne Karo na biyu dayaga murmushi Akan fuskarta,amma dariya kam bai taba ganin Amina tayi dariya ba, amma farin cikin data sashi yau, Shima yayi alqawarin zaisa ta, saiya nemo mata iyayenta, sannan dole zai ware mata Rana guda yakai ta wajan wasan Yara tayi abinda ranta yakeso
(=??=?"?>?&? @&?=??)

Afili yace "kiramin shi, jeki turomin Amjad din"

Juyawa tayi, ta koma d'akin mamy tana basu labari, ai suna jin abinda take fada musu duk suka dawo falon gaba dayansu, Rabon da mamy taga Asim yadanyi walwala tun mutuwar Widad, amma yau gashi Minal tasa shi, lalle taqara yarda minaal itace farin cikin Asim

Kunna computer yayi, ta kawo komai Yana nan yanda yake kawai keyboard dinta ne suka lalace, Amjad yabawa, yace yaje yadauke musu duk wani abu dayake kanta, yadena ajiye komai da komai Akan computer daga yau =??
Saide In abun yazama dole





*** ****** ***


Washe Gari Amjad yahau jirgi yakoma Yola,aranar kuwa baqin sukazo suka karbi takarda, hankalin kowa ya kwanta

Asatin
Amjad yadawo Lagos, yayiwa mamy maganar auren sa da Minal, tace masa kawai yaje yaci gaba da shirin biki, aikuwa nan da nan gida ya rikice, Sai siyaiyar kaya mamy take dan'autanta zaiyi aure



*** ****** ***




Muhsin ne ya shigo falon nasa, ganinsa da computer agaba yasa ya jinjina kansa "sannu da aiki abokina"

Saudaya ya kalleshi "sannu da zuwa Muhsin, Bari nasa a kawo ma ruwa"

"a a barshi, gani ga fridge din idan zansha zan dauka"

Asim yace "OK"

Muhsin yayi Shiru Yana saurarensa, yayi tunanin zai ajiye abinda yake yabashi lokaci sudanyi fira ko kadan ce, amma Sai yaga babu alamar hakan
Ajiyar zuciya yayi "amma Asim duk matar da zata aureka Sai tayi hakuri dakai, kullum aiki, Kai baka gajiya da wannan aikin ne? Office aiki gida aiki, haba, ya kamata ka ragewa kanka wannan aikin"

Murmushi yayi "Muhsin kenan, wanne irin hakuri kuma? Bagani azaune agida ba, tana ganina"

"to tana ganinka tana ganin photo, kaida photo ai duk daya Asim, yauwa Asim ina wannan yarinyar me manyan idanun nan?"ya qarasa maganar Yana kallon yanayin Asim

"wacce yarinya kenan?"

"wannan qanwar taka, kyakkyawan nan, Yama sunan ta.... Amina ko... Yawwa Minal"

Annurin fuskarsa ne yadauke, tuni ya kawar da computer tasa gefe guda, ya kalleshi yace "tambayarta kake?"

Muhsin yace "yes, saboda ai Nima kamar qanwa tace, tunda kaima qanwar ka ce"

Jinjina kansa yayi, sannan yace "ta'ina? Lalle Muhsin kanada kalan dangi dakuma cusa kai, ita Minal dinne harta zama qanwar ka?, to kashiga cikin gidan ka tambayesu, may be tana ciki"

Muhsin yayi murmushi ganin ya kunno abokin nasa, yace "tokai Asim menene na daukar zafi dannace qanwata? Koka fara Santa ne dakake kishi"

"inrasa dawa zanyi kishi Sai Minal? Karka manta bayan alaqar datasa na kawota gidannan, ina ganinta yarinya qarama, wadda inda ace nayi aure da wuri zan haifi kamarta" =??

Zaro ido Muhsin yayi, "yanzu Asim Minal din zaka Haifa? Lalle bakada mutunci, kuma Kai qaramin Dan renin hankali ne, Malam dama na tambayeka ne domin na gwada ka Akaro na biyu Inga kana sonta ko baka sonta, kasan ita yarinya qarama ce wadda zaka haifi kamarta amma ahakan kake liqe mata, kana yiwa yarinyar mutane wayo kana jin dumin qirjinta, =?H?
Nan nazo nasameka d'ame d'ame Akan qirjinta kana wani kuka saikace qaramin Yaro, kagama jin tudun qirjin yarinya kazo kana huramin hanci kai baka sonta, to qinta kake? "

Wani malalacin murmushi yayi" Muhsin kenan, wato kana bani mamaki wani lokacin, daka ganni Akan qirjin nata saime? Dama de kawai kacemin zuwa kayi Kamin hayaniya saboda rannan kazo kaganmu a haka, todana kwanta Akan qirjin nata cemaka akai wani abu naji? "

Muhsin ya Girgiza kansa" a a, ina zakaji wani abu kuwa, kaida kake waliyi, Nima bance kaji komai ba, amma ina baka shawara, ka gaggauta auren yarinyar nan, idan Bahaka ba duk lokacin da Amjad ya aureta wataran zaka aikata wa matar qaninka abun kunya "

Ransa ne yabaci sosai, ya saka hannu ya dafe kansa >?&? B&?
" Muhsin waye yafada ma zan iya auren Minal? Tayaya zankai kaina ga mutuwa? Bayan rasuwar mahaifina banqara jin tsoron mutuwa ba Sai da widad tatafi, da hankali na da komai tayaya zankai kaina cikin rijiya? Inason raina, saboda haka dan Allah katashi katafi Nina gode da wannan ziyarar "

Muhsin yayi murmushi yace"to Allah de yatsare gaba Asim, danna baya kam yariga ya faru" =??

Daga nan yafi ce daga falon, shikuma yaja computer sa yanaci gaba da aikinsa



*** ****** ***


Ganin shirin da ake yi a gidan, yasa Asim Kiran Amina falonsa
Taje tazauna a qasan kafet din d'akin,tana kallonsa, cikin ranta tace shide kullum aiki, inama inada dama wallahi dasai na qwace, mutum kullum babu hutu, daga aiki Sai aiki =?A?


Hankalinsa Yana kan computer daya sake Yana wani aiki, yace mata "akwai maganar danake so muyi"

Tace "to Yaya"

"kishirya anjima akwai inda zamu fita"

Tasake cewa "to Allah yakaimu, zan shirya"

Jinjina kansa yayi, wannan Karon ma be kalleta ba Yana aikinsa yace "medame kike shiryawa, me kike buqata wanda za'a siyo miki?"


Dago kanta tayi ta kalleshi, kamar bada ita yake magana ba, Hankalinsa Yana kan laptop din gabansa, tace "Yaya shirin me kuma?"

Kai tsaye yace "na aurenku mana, Keda Amjad"


Dam! Dam!!
Gabanta yayi wata irin faduwa, cikin sauri tace "Aure kuma? Wanne irin aure Yaya?ni bamuyi maganar dashi ba, be fadamin ba" ta qarasa maganar cikin rikici, kana ganinta zaka san cewa a rikice take

Batare daya Kalleta ba yace "yanzu kinsani"



Idanun tane sukai rau rau, ta kalleshi "nifa inada aure"

Computer gabansa ya ture, yajuyo yazubawa manyan Idonta wani kallo, shide yasan cewa a gabansa aka koreta, kuma da bakin ta tace kafin Ammar yarasu yasaketa, idan ma bai saketa ba to ai yariga yarasu, yaushe tayi wani auren? Tanaso tace masa tasake auren wani mutumin na bakwai kenan ko me? Kode batasan girma da darajar aure ba ne shiyasa zata fara wasa dashi? Sake kallon qwayar idonta yayi yace "yaushe kikai auren? Waye mijin naki?"


Gabanta ne yafara faduwa, cikin alamun tsoro ta dago kanta ta kalleshi sannan tace "Gaka"















Group d'inda basa sharhi insha Allah nadena yimusu posting


Masoyan littafin INSAAF nagode =?O?









Comments
Sharhi =?O?


Amnah El~Yaqoub
' [2/17, 12:07 AM] El~Yaqoub: INSAAF

Writing by:Amnah El~Yaqoub


27&28

Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493




Akwai abubuwa dayawa wanda ya kamata ace na rubuta saboda aso Widad, amma haka na ciresu saboda karma yarinyar tashiga ran mutane dayawa, saina rubuta page daya biyu amma ko sako yarinyar banyi aciki ba, ashe gudun Gara nayi =??, duk da haka ban tsira ba, ya kamata fa ace muna tunawa da mutuwa, bazai iyu a rubuta littafi haka babu wani wanda zai ta6a ran mai karatu ba, kenan ma soyaiya kadai zamu rubuta =??, mutuwa tana kan kowa, wanda basuji Dadin mutuwar Widad ba suyi hakuri please =?O?
Ina masoyan Daddy? Toku matso kusa=?
?


__________


Gabansa ne yayi wata irin faduwa, yanayin fuskarsa ya sauya, yayi quri da ido Yana kallonta cike da mamaki, yace "what? Kinsan me kike fada kuwa?"

Ahankali tadago idonta tana kallonsa, amma takasa ce masa komai, dama tasan cewa hakan zata iya faruwa koma fiyeda haka, daqyar ta'iya daga masa kanta, muryarta na rawa tace "E...eh wallahi, Allah da gaske nake"


Gaskiyar daya hango Akan fuskar yarinyar ne yasa yagane gaskiya take fada masa, but tayaya?, yaushe hakan tafaru? Shida yake gudun Amjad ya aureta ashe shine rikicin yake kansa?Ahankali Ahankali yafara maimaita kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji'un.... Cikin ransa =??
To inhakane menene ma amfanin daga Hankalinsa Akan neman computer? Shida yakusa mutuwa bai saniba? Yana yiwa Amjad kallon gawa ashe shine gawar, =??
Yana yiwa Amjad kallon zai auri bazawara ashe shine yake auren ta bai saniba

Hannunsa yasa ka cikin sumar kansa, yakasa furta komai, yanzu shikkenan Shima bin Widad zaiyi?

Kallonsa tayi, taga yakasa magana, Ahankali cikin nutsuwa tafara magana "tun muna qauyensu Malam mai Allo, shine wanda ya daura mana aure, lokacin bakajin dadi, yafadamin washe Gari zai sanar da kai amma Allah bai nufa ba washe Garin yarasu, idan baka yarda ba zan nunama sadakin daya bani yace shine sadakin aure na, matarsa ma sheda ce, tasan komai, tasan da auren, amma ni banason in qara yin wani aure a rayuwata, Bana fatan ace haqqin mutune yadinga taruwa akaina, Bana fatan ace tasanadina wani ya sake mutuwa, nasan cewa wata qila da haqqin rayukan mutanan da suka mutu ta Sanadina ne yasa har yanzu ban samu iyayena ba, Dan Allah karku min aure Akan aure, inaso ka sauwaqe min, ni bazan sake aure ba har abada.... "tana qarasa maganar hawaye ya silalo daga cikin idanuwanta, ahankli tatashi tafice daga falon, tanaso ta tambayeshi karfe nawa zasu fita? Amma babu Damar hakan Dan taga fuskarsa tayi wani iri kamar zaiyi kuka =??=??



*** ****** ***


Tunda ya zauna a falon yake sakin tsaki shi kadai, ga waya a hannunsa Yana danne danne, Amrah ta kalleshi "Amjad lafiya kuwa?"

Saida yayi Dan qaramin tsaki sannan yace "nida wani Gaye ne muke tafka fada a Facebook, Sai batamin rai yake, shine Nima nace masa inda zan ganshi Sai an qwace shi a hannu na" =?3?

Amrah batasaan lokacin data saki wata irin dariya ba, tace "Kaine zaka daki mutum har a qwace shi a hannunka?"

Shima dariyar yayi "ke duk kurin banza nefa nakeyi, Kinga mutane Sai hakuri suke bani, jisuke wani babba ne, Nima kuma Sai da naduba profile pic dinsa naganshi wani gabjeje, tayaya da hankalina zan yarda nahada hanya dashi? Hauka nake? Saide in bashi hakurima ince ya kamata mubar fadannan haka ">?#?>?#?

Me Amrah zatayi inba dariya ba, sosai takecin dariya sannan tace
"yawwa Amjad, Nika tunamin ma,kaga pic din wannan gayen, last month nahadu dashi"

Wayar datake bashi ya karba, ya kalli gayen sosai, babu qarya ya'iya dressing daga ganinsa Dan wanka ne, yace "A'ina kuka hadu?"

"Facebook"

"to inde Yana sonki da gaske yafuto mana"

Murmushi tayi "Yana sona gaskiya, kuma Nima Ina ganinsa Naga Yamin, amma nace yaushe zaizo, saiyace min Wai bayaso yazo gida da farko, yafuso mufara haduwa awani wajan, Sai kuma yasa time yazo gida"

Amjad ya Girgiza kansa Yana kallon Amrah cike da mamaki "yanzu Amrah idan ance miki yarinya kihau mutum da bala'i, tayaya zaki Ci gaba da kula shi, bayan daga jin wannan furucin nasa kinsan mayaudari ne, kirabu Dashi kawai, ba mijin aure bane, idan mutum yanason aurenki da kansa zai fara miki maganar aure, idan beyi miki ba dazaran kince yafuto zai futo, saboda shirme kin tsaya kina kula wannan gaulan, Karki sake kula shi nafada miki "


Amrah tasaki baki da hanci tana kallon Amjad yanda yadage Yana mata fada saikace wani Yaya Asim, cikin masifa tace"to Daddy"

Kallanta yayi shi ma cikin fishi yace"Daddy kuma? Namiki kama da Daddy ne?"

" to waye zaiyi abinda kayi inba Daddy ba?, kawai daga nunama pic din mutum saika hau yin fada kamar kasamu wata qanwar ka kokuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login