Showing 30001 words to 33000 words out of 80494 words

Chapter 11 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

Ash, yace "baban widad yagida ya ayyuka"

"Alhamdulillahi, ya iyali"

"normal, ina hajiya Lubna"

"taje gida, Bata nan"

"kace yau gwauro ne"

Kafin Asim yabashi amsa ta shigo falon, bakinta dauke da sallama, Muhsin ne ya amsa mata, tazauna a qasan kafet din falon tare bashi littafin tace "Yaya gashi"

Karba yayi ya ajiye a gabansa, sannna yafara yimata yan tambayoyi dangane da science,dakuma wasu na English tana bashi amsa kadan kadan, Muhsin Yana gefe Yana kallonsu

Da karatu yayi Nisa saita saita fara yin Shiru, yayi tambaya yayi tambaya yaji Shiru, gaba ya lura Bata fahimtar komai, haka yayi Shiru yaci gaba dayi mata Bayani, saida yagama tass sannan yafara jefo mata tambayoyi,da farko yace ta karanto masa part of speech, takawo guda bakwai kalau, Sai Ana qarshan ne maimakon tace interjection saitace injection, dariya takama Muhsin amma saiya danne beyiba, kawai qarfin hali yake gani irinna Asim, karatun yayi mata yawa a matsayin ta na wadda tayi karatu a qauye, kamata yayi yafara yimata da kadan kadan ahankali harta saba

Zuba mata ido yayi Yana kallonta, jiyake kamar ya ranqwashe mata kai, yace "gyara na qarshen dakika fada"

Amina tayi Shiru, gashi gabanta Sai faduwa yake, taqaici yakama Asim, ya kalli Muhsin yace "see, yarinyar danake cewa medicine zatayi itace takasa bani amsa"

Kafin Muhsin yabashi amsa yadaka mata tsawa "badake nake ba!!"

Zabura tayi Takoma gefe, jitake dukanta zaiyi, Ahankali murya na rawa tamkar mai shirin yin kuka tace "Yaya ni.... ni nafison... Arabic"

Cikin sauri yace "what? To bazaki Arabic dinba, boko zakiyi, kuma bokonma medicine"

Hawaye ne ya zubo daga idanuwanta, cikin kukan shagwaba tace "Allah nide Arabic nakeso"

Littafin ya wulla mata yace "Kinga tashi, tashi tashi kibani waje tun kafin na zaneki anan, ina fad'ar abinda nakeso kema kina fada, now.... band'ora hannu na ajikin kiba kin zauna kina min kuka, oya tashi kiban waje" =??=??

Hawayen idonta ta share, babu musu ta yunqura tatashi, ta dauki littafinta tafice daga falon


Kansa ya dafe da hannunsa >?&? B&?,ya tuna yanzu wannan takaicin Amjad zai dauka yakai gidansa, cikin damuwa yace "ka auri qaramar yarinya ma koka auri wahala"

Muhsin ya kwashe da dariya harda sunkuya wa, cikin haushi yajuya Yana kallonsa








Sharhi





Amnah El~Yaqoub
'

Writing by:Amnah El~Yaqoub


21&22


Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493



"menene abin dariya anan?"

Muhsin ya qyaleshi saida yagama cin dariyarsa sannan ya kalleshi "nifa Ina ganin al'amarin ta kamar akwai aljannu aciki, why not kakaita wajan malamai, ayi mata ruqiyya ko za'a dace?"

"aljannu kuma Muhsin?"

"of course Asim, saboda babu yanda za'ayi ace dazaran yarinya tayi aure Sai miji yamutu, ai kaima kasan akwai alamar tambaya"

Jinjina kansa yayi "amma tayaya zan kaita wajan malamai Muhsin? Kamar da cin fuska aciki..."

"bawani cin fuska Malam, ka taambayeta mana, ai zata iya sani, bazai iyu ace tanada aljannu amma Bata sani ba"

"OK, zanyi mata"

"yawwa ni ina ganin hakan zaifi"




*** ****** ***


Daga d'akin tafuto tana goge guntun hawayenta, Amrah tana falo tana kallo ita kadai.


Tadubeta "har kun gama karatun?"

"eh mungama Anty Amrah"

"to yanaga kina goge ido? kode dukanki yayi?"

Kafin tabata amsa Amjad ya shigo falon, ya kallesu yace "Amrah, kushirya muje musha ice cream"

Banza tayi ta rabu dashi, ya kalli yanda ta6ata fuskarta, shi kam mamy ta hadashi da aiki, takowa yayi yadawo dab'da'ita yazauna, ya kalleta yace " ai yanzu nadena cemiki Anty, tunda na kusa aure"

Amina ta kalleshi, ashe aure zaiyi shiyasa dazu suke maganar aure shida mamy, Amrah tace "to Ina ruwana kuma, saide kuje, nikam babu inda zani"

Murmushi yayi "haba Anty Amrah tah, Anty na takaina, aini dake kinsan Bama haka ko, nadena, I am sorry nadena"

Murmushi tasaki "to naji, tashi muje"

Tashi sukai, ta kalli Amina, " idan kin shirya muna jiranki amota "

Daga mata kai tayi, sannan tashige dakinsu tana tunanin wanne irin shiri kuma bayan na jikinta? Haka de ta sauya shiga zuwa doguwar riga, takama gashin kanta ta daure, amma duk da haka bai dauru sosai ba,tashiga toilet Dasauri ta wanke fuskarta, Bata shafa komai ba, tayafa mayafin rigar tafuto daga d'akin

Tana futowa taga Widad a falon tace "Widad yaushe kuka dawo?Ina Momynki?"

Dariya Widad tayi, batare data Bata amsa ba, tazari mayafinta tafice daga falon da gudu
Amina ta dafe kanta tace "kai! yau nashigesu"

Cikin sauri tabita da gudu, gudun datake yasa gashin kanta dabai Gama dauruwa ba yake tsalle Yana kad'awa, alokacin su Asim suka futo daga d'akin sa shida Muhsin,suna kallonta tafita da gudu kai babu dankwali, Amina batama San sun futo ba, tana zuwa harabar gidan taga babu Widad, tajuya tana Zagaya gidan anan taci Karo da Anty Lubna tajuya bayan ta tana waya qasa-qasa, cak taja ta tsaya awajan gabanta yafara lugudan faduwa, Ahankali tajuya zata tafi saboda kada tajuyo ta ganta, saita tsinci muryarta tana cewa "Kayi hakuri, karka tonamin Asiri, zanyi abinda kasani, amma karkazo gidan aure na ka tonamin asiri, wallahi zanyi duk abinda ka Umar Eni dashi, to Amma fa matsalar Shima computer yake nema, bai ganta ba, bai San inda take ba, amma insha Allah inde ya ganta, zansa flash na dauke komai dayake ciki, duk takardun da suke ciki da komai da komai zanturo su zuwa flash din, Nima fa Abin Yana batamin rai, komai Insaaf komai Insaaf, nida nake matarsa baisa sunana kodaya acikin harkar dukiyar sa ba "

Kan Amina yayi dummm haka, saita fara jin kunnanta yanason daina aiki, Ahankali ta d'ora hannunta tadafe kanta >?&? @&?
computer? to ai shaf ta manta computer tana wajan ta, dama nema yake? Innalillah...... Yanzu Yaya zatayi? Ta zalunceshi, ta sashi a halin tashin hankali Yana neman abunsa ta hanashi, to Amma ita Insaaf din ba'ita ce Anty Amrah tace mata yar gidan Anty Ishraqa bace? To inhakane menene hadinta da Yaya Asim dazaisa sunan ta Akan komai, gashi har matarsa tana kishi akaan haka, yanzu daama Anty Lubna saboda kudi take zaune da Yaya Asim? Kokuma saboda taga bayansa ne? To ita da waye suke shirya wannan maqarqashiyar? Dole tanada wanda yake Bata umarni, tunda koda yaushe awaya take jinta tana maganar, wani bala'in tausayin sa ya kama Amina, Anty Lubna kuwa sake gyara mayafin kanta tayi taci gaba da wayarta hankalinta kwance "wallahi Allah nasaka masa wannan maganin, wannan shegiyar yarinyar dayazo da'ita ne tamin Sanadin sa, amma da yanzu yaci, yanzu haka saboda ita nafasa kwana nadawo, Dan bansan meze faru ba, idan Bana nan,Kwanaki kamasu nayi cikin dare ita dashi, amma babu matsala kuwa idan nasaka masa gubar wadda zata karya garkuwar jikinsa? bazata kashe shi ba? "

Amina na jin haka tajuya tabar wajan, wannan al'amarin yafi qarfin ta, Gara tafada masa kawai ya dauki mataki da kansa, Abin yafi karfin ta, yafi karfin tunanin ta, bazata iya ita kadai ba, dole ne tasameshi tafada masa gaskiyar abinda take ji awajan matarsa

Compound din gidan tadawo, anan taga Widad, tare dasu Asim da Muhsin, Sai wasa take da mayafinta

Qarasawa tayi duk hankalinta atashe, sakamakon maganar dataji su Lubna sunayi, banda gabanta dayake faduwa, ko sallama bata musu ba ta miqawa Widad hannu tace "Bani mayafin"

Widad tasaki murmushi takama qafar Asim tariqe shi gam tana buya tace "nide wasa zanyi dashi, bazan baki ba"

Asim da Muhsin duk suna kallonsu, haushi yaci zuciyar Asim, danme zata futo haka kanta babu dankwali, kowanne kare da doki suna kallonta =??

Amina kuwa bataga bacin ran nasa ba, saboda tashin hankalin datake ciki ma ya'isheta, hannu tasa zata kamo widad a jikinsa, yarinyar tasake komawa daya bangaren, itama tabita suka fara zagaye jikin Asim, yanda take kokarin kama yarinyar ne yasa jikinta Sai haduwa yake da nasa, yanajin yanda take goga masa abubuwanta a jikinsa, tana nema ta haddasa masa fitina kuma Yaga alama ita ko kadan kamar babu abinda hakan yake haifar mata, yarasa meyasa wani lokacin Bata tsoron ta'bashi kamar wata matarsa, ko tana tunanin shidin Amjad ne dayake shirin aurenta?kokuma saboda tayi mu'amular aure da mazaje dayawa ne?
Wata irin tsawa ya daka musu "Wai miye hakane?!!"

Cikin shagwaba tace "to Yaya kace ta bani mayafi na, su Anty Amrah jirana suke"

Kallonta yayi yace "ohhh itama Widad din kukan zaki mata?" ya qarasa maganar Yana nuna mata Widad, aikuwa Widad tana jin haka tasaki dariya

Yajuya yace "ke Bata abunta"

Babu musu Widad tabata, sannan tayi mata gwalo, hararar widad tayi tace "zan kamaki ne yarinya" =??


Sannan tawuce tabarsu awajan, ko sake kallonsu batayi ba, Asim yabi bayanta da kallo yace "gaskiya na yarda da maganar ka Muhsin, yarinyar nan tanada aljannu, kaduba kaga fa da widad take fada"

Muhsin yayi murmushi "wannan aiba aljannu bane Asim, harda yarinta ma, yarinta ce kawai, shiyasa tabiyewa yarinyar suke wata yarintar" =??


Widad ta hango Anty Lubna, tatafi da gudu zuwa wajan ta





*** ****** ***



Washe Gari lahdi, kowa Yana gida, haka ta tashi sukuku tana tunanin hanyar zata da fada masa maganar dataji Anty Lubna ta nayi awaya, tarasa yanda zatayi ta ganshi bare suyi maganar, Amrah ta kalleta "kalau kike kuwa Minal?"

"lafiya kalau Anty Amrah, mekika gani?"

"Naga kina ta tunani ne"

Murmushi ta qirqiro tace "a a, babu damuwa"

Wayar Amrah tahau qara, tana dubawa taga Yaya Asim ne yake Kira, dauka tayi tana sauraronsa, daga baya tace "to Yaya"

Ajiye wayar tayi tadubi Amina, tace "kije falo, Yaya yana kiranki"

Hamdala tayi a ranta, cikin sauri ta miqe tatafi, har hakan yabawa Amrah mamaki

Tana zuwa falon ta ganshi Yana karanta jarida, sallama tayi masa sannan ta zauna aqasa, jaridar ya ajiye sannan ya nuna mata gefensa "tashi ki zauna"

Ahankali tadago idanuwanta ta kalleshi tayaya zata zauna agefensa? Idan matarsa tazo ta gansu kuma tahau dukanta, Ahankali tace "a a Yaya, nanma yayi"

"ki tashi nace"

Cikin sauri ta tashi tazauna a'inda ya nuna matan, Ahankali yajuyo Yana fuskantar ta,yanda yajuyo yake kallonta saika dauka wasu shahararrun masoyane, yanaso yayi mata maganar Amjad, ya kamata a matsayin sa na wanda yakawo ta gidan ace sun tattauna Akan maganar, ko yaya ne abata haqqinta, idan ta amince da auren shikkenan, idan Bata amince ba Sai tayi karatu, amma Yana fatan ace bazata amince ba, saboda a halin datake ciki yanzu karatu shine gatan ta, zai so ace tayi karatu me Nisa domin ta in ganta rayuwarta har zuwa lokacin da iyayenta zasu baiyana idan Allah yayi suna Raye

Ajiyar zuciya yayi "inaso zamuyi magana ne..."

Gabanta ne yake faduwa, ganinsa agabanta sosai yayi mata kwarjini,gashi yajuyo Yana fuskantar ta, Ahankali ta daga masa kanta

Yace "Akan maganar Amjad ne, kina ganin kamar...babu wata damuwa ne zaki iya..."

Amina tadago kanta ta kalleshi, meyasa yaqi yayi mata maganar kai tsaye? Meyasa yake wata irin hanya-hanya kamar bayason yin maganar? Da alamu duk abinda zai fada mata me wahalar fada ne awajan sa

Dan haka ta katse shi tace"Yaya, Nima akwai maganar danakeso muyi "

Shiru yayi Yana kallonta, kode itama ta ganene bayason yimata maganar shiyasa zatayi abinda zai fishsheta? >??

To bari yaji dame tazo kuma, yace "inajin ki"

"dama.... am dama fa.... Kwanaki ne..."
Daga nan tayi Shiru takasa qarasawa, tunani take a ranta tayaya zai karbi abun? ta wacce hanya zata fahimtar dashi abinda matarsa take qulla masa? Anya kuwa zai yarda? Karfa yace sharri take yiwa matarsa...

Dago kanta tayi ta kalleshi, taga yazuba mata ido Yana kallonta, gaba daya ya tatt???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ara Hankalinsa waje daya yabata, daga kansa yayi, alamun yanajinta taci gaba, Ahankali tafara wasa da yatsun hannunta tace "Yaya, kwanaki naji Anty Lubna tana waya... wai, wai zata saka maka magani acikin abinci, idan Kaci zaka mutu...."

Gabansa ne yayi wata irin faduwa, lokaci daya yanayin sa ya sauya, idanunsa suka furfuto, ya sake kallonta yace "Lubna kuma? Kinsan abinda kike fada kuwa?"

Cikin ranta tace dama nasani, nasan bazai taba yarda ba,to wannan na kwanakin bayan ma kenan yaqi yarda inaga tafada masa abinda taji jiya?

gabanta yaci gaba da faduwa, idanunta ya raina fata, Ahankali tace "Eh Yaya, kuma tasaka maganin a abincin, shine nazubar dashi, alokacin sau biyu tana marina"

Lokaci daya yatafi duniyar tunani, ya tuna lokacin daya shigo gidan yaga tana marinta saboda tazubar da abinci, Anya kuwa yarinyar nan da gaske take? Tayaya Lubna zatayi masa haka? Ita da kanta ta nuna tana sonsa aka hadasu aure to tayaya zataso yamutu? To idan tanaso yamutu su kuma wanda suke son ganin bayansa waye yake turosu?

Ahankali yakamo hannayenta duka biyun yariqe, ya hada idonsu waje daya, gabansa Sai faduwa yake, mamaki tattare saman fuskarsa yace "fadamin....,ki fadamin komai"

Lokaci daya tsoro ya kamata, ganin irin yanayin dayake ciki,to idan yaji harda computer sa take nema Yaya zaiyi?
Ahankali tafara kokarin cire hannunta daga nasa, tana tsoron ace wani daga cikin yan gidan ya shigo falon ya gansu a haka, uwa uba Anty Lubna, idan ita tana had'a jikinta danasa tasan cewa akwai aure atsakanin su, amma shifa? Bai saniba, sannan duk gidan babu wanda ya sani

Yanajin yanda take kokarin janye hannunta daga cikin nasa ya sake ruqo hannun, yaqi Bata Damar qwace hannun, domin ta taqaita maganar tasu Sai tace "Dan Allah Yaya karka sakecin abincin da Anty Lubna zata baka, wannan shine abinda nakeso nafadama, Amma fa Amana" (=?
?)











Da babu Gara dinga ragewa ko kadaanne >??>??







Sharhi









Amnah El~Yaqoub
' [2/14, 12:43 AM] El~Yaqoub: INSAAF


Writing by:Amnah El yaqoub


23&24

Like my page on Facebook =?G? https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493





"Amana"

Yamaimaita kalmar a ransa, Ana cikin magana ta hankali tasako masa wata yarinta Wai amana,wannan maganar ake kira da amana, yazuba mata ido Yana kallonta yaga idonta yayi wani tsuru tsuru, tsananin tsoro yataru yayi mata yawa, kamar ace mata kyattt tafita aguje, tsananin tashin hankalin data hango a saman fuskarsa ne yasa tasake tsorata, har tana dana sanin fadar maganar da tayi, hannunta dake cikin nasa ya sake riqewa kamar zai 6allata yace "waye yafada miki?"

Girgiza kanta tafara yi tana kokarin qwace hannunta tun kafin ya karyata, kafin tabude baki tayi magana ya daka mata wata irin tsawa "nace waye yafada miki?!!!"

"Babu kowa Yaya, amma...."

"dakata" ' Ya dakatar da'ita ta hanyar daga mata hannu
Sannan yasaki hannun ta dake cikin nasa yace "tashi kibar nan wajan"

Cikin sauri ta tashi tawuce daki, Dan dama atsorace take dashi, tana zuwa daki kuwa taji motsin ruwa a toilet alamar Amrah na wanka, kayanta na qauye tabude, ta dauko laptop din ta nadeta acikin wasu kayan, sannan tasake 6oyeta da kyau


Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa acikin ransa, ya saka hannu ya hargitsa sumar kansa kamar sabon kamu, tayaya haka zata faru? A'ina Yarinyar nan taji wannan maganar? Anya kuwa da gaske ne? To tayaya za'a ce Lubna tanason ganin bayansa?

Gaba daya kansa ya kulle, yama rasa wanne irin tunani zaiyi,mutum dayace ta Fado masa, yasan cewa kuma zata kamo masa bakin zaren, Dan haka kai tsaye ya nufi gidan Ishraqa, anan ya sake tadda wani abun mamakin, wannan d'akin daya sameta rannan yauma aciki ya ganta, shide yasan cewa Ishraqa Bata aiki da kanta, saide tasa me aiki tayi mata, saide abinda ya danganci mijinta ne kam Bata wasa dashi, tana kiyaye wannan bangaren, amma Sai gashi yauma yazo ya ganta tana gyaran gado tuquru, zama yayi tare da dafe kansa dayake masa mugun ciwo, yace "Ishraqa akwai matsala"




*** ****** ***

Tunda sukai waya da oga har yau takasa samun sukuni, yanzu tayaya zata zubawa Asim guba, wadda zata karya masa garkuwar jiki? Laptop din de tayi wannan alqawarin, amma guba kam, Sam Sam bazata iya zuba masa ba, to ai idan tazuba masa ma itace a wahale, hatta wankansa kanta zai dawo, komai itace zata masa, Gara ta haqura kawai, to Amma kuma idan batayi ba mutumin nanfa zai'iya zuwa gida yatona mata asiri awajan Asim, ita kuma Bata fatan Hakan, idan mutanan gidan sukaji abinda ta aikata kafin ta shigo gidan haqiqa kowa saiya tsaneta

Tashi tayi tana Zagaya d'akin, Ahankali tafara magana "gaskiya bazan saka masa ba, nahaqura kawai, idan nasaka masa ma nice a wahale, computer de idan naganta dole zan kwashe komai na basu, kodan wannan shegiyar Insaaf din"

"momy ba kince babu kyau Ana cewa mutum shegiya ba"

Ta tsinci muryar Widad tana doko mata tambaya, cikin sauri ta kalli yarinyar taga tana wasa da babyn roba, batasan ma tashi go dakinba

Ajiyar zuciya tayi tace "mekike yi anan? Tashi muje muyi lesson"

Widad ta daga mata hannu, babu musu Lubna ta dauke ta, tayi kissing kumatun yarinyar sannan suka fice daga d'akin






*** ****** ***




Ishraqa tayi Ajiyar zuciya bayan tagama sauraron Asim wanda yake mata Bayani idanunsa yayi jajir, tace "Nifa Asim kwata kwata ban yarda da maganar yarinyar nan ba, tayaya Lubna yanda idonta yarufe a kanka, matarda taqi jinin ace wata mace ta rabe ka itace zata kasheka, to inasu Mamy da kowa da kowa na gidan? Kisan kai aiba qaramin abu bane, kaima daka tsaya ka saurareta kafi 6atamin rai,haka kawai baka Santa ba, bakasan tushen taba, yarinya taga kakawo ta gida, tasamu waje ta wanke, ba dole tayi tunanin rabaka da matarka ba?, ni ranar nan naganta tare da Amrah, inda nasan haka halinta yake dana wanka mata Mari tafice tabarmin gidana, tun tuni kayi gaggawar sallamarta, inma gidan marayu ne kakaita, kokuma kasan inda zaka kaita, inba hakaba kanaji kana gani zata rabaka da danginka "

Dago kansa yayi ya kalleta "gidanki kuma?"

Cikin yatsina fuska Ishraqa tace "Um Wai na rungume ta, bansan meya sanyayamin raina ba harna kulata, nide na fadama, inma baka sallameta ba wallahi da kaina zanzo nafitar da shegiya daga gidan" (=?#?)

Ajiyar zuciya yayi, wannan furucin na Ishraqa shine yad'an kwantar masa da hankali, kuma saiya sake tuna irin soyaiyar da Lubna take masa, komai yimasa takeyi, tagama shagwaba shi, Ahankali yace
"hakane, nima nafi tunanin shirmanta ne kawai, Amma I am sorry Ishraqa, bazan iya korarta ba, ina tausayin ta"

Wannan kalmar tausayin da yayi ne ya sanyaya mata jiki, lokaci daya 'yarta mafi soyuwa a ranta tafado mata, batasan inda take rayuwa ba, tanacin abinci ko bataci, atiti take ko agida, a mace take ko araye, Sai tayi Shiru kawai batace masa komai ba, amma bacin rai kam yarinyar ta6ata mata rai, Wai Kisan kai =? ?
Kallan bedsheet din d'akin yayi yaga ta sauya, yace "mekike yi adakin nan ne?"

Ranta ad'an 6ace tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login