Showing 12001 words to 15000 words out of 80494 words

Chapter 5 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

taji bacci me dadi yafara daukar ta, Akan kunnanta wasu masallatan suka fara Kiran sallar farko, ihun dataji ne yasa tazabura cikin sauri tamiqe tsaye, kamar muryar matar liman takeji tana kuka, cikin sauri tabude kofar d'akin tafuto, qaran Bude kofar da tayi ne yafarkar da Asim daga bacci, Shima yanajin wannan kukan ya futo

Matar liman ta nufesu da gudu tana kuka kamar mahaukaciya, "Amina ku taimaka min, babu Malam yamutu" (=?F? @&?=?3?)

Amina tace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" tafashe da kuka itama, yanzu liman yamutu?jiya jiya yazaunar da'ita yayi mata magana Akan aure amma yau harya mutu? Anya kuwa batada nasaba da mutuwarsa? Gabanta ya tsananta faduwa, idan kuwa hakan ya tabbata haqiqa data shiga ukunta, tazama masifa, tazama annoba kamar yanda su Inna suka fada, Asim kuwa qamewa yayi atsaye, mutuwar tatabashi sosai, Amina kuwa zama tayi a gaban gawar liman tana kuka, ga kukan jiya gana yau, hakan saiya haddasa mata ciwon kai, lokaci daya taji duniyar tafita daga ranta, fatanta daya shi ne Allah yasa itama ta mutu tahuta da wannan masifa, har a kayiwa liman sutura aka kaishi gidansa na gaskiya Amina Bata dawo normal ba

Tundaga mutuwar liman saita dawo Shiru Shiru, saitayi awanni batare da tayi magana ba, Bata jin dadin komai, Bata tunanin tanada Rabon hutawa awannan duniyar, tunani yazama abokin hirarta, Bata damu da magana ba, babbar damuwar ta ma shine wannan auren da liman ya daura mata, batasan Yaya makomar sa zata kasance, tayaya zata tunkareshi da wannan maganar? Idan tafada masa ma qarshanta ya Musata, koba wannan Bama Bata fatan ace wani ya sake mutuwa Ata dalilin ta

Haka gidan yacika da 'yan'uwa, kuma tunda akai mutuwar Bata sake sakashi a'idonta ba, har akai kwana uku, a kayiwa liman sadakar uku data bakwai, yan'uwan matar suka shirya tafiya da' ita garinsu, gida yafara watsewa, Ana cikin haka kuwa Asim yashigo gidan bayan sun gaisa da 'yan tsirarun mutanan ya kalleta batare daya Kira sunan taba yace "kishirya mu tafi"

Itama batace masa komai ba haka tashige d'akin da'aka saukesu tahada kayanta waje daya tafuto dashi, lokacin da sukai sallama da matar liman saida kowa yazubar musu da qwalla,saboda kowa yayi tunanin yan'uwa ne, Amina tana kuka matar liman tana kuka sukai sallama suka tafi


A hanya ma Yana gaba tana binsa abaya har suka qarasa bakin titi, shine da kansa yafara tare musu Mota zuwa kano, amma duk motar daya tare idan yayi musu Bayanin bashida kudi saisuja motar su suqara gaba, sun Bata lokaci awajan sannan wani bawan Allah yadaukesu suka tafi, suna cikin tafiyama babu wanda yake yiwa dan'uwansa magana (>?#?)

Amina kam idonta ta lumshe ma tana tunanin wannan baqar rayuwa Tata, abubuwa sun taru sunyi mata yawa, babu iyaye, babu asali, batasan ainashin takamaimai sunanta ba, ga wannan aure da liman ya daura musu, ta wacce hanya zata fada masa andaura musu aure? Tayaya zata fada masa?Sunyi Nisa cikin tafiya taji ya tambayi Aron wayar direban dayake jansu, itade Bata Bude idonta ba Amma duk abinda yake yi tanaji, number mahafiyarsa yasa ka sannan yakira, saida wayar tayi ringing harta katse ba'a dauka ba, a lokacin kuwa mamy tana zaune da niyya taqi daukar wayar, tasan cewa bazai wuce masu yi mata jaje ba, a kullum haka take amsa kiransu harta fara gajiya,sake Kira yayi a Karo na biyu, Shima saida takusa katsewa sannan ta dauka tare da cikakkiyar sallama abakinta, Shiru yayi yakasa magana duk da kasancewar sa namiji qwalla yaji tana shirin zubo masa, mamy tasake cewa "Salamu alaikum"

Ahankali yace "Mamy"

lokaci daya mamy ta tashi tsaye, tace "Asim,Alhamdulillahi, Allah abin godia, dama nasan baka mutu ba, inaji a jikina zaka dawo gareni Asim"

Murmushin sa mai tsada yasaki yace "ban mutuba mamy, ina nan, mamy Amjad nasan sun kashe shi, kiyi hakuri mamy nakasa tseratar miki da danki" ya qarasa maganar Yana goge qwallar Idonsa

Tuni hawaye yagama wankewa mamy fuska, cikin kuka tace "Amjad Yana nan, yanzu hakama Yana bacci adakinsa, kana ina?"

"mamy kidena kuka mana, bagashi nadawo ba"

Hawayen idonta ta share cikin kuka tace "Allah yakaremin kai dana, Allah yarabaka da sharrin maqiya, kafadamin kana ina saina taho"

Ahankali yace "kano"

Duk firar dayake Amina tana jinsa, da alama da mahaifiyarsa yake magana, wani malulun abu ya tsaya mata awuya, shida yake da maahaifiya har ya kirata, amma ita ba tasan ma ko wacece itaba, batasan me matar tafada masa ba kawai de taji yace "to" daga nan ya kashe wayar yabawa direban, haka taci gaba da tunanin mafita
Har sukazo kano, Bata Dena tunanin mafitaba, tasaqa wannan ta kunce wannan

Kai tsaye ya cewa me motar yakaisu Airport, suna zuwa kuwa yayi masa godia, sannan yace yabashi account number dinsa a takarda, me motar kuwa jikinsa na rawa yarubuta yabashi, Ahankali tabude motar tafuto hannunta dauke da jakar bakko ta kayan ta
Kallanta Asim yayi, shida yake shirin tashin ta daga bacci ashe idonta biyu, me motar yaja abarsa yatafi, ahankli ta matsa kusa dashi ta kalleshi muryarta na rawa tace "Dan Allah... Ina... Inaso kakaini gidan Marayu"

Kallan qwayar idonta yayi, tunda yake arayuwarsa bayan mamy wannan ne Karon farko da yaji tausayin wata macen (=?3?)

Itama dago kanta tayi ta kalleshi tana jiran taji amsar sa, amma Sai taga kawai zuba mata ido yayi Yana kallonta, cikin sauri tayi qasa da kanta, saboda ba qaramin kwarjini yayi mata ba, gashi kuma babban mutum

Dauke Idonsa yayi a kanta batare dayace mata uffan ba, Ajiyar zuciya yasaki shi kadai, tasake kallansa idonta na kawo ruwa tace "Dan Allah..."
sai sharrr hawaye suka zubo mata

Kallanta yasakeyi da tsananin mamaki, koda yaushe kuka kuka ko gajiya batayi? Kafin yabata amsa yaji anyi masa wata irin runguma daga bayansa

Cikin tsananin murna Amjad yace "YAYA ASIM"

Sai a lokacin Amina taji sunansa, ASIM ta maimaita sunan abakinta

Murmushi yayi yace "Amjad yaushe zaka girma ne?"

Mamy ma ta qaraso wajan sa tajashi jikinta ta rungume shi, Shima tsamm ya rungume ta a jikinsa kamar za'a qwace masa ita
Ahankli ta zare jikinta tafara tattaba jikinsa, murdadden dantsan hannunsa ta riqe tace "babu de abinda yake damunka ko d'ana?"

Yace "babu Mamy, inaso mutafi gida akwai maganganun danake so muyi, ina daddy na da Baby da sauran yan gidan?"

"suna nan kalau Asim, basusan mun taho ba, nafiso kawai saide su ganka, amma kafin muje ya kamata kakira Maman INSAAF karkai laifi awajan ta, Dan nasan idan taji labari kadawo baka fada mataba har gida zatazo kuyi abinda kuka saba, kaima kasan sauran "

Daga mata kai yayi sannan ya kalli Amina data zama 'yar kallo yace "muje"

Sai a lokacin mamy da Amjad suka lura da'ita, Amjad yazuba mata ido Yana kallonta sannan yadubi yayan nasa yace

"Wow.... Yaya Asim wacece wannan? She's Preety wallahi Yaya"











Wacece maman INSAAF? shin mahaifiyar insaaf tanada alaqa da Asim ne?

Yaya makomar auren Asim da Amina?

ta wacce hanya zata fada masa wadda zai fahimceta cikin sauqi?

Wanda suke tambayar wacece Insaaf ina fatan yanzu kun samu amsar tambayar ku?




sharhi >??>??






Amnah El~Yaqoub
[2/6, 11:16 PM] El~Yaqoub: INSAAF


Writing By:Amnah El~Yaqoub


9&10


Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493


Dedicated to *FAUZIYA* *S* *MADAKI* My Admin sarkin gyara,=?? ina alfahari dake akoda yaushe =؃?



Sai a lokacin mamy ta lura da Amina, takai kallonta wajan Asim ko zataji yabawa Amjad amsar tambayar sa, amma saitaji baice dashi komai ba, asalima tafiya yafara yi, Ahankali mamy takai hannunta wajan Amina, takamota tace "taho baiwar Allah"

Amina ta dauki bakkon kayanta suka tafi, mamy takama dantsen Asim tariqe gam kamar za'a sake qwace mata shi, Amjad Kuwa hannunsa yariqe Yana tambayarsa "Yaya babu abinda yasameka ko?Allah nagode ma dabasu kashe min kaiba"

Mamy ta kallesu tayi murmushi, cikin ranta tana qara jinjina tsananin shaquwar datake tsakanin Asim da Amjad

Duk mutanan dasuka ganshi inde dama sun sanshi to saisun tayashi murnar dawowarsa, idon Amina yayi tsilli-tsilli yau gata a Airport, saida suka kammala komai sannan sukahau jirgin dazai tashi zuwa Lagos

Acan ma suna sauka motoci guda biyu suka gani na gidan sunzo suna juransu, already mamy tayi magana suzo tun kafin sutaho, rarraba idanunsa yake kozaiga daya daga cikin direbobin dasuka rakasu Yola, amma babu ko mutum daya daga cikin su, hakan yana nufin dama can sun shirya barin gidan kenan shiyasa aka hada baki dasu domin aga bayansa, to waye awaje dayake son ganin bayansa? Waye shi? Yasan cewa a cikin gidansu de babu, suna zaune lafiya cikin qaunar juna dukansu, family ne da suke da hadin kai sosai, to Amma tayaya wani a waje zaizo yahada baki da mutanan gidan domin a dauki ransa?

Wannan tunanin da yayi ne yasa shi ciwon kai,lumshe Idonsa yayi tareda dafe kansa, mamy da Amjad har rige rigen tambayar sa suke "lafiya kuwa?"

Bece dasu komai ba, kawai de ya d'aga musu kansa alamin babu komai
tun kafin su qara so wajan motar duka drivers din suka zo suna masa sannu da zuwa cikin farin ciki ganin yadawo gida, Allah ya baiyana shi

Awannan lokacin kam Amina tazama yar kallo, daga ganin yanda mamy take nan-nan dashi tasan cewa ba qaramin so suke masaba

Suna zuwa unguwar kuwa tasake zama yar qauye tuburan, domin kuwa saida aka tantancesuma suka shiga, hakan yana nufin unguwar akwai tsaro, Karon farko data fara tunani Akan abinda yasamu Asim, abinda yafara zuwa ranta shine unguwa irin wannan me cike da matakan tsaro tayaya wani daban zai shigo har inda kake ya cutar dakai batare da an kamashi ba?harbi fa ba qaramin abu bane, idan abun yazo da qarar kwana shikkenan mutum yamutu, amma a harbeka ajefaka cikin ruwa wacce irin tsanace wannan? Gaskiya dole ya shiga cikin damuwa,tunanin ta yayi Nisa har suka qara so cikin gidan, gida ne tsararre daya amsa sunansa,bazakace a cikin Nigeria yake ba,ga motoci Kala Kala da suke adane agefe,Bude musu motar a kayi, sannan suka shiga cikin gidan, mutum uku ne a zaune cikin nashahurin falon nasu, mata biyu matasa dakuma yar qaramar yarinya, mamy tana yin sallama suka maida kallansu bakin kofar, Gaba dayansu suka miqe tsaye cike da mamaki, da gudu Lubna tataho ta rungumeshi, lokaci daya tasaki kuka tana shafa kansa, itama dayar tana qarasawa tahada dashi da Lubna ta rungume su tana kukan itama, yar qaramar yarinyar cede tataho ahankali, hankalinta a kwance tana wasa da teddy ta tsaya awajan, mamy kuwa murmushi take amma hawaye ne yake zuba daga idonta

Amjad yayi Shiru yana kallon su, duk Sai kuka suke sun rungume shi, gyaran murya yayi sannan yace "to.., to to, Anty Amrah kukan ya'isa haka saiki cikashi"

Wadda yakira da Amrah tadago ta watsa masa harara, kallanta nasake yi sosai, kana ganinta kaga yar qwalisa kuma zakayi tunanin Amjad din ya girmeta, amma kuma gashi yakira ta da Anty Amrah

Shima dauke kansa yayi daga wajan ta Yana yatsina fuska, da alama basa shiri da juna (=??)

Amrah ta kwantar da kanta akafadar mamy cikin shagwaba tace "mamy..."

Mamy tashafa kanta,sannan tasa hannu tagoge mata hawayen idonta, takasa cemata komai

Amjad ya sake kallon Anty Lubna data maqalqale Yaya Asim ko kunyar mamy bataji yace "to Laila majnun, ai gaisuwar ta'isa haka"

Gaba dayansu sukasa dariya, sannan Lubna tacikashi, yar qaramar yarinyar ce ta kalli yaya Asim tace "Uncle ni nayi fishi dakai, shine katafi America kaqi dawowa ka manta Dani"

Kallansa yakaai wajan yarinyar yayi murmushi, sannan yasa ka hannu yadagata Sama, hannu tasa taja hancinsa tace "Daddy kakawo min tsaraba? Mamy tace katafi America kuma zaka dawo, zaka tahomin da jirgin Sama mai tashi"

Murmushi yayi yace "Am sorry my daughter...Daddy yayi laifi, gashi bankawo miki jirgin samah ba, amma zamu shiga jirgi muyi yawo, ki kalli ko'ina saimu dawo gida ko?"

"eh Uncle, I miss you" tafadi haka sannan tayi kissing din kumatunsa, daganan suka qarasa cikin falon

Amina de kallonsu kawai take, jikinta duk yayi sanyi, saida suka zauna sannan Anty Lubna ta lura da Amina, dammm!!! Gabanta yayi wata mummunar faduwa, haka kawai taji yarinyar Bata kwanta mata ba, wacece ita? Menene yahadata da mijinta har suka taho tare? Itafa Bata fatan kowacce mace ta ra6i mijinta, zata iya yin komai Akan mijinta, sosai take mutuwar sonsa, tsanar yarinyar ta darsu a cikin ranta, ta yatsina fuska tare dayin qaramin tsaki ta dauke kanta

Amrah datake zaune kusa dashi tadubeshi tace "Yaya, yakamata kayi wanka kahuta, zanshiga kitchen da kaina in hadama girki me dadi, yau ranarmu ce, Bata Anty Lubna ba" taqarasa maganar tana kallon Anty Lubna, ahankli Lubna tayi mata dariyar yaqe kamar zata fashe da kuka (=??)

Ajiye yarinyar datake hannunsa yayi, yashafa sukarta tace "My Widad, daddy zaiyi wanka OK?"

Tace "eh Kayi wanka kazo kabani labarin America"

Murmushi yayi ganin yarinyar da gaske ta yarda da maganar da Mamy ta shirya mata, sannan ya kalli Amrah yayi mata nuni da Amina "Amrah, kikaita d'akin ki tayi wanka, kiyi mata abinda ya dace"

Yana fadar haka yafara tafiya zuwa dakinsa, Luban ta Mara masa baya, Amjad ya d'aga murya yace "Yaya baka fada mana Sunan taba"

Cak yaja ya tsaya batare daya juyo ba

Mamy ma ta kalli Amina da murmushi dauke a saman fuskar ta tace "Yata Yaya sunan ki?"

Wasa take da yatsun hannunta, Ahankali tadago daradaran idanunta tace "Am.. Ami...."

Kafin ta qarasa taji muryar Asim cikin kwanciyar hankali yace "MINAL"

Amjad yace "gaskiya sunan Yamin dadi" yafadi hakan yana Dora hannunsa Akan setin zuciyar sa (>?#?)

Asim ya kalleshi yayi cikin dakinsa, itama Lubna tashiga sannan tarufo mana kofar (=??)

Amrah ta kalli Amina tace "Minal taso muje"

Bakkon kayanta ta dauka tabi bayan Amrah, ita kuma mamy ta dauki wayarta domin Kiran Daddy

suna zuwa d'akin taji waani qamshi ya dake ta,saida ta nuna mata komai sannan tafuto tabarta a d'akin

Tana futowa daga wanka tasaka doguwar riga ta atamfa daya daga cikin kayanta
Babu abinda tashafa ko mai babu bare powder, I fuskarta tayi fayau, sallah tafara ramawa sannan tazauna adakin tayi Shiru tana tunanin rayuwarta, har yau takasa Bude ledar da Inna ta Bata, wacece ita? Bata saniba, menene sunan ta? Bata saniba, Ahankali tabude jakar tafuto da ledar, sannan tafara kunce qullin dayake jikin ledar, gabanta yafara tsananta faduwa, hannunta ya dauki wata irin rawa, tana Gama kuncewa taci Karo da wata tsaleliyar riga ta Yara fara tas, doguwar riga ce amma taji adon net, hawaye ne suka fara tsiyaya daga idonta, muryarta narawa tafara girgiza kanta tana cewa "A a... A a... Bahaka bane, niba yar tsuntuwa bace, kune Iyayena Inna"

Haka take kuka tana magana ita kadai kamar ta fita daga haiyacin ta, rigar ta daga ta rungume ta afuskarta tana matsanancin kuka cikin kuka tace "ya Allah ka baiyana min iyayena" qaran wani abu taji yafado daga qasan rigar, Ahankali tabude idonta takai kallanta gareshi Dan qaramin zobe ne na gold amma nayara, hannunta har rawa yake ta dauki zoben tana kallonsa, yayinda idanuwanta suke zubar da hawaye, zoben ta kalla sosai a yanzu kam yayi mata kadan ta sakashi a hannunta, bazai shiga ba, kwalliyar zoben ta kalla taga anyiwa harafin { i } wata irin kwalliya, idonta Akan wajan tace " i ?" tome yake nufi? Iman? Inaya? Intisar? Kokuma iklima? Girgiza kanta tayi ta hada rigar da zoben ta rungume taci gaba da kuka, adede lokacin Amrah tashigo d'akin taganta, jikinta ne yayi sanyi, Ahankali ta qaraso ta ajiye abinci agabanta tace "Minal meyafaru kike kuka? Ko wani abun aka miki?"

Hannu tasa ta share hawayen sannan ta girgizawa Amrah kai

Batare data yardaba tace "to kiyi hakuri, ga abincinki nakawo miki, idan kingama ki kwanta ki huta"

Nanma Batayi mata magana ba kawai de tasake girgiza mata kai alamun to

Amrah tatashi tafuta daga d'akin har tana waiwayenta

Tana ganin fitar Amrah tamaida rigar da zoben cikin Jakarta, sannan tashige toilet ta wanke fuskarta, tadawo taci abincin Dan kadan, sannan tafara istigfari da yatsun hannunta, ahaka bacci yayi gaba da'ita a zaune




*** ***** ***


Da daddare suna zaune shida Mamy da Daddy afalon Daddy, kansa aqasa, ya sauya kaya zuwa qananu baqin jeans dakuma riga milk color, yayi masifar yin kyau, sumar kansa sai sheqi take, Daddy yace "Kaci gaba da Addu'ah my son, insha Allah nayima alqawarin Nima zan tsaya tsayin daka Inga an nemo wadannan mutanan da suke son ganin bayanka, ka kwantar da hankalin ka kaji, ai kunyi magana da commissioner of police ko?"

Ahankali kansa aqasa yace "eh"

Mamy ta kalleshi tana jiran taji qarin Bayani, saita ji Shiru, wannan hali na Asim Yana Bata mamaki, ace iyayenka ma suna ma magana amsa saide ta kasance ataqaice?

Dago kansa yayi suna hada ido da'ita ya sunkuyar da kansa, Dan yasan zai samu Rabon harara ne kawai, to Yaya zaiyi? Kullum de haka ake masa, za'a kawo masa farmaki amma maganar de itace guda daya za'ayi bincike za'ayi bincike amma daga baya kuma saide aji Shiru, ahaka case din zai mutu

Daddy ma da yaji Shiru yasan bazai sake samun wata amsar ba, Dan haka ya sake kallonsa yace "Toya kukai dasu?"

Yanzun ma kamar bayason maganar yace "Sunce zasu tsaurara" (>?#?)

Mamy ta dafe kanta da hannunta (>?&? @&?)
Tace "me zasu tsaurara? Kayi Bayani mana"


Kansa yadago ya kalleta yace "bincike"

Kafin mamy tasake bashi amsa anty Lubna tayi sallama tashigo cikin d'akin tace "Mamy angama hada dinner"

Tace "to Lubna gamunan futowa"

Daddy ya dauki waya Yana Kira daga nan yayi compound

Ahankali yadago kansa yace "mamy gameda yarinyar nan"

Mamy tazuba masa ido tana kallansa, tanaso taga yanzu zai Bude baki yayi mata Bayani ne kokuwa Shima Bayanin bazai Bude baki yayi ba

Cikin rashin damuwa tace "inajin ka"

Saida yayi kalar tausayi da fuskar sa sannan cikin shagwaba yace "Mamy batada kowa"

daganan kuma Sai yayi Shiru =??


Mamy ta jinjina wannan qarfin hali na Asim a cikin ranta, kallansa tayi cikin ranta tace zanyi ma ganinka, amma afili saitace "Allah sarki, to madallah"

Cikin sauri ya kalleta, ganin ta dakatar da maganar tasu daga nan, yayi Shiru Shima Yana jira yaji ko akwai abinda zatace amma Sai yaji Shiru (=?
?)

Ya kalleta yace "mamy inaso ta zauna tare damu kafin Allah yakawo iyayenta"

Murmushi tasaki ganin yabude bakinsa yayi mata magana, tace "Asim, kaga kadena saka damuwa aranka, Sai kwanan ka yaqare zaka mutu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login