Showing 24001 words to 27000 words out of 80494 words

Chapter 9 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

hannunta tariqe tace "Bari kiji in fada Maki, Kinga idan zaki sake acikin gidannan ki dinga harkokin ki toki sake, wallahi idan kika tsaya Anty Lubna tana marinki, bakya ramawa, rainaki zatayi, kisaki jikinka, kema gidanku ne, ki dinga daukan wanka kina kwalliya, kisaki ranki, kiyi walwala, kiyi Fara'ah da dariya kamar kowa, babu wanda yataba ganin dariyarki a gidan nan Minal, kullum fuska babu Fara'ah kamar fuskar Yaya Asim "(=??)

Murmushi tayi mai ciwo, tatuno asalinta, ba tasan wacece itaba,ba tasan iyayenta taba, waya sani ma ko shegiya ce shiyasa aka wullarta, idanunta yayi raurau kamar zatayi kuka tace"wacce irin walwala Anty Amrah,banda kowa, bansan tushenaba, bansan ta Yaya aka haifeni ba, ina Naga wani Damar da zanyi kwalliya?Kuma ni ban'iya Bama "

Amrah tasake matsowa tace" Minal, kowa baya wuce qaddarar sa, ni kinsan tawa kaddarar ne? Nayi soyaiya da Al'amin, munshaqu da juna, kowa Yana farin-ciki da hakan, saida nagabatar dashi awajan Daddy da Mamy suma suka ce yayi, bashida matsala, Rana daya yazo wajena Yana kuka yacemin anyi masa mata agida, auren dole za'ayi masa, nashiga cikin damuwa,Yana kuka ina kuka, alokacin yace muyi alqawari bazamu taba rabuwa da juna ba, komin Daren dadewa injirashi zaizo muyi aure,lokacin ina shekara a shirin da biyar,Minal shekara daya tawuce, biyu ta wuce, Shiru babu labarin Al'amin, ni kuma abin baqin cikin shine yanda na yarda dashi, duk abinda yafadamin ina yarda dashi, saida abin ya ishi Yaya Asim yaje neman Al'amin da kansa, domin yaji meyake faruwa ne, lokacin dayaje bai samu Al'amin ba, amma yahadu dawani maqocinsu, anan aka sanar dashi cewa Al'amin ba auren dole aka masa ba, kawai yaudara ta yake, yarinyar daya aura ma yar unguwar suce,kuma kowa yasan Al'amin Yana son yarinyar, a ranar da Yaya Asim yazaunar dani yayimin fada na hakura da Al'amin, kwana nayi banyi bacci ba, Minal niban taba zaluntar kowa ba, ina zaune da kowa lafiya, amma ga abinda wanda nayarda dashi yayi min, har gobe idan nayi sallah ina roqon Allah, idan nice na zalunceshi, Allah yasa ka masa, idan shine ya zalunceni Allah yasa ka min, Minal shekaru na talatin yanzu babu aure, Abin Yana damuna sosai, amma babu yanda zanyi da qaddarar ubangiji, gashi ina walwala ta, ina harkokina kamar kowa, duk abinda yasamu Bawa yamiqa lamuransa ga Allah Minal, da wannan tunanin da kike da Addu'ah kika Dage da'ita, zaifi, amma Dan Allah ki saki ranki mu dinga abinda mukeso a gidan nan, ni tunda naganki sainaji kamar nasami 'yar'uwa, tunda dukansu yan'uwan nawa maza ne, ba kamar mace ba"

Minal tasaki Ajiyar zuciya ta kalli Amrah tace" yanzu Anty Amrah kedin har kinyi shekara talatin? Naga jikinki bai nuna hakan ba"

Amrah tayi murmushi tace "inda nasake godewa ubangiji na kenan, yanzu babu wanda zai ganni nida Amjad yace nagirmeshi"

Zaro ido Amina tayi tace "waida gaske kinfi Yaya Amjad?, dama shiyasa yake cemiki Anty Amrah?"

Murmushi Amrah tayi tace "na fishi Minal, shekara daya nabashi, inde Kasa Allah acikin lamuranka ai zai taimakeka Minal, kema kisaki jikinki, kiyi gayu, ki daina yin Shiru, kuma inde kwalliya ce Karki damu zan koya miki"

Cikin mamaki tace "gaskiya hakane Anty Amrah, insha Allah Nima zan kamanta kamar yanda kika bani shawara, kuma dama Yaya Asim yace zai tayani duba iyayena"

Amrah ta kama ha6arta tana kallon Minal tace "Wai yaushe har kuke haduwa ne kuke fira ke dashi?, nifa mamaki nake, ganinake kamar ba Yaya Asim dinmu ba, Anya kuwa Minal babu wata aqasa?"

Rabonta da shagwaba harta manta, amma yau saita tsinci kanta dayin shagwabar, tace "Allah Anty Amrah babu komai"

Amrah tace "ai shikkenan, idan tayi tsami maji" (=? ?)
Daga nan tafuto daga d'akin tana tunani a ranta, Amjad dinne zai samu kokuma Yaya Asim? >??=??




*** ****** ***









Dawowarsa kenan daga wajan aiki, fuskarsa babu wata Fara'ah kamar kullum, Yana sanye cikin suit da tayi masa kyau sosai, Kai tsaye d'akin Mamy yawuce, Yana zuwa ya ganta tana sakawa d'akin nata turaren wuta, brief case dinsa ya ajiye Akan gadon, sannan yacire jacket dinsa, itama ya wullata kan gadon, sannan yafada gadon Shima ya kwanta, tare da fadin,"Wash! sannu mamy" sannan ya lumshe Idonsa, inda ace zai samu maiyi masa tausa yanzu daya so hakan

Murmushi tayi tace "kaje wajan matarka ne?"

"no, ban shiga ba, sonake nafara ganinki mamy"

Tace "naji, to ai kaganni, kaje kaga matarka, Kaci abinci saika kwanta acan kahuta, cinyata Bata hutaba, gadona ma bazaku barshi yahuta ba Asim"

Murmushi yayi yabude Idonsa batare da yayi magana ba

Turo kofar d'akin tayi ta shigo bakinta dauke da sallama, jin zazzakar muryar ta ne yasa yakai Idonsa ahankali ya kalli kofar

Idonsu ne yahadu dana juna,Yana daga kwancan yazuba mata ido, Idonsa ne yasauka Akan qirjinta, yatuno lokacin data rungume shi, yaji wani irin laushi, cikin sauri ta dauke idonta itama, tana tuno ranar data fada jikinsa ta rungumeshi, da yanda ya sake matseta a jikinsa Yana sakin Ajiyar zuciya , shi kuwa Kasa dauke Idonsa yayi a kanta, yanajin wani irin yanayi na shigarsa

Gaba daya saita diririce tarasa mema zatace, amma data tuno shawarar Anty Amrah, saita ji qwarin gwiwa yazo mata

Wani irin murmushi tasaki tace "mamy sannu da aiki"

Sake Bude Idonsa yayi ya kalleta da tsananin mamaki, dama yarinyar nan tana murmushi?

Mamy kuwa kallonta tayi tace "sannu Minal, yau kece adakin nawa?"

Gabanta ne yafara faduwa ganin yanda yazuba mata ido Yana aikin kallonta, tace "eh mamy, dama nazo neman Anty Amrah ne"

"Amrah Bata nan inaga tana wajan Lubna, kije d'akin Lubna may be suna tare" (>?#?)

Cikin ladabi tace "to mamy kawo na qarasa miki aikin"

Mamy tayi murmushi tace "a a Minal, jeki hutawarki, Aina gama ma"

Tace "to mamy afuto lafiya"

Sannan ta kalleshi, cikin sauri yadauke kansa, itama cikin ranta tace bayan nakama din, amma afili saitace "Yaya ina wuni"

"lafiya"

Abinda yafada kenan ya lumshe Idonsa, can qasan ransa yanajin Dadin yanda tafara sakin jikinta da 'yan gidan, laptop dinsace tafado masa, lokaci daya yanayin sa ya sauya


Tashi yayi, yafara daukan jacket dinsa zai fita, mamy ta dubeshi tace "Asim qaninka fa yabani saqo wajanka"

Kallanta yayi sannan yadawo kan gadon ya zauna yace "to mamy"

Itama zama tayi sannan tace "yace afada maka yanason auren Minal, ni kuma na amince masa"

Wata irin faduwar gaba ce ta ziyarci Asim, harya Kasa 6oye hakan saida yadora hannunsa Akan qirjinsa, mamy tana ganin yanayin sa mamaki ya kamata, Anya kalau Asim yake kuwa? Hannunta ta Dora Akan kafadarsa tace "lafiya kuwa?"

Kansa ya jinjina yace "lafiya mamy"

Bakomai ne yasa gabansa faduwa ba Sai tinawa da yayi yanda mazajen da Amina ta aura suke mutuwa, aure shida kowa Yana mutuwa, hakan yana nufin Shima Amjad kenan idan ya aureta mutuwa zaiyi? >??
Anya kuwa zai yarda da wannan maganar? To ai kuma mamy zata tambayeshi menene dalilinsa naqin yarda?

Mamy ta kalleshi da kyau tace "kayi Shiru Asim, ko baka amince bane?"

Fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "a a mamy, Allah ya tabbatar da Alkhairi"

Daga nan ya tashi ya dauki kayansa yafita daga d'akin cikin tashin hankali, da kallo mamy ta bishi, taga gaba daya yanayin sa ya sauya, Anya kuwa Asim bayason Minal? Meyasa yanayin sa ya sauya lokaci daya haka?

Yana futowa daga d'akin yafara furta kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, tayaya zai Iya futowa fili ya fadawa mamy cewa Amina duk mazajen data aura mutuwa suke? Hakan kamar tonon Asirin yarinyar ne
Dakinsa yashige, yaga Lubna da Amrah suna ciki, brief case dinsa kawai ya ajiye yafuto, Amrah tana masa sannu da zuwa ya amsa batare daya Kalle taba, daga nan yafi ce daga gidan, bai zarce ko'ina ba Sai wajan babban abokin sa Muhsin Wanda Shima acikin unguwar yake, a compound din gidan Muhsin ya tsaya Yana zagaye wajan cikin tashin hankali bayan yakira shi awaya

Muhsin yafuto daga gidansa yace "abokina mu qarasa ciki mana"

"no Muhsin nanma ya'isa"

Kallansa yayi da mamaki yace "amma lafiya kuwa?"

"lafiya, amma ba qalau ba" (>?#?)

Muhsin yace "tooo, to bari nasa a kawo mana abin Zama, amma ya zakazo gidana kuma mu tsaya atsaye"

"ai maganar danazo da'ita Muhsin Bata zama bace" (>?#?)

"ikon Allah" cewar Muhsin, sannan ya sake cewa "to inajin ka, meyake faruwa?"

"ina yarinyar nan dana baka labari nazo da'ita?"

Muhsin yace "eh nagane, koba Amina ba?"

Girgiza kansa yayi yace "no, call her Minal"

Mamaki ya kama Muhsin, yace "tonaji, meyake faruwa ne?"

"Muhsin komai ma yafaru, Amjad ne yake son aurenta"

"to menene a ciki? Ai wannan abun murna ne"

"awajan ka kenan, Muhsin yarinyar nanfa duk wanda ya aureta mutuwa yake, maganar gaskiya ina tsoron Amjad ya aureta Shima yamutu, aurenta shida, duk mazan basa wuce sati daya sun mutu, tayaya zan Bari ya aureta? Idan kuma Shima yamutu fa?"

Muhsin ya kalleshi sosai, bayan tashin hankalin daya hango a fuskarsa harda tsananin kishi ma, kafadarsa ya dafa yace "to menene aciki? Asim kowa fa yamutu kwanansa ne yaqare, idan Amjad bai aureta ba Kaine zaka aure ta?"

Cikin sauri yace "wa? ni? Wannan qanqanuwar yarinyar?to tamin me?"

Muhsin yayi dariya yace "tamaka abinda zaisaka kuka da ihu wallahi, d'an renin wayo, to idan ba kishi kakeba menene nashiga damuwa haka?"

Cikin zafi yafara yiwa Muhsin magana "saboda inason dan'uwana, kuma bazan Bari inaji ina gani yaje yamutu ba, tayaya zanyi kishi Akan hakan, kawai banaso Amjad yamutu ne, kuma ni Bana kishinta"

Muhsin yayi murmushi yace "to shikkenan, muyi musu Addu'ah kawai, shi ne mafita"

Kallan Muhsin yayi, wato har abinma ya tabbata kenan daza'aje ga yin Addu'ah? >??
kasa cewa komai yayi, daga qarshe ma saiyace "Sai anjima Muhsin"

Muhsin yayi murmushi yace "to saimun hadu"

Shima yajuya cikin gida cike da mamakin abokin nasan, haqiqa Asim Yana kishin yarinyar nan, gaskiya zaiso ace yaga wannan yarinya kosau daya ne, yaga yarinyar da tayi nasarar sace zuciyar abokin nasa, dukda da alamu shi Asim din baisan cewa yafara kamuwa ba



Yana futowa daga gidan ya tsaya a waje, shida yazo wajan Muhsin ko zaisamu wata shawarar wadda zaisa afasa wannan auren, shine zaice masa ayi musu Addu'ah? To yanzu Yaya zaiyi? Kode wajan Ishraqa zaije?

Nan take ya yarda da shawarar zuciyarsa, Yana zuwa gidan Ishraqa maigadi ya rissina ya gaidashi kasancewar ba boyaiye bane, har falon nata ya shiga, yazauna Akan kujera

Gidan yatsaru sosai, an narka masa dukiya kamar baza'a mutu ba

'yar aikinta tazo da sauri ta kawo masa abin motsa baki, baima kalli abinda ta ajiye masa ba, yace "ina Antynki?"

Saida ta rissina sannan tace "tana ciki Yallabai, Bari a kirata"

Daga mata kai yayi, tare da jingina da kujerar yarufe Idonsa

Dawowa tayi tace "Yallabai tace kashiga"

Bude Idonsa yayi, sannan ya tashi ya nufi d'akin dayaga tashiga, wanda Bana Ishraqa bane, shi kansa duk zuwan dayake gidan, bai taba shiga cikin dakinba

Yana shiga d'akin yaga wasu hadaddun photuna na yarinya dabata wuce shekara biyu ba, chocolate beauty ce yarinyar, babu ta inda take kama da Ishraqa, ga wani gado na Yara agefe harda matakalar da zata kaika saman gadon, banda uban kayan wasa dayake zube acikin d'akin, Ishraqa Yagani tana ta faman mopping din d'akin (>?#?)

Ahankali yazauna tare da dafe Kansa (>?&? B&?)

Tanaganin haka, tasan cewa ba kalau ba, tadawo gefensa ta zauna tace "Asim lafiya kuwa?, waye yamutu?" (=??)

"lafiya Ishraqa, ke kinji ki da wata magana, kawai kuma daga ganin yanayin mutum Sai maganar mutuwa? banjin Dadin jikina ne"

Tace "sannu, amma ka fadawa Lubna ne?"

Kansa ya Girgiza yace "ba tasan ma nataho nan ba"

Tausayin sa ya kama Ishraqa, kullum inde Yana cikin damuwa tarasa meyasa Lubna Bata kwantar masa da hankali, tace "a a Asim, kafadamin mana, menene yake faruwa?"

Ahankali yadago kansa yace "akwai yarinyar danazo da'ita rannan, saboda ita ne"

Ajiyar zuciya TASAKI tace "menene damuwar?"

"kawai de Akan maganar aure ne, Amjad yanason auren ta, ni kuma banso"

Tace "tokai sonta Kakeyi ne?"

Baqin ciki ya kama Asim, Wai meyasa kowa yake masa Kallan yanason Minal ne? Fisabilillah me wannan yarinyar zata iya Masa? Yarinya kullum kuka, tayaya zata iya tarairayarsa? Memakon ta bashi kulawa ma ai saide yaqare a rainonta (=??)

Danhaka yayi Shiru baice da Ishraqa komai ba, yaga alama itama bazasu daidai ta ba, yadaga kansa ya kalli d'akin, dakuma uwar dukiyar da aka narkawa d'akin, yace "me kike yi anan d'akin? D'akin waye?"

Jikinta ne yayi sanyi kalau, tayi Shiru takasa ce masa komai, Shima yasake kallanta yace "gaba daya kin maida d'akin kamar d'akin rainon Yara, ko 'yarki ce aciki ai Sai haka"

Kallansa tayi, wannan Karon hawaye ne suka zubo mata, yajuya ya kalleta yace "subhanallah... Meyafaru Ishraqa?"

Hawayen idonta ta share tace " d'akin tane"

Cikin sauri yace "Wai wa?"

Kai tsaye tace "INSAAF"

mamaki ya kamashi sosai, yace "Ishraqa Wai wacece insaaf ne? Menene hadinki da'ita?tsawon shekarun nan ya kamata ace nasan ko wacece"

Hawaye ne yasake zubo mata, Ahankali ta kalleshi fuska cike da hawaye tace " 'yatace Asim"

Cikin sauri ya kalleta yace"what?"

Girgiza masa kai tayi alamun hakane, sannan tasa hannu ta share Hawayen idonta tace" 'ya tace da qaddara tarabani da'ita tun tana shekara biyu a duniya, kayi hakuri Asim, bantaba boyema komai nawaba Sai wannan, Asim inada 'ya Nima, wadda muke qaunarta kamar hauka nida EL HAMEED, ita kadai muka Haifa alokacin danayi shekara daya da auren sa, kuma har yanzu bansake haihuwa ba, wayasani. ma ko banda Rabon ganinta harna koma ga mahalicccina, amma ina fatan ace duk inda insaaf take ta kasance mai taimakon naqasa da'ita, mutane su sota, tayi farin jini awajan kowa, tun lokacin da muka dawo Lagos muka ware mata wannan d'akin, muka zuba mata komai acikinsa, har yau gani nake kamar zata dawo gareni, shiyasa kullum babu ranar fashi sainazo nagyara mata dakinta "

Asim yayi Shiru kamar ruwa ya cinye shi, shida yazo da matsala gashi ya tadda wadda ta take tasa (=??)
Sai da aka jima caaan, sannan yace" yanzu Ishraqa kinada yarinya amma kikasa sanar dani? "

" Asim banason tuna labarin ne, da gani har El Hameed babu wanda bashida hawan jini saboda rashin insaaf "(=?F? @&?)

Cikin damuwa ya kalleta yace" to yanzu tana ina? Yaya akai kuka rabu? "

" labarin yanada tsawo Asim, amma zan samu lokacin saina fadama abinda yayi silar rabani da yarinya ta, dakuma yanda akai ta mallaki dukiya mai tarin yawa "

Tana kaiwa nan, wani Hawayen yazubo mata, kallanta yayi cikin tausayi, a ransa yace
"like Minal, abu kadan kuka" (=??)

Yace "kiyi hakuri Ishraqa, amma why not kije ki dauki widad, na baki ita"

Murmushi tayi tace "kuma mamanta fa? Lubna bazata bani 'yarta ba, Dade nice inda ace insaaf tana nan da saina baka ita ka aureta, harka samu kulawa sosai irinta larabawa"

Cikin sauri Asim ya katseta "haba haba Dan Allah Ishraqa, menene hakan? Kuma kirasa da wadda zaki hadani Sai 'yarki? da girmana da komai saina tsaya atsaye yarki ta shiryani, ai kema kinsan bazai iyu ba, in auri 'Yata, tacikina"

Yanda ya daddage Yana fada kaikace auren aka daura masa da yarinyar,harda wani
'yarsa tacikinsa kamar shine ya haifeta, Sai abinma yabata dariya, tace "Asim, Wai me ka daukeni ne? Bazan haifi yarinya in baka aurentaba? Wai tukunna ma wata nawa kabani ne? Sai wani abu kake kamar kai kafi kowa shekaru a duniya, to wallahi Kar insaaf tadawo kazo kanamin qaramar murya ehe" (=??)




masu son Insaaf complete kuyi hakuri babu


masu son complete dinsa zasu siya suma ina basu hakuri a kan haka


masu cewa a dinga turowa sau uku arana suyi hakuri ina zuwa makaranta


masu cewa a dinga yi safe da yamma suma suyi hakuri dasafe ina makaranta da yamma ina aikin gida>??

Duk soyaiyar wannan novel dince tasaku fadar haka, naji dadi kuma nagode,insha Allah zanyi kokari a dinga turo muku k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ullum
Amnah tana yinku sosai kamar yanda kuke yinta =؃?






Sharhi pls









Amnah El~Yaqoub
' [2/10, 11:17 PM] El~Yaqoub: INSAAF

Writing by :Amnah El~Yaqoub


17&18


Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493


Anty Amnah yaushe zaki fara novel, yaushe zaki fara posting INSAAF,saide kiyi typing ki ajiye kinqi kifara posting, ta gashinan nafara magana ta qare >??wannan page Din nakane kacokam *Unique* *Jamal*, Allah yabaku sa'ar jarabawa yasa ku gama lafiya =?O?

________

kallanta yayi, ya Girgiza kansa yace "wannan shirme ne irin naki Ishraqa, impossible"
ya qarasa maganar Yana yatsina fuska


Tace "to shikkenan, Yaya maganar computer?"

"babu labari, kawai saide Addu'ah"

Murmushi tayi tace "ka kwantar da hankalinka, insha Allah babu abinda zai faru, Sai Alkhairi"

Wani irin kallo yayi mata, wacce irin matace wannan? Ana fada miki kadarar wadda kika Kira da 'yarki tabata, bayan abubuwa na company dasuke ciki, amma kina murmushi kamar babu abinda yake damunki

Ajiyar zuciya yasaki "Ishraqa, nawuce gida"

"to abinci fa? Kona zubama katafi dashi?"

"matata tamin girki"

Daria tayi "Dade bansan halin Lubna ba shine zaka fadamin haka, harda wani kare ta, kullum saide taita ihu tana sonsa, amma munqi gani aqasa, Sai anjima to"

Shima ya kalleta yace "eh na ji Sai anjima"


Yana fita taji kanta yawani irin sarawa, tasa hannu ta dafe kanta, lokaci daya jira yafara dibanta tatafi zata fad'i, Allah ne yakawo mijinta El Hameed cikin sauri yataro ta tafada jikinsa, kan gadon ya kwantar da'ita yafara jera mata sannu, sannan yajuya cikin sauri yabude fridge din d'akin, babu komai acikinsa Sai ruwa, saboda ba kowa ne yake zama acikin d'akin ba, ruwan yabata Tasha sannan yasake kwantar da'ita yariqe hannunta"yaya kikeji yanzu? kokuma mutafi asbiti? "

" A a Habibiy, dama saramin naji yanayi, yanzu yadena "

"Habibty, ya kamata ki rage sa damuwa aranki, kina yawan tinani idan Bana nan ko?"

"dole ce tasa hakan, Asim ne yazo, shine nabashi labarin Insaaf, I think wannan ne dalili"

"nahadu dashi a waje, yanzu de ki tashi muje asbiti ko?"

"A a Habibiy, naji sauqi fa, saide muje wajan doctor din damukai magana dashi zai dubamu"

"to shikkenan, kibari gobe saimu tafi, but are you sure kinji sauqi dangane da ciwon kan?"

Ahankali ta lumshe masa idonta tabude, murmushi yayi, sannan yayi kissing goshinta, daganan suka futo daga d'akin




*** ****** ***



Washe Gari dasafe bayan sun Gama break fast zama sukai afalo itada Amrah, Amrah ta qarewa kayan jikinta kallo taga duk sun mutu, kuma koda wasa Bata taba nuna musu komai ba a haka take saka abinta, shikuma Yaya Asim irin yad'an dauke ta suje shopping dinnan ma beyi ba, wani lokacin har Gara Amjad ma zai dan kai mutum shan Ice cream(=?A?)
Amma Yaya Asim, idan kudin tambayeshi ma yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login