Showing 3001 words to 6000 words out of 80494 words

Chapter 2 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

maigarin muji ta bakinsa"

Baba yace "to muje asbitin"
kamashi sukai suka dagashi, baba yacire jakar laptop din yayarta anan, ya cacimeshi yariqo hannun, aikuwa jini nan yafara Bata hannun baba, shikuma Yaya Ammar yariqo qafafun, wucewa sukai dashi gefen titi suna tare Mota, suma su Inna sukabi bayan su, harsun tare Mota suna qoqarin sakashi Amina tajuya, ta kalli jakar da baba yacire ajikin wannan bawan Allah yayar, ta kallesu sun sakashi aciki suma suna kokarin shiga, da gudu tajuya taje ta dauko jakar ta ratayata a hannun ta, Inna kam ko lura da abinda Amina tayi batayi ba, sannan sukai sallama dasu baba, su suka dau hanyar komawa gida itada Inna, su kuma su baba suka wuce Asbiti

Suna zuwa gida kuwa tawuce dakinta da wannan jaka, zama tayi har zata Bude taga menene aciki Sai kuma tafasa, haka tazauna tazubawa jakar ido cikin ranta tana so taga menene aciki, Ahankali tasa dogayen yatsun hannun ta tabude jakar, computer ce ta baiyana mai launin brown, ruwa yagama cikata harta gaji da cika, rubutun sunan INSAAF dake jikin computer tashafa ahankali, daga nan ko budeta batayi ba bare tayi tunanin shanyata arana, tamaidata cikin jakar tarufe, sannan tabude bakkon kayan ta tasakata acan qasa, qarqashin kayanta (=??)

Sukuwa su baba kai tsaye suka ce driver yakaisu Mubi General Hospital, sunje anyi musu duk abinda ya kamata amma basu ta'bashi ba, Kai tsaye daga nan suka turasu Adamawa State Specialist Hospital anan aka fara bashi temakon gaggawa,daqyar suka yarda Akan zasu fara yimasa aikin saboda basuzo da kudi ba, saida baba yayi musu alwaqarin cewa Gobe gobe za'a kawo musu kudin

Daga nan aka shiga dashi Dakin tiyata har sukai nasarar cire masa harsashin, baba Yana zaune a waje shida Ammar, kawai tunanin yan shanunsa qwaya biyu yake yi, wanda yake kiwonsu saboda ranar Bikin Amina, yanzu dole saide yasiyar guda daya yanaji yanagani (=??)

Hakan ce kuwa ta kasance, washe Gari Ammar yakoma gida yayiwa Inna Bayani, aka saida saniya guda daya yakoma asbiti da kudin, bayan sungama biyan kudin aka basu wani Rasit dakuma magungunan da'ake buqata, baba yazubawa wannan takardar Rasit din ido yayi Shiru Yana kallanta, kawai hoton saniyarsa yake gani ajikin takardar (>?#?)

Haka suka siyo magungunan ma, saide kuma fatan Allah yasa marar lafiya ya farfado lafiya

Labarinsu :
Gidan Malam buba kenan, cikakken bafulatanine da yake zaune aqauyen Mubi, Yayansu biyu shida matarsa larai, akwai Ammar da suke riqewa awajan su, shi Dan ruqo ne, Ammar shine kamar babba a gidan, Sai kuma yarsu Amina daga ita kuma babu qari, Amina yarinya ce qarama sosai, kwata kwata shekarunta goma Sha takwas , amma Allah yayi mata jiki dakuma sura irinta manya, kasancewar aqauye suke ba kowane zai gane hakan ba, Tanada qirji manya,hips dinta yan daidai misali, Ba qaramar kyakkyawa bace, chocolate Beauty ce sosai, kalar fatarta kamar ta Sudanese, tanada manyan idanuwa, gashinta dogo ne sosai, danma baya samun gyara
Auren Amina biyar awannan qauyen nasu,duk wanda ta aura adarensu na farko yake mutuwa, muddin angon ta yazo karbar haqqinsa Tofa saide wani bashi ba, adaren zai mutu,aurenta nafarko auren soyaiyane da saurayinta datake mutuqar so Haruna d'an kande, d'an kande Yana bala'in son Amina, kamar yanda aka sani kowanne ango Yana murna ankawo masa amarya haaka ce ta kasance awajan d'an kande, duk da amaryar tana noqewa haka d'an kande yanemi haqqinsa, amma tun kafin yakaiga neman hanyar sa yaaji maqoshinsa yariqe, numfashinsa yafara yin Sama kamar me asma, awannan dare d'an kande yarasu, al'amarin yataba Amina sosai, saida aka hada da malamai masuyi mata roqon Allah

Aurenta na biyu ta auri wani abokin Haruna, aminin d'an kande ne sosai, shikuma be mutu adaren auren su ba, Sai washe Gari, Yana tsaka da wasa da amarya yaji yawun bakinsa Yana tsinkewa, daga nan wani irin kumfa yake futo masa, kafin safiya Shima Allah yayi masa cikawa

Daga nan Amina tafara Bawa kowa tausayi aqauyen, wasu suce kwanan su ne yaqare, wasu kuma sabanin haka

Aurenta na ukuma hakace ta kasance Bata sauya zaniba
Tofa daga nan aka fara gudun Amina, wasu har agabanta suke mata habaici cewa ita matsafiya ce, duk Iyayen dasuka San Amina tana qawance da yarsu saisu datse wannan alaqar, Abin Yana damun su Inna sosai, daga nan baba yafara karbo mata rubutu awajan liman tanasha

Ana cikin wannan hali wani babban mutum mai mata uku yace zai aureta,alhaji ilu mai kudin qauye ne, kullum haka zaka ganshi azaune akofar gidansa Yana zare ido shi Ala dole gamai kudin qauye, haka yadage Akan zai auri Amina, inma itace take kashe mazajen auren to shi shine ajalinta,awannan lokacin su baba suna cikin tashin hankali kotakan Amina ba'abiba a kayi aure, ango yazo da kazarsa da daddare, Amina tana zaune adakin ita kadai, Yana zuwa kuwa yazubawa qirjinta ido Yana kallo kamar maye, ko alwala basuyi ba bare sallah ya afka mata, haka ya turmushe yar mutane ko qanqantar shekarunta be dubaba, babu wani wasa haka yafara neman hanya, ita tsoro ma yabata yanda taga duk ya rikice, gaba daya tsoro yahanata sakin jikinta bare yasamu hanyar shiga, haka yadinga neman hanya amma wajan qamas yake babu komai bare alamar danshi, ahakan yacire tausayi zai shiga, itade Amina batasan Yaya a kayi ba Sai hango alhaji ilu tayi a bakin kofa, anyi jifa dashi Yana fitar da numfashi daqyar,Kasa tashi yayi daga wajan saboda gaba daya ma jiyayi besan inda kansa yakeba, daga qarshe ma saiya miqe kafa yaci gaba da kwanciya anan (=??=?H?)

Itama Amina da sauri jikinta na rawa ta tashi tazauna tatakure kanta a cikin cinyar ta, awannan Rana yanda taga Rana haka taga dare, washe Gari kuwa daga wannan kwanciya ta barci alhaji ilu ya zarce, ita batasan ma yamutu ba, saida uwargidansa tazo taduba sannan tafasa ihu da kururuwa, yayansa da matansa suna kukan mutuwarsa suna dukan Amina, haka suka Koreta daga gidan jina-jina

Al'amarin yabawa kowa tsoro, tundaga nan manya da Yara idan sukaga Amina kowa gudu yake, kowa ta kansa yake, gudunta suke sosai idan bakayi ban waje

Ana tsaka da wannan hali Dan maigari yadawo daga wajan karatu, Laminu Yaro Dan qwalisa tunda ya qyalla idonsa Akan Amina yace Yagani yanaso, shi bashida wata mata bayan Amina

Maigari yaso yaqi, amma Laminu ya nuna masa cewa duk wanda yamutu dama can kwanansa ne yaqare, bawai Amina ce take kashe su ba, haka a kayi wa Laminu auren gata, kasancewar sa Dan boko saiya raina shekarun Amina, Dan haka bai nemeta ba,Yana ganin kamar tayi qarama, itama dataga haka saita sake dashi, har shaquwa tafara shiga tsakanin su, saida auren su yayi sati daya, Laminu Yana nan ras da ransa, har Gari anfara gulmace gulmace Amina taga kudi shiyasa taqi kashe Laminu, ta ganshi Dan mai Gari gashi Dan boko, Laminu tun Yana daurewa harya Kasa, a kwana na takwas yanemi Amina, Shima a cikin ranar Allah yayi masa rasuwa

Gari ya dauka Amina takashe Laminu, maigari kuwa yanke jiki yayi yafadi, daqyar aka samu yadawo haiyacinsa saboda Yana qaunar Laminu sosai a ransa, tundaga nan yatara mutanan Gari yace yakori Amina daga Garinsa(=?F? @&?)

Al'amarin yadagawa baba da Inna larai hankali, daqyar suka hadu aka Bawa maigari hakuri, bai hakura ba saida yakafa musu sharadi muddin Amina tayi aure mijin ya sake mutuwa asanadinta,to kawai daga Dakin mijin tafice tabar masa garinsa, basai tabiya ta gidan iyayenta ba

Dahaka su baba suka amince, kowa yaguji Amina, duk wanda ya ganta tsakanin su dauke kai kokuma gudu, saboda wannan abun kowa yaqi ta, babu mai sonta bayan Yaya Ammar, Inna, baba, Sai kuma lubabatu qawarta

Back to story =? ?


*** ***** ***



Lagos, Surulere local government



"yanzu ranka yadade so kake kacemin Yaron nawa yamutu? In an'isa shege nake, wallahi tallahi bazai iyuba, banga gawar danaba danhaka dana bai mutu ba"

Dan sandan ya kalli magidancin mutumin yace "Alhaji hakuri zakayi, har yanzu munakan bincike ne, dole abinda bincike ya nuna dashi zamuyi amfani" Yana Gama fadar haka yajuya ya maida kallansa ga Amjad da'akayi wa aiki a goshinsa saboda bugewa da yayi, sakamakon kadeshi da Mota tayi, idanunsa yayi jajir kasancewar sa fari, har yanzu hawaye sunqi tsayawa a'idonsa

ya kalleshi da kyau yace "kayi hakuri kadena kuka, kaci gaba dayi mana Bayanin yanda abin ya faru"

Cikin kuka yace "sun kashe shi fa..., agabana suka harbeshi yafadi"

Gaba dayansu mutanan falon suka fashe da kuka, mamy tana zaune agefe tana Jan carbi, idanunta sun kumbura da alama Tasha kuka taqoshi, Amjad Yana jikin ta kamar Yaron goye, Sai kuma wata mata agefenta kana ganin ta kasan ba bahaushiya bace, balarabiya ce

Magidancin nan yanajin furucin Amjad yafara Baza babbar rigarsa Yana fadin "shikkenan, innalillahi wa Inna ilaihirraji'un... Shikkenan Asim, wayyo niya Allah na" Sai jagwab yazauna aqasa

Gaba daya yabawa 'yan sandan da suke tsaye tausayi, duk ya susuce kamar ma baya cikin haiyacinsa

Miqewa Dan sandan yayi yadubesu "kuyi hakuri hajiya, muna nan munakan bincike har yanzu, saboda awajan da abin ya faru kwata kwata babu alamar gawar sa, saita driver kawai awajan, shikuma Amjad yace agabansa suka harbeshi, hakan yana nufin cewa kode be mutu ba yagudu da kansa, kokuma wanda suka harbeshi sun tafi dashi, amma insha Allah zamu tsaurara bincike Akan hakan, sannan Commissioner da kansa yabada cigiyar photonsa agidajen television's dakuma gidan redio duk wanda yaganshi yatemaka yasanar a police station din dake kusa dashi, insha Allah za'a bashi kyauta mai tsoka"

Yajuya yabawa mutumin daya Kad'e Amjad da Mota hannu, yace"godia muke Yallabai, Haqiqah zuwansa yaqara taimaka mana wajan bincikenmu"

Mutumin yace "babu damuwa"

Kallansa yamai da ga Amjad yace"ko zaka iya binmu zuwa office domin sake amsa wasu tambayoyin? "

Amjad yanajin haka ya sake shigewa jikin mamy ya rungume ta, hakan dayayi shiya sake nunawa d'an sandan cewa babu inda zashi, gaba daya tsoron mutane ma yake yanzu, ko nanda bakin gate bayajin zai Iya fita batare da mamynsa tana kusa dashi ba

Dan sandan yayi murmushi kawai daga nan suka fita gaba dayansu




*** ***** ***



Amina da Inna suna zaune atsakar gida, Inna tana gyara daurin tsintsiyarta daya kunce, ita kuwa Amina tunanin wannan mutumin dasuka tsinta na cikin ruwa take, koya warke oho, amma gsky yanada kyau kam kamar bature, tarasa wazata Bawa labari ko zataji dadi

(kunsan idan gulma tanacin mutum=??)

Kamar an mintsineta ta tashi tace "inna zanje gidansu lubabatu yanzu zan dawo"

"saikin dawo, Karki Dade akwai inda zamuje"

Tace "to Inna"

Tana zuwa gidansu lubabatu taga ancika falon nasu danqam dayara da manya anata kallo, saboda duk qauyen daga gidansu lubabatu Sai gidan maigari nan ne kawai suke da kayan kallo

Yara yan kallo suna ganin shigowar Amina daya bayan daya suka watse, har bige juna suke wajan fita, jikinta ne yayi sanyi, duk saitaji ta muzanta, ita kuwa lubabatu da murmushi tatareta, tasa hannu zata janyota jikinta goggo ta daka mata wata uwar tsawa "ke Luba, koma daki kokuma yanzu inci mutuncin ki, sakara kawai wadda batasan ciwon kanta ba"

Lubabatu sum sum tashige cikin daki ganin ran goggon nata yabaci yanda Bata taba zato ba

Goggo tadubi Amina tace "kifita daga harkar 'yata Luba, ko'itama so kike ki lashe mata kurwa tabi sauran mazajen ki? To aniyarki tabiki, tsabar masifar naci irin naki yanzu Samari ko wajan Luba sun daina zuwa saboda Ana ganinku tare, to aniyarki ta kiyayi ramata...."

Dagudu Amina tajuya tafice daga gidan, cikin kuka tafado gidansu ko sallama babu, Inna ta kalleta takasa binta tabata hakuri, tasan wannan kukan nata baya rasa nasaba da qaddarar rayuwarta, toya zasuyi? Ita kanta abar abawa hakuri ce yanzu bare kuma ita kanta Aminan(=??)

Tashi tayi zata fara shara goggon lubabatu tashigo gidan, Inna tace "sannu da zuwa goggon Luba"

Cikin fishi goggo tace "ba wannan ne yakawo niba, zuwa nayi inyi miki kashedi da gargadi Akan yarki Amina, tarabumin da yata, babu ita babu Luba, kowa yayi harkarsa, idan bahakaba kuwa wallahi hukuma ce zata rabamu"

Tana fadar haka tajuya fuuuu tafice daga gidan, Inna tazauna Akan kujera da sauri tana ambaton sunan Allah, Sai yanzu ne tasan dalilin shigowar Amina tana kuka








Amnah El~Yaqoub
' [2/4, 11:52 PM] El~Yaqoub: INSAAF


Writing by :Amnah El~Yaqoub



5&6



Dedicated to :Itz Sadeek, Alkhairin Allah yakai gareka >??




Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493






Toyaya zasuyi da rayuwar su? Qaddara ce Allah yariga daya dorawa Amina, su kansu basusan takamaimai abinda yake damunta ba, kuma Malam Yana karbo mata rubutu awajan Malam liman tanasha duk lokacin da abin ya faru
Babu me'iya sauya Qaddara face Allah

Ajiyar zuciya tasaki, tayi wulli da tsintsinyar hannunta sannan tafara hada abinci awani kwanon silva mai Dan kyau, shinkafa da wake ce amma duk ta caku6e,(=??)
Dakin Amina ta nufa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????, tana daga labulen taganta a kwance tayi kukanta harta qoshi

"taso mutafi, wannan koke-koken babu inda zai kaiki, ki kaiwa Allah kukanki yafi miki wannan asarar hawayen"

Ahankali ta tashi suka tafi, ko wanke fuska batayi ba, suna cikin tafiya sukazo wucewa ta majalissar su isyaku yayan Lubabatu , Ada isyaku Yana ganin Inna duk abinda yake zai Bari yazo ya gaisheta saboda qawancen dake tsakanin Amina da Luba, amma yanzu yana ganinsu yadauke kai kamar bai sansu ba, qarshe ma suna hada ido da Amina yasakar mata wata uwar harara, Inna tana ganinsa, Sukuwa sauran yan majalissar duk suka watse

Abin yayiwa Inna ciwo sosai, ashe har yanzu haka Amina tana fuskantar wannan matsalar? Ashe har yanzu mutanan Garin basu saduda sunyi hakuri ba? Amma ahakan har take iya futowa aduk lokacin dataso?

Inna Bata Gama tunanin taba suka hadu dawasu Yara sun dawo daga makarantar Allo, mutum daya daga cikin yaran tana ganin Amina tadaga murya tace "la'ila wallahi ga Amina nan"
Atake yaran suka fara watsewa, kowa Yana gudu
Inna batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba, Ahankali take share hawaye tana kuka, Amina tajuyo ta kalleta zatayi mata magana kawai Sai taga tana kuka, cikin sanyin murya tace "Inna meyasa kike kuka...? Bata Gama magana ba itama taji wani qullulun abu yatsaya mata awuya, lokaci daya tafashe da kuka itama, haka suke kuka itada Inna babu wanda yabawa kowa hakuri, har suka qarasa bakin titi suka shiga motar da zata kaisu Yola, anan Amina tasan inda zasuje


Daqyar suka kawo kansu asbitin itada Inna, dasuka shiga ciki ne basusha wahala ba Allah ya nuna musu su baba Azaune a wata bishiya, bayan sun gaisa baba yace "Larai aida bakusha wahala kunzo da abinci ba"

"yanzu Malam muda mukazo dubiya tayaya zamu taho haka hannu babu komai"

Yace "Ai Ammar Yana siyo mana biredi, kuma akwai kayan shayi aciki" yadubi Amina yace "yanaga idonki sil haka ko kwalli babu 'yar baba? , kamar ma kinyi kuka"

Inna tace "munyi kuka de baban Amina, al'amarin Amina yafara bani tsoro Malam, Anya kuwa ba zamuyi qaura mubar Garin nan ba?"

Ammar dake tsaye yace "Inna Garin iyaye da kakanni idan muka barshi ina zamu? Duk suyi su Gama gulmarsu ai WATA RANA SAI LABARI {littafin takwarata miss suwara=??} yaci gaba da cewa "wanda zai baka labarin ma wata Rana bazaka sameshi ba"

Inna tana jinsa tayi Shiru,taga alama Ammar bashida hankali, Dan baiga abinda tagani bane yau shiyasa yake fadar haka, Inna ta kalleshi tace "kuje da'ita tadubashi, Nima gamu nan nida Malam"

Ammar yadubi Amina yace "muje qanwata"

Inna naganin tafiyarsu tadubi Malam tace "Malam al'amarin Amina fa yayi tsamari, yanzu futowar mu daga gida duk wanda yaganmu gudu yake, wallahi Malam bansan lokacin da nafara yiwa yarinyar nan hawaye ba, nikam Malam mezai hana muhada Ammar da Amina aure?inyaso daga nan mutattara yanamu yanamu mubar Garin? "

"wacce irin magana kike wannan Larai, Amina fa ta dauki Ammar ne a matsayin yayanta"

"hakane Malam, amma tasan cewa akwai aure atsakanin su, tunda munfada mata cewa shidin kamar d'an ruqo ne awajan mu"

Saida baba yayi jimmm sannan yace "eto hakanma shawara ce mai kyau, saboda a cikin Garin nan namu de babu wanda zai qara futowa yace zai auri Amina, kuma Amina bazataci gaba da zama haka agabanmu babu aure ba, dole zata tafi Dakin mijinta, idan a kayi auren kawai saina saida gidanmu mubar Garin, Larai kin kawo shawara mai kyau, hakan za'ayi "

Suna shiga Dakin tayi tozali da kyakkyawar fuskarsa data sake yin haske sosai, Yana kwance Yana bacci, ansaka masa robar qarin ruwa, zama tayi Akan kujera ta dubi yayan nata tace"Yaya ai kamar ma bacci yake "

" bacci yake qanwata, tunda muka kawo shi sau daya yafarka, daga Naan kuma baisake farkawa ba, amma sunce zai Iya tashi daga nan zuwa Gobe ko jibi "

Batace masa komai ba illa idanu data zuba masa, idan ta kalli farar fatarsa saita kalli Tata fatar, bakomai ne yake Bata mamaki akansa ba Sai gashin idonsa kamar na mace, haka taita kallansa ita kad'ai tana mamakin baiwar kyau da ubangiji yayi masa
Su Inna ne suka shigo itada baba, kana ganin fuskar su zaka hango tsantsar farin cikin da suke ciki, Inna ma tadubashi tayi masa Addu'ah sannan sukai shirin tafiya gida

Saida suka qara sati biyu a asbiti sannan aka sallamesu, ahakan ma shine ya matsa saboda yasan cewa tabbas 'yan gida suna nemansa, especially Mamy

Amina tana share tsakar gidansu suka shigo shida baba da Yaya Ammar, Ammar ne yake riqe dashi duk da Yana d'an daurewa Akan sauran ciwon da wajan yake masa saida ya gaza, yadawo Yana rintse idonsa
Tsintsiyar hannunta tayar tataresu da gudu tana musu sannu da zuwa, kallo daya ta yiwa baqon nasu, Yana sanye cikin suit dinsa wadda suka tsinceshi da'ita, amma jacket din nasa tana hannun Yaya Ammar , Sai ta cikin kawai white color tadubeshi cikin zazzakar muryarta tace "sannu"

Batare daya kalleta ba ya daga mata kansa kawai, Sai runtse ido yake, daga wannan Bata sake yimasa magana ba tajuya, cikin ranta tana fadin wannan daga gani bashida juriya (>?#?)

Inna tace "Ammar qarasa dashi dakinka, akawo muku abinci"

Yace "to Inna" ya kama hannun Asim yace "muje abokina"
Ahankali yajuyo domin ganin mamallakiyar wannan zazza kar muryar,Yana juyawa kuwa yayi tozali da dogon gashin kanta, tsananin mamaki ya kama shi, wannan qanqanuwar yarinyar ce harta mallaki wannan uban gashin? To Amma shi fuskarta yaso gani, dagowa tayi zata zubar da sharar data Gama, cikin sauri ya janye fuskar sa daga kallanta

Suna shiga Dakin Ammar yanuna masa kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login