Showing 45001 words to 48000 words out of 80494 words

Chapter 16 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

da zoben, rigar ma ta wullar da'ita =?3?=?F? @&?


Tundaga nesa yake hangota tana jifa da kaya, mamaki ya kamashi, kamar Minal yake hangowa, to meyake faruwa ya ganta anan?

Ita daya kamata ya ganta agida yadauke ta su tafi makaranta? >??

Gudun motarsa yaqara, Yana zuwa dede inda take ya tsaya, yafuto da sauri ya qarasa wajan ta yace "Minal, mekike anan?"

Kallansa tayi tace "Yaya Muhsin"

"na'am Minal, ina zakije? Asim Yamin waya dasafe inzo na daukeki zan kaiki makaranta"

Girgiza kanta tayi tace "babu komai Yaya Muhsin, ka kaini kotu Dan Allah"

"kotu kuma? Meza kiyi a kotu?"

"Yaya Muhsin inaso alqali yaraba aurena da Yaya Asim"

Kallan mamaki yake jifanta dashi, yarinyar nan kuwa tasan yanda Asim yake kishinta? Saboda me zatace Araba musu aure? Anya kuwa babu abinda yake faruwa?, Ajiyar zuciya yayi sannan yace "Kinga shigo Mota mu tafi"

Babu musu tashiga motar, shikuma ya tattara mata kayan data zubar awajan, suka dauki hanyar zuwa gidansa




*** ****** ***



Duk gaba dayansu kowa Hankalinsa atashe yake, musanman Ishraqa da El-Hameed, Dan kwalin abayar datayi rolling dashi tuni gefensa yajiqe da hawaye =??
El-Hameed dinne ma me dauria, Asim kuwa abu ne yataru yazame masa goma da a shirin, ga 6atan wannan yarinyar, ga kuma Amjad, duk Hankalinsa ya tashi,gashi wajan ba wajene dazaka dinga ganin mutane sosai ba bare ka tambayesu kosun ganta

Wayar sace tayi qara, amma be kula ta ba bare yadauka, Sai a Karo na biyu ne yad'auka tare da fadin "Muhsin"

Daga daya bangaren Muhsin yace "Abokina meyake faruwa ne? Naga matarka a hanya tana watsi da kaya" =??

"tana ina Muhsin? Ne manta mukeyi"

"tana gidana, suna tare da Nabila"

"Okey, gamu nan zuwa"

Yana kashe waya Ishraqa tazuba masa ido tana jira taji abinda zai fada musu, mamy tace "ya'akayi ne Asim?"

Cikeda aji yace "tana gidan Muhsin"

El-Hameed yace "Alhamdulillahi, Allah abin godia Bari nakira Hammudi" =??

Ishraqa kuwa murmushi take, yayinda wani hawayen farin ciki yake zubo mata, juyawa sukai suka koma daya layin, inda gidan Muhsin yake, El-Hameed Sai dariya yake, yakira Hammudi.

Hammudi Yana dauka yace "Wajadnaha ya Hammudi, Wajadnaha allailah, kuntu masrur wallahi"

Daga daya bangaren Hammudi yake tambayar sa "wa suka samu?"

Ishraqa ta qwace wayar tace "Insaaf"

Haka suka dinga waya da Hammudi har suka qaraso gidan Muhsin, su mamy da Asim de kawai kallonsu suke =??
Yanda suke farin-ciki abin tausayi



Har rige-rigen shiga falon Muhsin suke, Suna shiga kuwa suka ganta azaune itada Nabila matar Muhsin, duk yanda Muhsin yake Bata labarin amaryar Asim yarinya ce batayi tunanin takai hakaba, a ganinta tsaf Minal din zata iya dauke Asim =?J?

El-Hameed Yana qarasawa cikin falon Dasauri yaje ya rungume ta, Ishraqa kuwa tana zuwa Sai tayi turus jikinta duk yayi sanyi, amma haka ta zauna tana kallonsu itada El Hameed tana murmushi, yayinda hawayen farin-ciki yake zubo mata

Mamaki ne ya kama Amina, takai kallonta zuwa ga mamy taga itama Sai Fara'ah take, hakama Amrah, sai alokacin yashigo falon shida Muhsin, hannunsa Yana zube cikin aljihun Wandon Suit din dake jikinsa, saide babu jacket din yacire ta, kana iya ganin yanda murdaddan hannunsa yake ta cikin rigar, kallo daya sukai wa juna kowa ya dauke kansa, Muhsin Yana kallonsu gaba dayansu

Mamy ta kalli Amina tace "Minal 'yata, kigodewa Allah, yau Allah ya baiyana miki Iyayen ki"

Dasauri tatashi tsaye tana yiwa mamy wani irin kallo, mamy tasake jinjina mata kanta tace "hakane Minal, Ishraqa da El-Hameed sune Iyayen ki, yau Allah ya karbi Addu'ar ki"

Girgiza kanta tayi, idanunta qamas babu kuka, tace "mamy aini banida wasu iyaye, niba iyayena bane, suje su nemi 'yarsu"

Gaba daya falon babu wanda Bata Bawa mamaki ba, jikin El-Hameed yayi sanyi, ya kalli Ishraqa, itama kallansa tayi, wani irin kuka me ciwo yazo mata

Takai hannunta takamo na Minal sannan tace "Insaaf... Karki min haka 'yata, nice mahaifiyar ki, Kinga mahaifin ki Insaaf"

Taqarasa maganar tana nuna mata El-Hameed, fizge hannunta tayi daga cikin na Ishraqa, tafada jikin mamy tana kuka sosai

Dasauri Ishraqa da El-Hameed suka taso zasuzo wajan ta, mamy ta daga musu hannu batare datace komai ba, sannan takama hannun Minal din suka futo daga gidan

Har sukazo harabar gidan mamy Bata saketa ba, daga Ishraqa har El-Hameed jikinsu yayi bala'in yin sanyi

Saida suka shiga gidan Asim ya kalli Muhsin yace "yarinyar nan tanada damuwa wallahi, duk Sai wahalar damu take, Sai shagwaba takewa mutane sukuma su mamy suna biye mata"

Muhsin yace "a a Asim, ya kamata kuyi mata uzuri, damuwar datake ciki ai tanada yawa, kuma gashi kaima kace ba sonta kake ba, aikuwa kaga ni banga laifin taba" ya qarasa maganar yanaso yaga yanayin Asim din

Shikuma Asim kafadarsa ya d'aga yace "tokai yanzu kana ganin ya dace ace na auri 'yar Ishraqa? Da girmana da komai Sai a tambayeni wanake aure ince 'yar qawata, =??
Abin da kunya Muhsin, ita kanta yarinyar ba tafi karfin in raineta ba"

Muhsin yayi wani qaramin murmushi yace "Asim bafa haram bane, ni banga abin damuwa Akan haka ba, koda yake, ai itama yarinyar baso take ba, shikkenan saika sauwaqe mata ta auri wanda ra'ayinsu yazo daya, saboda kaga dazu ma Dana hadu da'ita roqona take yi Dan Allah nakaita kotu Araba aurenka danata "

Cikin sauri ya kalli Muhsin tare da zaro manyan idanuwansa yace"kotu fa kace Muhsin"=?3?

Dariya takama Muhsin, amma saiya danne yace "Of course, abinda tafadamin kenan, shine nace tayi hakuri muje gida"


"yanzu ita har tasan a kaita kotu Araba aure? Auren da Allah ne yahad'a abinsa?" =??

Muhsin yasaki dariya yace "to abokina me amfanin auren da babu kulawa, may be abinda tagani kenan, babu kulawa, gashi bataso kaima baka so"

"kaga Muhsin, Dan Allah kadena wannan maganar kotu kotun, tayaya zan saki yarinyar Ishraqa? Da wanne idon zan kalleta?inajin tausayin yarinyar, Gara na tausaya mata mu zauna ahaka"

Muhsin yace "tab! Tausayi manya, yanzu Yaya maganar Daddy?"

"bansani ba Muhsin, yanzu nakeso Nabi bayansu"

Muhsin yace "eh ya kamata muje, amma mu shiga gidan mu fadawa mamy, saimu wuce"

Asim yace "OK,no problem"

Daga nan suka shiga cikin gidan.



Suna shiga falon suka zauna, har lokacin Amina tana wajan mamy,Ishraqa jitake kamar taje ta janyota jikinta su dauwama ahaka, amma tasan ta6a tawa yarinyar rai, dole hakan zai Iya faruwa, Asim ya kalli mamy yace "Mamy kiyi hakuri, inaso naje wajan Amjad, Yana cikin damuwa mamy"

Amrah ma tace "eh mamy Dan Allah, kinji mamy, Nima zan bisu, Dan Allah mamy karmu tafi mubarshi"

"Dan Allah kudena min wannan maganar haba!"

Muhsin yace "Mamy kiyi hakuri, amma idan kuka tashi daga nan muma ba zamuji dadi ba"

Ishraqa ma da idanunta sukai jajir tace "kiyi hakuri mamy, tunda Allah bai bashi nasara ba, Allah ma gafurun rahimu ne"

Kanta ta sunkuyar qasa tace "Hakane, to shikkenan, zamu zauna insha Allah"

Turo kofar falon akayi, gaba dayansu suka kai dubansu zuwa ga kofar, Amjad ne yashigo duk Hankalinsa atashe, kana ganin idanunsa zaka san yasha kuka Bana wasa ba, mamy tana ganinsa tatashi tashige dakinta, Asim ya Girgiza kansa cike da damuwa yamiqe zaibi bayan ta

Ahankali yace "Yaya"

Asim ya tsaya cak awajan

Ahankali yataka zuwa wajansa yace "karka bita Yaya, na cancanci fiye da haka Yaya, kakoma ka zauna zan bita da kaina"

Yana fadar haka yasa ka kansa zuwa d'akin nata, batare daya jira amsar Asim dinba


Ajiyar zuciya Asim yasaki yadawo falon yazauna kusa da Muhsin, ya kalli Amina suna hada ido ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta

Yasake daga kai ya kalli Ishraqa suka hada ido,take maganganun datake fada masa Akan auren yarta yafara dawo masa, cikin sauri ya sunkuyar da kansa qasa >?#?=??

Cikin ransa Yana fadin shikkenan burin Ishraqa yacika,girma nade yariga yafadi













Mrs Usman ce
' [2/21, 10:14 PM] El~Yaqoub: INSAAF

Writing by:Amnah El yaqoub

33&34


Ina qara miqa saqon ta'aziyya ta ga dan'uwana Wato Its Saddik, Allah yaji qanta, Allah yayi mata rahma, Allah yasa tahuta =?O? Idan Tamu tazo ya Allah Kasa mucika da Imani


Like my page on Facebook =?G? https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493



_________


Tabbas idan yaci gaba da zama awajan, babu abinda zai hana Ishraqa tayi masa wankin babban Bargo =??
Danhaka yayi qasa da muryarsa yace "Muhsin, ya kamata mubar wajan nan" >?#?

Cikin mamaki Muhsin yace "saboda me?"

Da idanunsa yayi masa nuni da 6angaren da Ishraqa take
Nan take Muhsin ya fahimta, yayi murmushi sannan yace "muje"

Ko inda Ishraqa take bai iya kalla ba suka fice daga falon, suna compound din gidan Muhsin yasaki dariya yace "wai saboda kaga Ishraqa a falon ga kuma Minal shine kace mu futo?"

"Muhsin idan ganine Aida sauqi, kawai yanda nagama cikawa Ishraqa baki bazan auri yarta ba, shi nake tunawa, kuma nasan bazatayi fuska ta share ba"

Muhsin ya kwashe da dariya yace "lalle Asim, toba Gara ka tsaya ba, ayi wacce za'ayi?, yanzu dakasa muka futo ina zamuje?"

Kai tsaye yace "Wajan Daddy"

"Wajan Daddy kuma? Kasan abinda kake fada kuwa Asim?"

"nasani Muhsin, Saboda Amjad, muje"


Muhsin ya kalleshi ya Girgiza kansa, besan wacce irin zuciya abokin nasa yake dashi ba, koma menene yasan cewa haqiqa Minal tayi sa'ar miji, bece dashi komai ba suka tafi



*** ****** ***


Bayan tashiga d'akin Kasa jurewa tayi tafashe da kuka, Ahankali yaturo kofar d'akin nata yashigo jikinsa a sanyaye

Kallanta yayi yaga tabawa kofar baya, hakan yana nufin koma waye yashigo batason ganinsa kenan, gwiwo yinsa yazube aqasa, yace "mamy..."

Tana jinsa tayi Shiru, hawaye take amma takasa juyowa ta kalleshi

Yace "mamy Ashe zaki iya yin fishi dani?, zaki iyayin fishi da Amjad dinki? Autanki?"


Wannan maganar daya fada saita sa jikinta yayi sanyi, kukan ta ya tsananta

Shima ganin tana kuka Sai hakan ya sashi zubda hawaye yace "Mamy uwa Bata fishi da yaranta, tunda na tashi bansan kowa ba, bansan mahaifiyata ba kena sani a maimakon ta Mamy, kuma kin hadani da yaranki kinyi kana tarbiyar da kowacce uwa tagari take yiwa yaranta, mamy bantaba sanin wani abu waishi zalunci ba bare nayi, kuma Narasa wanda zan zalunta Sai Yaya Asim...., mamy meyasa laifin mahaifina zai shafeni? Kiyi hakuri Dan Allah na roqeki "

Yaqarasa maganar Yana hade hannunsa waje daya =?O? kuka yake sosai, kuma har lokacin Bata juyo ta kalleshi ba, cikin kuka yace" Mamy tun muna Yara kece kike fada mana mu daina ruqo, mu dinga hakuri da juna, ubangijin daya haliccemu ma muna aikata masa laifi kuma yayafe mana, meyasa ba zakiyi hakuri kiyafewa mahaifina ba? "

Hannu tasa ta share hawayen idonta, bazata iya fishi da Amjad ba, tana kaunar Yaron acikin ranta, amma mahaifinsa ya yaudaresu, kudi da Rudin duniya sun Gama dibansa.

Ahankali ya tashi zai futo daga d'akin, saboda mamy de ko kallansa taqi yi.

Tanajin alamun tashinsa ta juyo tace "toda katashin inane zakaje?" =?H?=??

Cikin sauri ya juyo ya kalleta, amma Yana tsoro yakasa qarasa wa wajan ta, Sai tausayin sa ya kamata, tace "kaje kanemi abinci Kaci"

"banajin yunwa mamy...."

Batace masa komai ba tanemi gefen gadonta tazauna, Ahankali yatako wajan ta, tare da riqe hannunta yace "mamy ki yafe mana nida Daddy please"


"Amjad me mahaifinka Yamin dazaka ce nayafe Mas....."

Bata qarasa ba taji wani irin taqaici ya kamata, har yanzu idan tatuna abinda alhaji yayi jitake ta tsaneshi, wani irin sabon kuka yazo mata, Bata Hana kanta ba, haka tafara hawaye tana sharewa, Shima kukan yasaka mata, tana ganin haka tajashi jikinta ta rungume shi, kowa kuka yake acikinsu, ita kuka shi kuka babu wanda yabawa dan'uwansa hakuri, da kansu suka gaji suka daina

Tashi tayi takamo hannunsa tace "muje nabaka abinci"

Haka suka futo falon inda suka Bawa kowa mamaki, ta kalli Ishraqa da ido ya kumbura saboda kuka, ta kalli El-Hameed shikuma yazubawa Amina ido Yana kallonta, takai kallonta wajan Aminan taga tana nan zaune inda ta Barta, amma ta lumshe idonta kamar me bacci

Murmushi tasaki, saboda Iyayen da yarinyar duk sun Bata dariya, kuda yarku amma kuna tsoron tunkararta?

Haqiqa yau Minal tazama boss, kuma da alama Sai daya Actor din yazo sannan ne zasu daidaita

Zama tayi, sannan tazaunar da Amjad agefenta, ta kalli Amrah tace "Amrah kawowa Amjad abinci"

Amrah tatashi tayi kitchen tana mamakin wannan shaquwa ta Amjad da mamy, kome yafada mata harta sauko cikin sauri haka?


Bayan yagama cin abincin Yana shirin tashi Asim yashigo, yayi mamaki dayaga har lokacin su Ishraqa suna gidan, yanayin Zaman nasu ya kalla yasan akwai sauran waani abun kuma, Allah Allah yake Kar Ishraqa ta kunya tashi a gaban Minal dakuma su mamy, shiyasa yaqi kallon inda take ma >?#?
Fuskarsa yad'an daure sannan ya zauna yakalli mamy yace "Munje wajan Daddy nida Muhsin, basu bamu damar ganinsa ba, sunce Sai kinje, Mamy kiyi hakuri Dan Allah"

Amjad dake zaune kansa ya Sara, Shima Hakan ce tafaru dashi bayan yabisu abaya, kwata kwata basu bashi Damar ganin Daddyn ba

Ahankali yamiqe ya kalleta yace "Mamy saida safe"

Daga nan yawuce dakinsa

Itama Amina kokuma nace Insaaf, tashi tayi ta nufi hanyar dakinsu, ciki-ciki tace musu "saida safe"

Asim ya kalli Amjad, yasake dawo da Idonsa ya kalli Minal, Ahankali yace "ikon Allah" >??
Yau kuma anta6o shagwa6a66e da wata shagwa6a66iyar babu Zaman lafiya

Amrah ce tatashi tabi bayan Amjad, saide tana kama handle din d'akin da nufin budewa taji shi a kulle, haka tadawo falon ta zauna jikinta a sanyaye

Ishraqa da sauqi tamiqe zatabi bayan Amina, mamy tayi sauri tace "karkije Ishraqa, kibata lokaci ta huce, zatafi saurareku"

Dawowa tayi ta zauna Akan kujerar tadafe kanta da hannunta >?&? @&?, idanunta nakawo ruwa =?"?

Kallanta Asim yayi yace "kuma wa zakiyi wa kukan?"

El-Hameed yayi murmushi, Amrah ma ta kalleshi tayi murmushi, mamy tace "Asim kabarta da abinda yake gabanta mana, idan bazaka lallashi Minal ba ai bazaka zo ka tunzura Ishraqa ba"

Shiru yayi bece komai ba, Ishraqa ta kalleshi takawar dakai batace dashi komai ba, besan cewa dama aciki take dashi ba, jira take tagama da matsalar gabanta sannan tadawo kansa

Amina kuwa tana shiga d'akin ta jingina ajikin kofar d'akin tana tunani, rayuwa kenan, yanzu ashe Anty Ishraqa itace mahaifiyar ta? Qwalla ce ta cika idonta,tatuno lokacin da Ishraqa take zazzaga mata masifa harda cewa inde Asim ne to tayi masa mata, ko waye yace mata ita din sonsa take?
Harda cewa Wai karta miqe kafa, to mezatai dashi itama tunda shima ba sonta yake ba, hawaye ne yazubo mata tasa hannu ta share

Tana shirin barin jikin kofar tajiyo mamy tana cewa "Ishraqa, ya kamata kifada mana dalilin dayasa yarki ta6ace daga hannun ki, nide nasan kintaba cemin Insaaf yarki ce, kuma kinaso na dinga kiranki maman Insaaf, amma duk cikin mu nan babu wanda kuka taba fadawa dalilin dayasa kuka rabu Kuda yarku"


Hawaye ne yazubo mata, ta kalli El-Hameed tace "ka basu labari"

Shima kallanta yayi yace "A a kibasu labari Ishraqa"

Asim yayi murmushi,cikin ransa yace yau Habibty Takoma Ishraqa =??

Ahankali tafara basu labari tace "kamar yanda na fadawa Asim, Insaaf Bata wuce yar shekara biyu ba, muka nemeta muka rasa,kafin muyi Candy muka koma Sudan nida iyayena, bayan nayi Candy aka daura mana aure nida El Hameed, iyayensa suna da hali kamar yanda nawa suke dashi, shekarar aurenmu daya Allah ya azurtamu da samun Insaaf,Iyayen El Hameed sun nuna mata gata sosai, sunyi mata kyautuka masu yawa, haka Nima nawa Iyayen, lokaci daya mahaifiyar El Hameed tarasu, daga baya Shima mahaifinsa ya kwanta ciwo, anan ne ya mallakawa Insaaf kadarori masu yawa, kuma aka saka sunan ta Akan komai, daga baya Shima Allah yayi masa rasu.

Insaaf nada shekara biyu muka zauna nida iyayena da Hameed cewa mezai Hana muzo Nigeria mujuya wa insaaf kudinta kafin ta girma tayi hankali, tayi ilmi me zurfi, taci gaba da kula da abinta, tunda abaya mun zauna a qasar munji Dadin haka,
haka kuwa akayi, alokacin Hameed yace muje, shi akwai abinda zaiyi, haka muka taho nida iyayena, bana mantawa alokacin tana sanye da rigar dana ganta da'ita dazu, dakuma zoben da El Hameed yasiya mata shi, mun sauka a Nigeria cikin Garin Abuja, kai tsaye babanmu yace muje kano anan ya kamata muyi komai, ahanyarmu ta tafiya ne mukai hatsari, Allah yayiwa iyayena duka su biyun rasuwa, ni kuma nasamu raunuka daga qarshe ma na suma, nide Sai a gadon asbiti naganni, nafarka na dinga tambayar yata insaaf amma wanda suka kawo mu asbiti sunce su basu ga wata yarinya ba, mutum uku kawai suka gani acikin motar
nashiga tashin hankali matsananci, babu iyaye babu yarinya ta,nakira El Hameed awaya nasanar dashi, alokacin yazo, munfi kwana da Kwanaki muna cigiyar Insaaf amma babu wani labari, haka muka hakura muka koma Sudan



Bayan munkoma hankali na yaqi kwanciya, koda yaushe ina kuka ina tunanin yarinya ta, haka muka Kasa hakuri saida muka dawo nida El Hameed, alokacin ne Naga Asim baya aikin komai, shine muka yanke shawarar mu bashi kudin Insaaf yadinga Juyawa, bayan mun bashi haka muka sake komawa Sudan, ahakan ma hankalin mu bai kwanta ba, koda yaushe gani muke kamar idan muka dawo Nigeria zamu sameta, haka muka tattaro, muka rabu da danginmu muka dawo Nigeria da zama, bayan mundawo shine muka sauka a Lagos, muka nemi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? gida kusa da naku "

Tana gama jin wannan labarin nata tafashe da kuka, ashe haka iyayenta su kasha wahala a kanta? Wacce irin qauna ce wannan? Hannunta ta daga Sama tana qara yiwa Allah godia, taga iyayenta, menene kuma yayi saura yanzu? Saide su Innah, sune kuma take fatan ace tasake haduwa dasu a rayuwarta koda sau daya ne

Hawayen idonta tashare, bayan tatuno gagarumar matsalar datake tare da'ita
Ta mutuwar mazajen datake aura, dole Yaya Asim yayi hakuri ya saketa, bazata so yamutu saboda itaba


Gaba daya falon yayi tsit, bayan sungama sauraren Ishraqa, mamy tace "Amma kuma Ishraqa kince a ahanyarku ta zuwa kano kukai Accident, shikuma Asim yafada min Ayola yahadu da'ita"

Girgiza kanta tayi tace"bansan Yaya akai taje Yola ba, wannan shine iyakar abinda nasani mamy"

Mamy ta kalli Asim tace "Asim Yaya akai Minal taje Yola ne?"

Cikeda aji yace "mamy wallahi bansani ba, itama fa tayi tunanin wadancan mutanan sune suka haifeta, tayaya zatayi bincike Akan Sanadin daya kawo ta Yola? Sannan Bata dadi muka rabu dasu ba, dama da saina tambayesu"

Dasauri El Hameed yace "mekake nufi Asim? Menene yahadata dasu har suka rabu Bata dadi ba?"


Asim yayi Shiru yarasa amsar dazai basu, Ishraqa tace "kafada mana man Asim, gudunta sukai ko? Suma sum qyamaci yata kamar yanda nayi acikin rashin sani? Sun gujeta bayan sun gaji da ruqonta ko?"

Dago manyan Idonsa yayi ya kalleta yaga duk ta rikice, tayaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login