Showing 39001 words to 42000 words out of 80494 words

Chapter 14 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

sa'ar ka?,harda kallon qwayar Idona kana cemin yarinya, ban girmeka ba? "

" to naji, karkuma abin naki yawuce gona da iri, ya'isa haka Karki kuskura kisake cewa kin girmeni "

" nafadama angirmeka Amjad kayi abinda zakayi, Dan renin hankali kawai, marar kunya "

" OK haka kikace ko? To nan gaba Karki sake kawomin shawararki, kije ki qarata da samarin ki masu qaton ciki "

" Nima karka sake kawomin labarin yanmatan ka, itama Minal din dakake shirin aura karka sake kawomin maganar ta daga yau, komai yazo qarshe tsakanina dakai "

Suna wannan fadan nasu Minal tazo tawuce su,gashin idonta duk sun hadu, alamun Tasha kuka, tashige dakinsu tareda rufewa



*** ****** ***


Hannuwansa zube cikin aljihun wandon suit din dake jikinsa, tunda tafita daga d'akin yakasa zaune yakasa tsaye, Sai Zagaya d'akin yake, gaba daya kansa ya kulle yama rasa Yaya zaiyi? Wazai fara tunkara da wannan maganar? Anya kuwa Amjad bazai shiga cikin wani hali ba idan yaji wannan maganar?

Wata iska me zafi ya furzar, ya qarasa kusa da computer sa da yayi gefe da'ita tun dazu, wayar sa ya dauka yakira Muhsin "Muhsin akwai matsala"

"matsala kuma Asim? Meyake faruwa?"

"kazo ka sameni please, ina cikin bala'in tashin hankali Muhsin"=??

"subhanallah... to gani nan zuwa" cewar Muhsin


Duk'da yakira Muhsin har yanzu yana tsaye yana zagaye qayataccen falon nasa, shaf ya Dade da mantawa da aikin dayake a computer
Muhsin ya shigo falon Hankalinsa atashe "Asim meyake faruwa? Gabana faduwa yake wallahi tunda Kamin waya"

"Muhsin dangane da yarinyar nan ne" yafadi maganar kamar zai fashe da kuka =?"?

Murmushi Muhsin yayi "Alhamdulillahi, tafada ma ne?"

Cikin sauri Asim yaruqo hannunsa, "mekake nufi tafadamin? Kaima kanada labarin abinda tafada min ne?mekake nufi da tafadamin?"

Muhsin yadafa kafadarsa "nifa ba komai nake nufi ba, ina nufin ta fadama ne tana sonka ne itama?"

"Muhsin kadena maganar wasa, yarinyar nan fa tafadamin akwai aure na a kanta, bansan... bansan Yaya zanyi ba"

Muhsin yace "Alhamdulillahi, Asim kace komai yazo mana cikin sauqi, kawai yanzu muyi kokari mujanyo hankalin yarinyar nan"

Kansa ya dafe da hannunsa >?&? B&?sannan yace "Muhsin fice daga gidannan Dan Allah kafin na Bude Idona"

Muhsin yasaki dariya, babu musu yafi ce

Yanajin fitar Muhsin zuciyarsa tagama yanke masa abinda ya dace, Dan haka cikin sauri ya nufi d'akin mamy.



Turare take fesawa a jikinta, tagama shiryawa kenan zata futo falo, ta ganshi ya shigo d'akin nata, yanayin fuskarsa ta kalla kawai tasan ba kalau ba, zama yayi a gefen gadon yace "mamy akwai damuwa"

Takowa tayi tazauna agefensa, "meyake faruwa? Ko bakada lafiya ne?"

"lafiyata kalau mamy, munyi magana da Minal ne... shi ne... shine..."

Daga nan yayi Shiru yakasa qarasawa, jansa tayi jikinta, ta sassauta muryarta "Asim, fadamin menene?"

"Mamy munyi magana da'ita, ina tambayarta metake buqata ne lokacin bikinsu, shine tacemin tanada aure"

Cikin sauri mamy tace "aure kuma? Dama ba budurwa bace? To Ina mijin nata yake kadauko ta kataho da'ita nan?"

Jikinsa ne yayi sanyi, ya kalli mahaifiyar tasa "cewa tayi nine"

Dasauri mamy tace "Kaine mijinta? Ina Minal din take?Bari nakirata naji daga bakinta"

Tana fadar haka tafara kokarin tashi, sake riqeta yayi sosai a jikinsa "A a mamy karkije, zan saketa!"


Dasauri ta kalleshi, taga alama kuma yanda yafada din zai Iya sakin nata, to meke faruwa ne? Dama baya sonta ne amma yake nuna kishi a kanta? To kode Shima besan yakamu da sonta ba? Rabuwa tayi dashi ta dauki wayarta takira Amrah tace taturo mata Minal da Amjad

Amjad ne yafara shigowa, Yana ganin Asim yakoma kusa dashi yazauna,tana shigowa d'akin ta gansu shida Amjad duk sun mamiqe ajikin mamy kamar wasu yan yaye, musanman Asim ma yawani rirriqeta kamar zata gudu ta barshi

Ahankali tazauna aqasa tace "mamy gani"

Mamy tace "Minal yanzu Asim yake fadamin wata magana, menene gaskiyar al'amari ne?"

Gabanta yafara faduwa, yau kam taga ta kanta, Ahankali tace "hakane Mamy, kafin muzo nan wani malami yayi mana aure ni dashi"

Amjad najin haka yazaro Idonsa waje =?3?=?3?

Cikin sauri yace "Aure kuma? Keda Yaya Asim din?"


Cikin sauri ta daga kanta sannan tace "Amma... Ni banaso, nafison na zauna haka, banason nasake yin wani auren"

Amjad yace "subhanallah... Minal meyasa zakice haka? Innalillah..., meyasa baki fada mana tunda wuri ba? Da yanzu alhaki Yana kaina" yajuya ya kalli Asim yace "Yaya Dan Allah kayi hakuri"

Fuskarsa cike da bacin rai ya tashi daga jikin mamy ya kama kunnansa yariqe "meyasa zaka ban hakuri? Kaine baka sanar da'ita shirin dakake yi ba, shiyasa, but Duk abinda kakeso inde baifi karfina ba zan mallaka mashi Amjad,saboda haka zan saketa ka aureta"


Cikin sauri Amjad ya manta da zafin da kunnansa yake masa, ya kalli Asim "A a Yaya, na hakura wallahi, Nima nabarma ita"

Asim ya Girgiza kansa yace "banason musu"


Mamy tace "ya'isa haka dan Allah, Minal tashi kije idan alhaji yazo zanyi masa Bayanin komai"


Tashi tayi, su kai ido hudu da Asim cikin sauri yadauke Idonsa daga kanta, idan tunanin ta yazama gaskiya saitaga kamar tsoron ta yake ji =??=??

Tana fita, Shima Amjad ya kalli mamy "Zanje nahuta mamy, kaina yanamin ciwo"

Mamy tace "to saida safe" daga nan bai sake magana ba yafuto daga d'akin, jiyake kansa kamar zai rabe gida biyu, mamy kuwa kawai de tace masa saida safen ne, amma dole zata bishi dakinsa taga halin dayake ciki, bazata iya barin autan ta cikin wani hali ba


Yana zuwa tsakiyar falon nasu yadora hannunsa aka, =?F? B&?
jiyake kamar yafashe da ihu, hanyar dakinsa yanufa, Sai kuma yajuyo ya nufi d'akin Amrah, budewa yayi yashiga, Sai kuma ya tuna dazu sunyi fada =??

Saiya dawo baya, yarufe musu d'akin, Amrah tana kwance Akan gado ta hango shi, tayi tunanin zai shigo Sai kuma taga yakoma,Ahankali tatashi tabi bayansa



Tana zuwa dakinsa ta hango shi acan qarshan gado yana kuka, cikin sauri ta qarasa wajansa tazauna kusa dashi tace "nashiga uku Amjad meyasameka kake kuka?"

Yana ganinta kusa dashi yafada jikinta Yana kuka wiwi kamar mace, mamaki ya kama Amrah, ta kalli yanda yafado jikinta abinda bai taba yiba tunda suka tashi gida daya, janye shi tafara yi daga jikinta tace "Amjad, kayi magana mana menene?"

Cikin kuka yace "Narasa ta Anty Amrah, Narasa Minal, ashe anyi musu aure itada Yaya Asim"

"ohhh, saboda kaji Minal tana auren Yaya Asim shiyasa kadawo kacemin Anty Amrah kenan ko...">?#?

Girgiza kansa yayi dake jikinta, cikin shagwaba yace "Niki daina yimin wasa"

Wani irin abu taji a jikinta, tafara kokarin janye jikinta, amma Amjad saiya dora kansa Akan cin yarta, ya Zagayo da hannunsa ta baya yariqe cikekken hips dinta

Lokaci daya taji wani yarrrr!
Hannunta tadora Akan hannunsa dayake kan qugunta tace "kai cikani, saikace kasamu mamy duk ka riqeni, kayi hakuri mana to, Kai saika dinga kuka saikace mace"

Hannunsa yadauke daga kan hips dinta ya share hawayen, cike da shagwaba yace "Toba ke ce kikaqi lallashi naba" =??

Gaban Amrah yafadi, tambayar kanta tafara yi, Anya kuwa kalau Amjad yake, menene hakan yake mata?


Cikin sauri tamiqe tsaye har Yana dago kansa Yana kallonta cikin mamaki, jitayi yanayin ta Yana sauyawa, wacce irin masifa ce wannan tarasa Akan wanda zataji feeling Sai qaninta?

"Anty Amrah tafiya zakiyi?" yadoko mata tambaya

Tace "Amjad banson shirman banza, nabaka hakuri kaqi hakura Sai rirriqeni kake kamar kasamu wata sa'arka, kuka kakeso na zauna na tayaka?"

Shima cikin fishi yace "to Kar Allah yasa ki tsaya din, kitafi mana, kifi ruwa gudu"=??

Mamy ce tashigo d'akin tace "kai innalillah... Wai yaushe zakuyi hankali ne? Amrah da girman ki ban hanaki kula Amjad ba? Miye ya shigo dake dakinsa?"

Baqin ciki ya kama Amjad, Wai da girman ta, to ba dole ma ta raina shi ba, tayaya za'ai mamy ta dinga fadar haka agabanta?

Haushi yasa ya maida kansa cikin fillo yaqi kallon mamyn =??

Amrah kuwa fuska babu walwala tafice daga d'akin, kullum mamy saita dinga cewa itace babba ta qyale Amjad, koda yaushe ita ce me daukar laifi, wallahi yasake yimata rashin kunya qararsa zata kai wajan Yaya Asim




Washe Gari suna zaune afalo bayan Break,Amrah tana danna wayarta, Amina kuwa kallo take, mamy na karanta Hisnul Muslim

Futowa yayi cikin qananun kaya, riga da Wandon jeans, amma rigar yadora mata jacket asama, kayan sunyi masa kyau sosai kasancewar ba sakawa yake ba, daga suit Sai manyan Kaya, sune kawai kayan sakawarsa

Qamshin turaren dayasa yacika falon nasu
Babu wanda bai daga kai ya kalleshi ba, idanun sane yahadu da nata, cikin sauri ya janye Idonsa daga cikin nata

Mamy tana lura dashi, Amina kuwa shaf tama manta da maganar auren da tayi masa jiya, saboda abin be dameta ba, ba auren ne agabanta ba, Bata fatan ace wani mutum yasake mutuwa adalilinta, haka babu abinda takeji a ranta game dashi, tasan de tana hashi girmansa a matsayin sa na babban mutum,
tsoron data hango acikin qwayar Idonsa jiya, yauma shita gani =??

Sai abin ma yabata dariya, Ahankali tayi murmushi ta dauke kanta daga kallonsa

Amrah ta rissina tace "good morning Yaya"

Daga mata kai yayi kawai, yanemi waje yazauna, already sun gaisa da mamy tun bayan asuba, amma duk da haka saida ya dubeta yace "mamy Barka da safiya"

Kallansa tayi taga yanda yake wani dauke kansa, tarasa gane wanne irin karfin hali Asim yake dashi, kanason yarinya amma bazaka nunaba, koda yake may be tunanin ta ne yazama gaskiya, Shima ba lalle yasan yanason Minal dinba

Ataqaice tace masa
"yauuwa"

Tamaida dubanta ga Amina tace "Minal, tashi ki kawo wa Asim break fast dinsa"

Cikin sauri ya kalleta, Minal kuma, Wai meyasa mamy take masa hakane? Bayan da itace take kawo masa da kanta, haka yayi Shiru yasake dauke kansa

Ahankali tatashi ta dubeshi tace "Yaya ina kwana?"

Batare daya dago kansa ya kalleta ba yace "lafiya"

Dan tabe bakin ta tayi tawuce kitchen din tana magana a ranta, idan auren ne bayaso ai komai yazo cikin sauqi, tunda itama bataso kawai saiya saketa

Kawo masa abincin tayi ta ajiye, ko zuba masa batayi ba Takoma wajan zamanta tazauna, ransa yaqara baci, Tome yarinyar nan take nufi? Shine zai zuba abincin da kansa kenan?

Mamy tana kallonsu ta gefen idonta, tanaso taga Yaya zasu qare

Bude abincin yayi, yayi Dan qaramin tsaki sannan ya kalli Amrah "ke taso kizuba min abinci" =? ?

Kafin Amrah tatashi mamy tace "Minal tashi kizuba masa"

Yanzun ma cikin sauri ya kalleta, mamy Sai saka yarinyar nan take tana kulawa dashi ba tasan gawa ake Bawa kulawa ba, shi kam yasan cewa yanzu tasa ta qare =?"?


Babu musu tatashi tazuba masa, tazauna kenan Amjad ya shigo falon cikin shirin fita

Kallan Amrah yayi, suka sakarwa juna harara, sannna yazauna kusa da mamy, Amina ta gaida shi ya amsa cikin mutunci

Yace "mamy zanbi Yaya office, yau tare zamuyi aikin"

"Autan mamy kabar naka aikin kadawo nan ka zauna ko?"

"mamy bazan iya missing dinki dayawa ba, amma zan koma insha Allah"

Tace "yawwa Autana, Allah yayi muku albarka, Daddynku fa Yana hanya, around 11 zai qaraso"

"Allah yakaimu mamy, idan mundawo daga office saimu gaisa"


Wayarsa ce tayi qara, yad'auka tare da amsawa

"Yallabai gobe kanada meeting din gaggawa a malesia, ticket dinka yazama ready, zaka iya tafiya yau ko gobe"

Tace "babu damuwa, zan tafi yau din" daga nan yakashe wayar ya miqe tare da kallon Amjad

Amjad ya tashi yafice Yana yiwa mamy sallama

Ta kalli Asim tace "to saika dawo, idan alhaji yazo zanyi masa magana Akan maganar ka data Amina"

"babu damuwa, zanje Malesia yau, zuwa jibi zan dawo insha Allah, kimin Addu'ah"

"Allah yakaika lafiya"

cewar mamy, takalleshi taga babu wani abun daya dauko, ko brief case dinsa ma yau bai dauka ba, idonta ya sauka Akan wayoyinsa guda biyu, ta kalli Amina tace "Minal dauki wayoyinsa ki rakashi compound"

Al'amarin mamy kuma yafara Bawa Asim tsoro, kallanta yayi yadauke kansa, cikin sauri yafice daga falon

Mamy ta sake kallon Amina tace "tashi mana"

Ahankali tatashi ta dauki wayoyin nasa akaron farko, tabi bayansa dasu, Amrah sai dariya take qasa qasa


Tana futowa ta ganshi atsaye a bakin kofar falon, hannunsa ya miqa mata batare dayace komai ba
Babu musu ta saka masa wayoyinsa akai tajuya zata koma ciki

Mamaki yakama Asim, wato idan ya matsu yaje lafiya ko karyaje duk shiya sani,duk da mamy tayi masa Addu'ah ai malamai sunce Addu'ar mata Akan mijinta batada hijabi awajan ubangiji, kawai zata bashi wayoyi ta juya ko Addu'ah babu >?#?


Ajiyar zuciya yayi yabi dogon gashin ta da kallo sannan yace " ke baki iya Addu'ah ba ko?"

Cikin sauri ta juyo ta kalleshi "Yaya ai danaga mamy tayi ma, amma kayi hakuri" taqarasa maganar idonta na ciko da qwalla

Cikin ransa yace yarinyar nan tacika shagwaba dayawa, afili yace "kina Jina, zanyi waya da Muhsin yazo yakaiki school, har yanzu ke qaramar yarinya ce, kicire tunanin aure aranki kiyi karatu,kuma banson kula qawaye da Samari kinjini?"


Cikin sauri tace "eh Yaya, Allah yadawo dakai lafiya"

"Amin" abinda yace kenan yajuya zuwa wajan motarsa da Amjad yashige tun dazu

Tunani yafara, ya kamata ace Yana dawowa ya tsaya ya nutsu yanemo Iyayen ta, ko hakan zaisa ta dinga dariya kamar kowa


Sai wajan 11:47 Daddy yadawo, bayan yaci abinci yahuta mamy ta kalleshi tace "Alhaji auren Amjad da Minal fa bazai iyuba"

"inajin ki, saboda me? Ko akwai abinda ya faru?"


"akwai Alhaji, babba ma kuwa, Asim ne yayiwa yarinyar maganar auren, saitake fada masa ai tun kafin suzo nan akwai Malamin daya daura musu aure"

Cikin sauri ya kalleta yace "tanan ta 6ullo kenan"

"bangane ba Alhaji kamar Yaya tanan ta 6ullo?"

Gyara zamansa yayi yace "Hajiya, kifita daga sabgar yarinyar nan, nagama lura da'ita kawai kwadayin kudi da son abun duniya ne yakawo ta gidan nan, da zata auri Amjad, tadawo tace Asim mijinta ne bayan tagama gane sirrin gidan tagano Asim ne me kudi, toni ban yarda da wannan batu ba, tayaya babu sheda babu komai haka kawai zan dauki Yarona inbata?
Taje ta kawo min mutumin daya daura auren, idan naji daga bakinsa zan iya yarda, idan hakan ne zansa Asim din yasaketa ta tattara kayanta tabar mana gida "


Mamy ta kalleshi cikin damuwa tace"Alhaji kayi hakuri mana, nifa na yarda da maganar Minal, alhaji ba zatayi qarya ba, tanada hankali"

"Mezai Hana kice haka tunda kece kika haifeta? Nace mezai Hana kice haka? Tunda itada Amrah duk daya kike ganinsu, Toni nagama magana, tashi kifice kibar min nan"

Babu musu mamy tatashi tafuto, falo ta zauna tarasa yanda zatayi, tayaya Alhaji zaice araba aure? Asim yanason yarinyar nan, ita uwa ce tanason farin cikin danta, tasan cewa Minal itace farin cikin Asim, agaba zasuji Dadin zama da juna bayan soyaiya tagama wanzuwa atsakanin su,
Kanta ne ya kulle, takira Aminiyarta, tafada mata komai, nan da nan qawarta tabata shawara takira Babban abokin Daddy tasanar dashi, insha Allah zaisashi ya janye wannan maganar

Suna kashe waya mamy takira Alhaji Umar babban abokin Daddy, Alhaji Umar ransa yabaci sosai, yace taje ta kaiwa Daddy wayar, zaiyi magana dashi, idan yaqi karba kuma tarabu dashi zaizo gidan da kansa anjima

Mamy tayi masa godia ta kashe wayar, sannan ta nufi d'akin Daddy


Kasancewar abude tabar kofar lokacin da zata futo baiji alamun shigowarta ba, Yana tsaye yajuya bayansa, yabawa kofar baya, yayinda yake kallon window din d'akin



Magana yake yi cikin fishi, gaba daya Idonsa yarufe, cike da tsananin bacin rai yake fadin "Zan koreta yanzu yanzun nan, ni yarinyar nan tun lokacin dana ganta naji na tsaneta, kuzama cikin shiri zan koreta daga gidana yanzu tana futowa ku kashe ta =?F? @&?
, duk itace Sanadin lalacewar komai, karka manta itace Sanadin barin Lubna daga cikin gidan nan, tayaya nida nakeso dukiyar sa data Insaaf duk sudawo hannu na zatazo ta hargitsa min komai?Akan kudi zan iya yin komai, sauran dukiyar gadonsu ina sane nahanasu,Dan haka sauran wadda take hannunsa ma zanyi kokari na qwace ta, Yaron ne akwai shegiyar basira shiyasa abin ya gagara, shikuma Amjad ta riga ta shanye shi bare nahada baki dashi, saboda haka ku kula, tana futowa agama da'ita, Shima Asim din Yana dawowa babu abinda zan jira, zan kashe shi..... Yauwa saboda..... "


Bata iya tsayawa tagama jin komai ba, jiri yafara daukan ta, haka tafara ganinsa bibbiyu, daga nan komaai na d'akin yafara rabewa a'idonta Yana zama guda biyu

Daqyar ta'iya daga qafarta tafuto daga cikin d'akin batare daya lura da'itaba

Ikon Allah ne kawai ya kaita dakinta lafiya, tana zuwa kuwa duhu ya mamaye idonta, tafadi a qasan tiles din d'akin


Amrah datake zaune tana kallo a system dinta cikin sauri ta diro daga kan gadon ta cicimeta tana kiran sunan ta "mamy...., mamy meyake faruwa?"

Kuka tafara tana jijjigata, ganin kamar mamy ta suma ne yasa tatashi Dasauri ta kawo ruwa ta yayyafa mata, cikin ikon Allah kuwa tafarka, tana Bude idonta tace "Amrah, tashi kikira Minal ku hada mana kayan mu, zamu bar gidan nan"




Gaban Amrah yafadi,kuka ne ya qwace mata, koma menene tasan cewa akwai damuwa mai girma, tace "mamy meyake faruwa? Meya sameki Dan Allah, kifadamin"

Jikinta ne ya dauki rawa, tace "nace ki tashi kikirata"
Amrah tatashi tayi dakinsu cikin sauri domin kiran Amina, mamy tana ganin fitar Amrah tafashe dawani irin kuka mai cin rai, sosai take kuka banda kanta dake mata wani irin ciwo, afili tafara furta kalmar "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"

Wayarta ta dauka takirashi, bugun farko ya amsa yace "Mamy nah"

Cikin dauriya Dan kada ya gane halin datake ciki tace "Asim kana ina?"

"ina Airport mamy, mungama komai, Ana sanarwa ma a shiga ciki"


Kasa riqe kukanta tayi, cikin gunjin kuka tace "Asim kadawo...."


"innalillahi..., mamy kuka kuma? Meya sameki? Meyasa kike kuka kifadamin waye ya6ata miki rai?"


Tausayinsa ya kama mamy, cikin kuka tace "Asim nacema kadawo gida yanzu yanzu, akwai matsala"









Sharhi
Sharhi
Sharhi>??







Amnah El yaqoub
' [2/17, 10:45 PM] El~Yaqoub: INSAAF

Writing by:Amnah El~Yaqoub

29&30

Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493


Wayar yakashe cike da tashin hankali, direban daya kawo shi Airport din yayiwa magana kawai suka juya
Gaba daya hankalin sa ya tashi, menene zaisa mamy kuka?
Tabbas akwai abinda yake faruwa agida, koma menene ya tabbatar ba qaramin abu bane, tunda har ta'iya cewa yafasa wannan tafiyar yadawo gida.


Suna hanyar komawa gidan yadubi direban yace "kayi sauri mana"

Cikeda ladabi yace "to Yallabai"

Gudu yaqara amma Asim Sai yake ganin kamar ma basa tafiya, wayar sa yad'auka yakira Amjad, bugun farko yad'auka tare da sallama

"Amjad kaje gida yanzu yanzu, ina tunanin akwai abinda yake damun mamy"

Cikin mamaki yace "Mamy kuma? Naga lafiya muka Barta agida, meyasa meta?"

"nacema kaje gida,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login