Showing 333001 words to 336000 words out of 388021 words

Chapter 112 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9526

karasa gurin da yake a kwance,
Idanuwanshi duk a lumshe suke tankar mai barci,
Ganin yanayin kwanciyar sa yasa ni zaton ko barci yakeyi a hakan,
Juyawa nayi daniyar in koma kada yaji motsina ya farka daga barcin da yakeyi, saboda gajiya ga aiki ga kuma sintirin asibiti don jikin na mama ya kara rikicewa sosai,
Da wata, kasalaliyar murya ya amsa min sallamata tare da dan gyara kwanciyar shi,
Still fuskan shi yana kallon ceiling din dakin kamar yadda na samay shi a kwance,
Ganin bai kalli inda nake ba har zuwa yanzu ya sakani karasawa bakin gadon cikin yi mai wani irin kallo,
Ai na zata barci kakeyi dana shigo, nake tambayan shi ganin idon shi a rufe suke ,
Ban samu amsa ba sai dai a haka na kai zaune a bakin gadon ina mai kura mai idanuwa na,
Shiru batare da yace uffan ba sai zuwa can naji ya furzar da iska daga bakin shi tare da sauke ajiyan zuciya,
Baka da lafiyane Yayana na samu kaina da kara tambayan shi, again,,
Idanuwan shi ya bude inda naga sun kada sunyi jawur, tankar wanda, yai kuka da su,
Kan shi, yadan girgiza min daga kwancen yace babu komai illa al,amarin ciwon nan na Mama da kuma ita kanta mama din da take kin bin dokokin likita ,
tana sauke ajiyan zuciya tare dan gyara zama ina mai fuskan tar shi da kyau nace,
Ai Alhamdullahi don naga zuwa yanzu ta samu lafiya sososai,
Mikewa daga zaune naga yayi yana, mai tsura min ido kamar mai nazari,
Sunana naji ya ambata a lokaci guda abinda yasa min natsuwa ke nan, yace nasan kina hakuri akan al,amarin mama to iana son kikara abisa wanda kikeyi da farko,
Cikin dan wani kallon jan hankali nace haba Yayana may kake nufi da hakan,
Kada fa ka manta cewa Mamafa uwatace nima, don haka banga abinda zai sa raina ya baci ba a kanta,
Fatana kawai mu rabu lafiya dasu kamar yadda muke addu,an mu rabu lafiya da namu diyan, nan gaba,
Murmushi naga yayi cikin dan jin dadin abinda na fada abin yai mai dadi har cikin ranshi, dama haka nake son nagani don samun matsayi na gaskiya azuciyan shi,
Meenatu naji ya ambaci sunana na amsa da cewa naam yace, sai naji yayi shiru kamar ya rasa abinda zai fada min,
Yayana ka kwantar da hankali mu dubi lafiyan mama da kyau don tasamu lafiya da sakewa ,
Ka daina tunanen komai da mama zatai min tana min ne a matsayinta na uwa agareni,
A hankali naji ya mika hannuwan shi yajawoni zuwa gare shi, yakai min kiss a saman goshina tare da sauke ajiyan zuciya,
Wani irin sanyi naji ya sauka min a raina don ko ba komai ai na samu natsuwan shi tun da naji ya sauke ajiyan zuciya,
Takalman dake saye a kafan shi na yunkura nafara cire mai su daga kafan shi tare da cire mai socks,,

****** ********** ******
Dakin babu kowa aciki kuma gashi tana son juyawa sai dai bazata iya ba,
Don haka a gurin da take kwance tasake, fitsari don matsuwan da tayi , saboda, hannun ta akwai, drip,,
Yaya Abubakar ya shigo dakin shida Lawal, mijin Fattu, zarnin fitsari ne ya daki hanncin su, a lokaci guda,,
Ga Anty Mariya bata a dakin basu san inda ta nufa ba, a lokacin,,
Babu hali a matsayin su na maza su taimaka mata, surabata da wanan kayan na jikin ta da sauran su,
Cikin ikon Allah sai gani na iso dauke da kayan su da naje dasu gida na wanke,
A bakin kofa na samay tsatsaye ganin yanayin su ya tayar min da hankali don sai nake tsan manin ko wani abune ya faru da Mama din,
Tambayan su nake a gagauce ko lafiya cikin dan bata rai yake ce min, Mama duk jikin ta ya baci gashi kuma Mariya bata dakin,
Subbahanallahi, da sauri na fada dakin inda na samay ta duk ta bata jikinta kace, kace,
Ba bata lokaci na shiga gyara mata jiki ta ko ina, duk sai da na gyaro na kuma ciro turare daga hand bag dina na fesa ko ina na dakin take gurin ya canza, kamar bashi ke wari ba dazun,
Mama da duk jikin ta babu lakka sai bina da idanuwa take har na gama gyara ta, tsab,
Nafito da kayan da ta bata daniyar naje na wanke su a lokacin Anty Mariya ta dawo tana cewa ashe kun zo ne wallahi ina can ina kallon wasu da sukayi hatsari aka kawo su wancan dakin,
Cikin bacin rai Yaya Abubakar yace haba Mariya may ranan zaman ki a nan da har zaki tafi kibar mara lafiya acikin wani irin yanayi na naiman taimako,
Irin halin da muka samay ta a ciki ba don Allah ya kawo muna Meenatu ba da ya zamuyi da ita,
Gurin da nake ta ke kallo tana kallon kayan da na debo zan tafi na wanke, a famfo,
Ki aje kayan ta wanke su, Yaya Abubakar ne ke fada min haka,
Cikin ladabi nace a,a Yaya bari kawai na wanke ta dan huta yau,
Baiso hakan ba amma sanin cewa nima yata ce Anty Mariya yasa shi yin shiru,
Dakin suka koma yayin da na wuce don wanke kayan kazantan da mama ta bata,
Sun samu, dakin tankar ba shi ba saboda yadda na tsabtace ko ina na dakin cikin dan kankanin lokaci,
Mariya ce tace ikon Allah lalai Meenatu tasha aiki dakin gane ya koma haka tsab,
Tunda nadawo daga wanke kayan nasamu tabarman dake a gefe na zauna, ina waya da Anty idon Yaya Abubakar yana a kaina, duk na dago idona sai munyi arba dashi ban san may yake kallo a jikina ba,
Stil ina kara daga ido muka kara hado ido da Yaya Abubakar, naga ya sakar min wani tsadaden murmushi, wanda yasani dan lumshe idanuwa na,
Kaina na kawar gefe guda cike da mamakin wanan kallon kurullah da Yaya Abubakar ke min,
Kamar may rada yace min kibawa Lawal key din motar ki zaikai ai maki service,
Kaina na gyada alaman toh ina kokarin ciro key din motan daga jakata,
Ba musu na mika ma Lawal din keys din motana yafita kamar yadda aka umurce shi dayi,
Dakin ya rage dani dashi da Mama da take daga kwance,saman gadon asibitin fuskanta yana kallon saman dakin,
Dan yunkurawa tayi kamar zata mike sai kuma ga amai yazo mata da sauri na mike nazo gaban ta tare da tara mata kwanon asibiti don tayi ciki,
Amai sosai Mama tayi duk ta galabaita zaban tausayi sai sannu muke mata,
Yaya Abubakar suka shigo tare da likita inda yadan duduba ta daga karshe yace muna ai reaction ne na alluran da ake mata,
Ranan bamu bar asibiti sai bayan sallah isha i ga Fatima wace ke ta faman kiran shi a waya tana cewa wai yana ina ne,
Bai bata amsa ba sai tsukin da yaja kawai, tare da cewa Polish woman, kawai mara hankali da tunane,
Wacece wai Anty Mariya ce ke tambayan shi, tankar ba da shi take ba don ko kallon inda take baiyi ba balle ya bata amsa,,
Muna a zaune munyi shiru ba mai cewa komai daga cikin mu,
Bayana na jingina a bangon dakin don naji dadin zama da kyau, idona yana a kan Mama wace ke barci a hankali take maida numfashi,
Dan motsawa Mama tayi kadan naga ya mike zuwa bakin gadon yana dan duban ta,
Ya juyo inda nake zaune fuskan shi babu walwala acikin ta ko kadan yace, muje na saukeki gida kada Amir yayi kukan nono,
Kala bance ba nafara shirin mikewa, don tafiya kamar yadda yace, din,
Yace wa Anty Mariya mu zamu tafi amma kila zandawo anjima,
Anty Mariya tace, ai dama ka zauna abinka tunda Mama ta samu lafiya,,
Mu kai masu sai da safe muka barsu a dakin ba tare da mun so tafiya ba,

****** ********** ******
Mun fara tafiya naji Yaya Abubakar ya da hura iska daga bakin shi, yace, cikin kasala, akwai abinda kuke bukatane a part din ku,
Nace cikin dan rausaya eh to gaskiya kayan tea mu ya kusa karewa, da kuma spices din mu,
Motar ya karkata zuwa shopping plaza don mu sayi abinda bamu, dashi a gida,
Sayayya sosai mu kayi, a wanan plaza din muka fito zuwa, gida duk a gajiye, mu ke,
A falo muka samu matan gidan namu gaba dayan su a zaune
Kallo guda zakai masu kagane cewa rayukan su a bace yake a lokacin,
Sam ban damu da su ba tunda babu wace tai min an dawo lafiya daga cikin su, sautin takalman kafana da ya cika ties din fallon da kara yasa aka dinga watso min harara
Ledojin da mu kayo sayayya su Aminu friends din su baba Ham???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?za suka kwaso zuwa part dina,
Ina shigewa shima maigidan ya shigo a gajiye, bai tsaya ta kan su ba sai ko karin hayewa sama yake abinshi ba, tare da ya tsaya, ta kan su ba,,
Fuuuu Fatima ta tashi tabi bayan shi atare suka shiga dakin nashi,
Inda take cewa ashe kana can tare da Meenat shine nake ta kiran waya ka ka kyaleni ,
Na kyaleki ne don banga amfani daukan wayan da zanyi ba naki tunda har kinsan inada mara lafiya a assibiti,
Tunda ba mahaifiyarki bace may zai sa ki damu da rashin lafiyan ba, ai,

ZEEE MAKAWA YELWA
[11/22, 10:17 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 7?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH,MAALIK UL-MULK

Na kyaleki ne don banga amfani amsa maki call din ki ba , don amsawa ai ba dole bane ko tsaye tayi sororo tana kallon ikon Allah,
Yace a hasale da ace mahaifiyar ki ce a asibiti ai da yanzu baki zauna ba, ina ranan cewa akayi bata jin dadi amma yini kikayi kina waya a gidan nan,
Gani maganan shi in serious yakeyin ta idan tace zara bijiro mai da zancen fita da Meenatu zaita sa zancen yakai wani high level ,
Don haka dole badon taso ba ta ja bakin ta tai shiru, don gudun bacin ran miji,
Amma tana fitowa daga part din shi muka hade a falo ina son na dauko, abu a store din mu,
Sai ji nayi tana cewa, idan dai mutum yace shi dan daukan alhaki ne sai ya matsa yai tacin hakin yan, uwa yagani,
Duk da bata ambaci suna ba nasan cewa dani take wanan zancen amma tunda bata ambaci sunana ba sai kawai na share ta,
Taci gaba da cewa don gadara har aiwa mutum sayayya shi kadai bada yan uwa ba,
Salawatu tace haba maman Aina, ai kawai kiyi shiru kibar wanan zancen, don bai da amfani, fadi,
A hankali na dubi Salawatu a cikin mamaki don na fahinci sun hada kai kenan a kan zancen, a kaina,
Inda Sadiya take tsaye a bakin TV na kalla sai naga tai min alama da inyi shiru murmushi nayi kawai don nasan fitina suke so,
Wanan cin amanan ai sai ke don kece mai son yin babakere da abin kowa,
Muryan maigida ne daga bayan mu yake cewa hakan,
Gaba dayan mu muka juya inda yake saukowa daga steps din a hankali, yana mai gyara hannuwan rigar shi da kyau,
Idanuwan mu duk a kan shi kowa na bukatan son jin mai zaifada daga karshe,
Fatima kina son ki sake min dokokin gidana da mugayen halaiyar ki da kika saba da su,
Wanan abin da Yaya Abubakar yakw mata yana ci matarai sosai don ita bata bukatan ace, yana saka bakin shi ga zancen matan gida,
Shiko a nashi bangaren baya kaunar wanan irin mugun halin kishin na Fatima ,
Tana son kawo mai rudani agida don babu wanda bata fada dashi a cikin abokan zaman ta,
Kafin ya karaso ta sa kai zuwa cikin part din ta buguzun, buguzun tana magana a ciki ciki,
Dakatawa yayi daga step din karashe ya rakat da harara tare da sake tsuki,
A inda muke tsaye yadan juya yana kallo yace zan koma asibitin naga ko ta farka, yanzu,
Sai a lokacin suka fahinci cewa mun dakata ne asibiti saboda jikin mama da yai tsami,
Daga inda nake nake cewa bari na kara masu zannuwa koda za,a bukaci hakan ko,
Yace, hakan na da kyau tunda batasu takeyi da zaran an canza mata shi,
Daki na shiga ban wani dadeba nafito da ledan zannuwa harda, dan abin tabawa nace a kaiwa Anty Mariya,
Ganin zai kara fita zuwa asibiti yasa Fatima bin shi da kallon mamaki don baya fitan dare haka,
Sadiyace gab da zai fita take cewa yau jikin na Mama ya matsane ko,
Daga inda nake tsaye nace a hankali yau jikin na mama gaskiya ba dadi, don maganin da ake mata allura yana bata reaction sosai wallahi,
Fatima wace take daga kofan shiga part din ta tana sauraren mu sai jikin ta yai sanyi,
Don sam tunanen ta bai kawo mata cewa asibiti muke ba tun dazun,
To amma idan hakane, wancan ledan da ta shiga dashi daki na may ye shi,
A hanya ke nan ya tsaya yai mata tsaraban shi ke nan, ko, koma nay ye a cikin shi dai ai, zai bulla,

****** ********** ******
Tuki yake yana waya da Aliyu wanda ke tambayan lafiyan jikin Mama Ladi,
A hankali ya kira sunan Aliyu inda yake sheda mai cewa gaskiya halin Fatima ya canza a yadda ya san ta da farko,
Subbahanallah tayi ma wani abin ke nan kum? ko ?
Nan yake fada mai irin abubuwan da Fatima take mai wa yan da basu dace ba sam, a rayuwa harda rashin kula mahaifiyar shi da bata yi dama kowa nashi,
Aliyu jikin shi yai sanyi don jin abinda ake fada akan yar uwar shi duk kunya ya rufe shi don baima san ko may zaice, ba,
Hakkuri ya fara bawa Abubakar inda yake cewa zai yi magana da mahaifyar su don ta kara tsawata wa Fatima din,
Ya isa asibitin ya samu Mama ta farka daga barci maganin ya dan saketa
Inda take ya wuce direct har bakin gado yadan rankwafo yana mata yaya jikin tare da dan yi mata tambayoyi akan yadda, take ji,,
Ledan hannun shi ta mikawa Mariya yace ga shinan wai a kawo maku inji Meenat ta karba tare da budewa da sauri,
Peppe soup din kassan rago ne yaji hadin kayan gargakiya sai kamshi ke tashi daga cikin sa,
Sai zannuwan da na aiko masu dashi daga cikin zannuwana, don su samu na canzawa,
A hankali Mama Ladi ta dan lumshe idanuwan ta tare da sauke ajiyan zuciyan
A cikin plate Anty Mariya ta zubo mata da yawa, tare da drinks
Kafin wani lokaci Mama ta lashe shi tas tare da shan ruwan drinks din da aka zouba mata,
Ya Abubakar yana daga gefe guda a zaune yana latse latsen wayan shi tankar baya kallon abinda ke faruwa a dakin,
Ya dago kai a cikin sauke ajiyan zuciya yana tambayan Anty mariya cewa jikin na Mama bai kara yin zafi badai ko ?
Mama da kanta tai yunkuri ta dan mike zaune tana cewa tun Aminatu ta goge min jiki da ruwan sanyi ban kara jin zafin jikin ya dawo ba,
Hmmm kawai yace ba tare da ya furta wani abuba don abin dariya da mamaki yaba shi a ran shi wai yau Mama ce da kanta ke cewa wai Meenatu ta taimaka mata taji sauki,
Amma a fili sai cewa yayi, yanzu tunda har kin sha wanan ai saiki kwanta ki barci ki huta ko zaki kara samun sauki,
Babu bata lokaci Mama kamar karaman yarinya ta dan koma a hankali ta gyara kwanciyar ta, bai bar dakin ba saida ya tabbatar da cewa Mama ta samu barci mai nauyi yai ma Anty saida safe ya dawo gida,
A lokacin shabiyun dare har yadan gwauta amna abun mamaki a falo ya samu Salawatu da Fatima zaune wai suna kallo,
A ran shi ya ja tsuki ya haye sama abin shi Fatima wace dama a cikin shiri take ta mara mai baya,
Salawtu ma yar ganin kwam bata wani dauki lokaci ba ta kashw wutan ko ina itama ta shige nata part din,

****** ********** ******
Washe gari ina idar da sallah na koma na kwanta saboda yadda na kwana da ciwon kai da zazzabi mai karfi, na damuna,
Ga gabobbina duk ciwo suke min agajiye nake jin jikin nawa ba dadi,
A cikin bacci na rika jin ana dan kiran suna na sama sama, nadan rika jin muryan Yaya Abubakar yana cewa Meenat, Meenat na farka adan firgice,
A cikin karfin hali na bude idanuwa na nagan shi a tsaye saman kaina dauke da Amir a hannun shi,
Lafiya kike yatambaya cikin kura min idanuwan shi lumsarsu, da ya kashe ni da su,
Da kyat na iya bude bakina ina cewa ban jin dadi ne yau da zazzabi na kwana,
Ido waje cikin nuna damuwa take cewa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login