Showing 276001 words to 279000 words out of 388021 words

Chapter 93 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

843

sai anjima ina cewa zan dan ke waya bayi ne please har tana min sheri wai ko a bin ne yazo ta taso,
Dariyan karfin hali nayi a cikin yar shagwaba nace aini Anty a gurin ki naso na haihu na sha gata tace aiko a nan din ma da kike Meenatu za ai maki gata,
Nace sosai ma tace to ai kinga ba matsala ke nan nace dashi don a nan fa anty ruwa masu mugun zafi ake wa mutum amfani da shi
Dariya sosai tayi tace ai yanzu nagane wayon ki watau gurin Anty asha ruwan sanyi ko nace wallahi ko,
Hiran duk yadda naso muyi shi baiyi ba don irin abinda naji yanzu yafi na dazun ciwo sosai,
Don haka ban san lokacin da na kashe wayan ba na kai durkushe, tare da murde baki idona yana wani fitowa waje gaba daya,
Nakai kusan minti uku a hakan kafin a bin ya sake ni, inda da kyat na samu na rarafa na hau gado azatona hakan zanfi dan samun sauki,
Ai kamar an kara min tsananin abin ne irin yadda nake ji a lokacin
Tunda nake duniya ban taba sani cewa akwai ciwo maka mancin wanan, ba, sai yau,
Ni kadai a daki cikin dauriya da karfin hali irin nawa, nake ta gumurzu a dakin Mama Dije, wace a lokacin tana can gurin da suke yin yar dawo, na shan gida,,
Ina daga duke a bakin gado na kifa kaina a saman gadon dakin yar dattijuwar matar kakan nawa,
Naji muryan maidakin tana cewa subbahanallahi yaya ankayi Meenatu,
Ban iya magana, ba sai dan kara dukar da kaina cikin cinyoyi na da nayi, don azaban da na keji a lokacin yafi karfin a fadi,
A hankali ta tako gareni a rude tana cewa cikin dan tausa murya kamar wace bata bukatan wani yaji ,
Yaya kike ji Meenatu ko dai in fadi ne mu tafi asibiti, yanzu,
Daidai lokacin abin da nakeji ya fada min a nadago kai na da goshina da yai zufa don azaba nace wai Dije marata ce ke min wani irin mugun murdawan da ban taba jin irin shi ba,
Tace sannu sannu kinji Allah dai ya raba ku lafiya sam yau ko a zuciyar da nake amsawa ban,iya amsa wa ba,
Da sauri mama,Dije naji muryan ta a waje tana cewa yaro aje gurin malam ace ya rubuto masu suratul Maryam,
Sai kuma naga ta dauko wani dan abu mai kama za an dunkule hannaye tana kokarin daurayewa daga bisani ta jika shi a cup,da ruwa mai yawa,
Suna tsaye a kaina daga ita har abokiyar zaman ta sai faman sannu, sannu yar nan su ke min,
Kafin wani dan lokaci wanan abin da Mama Dije ta jika a ruwa har ya wani babbaje a cikin ruwa ya bude kamar abin sihiri ta koma kamar yatsu,
Sai naji tana cewa ai yatsu Fatima da aka jika hae ya jiku alamar haihuwa yazo ke nan,
Gabana ya fadi da naji ta ambaci cewa haihuwa ya zo kenan watau ana nufin haihuwa zanyi ko may,
Wata zuciya tace min kai wanan shirmayn Mama Dije ce take ta faman kira min haihu da sauran time,
Yaro yazo da wanan rubutun da aka aika akawo daga gurin malam,
Yace wai ancd na shaye dukka a lokaci guda na kuma sha da Bissimillah idan zan sha,
Na karba bayan wancan ruwan Yatsun Nana Fatima da na,sha da farko, na kara kinkiman wani ruwan rubutun, a cikina,,
Wanan karon tun shan wanan ayan danayi na babu sauki ga al,amarin sosai nakuda ya taso man,
Duk da malam yasan cewa idan har mace zata haihu da yardan Allah da zaran an rubuta mata suratul Maryam, insha Allahu, zata, haihu aranan da yardan ubangiji bada dadewa ba,
Wani wani rubutun ya kara aikowa dashi wanda ya rubuta Bismillahi kafa 21 ya wanke da ruwan ganyen gwandan gida, yace na yi sha daya ko biyu zuwa uku gaba dayan shi , a gani,
Sosai hankalin mutane gida duk ya tashi kowa na part din malam tsoho da namu part din parents dina hankalin su yana tashe,
Yaya Ibrahim din na ya matsawa malam tsoho da cewa a fito dani zuwa asibiti tunda yanzu waye wan kaine,
Don may za,a ce a barni a cikin gida ana ta dura min rubutu kala, kala haka.
Motar makwabcin mu aka samu wanda bai dade da dawowa daga aiki ba,
Abin tsofafin mata Mama Dije wace tasan kan haihu sai cewa sukeyi ai dadai ayi hakkuri agani zuwa dan wani lokaci kadan ko zan haihu,
Ya Ibrahim yace don Alkah ku kamota mu tafi kada a tsaya wani tunane can,
Leda mama Dije tafara sakawa gurin da zan zauna a motan sanan na shiga tare da taimakon su,


ZEEE MAKAWA YELWA
[10/12, 6:09 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8? 3?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH AL MUQATADRI

JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALLOVER THE WORLD
ALLAH YASA MU DACE SAI KU TAYINI ADDU,AN AL,AMURORI PLEASE,
ALLAH YA RUFA MUNA ASIRI DUNIYA DA LAFIRA ALLAHUMA AMEEN=?O?=?O?

Zaune yake saman kujeran da ke a cikin office din shi , sai dai hankalin shi gaba daya yana ga computer dake gaban shi,
Sai dai a zahiri zaka zaci aikin ne yake har cikin zuciyar shi gaba daya,
Amma zancen ba haka yake ba a can ciki don sai faman yan tunane tunane yakeyi a ran shi,
Sam ba abin da ke masa dadi a lokacin sai faman tunanen yar mutane da ke dauke da cikin shi a jikin ta kuma ya iya halin ko in kula da ita,
Bayan yasan cewa yanzun haka a gida take, zaune kuma mutane za,su iya fahintar irin halin da suke ciki shi da ita,
Cikin sauri ya wani lumshe idanun shi cikin jin takaicin kan shi da kanshi,
Ya kara numfasawa tare da kiran suna ubangijin talikai da cewa Ya Salam,
Tausayin Meenatu ne yaji ya sauka mai a zuciya again don yasan cewa mace mai ciki tana a cikin wahala a koda yaushe,
Duk da dai laifin na Meenatu ce wace ke kokarin raina shi a ganin shi,
Kawai don yanzu yana auren Fatima kaunar Aliyu zasu dauki karan tsana su dorashi ga Aliyun,
Mayye na Aliyu a cikin wanan zancen da har su ke kokarin nisanta kan su da shi haka har suna kokari, kawowa alakar su da Aliyun wanda yazama dangan taka a yan zu,
Kawai ba don cikin nan ba da sai ya tabbatar wa Meenatu cewa shi fa har yanzu a matsayin yayanta yake ba wai miji ba kawai,
Gaskiya dole ne gaba dayan su ya nuna masu cewa shi fa ba a kawo mai raini ko kadan ga al,amarin shi,
Bai kai ga karshen tunanen shi ba akai nocking din kofan office din alaman wani zai shigo a lokacin,
Wanan bakon mai son hada alakar kwangilar haka, wata rijiyar mai da su ne ya katse mai tunanen shi, da yake sai dai duk da haka hankalin nakan yar amanar shi Meenatu
Irin yadda yake ji a lokacin duk hankalin shi yadaga ya koma gare ta da tausayin ta,
Mace mai ciki abin tausayi ce don son kulawa amma gashi shedan ya rude shi har yana dan share ta,,,

****** ********** ******
Yau sam bata gane wa Dodon ta ba saboda tun dare yake wani irin kugi, da hamma mai wari,
Duk wani abinda ya kamata ace taba shi tabashi tun safe da ya fara mata wanan saddabarun, shi,
I zuwa yanzu abin ya fara isar ta sosai don lalurar shi yai mata yawa ga jikin girma ya fara kamata,
Yanzu bata iya mai irin hidimomin da take yawan yi mashi a da can baya sosai,
Wanan hamman mai warin da ya keyi yasa duk hankalin Hajja ya tashi yau sosai,
Tun yana yin hamma har ya fara yin kuka a hankali wanda wanan kuka ne ya tayar mata da hankali,
Daga gurin da take a zaune tana tunane abin yi wanda zai fisheta zancen da bokanta yai mata ya fado mata arai,,
Nace solution gudane yanzu ya saura gare ta shine ta samu mahaifan gidan surukin nata ko kuma dan digon jinin mai jego ta lasawa Dodon ta,
Da sauri ta gyara zaman ta saboda karatunawa da zancen bokan da tayi
Inda take cewa ita ta yaya zata gane cewa Meenatu zata haihu har ta samu wanan abin tabashi,
Boka yace duk ranan da kika ji dodon ki yana kuka tankar na jariri to wanan ranan ne zata haihu,
Jin irin wanan kukan da boka ya suffanta mata cewa Dodo zaiyi shine yau taji yanayi da kunnuwan ta,
Hakan yasa ta kasa zaune ta kasa tsaye sai tunane takeyi na yaya zatayi, ta samu abinda ake bukata,
Jin Dodon sihirin nata yana ta kokarin daga murya shi gurin wanan kuka yasa ta figan gyalenta da sauri jikinta har yana ciri, tafita, batare da tasan inda zata dosa ba da farko,
Dabara ya fado mata saboda tasan cewa anyi haihuwa a gidan makwabtan su don haka sai ta nufi gidan don yin barka,
Har zata shiga sai wata zuciya ta ce mata ai da zaran ta shiga gidan asirin ta ya gama tonuwa ke nan don duk abinda ya faru za, a zargeta sosai,
Juyawa tayi zuwa kafan bayin gidan can ta bayan gidan don ta duba ko zata samu wanan irin jinin haihuwan ta kaiwa dan fitinan Dodon ta
Allah ya tai make ta tana zuwa sai ga irin jinin da take bukata takai mai tagani a makwararan ruwan gidan dake fita ta bayan gidan
Da sauri tunkafin wani ya ganta tai sauri dauka a leda tabar gurin gida gudun wani ya gan ta,
Ta isa gida jiki na rawa ta gi kamar yadda bokanta yace mata tayi idan ta samu jinin,
Hakan da tayi yasa ta dan samun saukin kukan da yake mata duk yinin yau din,

****** ********** ******
Yayana Ibrahim wanda ke a gaban mota zaune tare da Mama Abu uwar gidan mama Dije sai faman sannu sannu yake min,
Ni da Mama Dije ce a bayan mota sai cewa take min kiyi addu,a, a bakin ki kinji Meenatu,
Daga gurin da yaya Ibrahim ya ke yana jan motan makwabcin mu sai dan juyowa ya keyi yana cewa Sannu meenatu yi Salati kinji,
Yayin da yake jin irin yunkurin da na keyi idan abin ya motsa min, daga bayan mota,
Muna barin uguwar mu bada wani nisa sosai ba wani irin mugun ciwon mara yazo min a lokaci guda
Wanda ya sani yin wani irin nishi mai karfi a lokaci guda yayin da kukan Baby ya ruda motar a lokaci gudan,
Duk wanda ke a motar saida yaji irin nishin da nayi mai karfi yayin da Baby zai fito,,
Mama Dije sai cewa take masha Allah Alhamdullahi an sauka, kai Iro samu guri ka tsada matan nan don Allah,
Cikin rudewa tare da dan rikicewa yake kokarin samun gurin da zai parker motar da kyat ya samu ya tsayar da motar sai rawa jikin shi yake yi,
Mama Dije sai cewa takeyi abin yazo da sauki, har da uwar tafiya gaba daya,
Mama, Abu tana cewa mai muka samu ne Dije naji kukan kamar na maigida,
Shine muka samu yaya, gashi nan dan nema gudan babba da shi kamar dan shekara,guda,
Ina daga gefe ina mai da numfashi guda guda a hankali ina ji tankar a mafarki nake,
Cikin hikima su ka gyara min jiki ta yadda bazan sha wahala ba, gurin fita daga mota,,
Shiko jaririn sai tsala ihu yakeyi kamar mai sanar da sako a lokacin, ya iso a lokacin,
Ta gefen idona nake satan kallon dan kyakkyawan Baby dashi mai kama da mahaifishi da komai, sak,
Mun juyo zuwa gida yayin da nake duke rakube a gefen motan na nade kaina a cikin hijab dina,
A hankali yayana Ibrahim ya jawo motan da yake ja har zuwa gidan mu,
Tunda motar ta tunkaro gidan mu idon mutane yato a motar caaa gaba daya suna son su ji ko may ke faruwa sunga mun dawo,
A hankali aka bude motar wanda yaya Ibrahim ne ya fara fitowa daga bangaren shi,
Ya,fito yana kokarin bude marfin gefen da nake zaune ina dan murde baki na don wahala,
A yadda Yaya Ibrahim ya aje motan, mutanen dake daga gefe baza su iya ganin fitana na daga cikin motar ba,,

Kafin wani lokaci duk gida ya rude da ihun yara masu son harkan party idan an haihu,
Direct part din malam tsoho muka nufa inda aka shiga harkan jego gida duk ya rude da barka barka,
A lokacin da aka je gun mama Ladi yi mata barka sai cewa tayi ita don an raina ta shi babu, wanda ya fada mata cewa ina rusun, ne sai bayan na haihu, za,a fada mata,,
Kishiyar ta mama sa,a ce tace don muna gida guda zaki ce haka amma aikin san akaida yadda akeyi sai an haihu ake sanar wa sai ko idan abu yai tsauri ne ke fada har kowa yaji Allah ya sauwaka,
Baki Mama Ladi ta tabe tana cewa ai gamu gani dai ko yanzu ga fili ga mai doki,
Allah ya sa muga alheri inji mama Sa,a kishiyar ta ce daga part din ta inda take sakowa Mama Ladi magana,
A take a,kafara sanarwa yan uwa, makwabta da abokan arziki haihuwa na abinda nakeji ana fada yau gashi a kaina, wai na haihu,
Malam tsoho ne ya shigo cikin gidan da kanshi, nda ya kira mama Dije a turakarsa yai mata magana wanda babu wanda yasan may ya fada mata sai Allah,
Wanka akai min kamar yadda ya ke a al,adan hausawa ai wa mace wanka a haihuwan farko,
Nasamu dakin Mama Dije sai kamshin turaren wuta na tsinke yakeyi ba bata lokaci na koma a can gefen gado na kara gyara jikina tsab,
Ina zaune an zubu min kunun mai zafi a cup gudan mai yawa wai na shanye shi dukka inji mama Sa,a kishiyar Mama Ladi,
Dama aminiyar mahaifiya tace ita duk cikin gidan mu sun fi shiri da Mama na saratu,
Hakan yasa ta zage a yanzu tana nuna kulawanta gareni kamar yadda take yi a koda yaushe, akan al,amarin da ya shafi mahaifiyata,.
Anty Amarya na fara lalaba a wayana don na sheda mata, zancen haihuwan,
Kiran farko ta dauka tana cewa Allah Sarki Meenata yanzu yayan bk ta bugo min waya cewa ansauka, lafiya,
Na wani dan lumshe idona don farin ciki da tuna wasu yan abubuwa da suka wuce yan awowi da suka shige,
Anty Amarya tace ki kula da lafiyan jikin ki sosai Meenat don yanzu shine jegon yake,
Tundaga yau da kika haihu har zuwa nan da kwana hudu idan kin kiyayye ka,idojin jego shike nan zaki samu lafiya ingan tace har abada,
Kisan shi jego baida sabo baida tsoho duk guda ne yayin yin sa,
Don koda mace ta taba haihuwa idan ma na sha biyu zatayi dole ne sai tayi waban jegon sosai in ba haka ba ta lalace,
Nace a hankali subbahanallahi Anty tace wallahi haka abin yake Meenat don kinga idan baka kulla dashi ba shine da zaran girma ya fara zai fara baka problems kamar ciwon baya, ciwon kafa, mutuwan jiki,
Wanda akasarin matan yanzu shike yawan damun mu sosai sai kiga mace shekarunta bai,kai ko ina ba amma tana fama da baya da kafa da duk wani sign dake nuna girma a gare ta,
To don dan wahala da zakiyi kwana hudu zuwa sati shine bazaki daure ba kiyi ki huta
Kin,ga matan da can har wata uku suke kai suna shan ruwan zafi da wankan jego, amma yanzu inna bamu damu ba sam da kulla da lafiyan jikin mu,
Kici abinci lafiyayye kisha kayan yaji a tea ko a kunnu wanda zai kara maki lafiya a duk sassan jikin ki wanda yanzu duk mun bari saidai kawau muci abinda ke a ran mu,
Idan anyi maki wanan miyan na maijego da akeyi don Allah Meenatu ki zage ki shashi sosai don zai wanko maki duk wani abinda bakiyi tsanmanin sa ba a cikin ki,
Tambayan,ta nayi anty miyan maijego kuma tace cikin dari eh mana Meenat kinga wasu miyan kan ragi za ai maki yaji kayan kamshi har su dadddawa sosai ki shashi sosai ke kadai za,a ajewa shi gaba daya ki shanye,
Sai kuma wasu za,samu kifi mai kyau ma tsoka a bare shi sai a daka kayan yaji wada tacce yadda zaki iya ci don kin san cewa yanzu ulcer yayi karfi a jikin mutane,
Za,a samu ruwan toka mai kyau da kuka wanda dashi za a kada miyan da shi, sai a dan tsiyayaya ruwan toka kadan kada, yai mugun yawa a hada miyan da shi kema da ankawo maki anbude kamshin daddawa da kayan yaji zai daki hancin ki sosai kifi kuma zaki gansu a ciki da yawa ,
Wallahi Meenatu kina cin wanan miyan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login