Showing 282001 words to 285000 words out of 388021 words

Chapter 95 - Tarko Book Complete Hausa Novels by Zainab Makawa.doc

22 Sep 2025

9549

gama ga miya nan wanda zan diga sha,
Maganar Anty Amarya,ne ya fado min a rai na zancen miyan da tai min ida aka shigo dauke da kwanon tuwo again,
Banda daman in mussa cewa na koshi dole ina kallo aka jawo plate aka zuba min a cikin shi ,
Ganin yadda ake ta zuba min abinci da yawa wai duk ni zanci ban san lokacin da nace don Allah abarshi haka wallahi ko yanzu a koshe nake,,
Wanan dan abinci zaki ce kin koshi Meenat ai kawai bude ciki zakiyi ki ta zubawa,


ZEEE MAKAWA YELWA
[10/16, 9:56 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8? 4?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL MUQADDIM,

Ina mai baku hakkurin rashin jina kwana biyu da bakuyi ba wanan yafarune ga yan matsalolin rayuwa da fatan za ai min afuwan kamar yadda kuka saba,,,
Wanan cigaban labarin danaturo guntunshi ne shekaran jiya bissa ga kuskure,

Zaune suke gaba dayan su a dakin mahaifiyan su sai hira suke yi kowa da abinda yake fadi,
Anty Safiya wace fitowan ta ke nan daga part din malam tsoho gurin mu, tazo ta samu yan uwanta a dakin mahaifiyan su,
Nan ta shiga yabon irin kaman da jariri yayi da mahaifin shi take ran Mama Ladi ya baci da tsawa ta katse Safiya da cewa,
To uwar yan tsurku kowa ya tai yagani babu wanda yace kallallahu sai ke fadi ba antambaye ki ba,
Mama saboda kawai na fadin gaskiya ai don naga kaman su ya baci ne da yaya Abubakar shi nassa na fadi,,
Idon ki dai ya gwada maki hakan amma in ba ke ba nikan banji wanda yace hakana ba,
Sai babban yarta ke cewa aiko gaskiyan Safiya na walle kamar su yai yawa da mai sunan malam,
Dama ba wani fada ke ga yaya maimuna ba gurin mama kasancewar ta yar fari kuma bata da komai a kauye take aure ita,
Walle kada in karajin wanga zance har wani ya jiya yaji dadin fadin haka agaban su,
To ke Innan mu hallan mi ki ka nufi wai,?
Naga dai wanga Da dan Yaya Abubakar na shi yai ciki nai to mi yakawo wani zancen cewa abar danganta shi da shiya ?
Ke walle a hir din ki ban son maganar banza maganar wofi ace maku banda hankalina ,
Meenatu wace ar zaune sokoto shiko shina can Abuja,
Salati anty Safiya tasa tare da saurin duban hanyan shigowa part din sai kuma ta leka part din Mama Sa,a taji ko tana kusa,
Cikin tausa murya tace Innan mu walle bari bari ka da wagga magana tafita ko nan da can wallahi,
Don wanga zance na kawo muna bacin rai gaba dayan mu don ko shi uban Dan wallahi tallahi ana jinku dashi Inna,
Jinin ki ? jinikiza wa sheri irin haka acikin babban gida irin wanga walle abar zancen ga anan tun rayuka basu baci ba,
Za tai magana Anty Mariya ta katse da cewa Innan mu na fada maki tun wuri in rai ya baci hankali ka bido shi,
Bacin rai yasa ki barna wa jiniki suna ga banza cikin dubun dubada har gari ya dauka dan Allah dai Inna ki bari kawai,
Ganin duk yaranta basu goyi bayanta ba kuma sun bata rashin gaskiya yasa ta yin shiru,
Anty mariya tace ai naso in kawo shi Dije tace min wai malam yace kada a fita dashi ko ina sai anyi suna,
Hakan ya kara tunzura Mama ta fara yin sababi da jidalin cewa ita da dan ta amma ana gwada mata fin karfi ga al,amarin shi,
Duk wani abin mai sunan malam sai ai ta shige mata gaba a kan shi ita yanzu ta gaji da hakkurin hakan bazata kara yarda ba,
Anty Samira tashigo goye da goyon ta a baya tana cewa ashe duk kun rigani ganin Baby kai amma wanan yaro kamar Yaya Abubakar yai kaki ke har yan yatsun shi walle duk na ubanai na,
Wani irin tubure fusks Mama Ladi tayi don inda tana iyawa da ta ci masu mutunci don kada su kara, fadin haka a gaban ta,
Kafin ai wani zance sai ga wayan Yaya Abubakar a wayan Anty Safiya cikin murna ta dauka tana cewa Baban jego Baban jego hoo,
Ya ce hmm Safiya ya kuke ya gida da jama,a tace duk lafita kalau yayana,
Yace dama na kiraki ne ince duk abinda ya kamata ayi yadda akeyi a al,ada sai ki fada min munyi magana da Mustapha jiya da dare yace yau idan kin shigo zai gan ki , kuyi magana akai,,
Ta ce yanzu haka ma ina cikin gidan mu gamunan gaba dayan mu har Innan mu zaune,
Yace OK kina kusa da Mama ke nan ko ta ce gata yayin da take mikawa Mama Ladi waya a hannun ta,
Ta karba tare da wani yatsune fuska tankar Abubakar din yana a gaban ta,
Sama, sama suka gaisa dashi batare da wani dogon magana ba,
Ganin cewa ita batai mai murna ba ya sa,shi gane cewa, batai farin ciki ba da wanan haihuwan da akai mai,
Yace Mama barkan mu fa da haihuwan Meenatu Allah ya raya yasa dadin musulmi ne,
Amin tace cikin wani irin murya kasa kasa babu nuna farin ciki a tare da ita,,
Yace abawa Safiya waya bayan ya gaisa da duk kan yan uwan shi sun mashi barka abinda ya wanke mai bacin ran mahaifiyar shi ke nan tun da yaji yan uwan shi nata murna suna mai raha cikin jin dadi da so da kauna, irin ta yan uwan taka,
Bayan ta karbi wayan ne yake ce mata duk shawaran da ya dace suyi kafin taga yaya Mustapha din,
Bayan ta kashe waya take kara masu bayinin yadda sukayi da yaya Abubakar akan zancen abinda ya kamata, su yi,,
Anty mariya ce ta fara magana da cewa, gaskiya icce ya kamata ace ankawo tun da safe tunda shina jego,
Zubur mama tace wani irin Ice kuma ba gidana ba dukka sai ankawo wani ice can kuma ,
Har suna hada baki wurin cewa haba Mama ko gida na fa ai hakin shina ya kawo ice,
Safiya tace sai gero da kayan yaji ko, da sukari da kayan shayi tunda yana da halin su,
Samira wace ke tsaye tana jijiga dan ta dake goye a baya yana mutseniya tace sai abin kauri ko in anyi kwana uku,
Aiko acikin masifa Mama tayo kanta da fada tana cewa tunda baku san ciwon kanku ba shine har zakuyi irin wanan lissafin haka ga dan uwan ku,
Inna mu amma naga ko mu munka haihu ana kawo maki irin wagga abubuwan da munka lissafa ko,
Tace don kun haihu ankawo min fa ita ba gida bana dole na ankace sai anyi su,
Mafarin akashe masu jiki su mi aggare su mi zasu kawo wa iya ka cewa zasuyi aiduk gidana ba sai anyi komai ba, ,
Ikon Allah inji ?nty maimuna wace duk zancen da akeyi bata ce komai ba don tasan bata da wani power gurin mahaifiyan nasu tun da bata da komai ita,,
Tace haba inna wanga abu fa duk yiwa kaine da Meenatu dashi mai sunan malam duk gudana ai ko ?
Haba ina wuta Mama ta saka wanan boyar Allah, da ta fadi haka cewa duk guda muke nida yayana,
Nan ta shiga sake magana a cikin masifa da jidali tana wa diyan ta cewa ita fa bata yarda azo a kashe, ma wa yan nan matsiyatan mutanen kudi
Su zo komai ba su kashe, wa mutane ba don tun yanzu banga komai da su ka aje wanda zasu fitan wa mutane kunya ta na su bangaren,
Mama duk yadda an,kai muna ko ita sai an mata tunda duk guda na muke
Shin wai wa zai bada kudin da za ai hidiman ba uban Dan na ba, Yaya Abubakar zai bayar, kuma shina ya haifi dan shi, don ya kashe ma danshi kudi,
Don Allah ku, komai kada ku rage ga duk abinda yaje so ai ma iyalin shi, daga haka, ta sa kai zuwa waje abinta tana dan jijiga goyon ta Samirace mai wanan maganan,
To issasa ai sai ki taho kiyi wadda kika so tunda ubanki na ya bada kudin
Daga ida take waje tace a,a wallah uba Da dai na yaba da kudin ai mai kashin kunya,
Aiko Mama tashiga surfa ma Samira zagin fitan arziki har sai da Safiya ta dagawa Samira hannu da cewa tayi shiru,
Daga haka tabar part din mahaifiyar nasu zuwa part din mu, cikin bacin rai,

****** ********** ******
Malam tsoho ne ya shigo dakin Mama Dije inda nake jego, daga gurin da nake a kwance ga kaskon garwashin wuta a gefe guda sai dumama dakin yakeyi,
Ina ganin shi nai saurin mikewa zaune da ga kwanciyar da nayi, ina cewa sannu malam,
Cikin murmushi yake ce min Meenatu kun tashi lafiya yaya dare ina fatan babu matsalan komai ko ?
Kai ya na kasa cikin dan murmushi ina wasa da yatsun hannu na nake cewa ba komai malam ya dawai niya damu,
Yace waya fada maki ina dawainiya dake bayan kin ce baki son tsoho,
Dariya mukayi gaba daya daki sai Mama Dije ke cewa wai har yanzu baka bar wa takwaran naka ba yace yanzu kan ai dole na hakkuri su je su karata can birni taraiya tare,
Aka kara sa dariya adakin, alaman ganin zai zauna ga yar kujeran dakin yasa, ni, saurin cewa bari a gyara maka guri mana malam ya daga min hannu cikin dakatarwa yana cewa, nan ma ai ya isa Meenatu,
Yana zama yacewa matar shi miko min yaron nan Dije da sauri ta gyara shi cikin dan farin showel da yake ta miko mashi shi,
Idon ya kura,wa yaro zakace ko kallon shi ya ke yi amna idan ka lura da kyau, addu,a yake maron, tsayin wani lokaci ya dago kai yana kallo na tare da cewa wanan yaron tankar lokacin da mahaifin shi yake kaman shi sak,
Murmushi kawai nadan yi ba tare da na ce wani abuba sai Mama Dije ce ke cewa ai da shi kowa ke cewa yai kama amma ance Ladi tace wai sam abar fadan haka ?
Da sauri na dago kaina na dubi Mama Dije a cikin mamaki don jin Mama Ladi har da gudan jinin ta tana bakin ciki kuma,
Muryan malam ne ke cewa ai al,amari Ladi sai Allah kawai don abin nata bana kai sake bane,
Mama Dije tacd hassada ne kawai da bakin ciki mutum tun yana sheri har yai wa kan shi yanzu ai ita ake ji don kowa ya dawo daga rakiyan ta,
Murmushi naga malam yayi tare da kokarin mikewa tsaye yana fuskantar gurin da nake zauns yace,
Ameenatu zan sa akawo maki wani ruwan rubutu ki shanye shigaba daya Allah ya sa agama wanka lafiya ,
A hankali na, amsa mashi da cewa Ameen yaci gaba da cewa na tura Sahabi ya debo ganyen da zasuyi wanka dashi saboda yanzu ba a samun shi nan kusa don duk anyi gine gine a guraren,
Bayan fitan malam ne Mama Dije ke cewa ai dole na Meenatu kuga irin wanga abu don miyagu (muggai) sun,yi yawa yanzu,
Tace cikin ma dai ai Allah ne yanufa ki samu inba,shiba irin mugun daurin da macuciyar ga tayi aida ba hakan ba,
Da sauri na dago kaina ina cewa wacece macuciya kuma da har zata hana ai abinda Allah ya tashiyi,
Tace kaiyya Meenatu ke yarinyace baki san komai ba sai gaba zaki gane ke dai zancen ki, dutse da kikace Allah yanufa sai ko anyi komai wahala nai,
Amma baku san irin takai din da dan tsohon ga yasha ba kafin a kai ga hakan da sannu dai ai gaskiya zai baiyyana kowa ya sani,
Nace kai Mama Dije don Alkah bari qagga camfin haka wani ya isa yai wani abu batare da sani Allah ba na,
Tace to ko mijin ki da add, rikeken dan izala yanzu dole ya zubar da wanan kaihin nashi ya san gaskiya don ya gane cewa da kulli tare da shi,
Murmushi nayi mata ba,tare da nai mata wani magana ba again don nasan ba yarda zatayi da ni ba,
Kofan shigowa dakin ta naga ta dan leka a hankali kamar mai son dubawa ko akwai mai shigowa daga waje,
Tace con n tausa muryan ta uwar kishiyar ki ta saku a gaba ko wanan yaron ma da kika haifa kokarin ganin bayan sa takeyi,
Ai shiyasa kikaga malam da mijin ki duk hankalin su a tashe yake, saboda su san abin yi,
Amma insha Allahu bazata iya komai dashi ba don Allah ba zai bata iko ba, akan hakan,
Hajja ai takai macuci don ita abin nata bai tsaya ga yart ba kawai har saida ta hada da diyan mutane,
Yanzu kinga badon Allah yasa malam masanin bane acikin alkur,ani maigirma da sai kawai taita barna acikin ku ba,a gane cewa itace,
Don kinga kowa yasan da cewa ta na da Dodon sihiri a gidan ta wanda ke kawo mata kudi, kashi,
Sai dai abin takaici kuma ba kashin kudin takeyi ba don kudin sihirine basu ciyuwa mata yadda take so, tunda bata hanyar halas aka samay su ba,,
Mama daki dauke shi ku fita waje sai na dan kwanta da sauri tace min rufamin asiri yar nan aiko nan da kofan daki baza mu fita dashi ba sai anyi suna saboda dokan malam,
Zataci gaba da magana sai ga Samira tayi sallama, dakin inda fuskanta kawai zai nunawa mutum tana a cikin bacin rai,
Ganin Samira bai sa Mama Dije ta daina maganar da take yi ba sai cewa tayi ai yanzu saura kiris ya rage asirinta ya tonu tunda mutanen shiya gaba daya sunyi meeting a kanta,
Samira wace shigowanta ke nan a lokacin take cewa ita waye saura kirs asirinta ya tonuwai ?
Don a zaton ta da mahaifiyarta ake zancd don tana tsan manin aji irin surutun da take sakewa akan zancen haihuwan,
Amma sai Dije tace mata, Hajja mana bakar muguwa yar lahani,
Samira ta, ce wanan ai sunan ta yai kauri a gari don yanzu ko wani shiya cikin gari sai labarinta akai, tatara dukiya kamar ya kashe ta,
A hankali takai hannuwanta saman fuskan dan jaririn da ke kwance a gefen gado yana barci,
Ta,ce sai faman barci, ake tayi yayin da ta juta gurin da Mama Dije take tana cewa, yana bari ayi barci da dare ko,
Mama Dije tace gaskiya baida matsala duk da dai jiya jiyane haihuwan amma gaskiya baida fitina sam,
A hankali takai zaune bakin gadon tana cewa Meenat yanzu kan kin san duniya don duk macen da bata haihuba bata san maynene duniya ba,
Murmushi kawai nayi tare da dan kokarin gyara zamana, don itama taji dadin zama daga inda take zaune a gefena,
A hankali muka soma hira da ita wanda duk yawancin hiran namu akan zance haihuwan tane don ni ban yarda na fadi komai ba akai don na san yanzu matsayi biyu take dashi a gurina,
Bawai lalai ne tasan komai nawa ba kamar da can baya da muke zumuncin mu, da ita,
Dan Jaririn wanda ke kwance can bayan yai motsi koda wasa ban juya don na kalle shi ba badon komai ba sai don irin karamin da naga ga Mama Dije da Anty Samira duk hankalin su gaba daya ya koma a gare shi,
A hankali yaron ya fara dan yi kuka wanda, Mama Dije ke bashi ruwan zamzam, a hankali tare da kokarin lasa mai garin dabino da zuma a bankin shi a hankali,,
Sai dan wanan kukan ba kamar na wanda yayi da safe ba ne yanzu kan a hankali yake kara sautin muryan shi,
Muryan Mama Dije ce naji tana cewa Meenatu ki gyara a bashi nono yanzu kan,
Gabana ya fadi damm don jin may tace don sam na mance cewa yanzu na zama feeding Mama,
Jin shirun da Mama Dije tayi don gani ko gezau ban yiba daga ida nake kwanci ba bawani alaman motsin zan gyara in bada nono a lokacin,
Sai tsala ihu yaron ke faman yi a lokacin Anty Samira tace gyara mana Meenatu ki bashi nono ya sha,
Na gyara juya masu baya tankar banji su ba may yasa haka Meena inji Anty Samira a cikin yar hasala take magana,
Wanan ai zalunci ne a ce yaro na son abincin sa amma ki hana mashi ana magana kinyi wani biris da mutane,, don kada ki shayar dashi,
Mama Abu ce ta shigo dakin dauke da ruwan dumi a cikin wani roba mai fadi,
Tana cewa zauna da kyau a wanke nonon ko ? Ya fara sha ai yayi kokari hakana,
Binta nayi da ido ina kallon ta sai naga gadangadan ta haroni da roban ruwan daje hannun ta,
Yaron ya rike a hannun Dije wace ke tsaye a kaina tana dan jijiga shi a hankali,
Ita ko ?nty Samira sai cewa take kaji muguwa zata bar muna yaro da yunwa ya tsulance gashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login