Showing 1 words to 3000 words out of 39216 words
Chapter 1 - ZULFAH Complete Book 1&2 By Oum Maheer Miss Green.txt
 ZULFAH.
Na
UMMU MAHER(MRS GREEN
   *TEAM🔥GAWURTATTU 🤟🏻3*
_ƊAN ƊANO💋💋💋💋_
 *Ya Allah ubangiji ka jiɓanci lamuranmu,yadda na fara wannan littafi Allah yasa in gamashi lfy,ya Allah kasanyamin albarka awannan littafin nawa,ya Allah ka bani ikon sanar da abinda nake son isarwa awannan littafin,ya Allah kada ka bani dama ko iko akan rubuta abinda ba zai amfani al'ummarka ba🙏🏼ina godiya da masoyana aduk inda suke,wanda na sani da wanda ban sani ba🥰🥰💃🏼*
  
_*Page∆1*_
    Go sulow ne ya haɗu sosai ina cikin hamshaƙiyar motata wacce ta gaji da haɗuwa,kyau da tsarin motar ya fita daban sai walƙiya take tana wani shining.
Danna wayata nake cikin ƙwarewa ina chart da ƙawata  Benezar wacce take karatu a australia.
jin mun tsaya waje ɗaya yasa na kalli inda direban yake cikin ƴar ƙaramar muryata na ce"whats going on?".
Da ɗan sauri ya juyi gudun kada yayi laifi ya ce"sorry madam wallahi go sulow ne ya haɗu sosai amman ban san dalilin faruwar hakan ba."?
Wani kallo tayi masa bata ƙara ce wa komai ba.yasan yin shiru na zai iya haifa masa da matsala don haka sai ya ce"Madam bari in sauka inga abinda yake faruwa."
ƙala bata ce masa ba,daman kuma yasan ba lallai ne ta amsa masa ba.
yana fita ya fara kutsawa ta cikin motoci don ganin abinda ke faruwa?abin mamaki ba motocine suka tushe wajen ba,ashe wani tsoho aka kaɗe shine dalilin faruwar hatsarin.
sai salati mutanen wajen suke Tukur ya kasa komawa ya faɗawa uwar ɗakinsa abinda ke faruwa,don yasan halinta sam ita bata damu da matsalar kowa ba,ita dai matsalarta kawai itace matsala amman babu yadda zaiyi dolensa ya dawo ya sanar mata koda kuwa zata tsire sa,don ba zai yiwu yayi ta zama awajenba.
Yana dawowa ya ɗan kalleta ahankali cikin ladabi ya ce"sorry madam wai accidents aka samu awajen ne,anyi hatsari ne awajen amman zan san dabarar da zanyi mu fita".
Ya ɗan faɗi hakan aɗan hargitse don ya tabbatar aƙwai rigima.
Haryanzu ban ɗago na kallesa ba tunda ya fara maganarsa,kamar ma ban san me yake faɗa ba.?
na motsa laɓɓaina ahankali cikin sanin ilimin sarrafa baki,ammanfa bana harshe ba don sam ni ban iya magana ba,wala tayi maka daɗi ko kada tayi maka daɗi.
Ni dai daɗi na ɗaya ne inyi chart da ƙawaye ko kuma aje party ƙasa ƙasa ko kuma wani state ɗin.
tun daga nan ban ƙara ce masa komai ba,na fito ahankali daga motar,inda akayi hatsarin na ɓille Tukar sai bina yake yana ce min"madam don Allah ki tsaya kada kije cikin wannan taron aƙwai rana da zafi."
ko kallo bai isheni ba,balle yasa ran zan amsa masa ni dai kawai inje inda nake son isa ɗin.
dai dai lokacin tsohon yahau kekensa zai tafi,hannunsa da ƙafaraa duk yaji ciwo abin tausayi.
mutane sai magana suke masa akan ya dawo akaishi asibiti amman yace musu ba komai zaije chemist na unguwarsu.
Babu yadda suka iya dolensu su kyalesa,don babu wanda bai san sha'anin tsufa ba,idan mutum ya tsufa wani lokacin sai dai duk abinda yayi ayi haƙuri da gafara.
Ina zuwa na kalli tsohon sama da ƙasa,sannan na ce"kai old man?me yasa zaka dinga tafiya baka duba gabanka?wannan wani irin rashin hamkaline na talaka?yanzu gashi kayu min asarar party ɗina?wallahi yau ba gobe ba sai kayi ƙwanan sel nonsense kawai."
wayarta ta danna ta kira wata number,nan da nan sai ga ƴan sanda tamkar daman akusa da wajen suke,abinda ya bawa kowa mamaki bai wuce sanin abinda wannan matashiyar kyakkyawar yarinyar ke shirin yi ba?duk da a maganganunta sun gane komai,amman mamaki ya hanasu gane me take son aikatawa.?
da sauri dattijon ya kalleta jikinsa har yana kakkarwa cikin dakiya da kuma mamakin maganganunta ya ce"haba yarinya?anya kuwa kina da hankali?tsofai tsofai dani kice bani da hankali?shin ke me kika ɗauki kanki?saboda zakije fati shine tausayinki da imaninki suka gushe?har kike kirana da mahaukaci?babu mamaki anan saboda da daga ganinki kin fito ne agidan rashin tarbiyya da kuma rashin sanin darajar ɗan adam,saboda kina tinƙaho da kuɗi da izza da mul.. . . . ."
A zafafe na juyo saboda yadda kalamansa ke min mugun gudu a ƙwaƙwalwa,har nake tunanin anya kuwa wannan yasan ni wacece?ko da yake daga ganinsa ba sai an faɗa maka ba,ba shida hankali duba da yadda.kayan jikinsa suke wani wajen ma duk ya yayyage.
"ni Zulfah kake zagi haka yadda kake so?yau zanyi funishing ɗinka,ko da ma ace ba kada hankali to ayau ɗinnan za kayu hankali,don ni babu wanda ya isa ya nuna min hannu".
tana faɗar hakan ta juya ta fara tafiya cikin wani irin mugun taku,me matuƙar tafiya da hankalin masu kallonta don Zulfah irin matan nanne masu matuƙar iya juya salon jiki,ta yadda zaka ɗauka wata hawainiya ce ke canja tafiya da salo na jan hankali.
Ba iyayi bane,haka halittarta take komai tayi da jikinta me kyau yake kasancewa.
Zulfah fara ce tas tas,kallon farko da zaka yi mata zaka hango tsattsar kyau wanda baki ba zai iya fasaltasa ba,kyaunta ya ɗakko asaline daga ahalinta,Shuwa arab ne gaba da baya sai dai wani ɗan ratsi da aka samu na hausawa ta cikin kakkaninta,Babanta Shuwa ne shi saboda mahaifinsa shuwa ne,Mamansa kuma asalin bahaushiya ce,Maman Zulfah shuwa arab ce gaba da bayanta ita babu wani sirki.
Sun gaji kuɗi tako ina,abin dai ba zai taɓa misaltuwa ta misali ba har sai kasan su waye Familin ALFAH RASHEED.
Tuni ƴan sandan nan suka tisa ƙeyar wannan dattijon,abin tausayi amman babu wanda ya isa ya hana faruwar hakan,don sam babu fuskar yin magana saboda mota guda suka ciko ƴan sandan da bindigunsu,kai ka ɗauka wani ƙasurgumin laifin aka aikata.
Mutane da dama sai tofa albarkacin bakinsu suke akan abinda ya faru,amman fa sai da ƴan sandan suka wuce ihu bayan hari kenan.
Kai tsaye nayi  shigewa ta rantsatsiyar motata,wacce tafi tada kyau da tsaruwa Tukur yayi sororo yana kallonta,yana ɗan firfito da idanuwa don yana tsoron kada yarasa aikinsa,don tunda yaga Zulfah ta wuce sa ta shiga wata motar ya tabbatar da cewa tashi tazo ƙarshe don ya tabbatar Zulfah bazata ƙara sauraransa ba,amman duk da haka sai ya shige cikin motar yabi ta gida,don yana ganin wataƙila ta huce kafin nan.
Fasa zuwa fatin tayi ta wuce gida,kai tsaye sai da suka ɗan ɗan ɗauki hanya sannan Murassha ta ce"Zulfah baki gaya min abinda ya faru ba?ni dai kin kirani kuma na taho tamkar remote".
Ban amsa mata ba,na cigaba da kallon hanya kawai zuciyata sai tafarfasa take,don tsohon nan ya ɓata min rai sosai tunda nake babu wani mahaluƙi daya taɓa tsayawa akusa da ita ya faɗa mata magana irin haka,sai wannan tsohon wanda takeji dama tasa a ajje mata sji a cell ɗin har sai sanda ta buƙaci ya fito.
Murash-sha bata ƙara magana ba,saboda tsaf tasan halin aminiyarta ko zata ƙwana tana magana ba kulata za tayi ba,don haka taja bakinta tayi shiru zaman lafiya yafi ɗan sarki.
Suna zuwa naga sunyi hanyar wani estate,wanda a bakin gate ɗin gidan aka sa suna kamat haka:
ALFAH RASHEED ESTATE.
Gidane me part kusan ashirin,kowanne ɓangare da kalar design na ginin da aka masa,amman ko wani ɓangare yana ɗauke da kalar fari,sai dai idan kaso kayi wani fentin na daban,awani tamfatsetsen part naga Murash-sha ta faka motarta,wacce aka sa mata lamba abayan motar me suna ALFAH ESTATE.
Murash-sha da ta tuƙa motar,ita ce kuma ta fito da kanta ta buɗewa Zulfah murfin motar,amman sai da tayi kusan minti biyar sannan ta sako kyakkyawar ƙafarta,wacce take sanye cikin wani hamshaƙin zinaren takalmi me mugun tsinin tsiya,wanda aƙasan aka sanya Z&A akayi design kamar ƙwalba aƙasan don kana hango rubutun acikin ƙwalbar wanda akayi rubutu da kalar golden.
Ita kuwa Murassha ta kalli Zulfah ta baya azuciyarta tana me cewa'Allah ya shiryamin ke Zulfah'.
Tafiya nake cikin sanyi da yanga,wanda ya zame min tamkar ɗabi'a ta.
Masha Allah!wani falo na shiga wata wangamemiyar ƙofa ta buɗe da kanta kana iya hango komai na cikin falon,saboda ƙofar tamkar glass take.
a taƙaice dai sai dana wuce ƙofofi har guda biyu sannan na samu kai na a wani babban falo,me matuƙar kyau wata ƴar tsohuwa ce ta fito daga cikin ɗaki dake manne a falon,tana ta mita tamkar wacce aka hana yawo.
 "haba haba,wannan wacce irin rayuwa ce ace tun ɗazu ina jiran Memuna amman bata zo ba,sai dai kai da kanka ka tashi kayi aiki kenan kome?haba ni fa ana min ba dai dai ba a gidan nan,haba haba fisabilillahi".
Murassha ta samu waje ta zauna,tana ƴar dariya ita kuma Zulfah ta wuce ɗaki abinta ba tare da ta cewa kowa komai ba.
Hajiya Innah ta juyo tana fuskantar inda Murash-sha take ta ce"ke!maza faɗamin?wa ya taɓamin jika?haba haba fisabilillah me ya faru!?. 
Murassha ta ƙel ƙele da dariya sannan ta ce"kai Hj.Innah wai don Allah ba zaki dena haba haba fisabilillahi ɗin nan ba?arana na tabbata kina faɗarta kamar sau ɗari koma fin hakan"?.
Hj.Inna ta ce"ke to ina ruwanki don na faɗi haka?ko kakanku RASHEED ya yi har ya gama abinsa amman ban daina ba,don ya shiga maƙogwarona yayi fake fake".
Murassha sai dariya take tana buga ƙafa,kasancewarta mace meson raha da dariya yasa take tajan Innah,don sam bata son su sako maganar da xata ɓata ransu.
Don ita fa harka indai aka sako Zulfah ciki to tabbas daga bisani sai an samu ɓacin rai.
Ganin Murash-sha bata bawa maganarta wani bigire ba yasa ta ƙara maimaita tambayarta?.
Murash-sha taɗan ware hannu,alamar bata san me aka yiwa Zulfah ɗin ba.
Sai kuwa Hajiya Inna ta fara kuka kamar ƙaramar yarinya.
Baki buɗe Murash-sha ta fara kallonta,saboda tasan tabbas wannan kukan da Hajiya Innah ta fara bai wuce sababin ɓacin ran Zulfah ɗin ba,tasan tun ba yau ba Innar tasha kuka kan an taɓa Zulfah,sai ka rantse aiko mata da mutuwa akayi amman ina tsabar son da take yiwa jikarta ce shalelenta farin cikinta Zulfah.
Innar ta buɗe baki tana ce wa"haba haba fisabilillahi adinga ƙuntatawa yarinya?ni dai duk nice na jawo mata dana ce ta dawo daga ƙasar oman,gashi nan yanzu ana baƙantawa yarinya,kuma don mugunta kayi ta tambayar waye ya taɓa ta?amman adinga ware maka hannu tamkar wata filfilwa ko tattabara."
tuni Murassha ta gimtse dariyarta don ta gano so take ta ɗora alhakin laifin da aka yiwa shalelen na ta.
Ganin Innar tana ta faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba yasa ta tashi salin alin tana gimtse dariyarta ta wuce ɗakin dake kusa dana Zulfah.
Azuciyarta tana cewa ashe dai ke Zulfah ta gado da ƙwandon masifa,abu ɗaya ne bata gado ba cewa HABA HABA FISABILILLAH. . . . . 
tana tuno da hakan ta ɓarke da dariya tana cire kayanta don shiga wanka.......
*Polistation*
            wani matashi ne ya shigo amatuƙar firgice,yana kallon ofishin ƴan sandan baki ɗaya tamkar me neman sarƙar gold,ihu ya farayi yana ce wa"waye wa kamamin mahaifina ba tare da laifin komai ba? ne yayi muku?wani laifi kuka kamashi dashi?".
I.S.P ɗinne ya magantu cikin muryarsa me amo ya ce"kai!uban waye ya baka izinin shigo mana ofishi kana mana haushi?ko shi Baban naka ɗan gwal ne?"da sauri matashin ya matso kusa dashi ya ce"Babana yafi Gwal awajena,domin duk wanda yasan darajar iyaye ko kusa ba zai kama Babana . . . . . ."tun kafin ya ƙarasa ya magantu da ce wa"kai bakasan inda ka shigo ba ko?to tabbas yau sai kayi ƙwanan sel don nan kaf babu sa'an ubanka balle kai".
Jin hakan fa yasa Aliyu zafafa ya wuce cikin ofishin yana neman inda suka ajje masa mahaifinsa.
Cen ya hangosa a ɗan rakuɓe agefe,ya haɗa kai da ƙafafuwa yana kuka ahankali yana kiran wani suna.
Da gudu Aliyu ya ƙarasa yana ce wa"mlm!mlm!! Muna ta nemanka agari,akace wai ƴan sanda sun kama ka don kawai an kaɗe ka wata matashiya tace azo a kamaka".!
mlm ya ɗanyi shiru sannan ya kalli ɗansa ya ce"haƙiƙa Ali ban taɓa fuskartar irin rayuwar dana gani yau ba,Ali ashe aƙwai yara marasa tarbiyya da kunya?yau yarinyar nan baka yadda ta zage ni son ranta ba,ƙarshe ma tace azo a ɗaukeni a tafi dani".ya faɗi hakan yana kuka me sosa rai jikinsa sai kakkarwa yake saboda yunwa.
Wani ɗan sanda yazo kusa dasu yana waya ya sanyata a handsfree don suji me ake cewa.
Muryar Zulfah ce ta karaɗe wajen cikin cool voice ɗinta ta fara ce wa"kubarshi kawai sai sanda naga dama kuma na sanya lokacin fitowar tashi."
ƙit . . . . .ta kashe wayarta tana cigaba da chart ɗinta da ƙawarta me yi mata kiɗa ita kuma tana rawa wato Benezar.
Sosai ran Aliyu ya ɓaci cikin wani irin mugun ɓacin rai ya amshi wayar hannun wannan ɗan sandan ya jikake tarrrrrtssssss. . . . .
Cikin  wani irin fushi Aliyu ya fara magana"wai ku wasu irin mutane ne marasa tausayi da imani?kun kama tsoho kun kulle bisa umarnin wata wahainiya mara duban gabanta balle bayanta,sannan kuma babu wani dalili sai kuma ace za'a tsare mutum har illa masha,wato sai randa mahadi ya bayyana zaku sakesa?to wallahi yau babu inda zanje sai tare da mahaifina,sai dai idan zaku haɗamu mu duka ku kulle to bismillah".
Ko alamar tsoro babu a idon Aliyu sai ma wani irin ƙwarjini da ɗan sandan yake gani acikin idon Aliyun,wanda tuni tsoro da wata fargaba suka fita fit a idon Aliyu,tuni sauran ƴan sandan sukayo kan Aliyu wani daga cikinsu ya fara magantuwa.
"wato kai ƙwallon maras mutunci ko?to zamu haɗaka kai da wannan tsohon najadu . . . . ."
tun kafin ya ƙarasa yaji wani irin mugun bugu abakinsa,ya sanya hannunsa yana murza wajen,yayinda ganinsa yaɗan disashe yana iya hango wasu taurari masu mugun haske suna faman wulgawa a lungu da saƙo na wannan ofishin nasu.
taron dangi suka yiwa Aliyu,duk da Aliyun yana da ƙarfi amman sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi,don haka suka cukwikuyoshi suka jefasa a sel,suna haɗawa da nishi tamkar sun ɗauki buhun masara ko na shinkafa.
Mlm Shehu ya fashe da kuka me sauti yana ce wa"ka gani ko Aliyu?yanzu gashi nan kayi sanadin da kaima ka shiga inda na shiga,ka sani cewa kai ne me kula damu dukkaninmu,sannan yanzu gaka a ƙwance wa zai basu abincin yau Aliyu"?.
 "Allah".
Aliyu yayi maganar a bazata,Mlm shehu ya goge hawayensa ya kalli ɗan nasa cikin so da ƙauna ya ce"tabbas Aliyu bazan daina alfahari da kai ba,tabbas kai ne ɗa ɗaya tilo namiji dana haifa amman kuma sai ka zamar min tamkar ɗaya bisa uku ne,Allah Ubangiji Yayi maka albarka Ali".
Aliyu ya sharewa mahaifinsa hawaye,jikinsa sai kakkarwa yake kuma yasan hakan bazai rasa yunwar da yake ji bace ta janyo masa kakkarwar jiki ga tsufa,duk da bawai tsoho ne can ba amman wahalar rayuwa ta sanyashi agaba.
Haka suka kasance cikin wannan hali,babu me kulasu balle kuma halin kawo abinci.
Aliyu ya duba aljihunsa tuno da wayarsa dake jikinsa,lallai Allah yayi masa gyaɗar doguwa don da sun duba da tuni sun ɗauke masa wayar.
Ya latsawa abokinsa kira wato Saminu,kiran farko ya ɗaga yana ce wa"Aliyu lfy kuwa tun ɗazu bazo gidanku akace baka nan"?.Aliyu yaja numfashi sannan ya shaidawa Saminu komai.
Sosai Saminu ya yi mamaki sannan ya ce"ikon Allah sai kallo,to ita meye ribarta don ta tozarta talaka?don tana taƙama da kuɗi?sai ta taka wanda takesi har haka?amman kada ka damu aƙwai Allah kuma in sha Allah yanzu zan kira ƴan uwana ƴan jarida su shirya kayan aiki muzo ku sameku har nan ofishin idan sunsan wata basusan wata ba,kai idan da hali ma ka haɗa da sharri ta yadda suma zamu ƙuntata musu."
Aliyu ya shafa gemunsa sannan ya ce"bazan haɗa da sharrin komai ba,kasanni Saminu na tsani me sharri kuma har abada me sharri a taɓe yake,abinda ya faru shi zan faɗa a'i Allah ya sani abinda suka aikata mana suma sai anyi musu."
ya faɗi hakan yana fusgar iska tamkar wanda iskar ta ƙwacewa.
     Daman Saminu Yasan ba lallai ne ya amsa batunsa ba,amman koma dai menene ai kowa yasan abin babu adalci aciki don yasan abokinsa bazai taɓa yi masa ƙarya ba,Aliyu mutun ne kamili maras ɗaurewa ƙarya gaba.
Ƙwatance Aliyu ya yiwa Saminu sannan ya datse kiran......✍🏽
*mrs green ce*
_*Typing🤳🏼*_
_*🍏....ZULFAH....🍏*_
         Na
_*®UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍀_
   _*TEAM🔥GAWURTATTU 🤟🏻3*_
*_AREWABOOK🤳🏼_*
https://arewabooks.com/chapter?id=65006c1d80342613407c880e
   *Page∆2*
_*ZULFAH*_
      News muke kalla ni  da Hajiya Innah,muna zaune zaman kurmaye Hajiya Innah an ɗauro ɗaurin ɗanƙwali gaba ƙiris take jira ta fara masifa,ga masifar taf afuskarta amman babu wanda za ta yiwa,don Zulfa ko kallon inda take ma batayi ba balle tasa ran zata gane halinda take ciki.
Ana cikin haka Murassha ta shigo,ta kalli inda Zulfah take ta gwalo ido waje.
Mini siket ne ajikin Zulfah sai wata t.shirt iya cibiya me ɗan ƙaramin hannu,ta bazo uban gashi baya yayi wani yala yala, santala santalan cinyoyinta duk awaje sai wani ɗaukar ido suke,ita kuwa ko ajikinta ta tisa pop corn agabanta a wani babban mazubi tana ɗan ci ɗai ɗai tana kallonta.
Ƙafarta duk biyu akan ƙaton table ɗin da yayiwa falon ƙawanye me mugun tsada da kyau.
Hajiya Inna na masifar son wannan table ɗin, don duk jikanta daya shigo yasan inda yake zama sam ba'a zama ko kusa dashi gashi narkeke dashi yaji uban glass.
Ta juyo da akalar kallonta kan Innah wacce take ta cika tana batsewa amman babu halin yin magana,saboda ƴar gaban goshi ce tayi laifin.
Uwa uba gata da kaya matsatstsu wanda duk jikokin Inna sunsan ba'a shigo mata ɓangare da kaya matsatstsu ko da kuwa atamfa ce yadda ta tsani hakan har gaba sai ta ɗauka da mutum.
Amman yau babu damar yin magana saboda shalele ce tayi laifi,sai dai kawai ta girgiza ƙafa tana wani turo ɗam ƙwali ita a lallai tana masifa.ihi bayan hari don ita wacce ake abun don ita bata san ma anayi ba.
tintsirewa da dariya Murash-sha tayi tana ƙarasowa cikin tafkeken falon.
Tuni Hajiya Innah ya dawo da kallonta kan Murash-sha,daman yaya lafiyar kura haba sai kuwa ta fara faɗa.
      "Haba haba fisabilillahi,yanzu ni da ɗakina bani da wata dama Iye?sai azo ayi tamin dariya ta ɗibar albarka ana kassaramin kayan ɗaki?kuma babi damar kayi magana sai cibi ya zama ƙari?ni gaskiya bana son haka,haba haba Fisabilillahi".
maimakon ta daina dariyar har sai da ta tsugunna ƙasa,don ita mutum ce me saurin dariya ga fara'a saboda haka ta dawo wajen Innah da zama,saboda ɓangarensu kows takansa yake duk kuma wanda ya fita









