Showing 18001 words to 21000 words out of 39216 words
Chapter 7 - ZULFAH Complete Book 1&2 By Oum Maheer Miss Green.txt
 matuƙar ƙona wa mahaifiyarmu rai,saboda haka sai mahaifiyarmu ta ɗauki matakin hanamu zuwa ko hakan zai samar da zaman lafiya,don tunda mahaifiyarmu ta shigo gidan Hjy Raihana da mahaifinmu babu zaman lafiya kullum sai faɗace faɗace,don duk da banida wayo alokacin nasan wasu faɗan daga ciki,mahaifina yana iya ƙoƙarinsa don ganin komai yazo ƙarshe,amman kuma ita kullum cikin fitina take da mahaifina.
ana cikin haka rannan na fito da daddare,zansha ruwa na buɗe fridge na buɗe ruwan inasha naga gilmawar wani abu baƙi ƙirin...........✍🏻
*MRS GREEN CE*
07068606171
_*🍏ZULFAH*_
                 _page 11_
   _@🫰🏻Ummu Maher_
           *{MRS GREEN}*
_*@arewabooks*_👉🏼
https://arewabooks.com/u/Rabiattu0444
_*@Wattpad*_👉🏼
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
________________________
  _*GAWURTATTU 3*_
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA  NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari ɗangwauro house number 224
   Kano
OR CALL MY CONTACT
0904 470 9413
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻
_ZULFAH 1_
.............a haka na dinga bin wannan baƙin abinda naga ya wuce,har sai dana ga inda ya tsaya alokacin dana ga inda ya tsaya sai dana yi matuƙar kiɗima saboda a ƙofar ɗakin mahaifiyarmu ya tsaya,ba fito da idanuwa sosai duk da ban san wani abu wai shi asiri ba,a hankali na ke waya ta bayan tagar ɗakinta duk da dare ne amman hakan bai hanani lallaɓawa na leƙa ta window,na hango mahaifiyata tana ta barcinta tausayinta ya ninku acikin zuciyata,don kuwa nasan wannan abin daya tsaya a bakin ƙofar ɗakinta abin cutarwa ne duk da ƙarancin shekaruna,Murassha in taƙaice miki dai a haka na dinga kiran mahaifiyata ta bayan taga har sai da ta farka a birkice,tana tashi ta hango ni a firgice ta fara tambayata abinda ya kawoni?ban ɓoye mata ba cikin maganata ta yara na fara magana"Momi kada ki fito,wallahi wani abuce aka ajje miki a bakin ƙofar ɗakinki baƙi ƙirin ci ne na biyoci".da sauri ta tsare da manyan idanuwanta sannan ta ce"to maza je ki ƙwanta bazan fito ba".hakan da ta faɗamin yasa naji wani irin mugun jin daɗi,tunda Allah ya sani ina masifar son mahaifiyata sosai don itama tana nuna mana soyayya sosai tamkar dai mahaifinmu.
da safe kuwa mahaifiyata ta kira mahaifina awaya saboda ba a wajenta ya ƙwana ba,daman ta faɗa masa komai saboda haka kai tsaye ya kira wani malaminsa,wanda ya zama kamar na gida malaminr sosai don yasan qur'ani sosai,yana zuwa ya fara zuba ruwan tofin da yazo dashi ai kuwa ba'afi minti uku ba wani mugun hayaƙi ya fito baƙi ƙirin ya fice da gudun gaske,hankalin mahaifina ya ƙara tashi saboda haka malamin ya ce"to Alhaji yanzu dai babu wata matsala saboda haka zuwa gobe aƙwai abinda zan haɗa mata abata tasha saboda da dukkan alamu saboda ita akayi hakan,amman zan ƙara bincike sosai in sha Allah komai zai zo ƙarshe."
hakan da mahaifinmu yaji yasa zuciyarsa ƙuntata sosai,saboda tunda ya ƙara aure ma'ana ya auri mahaifiyarmu shikkenan komai ya damule masa,mahaifiyarsa ma an rabata dashi don ko wajenta yaje tashi take ta bashi waje,wannan abu yana damun rayuwarsa sosai don babu abinda ya rasa arayuwarsa Allah yayi masa arziƙi da komai amman kuma sam Allah bai basa uwar gida tagari ba,saboda haka ma yasa ya ƙara aure don Raihana ko agaban waye bata shakkar ci masa mutunci.
wannan abin da aka cire a ƙofar ɗakin mahaifiyarmu sai ya kawo babban hargitsi agidanmu,don kuwa mutum biyar ne suka ƙwanta mummunan rashin lafiya,hakan yasa hankalin kowa ya tashi agidan Murashsha ba zan faɗa miki mutanen da suka ƙwanta ciwo ko ɗayansu ba,saboda faɗa miki ɗin zai iya kawo matsala ga garuma,kuma zargin da ake musu yanzu ƴan ƙungiyar asiri ne,a sirrin dana ji agidan nan namu cewa akayi alokacin sun so ne su bada jinin mahaifiyata saboda tsanar da suka mata,amman da Allah ya kare ta sai gashi ta cigaba da rayuwa sai dai kash! duk da a wannan lokacin basu samu damar taɓa ta a gaba sai da sukayi nasara har suka kashemin uwa......"fashewa nayi da kuka Murassha tana ban baki,don so take in kai mata inda na ajje hujjar cewa Hajiya Raihana ce tayi nasarar ganin bayan mahaifiyata.
Na goge hawayena sannan na cigaba da bawa Murashsha labarina.
Murassha a wannan lokacin sai suka ƙara tsanar mahaifiyata sosai,rannan mahaifinmu ya haɗa mana birthday na zagayowar haihuwarmu Murashsha awajenmu ranar murnarmu ce,awajen wasu kuma ranar baƙin cikinsu ce,don muna can wajen fatin birthday ɗinmu aka sanyawa ɓangaren wuta,ta kama da komai na ɓangarenmu wannan rana mahaifiyarmu ta shiga matsanancin tashin hankali,domin kuwa aƙwai abinda Malam ya sanya a ƙofar ɗakin mahaifiyarmu,saboda kariyace sosai don wani lokacin ko kitchen idan ta shiga sai taji tamkar ana kiran sunanta,saboda haka yasa ta shiga cikin zullumin halinda za ta shiga duk da tana addu'ah.
ana cikin haka ƴar uwata ta fara rashin lafiya sosai,sai hankalin mahaifiyata ya koma kanta saboda tana masifar sonta sosai,ba komai ne yasa take sonta sosai ba illa rauninta,tana da haƙuri sosai kuma ba tada tsiwa kamar ni tana da surutu sosai ni kuma ba nida surutu amman kuma ina da wayo sosai,sannan duk abinda akayi min karyewa yake saboda haka sai suka sanyata agaba,wasu irin ƙuraje masu masifar wari ta dinga fitarwa abin tausayi ni da mahaifiyata muyi ta kuka.duk kuɗin mahaifinmu baiyi mata komai ba don kuwa har ƙasar waje aka fita da ita amma shiru,lafiya taƙi samuwa a haka suka tattaro suka dawo gida baki ɗaya,ni alokacin na koma wajen kakata Hajiya Innah ita kuma ƴar uwata tana wajen mahaifana har a lokacin bata samu lafiya ba.
rannan munje gidansu nace ni acan zan ƙwana,saboda ayanzu mahaifiyarmu tana ɗaya daga cikin gidajen mahaifinmu don zaman gidansu yafi ƙarfinta.Murashsha ashe a wannan ranar da mukaje da nasan abinda zan gani babu shakka bazan je gidan nan ba,da daddare bayan mun gama cin abincin dare alokacin ƴar uwata tana hannun mahaifiyarmu tana bata abinci,kallonta kawai nake yi amman zuciyata fal baƙin ciki duk da ina ƙarama ammanfa babu abinda bana ganewa,ina da basira sosai kuma na tabbatarwa kaina ce wa dangin mahaifina sune suka sanyawa ƴar uwata cuta.
da daddare wannan malamin suka shigo shi da mahaifina,ya tayamu alhinin rashin lafiyar ƴar uwata ya ce baya nanne yayi tafiya,amman yanzu komai yazo ƙarshe ya kawo wasu magunguna yana barbaɗe mata jikinta dashi,nan da nan jikinta ya fara dawowa yadda yake da ba ni kaɗai abin ya bawa mamaki ba,mahaifina da mahaifiyata suma abin ya basu mamaki sosai sannan ya fara tofa mata wasu ayoyi,nan da nan ta dinga sakin atishawa sai gashi ta tashi tana kallon mahaifiyarmu ta rungumeta tana kuka sosai,mu dukanmu muma muka rungumeta muna kuka sosai a haka mlm yayi mana sallama sannan ya bada wani abu da za'a sanya abakin gate ɗin gidan zuwa gobe.
da daddare ƙin ƙwana nayi a ɗakinmu na wuce wajen mahaifiyarmu,anan na iskesu sai hira suke ita da mahaifiyarmu ƴar uwara kuma tayi barci ina ganin hakan da sauri na wuce ɗakinmu,don bana son suna hirarsu in dirar musu,don rabonda su samu wannan ƙwanciyar hankalin har an mata.
cikin dare kawai na tashi,biyo bayan wani mummunan mafarkin da nayi akan wata mata ta biyo mahaifiyata sai gudu take wai sai ta kamata har ta faɗa wani babban rami mai mugun zurfi.a firgice na tashi na fito ina sanɗa a hankali,abinda idanuwana suka gane min shine ya tilastamin komawa na laɓe a bayan ƙofa.Hjy Raihana na hango da wasu mutane da wasu irin baƙaƙen kaya abin dai abin tsoro,sam basu san ina gidan ba saboda haka suka fice suna wasu surutai........."Murashsha ko da na isa ɗakin mahaifiyata tuni ya fara kamawa da wuta sosai,na dinga ihu ni kaɗai kawai sai naga kamar an jeho mahaifina,ashe lokacin har safiya tayi ɗaki ya ƙone ƙurmus baka ganin komai sai hayaƙi,sosai ya dinga kuka shima duk da ban san mutuwa alokacin ba amman tabbas mutuwar ƴar uwata da mahaifiyata ya taɓani sosai,har sai da mahaifina ya gaji ya kaini ƙasar waje karatu karatun danayi shekara goma cif ina yinsa har a wannan lokacin ina nan da wannan burin a raina ta yadda nake son ganin bayan Hajiya Raihana,yadda ta kashe min ahali nima sai na kasheta ta hanyar gobara..........."✍🏻
*MRS GREEN CE*
domin chart dani kai tsaye 07068606171
*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER._*
_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
       _ZULFAH_🍏
👇🏽
*Ummu maher(mrs green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
07068606171
Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.
08104335144
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
07068606171
08179523215
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼
*@MRS GREEN*
         *_ZULFAH🌪️_*
Book 2 page 12
*follow Zulfah on Arewa books*
https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
*VIA GROUP ZULFAH FANS*
https://chat.whatsapp.com/KVTgSsodCRZGcEjERSEsBY
*_DOMIN RANAR HAIHUWAR MANZON ALLAH(S A W) NA SAKKO DA DUKKANIN LITTAFAINA DUKA GUDA  7 NA KUƊI NA BAR SU AKAN 1K KACAL_*
1 DARASI
2 SILAR FYAƊE
3 DOCTOR NAWWARA
4 ƊINYAR MAKAHO
5 ABIN CIKIN ƘWAI
6 BASMA
7 INDA BA ƘASA
 GA MASU NEMAN ƘARIN BAYANI.
07068606171
*Cigaban labari*
_____Murashsha ta kalle ni sosai sannan ta ce"kash!gaskiya Hjy Raihana bata yi wa kanta adalci ba,yanzu meye ribar yin hakan?don ta zauna ita kaɗai agidanta kenan?wai me yasa mata da yawa suke son ganin bayan kishiyoyinsu ne?me yasa ba suda tawakkali ne?ai duk abinda Allah ya tsara dole sai ya tabbata,ƙarin aure da mutuwarsa ai duk na Allah ne,abinda bata sani ba yanzu haka mahaifinki Zulfah ya kusa aure."
Da mugun sauri na kalleta sannan na ce"aure kuma?wa zai aura kuma?".
Murashsha tayi murmushi sannan ta ce"nima Hajiyarmu naji suna maganar,amman ban san wa zai aura ba sai dai ina kyautata tsammanin bata san zancen ba".
ni dai mamakine ya kusa shanyeni a zaune,saboda ban taɓa tsammanin Dad ɗina zai iya ƙara aure ba sai gashi cikin lokaci ɗan ƙanƙani ya canja akalarsa.
¢¢¢¢¢¢¢
*ALIYU*
......"Ahmad aƙwai wata yarinya me suna Zulfah,tun da nake ban taɓa tsanar wani abu kamar yadda na tsane ta ba,Ahmad ka sanni kasan halina ni mutum ne mara ruƙo duk abinda kayi min mantawa nake,amman ban san me yasa na kasa manta na ta ba,Ahmad inason sanyata kuka kukan da zatayi tayinsa har ƙarshen rayuwart........"da sauri Ahmad ya ce"haba Aliyu wannan wani irin mugun alkaba'i ne?mw tayi maka da ta cancanci wannan hukuncin?mu fa musulmai ne?duk abinda tayi maka ka yarda da Allah sannan ka yafe mata....."da sauri nima na dakatar dashi don ban san ma har na tashi daga inda nake ba,cikin faɗa na fara yi masa magana cikin fushi da kuma tsananin zuciya,tamkad zata faso ƙirjina ta fito na fara magana ina fesar da wani irin zafi wanda ke fitowa tun daga ƙasan zuciyata har jinina.
"Ahmad!Ahmad!!Ahmad!!!.sau nawa na kiraka"?.
tabbatar da sanin halina na zuciya yasa ya zaunar dani ina huci ya ce"dawo ka zauna Aliyu,sau uku ka kirani menene"?.cikin hucin na fara cewa"kasan wacece Zulfah kuwa?kasan zafin kan yarinyar nan?da girman kanta?kasan waye ubanta kuwa?kuma shin kasan me tayi min?".
Ahmad ya ce"ban san me tayi maka ba oga Aliyu".
"Ahmad tunda nake ba'a taɓa wulaƙantamin mahaifina ba,sai Zulfah ce ta fara wannan kuskuren don tabbas tunda ta yarda ta shiga gona ta wallahi tallahi,sai na wulaƙantata a idon duniya,sai na nuna mata talaka da mai kuɗi dukka Allah ne yayi su sannan sai na banbance mata wuta da ruwa,kai ba ma ita ba dukka ahalinsu sai na nuna musu sunyi sakaci da suka bari ahalinsu ya taɓa ni."
Ahmad ya ce"gaskiya bata kyauta ba,tabbas tayi abinda ya kamata a nuna mata banbancin aya da tsakuwa,saboda irinsu basa gane gaba balle baya dole a nuna mata,to amman kai yanzu ta yaya zaka nuna mata kuskurenta"?.ya faɗi hakan yana fuskantata sosai,sai alokacin nayi wani murmushin mugunta sannan na ce"har yanzu ban gama shawarar ta yadda zan aiwatar da ƙudurina ba,amman kai Ahmad ta ina ka ke ganin zan biyo mata ta ruwan sanyi."
Ahmad ya ɗan nisa can kuma sai ya bani hannu muka kashe,sannan ya ce"yauwa ga dabara ɗaya mana,kaje kawai kace kana buƙatar direba agidan,kuma direban Zulfah kaje mata da duk siffar da take son mai aikinta ya kasance,sannan ka ɗora wani wanda zai binciko maka komai nata,sannan idan zakaje kayi ɓadda kama ma'ana ka sanya ɗan gemu sannan ka dinga saka irin wannan hular wato tashi ka fiya naci".tafawa muka ƙarayi sannan naji jikina yayi sanyi sai kuma na ce"abokina ni fa kamar gani nake wannan shawarar batayi ba a canja shawara,saboda ni dai kasan halina ba zan taɓa iya yi zuwar mata a matsayin mai aiki ba,bakazo mata a mai aiki bama ya ta kasance ballan tana kuma kazo mata a matsayin bawanta"?.
Ahmad ya yi dariya sannan ya ce"kai Aliyu gadanga ƙusar yaƙi,yanzu kai a ganinka sai ta raina ƙusar yaƙi?wane ita ai ta koma garinsu wallahi".banxan kallo na yi masa sannan na ce"wannan yarinyar fa idan ba don ni ɗin bane da ban isa ma in tunkare ta ba,saboda yarinyar nan ta wuce duk inda ka ke tunaninta,tsoronta maza da dama sukeyi saboda haka ni tunanin zubar sa mutuncina na keyi".
Ahmad ya ce"to naji mi dai yanzu banda wata shawara kuma bayan wannan,saboda itace shawara sauƙaƙƙa wacce zaka cika burinka akanta,amman idan har hakan baiyi maka ba zaka iya canja wani,ko kuma kaje kayi shawara kasan komai yana son shawara,don zuciyarka ma tana da haƙƙin shawara da ita saboda haka ni bari inje ina da gyare gyare sosai......"
Bai gama rufe bakinsa ba sai ga Ruƙayya ƙanwarsa ta kawo masa abinci,tun da yarinyar ta tawo nake kallonta tamkar dai akanta na fara kallon mata,sam na manta yarinyar domin kuwa ba wani ganinta nake sosai ba,baƙa ce sosai amman yarinyar tana da kyaunta sosai ga ta komai cof cif gwanin ban sha'awa don dukkanta bata wuce 16 ba.
Har ta ajje abincin ban daina kallonta ba,har ta fara gaisheni duk ban san da hakan ba,har sai da Ahmad ya ɗan taɓani yana dariya sosai ya ce"to hanga ƙofar gari rufe bakin naka kada ƙuda ya faɗa".sosai naji kunyar hakan na shiga sosa ƙeyata sannan na ce"eh am'am dama".ɗan murmushi yarinyar tayi wanda fararen haƙoranta suka bayyana ta wuce tana sauri.
Ahmad ya ɗan murmusa sannan ya ce"Ruƙayya ce fa ƙanwata,kana kallonta haka ai sai ka janyo mana raini ko"?.banza nayi masa don ba raini ba ko meye sai na kalleta don kallon farko naji yarinyar tayi bala'in ƙwantamin,a hankali da sanyin jiki na ce"Wow!gaskiya yarinyar tayi min Ahmad,kuma wallahi ban ma kawo ita bace lokacin da na santa tana ƙwaila sosai,sannan kuma ita batayo farin ku ba sai dai kaf ɗinku ta fiku ƙyau wallahi,ga hankali da nutsuwa".
Ahmad yana dariya ya ce"eh ai tunda kana so dama bazaka ga muninta ba,amman wannan yarinyar ai duk itace mummunar gidanmu,baƙi kamar baƙin tukunya".ɗan dukan wasa na kawo masa ina ce wa"eh koma meye ni a hakan nake sonta,kuma don Allah yayanmu kafin nazo ayimin iso".murmushi yayi sannan ya ce"shegen kaya wato yau nine ma yayanku,to nima akaimin saƙo wajen Rabi nima ina nan zuwa,don wallahi nima dama faɗa ne banyi ba,tun tuni inason Rabi to gani nayi tayi ƙanƙanta alokacin shiyasa amman yanzu kam ai sun girma tunda suna da 16 ita da Ruƙayya."nima dariyar nayi ina cewa ashe munada yawa masu zubar da girman kaga anyi 1@1 kenan".muka saka dariya mukaci abincin da aka kawo masa kunnenka kamar ya gutsire saboda daɗi,shinkaface fara da miyar jajjage da kifi tayi daɗi sosai,sai dana tambayi Ahmad ko ita ke yin girki ko Basira yayarta,ya amsa min da cewa ita ce".sosai abin ya burgeni saboda ina masifar son mace mai iya girki.
            ¢¢¢¢¢¢¢
*ZULFAH 2*
______har ƙofar gida ƴan sandan suka rakoni na shiga gabana yana masifar faɗuwa,saboda alokacin wajen ƙarfe 1 dare ne ina shiga na hangota a zaune,ta haɗa kanta da gwiwarta sai kuka take wani irin mugun tausayin mahaifiyata ne ya kamani sosai,duk da ba tada hankali amman ko yaya aka taɓani sai ka gane,saboda yadda take sona tana ganina kuma ta zabura ta taho da gudu ta rungumeni tana kuka sosai,tamkar mai hankali da ƙer ta barni na zauna,gashi dama jiri jiri nakeji saboda yunwar da ke nuƙurƙusar cikina,don yau ɗan aikin dana ke yi ma na goge motoci yau ban samu nayi ba,saboda haka har wani irin jiri nakeji saboda yunwa ƴaƴan hanjina sai gamewa suke suna bada wani irin sauti ƙuuuuuu.
share mata hawayenta nayi sannan na ce"to Umma ba gashi na dawo gida ba?Xulfanki ta dawo gida lafiya,sai ki daina kuka ko".?
Murmushi tayi sai naga ta ƙara yimin kyau sosai,ta ƙara yin haske har wani ƙyalli take ban kawo komai arai na ba,sai ta miƙomin wani biredi babba dashi sosai nayi mamaki ina tambayarta inda ta samoshi?.
ɓata ranta tayi alamar ita dai bata yarda ba sai na ci wannan biredin,tasan halina da kafiya ga taurin kai idan har bata faɗamin ba bazanci ba,sai ta janyo hannuna ta buɗe katangar kangonmu tana nuna min mai shagon dake kallon kangonmu.ɓata rai nayi sosai









