Showing 30001 words to 33000 words out of 39216 words
Chapter 11 - ZULFAH Complete Book 1&2 By Oum Maheer Miss Green.txt
 ganin abinda ke jikin mahaifiyata,ban tsaya haka ba har sai da hannuwana suka kai kan cikinta wanda ya yi bala'in fitowa,sosai tsoro da fargaba suka bayyana  a kyakkyawar fuskata,wasu hawaye masu ɗumi suka shiga zubomin ina kiran sunan Allah kalma ɗaya nake ta faɗa,"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!".ko ba'a faɗamin ba nasan tabbas mahaifiyata ciki ne da ita,tashin hankali wanda ba'a saka masa rana daga wannan masifar sai wannan?daga wannan ƙarnin sai wannan?wannan wacce irin rayuwa ce?tun da na farka da wayo na ban taɓa fuskantar baƙin ciki irin na yau ba,duk da aƙwai wasu zamani daya wuce wanda nasha baƙin ciki da dama kuma na iya haɗiyewa,amman a wannan karon ina ganin bazan iya haɗiye wannan baƙin cikin ni kaɗai ba,kuka nake sosai na rasa wanda zan faɗawa ya bani shawara?to shin waye nake dashi ɗin da zan faɗawa damuwata?shin mutane da dama suna iya haɗiye baƙin ciki irin nawa?ƴan uwa kuyi min adalci ku ƙwatanta hakan akan akanku ya faru?wani irin hisabi zakuyi kanku?rana ɗaya rana tsaka wanda kuke tare dashi musamman mahaifiyarka,ace rana ɗaya ka ganta da ciki?alhali ba tada muharrami?wannan ba ƙaramin baƙin ciki zai haifarwa rayuwarka ba,musamman ma idan ka kasance mai rauni kada ma ka duba wulaƙancin da zaka fuskanta awajen mutane,ka alaƙanta hakan akan irin wulaƙancin da zaka fuskanta awajen mutane.
ranar naji haushin kai na,kuma a ranar naji haushin mahaifiyata don me bazata kare kanta kamar yadda nake kare kai na ba?sai dai hakan ba lallai ne ya iya yiyuwa ba,biyo bayan taɓin hankalin da take dashi kuma sannan nima ba fa wayona ne ya kare ni ba,Allah dai shine ke kare ko wani bawa ba wai wayon bawan ba,ranar nasha kuka ni da kaina na bawa kaina haƙuri don tabbas ba yadda zanyi dole ne inyi haƙuri inci gaba da fuskantar rayuwa,har ranar da Allah zai kawo min sauƙi.
              ¢¢¢¢¢¢¢
_MD_
Tunda ya baro Zulfah yake jin zuciyarsa a matuƙar ɗaure,tabbas wannan yarinyar tana cikin matsalar rayuwa babba,tunani yake aransa anya kuwa aƙwai wani abin tausayi a doron ƙasa wanda ya kai na Zulfah?tausayinta yake ji sosai,ranar baiyi wani aikin kirki ba ya tashi daga aiki ya wuce gidansa,hankalinsa duk ba a ƙwance ba don gani yake in har ya tafi ya barta wani abu zai iya faruwa da ita,tunda yake bai taɓa jin zuciyarsa ta tsinke irin na yau ba,ji yake dama yayi ta kuka ya huta,ko zaiji sauƙin abinda yake damar masa zuciya har ya iso gidansa baki ɗaya ba shida wani sukuni.
  yana shigowa ƙasaitaccen falonsa ya tarar da Ni'ima da su Nimrat bai yi musu yadda ya saba yi musu a kullum ba,hankalinsa dai baki ɗaya yana cure awaje ɗaya ne baki ɗaya Ni'ima ta taso da sauri tana masa sannu da zuwa,ya amsa cikin fara'a amman ba tare daya saki jikinsa ba,ya ɗan ɓanɓare su Nimra daga jikinsa a hankali ya nufi sashensa.
Ni'ima na ganin hakan sai taji duk jikinta yayi sanyi don ganin sauyawar Dad ɗinsu,don tasan shi mutum ne mai fara'a da kuma son yara sosai.
da ɗan sauri ta ƙarasa ɗakin mahaifiyarta,ta ɗan shiga da gudu don ta sanar mata don ta tsani taga mahaifinta cikin wani hali,da sauri Anty Fati ta juyo cikin masifa ta fara mata magana.
"Ke!Nima meye haka zaki shigomin ɗaki babu sallama ki faɗomin?,ban hanaku irin haka ba?".Nima take kiran Ni'ima dashi,akan wai an sanya sunan uwar mijinta ita kuma bata son sunan to don ta ɓata aji haushi sai take ce mata Nima.
saboda haka ta tsani yarinyar aduk cikin yaranta guda shida,babbar ƴarta itace Rufaidah,sai Khalil,sai Ni'ima,sai jawahir,sai Nimra da Na'im ƴan biyu kenan.
ɗan rau rau tayi da ido don daman tasan hakan zai iya faruwa,sai dai ya zamar mata tilas tazo ɗin don bata san ganin dadynta acikin matsala,kuma tasan Anty Fatin ce kawai mai iya magance masa halinda yake ciki,don tun ba yau ɗin ba ta gane mahaifinta mutum ne kamar yaro,yana masifar son care(kula)indai har zai shiga wani hali to yana buƙatar matarsa akusa dashi,saboda haka duk sanda ransa ya ɓaci gida yake yowa,sai dai randa ƴan rashin mutuncin Anty Fati na kusa cewa take babu inda zata ai ba akuya bace ita balle ya mayar da ita inji.
"am am dama Momi Dady ne na ganshi duk jikinsa a sanyaye,amman ban sani ba ko wani abu akayi masa b............."
"Shut up!ki fitar min a ɗaki malama,kada ki ƙara kawomin munafurci munafuka mara hali kawai shi uban naki ya nemeni mana,sai ke ce ƴar kanxagi anyi gadon munafurci wajen mai dattin hula tsohuwar ubanki,ai dole kizo kina min laɓe get out of my side!".
ta faɗi hakan cikin hargagi,don har a zuciyarta bata san yarinyar tun fil azal,gashi dai ita ce da kanta ta haifi ɗiyarta amman kuma sam bata jin ɗigon sonta,don tun farko ta cire ta acikin ƴaƴanta saboda katsalandan ɗin da surukarta tayi mata ta dage sai an sanya sunanta,ita kuma ta dage sai an sanya sunan nahaifiyarta rana ɗaya kawai taji ya raɗawa ƴarsa sunan mahaifiyarsa,tun daga ranar ta bar musu ƴar tace ta yafe ta don ko shayar da ita bata yi ba sai mai shayarwa aka samu ra shayar dashi,wata ƙanwar Muhammad wacce suke ƴan uba da ita itace ta shayar da ƴarsa bayan tayi shekara biyar ya ɗakkota agidan mahaifiyarsa,don Allah ya ɗora masa son yarinyar sosai.
tana fita Anty Fati ta dafe kanta,don sam bata son damuwar Mohd amman ya zama dole tayi biria dashi,don shi duk sanda yayi fushi sai ya buƙaci mace ita kuma macece mai rauni bata son damuwa,saboda haka ta naɗe ƙafarta ta cigaba da chart ɗinta da ta buɗe na matan tiktok.
Uhm to fa kunji wani grp?😂
               ¢¢¢¢¢¢¢
_ALIYU_
Da sauri na juyo ina murmushi nace"to naji Ahmad na kuma gode da abin alkhairin da kayi min,yanzu dai abu ɗaya ne ya ragemin ta yadda zan shawo kanta ta yarda ta cigaba da aiki dani"?.Ahmad ya murmusa sannan ya ce"haba man kada fa ka zama rago,yanzu ɗan wannan aikin ma sai na faɗa maka yadda za'a aiwatar dashi?ai shiyasa na faɗa maka kai zaka ƙarasa sauran game ɗin,taimako ɗaya zanyi maka wanda ya zamana dole inyi makashi,idan har ta dawo zamuje ni da kai sai in bada uzurin cewa zan tafi ƙari karatu,ammanfa sai mun haɗa da addu'ah don wallahi wannan yarinyar ƴar rigima ce".
nan dai muka cigaba da hirarmu,ina saƙa yadda Zulfah zata karɓi abinda ta shuka.
Soyayyarmu da Ruƙayya,tayi nisa sosai tana sona ina sonta kamar yadda shima Ahmad da Rabi suka ɗinke gwanin ban sha'awa,shi dai Ahmad ya kusa kai kuɗi ni dai da saura tukunna don so nake in ɗan ƙara zama da ƙafafuna ba kamar Ahmad da ayanzu ya ke aikinsa ba.
¢¢¢¢¢¢¢¢¢
_ZULFAH 1_
ina ƙwance cikin komin wanka,wanda ya ƙawatu sosai sai ƙamshin roseflower yake,kamata yayi inji daɗin wankan da nake saboda yadda ruwan mai ɗan ɗumi yake ratsa jikina,amman kuma me?zuciyata a cunkushe take sosai ban san me yake faruwa dani ba?kusan ƙwana biyu bana jin daɗin zuciyata ko kewar gida nake oho?gashi dai ina waya da Dad ɗina har ma da hjy Innah amman kuma zuciyata a cunkushe take sai dai abu ɗaya nake ganin zaiyi min amfani shine in koma Nigeria?a fili na ce"no no".don nasan bazan iya komawa ba,a fahimtata Nigeria ƙasace ta takura da sanyawa mutum damuwa ko da bai shirya zuwan hakan ba,ga Bilal daya damar mata rayuwa  anya kuwa komawarta zata yiwu a wannan time ɗin?.
Ahankali na fito daga komin wankan na sanya tawul na fito,na zauna na shafe jikina da maya mayai masu daɗin ƙamshi da sanya nishaɗi,ni ma'abociyar son ƙamshi ce sosai duk da na kasance shuwa amman Allah ya ɗoramin son ƙamshi da dukkanin son wani ma'abocin ƙamshi.
Bayan na gama ne na zauna kan sofa na buɗe iphone ɗina na shiga neman layin Murassha,buga na biyu ta ɗaga tana ce wa"kai Zulfah tunda kika tafi sai yau kika nemeni?yanzu ma inajin wata buƙatar kike da ita shiyasa kika bugo,inason kiranki amman nasan idan na kiraki cewa zakiyi na fiya surutu,shiyasa na barki ki shana sosai ƴar gidan hjy Innah."
surutunta nake ji yana ratsa dukkanin kunnuwa na,da yakw earpice na sanya sai da ta gama tsaf sannan na ce"kai gaskiya mutanen Nigeria kuna da surutu da yawa,yanzu tunda na kira ai shikkenan ki kaiwa Hjy Innah muyi magana na nemi wayarta switch off".
Murassha taƙi yin shiru ta ce"oho dai da ba'a san asalin belbela ba da sai tace daga misra take".
ƙin tanka mata nayi na ɗanyi murmushi,i like this  poems don a rayuwata ina son karin magana ammanfa ni ban iya ba sai dai idan anyishi inji tamkar ana waƙa ne.
tarwal na hango ƴar rigimammiyar tsohuwata akan kafet ɗinta,sai mita take ko ita da waye oho?.ɗan murmushi nayi sannan na ce"hi old woman me ya faru ne"?.
Da sauri naga ta wawuri wayar da bata san na kira ba,Murassha ta miƙa mata wayar sai kuwa naji ta ce"kai Muraisa agaskiya kin iya tallah?yanzu shine kike ɗaukata hoto ina faɗa?ashe dai kinyi gadon gulma gun uwarki ƴar maiduguri,kai ni dai Allah ya bani surukai masu ƙarfin jini don gashi duk sun goga muku baƙin hali".
dariya na dingayi sai a sannan ta gano ai vedio call ne sai kuwa tace"kai nasara mugun iri,Zulfah ashe kece ki yimin viriyo gall".?dariya muka dinga yi ni da Murashsha tana ce wa"oh duk faɗan mutum turanci ma bai iya ba,sai mu waɗanda aka gogawa ƙarfin jini kinga ai dole mu iya turanci."
bata haƙura ba har sai da janyo Murashsha ta ranƙwasheta tana ce wa"ƴar jakar uba mai ƙaton kai irin na uwarta".
dariya nake musu kawai,don nasan nayi missing ɗin faɗan hajy Innah.
munyi hira sosai har na kira Illelia wato ƴar tsohuwar da take kula dani suka gaisa a ƴar hausar da nake koya mata.
tana tafiya Hjy Innah ta ce"wai Zulfah wannan matar mutum ce kuwa?ni naga kunnuwa kamar na ɗan maraƙi?kunnuwa a wani lanƙwashe kamar ƙaho?gashi idonta fici fici dasu?".
ɗaure fuska nayi sannan na ce"ke fa matsalata dake kenan fa?babu dama kiga mutum sai kin aibatashi?to haka kamarta take ba aljana bace".
sai kuwa ta ce"oh haba shiyasa akace su waɗannan masu fararan kunnuwan ba suda kyau ko na ɗigo,mu dai baƙaƙen mune masu kyaun da kuma juriya shiyasa kakanmu ma ba shida wani ƙwari,idan yana ciwo har kuka yake kiji fa?sai kace ba namiji ba?".
dariya ta bani na ce"wo wo wo Hjy Innah wai ke baki bar kowa ba?har mijinki ma baki barshi ba"?.
sai kuwa ta fara kuka tana ce wa"oh ke dai Bari Zulfah har kin tunomin da mijina,wallahi shiyasa naƙi yin aure don mu tashi tare dashi a ranar yaumi tanadi,Allah yasa kada ya tashi da wannan mai shanyayyiyar ƙafa kamar ta kuturu".
dariya na ƙara fashewa da ita,don na gane da kishiyarta take wacce ta mutu wajen haihuwa ta mutu da ɗan ba tare da ta haihu ba.
sai kuwa na ce"haba Innah harda wanda ya mutu ake kishi........"? da sauri ta ce"ke bari dai ai wannan ta shimfiɗa mulki ƴar jakar uba ashe lokacinta ya kusa........"tun kafin ta ƙarasa na hango fuskarsa tarwal cikin wayar,gabana yayi mugun faɗuwa ya kafe ni da ido sosai tawul ɗin jikina ya kusa faɗuwa da sauri na kashe wayar don yadda gabana ke dukan uku uku.............✍🏻
_MRS GREEN CE_
domin chart dani kai tsaye 07068606171
*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER._*
_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
       _ZULFAH_🍏
👇🏽
*Ummu maher(mrs green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
07068606171
Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.
08104335144
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
07068606171
08179523215
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼
_Typing🤳🏼_
   *_....🌪️ZULFAH🌪️...._*
_UMMU MAHER_
        *@MRS GREEN🍏*
_GAWURTATTU 3_
Book 2 page 18
*_follow Zulfah on Arewa books_*
https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
*_VIA GROUP ZULFAH FANS_*
https://chat.whatsapp.com/KVTgSsodCRZGcEjERSEsBY
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA  NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari ɗangwauro house number 224
   Kano
OR CALL MY CONTACT
0904 470 9413
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻
_ZULFAH 1_
______A hankali ya karɓi wayar yana ƙaremin kallo sannan ya ce"Zulfah kin manta damu ko?number ɗinki ma idan na kira bata shiga?,ashe ni ne bakison yin waya dani?".
banza nayi masa kuma ban kashe wayar ba,haushi kawai yake bani nayi nadamar kiran Hjy Innah don da ban kira taba da ban kalli fuskarsa ba,ganin ya buɗe baki zai ƙara magana na kashe wayata ba tare dana ƙara saurararsa ba.
_BAYAN ƘWANA 2_
da sauri na tashi daga barcin daya ƙwasheni lokaci ɗaya,wani mafarki nayi da mahaifiyata tana gargaɗeni dana koma Nigeria hankalina ya tashi sosai,aranar na fara shiri mukayi sallama da illelia sai kuka takeyi wai yanzu bana son zaman nan nafison zaman Nigeria.
*****
Hjy Innah tana ganina ta fara kuka tana ce wa"Allah sarki ashe mahaifinki ya shaida miki maganar bukin naki da Bilalu ko?". da sauri na kalleta ina ɓata fuska tare da hawaye na ce"wai ni me yasa ina dawowa Nigeria nake fara haɗuwa da musibu kala kala ne?daga wannan sai wannan?ni nace inason auren Bilal ɗinne?to ni wallahi bana sonsa kuma idan aka auraminshi duk abinda ya faru ku kuka da kanku".ina faɗar hakan na wuce ɗakina kai tsaye,ina shiga na faɗa kan gado na fashe da wani irin kuka mai mugun ɗaci,da na sanin dawowata nake saboda daman nasan hakan zai iya faruwa dani.
Bilal yayi murmushi wanda yafi kuka ciwo,don duk abinda na faɗa yaji ya zauna yana kallon Hjy Innah wacce ke kallonsa cikin idanun tausayi,ta riƙe hannunsa sannan ta ce"zauna jikana inason kayi haƙuri,Zulfah yarinya ce ƙarama saboda haka bata ma san wata soyayya ba,kai ne dai zaka koya mata saboda haka a hankali zaka dinga binta wannan ranar auren naku da aka saka baza a canja ta ba tana nan akan wata biyu masu zuwa insha Allah".
sai alokacin yaji zuciyarsa ta ɗan sassauta bugun da take masa,ya kalli ɗakin da Zulfah take ƙofar a buɗe yana son shiga don ya rarrasheta amman kuma yana tsoron abinda zai iya biyo baya,don haka ya koma ya zauna sai kuwa yaji Hjy innah ta ce"bita mana ko tsoronta kake ji ne?kar dai fa tarihi ya maimaita kansa don hakama ubanta ya yi da gyatumarta,yayi ta tsoronta kamar uwarsa don haka kada ka zama sako tumaki ɓallo jakai".
ɗan murmushi yayi,don yana da tarihin mahaifiyar Xulfah tsaf don mahaifiyarsa ta karanta masa komai nata,har da cewa ita ba zata bari ɗanta ya auri ƴar gidan Rabi'atu ba,saboda tasanta da iya salo na yaudarar miji shiyasa alokacin zamaninta tayi baƙin jini sosai.
ya ɗan sosai kansa sannan ya tashi jikinsa duk asanyaye don yana tsoron abinda zai biyo baya,Hajiya Innah ta ce"haba haba fisabilillahi wannan wani irin abune?namiji da tsoron mace?ni nasan wallahi wata'ala idan akayi auren nan shikkenan sai abinda Zulfah ta kimtsa maka,kamar yadda gyatumarta ke yiwa gyatuminta".
Murmushi yayi sannan ya ƙarasa ɗakin da murmushinsa mai ƙawata kyakkyawae face ɗinsa.
motsi naji a bayana da sauri na waiga da idanuwa na waɗanda suka kaɗa sukayi jawur.
Zan fara fidda yayyafin masifa kawai sai naga ya hayo gadon ya rufemin bakina gam,sannan ya fara magana yana kallon ƙwayar idona wacce take shining tamkar na shafa mai,abindq ke ƙara sanyasa wani yanayi kenan indai har yayi tozali da Zulfah,shiyasa bai cika son kallon Zulfah ba abinda ke sa da yawan maza basa kallon idonta saboda ƙwarjininsu.
ya lumshe ido ya buɗe ya ƙara jaddada godiyarsa ga ubangiji sannan ya ce"Zulfah bana son kukanki don Allah ki daina,ya zanyi ne?Allah ya jarabceni da sonki duk da nasan bakya sona amman ki rufamin asiri ki aureni ko zuciyata zata sararamin,wallahi Zulfah idan har na rasaki tabbas na rasa rayuwata domin kuwa nasan bazan rayu babu ke ba."
da mugun sauri na cigesa don jin zuciyata nake tamkar zata fashe,yaji zafin cizon sosai son har sai da yayi ƴar ƙara don ba ƙaramin cizo na garƙama masa ba,na tashi daga kan gadon ina kuka na nunasa da yatsa na ce"Bilal kake ko wa?ka buɗe kunnenka da kyau ka jini?indai har kaga na aureka to ni Zulfah bana numfashi domin kuwa ban dace da auren mutum mara zuciya irinka ba,da za ka yiwa kanka adalci da ka koma inda ake sonka amman ba ni Zulfah b............."
Wani irin zafaffan mari naji an saukar min a dukkanin kuncina guda biyu,da sauri na juya don ganin waye da wannan aikin?fuskar da ba'a taɓa yi mata ko da marin wasa ba?sai gashi yau an yimin marin daya nemi gigita ɗan ƙaramin tunani na?.
Wacece wannan wacce ta mari Zulfah?????.
da sauri na juyo don ganin wacce ta mare ni,sai wa?Hajiya Innah nagani tsaye akaina tana wuci ta nuna ni da yatsanta cikin fushi ta fara magana.
"wacece ke har haka?da kikq ɗauki kanki da zafi?don kinga yana sonki sai ki nemi ki halakasa?ke wacce









