Showing 3001 words to 6000 words out of 39216 words
Chapter 2 - ZULFAH Complete Book 1&2 By Oum Maheer Miss Green.txt
 tun safe sai kuma yammah ko dare,shiyasa ma ɓangarensu sam yake ame baƙin jini awajenta,duk masifar Innah tafi son zama wajenta.
Duk wannan abin da ake haryanzu Zulfah bata ma nuna tasan abinda akeyi ba,Innah ta ƙara harzuƙa ta juyo tana huci ta ce"ke wai ni Muraisa Sale ne ya ginamin ɓangare?da akazo aka taremin kamar ɓangaren tasi no gareji?haba haba fisabilillahi don Allah Abarmin ɓangare a koma wajen wannan guzumar uwar taki me kama da giwa,aikin ɓur ayi ta cinyewa ƴaƴana abinci ana ɓarnar kuɗi ana kaiwa meduguri,haba haba fisabilillahi".
Me makon Muras-sha taji haushi sai kuwa ta dubi ɓangarenda Zulfah take ta ce"uhm uhm ni fa Hajiya Innah bani nakar zomon ba rataya nima aka bani".
Ta faɗi hakan da dariyarta wacce ta cika falon.
Zulfah ta ɗan kallesu tayi magana ahankali.
"I dont went hear noise please!".
Ta ɗan Faɗi hakan cikin iyayinta da ƙwaini,haba nan fa Hajiya Innah tahau kuka wiwi wai an zagi ubanta Ummaru dake ƙwance dama,don bata jin turanci ko kaɗan dayake ada ba damuwa akayi da karatun ba.
Murash-sha fa ta samu abinyi,Zulfah ta galla mata wani banzan kallo wanda ya haddasa shirun nata don tasan tsaf zata yi mata wani zagin da zai haddasa mata ciwon kai.
Hajiya Innah ta ƙara hawa sosai ga bukin zuwa babu zanin ɗaurawa don tasan bata isa tayi magana ba yanzu sai a tada musu tambotsai.
Ana cikin haka ta fara jin muryar wani matashi acikin tv,saboda lokacin hankalinta na kan cika da batsewar da Innah ke yi wanda tasan maƙasudin yin hakan,amman don ta manna mata sai ta kyaleta.
"Azzaluma ce,mara adalci sannan sam bata san martabar ɗan adam ba".
Sosai ta maida hankalinta kan saurayin da ake magana dashi.
Ƴan sanda na korar ƴan jaridan su kuma sun maƙale suna ɗaukar rahoto.
Ɗan jaridan ya ce"ko zamu iya sanin sunanta?".
Maganar da taji ce yasa kanta ya fara tartsatsin wuta me ci bal bal.
Sunanta"Zulfah Alfas family waɗanda ke cikin garin nan azzalumai masu ƙasƙantar da ɗan adam."
ba ita kaɗai ba,hatta Innah da Murash-sha sai da abin ya girgiza tunaninsu sosai,suka shiga rattabowa kawunansu to ayaushe ne hakan ya faru?kai wannan ma dagaji sharri ne.
Zulfah ta juya eyes ɗinta cikin ɓacin rai ta wuce ɗakinta.
Tsaye tayi bakin mudubi tana kallon kanta,from head to toe ta kasa tuna ranar da wani yayi mata irin wannan tuzarcin me kama da kamawar wuta.
Ta nuna kanta"ni Zulfah wani yakewa wannan zagin?".
Tuni ta fara shiga wanu hali,daman kuma aduk lokacin da ɓacin ranta ya sauka kasa gane kanta ake baki ɗaya.
Tuno da hakan yasa Hajiya Innah ta taho da sauri zuwa ɗakin jikarta Xulfah.
sai dai ko kafin tazo tuni an datse ƙofar gam Innah tahau bugawa iya ƙarfinta amman Zulfah bata buɗe ba.
Tsoro da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo tsoro da fargaba suka samu gurbi azuciyarta,tuni ta sau kuka don tasan yau sai ta Allah kenan.Murash-sha ma hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,da ta tuno da gumurzun daya faru wasu ƴan ƙwanaki da suka wuce.
Hajiya Innah na kuka ta ce"Murash-sha miƙomin wayata ki dannawa Malik kira yazo yanzu yanzu".
Nan da nan kuwa ta kirasa,mahaifin Zulfah kenan yana cikin meeting aka kirasa sai da gabansa yaɗan faɗi dayaga number mahaifiyarsu.
Amman bai kawo komai ba ya ɗaga.
abinda yaji ne ya tsoratar dashi sosai nan da nan ya fito da ɗan sassarfa tuni ya fara jiƙewa da gumi,don tsabar tausayin halinda ƴar tasa take ciki.
kai tsaye ya shigo ɓangaren mahaifiyar tashi,hawaye sharkaf a kuncinsa ya fara doka ƙofar yana kuka yana magana haɗi da kuka tamkar ƙaramin yaro ɓaganarsa na sarƙewa
 "Zul. .  . .Zul. . . . .Zulfah don Allah ki buɗe magana zamuyi".
Shiru babu amsa sai wani gurnani da suka jiyo Zulfahn nayi da ƙarfi,sai da masu aikin sukazo sukayi ta bugun ƙofar sannan ta buɗe,Hajiya Innah ce ta samu ta riga kowa shiga wai ita me jika.
Gam ƙofar ta rufe bayan hjy Innah ta shiga,sosai ta zato ido ganin Zulfah ta koma tamkar ba ita ba,gashin kanta ya barbazo har yana rufe fuskarta ga idanuwanta sunyi jawur,jini na fitowa ta idanuwanta tamkar an buɗe famfo tana zaune a saman gadonta ta naɗe ƙafarta tamkar wani boka me jiran siddabaru.
Hajiya Innah tsoro yasa ta fara fitsari tsuuuu awando tana ce wa"wayyo Allah na,yau shikkrnan na shigo hannu sai yadda akayi dani,don Allah Zulfah kiyi hƙr wallahi baza a ƙara ɓata miki rai ba".
Wani irin ihu Zulfah ta saki duk gidan nasu sai daya amsa,mutanen Alfas house duk suka firfito baki ɗayansu suwa sashen Innah wanda yake ta amsa kuwwar kiran jama'ah.
Hajiya Innah fa ido ya raina fata,sai ga gudawa ta fara samun wajen gudu tsuuu,faɗi take haba haba fisabilillahi tsabar mugunta a kulle ni aɗaki,wayyo Allah ni ƴar Abubakar jikar Ibrahim Ɗan magori Allah Ka kawomin ɗauki wayyo Allah na . . . . . . ."
Kowa yayi cirko cirko a bakin ƙofar ɗakin,kowa na faɗar albarkacin bakinsa gashi kuma an kasa zuwa bakin ƙofar,Dad Malik ne kawai awajen sai kuma Murash-sha wacce keta kuka yayinda suke jiyo ihun Innah acikin ɗakin har tana bugo ƙofat don azo akawo mata ɗauki.
Allah ya taimaki hjy Innah ƙofar banɗaki abuɗe take tayi wuff ta faɗa tana nishi ƙasa ƙasa.
Da ƙer aka samu ƙofar ta buɗu,sai dai ana shiga aka tarar da Zulfah ƙwance akan gadonta tamkar ma dai babu abinda ya faru.
Jin mutane acikin ɗakin yasa Innah ta fito da gudu har tana haɗawa da faɗuwa jikinta dama dama da kashi harda fitsari.
Chuchu ce ta fara dariya,yayar Zulfah wacce suke Baba ɗaya sai kuwa ta ce"oh yau Haba haba harda gudawa hhhhh".
duk da Dadynta yana cikin wani hali sai daya yi mata wani banzan kallo sannan ta kame bakinta,cike da jin haushin irin kulawar da mahaifin nasu ke yiwa ƙanwarsu.
Ƴaƴan Innah su shida ne,huɗu maza biyu mata duk kuma suna wajen abin ya faru saboda ranar weekend ce kowa yana gida.
Malik kallon Zulfah ya shigayi yana lulluɓe mata jikinta saboda yadda surar jikinta ta bayyana,su kuwa sauran iyayen nata ficewa sukayi suka zauna afalon Innah suna jimamin halinda Zulfah ke ciki.
wasunsu daɗi ne fal ransu,wasunsu kuma akasin hakanne azuciyoyinsu tausayin yarinyar fal aransu.
yarinyar da take da shekara 20 amman ace wannan muguwar lalurar ta same ta?wacce haryanzu aka rasa gane kanta.
hjy Innah dai babu bakin magana sai muzarai take,jikokinta kuwa sai danne dariyarsu suke saboda yadda Innah ta zama tamkar wata yakuwar da aka tsoma aruwa.
Tuni ta shige banɗakin don kunya,ta wanke jikinta tsaf sannan ta ɗora dayin wanka ta fito,har lokacin kuma waige waige kawai takeyi saboda tsabar tashin hankali,ko waccen karon da Xulfah tayi bai kai wannan ba abin yayi sauƙi.
Tana fitowa daga wankan ta iske Malik,zaune yana riƙe da hannun ƴarsa yana kuka wiwi tamkar ƙaramin yaro.
Sosai tausayinsa ya ɗarsu azuciyar Innah,tuni itama taji idanuwan nata sun kawo ruwa,don ta tabbatar da ayanzu dukkansu da za a auna jininsu to babu makawa sai ance jininsu ya hau.
Tasan ƙaddara ce ke zuwarma mutum aduk lokacin da Allah Ya kawota,amman bata taɓa tunanin wannan ƙaddarar ba,shiyasa idan zaka roƙi Allah Ka roƙesa akan kada ya ɗora maka ƙaddarar da bazaka iya da ita ba.
A hankali ta dafa kafaɗar ɗanta tana share hawayenda ya cika mata ido,suna buƙatar su samu sarari nan da nan suka shiga zuba murya a ɗan sarƙe ta ce.
"Malik inason ka daina damuwar nan,ka sanyawa zuciyarka salama ita dai ƙaddara ta riga da tazo,kuma babu yadda zamuyi da ita sai hƙr."
idanuwansa akan ƴarsa ya ce"babu abinda yake dawomin a halin yanzu sai Jidda . . . . . . ."
hjy Innah ta ce"tabbas Jidda ta tafi tabar baya da ƙura Allah dai ya jiƙanta da rahama yasa mutuwa hutuce agareta."
Malik ya amsa da amin amman zuciyarsa duk babu daɗi,musamman halinda Zulfah ke ciki wanda magani iya magani anayi amman kullum abin ƙara cutura yake.
*********
*ƳAR MAHAUKACIYA*
 
Adai dai lokacinda wasu suke cikin farin ciki,alokacin wasu suke cikin halin baƙin ciki,tabbas rayuwa ilimice duniya kuma makaranta ce daban ga bayi masu maida bauta tamkar abincinsu.
Adai dai lokacin da rana tayi zafi.wasu suna cikin inuwa saboda basa son zafi wasu kuma alokacin suke cikin matsin rayuwa,da tartsatsin wutar wahalar rayuwa.
Kuka na fashe dashi na janyo mahaifiyata jikina,alokacin da take tacin biredi na bola tana cinsa tamkar mayunwacin zagin daya shekara baici nama ba,wasu zafafan hawaye suka zubomin aƙwarmin idanuwa,na sanya bayan hannuna na sharesu,ta kalleni sosai tamkar dai me hankali ta miƙomin biredin hannunta ba tare da ta cinye ɗin ba.
Sosai nake ƙyanƙyamin biredin amman babu yadda zanyi,tunda dai da shi na girma ko abinci abola haka muke ɗauka munaci.
Haka na taso bansan ƴan uwan mahaifiyata ba?bansan kowa ba sai mahaifiyata,mun taso a matuƙar wahalar rayuwa ta yadda duk inda mukaje sai kaga ana mana waƙa ni da mahaifiyata wai ga ƴar mahaukaciya da mahaukaciya,wannan batu nasu yana matuƙar suya min zuciyata amman babu yadda zanyi,tunda na tabbatar da batunsu haka yake babu abinda zance sai dai Allah Ya kawo mana sauƙin rayuwa,nasha kuka da idanuwa na akan matsalar mahaifiyata amman sai dai inyi kuka inshare hawaye na,addu'ah kaɗai nake akan wannan halin da muka tsinci kanmu ni da mahaifiyata.
Zakuyi mamakin inda na yi ilimi,aƙwai makarantar allo akusa damu,don haka kullum ina zuwa amman jan hannun mahaifiyata nake mu shiga makarantar tare,takuwa zauna har sai an tashi in sake riƙo hannunta mu tafi.
Ina mamakin yadda haukan mahaifiyata yake?duk yadda akayi ita ɗin asalinta macece me nutsuwa.
Don bata tsokana,ita dai haukanta akaina ne don duk wanda ya taɓani duk abinda yasamo sai ta ƙwala masa.
Ana haka rannan na tafi samo mana ruwa,don a wani kango muke zaune abin mamaki tunda na taso muke cikin wannan  kangon,amman ban taɓa ganin wano yazo yace kangonsa ne ba,muna dai zaune abinmu aƙwai banɗaki har ma da ƙofa agidan,kayanda muke sanyawa wani lokacin bara nake in samo mana su.
  Ƙaddarar da ta ƙara fuskanto rayuwata bata wuce wadda muka fuskanta ni da majaifiyata ba,wato abinda ya faru bayan na fita samo mana ruwa ina dawowa kawai sai naga wani mutum ya fito daga cikin kangonmu,ya hau wata rantstsiyar motarsa amman bai bari anga fuskarsa ba,yana hawa yaja motarsa da mugun gudu.
Da sauri na shiga kangonmu,abinda nagani ne yasa na ƙwala wani mugun ihu ina dana sanin ganin wannan ƙaddarar. . . . . . .✍🏽
Nasan zakuji labari biyu,to labarin de guda biyu ne na ƴar mahaukaciya da kuma Zulfah . . . .
*ku biyoni yanzu labarin ya fara aƙwai daddaɗar tafiya nan gaba* . . .  .
*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER_*
_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
       _ZULFAH_🍏
👇🏽
*Ummu maher(mrs green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
07068606171
Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.
08104335144
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
07068606171
08179523215
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼
_*Typing🤳🏼*_
_*🍏....ZULFAH....🍏*_
         Na
_*®UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍀_
   *_TEAM🔥GAWURTATTU 🤟🏻3_*
_*AREWABOOK🤳🏼*_
ZULFAH:: https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
   _*Page∆3*_
_*Zulfah2 pov*_
        da mugun gudu na ƙarasa wajen mahaifiyata,na rirriƙeta ina kuka ina tambayarta waye wannan mutumin?sai kace me hankali nakewa tambayar?kamar yadda kuwa na tsammata shiru tayi min,idanuwanta duj awaje da alama abin ya taɓa zuciyarta nayi saurin rufe idanuwa na,na rufe mata jikinta yadda kai na ke sarawa yadda kasan an sanyashi atukubar tsire tsabar azabar da zuciyata ke yimin,sai naji dama  ace mafarki nake bada gaske bane,yanzu mahaifiyata aka yiwa fyaɗe?waye wannan?wani daliline yasanya shi yiwa mahaukaciya fyaɗe?babu me bani waɗannan amsoshin nawa masu kama da kibiyar mashi,don har sunfi mashi tsini da gudu na tashi na arta ana kare tamkar mahaukaciya nayi waje ina kuka,inda bawan Allahn nan nayi da gudu amman babu kowa awajen sai shatin motarsu.
Duƙushewa nayi ƙasa na fara wani irin kuka me cin rai,tabbas rayuwa juyi juyi ce bantaɓa tsintar baƙin cikin daya kai min na yau ba,tabbas ƙaddarar yau ɗin ta dabanne sai na ƙara fashewa da kuka me mugun raɗaɗi da zafi,tabbas rashin gata da rashin galihu ya samu babban bigire aruwarmu,tabbas muna fuskantar rayuwa me tartsatsi tamkar garwashin wuta.
_*ZULFAH1 pov*_
     a hankali na tashi daga nannauyan barcin da ya ƙwasheni ba tare dana sani ba,ɓarin kaina sai ciwo yake na buɗe idona ahankali ina kallon ɗakin tunda dishi disho har na gama buɗe sa tsaf,a hankali naji wani baƙon yanayi na duba hannuna sai naga hannun mutum sarƙe da nawa,gabana yayi mugun faɗuwa a hankalo nakai dubana wajen dana ke tsammanin anan fuskar mamallakin wanda ya gaji wannan hannun.
Sanyayyiyar ajiyar zuciya nayi,ina kallon kyakkyawar fuskat mahaifina tarr akaina yana jeromin sannu,idanuwansa sun faɗa sosai daga gani ma kuka yayi,naji tausayinsa don nasha kamashi akaina yana kuka sosai.
Murmushin dana yi masa yasa ya mayarmin,yana goge hawayensa ya ce"sweet daughter kin tashi?ya jikin naki?babu inda ke miki ciwo?".
Duk alokaci ɗaya yayi min wannan tambayar?nama rasa wacce zan amsa masa sai na ce
 "Fine. . . ."
Tun daga nan ban ƙara koda uffan ba,daman yasan ba lallai ne in cigaba da cewa komai ba,don haka ya tashi ahankali yana kallona yana murmushi har ya fita.
Inason mahaifina sosai,zan iya rasa komai saboda shi duk abinda nakeso mahaifina shi yakeso,ko da kuwa wannan abin shi bai gamsar dashi ba amman ahakan yake haƙura yayi abinda nakeso,dama ni hakan nakeso don duk inda na shiga jin kaina nake tamkar wata giwa kuma nafison kowa na wajen ya bani girma ko da kuwa ya girme ni,ni dai abinda nakeso kowa ya zama ƙasane dani.
Tashi nayi ahankali ina ɗan gyara yalwataccen gashina zuwa dunƙulesa waje ɗaya.
wanka na faɗa,sai danayi kusan awa ɗaya ina wankan ruwan red rose ma nakai kusan minti talatin sannan na fito.
don ni mutum ce me mugun son ƙamshi da gwalli.
Ina fitowa na xauna bakin mirror ina goge lallausar fatata tamkar audiga yadda take wani glowing tamkar ta jariri,saboda tsabar hutu da cin me kyau da kuma shafa me kyau,iya manda nake shafawa a wannan tsadaddiyar fatar tawa sun tasamma guda goma,ko wani bigire na jikina da mansa haka kusurwar jikina ma,ƙamshi kuwa yadda kasan gidan turare aka buɗe don wasu ma namune na shuwa,don ina masifar son turarukanmu na shuwa arab duk wanda yasan shuwa yasansu da bala'in ƙamshi,fintinkau ne su awajen ƙamshi na jiki dana tufafi.
Yau ma kamar kullim t.shirt ce ajikina kalar maroon wacce aka manna hoton mage ajiki fara sol,sai wani wando ɗamamme kalar dark blue,wanda ya kamani sosai sai ɗaukar ido nake,na bazo da gashina ta baya na danna sweet abakina,na saka takalmina ƙirar prado me ɗan tudu sannan na fito ina taku ɗai ɗai,ba iyayi bane a'a haka tafiyata take cikin yauƙi da gwalli.
A falo na haɗu da ƴan dubiya,bance da kowa ƙala ba nayi hanyar fita har hjy Innah wacce keta zuba tamkar makaɗi.
Da sauri ta tashi jikinta na rawa ta nufoni,sai dai gabanta sai faɗuwa yake  saboda bata manta azabar da ta sha jiya ba,ta idanuwanta na hango komai amman sai na maze na kalleta kawai.
"Haba haba fisabilillahi,ina zakije kuma baki gama samun lfy ba"?.
Kallon tsaf nayi mata,shima ba kallon rainin hankali bane hakan kallona yake na juya eyes ɗina,masu matuƙar tafiya da ma'abocin kallona sannan na ce"kina da matsalane dani"?.
ina kallon yadda ta tsorata da magana ta,amman da yake Innah tasha miya aduniya sai ta haɗiye tsoronta ta ce"haba masoyiya ta kada ki fita baki gama samun sauƙi ba,kuma kinga fitarki sakaka aƙwai matsala,tunda aƙwai masu harar rayuwarki".
Tunda ta fara magana nake kallonta sannan na ce"to naji matsa zan wuce".
Da mamaki ta matsa amman mamakine fal azuciyarta,don gani take wannan ciwon da nayi jiya da yau sai taga tamkar an ƙara canjani.
Naga hakan ne a idonta lokacin da nake wucewa,sam arayuwata bana son takura ko kaɗan shiyasa sam banso dawowata daga ƙasar Oman ba,kowa rayuwarsa yake babu ruwan kowa da kowa.
Ina fitowa dakaruna suka biyoni a baya,afusace na juyo ina musu wani kallon banza,babu wanda ya kalleni acikinsu saboda yadda suke ƙoƙari wajen yin duk abinda na umarcesu gudun kada su rasa aikinsu.
ni kaɗai na shiga haɗaɗɗiyar motata,wacce faɗin tsaruwarta ma ɓata bakine,tafiya nayi me nisa sannan na gangara ƙasan titi,ahankali na fito da wani hoto aƙasan motar,kallon matar nake sosai don babu abinda ya banbatani da ita,ina da taurin zuciyar daba komai ne yake sanyani kuka ba,zuciyata irinta maza ce mazan ma ba mazare ba,amman ayau kukan na fashe dashi ina rungumar hoton dake saman ƙirjina,kuka nake sosai ina magana da ihu ni kaɗai acikin motar.
 "Why momi me yasa kika mutu kika barni?na saba dake na saba da zama ajikinki,bansan yadda zanyi da rayuwata ba,idan akace haka zan cigaba da rayuwata babu ke adoron ƙasa,ina kewarki Momi!Momiiiiiiiii".!!
*HAJIYA RAIHANA*
       "Momi yanzu kina ganin abinda ke wanzuwa acikin gidan nan?ƙwanan nan nace wa Dady ya canjamin mota,amman cemin yayi sai ƙarshen shekara zai siyomin,amman wannan yarinyar daga dawowarta har an siyo mata fitinanniyar mota,ni ce baragurbi kenan daba za'a canjamin ba?to wallahi abi ahankali dani kafin in fara ɗaukar mummunar fansa akan wannan yarinyar."
  Tana huci ta gama maganarta,tana kallon mahaifiyarta da wani irin duba na ɗaukar fansa ta kowacce hanya.
Hajiya Raihana ta kalli ƴarta Hibba tana jinjina yadda Allah ke ikonsa,tsaf halinta Hibba ta ɗakko babu abinda tabari na halinta yadda kasan kofi ɗinta ce.
Hajiya Raihana ta fara magans fuskarta fayau tamkar babu wani abinda ya faru.
Tsabar sanin takan makirci kenan ta ce"ke Hibba ki dinga iya takunki asannu,ahaka na gama da uwarta cikin ruwan sanyi,don haka ki dinga ɓoye fushinki akanta idan ba haka ba ƙwaɓarki zatayi ruwa,don haka ki ƙwantar da hankalinki,yadda na gama da mahaifiyarta kema itama haka zan gama da ita ta shuɗe baki ɗaya,sai dai labarinta gwara ma uwarta ita ta haifa ana tuno da ita,to ita bazan taɓa bari ta tayi aure bama ballantana har ta haifi ƴaƴan,don haka inason daga yau kibi









