Showing 27001 words to 30000 words out of 53080 words

Chapter 10 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt

05 Nov 2024

13053

shigowa"
Daga haka yah shige gidan da gudu,muna nan tsaye saida wata koriyar danja ta haska kofar gidan kafin kkwannensu yayi nasa wajen,jikinsu har wasu juyawa yake saboda tsabar murdewa.ga kuma rigar bullet da aka saka musu,tunda nake banda ba kallon karen farauta haka ba.
Karisawa mukayi cikin gidan babu wanda yace wani abu har muka isa falon.
Sameemah muka samu farouq ya dora kansa akan cinyarta sai surutu yakeyi itakuwa ko magana batayiba.
Daga kanta tayi ta gaisheda hajiyah fatima wacce muka shigo tareda ita,daga ni har saleema kuwa ko kallon inda muke batayiba.
Hajiyah fatima ce tafara magana cikim dattako kaman yanda ta saba.
"Da farko ina baku hakuri dukka sannan zamantare dole saida hakuri musammman kai sameer wanda suke karkashinka.
Duk da bansan mai yah hadaku ba a baya amma ke sameemah ga saleema nan ta dawo dakinta bayan lokaci da bata nan sai kuyi hakuri a cigaba daga inda aka tsaya.
Idan wani abune ku sanar da mijinku ba kudau hukunci a hannu ba"
Saleemah ce tayi saurin cewa,
"Kuma a ja mata kunne kar ta kara gigin aikata min wani abun dan hukuncin dazai biyo baya bazaiyi mata dadiba.sannan kuma ta bani hakuri akan abinda tayimin kafin zance yah wuce"
"Ke Wacce kika aikatawa kin bata hakurine har ta mutu?"
Hajiyah fahima ce tace,
"Wacece ta mutu kuma?"
"Ita tasani ai ki tambayeta kiji"
Kallon tane yakoma kan saleemah wanda cikin borin kunya tace,
"Danna yiwa karyah hukunci manene,da har zaki hadani da itah a daraja"
Shiru kowa yayi nan na zayyanewa hajiyah fatima abinda saleemah tayi da kuma,amma bansan karyar ta mutuba saida ta fada yanzu.
Ran hajiyah fatima in yayi dubu yah baci,bata san lokacin data zabgawa saleemah mari ba,
"Yanzu duk wahalar dakika saka mutane a she kece ummul aba isin faruwar komai,wai kishi haukane harda zaki kama dabab ba abinda tayimiki kiyi mata duka da tsofon ciki har ta mutu ita da wssu daga cikin yan cikinta,wannan wane irin zaluncin ne haka,nidai bansan halin wa kika daukoba dan duk dangina babu wanda yake da wannan halin"
Kuka saleema ta rushe kafin tayi hanyar dakinta tana cewa,
"Wallahi saina fadawa mommy maryam duk abinda akemin nasan ai zata bi bayana idan taji abinda kae min."
Babu wanda yah kulata bare yasake bi takanta,itama hajiya fatima tashi tayi domin tafiyah,anan take fadawa sameemah ta,bata farouq halak malak idan tana da bukatar rikeshi,godiyah kawai tayi kafin tayi Murmushin da bakai yi nisa sosaiba.
Da safe da,wuri na tashi domin akwai meeting da major nazeer yah bukaci ayi.
Na shiga kitchen din da niyyar dan hada wsni abu naci naga sameemah ta,juya baya tana wsni abun,mantawa da abinda ya kawoni nayi na tsaya ina kallon bayan ta yanda yake murzawa da kuma juyi.
Lallai allah yayi halitta anan,shine abinda nafada,dan kunkuminta ma kadai abin kallone bare kuma duk jikinta,ganin kallon bazai kaini bane yasa na karisa tareda sakala hannuna a kunkuminta,saurin jiyowa tayi muka hada ido har numfashinmu yana haduwa dana juna.
Juyawa tayi ta cigaba da abinda take amma ta saka daya hannunta ta ture hannuna daga kan kunkuminta batareda tace komaiba,nima banyi kokarin maida hannunba sai cewa danayi.
"Ina kwana maman farouq,idan abin karyawa ake hadaamsa a danyi dani please ina bukata"
Bata cemin komai ba saidai daga yanyin kallon nasan maganar bata bata mata raiba ko kadan.
Daga haka na juyah na koma dakina domin na shiryah.
Lokacin dana fito shima farouq yah fito da jakarsa a bayansa shida sameemah,da alama ita ta shiryashi.
Abincin ta zuba masa nima ta zubamin kafin ta,ajiye masa wanda zai tafi dashi makaranta.
Wucewa tayi dakinta kaman mai saurin yin wani abu.
Nidai dana ga cikina ya dauka fita nayi zuwa wajen motata domin zuwa headquarter.
Kowa yah hallara ana zaune amma wasu har sannan basu zoba,mutsutsuka idona nayi domin ganin wacce ta shigo cikin hall din kuma ana fadin wai mai kulada tsaron duk camp din ce dakuma kulada harkar horo.
Bakina saki ina kallonta musamman yanda tasha kaya ga kuma hade fuska da tayi kaman wanda take fagen daga.
Nima dauke kaina nayi daga kanta ganin ko inda nake bata kallaba.
Shugabane ya shigo tareda masu tsaronsa aka fara meeting,shima daga gani kallom mamaki yake yiwa sameemah kaman yanda nayi mata.
Major nazeer ne ya tashi yafara zayyana irin gwagwarmayar da sameemah tayi a cikin barracks din da kuma irin nasarorin data kawo harma da daliban data yaye da kuma jajircewarta a wajen aiki.
Duk wannan bai basu mamaki ba sai da suka ji cewa nice Raudah abdulsalam wanda suke jin labarinta.
Da haka aka gama meeting din kowa yah koma bakin aikinsa,nima office dina na shige daga nan,dayake nawa a wani branch din ne daban ba ainihin cikin barrack ba saida nayi tafiya zuwa cikin gari tukunna.
Bani na dawo gidan ba sai wajen magriba hakam badan nagama aikinba sai dan kawai na hakura sai gobe na cigaba.
Tun daga shigowa nake jin kamshin abinci a kitchen,ko ba tantama nasan ba saleemah bace a ciki,aikuwa hasashena ya zama gaskiyah domin sameemah ce daga itah sai boxer na mata iyah gwiwa,sauran fararen cinyinnan duk a wake,wayyo matar nan zata kasheni ina ga.
Mtswww naji tsuka a bayana,ina juyawa naga saleema ta cika tayi fam,muna hada ido da ita ta juya ta bar wajen tana cewa,
"Aikin karuwamci kawai"
D'aki na shiga na canja kaya kafin na fito zuwa masallaci.
Lokacin dana dawo gidan tsitt dashi kaman ba mutane kowa yana dakinsa.
Leka dakin samemah nayi farouq yana zaune a tsakar daki yana assignment,ita kuma tana nade masa kayansa na makaranta.
Zama nayi a gaban gadon ina kallon yamda yakeyi,lallabashi nayi yah fita falo domin yah cigaba da yin assignment din.
Ta shi nayi na nufi inda sameemah take tsaye,hannuna na sakala a kunkuminta na jawota zuwa jikina,shiru mukayi daga ni har ita ba wanda yace komai,wani irin yanayi nafara jina a ciki sanadiyyar yanda dumin jikinta yake shiga cikin jikina.
Bakina na kai wajen kunnenta cikin muryar dani kaina bansan inada itah ba na fara yimata magana.
"Menene yah faru lokacin da bana nan,yah akayi kika hau matsayi kuma baki taba fadamin nabaki umarnin yin hakanba,amma kinsan ke mallakinace koh?,sannan ya akayi kika zama Raudah abdulsalam,please ki fadamin,duk da nasan kina da taurin kai amma bana son kiyimim gardama kinji"
Shiru nayi daga hakan ina hura iska cikin kunnenta a hankali yayinda hannuna kuma yake yawo a cikin ta da kuma kan kunkuminta.
"Baka bukatar sanin amsar hakan,idan ma kana bukatar sani toh kaje ka tambaya mana,amma bani zaka tsare domin samun amsarka ba.
Juyo da fuskarta nayi izuwa kan tata fuskar ina fesamata kallon da yake dauke da ma'anoni dayawa ,mun dade muna kallon juna kafin ta dauke idonta daga kaina,banso hakanba saboda hada ido kadai da mukayi ba karamin kawo wani shauki cikin zuciyata yayi ba.
Kara dago da fuskarta nayi nasake hade kallon da muka fara a baya,dan murmushi nayina dan gefen baki kafin nasake cewa,
"Please kanwata kidaina amsa magana a haka idan na tambayeki,banajin dadin hakan,idan ina yimiki wani abu wanda bakyaso ki fadamin,nayi alkawarin dai nawa inshaallah,amma kallonki kina abu cikin kadaici kaman bakya da kowa hakan yana damuna"
Ture hannuna tayi cikin zafin rai wanda bahaka takeba lokacin dana fara maganar,da alama na tabo mata wani tabo a cikin ranta wanda yake mata kaikayi.
Yin gaba tayi kadan yanda bana ganin fuskarta kafin tace,
"Sai a yanzu dana girma tukunna kadaicina yake damunka,lokacin danake tsaka da bukatar lokacinka ka tsallake ka barni a garin da babu wanda yake bukatar yaganni na kwana na tashi a raye baka ji zafin hakan ba sai yanzu da jikina yah fara daukan hankalinka tukunna ka tabbatar da cewar ni matarkace a yamzu ba kanwarka ba koh? ........kaine sanadiyyar daka sa na kulle zuciyata sannan nadaina yarda da kowa a cikin duniyaranan,na yarda kunci yacigaba da lullubeni har lokacin suka sauramin na bar cikin duniyarku suzo"
Saurin jawota nasake yi jikina a karo na biyu wannan lokacin zuciyata tayi nauyi dajin kalmar da take fitowa daga cikin bakinta.
"Mai kike fada haka sameemah ,ki fayyacemin komai naji daga bakinki,duk abinda kika san zakiyi mim wanda zai dauke wannan kadaicin a rayuwarki na yarda kiyi,ko horo kike bukata kiyimin na barin ki lokacin da bakida yawo naji na dauka zan karba duk da bayin kaina bane hakan."
Kallona take da alamar bata fahimceni ba,nima daga mata kai nayi alamar haka ne,
"Tun bayan rasuwar ummah da kwana uku komai yah sauya daga cikin rayuwata,ba abinda na tsana kona budi ido na gani kaman ke da kuma yan uwan ummah,abin yana damuna kuma nasan akwai abinda yake damuna,a duk lokacin da kika matso kusa dani ji nake kaman na shakeki har sai kin daina numfashi,domin duk wani laifi da akayimin sai na ji kece kikayi sanadiyyar yinsu.
Ana nan bayan kwanaki sai ya zamana garin ma yah fara fita a cikin raina,kullum da kyar nake kwana nake tashi har yah zamo nafara aman jini musamamn idan ina cikin gida,wata rana ne da muka fita daga garin nida abokina sai naji babu ciwon danakeji yah tafi kaman an zare shi. Hakan yasa na tatttara kayana nabi wani soja a anguwarmu saboda na samu abinda zan dogara da kaina,sannan na nemi magani na dawo domin kulada ke.
Lokacin dana samun gidan dazan zauna nayi murna sosai,hakan yasa na shiryah naje har gidan gandu domin daukoki,saboda ina tsoron abinds yah cutar dani kema zai iyah cutar dake,saidai mai zam tarar wai bakyanan kin shiga duniyya haka aka fadamin.
Nayi bakin ciki har kuka nayi,shin mai zam je duniya na fadawa umma akanki da wane ido kema zan kalleki idan mun hadu.
Ban sake haduwa dakeba sai lokacin dana ganki kin fito daga mota lokacin nayi aure naje da saleemah,tambayar danayi miki amsar farko danaji shine budurcin ki kika bayar aka baki itah.
Bayan tsawon lokaci dana dauka ina nemanki gari yah gari amma sai na karbi wannan amsar........rudu fargaba da tashin hankali gameda bakin ciki su suka tattaru a cikin zuciyata lokaci guda.






Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150


Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.


💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎










*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*




💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}






💎27~28💎




Hakanne yasa na cika da bakinciki har na fara miki fada,banida niyyar sakaki cikin kadaici sameemah duk abinda yah faru yah fi karfina ne sannan ina baki hakuri akan rashin fahimatar dake tun daga farko"
Duk da bana kallonta amma nasan maganganuna suna shiga cikin kunnenta,samun waje ta samu ta zauna a bakin gado,yayinda nima na bita na zauna a gefen ta tareda jawota zuwa cikin jikina sanann na cigaba da maganar danake yi.
"Bazan tursasaki ki yarda da abinda nake fadaba,saidai ko wata rana zaki iyah bincike akan hakan,ki yafemin da barki cikin wannan halin,bazan gazaba waj en baki hakuri a koyaus Koyaushe ,idan bazaki damuba inaso naji mai yah faru dake har kikabar gida sannan a ina kika tsinci kanki"


💎*Sameemah a madubin gani*💎




Shiru mukayi daga ni harshi,ina jin yadda zafin jikinmu yana gauraya zuwa guda d'aya,
Wani irin yanayi nakeji yana shiga cikin jikina wanda na ji a duk lokacin da farouq ya matso kusa dani,duk da banason yanayin saboda yanda yake saka zuciyata yin rauni a lokaci da ya,amma kuma bazanyi karyaba yana sakawa najini kaman ina raye nima kaman sauran mutane,duk da cewa zuciyata bugawa take saboda ina tsoron kar na cutar dasu acikin kowanne irin lokaci.
Musamman danaji dalilin tafiyar yah sameer daga gida sai na tsinici kaina da son kai saboda kullum tawa matsalar nake gani ba matsalar wasu ba,hakan yasa nake kara ganin laifin mutane fiyeda abinda sukayimin.
Dago da fuskata nayi ina kallon fuskarsa wanda yasake matse jikina acikin nasa kaman zai maidani cikin nasa.
Haka kawai bansan mai nene yasami shiga cikin kaina ba na tsinci kaina da bashi labarin yanda nayi kokarin tafiyah birni aiki da yanda yan fashi suka taremu na cececi sauran yaran ta hanyar mika kaina garesu har zuwa yanda nayi rayuwata a kasar palastine da kuma kasar Brazil. Abu daya na boyemasa shine yanayi halittata da kuma dafin dayake kwance a cikin jikina harda kuma shaidanun danake magana dasu.
Wanda kuma nayi hakanne saboda lafiyarsa,dannasan idan suka tabbatar yasani to zasuyi kokarin hallakar dashine wanda hakan shine abinda har karshen rayuwata bazan yafewa kainaba.
Dora habar sa yayi akaina kafin yace,
"Kiyi hakuri da rayuwa sameemah hakika munga jarabawa kuma muna kan gani,saidai ko kusa ban fada rayuwar da kika shigaba,ke jarumace nasake fada ke jarumace sameemah,wanda ko cikin maza ba kowane zai jure abinda kika jureba,saidai ina fatan wahalar rayuwa yah tsaya miki iya haka,sannan kuma yah baki ikon karbar hakan a matsayin kaddararki,ina fatan nacigaba da zama dam uwa a gareki mai sharemiki kuka,sannan ina saka ran kasancewa miji nagari agareki idan kin bani damar hakan,sannan kuma uban y'ay'anki"
Gabana ne yah buga rigifff,saboda nasan abinda yake hasashe ba abune mai yiwuwa ba koda kuwa mun so hakan a tsakaninmu,yau daya a rayuwata naji babu dad'i kasancewata daban da irin rayuwar mutane,saidai cikin sauri na katse tunanin hakan daga cikin raina tareda cire jikina daga na yah sameer ta hanyar matsawa gefe.
Shima dayaga hakan light kiss yayimin a kumatu tareda da cewa "saida safe"




💎*salma a madubin gani*💎




Tun da nazo gidannan ko na muka zo nida sameerah babu wanda yaji dadin gidan.
Ni kullum a gaban mijina da akwai da babu duk dayane,ita kuwa sameerah mijin ma bata ganshi ba,dan yanzu an shiga wata na hudu kenan da barin daga kasar,yah tafi can wai an turashi da sunan karatu yana ta sharholancinsa.
Tun daga yanzu banyi shekara da aureba amma danasanin auren nakeyi ,kullum cikin aiki mukeyi,idam kuma kasamu ka kwsnts baka da aiki sai tunanin yanda rayuwarka zata kaya washagari.
Nida sameerah sai murna muke hajiya mairo zasuyi tafiyah itah da alhaji bala zuwa kasar india,zataje a duba mata kafarta.
Dan yanzu mun hade kanmu nida itah,dan dolen uwarmu,koba komai naka nakane,da muka uwar bari sai muka hade kanmu,amma hajiyah mairo batada masaniyar hakan.
Muna gani suka shiryah suka tafi sai rankwada kai takeyi,shikuwa duk yanda tayi sai ya yi mata sannu,bakinciki kaman zai kasheni danna tsani hakiyha mairo kaman na kasheta nakeji ,shegiyah tsinannaniyah.
Ita kam zainab taji dadi yamzu,duk da a baya itama tasha wuya,yanzu suna can ita da mijinta da kuma yar ta.
Waya san halinda sameemah kuma take ciki oho. Da haka dai muka rakasu sai hararar mu takeyi,nidai dauke kaina nayi a raina nace zaki san kin gasamu aradu,wallahi duk saina juye tijarar daki yi mana a kanki.
Zamuyi shiri muna nan zuwa kanki muma.
Aikuwa hakanne ta faru,dama munyi shirin idan sun tafi muyiwa alhajin kira,dole yah barta ya dawo koyana so ko bayaso,daga nan zanyi duk dabarun dazanyi na naja hankalinsa izuwa gareni,idan ta dawo bata da ikon yin komai sai abunda muka yi.
Ni da sameerah kullum muna kulla yanda komai zai kasance cikin sauki ba tareda a ansha wahala ba,maida hankalina kan sameerah nayi kafin nace,
"Nikam inaga sameerah idan har alhaji yha dawo da hankalinsa toh bazan yi masa asiriba zan jawo hankalin sa ne da duk dabarun danake dasu,saboda nagane duk mallakar asirinnan aikin banzane idan ya karye shikenan ya barka a tutar babu"
"Kuma fah hakane salma yamzu kina ganin umaruje da bani yake soba,duk lokacin da asirin yah fara karyewa sai na rasa kansa bare gindinsa fah. Gaskiya nima na gane,idan har zan iya shawo kansa zuwa kaina da karfin kissa irin ta mata to ina ga hakan za'ayi,muje kawai na biki muyi musu kiran a tare,idan mukayi sa'a kafin ta dawo mun shawo kansu sai muga ya zatayi kuma"
Hakan kuwa akayi mukaje wajen malami mukayi masa bayani sanann muka bashi suanan alhaji bala da dansa,da niyyar idan sun dawo tamu basirar zamu hada muyi amfani da itah a kansu.
Washagarin ranar da muka je wajen malamim kwatsam muna zaune sao ga alhaji bala ya shigo gidan,bamuyi masa maganar ina hajiyah ba sai sannu da dawowa da mukayi musu,sameerah ce tayimim signa akan ma dam gwada action,aikuwa cikin dakewa na matsa kusada shi dama nayi kwalliya nasha turare.
Karbar jakar hannunsa nayi niyyar yi,abin mamaki kuwa sai ya sakemin ita dukka kafin yayi hanyar dakinsa,shewa mukayi nida sameerah marar sauti kafin na bi bayansa da Sauri.
Bai koreni ba haka bai yimin magana ba har na hada masa ruwan wanka ya,shiga sannan na kaimasa abinci.
Har yagama cin abincin ina zaune a gafensa amma bayyi magana ba,hada kayan abincin nayi da niyyar fita zuwa kaiwa kitchen sai naji ya zawo hannuna tareda cewa,
"Salma Idan kin kai abincin ki dawo,inajin kaman jikina babu dadine shiyasa na kasa yimiki magana,daga gani dai kaman ba yau aka kawoki gidannan ba amma kuma sai naga kaman ni yau na fara ganinki a gidan kai na ya daure sosai"
Saurin saka hannuna nayi a bakinsa kafin nace,
Shshh alhaji komai ya wuce yanzu,bari nakai na dawo"
Gyada min kai kawai yayi,ina fita muka tafa nida sameerah wanda muna cikin hakan mukaji alamar jefar da jaka a kasa,dukknamu bakin kofa muka kalla inda umaruje yake tsaye,kallon sameerah yayi cikin takaici kafin yace,
"Mtsww ni wallahi narasa ma maiyasa ma dawo akanki,kwata kwata ma ya akayi na aureki oho,aikin banza kawai,dallah kawomin abinci ni"
Jikinta yana rawa ta gyda masa kai,nidai wucewa nayi na ajiye kayan kafin na zo na wuce wajen alhajin,dan dama ba magana nake da umaruje ba.
Yamzu zamanmu da alhaji bala ba yabo babu fallasa,saidai abin farincikin shine kullum kara sakewa muke dashi,sannan mukan zauna muyi hira dashi ta fahimtar juna,har sameerah wani lokacin ma da ita ake hirar,kasancewar umaruje har yanzu tsakininsu abin yaci tura,dan dama ba da soyayya sukayi aurenba,yah aureta ne ba a cikin hakalinsa ba,shiyasa abin duk yaki daidai tuwa.
Muna nan nafara jin kaman banida lafiya,nice ba nice ba kullum cikin kawanciyah da kuma amai,alhaji na samu na fadawa halin danake ciki.
Nan da nan kuwa muka tafi asibiti,gwajin farko aka tabbatar da cewa cikine dani,koni kaina banyi farincikin da alhaji bala yayiba,kaman shine haihuwarsa ta farko.
Dawowa gida mukayi bayan sun damin bincike akan komai lafiyya,sameerh ma ta tayani murna sosai,dan ma sa'a ta daya cikin baya bani wahala sosai kaman yanda yah fara a farko kafin naje gwaji,kaman dama jira yake musan yana nan.
Soyayya Mike zubwa nida alhaji bala kaman wasu yara,komai nayi biyeni yake babu ruwansa,danshi kansa naga yayi laushi dayaga hanyar dayake a baya bamai dorewa bace.
Cikin yana da wata hudu wanda yakama hajjyha mairo tayi wata hudu kenan a kasar india,dan duk a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login