Showing 48001 words to 51000 words out of 53080 words

Chapter 17 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt

05 Nov 2024

13060

hannunta da kafarta nikuma na daure karshensa a kunkumina. Da haka aka kinkimota zuwa cikin mota kowa sai bugu kirjinsa yake.
Driver alhaji musa ne yake tukamu sai alhajin a gefensa,a baya kuma nida ummee ne sai kuma sameemah da take cinyata a rike. Motar da take binmu kuma su baba umaru ne a ciki harda malamin da yayi mata magani,ba yanda ba ayi na baba umaru ya tsaya a wajen inna ramatu amma yaki yarda,a cewarsa likitoci zasu kula da ita.
Tafiya Muke a hankali har mun kusa kauyen mun fita daga cikin gari,mutsuniya naji sameemah tafarayi kaman wanda ake tsikararta,saurin dubawa nayi naga idonta a bude,saidai bakikkirin suke kaman an zuba gawayi a cikinsu,wani rin mika tayi tareda yin wata kara saida muka rufe kunnuwanmu dan karta bata mana dodon kunne.
Jijjigar datake ne yasa dole saida driver ya tsayar da motar,saboda tana koarin jawo muyi hatsari,kofar da take kusada mu ta banke da wani irin karfi tafita da gudu.
Jana take saboda hannunta a daure yake kuma sarkar tana kunkumina,tirjewa nake tana jan mu yayinda suma malamin suke binmu a baya,gashin kanta ya tattashi sai gurnanai takeyi ,danni kaina kallon naci amanarta take min,dabarace ta fadomin ganin bazan iya tsayar da ita da haka ba saina nannade sarkar a jikin wata bishiya ina numfarfashi dannima a matse nake a jikin bishiyar sosai.
Wani mutumine mai dogon gemu da cikar gwarzini yazo inda muke,kallo na karemasa dannasan ba malamin da muka zo dashi bane,kara tirjewa take tana ja da baya tareda sake daga sautin kukanta lokacin da mutumin ya tunkareta,wani abu ya shafa mata a goshinta take ta yi wata mika ta fadi a wajen kaman ta mutu.
Motar muka koma domin karisawa gidan babban malamin,sai a sannan na kula aahe shine wanda yazo wajenmu a jejin,gidannasa babu nisa dan mun iso garin ma ashe.
A wani dakin kumadu aka saka ta saidai wannan duk jikin dakin rubutun Qur'ani ne,hadda wasu addu'oin da baka sansu ba ma.
Muna isa aka kaimu masauki domin muyi sallah azahar dan a ranar za'ayi mata rukiyya basai gobeba,dan yawan jingirtawar da akeyi yawan kara mallake jijinta da sujeyi .munayi sallah bayan munci abinci,dan abincinma dabawa mukayi saboda tashin hankalin da muke ciki.
Kafin mushiga dakin da take saida ya kafa shaidu tukunna. Banda wacce take haila,banda wanda yakeda aljanu a jikinsa,haka kowa sai yana da alwala,kuma bakinsa bazai daina kiran sunann allah ba har a gama.
Haka muka amince da duk sharadinsa kafin muka zauna a wajen,sameemah tana tsakiyar wajen an saka mata wata doguwar riga fara,bayan mun zauna ne malamin ya umarci wani a wajwn akan ya sinceta daga sasarin da take daure dashi.
Mudai muna ganin ikon allah har yagama sunceta amma bata ko dago kaiba bare ta motsa daga yanda take.
Karatu aka fara yana amsa kuwwa a cikin dakin,kadan kadan jikinta yafara rawa kaman ana jona mata shokin,bayan an dan dade da karatunne ta fara ihu tana yagar jikinta da karfi.
"Kai Wai miye kuke hakane,ba dama ku barmu mu zauna lafiya mai muka muku haka,dan mutum daya bazaku barmu mu dauka a matsayin namu ba?"
"Badaku nake ba kananan shedanu ,so nake shugabannaku dayake turoku yazo da kansa,ku fada masa shine ke nema,ku kuma idan nan da wasu mintina baku fitaba to sunan ku matattu"
Cigaba tayi da ihun bayan ta tayi magana malamin yabata amsa,can kuma sai tayi shiru alamar abun ya lafa.
Ganin malamin yafara karatun dayafi na farkone yasa muma muka fara babu tsayawa,fatar jikinta ce take sauyawa zuwa baka,ga farcuna da duka fito sunfi na farkon kafin zuwan mu nan,tsorone yashiga zukatanmu saidai bamu daina karatun da muke ba har saida mukaji ta fara gunji,malaminne yatashi da sauri ya debi wani ruwa a kofi ya watsa mata,bayan ta gigicene yasake diban wani ya zuba a cikin bakinta ta hafite da sauri tana kama makogaranta tareda sakin wani ihun dayafi na farko,magana ta fara cikin wata babbar murya,
"Ka bukaci nazo amma kuma kana cutar dani ai ba haka mukayi da kaiba ko,zancen na sauta kuma bazai yiyu ba dan itadin muna tareda itane tun tana shekara uku a duniya"
"KO tare aka haifeku da ita yau zaka barta,sannan kuma ka dawo mata da kuruwarta daka dauka,wacce kasaka mata a jikinta kuma yanzu zan fitar da ita ko kana so ko bakaso"
"Ahah karka cire ruhin mu dayake jikinta ka fadi duk abinda kake so zamu baka,bakasan tsawon lokacin da muka dauka muna rainansa a cikin jikinta bane,saida lokacin tashinsa yazo sanann zaka bata komai,zakayi mana asara dayawa,dan haka duk abinda kake son a duniyar nan zan baka matukar zaka bar ruhin dayake jikinta lafiya,har nata ruhin ma zamu dawo mata dashi indai zaka bar wannan baxaka fitar dashi ba"
"Eh shikenan na yarda da yarjejeniyar da mukayi dakai,zaka bani wani abu,sukuma yan uwanta zamu mantar dasu,amma da sharadin ruhinta ma zai zauna a jikinta kafin daya bak'in ruhin ya tashi"
Mai kunnuwana suke jiyomin,ai malamin ya yadda da abinda shedanin ya fada kenan,har na tashi zanyi wani abu sai naji nakasa tashi daga inda nake ,murmushi fuskar sameemah tayi wanda daga gami ba ita bace wannan.
Can Bayan wani lokaci muna zaune mun zubawa sarautar allah ido,vanda kiran sunan allah babu abinda nake a cikin raina,wani haskene yashiga jikin sameemah kafin ya bace kamar bai shigaba.
Hakan yana faruwa malamin yayi sauri yah watsawa sameemah wani ruwa dan kadan dayake cikin wata jarka,wani kara tasaka kafin tafara cewa,
"Ka cucemu ka yaudaremu saida muka dawo mata da ruhin ta sanann zaka juya mana baya,mai yasa zaka kafe ruhinta ta yanda bazamu iya kara dauke shiba bayan kasan munyi yarjejeniya akan bazaka cutar da ruhinmu dayake jinkinta ba sanan........."
Saurin yin shiru tayi sanadiyyar wani ruwan da malamin ya zuba a bakin sameemah sannan ya matse bakin saida ta shaye shi,wata addu'a ya cigaa dayi kafim yayi mana alamar mucigaba dayi,muna cikin yine mukaga ta fara rike cikinta can kuma sai ta koma rike makogaro,shakewa muryarta tayi tafara kokarin amai.
Wani bakin ruwa ta fara amarwa can kuma saiga kan wani abu kaman maciji bakikkirin,zuwa lokacin kadan daga cikinmu ne suke iya bude bakinsu suyi addu'a ,ciki kuwa harda yarannasa idon su yayi wuri wuri.
Cigaba tayi da kokarin amai abin yana fita dogo dashi har ya kare fitowa daga cikin bakinta,motsi kadan abin yayi kafin yadaina motsin can kuma malamin ya zuba masa wani abu kaman farin gari nan da nan ya bace kaman bai daba wanzuwa ba.
Kan sameemah dukka muka nufa wanda ta fadi tun lokacin da abin ya fita daga jikinta.
Ru wan mag an in ya cigsbs da shafa mata,yana addu'oi kafin ya kalleni .
"Mashaallah in allah ya yarda an samu nasara,saidai banida tabbcin tashinta,dan da kyar idan bai yi mata lahani a cikin ta ba lokacin daxai fito,musamman ma daya dade a jikinta,shine yake sakata komai sannan da dafinsa take amfani wajen kisa da kuma bada kariya ga kanta badan komai ba dan yasamu kariya jikinta har zuwa lokacin da zai mamaye jikinta.
Yanzu munyu nasarar fitar dashi dama dashi suke iyah nemota har su san inda take,sannan kuma sun dawo mata da ainihin kuruwarta,dan haka ku gaggauta kaita asibiti a duba lafiyarta,sannan ga wannan ruwan shi zata dunga sha daga lokacin data farka har na tsawon sati guda,idan kuma ta manta wani abun kar a tursasa mata,in ma kuma babu matsala shikenan,zaku iya tafiya allah ya kiyaye ya kuma sawwake ameeen"
Kinkimarta nayi da sauri muka nufi mota domin kaita asibitin,su alhaji musa da kuma baba umaru sai godiya suke masa,har sannan hankalin su bai dawo jikinsu ba sa abinda suka gani.
Bamu wani dadeba muka iso asibitin cikin barrack din kasancewar gudu muke a motar ba kamar lokacin da muka tafiba.
Muna zuwa ummee ta saka kayanta na aiki,duk da jikinta har sannan a sanyaye yake daga ka ganta kasan ba karamin kokari takeba kawai.
Dakin taimakon gaggawa aka shiga da ita,inda aka shiga bincikar ina ne yake da matsala a jikinta,babu wani rauni a jikinta saidai duk ilahirin halittar cikinta ta gaji sosai wanda hakan yasaka ta shiga coma saboda shock din da jikinta ya shiga.
Duk mun ji dadi da babu rauni a cikinta amma shiga coma din ma bai mana dadi ba sam.
Dakin kulada ita aka mayar da ita,duk an manne hancinta da wayoyin dazasu dunga kai mata abinci zuwa cikin jikinta.
Kasan cewar akwai ummee dazata dunga kulada ita sannan kuma akwai wasu nurse wanda suke shige da fice sai yazamana ba sai mun zauna tareda ita ba saidai mu dunga zuwa dubata kawai.
Duk da cewa hankalin mu ba tashe yake kaman da ba amma kuma ba a kwance yake ba sam,domin yau kimanin sati biyu kenan da kawai sameemah wajen mai magani amma ko motsi batayi,saidai na'ura da take nuna cewa a tana raye ba ta mutuba.
Tunda sameemah tashiga sati biyu da shiga coma hankali na yafi na kowanne lokaci tashi,saboda gani nake kaman bazata tashi ta dawo gareniba,a bakin kofar na tsaya ina kallonta yanda take kwance,ita da matacce basuda maraba,karisawa nayi a hankali har zuwa onda take kwance na zauna a kujerar da take gefenta,kama hannunta nayi na rike wanda karin ruwa yake shiga ta cikinsa,muna nan zaune har na kara kaina da katifar da,take kwance akai,can kamar a mafarki naji kaman tana motsa hannunta dayake cikin hannuna,basarwa nayi danna san bazai wuce gizo takemin ba kaman yamda ta sabayimin acikin mafarki,cigaba tayi da motsa hannun wanda zuwa lokacin kuma abin yawice gizo,yafara zama kaman gaskiya ,kodai da gaskene kai itace take motsi ???......


Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150


Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.


💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎










*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*




💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}








💎47~48💎




💎*sameemah a madubin gani*💎






Na Dade ina kokarin bude idona domin naga hasken dayake cikin duniya amma nakasa samun damar hakan said yanzu,duk da dishi dishi nake gani amma nasan ba a gida nake ba.
Abubuwan dasuka farune suka fara dawomin cikin kwalkwalwata,inajin na kamar bani bace,saidai nafison yanayin yanzu akan na baya,dan yamzu inajin kaman ina da yanci ba kaman lokacin baya ba.
Motsa hannu na nayi sai naji kaman an rikeni ,juyowa nayi a hamkali amma vana ganin abinda yake faruwa sosai.
Lokacin da idona ya fara komawa dadaine na hada ido da fuskar da na cire tsammani da sake ganinta a rayuwata,dakyar bakina yake motsawa dason furta sunansa akan harshena,
"Ya.......hhh....sameeer"
Murmushin da yayiminne idonsa cike da hawayen farinciki yasaka ni nima jin dadi,saboda yamzu na gane ba mafarki nake ba yah sameer ne a gabana.
Bayyi magana ba said rungumeni da yayi a jikinsa kaman za'a kwaceni,karar murda kofa mukaji wanda yasa ya dam zare jikinsa daga gareni.
Ummee ce tashigo itama fuskarta dauke da farinciki,bayan ita wasu nurse ne suka shigo amma daga baya suka tsaya,danna kula har yanzu tsorona suke,dan murmushi kawai nayi dan banga kaifinsu ba ko kadan.
Ciremin karin ruwan tayi da kuma wasu na'urori a jikina saboda nasamu damar tashi na zauna
Yah sameer ne ya taimakamin na tashi saboda rashin karfin jiki,tunda nace yah sameer ban sake cewa komai ba sai jijjiga kai kawai danake idan aka tambayeni.
Haka nake ga kaman shine ainihin halina rashin magana,sainaga dama,dan banajin yin rashin kunya amma kuma vanajin yin magans ma saidai kawai kallo da ido.ummee ce ta kalleni kafin tace,
"See my daughter now,bazatayi fadi abu da baki ba saidai ta nunawa mutum tana son abu,babu sakewa da mutum sai wanda ranta yaso zama dsshi,ko mutum zai kwana yana zolayarta sai taga dama ta kulashi,ko ba haka ba baba umaru"
"Murmushi yayi irinna manya kafin ya daga kai alamar hakane.
Dukka dakin dariya suka saka harda yah sameer da kuma anty saleemah wanda itama dazo dubani da taji na tashi.
Farouq kuwa ta gudu yazo gefena yana dariya,yah sameer ne ya dorashi akan katifar danake a kusa dani,shima iya Murmushin kawai nayi masa banyi magana,abin yabani mamaki sosai kuma sai na tsinci kaina da jin hakan normal ne babu matsala.
Kwana na biyu a asibitin na koma gida,duk da haka mutane basu bar zuwaba,harda zainab ma tazo daga gidanta,sameerah ce kawai bata zoba saboda abinda ya faru,nikaina na girgiza danaji abinda yah faru,inda nace idna komai ya daidata janze gida na gaishesu.
A zaune nake a bakin gado ina tunanin abinda yafaru ni kadai,wani nayi dariya wani nayi jimami musamman kisan danayi da kuma rashin sallah,shiyafi damuna sai kuma zaman danayu a palastine wanda yamzu ma ina son sake zuwa dan akwai abinda van karisa ba tukunna.
Jinayi an dafani ta baya hakan yasa na juya da sauri,dan yanzu bana jin sautin bugun numfashin mutum ko kuma sautin dayake yi daga nesa,sannan jikina baya warkewa da sauri kaman da ,hujin allaurar da akayimin a asibiti ma suna kan fatata basu goge ba ,ta haka na fa him I yanzu dadai nake da kowanne mutmu mai lafiya.
Juyowa nayi muka hada ido da sameer,
"Tunanin mai kike kedai,ba ance ki dunga hutawa ba"
"Yanzu ma ai hutuwa nake tunda ba aikin danake yi "
"Wannan ba hutune bane bawa kwalkwawa service ne,yakamata ki huta sosai komai yakoma normal tukunna"
"Yah sameer na gode "
"Godiyar kuma ta menene kike min yanzu"
"Ta taimakona dakayi,ta kuladani da kayi,ta zama a kusadani da kayi,ta rashin jin tsorona dakayi ,ta rashin kyamata dakayi,bazan iya yimaka godiya a kan hakan ba dan allah kayafemin abinda nayi maka a baya,ka tayani bawa kowa hakuri dan......."
"Shhhh,banason jin wanann daga bakinki sameemah,komai nayimiki ne dan allah da kuma soyayyar danake miki,babu abinda nake nema daga gareki sai ki soni kaman yanda nake sanki sannan ki kasancen mace ta gari kuma uwa ta gari a gareni"
"Inshaallah zan yi kokarin wajen kasancewa haka a gareka,burina ka kasance bango a garemu mu iyalanka"
Budemin hannusa yayi akan nazo jikinsa vanyi musu ba kuwa dan a lokacin ina bukatar wanda zaimin rarrashi,mun dade a haka kafin ya fita masallaci dan an kira sallah r isha.
Nima alwalar na iyo na fara jera sallah iya adadin da jikina zai iya dauka,dan doke sai na biya bashi nsallalon a dake bina.
Ina cikin sallah yah sameer ya leko dakin dayaga ina sallah ya barmin sakon na sameshi a dakinsa.
Wanka na shiga na duje jikina sosai,lokacin dana fito mulke jikina nayi da lotion mai sanyin kamshi kafin na fito da wasu kayan bacci sabbi dal.
Lokacin dana sakasu nikaina nasan nayi kyau sosai,bare kuma mabukacin na namiji ya kalleni,hijabi na dauko mai girma nasaka kafin na fito daga dakinnawa zuwa dakinsa.
A hanya na ci karo da saleemah zata shiga kitchen,har na dauke kaina zan wuce tasha gabana da sauri. Sunkuyar da kaina nayi amma kuma saina ji tace,
"Kiyi hakuri da abinda ya faru sameemah,duk da kinsan zan iya cutar dake idan na samu dama amma haka kika ceci rayuwata a hannun wannan mutanen,zuciyarki mai kyauce tun da bare kuma yanzu,hakika dab vansan kece kanwata data bata bane,babu wacce nake so kaman lokacin kina karama kullum har na girma sai na kalli hotonki da tunanin ina kike,nayi kewarki kasancwar nikaidai na tashi mace,ashe ban sanj ba kaddara zata kawoki har cikin gidana mu zauna tare a karkashin miji guda daya,kiyafemin abinda ya faru a baya,ina tabbatarmiki hakan bazai sake faruwa ba ,dama daga vangarena ne komai yake faruwa ke bakya tankamin har se na shiga gonarki da yawa"
"Babu komai anty saleemah allah ya shige mana gaba"
Dariya tayi kafin tace,
"Hmm a baya ina ta mahaukacjn kishi ashe vansaniba ke bakida ikon morar mijinma,kai ai nikam anyi wawiyar yaya,yanzudai karna bata miki rai aje a yi amarci lafiya,kar ku damu zan hada komai kafin ku tashi,yau daya first in history zan shiga kitchen saboda kanwata gobe".
Shigewa nayi zuwa dakin yah sameer din ita kuma ta nufi hanyar kitchen din domin debowa zuhrah ruwa.
Lokacin dana murda kofar kirjina ne naji ya buda,abinda banyi mamaki ba gashi zai kasance,wai nice zan shiga dakin mijina kuma da tunanin bazan cutar dashi ba,sannan nasan bazan fito haka kawai ba face ya karbi hakkinsa a wajena.
Saida na leka babu kowa a dakin kafin nasaka kafata a cikin.
Zama nayi a bakin gado ina jiransa dannaji karar ruwa a bandak8n.
Fitowa yayi da towel a kugunsa,ruwa yana zuba a jikinsa,kamshin sabulun ne ya daki hancina take kuwa ya saukarmin kasala mai nauyi a cikin jikina.
Shikansa yakula da halin dana ahiga domin naga wani karamin murmushi a gefen fuskarsa,juyawa nayi na bashi baya domin yah shirya,amma maimakon haka sai damshin ruwa naji a hannuna dayake gefensa.
Juyowa nayi numfashinmu yana gwauraya dana juna kasancewar kusancin dayake tsakaninmu bashida yawa,bakinmu ne yayi saiti dana juna hakanne yasaka yah sameer yunkurin sumbatata,ban nuna alamar zan hanashi yin hakan ba ko banza na tsaya naji mai ake ji,dan abune dana fiddda ran a rayuwata zan taba yinsa.
Had'a bakinmu yayi waje daya da dan sakkanni kafin ko wannenmu ya ja baya yana kallon idanun dan uwansa dayake dauke da sako kala kala.
Yah sameer ne yayi karfin halin yin magana kafin yace,
"Turarenki Yana da matukar dadi,dam cikin kankanin lokaci har ya gama da kwalkwalwata,sannan wannan hijabin fah,daga gani akwai wani abu a cikin.
Murmushi nayi tareda sunkuyawa,yayinda shikuma ya yaye hijabin dayake jikina,dan zare ido yayi ganin kayan dake jikina,kuma da alama ya yaba da shigar danayi.
"Duk wannan ni'imar nikadai ne,mallakina ne batareda wani ba,ah na manta Ashe fah wani ya rigani ,dan har kyautar mota aak bayar akai"
Harararsa nayi tareda kai masa duka a kirji,danna kula tsokana ta yake,jana yayi muka fada gadon ta baya,shafa man da bayyi ba kenan aka lula dani sabuwar duniyar da ban taba tsintar kaina ko tunanin zan shigeta ba,sai gashi gwarzon yayannawa ya nunamin karna sare da yin nasara,sannan ya taimakamin wajen nunamin yanda yancin rayuwa take,mai zanyi a duniyarnan daya wuce na yi masa biyyaya sannan na faranta masa rai.............(toh kunji masoya fah)


Kaman yanda anty saleemah ta fada kuwa da safe tahada mana karin kumallo mai rai da lafiya,daga ni har yah sameer bamu muka tashi ba sai wajen karfe sha daya,kasancewar rashin bacci a idonmu tunda mukayi asuba muka kwanta kaman mun mutu.
Bayan mun tashi dakina na nufa saboda sanja kaya,tunda banida kaya a dakinsa.
Lokacin dana fito dukkansu suna zaune,yah sameer sai yuwa anty saleemah tsiya yake wai tayi abijci saboda kanwarsa,amma lokacin da suna zaune yayi yayi taki yin abinci saidai yan aiki suyi.
Haka muka gama cin abincin cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login