Showing 15001 words to 18000 words out of 53080 words
Chapter 6 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt
aiki daga gani,sai fah kin dage,dan ma kincemin baya kulata,amma duk da haka saifah kin dage,ba a shaidar ɗan kuturu sai yah shekara da ya tsunsa tukunna"
Murmushi nayi kawai,danni kaɗai nasan irin abinda na shuka zam aiwatar a gidannan,duk abinda zanyi na kori sameemah a gidana to zanyi,domin itah ɗin hatsarine zaman ta cikin gidan.
Hirar mu muka cigaba da suhaila kuma duk bata wuce akan sameemah bane.
Sai wajen magriba kafin suhaila ta tafi gida,lokacin sameer ya dawo daga aiki suka gaisa ma a waje.
Tare muka shigo dashi,ina kalllonsa yama kallon gefen ɗakin sameema,haushine yakamani duk da nasan ba komai ne a tsakaninsu ba,jakar hannunsa na karba tareda kamo hannunsa cikin tattausan hannuna duk dan na ɗauke hankalinsa daga tunanin ta,kallona yakeyi da idonsa da sukayi ɗan ja saboda yawan aiki.
Nima sansanyan kallo nake aika masa wanda nasan yana narkar da zuciyarsa a duk lokacin danayi masa,musamman idan yana a yanayi na buƙata.
Ɗakinsa muka shiga yah rage kayansa yah shiga banɗaki,nikuma na ajiye jakar tareda zuwa ɗauko abincin da kareematu mai abincina tayi.
Lokacin dana shigo ɗakin har yah fito daga banɗakin yah saka ƙananan kaya marasa nauyi,hada ido mukayi dashi,lokaci ɗaya na karanci duk abijda yake kwance a cikin idonsa,kirjina yabada ƙarar bugawa fatt,saboda nasan in yana wannan yanayin bana karewa da ɗadin jiki,dan sai nayi gashin jiki tukunna.
Kawar da tunanin hakan nayi a raina na cigaba da zuba masa abimcin,saƙƙowa yayi inda nake zaune daff da dani,ɗan matsawa nayi kaɗan domin bashi damar cin abincin,saidai daga fuskarsa nagane bahakanne a gabansa ba.
Ko kuma mai yah tuna sai kuma naga ya jawo plate ɗin abinci yah fara ci.
Lokacin dayah gama an ƙira sallahr magriba,dan haka alwala yayi yah tafi masallaci,yayinda nima nayi nawa ɗakin.
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎15~16💎
💎*sameer a madubin gani*💎
Har na isa masallaci babu abinda nake sai tunanin yanayin gidannawa,a yanda halitta ta take nasan nayi ma saleema karfi saboda yanayin jiinta,idan har nace zan tursasa mata toh zan iyah shiga rayuwarta.
Bangaren sameema kuwa banajin koda mun shryah zan iyah zaman aure da ita,saboda har yanzu idanuna sun kasa ganinta a matsayin matata sai ƙanwata.
Zaman damuke yi da itah a gidan ma ya isheni bare kuma zancen wani abu daban.
Da ƙyar na samu na yage tunani a cikin raina nayi sallah.
Bayan an gama sallah ma ban koma gida ba sai addu'o'i da nakeyi dan samun kusancin ubangiji da kuma neman sauƙi akan abinda yake shirin faruwa.
Sannan ya,zabamin abinda yake mafi alkhairi a game da mafarkin danakeyi na sameema da kuma dukkan ayalina a cikin wani yanayi marar daɗin gani.
Lokacin dana ɗauko hanyar gida goma ta kusa,sojojin da suke patrol ɗin dare har sun fara,ɗaga min hannu sukayi tareda buɗemin kofar gidan na shige.
Har nayi niyyar wucewa sai kuma na shiga ɗakin sameema,duk da nasan bata son ana shigemata ɗaki,saidai ba ra'ayinta nake biba nice da iko da itah ba itace take da iko dani ba.
Murda ƙofar danayi a hankali ko a rufw yake,saidai cikin sa'a naji kofar tah buɗe.
Ina gama shiga ɗakin ita kuma ta fito daga banɗaki ta towel a hannunta ɗaya kuma tana goge ruwan daya taba gashin kanta.
Tun daga ƙasa idona yafara yawo a jikinta,yah wuce dogayen kafafunta farare masu matsakaicin ƙiba,har zuwa laffaffen cijinta da ko kaɗan bai ɗago towel ɗinba,saukewa nayi akan fuskarta wanda ita ma ni take kallo,saidai muna haɗa ido da itah ta ɗauke kanta tareda zefar towel ɗin dake hannunta ta nufi gaban madubi.
Yanda take yin kowane motsinta sia yake nuna kaman dani takeyi,amma itah a nata bangaren yi kawai take.
Lotion ta ɗauko ta ɗage towel ɗin har zuwa kusan kunkuminta kafin ta fara shafa man.
Babu abinda nake ayyanawa a raina sai yin salati da kuma yiwa zuciyata gargaɗin kan cewa,abinda take gani fa miliyoyin mutanene suka gani kuma suka taba,dan haka babu abin zan hankali akan abinda ya riga yagama zaga duniyah.
"Wai binciken kazo sake yimin koh kuma yau turoka akayi ka tsareni da ido duk abinda nakeyi"
Duk da abinda ta faɗa gaskiyane ita nake kallo,amma yanda ta faɗi ina kallonnata sai abin yah bani haushi.
"Mai zan kallah akan abinda yah riga yagama zaga duniyah,kowa yah gama kwasar romonsa yah bari"
Murmushi tayi saidai har yanzu bata ɗago tah kalleni ba,saima tashi da tayi ta nufi wajen kayanta na bacci,ɗauko wasu pink tayi masu kyau ta ajiye akan gado kafin ta juyo ta kalleni,
"Toh zan iyah sanin mai yah kawoka ɗakin wannan karuwar da karfe sha ɗaya na dare har kakemin wannan kallon ,bayan kana da mata,ko ta kasa kashe maka kishirwarka ne kazo muyi cinnki.
Saidai kasani farashina yana da tsada sosai,amma karka damu nasan zaka iyah biyah ai,yanzu sai muyi ciniki,dama kuwa na dade ban sayarda hajata ba gashi na samu costomer da wannan daren,kuma kaima ka taki sa'a da bakayi booking ba bare kuma bin layi kawai ka samu a kyauta"
Duk baƙincikin danake ciki a yinin ranar nan baikai kwantan kwacin maganar da sameema ta faɗa min ba,wannakuwa anya mutunce,abinda nah fada a ransa kenan.
Ganin koda nayi niyyar faɗar wata kalmar bazata samu damar fitowa ba,juyawa nayi kafafuna suna rawa ga raina yana tafarfasa.
Ɗakina na nufa dan ban ra'ayin ganin itah kanta saleema ma a lokacin,tambaya nayiwa kaina ,meyasa nake jin haushi dan ta faɗi hakan,meyasa nekjin maganar tayimin zafi?,nidai ba kishinta nake jiba koh?.
Kodah yake dole nayi kishinta ai ƙanwata ce.
Da wannan amsar zuciyata ta yada har na kwsnta bacci bansan sanda barawon baccin ya ɗaukeni ba.
💎*sameemah a madubin gani*💎
Ina jin sanda yah bugomin kofar da ƙarfi bayan ya fishe,ko ba a faɗaminba nasan yah ji zafin maganar danayi masa,hakan yanamin daɗi idan mutane suka ɗaukeni a wata siga da zuciyarsu ta raya musu ba tareda sunyi bincike akai ba.
Kayan baccina na saka tareda bin lafiyar gado,har sannan ban daina murmushiba da kuma tuno yanda yake bin jikina da kallo,wanda kuma hakan zai ganshi yah bari,dan bana kowa bane na wane ni ka kadai.
Washagari da safe ina tashi da feɗuwa na sauƙo daga kan gado,dan yau kam nakoma sameemah tah kuma,na gaji da waccar wacce bata yin abinda taga dama,kokuma ta dunga barin abu idan anyi mata.
A wajen saka kaya dama wani wando na samu jean irin mai ɗamewar nan,sai wata me ɗan tsayi,itah ɗinma saboda rashin mutunci ban barta hakaba saida na ɗaureta ta koma dadai inda wandon zai fara,facing cap na ɗauko irin rigar na nasaka sannan na sneaker suma masu adon pink.
A taƙaice dai na fito kaman wata mawaƙiyah a ƙasar turai dama kuma ga farina mai harkene sosai.
Fitowa nayi falon dadai su saleema suna karya wa ita da sameer a table,farouq ma yana gefensu yana cin taliyar yara.
Ɗago min hannu yayi tareda cewa,
"Hi anty"
"Ya kke ka tashi lafiyah"
Dariyah yamin irin ta yara yana ɗaga kai,kallon iyayennasa nayi tareda ɗaure fuska kaman banice nayi wa yaron murmushi ba.
"Ku kuma na tafi juggling na exercise kwana biyu ina zaune har na fara tara cholestrol.
Sameer ne dayakai shayi bakinsa yayi saurin zubarwa har yana ƙwaruwa kafin yace,
"Me......menaji kince,excercise?"
"Ashe kaji mai nace ɗin kake neman na maimaita"
"Toh bazakije da wannan kayan ba kam"
"Saikuma kayi ai wai karuwa taga mai wa'azi"
Juyawa nayi na fita hankalina kwance,dan tundaga cikin falon na fara juggling ɗin ban fitaba.
Hanyar dazai kaini jejin cikin wajen na nufah,dan daman dan yaganine nace masa cikin wajen zan shiga,amma dayasan yanda banason cikin mutane daya sau ransa a inuwa.
Bani na dawoba sai can wajen tara da rabi,dayake tun bakwai na fita.
Wanka nayi tukunna na fito falon.
Wayata ca tayi ringing ina ɗauka naga baƙuwar lamba,saidai nasaka a kunnena naji ashe wanda aka bawa saƙon kawomin karnuka nane yazo yana bakin barinki sojojin an hanashi shigowa.
Fita nayi zuwa bakin wajen,dayake akwai tazara na jima ina tafiyah kafin na iso bakin wajen,su bingo suna kallona suka fara ƙoƙarin ƙwacewa a hannunsa.
Alama nayi masa da ya sakesu,dan daga gani a tsorace yake dasu sosai.
Aikuwa kaman jira suke suka rufo da gudu kaman sunga nama,tsugunnawa nayi na taresu,sai kaɗamin jela sukeyi.
Maganar wani soja ce tah ɗago dani wanda yakeyi kaman mai koyon hausa.
"Hajiyah zakina biyamu kuɗin ƙarba saƙo fah"
”kudin me kuma ana zaune kalau,ba abinda zan baku idan kunga kuma zaku iyah toh ku biyoni gidanan ku karba"
Har zai sake magana wani a cikinsu yah raɗa masa abu a kunne,yana jin hakan yah yi shiru yana juyah fuska.
A hanyane muna tahowa na kulada yanda raze taƙi sauri shikuma bingo yaƙiyin gaba ya barta kaman yanda suke wani lokacin,tsayawa nayi ina ƙaremusu kallo,sai a sannan na kula da yanda cikinta yayi faɗi yai ƙasa,kallon bingo nayi mai kama da harara,saurin juyawa yayi yana shinshina bushasshiyar ciyawar da take wajen,shafa kanta nayi kawai kafin na ce,
"Allah ya sauƙeki lafiyah"
Da haka muna tafiyah har muka iso kofar gidannamu,wannan wanda yayi mana tambayoyine lokacin farkon zuwana gidannan,dan na kula a duk cikin sojojin da suke gadi yah fi kowa iyayi da taƙaama.
Kabani wajen na wuce,kafin na maimaita sau biyu,idan kuma ba haka ba wallahi zan iyah shiga na fita aikin soja sai yah gagareka a rayuwarka.
"Ina zakije a da wannan dabbobin,ko karnukan sojoji baza'a basu damar wucewa ta nan ba,bare kuma wannan"
Tahowa nayi zan wuce sai ya tare kofar dan yaga mai zanyi,tafiyah nake zuwa wajen get din,nima ban fasaba,har saida nazo gaf dashi amma yana tsaye bai ko motsa ba.
"Nayi maka last warning ka bani waje na wuce tun kafin raina ya baci"
"Bazan ........"
Tun kafin ya karisa maganar nayi masa wani naushi a hanci,taga taga yayi yai baya zai fadi,amma duk da kokarinsa saida yah daku da kasa,ta gefensa na tsallaka na wuce koh kallonsa banyiba,injinsa yana rike da hancin yana face majinar dole.
Direct cikin falon na shiga suna biye dani har dakina,saleemah tana zaune a falo sai ganinmu tayi mun shiga,tashi tayi tana kallona har na wuce dakina.
Gyalen dayake wuyana na cire kafin na jawosu muka fito zuwa kicin,robobi guda biyu na ɗauka a wajen set ɗin robobi,ja da kuma koriyah.
Abinci na diba na cika kowacce roba kafin na fita,suna biye dani kaman jela har garden din cikin gidan.
Ajiyewa nayi tareda komawa debo ruwa,a hanyar komawar ne mukayi karo da sameer wanda dawowar sa kenan da key din mota a hannunsa,
"Meyasa kikawo karnukanki gidannan batareda izinina ba,bayan kisan koh sanda muka je gida ma ba sonsu nakeba,kina mace mai zakiyi da karnuka hakan ma a kina mayar aure,abimda kike yakamata ke a ganinki"
"Kai wanda kakeyi na ya kamata ne,karnuka kuma nawane ni naga damar zama dasu shiyasa na taho dasu,kuma babu mai fitar dasu a gidannan,dan zamana sukeyi,idan zasu var gidannan saidai mu tafi tare"
Kedai kika sani,amma koda wasa karna kuskura naji akan wasu wata maganar ta fito,idan kuwa ba hakaba zasu bar gidannan koh kinaso ko ba kyaso"
Kafi kowa sanin halina akan hakan,amma idan aka daboni bana shiru saidai koh maima yah faru"
Daga haka yah juya yabar wajen zuwa cikin gida,saida na tsaya na tabbatar suna cin abinci kafin na shige cikin gidan.
Hayaniyah na ji a falon inda na tsinkayo muyar saleema tana faɗin bazata zauna da karnuka a gida d'aya ba,harara ta bini dashi dana shigo da alama bataso zaman karnukan ba,nikuwa babu yanda zatayi dani nan gani nan bari ɗumamen mayyah.
Satin su bingo ɗayah a gidan har sun washe da gajiyar mota,babu inda basa shiga a cikin gidan,ɗakina kuwa saidai idan gari bai wayeba,duk da reza bata fiye zuwa wajena ba saidai idan na je inda suke,kasancewar cikine da itah.
Sojan dana bigewa hanci kuwa,wanda naji sunansa wai samuel,kullum muka haɗu sai yah harareni da alamun zamu hadu,ni har dariyah ma yake bani.
Fita exercise yanzu da bingo nake zuwa,tun sameer yana masifah,har kusan marina yayi amma ban fasaba,kwata kwata banajin daɗin zaamn gidan,bayyi kama da inda zan zauna ba a yanayina,dan ma nakan je cikin maakrantar koyar da ƙananan sojoji da akeyi wani lokacin ina kallonsu,hakan yakan dan debemin kewa,sannan kuma mukan fita yin training nida bingo,dan ɗan barshi danayi a gida har yayi laushi wajen gudu.
Tun da safe naji motsi a ɗakina amma bana su bingo bane ,ƙin juyowa nayi saboda nasan waye a wajen,
"Nasan ba bacci kike ba,nazo na fada miki cewa ki shiryah zan kaiku gidan su saleema ku yini,saboda tunda kikazo basu gankiba,yakamata kije su ganki"
"Bazan jeba mai zasu min idan sun ganni din"
"Kinba ba gardamarki nazo jiba,magana ce na fadamiki kishiryah nan da karfe goma zan kaiku,saura kuma naji wata maganar ta fito kuma"
Lokacin dana jiyo wayam naga wajen babu kowa da alamar har yah fita bayam yayi maganarsa ta karshe.
Tsuka nayi na juya na cigaba da baccina saboda safiyah bata wayeba sosai,dan dai yah ci sa'a bana rude kofa ne shiyasa yake shigowa yanda yaga dama.
Jeans da t-shirt nasaka sai kuma kimono dana ɗaura akai baƙi da mayafinsa.
Lokacin dana fito saleema tana gaba da zuhrah a akan cinyarta faruoq kuma yana gidan baya,sameer ne daya taho daga bayana yake magana.
"Ke wannan wane irin kayane,koh gidan kawarki bazaki je dasuba bare kuma wanda suke kaman a matsayin surukanki,dan su tamkar iyayena ne a garinnan".
"Kai suke matsayin iyayenka amma ba niba,ni bani da wasu surukai kuma ban shiryah yin wasuba,idan kuwa dole saina canja kayannan,toh wallahi bazanje na saidai na zauna,na gaji da wannan juyin,saikace zanje ganin Annabi."
Jijjiga kai yayi alamun na isheshi,hakan nakeso,wayace da aka daura masa ni baice ba zai iya ba,buɗe gidan bayan nayi inda farouq yake na shiga.
Yaron ne ya ɗago ya kallaeni fuskarsa dauke da murmushi yaca,
"Morning aunty"
Tun kafin nace wani abu,saleema tace,
"Idan kasake gaisheta sai na cire ma harshe,mai shegen surutu kawai,wanda yake gaisuwa ake gaisarwa,ba wanda bai san darajarta ba"
Sameer ne ya katseta daga maganar da takeyi,
"Ke saleemah bana son irin wannna halin,bai kamata ki dunga nunawa yaro hakaba,karna sake ji"
Maganar su suke tayi har muka zo gidan banyi saka musu bakiba.
Shiga mukayi cikin gidan,babbane sosai dan yah fi wanda muke ciki girma,dan jikin bangon gidanma abin kallone ga wanda bai taba ganin irinsa ba
Zama mukayi a kujerun gidan dukkanmu,saidai jin alamar sakkowa mutum daga daga samane naga sameer ya sauka daga kan kujerar a yah zauna a kasa,kallona yake da alamar nima nayi,a raina nace kana ruwa kenan,idan ni zan yi yanda kace.
Kara bude kimonon dayake jikina nayi tareda sake gyara zamana a kan kujerar yanda jeans din jikina zai dan fito waje.
Cize baki sameer yayi yana kallona cike da daya sanin tahowa dani,hmm wayace yah taho dani.
Dattijuwar matarce ta zauna a akan kujera fuskarta cike da fara'a,.
Muna hada ido da ita naji matar ta kwantamin arai duk da bansan mai yasaba,jinai bakina yah bude ina gaisheta bayan banyi niyyar hakanba.
Nikaina nayi mamakin hakan bare kuma mutanen da muka taho da su.
Yar magana kadan muka yi da ita sameer yah tafi,da niyyar zai zo daga baya yah daukemu,nidan shiru nayi in kallonsu,duk da banajin gidan ya isheni kaman yanda nakeyi idan naje wani gidan,abin yabani mamaki sosai,dan matar har ɗakinta ta jani,akan nayi sallah.
Kallonta nakeyi dan bansan mai zance ba,itama kallon nawa takeyi bayan ta shimfidamin sallayah,ita kuwa saleema tunda taga mahaifiyarta ta kukani,tayi fishi da mamar tata ta fi dakinta,da ubanta yadawo kuwa wajensa ta nufah.
Tun daga nan na kula ubantane ya sakaltata ba mahaifiyarta ba,dan daga idon mahaifiyatata ina ganin rashin jin dadinta game da halin y'ar tata.
"Uhm dama hajiyah ina period ne"
"Period kuma,amma bakiyi kama da mai period bah,danna karanci likitan matane,babu abimda bansaniba akan mata sai abinda baza'a rasaba. Saidai ban saniba koh bakya son yi ina nan ne"
Tana gama fadar hakan cikin murmushi ta fice daga dakin,bandakin cikin dakin na shiga jikina a sanyaye,dan babbban abinda duk duniyah bazan iyaba shine sallah,koda na nayi niyyar aikatawa nasan bazan iyaba.
Alwala nayi na fito zuwa inda sallayar take,kallonta nake kaman mai nazari kafin na dorah ƙafata akai.
Runtse ido nayi saboda jin wani abu kaman allaura ya huda kafata har zuwa cikin kaina,idona yana rufe nasake ɗaga ɗaya kafar nasake ɗorawa akan sallayar.
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎17~18💎
Cikin dauriyah dakuma san gwadawa nafara tada sallar,saidai bankai gayin ruku'u ba nayi saurin zama a wajen ina rike kaina,dan nasan yau kam bazanyu bacciba koda naso hakan,nasamu najima da fitinar boyayyun mutanen can.
Ina zaune a wajen mahaifiyar saleemah tah shigo dauke da wani kwano a hannunta,miƙomin tayi tareda cewa,
"Ƴata maza shanye wannan zai miki amfani kinji"
Girgiza mata kai nayi alamun banaso,mamaki hakan yabata
"Meyasa bakyaso,karki damu bamai cutarwane ba nice nake hadawa da kaina,sannan karkiyi tunanin zan cutar dake,dan wallahi har cikin rai na nakejinki tun lokacin da na hada ido dake"
"Nasan bazaki cutar dani ba,sannan nasan ba abun cutarwa bane,hasalima nasan menene kawai dai bana bukatar sa rayuwata ne,shiyasa"
"Kamanyah kenan,kina mace amma bakya gyara kuma"
"Ina gyara mana irinna wanka da wanki,saidai irin wannan gyaran dakike nufi nasan bazanyi shi a rsyuwar data ragemin sauraba,saboda wanda akeyi dan shi wato miji bana bukatarsa a rayuwata sam"
Zata sake wata maganar ne nayi saurin katseta ta hanyar cewa,
"Babu abinda yake hadamu dashi shiyasa"
Saurin daure fuska tayi lokaci daya kafin tace,
"Me saleemah tah aikata da har hakan ta faru"
,ƙoƙarin tashi take na dakatar da itah ta hanyar cewa,
"Babu hannun ƴar ki akan hankan,wanna zabina ne bana kowaba,kuma kiyi hakuri bazan iyah fadamiki daliliba,kawai ki dauka haka nake,sannan ki gargadi yar ki ta rage shiga harka ta idan tana son lafiyar ta a jikinta"
Daga haka na fito na bar dakin na zauna falo,dan hakan shine mafi saukina,narasa miyasa na yarda da matar har nake fadamata irin wannan sirrin,inaga idan muka dade zan iyah fadamata komai bansaniba,daga bay nazo ina nadamar hakan.
Ina nan zaune har sameer yadawo daga aiki yazo ɗakarmu,sallama nayi mata saidai yanzu babu murmushi akan fuskar matar,sai kallon tausayi da take bina dashi,shareta nayi tareda cewa ke ta shafa kuma,bazan sake dawowa gidannan ba gaskiya,duk da zuciyah ta tana son dawowa gidan koda kuwa a gobene.
Kwanaki sunja da tafiyah ta