Showing 51001 words to 53080 words out of 53080 words
Chapter 18 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt
kwanciyar hankali,babu aiki saboda weekend ne dan haka zama akayu a falo ana tadi.
Raba kwana akayi kwana bibbiyu kowa,anty Saleemah ce ta raba kuma mun yadda da hakan gaba dayanmu.
Ranar litinin na koma aiki saidai yanzu banice mai bada training siadai zaman office kawai,da farko naso kin komawa aiki amma yah sameer yabani kwarin gwiwa hakan yasa na koma da goyon bayansa.
A yanzu nayi kusan wata guda da warkewa daga ciwon dana ke fama dashi tsawon shekarun danayi a rayuwata,yanzu nagane cewa dukkan abinda yafaru dani ubana ne sanadi.
Ranar dana ji labarin nayi kuka sosai,abin ya girgizani matuka,kaman yanda kowane d'a yake samun gata daga ubansa ni kuma nawa ubanne yajefani matsala,yanzu na daina ganin laifin soyayyar da mahaifin saleemah yake bata,koba komai shi bai halakar da ita ba kaman nawa uban.
Tunda naji labarin abinda mahaifina yayi nakara ganin kimar mahaifiyata,fiyeda lokacin dana fara saninta a matsayin mahaifiyar tawa.
Yanzu rayuwarmu ta daidaita da irin kowanne rayuwar da take faruwa a gidan ma'aurata masu kwanciyar hankali.
Nida yah sameer mun saka lokaci sanda zanje zariya ganin gida,duk da banyi wani murna da zuwan ba amma kuma inason zuwa din.
Ana gone zanje ina ta shirye shirye a daki,saidai komai yinsa nake cikin dauriya,tun safe nakejin tashin zuciya zuwa dare kuwa nafara amai ba tsayawa lokacin da ya sameer ya shigo dakinma a bandaki nake ina ta kwarara amaai.
Shiryawa nayi muka tafi asibiti anty saleemah tana ta yimin sannu,ummee bata asibitin lokacin da mukaje wata ce ta dubani inda aka gano ciki a jikina mai kimanin wata d'aya da sati d'aya.
Nayi murna sosai sannan na girgiza da jin lamarij,lokaci daya rayuwata sai sanjawa take a hankali.
Gida muka dawo tunda babu wata matsala laulayine kawai shikuwa dole daurewa zanyi bar mu rabu da abinda yake cikina.
Daga tafiyata yah sameet yayi akan sai cikina yayi dan kwari tukunna,nima naso hakan dan kwata kwata jikina babu karfi,komai cikin dauriya nakeyi.
Lokacin dana tashi tafiya cikina yana da wata hudu ciff na kama hanyar gida kuma gidan gandu,wanda rabona dashi tun lokacin da aka kaini gidan ya sameer.
Abayace a jikina baka tasha duwatsu sai yane sai hijabi dana dora akai,dam yanzu shigata kenan.
Tare muka taho da farouq da akayiwa hutun makaranta.
Na Dade a bakin gidan a tsayae ina kare masa kallo,abubuwa da dama da suka shafi rayuwata wanda nayi a gidan suka fara dawomin dallah,hakika ko naki ko naso gidan gandu ya taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwata wanda bazan taba iya gogewa ba,shine gidan dana budi idona na ganni a cikinsa. Tunanin ummah hajara ne yadawo min cikin kaina,lokaci daya idona yafara zubar da hawaye dana tuna da uwata takaina d'aya tamkar da dubu,dai kuma mutuwar salma ma da ta dokeni ba kadan ba.
Dawowa nayi daga tunanin danake kafin na kama hannun farouq muka shiga cikin gidan.
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎49~50💎
Sallama nayi lokacin dana shiga gidan abinda ban tabayi ba kenan a kundin tarihina na gidan.
Inna Karima ce tsakar gidan tana diban itace,da alama wani abun zata dora,sakin baki tayi har yawu yana shirina zubowa da ta gane mai yin sallamr,bata amsa ba sai marabanku da zuwa da tace,
Dakin mu na yanmata a da na nufah,wanda yanzu yake a matsayin na su hanifa da kuma sauran yam matan da suke sa'anninta harda yayunta.
Kayanmu na ajiye a gefe nida farouq kafin na je iyo alwala domin nayi sallah.
Bayan na idarne naji maganar baba umaru shida farouq a bakin dakin,fitowq nayi muka gaisa sai albarka yake sakamin ganin nasan ja daga yanda nake a baya sosai.
Anan ne yake fadamin ai baba ramatu tama asibiti,tun cizon danayi mata a gidan malam kafarta ta rube tana rozayewa.
kunyar kaina ce takamani ganin abinda nayi mata lokacin dana ganta a gadon jinyar tats.
Aunty sameerah take tausar zuciyata dayaKe ita take wajenta,little salma tana bayanta tana bacci.
"Kidaina fadar haka sameemah,nayadda yanzu duk wanda yayi ba daidai ba tundaga duniya yake ganin sakayya,dan haka bana jin komai na haushinki a rai na,kema ai ba'a hankalin ki kike ba,ki daina daga hankalin ki kinga bake d'aya bace yanzu,akwqi wanda alhakin kulada shi yake kanki"
"Duk da haka anty sameerah abin akwai dimuwa a cikinsa,na manta banyi miki gaisuwa ba ,ya hakuri kuma"
"Hakuri yazama dole saidai muce allah ya jikan wanda suka rasu"
A sibitin na yini,inda umaruje dayazo kawo abinci ma inji hajiya mairo mukayi ta hirar yaushe gamo,little salma kuwa tayi bul bul da ita sanadiyyar kulawar da take samu a wajen ahalin gaba d'aya,koba komai naji dadin ganin bazatayi maraicin rashin uwaba,rashin uwa babu dadi nizan bada labarin hakan.
Kwana na uku a gidan gandu na zazzaga ko ina har gidan Surayyah saida naje,ba karamin dadi tajiba da ta ganni,dan ta yayi wayo dan harta yaye shima da wani cikin,sai tsiya nake musu akan zasu tara garke.
Har kyauyen su ummah hajara saida naje,suma sunyi farinciki sosai da samun lafiyata,musamman ma inna rabi sai tsokana ta take wai mai rashin kunya,sannan bata barin ta kwana,nidai Murmushi kawai nake mata dan ba sosai nake maida magana ba sai idan hakan yana da muhimmanci tukunna.
Sati guda na dawo garij porthacourt hakanma yah sameer sai kirana yaka wai ya ishemu haka,saida na d'an koma seemah jar wuya kafin ya sarara min.
Lokacin da muka isa gida anty saleema tayi mana girki muna zuwa muka sauka akai,sai tsiya take mana wai mun dauko gajiya,nidai ban kulata ba saida cikina ya dauka tukunna.
Lokacin da cikina ya kusa watan haihuwa koyaushe sai ummee ta aikomin da magani,wani lokacin kuma tazo ta dubani,nidai na zuba ido kawwi naji girif tukunna.
Cikin bayyi nauyi dayawa ba dan babau abinda yake hanani yi komai normal sao dan abinda baza'a rasaba.
Lokacin da abu yazo gaff kuwa da daddarene kowa ya kwanta amma ni ina zaune kaman mayyah,inajin haushin su blacky a waje sai kuma kukan kwari.
Tun ina daurewa amma naji abu sai gaba yakeyi,dukkan jikina rawa ya dauka saboda wani irin ciwo dayake shigata ta kowacce gaba ta jikina.
Wayata na lalubo da kyar na bugawa sameer waya tunda yau ba a dakina yake ba yana dakin anty Saleemah.
Ina jiyo hayaniyarsu lokacin da suka shigo dakin su biyu,sai kuma yah sameer dayake kiran ummee a waya yana fada mata abinda yake faruwa.
Dakyar na yunkura na tashi anty saleemah taba jan hannuna,saidai kafin nakai ka tashin naji wani ciwon yaketa marata hakan yasa nakoma na zauna,nishi na fara babu tsayawa yayinda naji abu ya tokaro daga cikina zuwa wajen marata,salati nake yi tareda fadar wani abun davan wanda nibansan ma mai nake cewa ba.
Kukan yaro naji a kasana hakan yasa na leka domin ganin mai yin kukan.
Jinjira ce wadda cibiyarta har sannan take jikina sai kuka take,ita sanann da zo duniyar bata san komaiba sai yanda akayi da ita tukunna.
Ummee ce tashigo da sauri,amma ganin yarinyar a hannun anty saleemah ga kuma mabiyya a gefe yasata sakin ajiyar zuciya tareda yin hamdala.
Kokartawa nayi na tashi domin na nufi bandaki,dan ba abinda nakesonyi a lokacin sai yin wanka sannan kuma na samu na kwanta,dannagaji sosai.
Aunty Saleemah ce ta biyoni bandakin ta hadamin ruwa mai zafi sosai,ina saka hannuna a ciki na cire da sauri tareda yimata kallon alamar tambaya,araina ina cewa anzo wajen.
Itama kallona tayi tana bata rai,ganin banida niyyar sake saka hannuna yasa ta fita sauri ta kiramin ummee wacce take gyara yarinyar dana haifa yanzu.
Haka ta tursasani ina tirjewa da komai saida na zuba wannan ruwan a jikina,gayyar bata fata da kuma zafin ruwa.
Lokacin da na fito har turiri nake na ruwan zafi,zama nayi a bakin gado ina kallon ummee tana yiwa yariyar wanka,abinne yabani mamaki wai ni nahaifeta a cikina,abinda ko a mafatki bana kawowa ko kadan sai gashi yafaru,kuma fah ina sonta sosai,dan gabadaya hankalina yana kanta taya zan bata farinciki na kulada ita naga bata nemi abu ta rasaba,ashe haka iyaye sujeji akan y'ay'an su.
Ina nan zaune har aka gama gyarata,ban zata ba saigani nayi ummee ta mikomin ita tana kallona,tubulbulcewa nayi tareda tambayar mai zanyi,
"Oh wanine zai shayar da ita bakeba?"
Karvarta nayi ina kallonta cikin sanyin jiki,towel din na same ina kallon ta inakallon maman,saita mata nayi a bakin ta kama,dan zafi saida na cije bakina,daga bayane dana naji zafin ya ragu.
Tun kwana uku da haihuwata gidan yafara cika da mutane,saboda al'adar dakan yaji.
Shikansa idan mutum yagani dauka zayyi sunan akeyi,anty saleemah ce ita da surayya akan komai sai shige da fice sukeyi.
Ranar da ta cika kwana bakwai da haihuwa aka rada mata suna HAJARAH taci sunan ummah mu,wanda ranar ma saida nayi kuka na koshi,musamman yanda yarinyar ta dauko wani abu irinna mahifinta wanda yake kama da ummah nah,bazan taba mantawa da ita ba.
Nida kaina na sakamata lakabi da ummulkhair saboda boye sunan,shikansa yah sameer ya ji dadin lakabin danayi mata dan ta cancan ci fiye da hakan.
** * *
Shekarata biyu da haihuwa nayi niyyar zuwa garin palastine wajen mu'allim da kuma shaheedah,sai kuma wajen ogah binlad danna san yana ta nemana har yanzu.
Tare muka tafi dukkanmu umarah,inda bayan mungama su hajiyah fatima da kuma anty saleemah suka dawo Nigeria nikuma muka wuce kasar palastine nida yah sameer da kuma Y'a ta ummulkhair.
A bakin kofar gidan mu'allim muka tsaya nida yah sameer wanda yake gefen prison din yara dana zauna a baya,shiga mukayi da sallama matarsa ta amsa,bude baki tayi dan da alama ta ganeni.
Gaisawa mukayi kafin ta kaini dakin mu'allim din wanda yanzu yah tsufa sosai karatu yake bayarwa a gida,dan tun randa na fada musu shugabansu yana munafurtarsu matarsa take fadamana yah daina zuwa kungiyar a gida yake karatu.
Shima lokacin daya ganni yayi mamaki sosai,saidai yayi farinciki ganin yanda na koma uwa kuma mata ta gari abar alfahari ga yan uwa musulmi.
A nan muka yini har dare kafin muka koma masaukinmu,washagari gidan su shaheedah naje,saidai mamanta tace tana kasar aurenta da yara hudu,sshaheed ne suke tare shima da matarsa da yara uku,ba wani gaisuwa sosai mukayi dashi ba dan ba shiri mukeyi ba.
Ogah binlad kuwa danaje inda muke zaune van samesu ba sai filin wajen kawai,bansan kuma wazan tambaya inda suke ba dan haka dole na ha kura watakil sunyi wani wajen daban.
Haka muka koma masaukinmu yah sameer yana ta yimin kallon alamun tambaya,shareshi nayi dan gaji sosai so nake na huta.
Muna zuwa na fada bandaki nayi wanka nazo na bi lafiyar gado,ina dosana hakarkarina naji kukan ummulkhair a falo,shareta nayi na kwanta dan yarimyar ta fiye fitina ba laifi.
Bankai gayin baccin na moreba naji yah sameer yans jijjiga kafada ta,tashi nayi na zauna ina lumshe ido tareda cuna baki.
"Menene kuma yah faru"
"Hhhhh uwata tayi kashi a tashi a gyara mata,kuma ma anyi sallah la'asar sannan ke kikacemin zamuje sha iska"
"Uhh haba yanzu ba dama na huta wai,naga kashin kaima zaka iyha wankewa"
"Kinga comon tashini kin faye bacci kwannan da kuma shagwaba baccin y is haka,kuma sonake ki bani labarin duk abinda yafaru dake a kasar nan"
"Naji dama nasan zaka tambaya,yanzu bari na gyarata mu fita tukunna"
Ta shi nayi babu yanda zamyi,kai rainoma babu dadi fah,ina yi mata wanka tana tirjewa tana rigima da haka na shiryata muka fita zaga cikin garin dan gobe zamu koma gida.
Mun dade muna zagayawa ina fadaasa wajajen da mukayi aiki wani lokacin a ganomu muyi ta gudu.
Dariya yadungayimin wai allah ya hada y'ay'an sa yar rigima da kuma daba,saida yaga naji haushi raina ya baci kafin ya daina yana bani hakuri,aikuwa yajawa kansa dan daina bada labarin nayi yayi ta tambayata amma nayi shiru.
A Gidan hajiyah fatima muka yada zango lokacin da muka dawo dan itama anty saleemah tana can,ana ta dariya wai na dawo da tsarabar kasar palastine na ciki.
Babu abinda zamuce sai allah ya barmu cikin sunnar manzon allah.
Alhamdulillah nasamu sauyi mai kyau daga duhu zuwa haske,allah yahadani da miji gwarzo mai sona da kuma bani kulawa,ga kuma abokiyar zama dana samu wacce bazata cutar dani ba koda a bayan idona.
Yanzu aiki na gaba shine yanda zanyi na inganta rayuwar gidan gandu daga rashin kyakykyawan muhalli da jahilci zuwa wayewar kai da kuma waje mai inganci.
Idan allah yana taimakonka ba abinda zai gagareka musamman idan kasamu gwarzon abokin rayuwa kamar yah sameer.
ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN.
Godiya ga allah subhanahu wata ala daya kawomu samun nasarar gama wannan littafin,allah yayi mana mai kyau da iyawarsa.
Sannan godiya ta musamman ga wanda suka bani goyon wajen
Daga taskar *sadi-sakhna* ______✍🏼