Showing 24001 words to 27000 words out of 53080 words
Chapter 9 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt
gun mai aikinta,ganin hakanne yasa nace su dawo nan shida itah su zauna,tunda a kwai wani dakin a wajen.
A kitchen din nasmaeshi yana tsaye,har na wuceshi sai kuma nadawo na ce,
"Menene naganka a nan wajen da wannan lokacin,akwai abinda kake bukata ne?"
"Eh aunty,uncle have muje makaranta da wuri yau akwai abinda za'ayi,kuma naga lokaci ya kusa gashin anty nanny bata tashiba"
Kama hannunsa nayi muka shiga dakina nayi masa wanka da brush kafin na aikeshi yah dakko kayan uniform din,da sauri yah tafi yana murna.
Kayan na saka masa kafin na zuba masa abinci yaci,na saka masa wani a cikin basket dinsa.
Tunda nafara sakawa yake tah murmushi ,lokacin dana bashi ma har yah tafi saida ya dawo da gudu yah rungumeni kafin yah juya da gudu yah fita wajen drivernsa.
Yau daya a rayuwata naji wani shauki wanda ban taba jiba yah soki cikin kirjina,saurin rike wajen nayi ina dan sunkuyawa,tambayar kaina nayi mai hakan yake nufi?.........
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎23~24💎
Fitar da tunanin nayi a raina na wuce dakina damin nima nayi nawa shirin.
Kayan sunyimin kyau sosai a raina naji dadi sosai,ganin nasake samun wani aikin a karo na biyu.
Lokacin dan isa wajen da masu training din suke duk ansaka su cikin sahu na layi.
Dama daga gani suna jiran isowata ne dan idon su duk akaina lokacin da major nazeer yah ke gabatar dani,shima ina kallon dan alamun girmamawa dayake min,wannan al'adar sojane nuna girma ga wanda yafika matsayi.
Babu Bata lokaci muka fara abinda yah taramu wanda muka aiwatar dashi a wani fili na koyon harbin,dukkansu kowa ka ganshi yayi laushi kaman an yimasa duka,saboda aiki dani ba sassauci,kallon mugunta nayi musu kafin nace kadan ma kuka gani indai nice mai koya muku abu.
Direct wajen masu koyon tracking da hacking na wuce bayan na gama da masu harbin,zasuje wani ma yah cigaba daga inda na tsaya .
Sai wajen la'asar sukam muka tashi,domin aikin dana basu ba karami bane,kuma da gangan nayi musu hakan dan su san ba wasa ne yah kawosu ba.
Ina is a gida na hada gumi shirkiff ,wanka nayi nasaka kananan kaya kafin dare kuma yayi nafara nasu blacky dan zuwa yanzu suma sunyiwa sauran karnukan barrack zaryah tun daga yanzu suna kanana,dan jikinsu haryah fara murdewa irin na karnukan manyan yan daba.
Idan muka gama training kuma na barsu a jije su kwana suna maimaici,wanda bayyi ba kuma yakarbi hukunci mai tsanani,sannan bana barsu su saba da kowane mutum,daga ni sai yaseer,sannan abinci su koyaushe nama ne saidai a sarrafashi tah hanya daban yanda zai kara karfafa jikinsu.
Fitowa nayi daga dakin na wuce kitchen na hado custard,dan bana bukatar abinci a lokacin,farouq ne yah ganni kasan cewar babu islamiya yau yana gida,mikamin kofi yayi yana min kallon dolly irinna yara idan suna son abu,karba nayi na zuba masa dam ba lallai na shanye shiba.
Komawa falon mukayi muna kallo,wanda ni hankalina ma baya kai saboda duk cartoon ne,sai anyi abune yake taboni ya nuna min,ko banganeba to nake cemasa kawai.
Muna nan zaune har aka kira magriba,kallonsa nayi nace,
"Farouq tashi ka tafi masallaci an kira sallah maza"
Cuna baki yayi bayason zuwa,amma yana kallon fuskata yah tashi da gudu yah fita zuwa masallacin.
Jijjiga kaina nayi kawai bayan na kashe kallon,dan idan ban kasheba yazo yah gani bazai je lessons din dare ba yau. Kuruciyah da daɗi.
Lokacin daya shigo gidan dakina ya shigo da gudu har yana tuntube,kallonsa nayi da takaici,badama baya son zama waje daya kullum cikin rigima yake.
"Yanzu farouq bazaka tafi a hankaliba kaman ana binka a baya?"
"Aunty yi hakuri,dama sauri nake karki tafi wajen su blacky kibarni tunda kince yau kam zanje koh?"
Shiru kawai nayi ina tunani,kusantuwa ta da yaron kullum kara yin gaba yake,ina tsoron kar hakan yajawo matsala idan iyayensa suka dawo.
Sai nayi niyyar yimasa fada sosai ko nesan tashi daga saikuma na kasa,saboda kama da yakemin da sameer haka ummah tah,sannan bayan wannan inajin yaron a cikin jikina sosai.
Dan sunkuyawa nayi na kama kafadunsa kafin nace,
"Suna cizo sosai sannan kaga dare yayi ka bari gobe sai muje da yamma idan ka dawo daga makaranta koh"
Daga kai yayi alamar yah amince,sai kuma yayi murmushi,gyara masa gadon nayi yah kwanta bayan na bashi chocolate din dare,duk dan kar yah biyoni,dan nanny dinnasa wani lokacin ba gidan take kwana ba tana wajen mazan sojoji,kuma wai ita suka bawa tarbiyyar yaronsu,dan sati guda kenan bata gidan.
Zuwa yayi yah fadamin akan yana tsoron kwana shikadai kullum,wanda nima na kula da hakan.
Tun daga lokacin na dawo da duk kayansa zuwa dakinnawa,shima dayaga hakan murna yayi tayi,ko yaushe sai yah shiga yah fita,wai yah zama dan dakina.
Tun daga lokacin idan na tashi nayi abin karyawa sai na tasheshi na shiryashi nima na shiryah,idan muka gama komai saina fito na kulle gidan shikuma na kaishi wajen mai kaishi makaranta.
Idan ya dawo kuma sai yaje inda nake bada horo mutaho gidan tare,idan nayi mana abinci muka ci,saina shiryashi cikin kayan islamiyyah bayan yayi sallah,duk da bana takurashi amma yah sani idan yah yi ba daidaiba ina horashi yanda yakamata,dan banason sakalci ko kiyuwa ko kuma raini ga wanda suka fishi.
Shi ma daya ga haka yana kokarin kiyayewa,koda ya manta yayi da sauri yake bada hakuri idan yah tuno mai zai biyo baya.
Yanzu nakan barshi yaje wajen su blacky shikadai bayan na tabbatar sun dan saba dashi bazasu cutar dashi ba,dan karnukan sun sanja kama zuwa wani abu mai hatsari ga duk wanda yah gansu,saboda zaman cikin jeji da kuma bada horo mai tsanani.
*****
Zuwa yanzu nasamu wata guda uku kennan da karbar matsayin mai bada horo a cikin bori camp dake cikin porthacourt barrack.
Na sauya abubuwa da dama a cikin haron daliban,ciki harda kara tsawon lokacin yin train,sannan banda wasa ko shiririta,yanzu na zamo kusan duk taro da za'ayi a cikin wajen toh sai an turomin takardar gayyata,wani nakanje wani kuma nace bazanjeba,dan haka suke hakuri dani,bana nuna respect ga kowa,dan wannan dabi'ar ita kadai na rasa a cikin aikin sojan,wato respect ga na gaba dasu.
Watarana ne ina zaune major nazeer yah kirani,nayi mamaki daya nunamin wani office an kawatashi wai nawane,sun bani alhakin kulada horon sabin sojoji,sanann kuma ga kudi da,suka bani mai yawa,wanda kuma zasu cigaba da biyana wata wata,kallon office din nake har da motar da take bakin wajen mai paint din sojoji,kuma wai tawa ce.
Biki akayimin na hakan ,wasu manyan sojojin daga wasu jahar ma saida suka hallara,musamman dasuka ga irin aikin danayi da kuma sabon salon horo dana kawowa barrack din.
Gaskiya nayi mamakin abinda sukayimin ban zata zai kai har haka ba,sai ganina nayi na daukaka lokaci guda an bani matsayin mai bada horo da kuma saka hannu cikin tsaron wajen,zan iya gyara duk abinda naga dama a kuma lokacin danake so.
Yanzu daliban dana yaye a cikin wata hudu gwarazan da suke cikin su sune suke gudanar da wasu ayyukan,ni yanzu banida time sosai,koyaushe ina office.
Farouq ne yah shigo office din da sauri yana narai narai da ido,kallonsa nayi naga har hawaye yakeyi.
"Menene yah faru ka dawo da wuri haka"
"Ba .....ba cikina ne yake ciwo ba"
"Wani Abu kaci ko,bayan na hanaka"
"Ahah anty"
Ajiye aikinnayi na kira yaseer ya karisa dan yanzu shine mataimakina,kuma nina bukaci hakan,mahaifiyarsa takanas tazo tayimin godiya.
Daukarsa nayi dannaga harda sakalci yau yake ji daga gani.
Gida muke je na ajiyeshi a bakin gado,bandaki na shig na hada masa ruwan wanka,lokacin dana fito har yah cire kayan makarantar,koh magana banyimasa ba yah shige bandakin,dan zuwa yanzu babu abinda bai saniba na dokokina basai na fada da bakiba.
Fita nayi na hada masa abinci. Kallonsa nayi lokacin daya fito daga dakin sanye da gajeren wando irinna sojoji da kuma farar T-shirt.
Mika masa abincin nayi,yana karba yace,
"Nagode ummah"
Saurin kallonsa nayi jin sunan daya kirani dashi,daga haka bai sake cewa komaiba har muka gama cin abincin yah fita zuwa gidan major nazeer wasa,dan tanada son yara.
Har sannan kalmar mommy bata daina yawo a cikin kaina ba.
A satinne na kira meeting kan cewar bai dace ace an saka kaso na sojoji a bakin wani gida kawai dan tsaro ba,sannan kuma kamata yayi ace sojoji guda biyu a kowanne gida,shima kuma za'a dunga sanjawa wasu su tafi training wasu kuma suje wajen iyalansu.
Cikin saurin bukatata ta karbu dan hakan shine yah fi,a kofar gidanmu kam,duk sallamar su nayi nasaka iyah guda biyu da rana,idan dare kuma yah yi su blacky ne suke tsaron bakin kofar,ko kafi uwarka kokari baka isa ka wuceba sai sun baka dama,shima sai na yadda tukunna,ta hanyar ganin hotonka a camera kofar gidan,idan na yadda zan kunna green idan ban yadda ba sai na danna red,toh dole ka juya badan kanaso ba.
Tun daga wannan lokacin farouq yakoma kirana da mommy,dan a cewarsa yanzu babu wanda yake kuladashi saini,nima banyi kokarin hanashiba dan yanzu yaron ya shiga raina sosai.
Washagari da safe aka bada sananrwar dawowar general musa daga jinyar yarsa daya tafi yi a kasar Germany,hmm abin ma ba tsari ko kadan,tun wata biyu da zuwansu ta warke amma tace baza ta dawoba sai anyi mata aikin fata an cire duk tabon zanen bulalar dayake jikinta,wannan ne ya daukesu har tsawon wata hudu acan.
Nikuwa naji labarin dawowar tasu amma babu abinda nayi a ciki,tashi nayi kamar kullum na shirya farouq zuwa makaranta,nima na fita nawa aikin,a hanya duk sojoji sai sara min sukeyi,dayake yawancin dalibaina ne dana yaye wata uku da suka wuce,sannan su san bana wasa sanann bana mugunta ko zaluntar wani,da haka na kankaro mutuncina a wajensu.
Yau ban tashi da wuri ba,dan farouq ma daya dawo daga makarantar safe anan na bashi abinci yaci yah kawanta,sai la'asar tukunna na sabashi a wuyana zuwa gidannamu.
Dan zuwa lokacin nasan su yah sameer sun dawo,kuma da gangan na ki dawowa da wuri duk da nasan tahowar wajen azahar zasuyi.
💎*sameer a madubin gani*💎
Tun jiya da akacemin zamu taho nakejin kamar nayi tsuntsuwa,babu yanda nayi haka na zauna a kasar badan komaiba sai dan kar na taho ace matata ce tayi mata illah amma na barta na tafi,haka badan nasoba mukayi tsawon wata hudu acan.
Kusan karfe daya dadai muka iso Nigeria,itah dama direct wucewa sukayi gidansu,nikuwa wani sojane ya dawo dani gida,tun karfe biyu nake tsaye a bakin kofar gidana amma bahu sameemah ba alamunta,ina taje oho bansaniba.
Har naje sallahr la'asar nadawo ina tsaye kenan na hango wata mace ta dosoni da kayan coach a jikinta,abinne yaban mamaki yau she aka samu mace mai bada horo kuma,ni kadai na tambayi kaina.
Ga kuma duk Wanda tayi karo dashi sai yah bata girma kaman wata general.
Saida tazo tab dani naga ashe sameemah ce,dan tsabar mamaki kasa cewa komai nayi,ga kuma farouq a wuyanta yana bacci.
Wuceni tayi ko magana bata minba ta bude gidan,danji komaiba dan dama ban yi tunanin sun gaisuwarba ko kuma maganar.
Bin ta nayi a baya bayan ta bude gidan,sai kuma naga ta nufi dakinta da farouq din a wuyanta,nima binsu nayi dannsan nawa dakin bazai shiga ba saboda kura.
Sanda nashiga dakin har farouq ya tashi ita kuma ban sameta ba tana bandaki,kallona yayi da mamaki sai kuma ya rungemeni da karfi yana dariyah.
Karar budewar kofar bandakice tasa shi sakina da sauri yana ja dab baya,sai kuma ya dan sunkuya tareda cewa,
"Barka da hanyah daddy ka dawo lafiyah?"
Dan Mamakin Sabin halin dana ganshi dashi ma kasa magana nayi,bai jira amsata ba yah juya wajen sameemah wanda take rike da hannun kofar bandakin.
"Kiyi hakuri mommy bazan kara haka ba"
"Apology accepted"
Tana fadan hakan ya tafi da gudu yah wuce bandakin ta hanyar data bashi a kusa da itah.
Wajen kaya ta bude a kusa da nata inda naga kayan farouq a ciki an gogesu.
Wasu riga da wando ta fitar marasa nauyi sai kuma tah fesa musu turare kadan ta ajiye akan gadon.
Fita tayi zuwa kitchen inda nima na bita a baya,amma ko kulani bata yi ba.
"Yanzu sameemah ko ba magana babu bare sannu da dawowa"
"To mai kakeso nace maka,tunda gaka kadawo ai na ganka ko tunda ba makahuwa bace ni"
Hmm kawai nace kafin na dawo falo na zauna ni kadai ina tunani amam narasa na menene.
Can Bayan wani lokaci farouq yah fito da sauri bayan yah saka kayan da ta fitar masa dazu,a hankali ya shigo falon kafin yah samu waje a kusa dani yah zauna sai murmushi yakeyi idan muka hada ido.
Nima Murmushin nay masa kafin nace,
"Yaushe yaron daddy yayi hankaline haka uhm?"
Bayyi magana ba sai murmushi kawai dayake yi,muryar sameemah ce daga cikin kitchen tana kiran farouq.
Da sauri yah tashi yana cewa ganinann mommy.
Plate ne a hannunsa na abinci yana zuwa yah ajiye min a gabana,sannan yah koma kitchen din da sauri yah kawomin ruwa a jug da kuma cokali.
Wannan karon tare suka fito shida ita tana rike da wani plate din a Han nun ta.
A jiyewa tayi a kasan carpet din da cokali biyu a ciki sannan kuma da kofin ruwa guda biyu.
Har yah zauna a daya gefen tace,
"Jeka canja tashar nan zuwa taka"
"Toh"
Remote ya dauka ya maya zuwa tashar yara mbc 3,daga wrestling din dana kunna.
Ɗaukar abincin nayi ina ci,saidai rabin hankalina yana kansu sameemah yanda suke cin abinci,da kuma yanda yake diban abinci a gabansa a hankali yana kaiwa bakinsa,yaushe ya,sauya daga yanda yake zuwa haka oho,sannan ina nannyn sa take shima oho.
Mai aiki na kira daga bangarensu dan su sharemin dakina ,ita kanta dana kirata saida tayi mamaki,daga gani sun dade basu shiga sashenba.
Har na saleemah ta gyara tsaf kafin tazo ta fita,zuwa lokacin ana magriba.
Kama hannun farouq nayi nace,
"Abban zo mu tafi masallaci tacan muje dauko mommynka"
Saurin zame hannunsa yayi yana kallon sameemah.
"Zaka iya tafiya amma iya yau kawai,hakan ma kuje da abbannaka ka fada masa yau ba karatu"
Muna fita na tambayeshi menene,
"Uhm uncle ne mai yimin lesson,amma sabone dan ummah tah kori wancan din tun ranar data ga yah kun na min waka muna ji,yanzu uncle yaseer ne yakemin,ummah take biyansa,tace idan ban jeba yah zaneni,sannan kuma tace idan an ce nayi abu banyiba ya fada mata"
Muna cikin tafiya a hanyar mu ta zuwa gidan su saleemah yana tamin tadin abinda yake faruwa ,jijjiga kai kawai nayi tareda Mamakin hali irinna sameemah,yamzu a yanda take zata iya bawa wani tarbiyya amma kuma idan ita ce bazatayi ba koh?.
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎25~26💎
Lokacin da muka shiga cikin gidan ma suna zaune a falo har da abokananta,sakin hannuna yayi yah tafi wajen hajiya fatima da gudu,dan ko ta kan saleema bai biba,ita ma bata wani kulaba sosai.
Gaishe da hajiyah fatima yayi kafin yah je wajen saleema ya gaisheta da kuma yimata yah hanya,har da abokannata,dukkansu tsayawa sukayi suna kallonsa da mamaki kaman yanda nayi a baya.
Wata ce daga cikin matan ta fito da chocolate ta bashi,bai mika hannu ba said jijjiga kai da yayi.
"Ummah ta hanani shan chocolate,da tana siyamin amma daya sakani ciwon ciki shikenan sai ta daina bani saboda da muka wsjen likita cewa yayi ta daina bani chocolate,kuma tace ko an bani kar na sha"
"Wacece ummah taka wacce bansan ta ba"
"Anty sameemah nake cemata amma yanzu nakoma cemata ummah"
Wani ashar saleema ta ruga tareda mikewa tsaye ta kamo farouq a hannunta,
"Dan ubanka ita ta haifamin kai tayi zafin nakudarka da zaka cemata wata ummah ina raye da raina,iyee wato ta lahantani ta turani neman magani kai kuma ta mallakeka ko saboda taga bazata haifi nata ba "
Hajiyah fatima ce tayi saurin fincike yaron a hannunta har yah fara kuka,sannan ta fara mata fada,saidai babu alamar fadan yana shiga kunnenta.
Share masa hawayen take tareda tambayar sa meya faru,cikin kuka yafara cewa,
"Ammee ba ita tace na dunga cemata ummah ba nine na fadamata,saboda lokacin da nanny take barni nikadai na kwana a daki da daddare sai da safe ta dawo itace ta maidani dakinta take kwana dani,kuma kullum take shiryani zuwa makaranta da wuri,idan na dawo ta bani abinci sannan ta kori mai yimin lesson saboda baya min karatu ta daukomim wani,idan banida lafiya ta kaini asibiti,har kudin makaranta ta da aka ce na kai ina gani da kudinta ta bayar na albashinta,dan a gabana tayi waya tace su biyata kudin zata yi wani abu dashi,da muka je makarantar tabiyamun sannan ta tari mai mashin ta dawo gida.
Koyaushe ita take kuladani tunda kuka tafi,da nanny ta dawoma korarta tayi da daddare,banyi bacci ba ina ji tana ce mata wai,ta sallameta bazata bari ta bata tarbiyyata ba ta tafi can wajen sojojin da take zuwa wajensu,kuma ammee...."
Yah isa haka farouq duk munji mai kace sannan nasan da gaske kakeyi,shin kanason cigaba da zama a wajen ta?"
"Eh ammee zan zauna a wajenta mommy kuma ta rike zuhrah"
"Toh shikenan a wajenta zaka cigaba da zama idam har abbanka ya yarda"
Jiyowa yayi yah kalleni na daga masa kai da sauri,har saleema zatayi magana hajiya fatima ta zefa mata wata harara,da sauri tayi shiru.
Da muka tashi dawowa harda hajiyah fatima muka dawo wanda alhaji musa yah tursasa mata akan sai taje tayiwa sameemah gargadi.
Bayan mun shigo hanyar gidan muna zuwa saitin gidannawa gurnanin wasu abubuwa suka doki dodon kunnenmu,kallon saleemah nayi wanda itama ni take kallo lokacin da wasu hallotu masu kaman zakuna suka bayyana a gaban mu.
Farouq ne dayake gidan baya yah bude yah fita da sauri lokacin da muka tsaya a gabansu a bakin kofar gidan.
Nima fita nayi da sauri domin taro shi kafin suyi masa illah,saidai ban karisa fito da kafata ba naga yah tsugunna a gabansu sukuma suna shinshina shi.
Ina karisawa kusa da su daya yah boyeshi a bayansa dayan kuma yana min gurnani na alamar karna kariso.
Dariyah farouq yah tuncire dashi kafin yace,
"Daddy barin naje gida na danna muku alamar bada damar