Showing 39001 words to 42000 words out of 53080 words

Chapter 14 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt

05 Nov 2024

13056

ciki zai shiga damuwa,shiyasa nake toshe duk wata hanya dana san zai gano wane hali na ke ciki.
Madubi na kalla inda naga bakin abu kaman jijiya yana bin wuyana,zaro ido nayi dan ban taba kulada shi ba sai yanzu,hoda na dauko mai kalar jikina na shafa a wajen,domin boyewa kar wani yagani,kawar da damuwar data shiga cikin zuciyata nayi kafin na fito zuwa office.
Har nayi hanyar zuwa asibiti wajen doctor maryam ta dubani sai kuma wani tunani yazomin,ida naje mai zance mata,sannan idan ta duba bata komai ba nan ma mai zance?,da haka na juya cikin sanyin jiki na wuce wajen aikina.
Dakyar na bari lokacin tashi yayi na koma gida,saboda haka kawai banason naga mutane suna matsowa inda nake,gani nake kaman sudin ba jinsi na bane,kuma wannan yanayin ya farune saboda shigowar sabon wani shedani zuwa jikina a daren jiya da daddare.
Ina shigowa gidan na samu saleemah a zaune,sannu da dawowa tacemin cikin magana kasa kasa,duk da najita amma ban kula ta ba,ina shiga daki nayi wurgi da jakar hannuna ina huci ni kadai,nasan wannna abu danake ji kuma nake aikatawa bani bace,amma babu yanda zanyi inaji ana iko da jikina.
Washagari ban je aikiba saboda munyi da yah sameer zai kaimu wajen doctor maryam mu yini,haka kawai na tsinci kaina da jin dadin maganarsa,dan ba kadan ba matar take birgeni sosai.
Tun safe mukayi shiri nida saleemah,dan ina kulada itah bata so aka ce da ni za'ajeba,duk da wani abu baya hadamu na kiyyaya haka ma babu Abu na so dayake hadani da ita.
Lace na saka milk mai adon chocolate,sai kuma nasaka gyale kalar adon lace din,dan a rayuwata banason saka hijabi duk da a ina da bukatar yin hakan,da gangan wasu kuraje suke fitomin wanda nasan ba na allah bane.
Sai da mukayi dan tafiya kafin muka isa,kasancewar gidanta yana da dan nisa da inda muke ,duk da tana da gida da aka bata a barrack din amma tafison zama a nata gidan.
Shiru gidan babu motsi kaman babu mutum a gidan ,shiga mukayi da sallama cikin gidan,wata yarinyace bazata wuce shekara sha biyar ba a falon tana rubutu,da alama assignment takeyi.
Dagowa tayi ta kallemu tanayi wa farouq murmushi,shima sunkuyar da kai yake da alama yasanta .
Gaishemu tayi a hankali said kuma tashiga cikin daki domin kiran doctor maryam din,itama saleemah bin yarinyar tayi zuwa cikin gidan.
Nikuwa ganin nikadai ce a tsaye yasa na koma kan kujera na zauna,shima yah sameer din zama yayi kaman da alama zuwansa na farko gidan kenan .
Idon nane yakai kan wani hato dayake rataye a falon,kallon yah sameer nayi da sauri wanda shima idon sa yake kan hoton,da alama yaga abinda nagani.
Tashi nayi zuwa gaban hoton kafin na maida kallona zuwa kan sameer wanda shima ya zare ido cikin mamaki.
Muna cikin hakane doctor maryam tashigo falon hannunta rike da na farouq,kallon mu take da mamaki ganin munyi cirko cirko bama cewa komai .
Nice hannuna yana rawa na nuna hoton ina kallonta amma kuma na gagara furta ko kalma daya daga bakina.
Murmushi tayi irinna manya kafin tace,
"Lah wannnan hoton mai kuma yah faru naga kina mamaki wasu masu aikina ne wanda nake jinsu kaman yan uwana wani abune yah faru"
"Ahah kawai dai nasan na jikin hotonne amma bansan ya akayi hotonsu yazo nan wajen ba"




Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150


Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.


💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎










*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*




💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}








💎37~38💎


"Hmm dolene hotunansu yazo nan wajen,kuma duk inda nake ma hotunansu zai zo wajen.
Sudin mutanene da bazan manta dasu ba a tsawon rayuwata,saidai bansan a ina zan sake ganin su ba,hakan yasa na dauki hotonsu da muhimmanci har nake tunawa dasu a rayuwata,amma naji kince wai kinsansu a ina kenan?"
Sunkuyar da kaina nayi a raina ina cewa,kar ko abinda nake Tunani yakasance gaskiya,kallon yah sameer nayi wanda shima idonsa ya nuna alamar hakan.
"Su din iyayenmune nida yah sameer,ummah hajara ta rasu inada shekara goma a duniya,baba umaru kuma yana gida"
Tashi tayi tsaye tana kallona,kafin kuma tace,
"Inalillahi was inna ilaihi raji'un, Hajara ta rasu?kincemin ke yar tace shin ta kara haihuwa ne bayan mun rabu,kuma baga sameer ina mijinkine"
Yah sameer ne yakatse maganar mu nida doctor maryam ta hanyar cewa,
"Shin kece hajiya maryam da baba umaru ya bamu labarin yayi aiki a gidanki a garin bauchi shekarun baya da suka wuce?"
Daga kai tayi da sauri kafin tace,
"Eh tabbas nice wanda muka zauna da su a gidana dake garin bauchi"
Dan tsabar kaduwa bansan lokacin da na zauna a wajenba,kenan doctor maryam mahaifiyatace ,kuma nida saleemah yan uwa ne kenan,mahaifiyarta yayar mahaifiya tace,wannan wane irin al'amarine haka.
Dago da kaina nayi ina kallon doctor maryam wanda itama take bina da kallo,sameer ne yasamu damar cewa wani abu bayan dukkanmu munyi shiru.
"Indai da gaske kece wacce baba umaru ya bamu labari to ya tabbata kece mahaifiyar sameemah wanda take zaune a gabanki a halin yanzu"
Sakkowa tayi daga kan kujerar da take ta matso zuwa kusa dani,har numfashinmu yana bugar na juna,hannunta tasaka ta rungumoni zuwa jikinta wanda yake rawa kar kar,
"Kece sameemah meyasa ban dago sunan ba bayan nasan sunane da ba'a cika jinsa a gun wasu ba,tabbbas kece kam babu tamtama,allah sarki kawata ta kaina hajara itadin mutumce mai wuyar samu,hakika ba karamin babbar ni'imace ba dana hadu da ita,nasan ko ban tambaya ba tayi miki rikon da koni iyakaci kenan"
Dagowa nayi daga jikinta duk da ban ki mu shekara a haka ba saboda wata sabuwar nutsuwar da take shigamin,saidai dolene na yi mata tambayoyi na dalilin bayar dani ga ummah hajara da tayi, bakina yana rawa kaman bazai budeba na ce,
"Amma in da gaske kece mahaifiyata kuma kina sona kaman yanda na gani a cikin idanunki, mai yasa kika rabu dani kika raba rayuwata da taki a lokacin danake tsaka da bukatar kulawarki"
Lokaci daya daga gama jin tambayartawa yanayin ta ya sauya gabadaya,hawaye yana zubowa daga idanunta kuma tana jijjiga kai.
"Ban rabu dake dan son raina ba,sai dan tseratar da rayuwarki sameemah,kuma har yau bana nadamar yin hakan,amma kiyi hakuri bazan iya fadamiki dalilin ba,banida ikon yin hakan"
Kallon ta koma kan sameer wanda yake goge hawayen tausayinmu nkda ita,
"Tabbas kam kai dan kawata hajarane dan ga kamar tanan a fuskarka,duk da ban taba ganinka ba amma nashajin labarinka sosai a wajen ta,fatana allah ya jikinta da rahama,sannan allah yasa halinta ya bita,yanzu kutashi mutafi wajen yaya fatima tukunna"
Daga haka ta mike daga tsugunnen da take kafin ta kama hannun sameemah wanda har sannan kanta yake sunkuye.
Dukkan mu gidan hajiya fatima muka tafi,cikin motar babu wanda yake cewa komai,saidai lokaci zuwa lokaci muke hada ido da saleemah,wanda said ta kawar da kanta kaman mai kunyar wani abu.
A falon muka sameta tana kallon news hankalin ta gaba d'aya yana kai,dan ko sallamar ma bataji sosai ba.
Kallonmu take da mamaki ganin mu har da doctor maryam sannna kowa fuskarsa tana dauke da wani abu daban.
Hannuna ta kama zuwa gaban hajiya fatima kafin ta kama nata ita ma ta rike,
"Yaya fatima kinga sameemah na ganta,saidai mahaifiyar tata wanda na bata ita ta rasu ,bansamu damar ganinta a karo na biyu ba,saidai nayi ta mata addu'a a kullum,dan ta nunamin kauna haka ma ta nun aw a jikina tsakininta da allah,tunda har ta raineta sannan kuma ta hada ta d'anta aure,babu abinda zan iya saka mata dashi yaya fatima"
Kuka take sosai wanda nake jinsa har cikin raina,ban san meyasa ba amma kukan sosai yake taba cikin zuciyata,hannuna na kai zuwa bayanta na dafa duk da bakina yagaza cewa komai.
Its kanta hajiya fatima bata ce komai ba sai tsshi da tayi ta nufi dakin ta tana cewa,
"Bari na Kira alhaji tukunna,dan maganar ba tawa bace ni kadai,yazo ga y'ar amininsa a raye bata mutuba kaman yamda muke zato"


Bayan kamar awa d'aya kowa yah hallara a falon,har da matan da nayi musu gargadi farkon zuwa na gidan sameer,ashe suma kannen mahaifiyata ne wanda suka uba daya,kallona suke da alamar sun ganeni,yayinda nima din nake kallon su din.
Alhaji musa ne yafara gyaran murya kafin yace,,
Toh hakika wannan abin mamakine,ashe muna zaune da y'ar mu har tana kishi da tamu y'ar amma bamu saniba said yanzu,babu abinda zumuce said yiwa allah godiya.
Sannna kuma zamuso jin ya hakan ta kansace kafin asan yanda za'ayi"
Nidai banyi magana ba har yah sameer yagama basu labarin rayuwata a gidan gandu tundaga farko har karshe,kama daga labarin zamana a palastine da kuma zamana a kasar Brazil,har da yanda aka sha fama dani a akan aurensa na ki amincewa,siada aka cemin wasiyyar mahaifiyata ne tukunna.
Abu d'aya ne naji dadinsa daya boye sirrina na halittata bai gada ba,hakan yayimin dadi sosai,kuma yasa nakara yarda da sameer fiyeda yarda da nayi masa a baya.
Lokacin daya gama bada labarina babu wanda bai yi ta'ajjubiba,hajiya maryam kam harda kukanta wiwi wai ta tausayamin,nidai ban dau tausayin a matsayi sosai ba tunda ta barni ta tafi.
"Hakika gaskiya munyi mamakin yanda ta sameemah ta rayu a wajenku,sannan kuma bamu da bakin godiya akan hakan,dolema said munyi shiri munje har wajen Malam umaru munyi masa godiya bisa namijjn kokarin dayayi akan rayuwar ita sameemah.
Duk nan mu yan uwantane ga hajiya fatima mamar saleemah,itance yayar mahaifiyar ta wanda suke uwa daya uba daya,sai hakiya delu kanwarsu ce itama ,saikuma hajiya bebi itakuma kanwar mahaifinki ce wanda shikuma amininnane da muka tashi tareda har girma,zamane ya kaishi garin baushi a lokacin baya.
Toh haka kaima sameer dama kai dan gidane sannan faruwar hakaan tasa munakara yarda dakuma son jawoka cikin danginmu,kuma gashi kana auren wa da kanwa.
Dama saleemah tun suna yara ta girmi sameemah da shekara hudu,dan haka dama yayrtace,to a yanayin zamansu cikin gidanka ma tarigata shiga,dan haka idan wata matsala ta faru kar wani yaji kunyar zuwa yah tunkatemu a cikinku.
Abinda akayi a baya kuma a sai a yayyafe,musamman ke sameemah da na nuna sonkai akan lamuranki har hajiya fatima tana nusar dani,ashe bansaniba kedin Y'a tace kema,wanda zan iya komai dan samun farin cikin ki.
Dan lokacin da maryam ta zo gida duk jikinta faca faca babu wanda baiji tsoroba ,mun tambayeta tace ta bada ke ga wasu Wanda ta yarda dasu,tun daga wannnan duk tambayar da mukayi mata bata bada amsa,idan muka takurata ma said ta birkice sai an dade ta dawo hayyacinta.
Tun daga wannan yanayinta ya sauya,kullum tana zaune ita kadai,bayan an debi shekarune ta ce zata koma karo karatu India,ban hanataba saboda a ganina zata samu nutsuwa,daga haka ta tafi karo karatu,da ta gama ma tayi zmanta a can tana aiki,sai yanzu allah yayi dawowarta da rabon zata gamu da y'ar ne ashe.
Daga haka aka fara hira kowa yana fadin albakrkacin bakinsa,nidai shiru nayi amma a labarin da aka baya akwai abinda babu shi a ciki,tambaya nayi wa akaina cewa,toh ina mahaifina,me mahaifiyata ta gani da har ta zabi a rabuwa dani a lokacin danake da kananan shekaru,sanann me yasa take shiga firgicin idan anyi mata maganar meya faru? Ko ita ma bazata iya bada labarin halin da take cikiba kaman yanda nima bazan iya bayarda labarin ba,kenan haka take yamda nake nima?,kai anya kuwa?.
Wannan amsoshin banida su sanann bansan waye zai bani amsoshinsu ba a halin yanzu,kuma koma menene ba shakka suna da alaka da yanyin halittata danake ganin ta sha banban da ta sauran bil'adama.
Sallah aka fara kira ta azahar inda kowa yah tashi domin yin sallah,bin hajiya maryam nayi a baya wanda take a matsayin umma ta yanzu,domin naga shin itama bata iya sallah kamanni ko kuma ita tanayi.
Dakin babu kowa sai motsin ruwa da alama alwala takeyi,zama nayi a kan gado har ta fito murmushi kawai tayi min da muka hada ido nima na mayar mata.
Hijabinta ta gyara ta tada sallah har ta gama ta fara addu'a ina zaune,mamaki abin yaban ganin tana sallah ta normal babu abinda ya sameta,nikuma bana iyaww,to ni da ita ba iri daya bane,wa na iyo kenan idan ba ita bace.
Juyawa tayi ta kalleni,saida tayi magana kafin hankalina ya koma kanta.
"Ina sallah zakiyi,kije kiyi alwalar mana ai na idar"
Uhm kawai nace nasake zamana,
"Period kike kenan?"
"Uhm "
Ina jin dar dar na fada mata hakan,saboda kar naje ta ganoni kaman yanda hajiyah fatima tayimin.
Daga haka dagani har ita babu wanda yasake cewa komai har lokacin tafiya gida yayi.
Yah sameer ne yazo daukarmu amma sai alhaji musa ya dagatar dashi ta hanyar cewa,
"Major in a ga da ka barta taje gidan ummah koda sati d'aya tayi kafin ta dawo dakinta,hakan ina ga zaisa su fahimci junansu koda kadanne"
Jijjiga kai yayi alamar ya yarda da maganar alhaji musan,amma nikam ban so hakan ba saboda banason zama sa mutumin da zai dunga ganin mai nakeyi,shiyasa naji dadi da dakina nikadai nasan mai nake aikatawa a gidan sameer.
Murmushi hajiya maryam tayi alama taji dadin hakan sosai,dan daga gani tana so na dunga zama kusada ita.
Hakan kuwa akayi ina zuwa gida na hada kayana da safe yah sameer ya ajiyeni a kofar gidan hajiya maryam,farouq kuka ya dunga yi akam sai mun tafi tareda shi,hakan kuwa akayi inyaso sai driver ya dunga zuwa yana daukarsa a can,nima dama bazan ji dadin barshi din ba,saboda mun saba kwana tare.
Lokacin danazo fitowa ciki ciki Saleemah tayumin a dawo lafiya tareda cewa na gaida hajiya maryam,nima daga mata kai kawai nayi.
Ina Shiga Gidan na samesu a zaune,yarinyar da muka samu a gidanne rannan tazo da gudu ta karbi akwatin hannuna tareda cewa,
"Aunty Sannu da zuwa dama ummee tace zakizo ki zauna damu"
Murmushi nayi mata tareda cewa,
"Eh hakane amma sati d'aya zanyi kawai"
"Ayyah duk da haka naji dadi Sosai"
"Toh humairah kai mata akwatin mana sai ki dawo ko"
Saurin jan akwatin tayi farouq yana binta a baya.
"Ina kwana ummee"
Nafada domin kama sunan da yarinyar da ta kira da humaira take fada mata.
"Lafiya kalau sameemah,ya mijinki da kuma yar uwarki"
"Duk lafiyar su kalau"
"Mashaallah barkan ki da zuwa to,bari na gama kawo abincin dama yanzu na gama"
Binta nayi kitchen din domin dakkowa abincin,hira muka dan farayi saidai duk akan zaman da tayi dasu baba umaru take fadamin,wani lokacin idan ta tambayeni na bata amsa,wani kuma na daga kai kawai,dan harga allah nakasa sakewa da itah duk da ina da bukatar hakan.
Hakadai zamannamu ya cigaba da tafiya,har nayi kwana uku a gidan,zuwa yanzu nafara sakewa da ita muyi hira,saidai har yanzu bata fadi abinda nakeson tayi magana akaiba shine mahaifina,nikuma na kasa tambayarta hakan, duk da shine abinda ya tsaya min a raina.
Ranar ta hudu danayi a gidan muna zaune muna kallo ,duk saina jini wani iri saboda bana zuwa wajen aiki,kiran sallah ne ya doki cikin kunnena,humairah ce ta shiga dakinta domin yin sallah,ummee ce take kallona taga ko zan tashi amma babu alamar yin hakan,
"Sameemah har yanzu kina period ne?"
"Eh ina yi"
"Bakiyi Kama da mai period ba sameemah,dan tun a farko na gano hakan amma na zubamiki ido kawai,meyake faruwa da bakya sallah kina matsayin musulma kuma hakan bai dameki ba,kina tunanin hakan zayyi miki kyau barekuma wanda kike tareda su,meyasa bakya sallah sameemah,sannan kuma bakiyu kama da wanda bata da ilimi ba,menene yake faruwa?"
"Akwai abinda yake faruwa ummee,saidai idan har zaki iyah fadamin ina mahaifina yake,sannan kuma manene yasa kika badani ga ummah,kuma meyasa kike firgicewa idan aka tambayeki mai yake faruwa,to nima zan iya fadamiki dalilin dayasa banayin sallah"
Lokacin danayi maganar mun kai wani lokaci amma babu wanda yayi magana a cikinmu,kowa yana zullumin abinda ke cikin zuciyarsa.
Tashi tayi cike da damuwa ta wuce dakinta,ina nan zaune humaira ta zo falon tana cemin naje ummeee tana kirana.
Ina Shiga na same ta a zaune da carbi a hannunta,gabana ne ya buga dan ba abinda nake tsoro ya carbi,tun horon da mu'allim yayimin dashi,tambaya nayiwa kaina cewa mai take shirin yimin dashi to.




Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150


Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.


💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎










*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*




💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}








💎39~40💎




Hannu ta dagamin alamar na zo,cikin sanda na kaman wanda kwai ya fashemin a ciki na isa wajenta na durkusa.
Hannuna ta kama dukka biyun kafin tace,
"Duk da bansan wane hali kike cikiba amma nasan abin akwai wahala,saidai ina so ki sani duk da halin dakike ciki kar ki bari wuya ko kuma wani yanayi ya hana ki kusanci zuwa ga ubangijinki,tabbas nasan akwai abinda yah faru a daren dana badake ga ummanki hajara,amma nakasa koda abinda nayi lokacin barekuma mai ya faru,abinda nasani kawai shine idan nayi kokarin tuna mai yah faru nakan ji duk kaina ya juye ina kokarin fita daga cikin hayyacina,bansna mai ya faruba kwata kwata,har shikansa Abdulwahab bansan mai ya faru dashiba.
Sameemah muna cikin jarabawa dagani harke amma karki yanke kanki daga neman sauki a wajen allah ko kuma neman agajinsa,a duk inda kika samu kanki ki kasance mai mika lamarinki ga allah,a cikin dad'i harma da cikin wahala"
Wani irin rauni nakeji zuciyata tanayi lokacin da nake sauraron abinda yake fitowa daga bakinta,hawayen danaga yana zuba a cikin idonta ne yasani rungumeta a jikina kaman kar mu rabu.
"Nagode ummee inshaallah zanyi kokarin yin amfani da abinda kika fada min"
"Kici gaba da addu'a komai zaizo da sauki watarana sai labari inshaallah"
Daga haka tacigaba da yin lazimi ina zaune a gefenta,zaman wajen kadai tayarmin da hankali yakeyi amma haka dole na daure saboda naga farincikin a kan fuskarta.
Ranar na biyar da zuwana gidanne da rana ina kwance a kan gado naji ana kiran sallah,abinda ummee ta fadaminne yadawo min cikin kaina,saidai duk da haka ban taba gwada yin sallahr ba koda wasa,kenan ban dauki maganarta da kima ba koh,kuma ban kasance Y'a tagariba,bar batun wannan ya tsakanina da mahaliccina to,wanda shiya halicceni amma kuma nakasa bautamasa tsawon shekara da shekaru saboda bin umarnin wasu shedanu can,yanzu idan na mutu mai zancewa ubangijina,shin hujjar danake da ita na sun hanani yin ibada nikuma ban yi wani kokariba ta isa kareni daga ranar karshe??.
Wani saurin tashi nayi daga kan gadon hawaye na zuba a cikin idona,yayinda jikina yake rawa kaman an jonamin spring,tabbas akwai kalubale a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login