Showing 18001 words to 21000 words out of 53080 words
Chapter 7 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt
garin porthacourt ko kuma nace da zamaan a can,har surayyah ta haihu mace sun saka mata sunana,nidai da sun nemk shawarata da basu saka mata suna na ba,saboda ina tsoron kar wani abun yasameta ,sannan wane abin kirkin na ajiye da har na cancanci hakan, bayan suna da mukayi waya da burgu yake cewa yaji labarin zainab ma ta kusa haihuwa,toh kawai nace dan banga ta inda hakan yah shafeniba,ni har na manta dasu ma saida yah fadi hakan tukunna.
💎*sameer a madubin gani*💎
A hanyar dawowa ta daga wani wajene na tsaya nayi nama ɗauri guda biyu,duk da nasan cewar akwai a gida amma ihsani yana da dadi.
Lokacin dana shigo har zan wuce dakin saleema sai kuma naga danaje dakinta na sake dawowa na sameema wanda yake farko gwara na mikawa sameema inyaso sai na kaimata nata,gashi na gaji daga wajen aikin da muka tafi,dan kwannan kullum cikin harim yah ta'adda da yan boko haram muke.
Ban kwarkwasa kofar ba shige wa kawai nayi danna san a bude yake dama.
Duhune dakin hakan yasa na kunna wutar dakin tun daga bakin kofah,saurin runtse idona nayi saboda ganin irin kayan dayake jikinta.
Daga ita sai pant da breezier a jijinta baƙaƙe,duk da cewa ana zafi amma ai zata iyah kunna AC idan tana bukata.
Ido daya ta bude kaman wata munafuka kafin ta mayar dashi ta rufe tareda juya bayanta.
Hakan da tayine yasake dukan kirjina kaman ana sokamim wani abu,dan yarinyar babu karyah akwai zubin halitta mashaallah,dakyar na samu na tattaro wasu yan guntayen kalmomi nayi amfani dasu wajen cewa,
"Wannan wace irin kwanciya kikayi sameemah,sannan wannan kayan kuma fah"
"Ina ruwanka da kayana,kwanciya kuma wacce naga dama zanyi,tunda dakinane,kona kiraka dakinne bare kayimin kutse cikin rayuwata"
Duk maganar da takeyi ta dayah bangaren takeyi,dan tajuyah bayanta can,murmushi nayi dan dama nasan hakan zata faru,domin kwata kwata batada burki a bakinta wajen yin maganar da ranta yakeso,kaman wata GOYON GWAURO,batasan tauna magana ba kwata kwata.
Ficewa nayi daga dakin tareda kashe mata wutar bayan na ajiye mata hakkinta.
Dakin saleema na nufah ,saidai ina zuwa na jishi a rude kirib,nasan ba bacci tayi ba duk da kwankwasawar danayi amma bata budeba,kome nayi mata itakuma oho,....kai mata! Na fada a raina.
Da safe da wuri na shiga dakin saleema,a zaune na sameta a tsakiyar gado,zuhra kuma ta kama bakin gadon tana ta zuwa tana dawowa irin na yara masu koyon tafiyah.
Duk sallamar danayi mata bata amsaba,haka maganar danyi mata,
"Ina miki magana kinyimin shiru wai me yafarune haka,nace miki kishiryah zamuje bikin samun matsayi na abokina a katsina koh"
"Bazan jeba,ka dauketa ku tafi ,kodan kana tsoronta,saika nunamin fada kukeyi a haka itama,amma daga dare yayi saika shige dakinta kuyi ta soyayyarku,wato kun maidani shashasha,toh allah ya toni asirinku,da idona naga shigarka dakinta kuna magana,dan haka ka dauketa ku tafi amma ba niba kam"
"Mai kike nufi,wai daman dan kina ganine nake kin shiga dakin sameemah?,toh tun wuri kisanja tunani,babu abinda zaki hana a alakata da itah haka rabuwarmu,batun abinda yakaini dakinta kuma bakya bukatar sani tunda kin baiwa kanki amsa,batun zuwa da ita kuma zanje da itah dunta kin ce hakan"
Fita nayi daga dakinnata daga haka,dan gsskiyah ta fara bani haushi,mutum bashida aiki said kishi kuma akan abinda ba hakaba.
Dakin sameemah na nufah lokacin tah fito a wanka,fuskata babu alamar wasa bare tayimin taurin kannata daya zame mata jiki.
Ina Mamakin yanda duk daure fuskata amma koda wasa tayimin kallon ta ga kwarjinina batayi,abinda koh maza ma sai na maji tukunna yake kawomin wargi.
"Ina so ki shiryah bamu je wani waje yan zunnan"
"Wai nikam mai ........."
"Sameemah banason jin dogon surutunki a halin yamzu,kedai kawai ki shiryah mu tafi,ba dadewa zamuyi ba"
Na boye matane saboda nasan idan ta san inda zamuje koh tsafi nake da baƙar zaba bazatajeba.
Da haka allah yabani sa'a ta shiryah dim.
Sauke ajiyar zuciya nayi ganin ta fito da wani material a jinkinta purple,yayi mata kyau kuwa sosai,baƙin gyale ta yafa irinna adon kayan.
Mota muka shiga babu wanda yake cewa wani abu har muka dau hanyar barin gari.
Kallonta nayi tah gefen ido dan naji mai zatace,amma bata ce komaiba saima danna waya da takeyi lokaci zuwa lokaci takan daga ido ta kalli titi.
Tabb wannan wace irin mutum ce haka,na faɗa a raina.
💎*sameemah a madubin gani*💎
Ina kallonsa yana min kallon gefen ido lokacin da yah kama hanyar barin cikin gari,nasan dan yaga mai zancene koh yah fuskata zata nuna.
Bai san duk maganar da suke shida saleemah ina jinsu ba,dan tundaga dakina ina jin duk abinda suke fada,saidai idan ban ga damar jin abinda za'a ce ba,ta wannan ma nasan nisan jin maganata yah fi na sauran mutane duk da bansan su ya suke jiba.
Lokacin dana ji mai yaca nayi niyyar idan yazo nace bazanjeba,amma kuma ta wani bangarena na zuciyata yace na bishi mutafi dannaga mai ita saleemah zatayi.
Har muka isa garin bayan azahar babu wanda yayi magana nidashi,a bakin wani katafaren gida yah tsaya,wanda tundaga bakin kofar gidan mutum yasan nairah tana kuka a ciki.
Harabar gidan an kawatashi lokacin da muka shiga,da alamun a wajen za'ayi walimar da mukazo dominta,lallai mutane ma,yanzu haka kawai na bata lokacina tundaga wani gari nazo waje dan walima,kawai dan ace nazo?.
D'aki guda aka kaini domin na huta na kuma yi sallah na ci abinci,saidai iyah cin abincin nayi da kuma hutawar.
A wajen taronma bamu wani dade ba muka juyo da niyyar komowa gida,saboda tafiyar hanya,babu yanda abokinnasa bayyi dashi mu kwana ba amma yace yanada aikin da zayyi washagari.
Lokacin da muka dawo gidan yayi tsitt kowa yayi bacci,muna zuwa yah shige dainsa koh magana bayyiminba,nima na wuce nawa dakin,dan daga ganin yanayinsa ba karamin gajiyah yayi ba,saidai dauriyah kawai.
Sanda na shiga daki ban yi niyyar kwanciya ba,dan ko alamun wata gajiyah banjiba saboda nasan jikinnawa yasha banban dana sauran bil'adama.
Har nayi shirin zuwa dubo su bingo amma kuma dana leka window sai naga dare yayi sosai.
Dole na ha kura badan nasoba,saboda tunda muka shigo nakejin kaman wani abu yasamesu,da kyar na daure na kwanta akan zuwa gobe naga yamda suka yini.
Da safe kuwa tun kafin nayi komai na fita wajen su,da kayan baccima a jikina gyale kawai na yafa.
Ina zuwa wajen naga reza a kwance,yayinda shikuma bingo yake kwance a gabanta yah tsura mata ido.
Karisawa nayi inda suke,mai zan gani........! A kwance take tana nishi,duk jikinta zanen bulala ne raɗa raɗa,sai jini yakeyi.
Tabdijan,lallai an tabo rina a kaba,tambayar bingo nayi akan wanene yayi mata haka?.
Jan rigata yakeyi yana tafiya har zuwa inda Samuel yake zaune yana jiran kofah,haushi ya fara a gabansa ,shikuma dayaga haka sai dauki dutsi ya zefeshi dashi.
Duk abinda suke na ina kallonsu daga nesa,dana cije fatar bakina saida tah fashe dan bakin ciki,babi abinda ake fada a cikin kaina sai irin kalar hukuncin dazan yiwa Samuel ko zan huce haushin danake ji.
Bingone yadawo inda nake said kuma yayi cikin gidan yana min alamar na biyoshi.
Ina cikin hakane Yaseer yazo wucewa,wani sojane sabon zuwa wanda nake haduwa dashi a wajen training can Bori camp Idan Naje kallonsa. Bayan mun gaisane na tambayeshi tareda cewa,
"Yaseer Akwai abinda zakayi ne?"
"Ahah aunty,Akwai matsala ne?"
"Eh toh zaka dan kulamin da wata karyane anyi mata duka kuma tana da ciki,akwai abinda zanyi kafin na dawo"
Muna magana har mukaje inda reza take,shima kansa saida ya tausaya mata,amma ina famasa wanda yayi yace zai aikata,dan suma mugunta yake musu sosai,a raina naji dadin wannan labarin,koba komai zan samu damar hukun tashi da dalili mai karfi.
Komawa nayi inda bingo yake,muna tafe har bakin dakin saleema,karkada mun jela yayi a bakin kofar dakin kafin yah juya yah fita.
Kama Baki nayi ina jijjiga kai,wato harda itah a wannan aikin kenan dan taga jiyah bana nan nabi sameer koh,sai yanzu na tabbatar babu abinda suka mata kawai zallan mugunta ce,zakuwa taga yanda ake mugunta akanta.
Komawa nayi inda yaseer yake na aikeshi ya siyomim magani,nikuma nasaka musu abinci suka,duk da yanda take ciki amma hakan bai hanata cin abinci dayawaba abinka da dabba.
Lokacin dana koma falon saleema ta fito,hankalinta kwance kaman babu abinda tah aikata,dan ko wanka daga gani batayiba daga ita said kayan bacci,cuna min baki tayi da muka hada ido,nikuwa Murmushin gefen baki nayimata,da tasanni sosai da zata gano mai Murmushin yake nufi,saidai kash bata masaniyah akan hakan.
Lokacin da ta koma dakintane naji alamar sallamar yaseer a waje,fita nayi na karbi sakona,maganin kam karba yayi yace zai bata,sannan zai dunga kulada ita,godiya nayi masa bayan na bashi maganin.
Komawa dakina nayi tukun kafin na fito na nufi dakin saleeman.
Babu kowa a dakin sai karar ruwa a bandaki,hakan ya tabbatarmin da cewa tana wanka,zama nayi a hankali kwance na jirata har ta fito.
Lokacin data fito turus tayi a bakin kofar bandakin ganina a cikin dakinnata,abinda bata taba tsammata,shiru tayi kaman mai nazari kafim kuma ta matso zuwa ainihin cikin dakin.
Ta shi nay I daga bakin gadon tareda nufar inda take,duk da akwai tsoro cikin idonta amma hakan bai hanata tattaro jarumta ta yafawa kanta ba ta hanyar cewa,
"Me kike min a dakina kuma da wannan lokacin,akwai abinda kike bukata ne"
"Ba abinda nake bukata,kawai dai nazo yimiki tambaya ne,shin mai reza tayi miki kikayi mata wannan dukan lokacin da bananan jiyah"
"Au hhhhhh dama akan wannan dabbar ne kike wannan tambayar,ai said ki fadamin tun wuri,baki sakani tunanin wani abu ne ya kawoki ba"
"Duka na daketa kuma ko gaban waye zance na daketa,dama ina jin haushinta kuma tashigo har cikin falona,dan rashin mutunci,ko kuliya bazan yadda da zamanta cikin gidana ba bare kuma kare kazami,dan haka shiyasa na kamata nasa Samuel ya rike min itah na dakata,idan da abinda zaki iyah yi kiyi akan hakan"
"Oh haka kikace a ko gaban waye zakice ke kika daketa kuma ayi duk abinda za'ayi?,zakuwa kiga abinda mai itah zatayi yanzunnan,dan ko kasa da sama zata a hade a lokacinnan said nayi miki ninkin abinda kikayi mata,dama ina taraki da rainin dakike min,ko kina tunanin dan nazo garin da ubanki yake shikennan bazan iyah miki komaiba koh?"
Ina gama fadar hakan na bita da kyawawan maruka har gida biyu a ta kowanne kumatunta,fadawa kan gadonta tayi tanna ihu,hakan bai dameni ba sai ma komawa danayu nasaka key a kofar sannan na dauko bulalata dana ajiye a wajen.
Jijjiga ta nayi kafin na fincike towel din dayake jikinta na zuba mata itah gadon bayanta iyah karfina,murmushi nayi danaga ta shigeta sosai, ɗagawa na sake yi na zuba mata,a na ukunne naji bugun kofar tata da alamar sameer ne dannaji muryarsa........
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎19~20💎
Duk da bugun kofar dayake yi kaman zai balle kofar hakan bai hanani cigaba da zambada mata ba,har saida naga bata motsi sosai,fatar jikinta kuwa duk ta yi ja sai zubar da jini takeyi abinka da Wanda hutu yah ratsashi sosai.
Shima bani na bude kofarba kallonsa kawai nayi a gabana ya fizge bulalar da take hannuna kafin yah wanka min mari.
KO kusa banji zafin marinba saima murmushi danayi masa ganin aika aikar danaso yi ta tabbata raina yayi fari tass kaman farin dutsi.
Karisawa inda take yayi da sauri yana dagata a hannunsa,wata harara ya aikamin kafin yah fice zuwa wajen da motarsa take.
Nikuwa ɗaga kafaɗata nayi ko a jikina,na rama abinda naga bazan iya bariba yah tafi a banza.
💎*sameer a madubin gani*💎
Lokacin dana dauki saleema a hannu na na nufi motata ko motsi bata yi,lokaci zuwa lokaci nake leka ta a bayan mota inda na ajiyeta, amma koh motsi batayiba har muka isa asibiti.
A hanya na kira hajiya fatima nake fadaamta,dan bazan fara kiran alhaji musa a lokacin ba,nasan abin bazai tafi da kyau ba.
Kusan tare muka isa da itah dayake dama ta fita anguwa tana kusa da asibitin.
Har nursing suka karbeta suka turata a keken asibitin bata tambayeni mai yah faruba,saida muka ga anshiga da itah an fara magance ciwukan jikinta sannan an saka mata ruwa tukunna muka zauna,kallona tayi cikin kwanciyar hankali kafin tace,
"Menene yah faru haka sameer?"
Bata labarin abinda yah faru kawai nayi mata,shima wanda nasani kadai,na manta key din drawer tah ta office,ina dawowa naji kukan saleemah a dakinta,dana buga kofar kuma najita a rufe,jijjiga wa na cigaba dayi,amma ganin bazata budeba ne yasa na tafi dakina na nemo spare key na bude dakin.
Nan nasamu sameemah a tsaye a bakin gadon tana ta dukanta kaman an aikota.
Numfasawa tayi bayan taji abinda yake faruwa,saidai abinda yafito daga bakin hajiyah fatima ne ya bani mamaki inda tace,
"Amma yakamata a bincika dan aji mai tayi mata,idam babu toh inaga ita ma tana da matsala yakamata a binciki lafiyarta,dan abinda takeyi bana mai lafiyah bane,dannaso gano hakan lokacin da muke magana da itah a dakina,sannan kaman tana cikin kadaici sosai"
Kallonta nake da alamar mamaki,anyah kuwa ana samun irin wannan matan,wata tayiwa ƴarki irin wannan dukan amma kina kokarin sanin ko tana da lafiyah,ba ta ma yattaki kike ba.
Muna cikin hakanne alhaji musa yah iso wajen cikin rawar jiki dan yaji ance tana asibiti.
Tambayar abinda yah fari yafarsyi cikin daga murya,hajiyah fatima ce ta kamo hannunsa tareda bashi labarin abinda yah faru cikin kwanciyar hankali,saidai bata kai ga gama fada masa ba ya tashi da sauri yana danna waya yana fadin.
"Ina baza'a yiyu ba,ni dama tundaga farko banso zaman wanna matar kusa da ƴataba,kece kika nace sai an bi ta mijinta ,toh gashi nan tana neman kashe mana yarinya a aikim banza,kuma billahillazi babu mai hanani hukuntata a cikin garinnan .
Kai kuma ka shiryah zan yimana booking jirgi in anjima duk zamu tafi mu uku harda itah muje ayi jinyarta dan nan ba abinda suka iyah,awa guda amma har yanzu bata koh farfaɗoba"
Yana gama faɗan hakan yah amsa kiran daya shigo cikin wayar,dsyake a handsfree take kana jin irin girmamawar da na ɗayah gefen yakeyiwa alhaji musan.
"Kai ba wata doguwar magana nakeson muyi ba,inaso ka tura sojoji suje gidan sameer su ɗauko wata mai laifi,kuma so nake ku kaita ɗakin horo dayake a bakin daki"
Daga can mutumin ya amsa da cewa an gama ranka yah dade.
Duk da cewar abinda sameemah tah aikata bai daceba,saidai hukuncin akamota har cikin gidana kuma ɗakin dayake nata na aurena sainaji abin bayyimin daɗiba,koba komai yakamata a barni naji abinda yake faruwa,ba kawai akama matata a saka cikim cell,kuma sannan a saka gardawa suyi tah dukanta.
Sannan wani abunma wai saina ajiye aikina na bisu wajen jinyarta a wata ƙasa daban.
Haka muka cigaba da zama amma shiru babu alamar zata farka,anan muka kwana har washagsri kafin na tafi gida zuwa dauko kayana wanda zamu tafi can kasar Germany inda za'ayi mata maganin.
Banda kudi baya yiwa wasu wahalar cirewa menene abin tafiyah wata kasar,ita wacce aka kai wajen horo na kasa (dungeon)ai saita fita shan wahala ba kadan ba.
Ina isowa da mota naga nashiga cikin gidan,fayau naga falon bakowa sannan kuma babu alamar motsin mutum,dan farouq yana wajen nanny sa ita kuma zuhra tana wajen hajiyah fatima.
Dakin sameemah na leka,ina tuna yanda nake ganinta idan na shigo dakin,duk da wsni lokacin bata kulani har na fita.
Dakina na nufah na hada kayana,har na zo shiga mota sai kuma na nufi hanyar garden dannaga wulgawar mutum,yaseer nasamu sabon sojan da bai dade da zuwaba,abinne yabani mamaki mai yake a wannan yankin shida yake zaune a cikin bori camp.
Turus mukayi dashi yana shirin fitowa,dauke kansa yayi yana kkkarin wucewa,hannunsa dauke da karyar sameemah wanda take ta numfashi dakyar,jikinta duk zanen bulala.
Tambayarsa nayi menene yasameta,kallonta yayi tana hannunsa kafin yace,
"Nima ban Sabina,kawai jiya naga anty sameemah tana dubata ganin irin abinda akayi mata,daga nan ta ce nasayo mata maganin dazai warkar ciwon sannan na sayo mata bulala dorina mai kai biyu. Jiya kuma da azahar tacemin idan naji lbarin an kamata to na kulu mata da karnukanta kafin ta fito"
Hanya nabashi ya wuce da itah dayan ma yana biye dashi har suk bar wajen.
Shiru nayi ina tunani har na isa inda cell din da samemah take,wato karenta ta,ramawa dukan da saleemah tayi masa,kuma tasan za'a daure ta amma tsyi hakan,wannan wace irin macece ne?.
Da kyar mai kulada wajen yabarni na shiga wajen dan nafishi matsayine da nasan bazan samu kallonta ba.
A zaune na sameta an daure hannun ta baya,rigarta ta wani wajen duk ta yage saboda duka,hakika na tausaya mata ganin akan ceton kare ta saka rayuwarta a haka.
Karisawa nayi har inda take na tsugunna,dago kai tayi tah kalleni kafin ta kawar da kanta.
"Yanzu abinda kikaga yafi kenan,kisaka rayuwarki a haka saboda karya?"
"Hakan jai shafeka na ni kadai ya shafa,sannan bannemi taimakonka akan hakan ba,naga zan iyah shiyasa na yi,kuma da kake zancen na saka rayuwata a haka dan kare,ta cancantane wani ko da kudi yasakani bazanyiba,saboda suma zasuyi min abinda yafi haka idan ina bukata.
Karka damu dani ka tafi jinyar matarka yafi ka tsaya kana bata lokacinka annan"
Rasa ma abinda zance nayi lokacin da ta gama maganarta,tashi kawai nayi na fita ina fadin allah yah kyauta a raina.
Lokacin dana je har an gama sakata a jirgi dan haka shiga mukayi kawai muka tafi,nidai da da yadda zanyi da bazan bisu ba,saidai ko mai zanyi nasan alhaji Musa bazai fahimtaba,illah ma yace da saka hannuna akan hakan.
💎*sameemah a madubin gani*💎
Ina kallonsa lokacin daya fita,haka kawai na tsinci kaina dajin haushin yanda bai tambayi dalili ba saima kokarin gani laifina dayake yi,nasan a halin danake ciki da zuciyar mace ce dani da saina rushe da kuka,saidai babu yamda zanyi saidai na hadiye bakincikina kawai.
Bai dade da fita ba wani yah shigo da abinci a hannunsa a wani kwano irinna bawa dabbobi abinci.
Ina kallonsa har yah ajiye abincin,maimakon yah fita sai yah matso kusa dani yana tanɗe baki,hmmm maza wani lokacin suna bani mamaki dole sai mutum yasakawa ransa taba abinda ba nasa ba.
Hannunsa yah miko har yakusa taba cinyah ta na kalleshi.
"Karka kuskura wannan kazamin hannunaka ya taba cinyata in kanason zama da lafiyarka,idan kuma ba haka na ka gwada"
Baiji gargadin danayi masa ba sai ma kara matso da hannunsa dayake kokarin yi.
Shiru nayi masa har yakai hannunsa yagama shafa cinyata kafin yah dauke,
"Yanzu kaji dadi daka taba cinyata koh?,saidai inaso na sanar maka cewa,bazaka kara yin