Showing 33001 words to 36000 words out of 53080 words
Chapter 12 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt
dishi nake ganin komai,bude idona nayu dukka akan fuskar masoyinna wa kafin namayar na rufe da sauri wani duhu ya lullubeni.
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎31~32💎
💎*sameer a madubin gani*💎
Duk maganar dake fita daga bakinta ban saka su cikin madubin fahimta ba saida naga lagababbben jikinta yayi kaca kaca da jini akan kirjina,babu abinda nake maimaitawa a cikin raian sai innalillahi wa innna ilaihi rajiun,dan na rasa mai zanyi,babu abinda kwakwalwata take haskomin sai kokarin rasata da nakeyi bayan nayi kuma rashin ummah ta a baya.
Mika hannuna dayake rawa nayi na dauki waya ta,da kyar ma na samo number dake farkon call log dina na danna kira,saleemah ce ta daga tareda cewa lafiyay?.
Cikin magana a rarrabe nacemata,
"Salee......mah ddddakina.... Samee. ....mah ce"
Da sauri ta kashe wayar ta shigo dakin,yamda muke zaune ta rankwafo akan kirjina haka saleemah ta samemu ko motsawa na kasa yi.
Jinin da taga yana zuba a bakin sameemah ne ya razana hakan yasa ta koma da sauri dakinta ta dauko waya tareda danna number doctor maryam.
Ina nan zaune har suka shigo suka dagata daga jikina ita da doctor maryam din zuwa cikin mota.
Bayan sun tafi da wasu mintuna ne na tashi na bi bayansu,ko tunanin sanja kayan dake jikina banyiba,burina kawai bai wuce naga halin da take cikiba.
Tun daga bakin kofar shiga wajen doctor maryam ta kama hannuna ta zaunar dani tareda yin magana cikin kwanciyar hankali.
"Ahah bai kamata kashiga a haka na hakanma da wannan daren sameer,matarka tana da rai yanzu hakama mun saka mata karin ruwa saboda anyi sa'a jininta bai kai a kara mata ba,saidai akwai bukatar ta ringa cin abinci mai saka kujari.
Yanzu kai kuma kaje ka cire kayannan kasaka wasu in san samune ma sai gobe ka dawo,domin zamu kulada ita sosai.
Haka badan nasoba na juyo da baya zuwa gida amma hankalina gabadaya yana kan sameemah da kuma wane hali take ciki.
Haka na kwana banyi bacci ba ina kai kukana ga allah,da safe kuwa tun kafin garin ya waye sosai kama hanyar asibitin.
Murmushi doctor maryam tayi data ganni a wannan lokacin.
Dakin da sameemah take kwance ta rakani,a kwance take tana kallon silin kamar mai tunani,lokaci daya tausayinta ne yakamanni lokaci guda ,abin tashin hankain ma shine bansan mai yake damunta ba.
Karisawa inda take kwance nayi a hankali kaman mai sanda,juyo da idanuwanta tayi kana ta saukesu a kaina,kara mayar dasu tayi zuwa inda take kallon tun farko kafin shigowata dakin.
Hannu nakai zan rike nata wanda baya dauke da karin ruwan a jikinsa,amma sai tayi saurin janye hannun tanamun gargadi da idonta akan kar na tabata,banyi yunkurin sake tabata a karo na biyuba saima tambayar ta danayi yha jikinta.
Motsa baki kawai tayi kaman zatace wani abu amma batace komai ba.
Doctor maryam ce ta shigo dakim da tire a hannunta,ajiyewa tayi a gefen tiren tana cewa,
"Patient a ta shi a ci abinci ko tunda jiki yayi sauki"
Dago da idonta tayi ta zubasu a cikin na doctor maryam din,wanda hakan yasa ta dan ja da baya tana karewa sameemah kallo kaman mai nazarin wani abu,can kuma ko mai ta tuna sai kawai ta kawar da tunanin tareda mika hannun ta domim taimaka mata ta tashi.
Hannun doctor maryam din ta kama ta tashi,maimakon ta saki hannun sai ta,rikeshi gam kaman wani yana son kwance hannun doctor maryama din daga nata.
Matsawa kusada ita nayi domin rikota amma sai ta matsa jikin doctor maryam kaman zata koma cikinta,magana tayi cikin dashshshiyar murya irinta marar lafiyah.
"Yah sameer bawai ina gudunka bane amma dan allah ka bani lokaci tukunna matsowarka kusadani akwai matsala a halin yanzu"
Ina jin hakan na daga mata kai alamar na fahimta saidai hakan bai yimin dadiba ,itama ta fahimci hakan sannan nasan kaman yanda nake bukatar ta a kusadami koyaushe nasan itama tanajin hakan.
Alama doctor maryam tayimin akan na bata lokacin.
Cire karin ruwan dayake hannunta tayi kafin ta jata zuwa bandaki domim ta gyara bakinta,basu dadeba suka fito har sannan sameemah tana jikinta kamar wata karamar yarinya,abinne yaban mamaki domin nasan halin sameemah sarai,bata nuna ita yarinya ce sai a gaban ummah kadai,tunda ta rasu kuwa tafison komai tayi da kanta basai an taimaka mata ba.
Abincin ta saka a plate ta fara bata tana ci har taci da dan yawa,komawa tayi ta kwanta kaman yanda take a farko.
Fita doctor maryam tayi sannan tayimim alamar na biyota zuwa office dinta.
Muna fita wata nurse kuma taje domin kula da itah. Saida ta zauna akan kujerarta kafin ta nuna min waje akan na zauna.
Min dan samu sakanni a haka kafin ta fara yimin magana.
"Hakikanin gaskiya sameer bamuga komai ba gameda abinda yake damu matarka,da farko nayi mata gwajin ciwon zuciya amma sai na samu kalau babu wata matsala,sannan abin mamakin shine yanayin yanda ta zubda jini bakai ace ma zata iya rayuwa ba amma kuma da muka gwada sai mukaga jininta normal ne bayyi wani low sosaiba.
Komadai menene yasameta yanzu komai normal ne babu abinda yake damunta saidai dan gajiya kawai da tayi amma babu wata matsala,zuwa nan da yamma zamu iya sallmar ta.
Godiya nayi mata bisa kokarin da tayimana kafin na koma wajen sameemah,dan yau kam babu batun aiki.
Nursing din data ga shigowa ta fita tayi ta bamu waje nikuma na zauna akan kujerar da ta tashi din.
Banyi zaton zatayi magana ba amma kuma sai na ji tace,
"Yah sameer kayi hakuri da abinda yah faru sannan ina mai baka hakuri a gameda halina,saidai alfarma guda daya zan nema a wajenka ita ce dan allah karka tambayeni abinda yake damuna"
"Shikenan zan yi kokarin yin hakan tunda shine burinki amma ki sani badan nasoba zanyi kuma bazanyi miki karya ba hakan zai dameni matuka"
💎*sameerah a madubin gani*💎
Tunda mukayi wanann zancen da salma ta daina tambayata akan wane hali nake,saidai kuma koyaushe idan muka hada ido ina kallon yamda take bina da kallon tausayi.
Hakan na cigaba da zama da umatuje cikin halin bakinciki da rashin walwala,bai san ya na tashiba ina lafiya,mai nake bukata ko kuma mai nake so daga gareshi,duk yah tsallake wanann abubuwan.
Kullum cikin sakani ayyuka yake nayi masa kaza nayi masa kaza,duk da nace naji nagani zai jure amma nasan hakan da matukar wuyah,kawai namika lammurana ne ga mai duka,da burin watarana zai iya kawomin dauki a rayuwata.
Zancen aurensa da mufeedah kuwa kullum dada hau hawa yakeyi,wani lokacin ma akan gadona a cikin dakina zai tsiri waya da ita dan kawai naji haushin hakan,haka zan juya masa baya nayi ta kukan zuci har bacci yah daukeni a haka.
Da safe dana tashi kitchen nashiga domin yin abinci karyawa,yanzu nikadai ce nakeyi kasancewar na hana salma shiga kitchen din,saboda cikinta yana bata wuya tun sanda yah shiga wata na biyar,kullum cikin zuwa asiniti sukeyi ita da alhaji bala,wannan abinba yakara wutar tsana tsakanina da hajiya mairo domin na daukewa salma girki ni nakeyi ni kadai.
Wani lokacin da gangan zata tsiri yin abincin sadaka badan allah ba sai dan nasha wahala,duk abinda takeyi na tura mata aniyarta nasan idan ma bata daina ba dole ai akwai mutuwa,idan na mutu shikenan ai.
Yamzu bikin umaruje da Mufeedah yakama saura sati daya,saboda tsabar samun gindin zama a cikin gidamnmu ake hidimar bikin harda na dangin amaryar,dan hajiya mairo ce ma ta dauki nauyin gyaran amare da kuma kwalliya.
Tun safe nida masu aiki muke kwabin fukawar cincin har kusan magriba muna aikinnan,duk wanda yaganmu sai ya tausaya mana saboda yanda muka kode kamar tsohon kaya.
Salma ce ta shigo kitchen din wai zata tayamu suyah,hannunta na rike na karbi matsmin kafin nafito domin rakata dakinta,a falon muka hadu da hajiya mairo ita da hajiya zulai mahaifiyar Mufeedah.
"Ke ya naga kin fito daga wajen aikin,kun gamane iye"
"Bamu gamaba barin na raka salma dakinta tukunna zanje mu karisa"
"Ita batada kafa ne da bazata iya tafiya dakin dakanta ba,ko munafurcin za'a gwadamin,hmmm ke wai mai yar uwa ko,shine kika hanata aikin komai a gidannan kika karba kikeyi,zubamiki ido nayi zanga lokacin dazaki kasa ko kuma kikasa zaman cikin gidannan ki karbi takardarki,dan wallahi dama banda aikin asiri ai dana yafi karfinki guzuma kawai. Yanzuma ina samun suruka zaki tattara naki ya naki ki bar gidannan"
Wannan kalmomi na hajiyah mairo sun dade da haddatuwa a cikin kunnena saidai duk da haka ko yaushe idan na jiSu komawa suke tamkar sabi dall a zuciyata.
Salmace ta rike hannuna tareda yimin murmushi karfin hali kafin tace,
"Bantaba sanin duk zamana danayi dake a gida kina da irin wanann halinba,zuriyah da kuma tawakkali wanda ba kowace macece zata iya ba,inshaallah zakiga haske a cikin rayuwarki anty sameerah,ina alfahari dake sosai"
Kwallah ce ta zubomin wanda nake ta kokarin mayar da itah lokacin da salma ta sau hannuna ta shige cikin dakinta da sauri.
Share hawayen nayi na koma wajen aikin da mukeyi na cigaba .
Sai wajen isha kafin muka gama wannan aikin,ko ina a cikin jikina ciwo yakeyi kaman an sassaramin shi. Dakyar cikin dauriya naja jikina na shige nawa dakin,bandaki na shiga da sauri na tari ruwan dumi mai zafi na fara gasa kowacce gaba ta jikina,na dade inayi kafin na dawo na haye gadona,dan dama nayi sallahr isha tun sanda muke aikin,batun yin hadda kuwa wanda zan kai wa malaminmu babu zancenta dan bazan iyaba koda naso yin hakan.
Da haka ina nan kwance bacci yah fara daukata,gashi nasan zamana acikin gidan yakusa karewa,saboda gobene za'a daura auren Mufeedah da mijina kuma ko naki ko naso nasan ban isa nayi kishi da ita ba,dolene na bar gidannan na basu waje su yi rayuwarsu,dan duk wanda yaga kallon da umaruje yake yiwa Mufeedah yasan ita ce zabinsa kuma muradinsa.
Can cikin dare wajen goshin asuba naji hayaniya taki karewa a cikin gidan,lalumar zanina nayi na dora akan rigar baccina na nufi kofa domin naga mai yake faruwa,nikadai ce kuwa a dakin umaruje baya nan ya tafi wajen abokinsa a Sokoto,ko yana nan ma dama baza'a sameshi a dakina ba,dan mun daina hada daki dashi tun waccen satin,a cewarsa shi ya gaji da hada daki dani ma.
Murda kofar nayi a hankali na fito zuwa falo,hajiya mairoce a tsaye sai karkarwa jikinta yajeyi,itama hajiya zulai din haka na fanta,ganin salma a zaune a gefensu ne daya gefen kuma Mufeedah ce da kawayenta a zaune.
Matsawa nayi gefen salma tareda tsugunawa na tambayeta mai yake faruwa cikin murya kasa kasa.
Kallona tayi kaman bazata ce komai ba sai kuma tace,
"Anty sameerah umaruje ne yayi hatsari a hanyarsa ta dawowa daga sokoto dazu,wai tafiyar dare suka dauko sai babbar mota tabi ta kansu,shi dayan ya rasu amma umaruje baijj ciwo sosai bama sai kunkumin sa daya bugu yanzu haka an taho dashi asibitin garinann suna hanya"
Jin maganar nake tana yawo a cikin dodon kunnena,hatsari umaruje yayi hatsari,mjina fah kenan.
Saurin tashi nayi daga tsugunnen danake ina kokarin saita numfashina dayake barazanar daina shiga cikin huhuna.
Inna lillahi kawai bakina yake furtawa babu adadi,ganin zaman ma bazai kaini bane yasa na koma dakina da sauri na dakko kayana nasaka sannan na dauko karamar wayata da nokia na dawo falon ,sannan har an fara shiga mota domin tafiya asibitin saboda an iso dashi.
Nima kama gidan baya nayi na mota nashi ga da sauri,ina ji hajjya mairo tana zagina amma bata ita nakeba a halin yanzu.
Muna isa asibitin kowa yah fito daga motar muka tafi ruuu harda mamar Mufeedah da ita kanta Mufeedah da kuma wasu kawayeta.
Wata nurse ce tayi saurin taremu tareda cewa bazai yiyu mushiga sanann ba.
Komawa mukayi wajen jira dukka muka zauna,bakina banda motsi wajen kiran sunan allah ba abinda nakeyi,duk lokacin da muka hada ido da hajiya mairo sai ta watsamin harara.
A raina nace keda danki yake kwance a sibiti kiyi ta kanki mana.
Muna nan zaune har akayi kiran sallah nafarko,tashi nayi na tambayi wata mai gogegoge inda zam sami ruwan alwala,nayi sa'a kuwa ta bani ruwan.
Ina jin hajiyah mairo tana cewa,
"Dama ai munafurcine yasa ta biyomu dan taga mai ya sameshi ta dora a gaba,dangin tsiya kawai"
Ina jinta banyi magana ba har na tada sallah nayi raka'atainul fajari. Sannan nacigaba da addu'o'i dakuma domin nemawa umaruje lafiya.
Har na idar sallah likitan bai fito daga dakin ba sai can wajen rana ta kusa fitowa kafin ya fito daga dakin.
Dukkan su tashi sukayi domin nufar inda yake,nima tashi nayi daga kan dan kwalina nayi wajen sa da sauri.
Kallonmu yakeyi kaman ba zaije wani abu ba sai kuma yace,
"Idan Yana da mata to ta sameni a office dina ita da matarsa"
"Eh likita yana da mata amma kuma akwai wacce za'a dauramusu aure yau dan haka itace zata zo taji mai yake faruwa"
"To shikenan itama wacce zai aura din zata iya zuwa taji mai yake faruwa dashi,amma matar tasa ma tajo"
Haka ba yanda hajiya mairo zatayi na bisu a baya zuwa office din likitan domin jin mai yake faruwa.
Lokacin da muka shiga a bakin kofa natsay amma ina jin duk abinda likitan yake cewa.
"Toh hakikanin gaskiya hajiya d'an ku bai samun raunika sosai ba a jikinsa amma yasamu wata matsala sakamakon buguwar da kunkuminsa yayi yah taba mazakutar sa,wanda ina mai baku hakuri akan abinda zakuji amma gaskiya bazai iya haihuwa ba a halin yanzu .........toh fah
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎33~34💎
Shiru dakin yayi babu wanda yace wani abu jin abinda likitan yah fada,sai shine yasamu kwarin gwiwar cigaba da cewa.
"Sannan kuma koda mun sallmaeshi zai iya samun wata guda kafin yah fara tafiya saboda yanayin buguwar da yayi,wannan shine sakona a gareku ina fatan ku kasance masu tawakkali da kuma karbar kaddara a duk yanda tazo muku"
Dukkanmu juyowa mukayi domin fitowa daga office din,a bakin kofar muka hadu da alhaji bala shima dawowar sa kenan daga tafiyar dayayi yaji abinda yah faru,rabewa yayi ta gefenmu yah shiga office din zuwa wsjen likitan.
Mukuwa hanyar dakin da umaruje yake muka nufa dukkanmu.
A kwance yake yana kallon sama,an saka mayafi irin na asibitin a kunkuminsa zuwa kasa,in ba kaji abinda yake faruwa dashi ba bazaka ce baida lafiya ba.
Samun waje hajiya mairo tayi ta zauna kusada shi tareda yi masa sannu cikin murya mai dauke da damuwa.
Kallon hajiya zulai tayi kafin tace,
"Ina hajiyah zulai zancen daurin aurennan saidai a daga sai yah warke koh?"
"Wane daga auren kike magana akai hajiya mairo,kunnenki bai jj abinda yake damun danki bane,amma duk da haka kike kokarin hadashi da dana,toh wannan zancen babu shi kwata kwata,dan ina ji ina gani bazan hada Y'a ta da juyaba wanda bazai haihuba"
Itama Mufeedah share hawayen dayake idonta tayi kafin tace,
"Gaskiyar ummah ne bazan iyah aurensa bayan nasan bashida lafiya,koda an daura auren ma dole za'a warwareshi bare allah yah taimakeni ba a dauraba dama,dan haka sali alin babu abinda ya hada"
Baki hajiya mairo tasaki tareda cewa,
"Hajiyah zulai kinsan abinda kike fada kuwa keda yarki,kanmu a hade zamu hada wannan auren amma dan kawai wani abu yah faru shine zaku watsamin kasa a ido?"
"Kai kaji hajiya mairo dan allah,banda kina so ki cutar da Y'a ta dan kinga ba y'ar ki bace naki yarda shine laifina,wannan ai son kaine,ina ganin fah yanda kike zaluntar y'ar wata dan kawai tana auren danki"
Har hajiya mairo zatace wani abu alhaji bala yayi saurin katseta ta hanyar cewa,
"Hajiyah mairo ya isa haka,gaskiyar tane abune na kowa yana da hakki dan haka tunda bazata iya aurensa ba shikenan,kuma koda anyi auren tace bazata zauna dashiba dole a raba auren haka shari'a tace"
Kuka hajiya mairo ta fara ganin abin yama neman fin karfinta,babu wanda yah kulada ni a cikin dakin sai lokacin da alhaji baka yamin magana,dukkansu harda hajjya zulai da suke shirin fita daga dakin kallonsu ne ya dawo kaina.
"Kema kina da zabi sameerah akan zama da umaruje,kindai ji mai likita yace kan cewa bazai kara haihuwa ba,shin zaki zauna dashi ko kuma kina neman takardar ki a wajensa na ya sawwakemiki?"
Saurin jijjiga kaina nayi tareda cewa,
"Zan Zauna dashi abba"
Kowa kallona yayi da mamaki harda hajiya mairo da take share majina,magana alhaji bala yasake yi a karo na biyu cikin tabbatarwa,
"Shin kin yarda da zabin da kikayi,idan harkin amince ki zauna dashi akwai sharadin banason kuma wata maganar ta fito daga baya,idan ma lokaci kike so a baki na tunani duk za'a baki amma kiyi tunani"
"Bana bukatar lokaci nayi tunani,dan dama hakan shine zabina tun kafin hakan ta faru,nayi wa zuciyata alkawarin cigaba da zama dashi cikin kowanne yanayi da kuma hali har karshen rayuwata,saidai idan shine yayi ra'ayin sawwakemin saboda yagaji da zama dani,toh yanzuma hakanne idan yaga bazai iya zama daniba xai iyha sawwakemiin ,kuma ina mai sake bashi hakuri bisa hanyar damabi na aureshi ba tareda yardarsaba,dan haka duk abinda zaimin bazanga laifinsa ba ko kadan kuma zan cigaba da zama dashi har karshen rayuwata ......saboda ina son..sa sosai har zuciyata,haihuwa kuma dama allah ne me bawa mutum kuma zai dauke a duk lokacin dayaga dama,dan haka banida matsala da rashin haihuwarasa a gameda zamana da shi,ina fatan allah ya bashi lafiya yah tashi kafadunsa"
Ina gama fadan hakan na rushe da kuka wanda dama yake cina kwana da kwanaki,ganin abin zai min yawane yasa na bar dakin da sauri nayi waje domin na samu zuciyata ta yi sanyi koda kuwa dan kadanne.
Na dade a zaune a waje ina ta tunani sai wajen azahar tukunna na raba na shiga dakin,babu kowa sai hajiyah mairo itada yusrah,shikuma umaruje akan gadon ,babu wanda yake cewa komai a cikinsu,nima daga sallma ban sake cewa komai ba na shige bandakin kaman wata munafuka.
Fitowa nayi na shimfida dan kwalina a gefensu na tada sallah,lokacin dana idar na dade ina addu'a kafin na shafa na koma gefe na Zauna.
Dire bane ya shigo dauke da kula a hannunsa inji salma wai,karba hajiya mairo tayi ta bude,shikaface da miya sai kuma farfesun hanta a daya kular na marar lafiya.
Had'a ido mukayi da ita nayi saurin dauke