Showing 45001 words to 48000 words out of 53080 words
Chapter 16 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt
jin kalar nata sautin yasha banban dana sauran,duk da cewa suma sauran zuciyoyin inaso naga sun matso kusada ni amma nafi burin wannan zuciyar ta matso kusadani,kodan na fita daga kangin abinda suka zagayeni.
Shikadaine idan yazo nakan samu kaina da dagawa yana kallonsa,saidsi babu yanda na iya haka nake ganinsa ya juya ya tafi,duk da inason yah matso inda nake amma nafisan yakasance a nesa saboda kar na cutar dashi.
A inda nake ɗaure ina jin karar takun sawun wani ruhi yana tunkarowa inda nake,dan tun daga nesa nake iyah jiyo karnin jininsa yana dukan hancina.
Tun daga bugawar zuciyarsa na tabbatar wannan ruhinne wanda yake tamkar haske a baƙar duniyata,ba abinda zuciyata take muradi sai kasancewa dashi a kowanne lokaci.
Duk da nisanta dashi yana cutar dani amma babu yanda zanyi,domin idan na kasance mai yi wa ruhin soyayyar gaskiya,toh bazan so ifiritan ta suje jikina su cutar dashi ba.
Hannuna na kalla wanda farcen yayi tsawo yana zubar da jini,ga kuma gashin kaina dayayyi wani tsayi kaman na sabuwar fatalwa,ɗaga idona nayi na kalli ruhin daya shigo ɗakin,tun daga idonsa ya nuna bayason kallona a wannan halin,saidai babu yanda zayyi,domin hakan shine ƙaddarata,wanda bana tunanin zai iyah cika alƙwarin daya ɗauka na fiddani a cikin wannan halin.
Saboda duk maganar da suke ina jinsu,yanda yake fadar zai iya komai duk wahalar sa idan har zan samu lafiya matukar bai sabawa mahaliccinsaba.
Dawowa nayi daga tunanin dana tafi ganin ya wuce wani layi a gabana yana shirin karisowa daf da inda nake,kallonsa nake da alamar gargadi wanda nasan ya fahimci mai nake nufi,amma kuma bashida niyyar juyawa da baya.
Hannunsa yasaka a kunkumina tareda jawoni zuwa jikinsa ya kankameni,a duj tsawon zamana a wsjen yau ne kadai najj wani abu wai ita nutsuwa ta jiyarci jikina,sannan bakin dana dulmiye a ciki yafara wsshewa ina kallon hasken daya zomin dashi a gabana,har na samu kaina dason yi masa magana saboda abinda naji yana cewa,
"Kiyafemin sameemah,koda kowa zai ji tsoron zuwa inda kike ni bai kamata na yi hakanba,ko umma idan tana kallo bazata yafeminba saboda nima na taak rawa wajen zamowarki haka dana kasa rike ragamar kulada ke wsnda aka bani.
Sameemah inasonki sosai,har yanzu ban fidda ran zaki dawo gareni muyi rayuwar da muke da burin yi ba,kiyi yaki da abinda yake jikin ki sameemah,karki bari suyi galaba akanki,ke jarumace nikaina nasani matata jarumace,zaki iya sameemah kituna muna jiranki zamu iya komai dan gsnin kin fita a wannan kangin da izinin allah,amma zaman ki a wajennan yana cin zuciyata,komai nafara idan na tuno inda kike bana iyawa ..............."
"Yyyyyyaa.....sssammmeerrr".
Saurin dagowa yayi ya kalleni dayaga nayi magana,abinda bai taba tsammaniba,duk da maganar bata fita sosai ba kasancewar na dade banyi ba amma nasan yagane abinda na fada ,nima naji dadin hakan dana ga yaji sunansa dana ambata.
Hawaye naga ya ciko a idonsa sai kuma naga yana murmushi,kai na yarike yasake rungumeni a jikinsa yana fashewa da kuka,dago kai na nayi kafin na dage nace,
"Wanke jiki datti banaso sune suke so ni banaso,ka wankemin datti banaso ba dadi datti jikina da jini"
Saurin kallon jikina yayi da alamun ya gane abinda nace,tsugunnawa yayi wajen kafafuna inda jinin daya fito daga jikina ya daskare babu dadin gani,duk da banajin komai sai karnin jinin mutane amma nasan akwai wari a tattare dani.
Sautin wata zuciyar naji tana matsowa inda nake,wacce take saka firgici a cikin rai na,gurgana nin danayi ne yasaka sameer dagowa ya kalli bakin kofar,tashi yayi tareda tsayawa a gabana yana kallon malamin.
"Meyasa kashigo har nan wajen sameer,bakasan hadarin hakan ba ko?"
"Ba abinda zai faru malam,saida ina ga yakamata a tsaftace mata jikinta,dan tace dattin yana damunta,ga kuma al'ada da tayi a jikinta"
"Yaushe tayi maka magana da har ta fadi hakan,idan magana zata fito daga bakinta to ba yaren dazaka gane takeba,sunayine dan a kuncesu"
"Amma malam da hausa tayi magana,kuma tace wai kazanta suke so ita bata so,kuma suna kara karfi a hakan"
Shiru malamin yayi kaman mai zullumi,nikuwa fargabata kar ya kori sameer daga inda nake ,ajiyar zuciya nayi danaji yace bari ya nuna mana bandaki,amma sai an zagaye dakin tukunna da tsari.
Juyowa sameer yayi tareda since igiyar datake hannuna,yi nayi kaman zan fadi naji ya rike ni gam a kirjinsa ko kyankyamin bayaji.
Irin daukar amarya yayimin tareda nufar dakin da aka nuna masa,a jiyeni yayi a gaban wani baban baho wanda yake cike da ruwa.
Kayan jikina yafara cirewa a hankali,har yagama rabasu da jikina.
Wani cup ya dauka a gefe yana debo ruwan yana wanke abinda yayi cinyoyina zuwa kasa.
Lumshe idona nayi ina jin azabar da ruwan yakeyi akan fatata saboda na hadashi da wani abin,da kuma sanyin da hannunsa yake haifarwa akan fata ta yana maye gurbin zafin.
Bayan yagama wanke dattinne ya daukeni zai sakani a cikin ruwan,hannunsa na rike ina rokonsa da idanuwana,murmushi yayi kafin yace,
"Kiyi hakuri kinji,babu abinda zai faru kisaka hakan a cikin ranki,komai zai zo da sauki,ina tareda ke kinji"
Sauke ajiyar zuciya nayi kamin yasakani a cikin ruwan,ina kallon yanda yake kallon jikina amma haka ya kawar da duk abinda yake cikin ransa ya wanke ni tass.
Wani kaya ya dauKa masu duhu ya sakamin.doguwar rigace amma tana da laushi sosai.
Motsin shigowar wani naji hakan yasa na matsa jikinsa da sauri ,shima ya rungumeni yayi sosai wanda hakan yasa naji nutsuwa a cikin raina.
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎43~44💎
💎*sameer a madubin gani*💎
Tun lokacin da sameemah ta fada cikin hali na rashin lafiya ban taba jin tsoronta koda da na minti daya bane,saidai zamanta a wajen babu mutane a kusada ita yana cimin tuwo a kwarya,musamman kazantar wajen.
Bayan na gama yi mata wankan na saka mata kaya kamanta har ya fara dan dawowa duk da kowaye ya kalleta yasan ba lafiyar ta kalau ba,ita ma kanta naga taji dadin tsaftace jikin.
Karar shigowar mutunne yasa ta manne a jikina kaman wanda za'a yankata,har yaron malam din ya kawo ruwan magani ya ajiye amma bata dago idonta ba.
Kawowa nayi kusan fuskarta amma ta hade rai tareda kawar da baki,nima bata fuskar nayi tareda nuna mata da gaske nakeyi,saida taga ina kokarin cireta daga jikina kafin tayi saurin kaiwa ruwan maganin bakinta,shima tana hawaye da kuma cuno baki.
Kurba biyu tayi ta mayar da kanta kan kirjina tayi shiru.
Lokacin danazo tafiya rikeni tayi tana gunzin kuka kamar ana zare ranta,kallon malamin nayi nima zuciyata a karye,dan har ga allah banason barinta nima,sunkuyar da kai yayi kafin yace,
"To gaskiya sameer ban san ya zacayi ba amma fitarta waje a kwai hadari sosai,baga iyah mutane ba harda ita kanta,saboda zamanta ananne yasa har take iya control din kanta wani lokacin,amma idan ta fita gaskiya rabata dasu ba abune mai sauki ba"
Nima kaina na fahimceshi,haka duk da zuciyata tana so amma na cireta daga jikina na fita da sauri,dan banason jin ihunta kuma tanayine danni ba dan kowaba.
Haka Har rayuwa ta sake daukar mu zuwa sati biyu,amma babu wani cigaba sosai,kullum ina zuwa na dubata nayi mata wanka sannan na bata magani saboda ni kaidaine take karba tasha a wajena batare da anyi mata dole ba.
Idan ka ganta fes da ita amma wani lokacin sai fatar jikinta tayi duhu gashinta ya tashi,to a lokqcin ne muke gane cewa ba ita bace.
Kowa hankalin sa a tashe yake,saboda yanayin da sameemah take ciki,har saleemah ma takan damu tazo ta ganta,idan tazo tayi da kuka kenan tana lekata,ummee kuwa ba'a magana,dan in ka ganta ta bar kan sallaya to wani uzurin zatayi.
Ranar ina office malam ya kirani akan wata magana,da sauri nabar abinda nake nayi hanyar gidansa.
Ina zuwa na tarar su baba umaru da su ummee a zaune da alama kowa yana wajen ni ake jira.
Kallona yayi tareda cewa,
"Wato abinda yake faruwa sameer shine,malamina ya dawo daga sudan jiya,wanda nake da niyyar turaku wajensa,saidai ba anan yake zaune ba yana cikin kauyene,sannan fita da ita zuwa can akawai hadari sosai,zakuyi matukar kokarinku wajen ganin kuna tareda ita kafin a isa can din,kar ku bari ta bace muku ku rasata a jejin zuwa wajensa. Idan kukaje kuce nina turoku munyi magana dashi akan matsalar,inshaallah za 'a samu dacewa da izinin allah,amma fah saikun kula sosai,karku bari a samu matsala idan ba hakaba kuma bazata taba warkewa ba sai wani tsananin ikon Allah"
Tunda mukaji yana wannan gargadin munsan ba abune mai saukiba,saidai munji mun gani inshaallah zamuyi da izinin allah.
Shirye shiryen tafiya wajen maganin muka fara,dani da ummee da alhaji musa da kuma baba umaru.
Muna shirin tafiyar ne wani labarin daban shima yazo mana wanda yasa muka daga tafiyar zuwa bayan kwana uku.
💎*Sameerah a madubin gani*💎
Yanzu zaman mu da ummaruje babu yabo babu fallasa,an cire masa karfen dake kunkumin sa yanzu yana tafiya da kansa,ba said da wheelchair ba,saidai har yanzu wani abun sai a hankali tunda dama ba sona yake da farkoba duk da yanzu naga zuciyarsa tana karkatowa wajena.
Hajiyah mairo ma ta daina abinda take,dan idan na tura umaruje muka je falonnata hira har sai mukai sha dayan dare,wani lokacin harda salma ake idan jinyar cikinta ya daga mata.
Dan ba karamin wahala take sha ba,koyaushe cikin zuwa asibiti akeyi,wani lokacin ma hajiya mairo ce take kaita idan alhaji bayanan,yanzu ba karamin tausayinta takeji ba,dan dui mai guntun imani idan ya ganta zai tausaya mata matuka.
Ranar da umaruje ya fara tafiya har yar walima hajiya mairo da hada saboda murna da farinciki.
Gaskiya kam munyi murna sosai ganin cigaban da ake samu,musamman ma shikansa uban gayyar,yagaji da zaman gidan ba wajen zuwa,a ranar ne kuma alhaji bala yabashi takardar aikin daya sama masa wanda zai fara zuwa wani satin.
A zaune muke da daddare ina gyara kaya shikuma yana kan gado,hankalina ya tafi wani daban ban kulaba said jin hannunsa nayi a bayana,juyawa nayi ina kallon idanuwansa wanda suke dauke da yanayi kala Kala.
"Kiyafemin abinda nayimiki sameerah,tabbas ba shedar mutum daga farkonsa ko kuma daga waje said na zauna dashi,sannan baka gane mai sonka sai ka shiga wani hali,nikaina shaidane akan son dakikemin sameerah,fatana allah yabani iko nima na soki na baki farinciki kaman yanda kika sadaukar da farincikinki domin zama dani duk da kinsan bazan baki abinda kowane miji yake bawa matarsa ba na d'a"
Saurin saka hannuna nayi a bakin sa tareda cewa,
"Wayace naka baka bani farincikiba ,kaine ka bani farinciki tunda har ka yarda na zauna tareda kai,duk da kana da damar nesantani da inda kake,ba abinda nake bukata daya wuce muyi rayuwar farinciki kaman yanda kowane ma'aurata sukeyi,y'ay'a bayarwace ta allah ba akanmu aka fara hana haihwa ba kuma ba a kanmu za'a kareba"
Runugmeni yayi kaman zai maidani cikinsa yayinda nima nayi yanda yayi din.
Hayaniya mukaji a sashen su salma hakan yasa nasaka hijabina akan kayan baccina muka fito nida umaruje.
Hajiyah mairo ce rike da salma alhaji bala kuma yana binsu a baya.
Asibiti muka nufa inda akayi dakin haihuwa da ita da sauri.
Muna nan zaune har akayi sallah gari ya waye amma babu alamar sauki a lamarin,sai ihunta damuke ji kawai da nishi.
Zuwa rana su inna karima sunzo harda inna larai,dukkanmu kowa jikinsa yayi sanyi ganin halin da take ciki.
Ganin ana shirin kwana biyu amma babu alamar haihwar ne yasa likita ya nemi alhaji bala yasaka hannu ayi mata aiki kawai.
Hakan kuwa akayi muna gani aka wuce da ita dakin tiyatar ko motsin kirki batayi sosai,fargaba bazata fassaruba a wajenmu kowa yayi kozai kozai.
Muna nan zaune nurse ta fito da yarinya a hannunta an nannadeta a towel,katuwa da ita cikin koshin lafiya.
Karbarta nayi da sauri saboda nice a bakin kofar,kallon yarinyar nake wanda take kama da umaruje sak,mamakin hakan nayi saidai dana tuna kaman alhaji bala suke sai koma tunanin wani abu daban na ya halin da uwar y'ar kuma take ciki. Tun kafin nayi magana nurse din tace,
"Wacece sameerah,mai haihwar tana nemanki keda mijinta da kuma mahifiyarta"
Da sauri nabi bayan nurse din gabana yana bugawq saidai bansan mai yake faruwa ba.
A kwance take akan gado da kayan marasa lafiya a jikinta,karisawa wajenta nayi ina rike hannunta,murmushi tayimin na dauriya kafin tace,
"Anty sameerah kinga yarki dana haifamiki koh?,ban taba tunanin a duniya zaki kasance yaya a gareni mai son farincikina ba saida na samu kaina a inda ke kadai nake da ita,ina alfahari dake,to nasan Y'a ta ma idan yakasance tana karkashin kulawarki bazaki bari wani ya lahanta rayuwarta ba sai inda karfinki ya kare,dan haka ni salma nabaki Y'a ta dana haifa halak malak kece mahaifiyarta ban yadda ta nemi wata uwaba bayan ke.ki yafemin abinda nayi miki sannan ki taimaka wajen nema min gafara a wake duk wanda na zalunta"
Kuka nake son yi ko kuma zuciyata ce takeson tsayawa na kasa tantancewa,mai salma take nufi ai wasiyya takemin yamzu haka,ina kallom sanda ta daga kanta tana kallom mijinta da kuma mahaifiyarta wanda suma sun so daurewa amma sun kasa yin hakan.
Kai na narike wanda yake barazanar fashewa saidai babu yanda zamuyi muna kallon sanda numfashi na karshe ya fita daga cikin huhun salma,ta mutu kenan ta bar duniyar kamar bata taba wanzuwa a cikinta,saidai hotunan ta dakuma tunanin ta acikin zukatan mutanen da tayi rayuwa dasu.
Hannunta data rikeni ne ya shika yayi samyi kalau kaman ba nata ba.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun
Kullu nafsin za ikatul maut
Haka Muka fito daga dakin da take kwance babu mai cewa wani abu a cikinmu.
Gawar muka karba muka nufin gidan mijinta domin ayi mata sutura a can,kowa ka gani mutuwar ta bugeshi ba kadan ba ,musamamn mu da muke zaune da ita.
Ina runtime da yarinyr a kirjina ,duk duniya ji nake babu wanda zaizo yarabani da ita,idan kuwa yace dole sai yayi hakan to saidai yafara ta kaina tukunna.
Kwananmu uku muna karbar makoki amma sameemah bata zoba,iya yah sameer ne ya taho da kuma anty saleemah,sai wata mata itama mai kama da sameemah,nan ake bada labarin mahaifiyarta ce kuma kanwar mamar antu saleemah,har ma da rashin lafiyar da sameemah takeyi na bata gane komai,ni dama banyi mamaki ba dan ni kaina shaida ce sameemah ba ita daya bace,dan haka fatan samun sauki mukayi mata.
Abinda mukafi girgiza dashi shine ashe mahaifinta ne sanadi kuma tash wahala tun tana yarinya na kokarin boyewa da kuma halayyar da takeyi dan ta nesanta yan uwanta daga garets,hakika ta bani tausayi matuka,ashe duk abinda muke cikin duhun kai,bamuyi amfani da lokacinmu da muke tareda ta hanyar da ta daceba ,mun cutar da kanmu mun kasa fahimtar matsalarmu har saida mukayi nesa da juna lokacij babu wanda yake gani kowa kafin muka fahimci kuskuren da muka tabka na asarar lokaci.
Tare muke kwana da zainab wanda itama d'anta yayi wayo sosai,dayake suna jigawa wajen aikin mijinta sai sanda suka zo tukunna.da kuma anty saleema sai jinjira salma wanda aka maida mata sunan mahaifiyarta, duk kukan takemin bana gani sai ma kuka danake sakawa,sainaga kaman mahifiyata take nema,saida su zainab suka nusar dsni akan dole na jajirce daure damamrar zama uwa ta gari ,sanann na runtse ido na hukuntata idan batayi dadai ba nan gaba,ta hakane kawai zan yi mata tarbiyya sabanin yanda akayi mana.
Saida akayi sadakar bakwai kafin kowa ya watse ya barmu dagamu sai mu,ni kuwa nacigaba da rainon little salma dan ba a boyemata sunaba.
Shikansa umaruje yana zon yarinyar a ransa,dama jininsa ce yanzu kuma zai reneta tamkar yar sa..........
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎45~46💎
💎*sameer a madubin gani*💎
Hakika lokacin da mutuwar salma ta doki kunnen mu ta gigizamu matuka.Tabbas mutum ba a bakin komai yakeba ,duk abinda kake allah yana kallonka.
Shirin da muke na kaiwa sameemah wajen magani muka bari domin zuwa gida gaisuwar mutuwar salma.
Tunda muka je kullum said nayi waya na tambayi ya jikin sameemah,saidai maganar daya ce kullum saukin bahaushe.
Bayan sadakar uku muka taho saboda kowa yasan halin da muke ciki na jinyar sameemah.
Bamu muka iso garin porthacourt ba sai wajen karfe takwas na dare,a lokacin na ajiye saleemah a gida na nufi wajen sameemah,itama saleemah bani gaisuwa tayi akan na kaiwa sameema duk da tasan ba amsawa zatayi ba.
A zaune na sameta a dakin da ake killaceta ta sunkuya kaman wanda tayi bacci,tausayinta ne ya kamani musamman ganin kayan dayake jikinta tun wanda nasaka matane kafin mu tafi,banyi mamaki ba danna san bazata bari wani ya matso kusada ita ba,ga duhu da kuma sauro,wannan bai sa na damu ba saboda nasan ba cizonta zasuyi ba.
Karisawa nayi gavanta na tsugunna,dagowa tayi a hankali tana kallon fuskata kaman mai nazarin wani abu,can kuma sai ta rungumeni da karfi,da alama tayi kewata dayawa,hakan yayimin dadi ba kadanba,duk da halittunta da siffarta sanjawa suke da kadan kadan amma hakan bai sa kida da rana daya naji kyamar matsowa inda takeba,saima tausayinta dayake kama zuciyata.
Cikin dabara kaman ko yaushe na tsaftace mata jikinta kafin nasaka mata rigar ta,banyi niyyar barin wajenta ba dan na kudiri niyyar gobe zamu kaita wajen malamin da aka turamu wajensa.
Washagari da safe nayi nayi taci wani abu amma taki kulani,nima nasan bazata ci ba kawai gwadawa nake ko za'ayi nasara wani lokacin,muna cikin hakanne su ummee suka zo tareda su alhaji musa,har da inna ramatu wacce ta biyo baba umaru dan taga jikinnata.
Suna hada ido da sameemah tayi kanta da sauri tareda kaman kafarta da garzamata hakoranta,ihu take tana kara amma bata sauta ba saida muka hadu tukunna.
Lashewa bakinta take wanda yayi ja da jinin inna ramatu kuma tana murmushin mugunta,kokarin komawa takeyi amma su baba umaru suka dauki inna ramatu zuwa asibiti dan suma tayi dan wahala.
Ba karamin rauni sameemah tayi mata a kafa fa hadda cire mata naman cinya.
Dukkan mu mamaki mukayi da abinda ya faru,sai a lokacin na kula ba abinci take bukata,so take ta dunga cizon mutane amma kuma ta kasa cizon wanda suke masoyanta.
Wani ruwan magani aka sake yi mata wanka dashi wanda zai saka jikinta ya shika kaman bata da laka,sannan akasaka wani sasari a