Showing 6001 words to 9000 words out of 53080 words

Chapter 3 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt

05 Nov 2024

13048

kuma boye ta?"
"Dazan iyah hakan danayi tuntuni,ku tafi kawai wannan shine iyah abinda zan iyah,zanyi mata alkhairi daga inda nake ma"
Tana gama faɗamana hakan tah juya cikin gidan da sauri,hawaye yana zuba a idonta amma sai ƙoƙarin hanasu zuba takeyi,saidai ko daga ganinta tah ɗan aamu nutsuwa data raba ƴarta da koma menene yake tunkarowa.


A daren muka fara tafiyah har da gudu gudu,domin muma babu abinda yake cikin ranmu sai ƙoƙarin ƙubutar da rayuwar baiwar allah da take bacci a bayan hajara,batasan ma me akeyi a duniyarba.
Kafin gari yah waye har mun kai wani kauye dayake kusa da bauchin a hanyar gidanmu,tsaywa mukayi domin hajara ta huta saboda gajiya ga kuma goyon yarinyah ƴar shekara biyu.
Anan muka tsaya muka sayi ƙosai muka ci,kafin muka tsaya jiran motar garinmu a wajen.
Cikin sa'a kuwa saiga mota bata cikaba muka shiga sai gida.
Da tsakar rana sai gsnimmu akayi babu tsammani,sai tambaya suke mai yasa muka taho yau bayan sai wani satin,cawa muka kamawa takeyi kawai,sauran mutan gida sai tambayar hajara suke akan suga ƴartata,ba musu kuwa ta sakko da sameemmah wanda take tah bacci abinta,jin hayaniyane yasata farkawa,aikuwa tana ganin inna Hauwa matar mumkaila wanda amaryace a lokacin zata ɗauketa tayi saurin maƙalrewa a jikin hajara,tana kukan rikici.
Kowa mamaki yakeyi da kyau irin na sameemah har ma kyau na kayan jikinta,marasa haƙuri kam ma har saida suka yi magana irin su inna ramatu.
Nidai daga ni har hajara babu wanda yace wani abu,sai sunane muka ce musu an samu sabani ne sunan ta sameema ba maryam ba kaman yamda aka faɗamusu,dan haka bamu sha wahala ba wajen boye ainihin tarihin sameemah a wajensu.
Tun daga lokacin sameemah ta ware tamkar ƴar gida,dan dama ta saba damu sosai musamman ma hajara.
Shekarar sameemah huɗu hajara tah dara ciwon ƙafa,wasa wasa ana tah magani amma ciwo sai gaba yake yi,sannan nikuma kulawar danake bawa sameema sai yah fara zuwa idon mutanen gida,hakan yasa dana ga za'a samu matsala na fara ja baya da lamarinta ba kaman da farko ba.
Haka na shigaba da kulada itah,har zuwa wasu shekaru inda tace itama ga garinmu.


Wannan shine iyah abinda nasani a game da abinda yake faruwa,
Ina mahaifin sameemah bansaniba kawai nasan yana aiki a india sannan kuma mahaifiyarta bansan koh tana rayeba,dan maganar da take yi mana kaman wasiyyah haka take yinta.
In kuma tana raye bansaniba,dan nasan danginta amma ban san a wane gari suke ba,abinda nasani shine itah ba ƴar garin bauchi bace kawai.
Amma tabbas tah kargaɗeni akan kar na sake na barki kije garin bauchi.


💎~~~💎


Yana kawo nan a labarin sa saida kowa ya zubar da kwallah na tausayin hajiyah maryam da kuma tunowa da mutuwar inna hajara musamman ma inna rabi an taso mata da tsohon mikin mutuwar ƴar uwarta mai sonta,banda sameemah wanda fuskarta babu alamar rauni a cikinta,saima kallon gefe da tayi kawai.
Tashi baba umaru yayi ya ɗauko wani ɗan akwati ƙarami ja.
Buɗeshi yayi da wasu lambobi yah ciro wani kati a ciki,na shaidar sumun asusu a banki.
Miƙawa sameemah yayi tareda cewa,
"Wannan shine abinda mahaifiyar ki ta bamu akan cewa mu baki idan kin girma ko kuma muyi amfani dashi,saidai bamu taba ba dan aduniya babu abinda bazamu yiwa jinin hajiyah maryam ba,dan tayi mana abinda bazamu taba mantawa dashiba.




Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150


Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.


💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎










*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*




💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}






💎7~8💎






💎*Sameemah a madubin Gani*💎






Duk abinda yake faɗa ina sauraronsa,har yah ɗauko wani akwati yah miƙomin wani kati wai inji mahaifiyata,dan kuwa wai ne,dan jin zancennasa nake kaman a mafarki,kar ba nayi ina kallon katin batareda nace komai ba,sukuwa sai kallona suke dan ganin mai zance,inna rabi kuwa idonta yayi luhu luhu na munafurci,saika ce addu'a take wa ƴar uwar tata idan ka tsareta,kowa sai munafurci na iyah shege.
Tsallakewa nayi na fita a ɗakin na barsu sai ta'ajjabinsa sukeyi wanda bashida dalili,babu yanda za ayi na tsaya wannan abu tunda na samu abinda nake buƙata shikenan kawai.
Kayan aikin na cire badan na soba,duk da ina da taurin kai amma idan na ɗau alkawari nakan iyah ƙoƙarina dan naga na cikashi.
Ninke kayana nayi na adana dan ban cire ran cigaba da,aikina ba koda nan gabane kuwa.
Inna rabice tah shigo ɗakin har sannan idon ta bai washeba da kukan munafurcin,dan haka sukayi a mutuwar ummah ɗin,duk wanda yagansu sai yayi zaton idan dare yayi kwana zasuyi suna yi mata addu'a,amma kowa ana yin sallar isha ta sau baki tayi bacci.
"Yamzu kam tunda kinji mai akace sai kizo kuka ki tsefe wanan kan kuma da kuma lalle saboda yin kwallliyar amare kaman kowacce amarya idan za'a kaita ɗakinta."
Kallonta nake ina mamakin katsalandan irin na wannan matar,itah ko gajiyah batayi da shiga rayuwar mutum,narasa ma mai zan mata ta rabu dani,dan nakula koh zuciya batayi koh wacce irin magana mutum yafaɗa mata.
Ko magana banyi mata ba na jawo system ɗin na fara wani aikin,dan shiru ma amsa ce idan tana da hankalin hakan.
Aikuwa haka tah fita,nayi zaton tah haƙura ashe nacinta yah wuce hakan ashe,dan kuwa dawowa sukayi da baba umaru,
"Meyasa kika kasance mai taurin kai ne sameemah,kince idan aka faɗamiki mai yake faruwa zaki amince kibi mijinki gashi yanzu kuma an faɗamiki amma har yanzu abu bai sanja zani ba"
Toh tanan suka bullo kuma,mai yasa akeson takurani ne haka,kullum hankakin kowa yana kaina dole sainayi abinda yake so,wai baza'a barni na yi abinda nakeso bane?,ɗago kai nayi na kalli baba umaru tareda cewa
"Toh shikenan naji zanje wajen kitson amma daga nan bazan karbi koh komaiba,sannan bayan shi babu abinda zan sake yi,koda kuwa me zakuyi kuwa"
Dan nasan idan ba haka nayi musu ba zancen bazai wucewa,jijjiga kai kawai baba umaru yayi kafin yabat ɗakin yah barni daga ni sai inna rabi,wanda duk tabi ta takurawa rayuwata.
Haka babu yanda zanyi na ɗaga wayah nakira burgu sabon ango,shima saida yayimin tsiyah tukunna abinda banaso kafinnan na faɗa masa saƙona kan ya turomin mai kitso da fulawa,amma kar ta daɗe,dan idan yakai yamma na fasa.
Saida yah sheƙe da dariyah kafin yace,
"Amaryah amarya ranki yahdaɗe amaryah,da girman kujerarki amaryah a wajen ogah sameer gashi..........."
Ban gama jin abinda yake faɗaba ba kashe wayar dan ba abinda nakeson ji ba kenan.




💎* Sameer a mdubin gani*💎




Lokacin da baba umaru ya,gama bada labarin abin yayi matuƙar ɗauremin kai sosai,dan tsawon wannan shekarun kallon sameemah nake a matsayin ƴar uwata ashe ba haka bane,dan yanzu gashi lamarin yayi zuwa yanda bana tsammani na samu kaina da zama mijin aure a wajentah,tabbas ina cikin cakwakiyah na wanne irin zama zamuyi da itah a can tukunna,danni shaidane bata tankwasuwa gata da ɗan banzan rashin mutunci na bugawa a jarida.
Duk labarin da aka bayar kamata yayi tafi kowa shiga cikin damuwa amma koh a jikinta saboda gasheshshiyar zuciyah ce da itah,sam baka sanin mai yake cikin ranta,nine zan zama shugaba aknata ko itah ce shugabar,saidai kowa yayi rayuwarsa dan allah yagani bazan takurawa kaina ba.
Ganin wani karbar katin da tayi a hannun baba umarune tareda ficewa a ɗakin yasa kowa yah bita da kallo,nima ganin hakane yasa na tashi domin shirina dan yau zan koma gida,dan na samu abinda zan saita kafin zuwanta nan da kwana uku.
Ɗakin da kayana yake na nufah,duk lakar da take jikina ta shika,banda faɗuwar gaba ba abinda kirjina yake yi,danni kaɗai nasan irin matsalar dazana fuskanta.
A katifar ɗakin na zauna,nafi awa guda kafin na fito da jakata a hannuna na nufi ɗakin ƴanmatan gidan inda sameemah take,yau ne karon farko da shigata ɗakin tun bayan raauwar ummah a ciki.
Tsayawa nayi ina kallon cikin ɗakin bayan nayi sallama.
Saidai ko sallamar bata amsaba bare tah ɗaga kai ta kallleni,uhmmm nafaɗa a raina.
"Ina sallama keba musulma bace bazaki amsaba,koh nima tsiyar taki zakimin dan kin rainani"
Nan ma bata kalleshiba sai amsa sallamar da tayi kawai,katin cire kuɗi na fitar a aljihuna na miƙa mata tareda cewa,
"Gashi wannan ki sayi duk abinda kike buƙata,saidai karki sayi sutura koh kuma abin amfani dukka akwai acan,idam ma da wani abun ki kiranj ki faɗamin"
"Bana bukatar kuɗinka saboda ina dashi basai ka baniba,kuma duk abinda nakeso zanyi ba wanda wani yakasaniba tunda babu wanda na dogara sashi bare yayi min yadda yaga dama"
"Dama badan kina dashi na bakiba,na bakine saboda kina da hakki a kaina na hakan,sannan karkiga dan zakizo gidana kinemi yimin tashin hankali ina gargaɗinki da ki shiga hankalinki"
Sabanin abinda na tsammata tayi,dan iyah murmushi tayi na gefen baki wanda sai mutum yah kula kafin yagane shi.
Nima juyawa nayi na fitah daga gidan zuwa cikin motata,baba umaru dama munyi sallama dashi ɗazu,bazan iyah sake tsyawa ba kuma,dan anyimin abinda kwata kwata naji babu abinda nakeso sama da bawa garin baya kk zanji sanyi a raina.
Tun a hanya kiran saleema yake ta shigowa,ina gani naƙi ɗauka dan tun ranar ɗaurin auren take ta ƙirana tun ina amsawa har na daina.
Kafin na isa gida saida tayimin ƙira ya kusa goma ina katsewa,dan idan na ɗauka bansan mai zan ce mata ba,dan haka kawai na barta idan na ja koma menene zanji daga gareta.
Banfi shafe wasu awanni masu yawa ba na isah garin porthacourt sakamakon gudun danakeyi yah wuce na hankali,burina na isa kawai domim nasan mai zanyi.
Ina shiga sojojin da suke bakin kofar suka buɗemin na wuce,tun daga bakin falon na tabbatar cewa na daeo gida,hakanma farfajiyar hajiyah saleema,dan komai da gindinsa yake zaune a falon,duk da babu datti amma fah babu tsari ko kaɗan irinna na ɗakin ƴa mace.
Fitowa tayi daga ɗaki muna haɗa ido da itah,babu sannu da dawowa bare yah hanya sai ƙorafi dayah min sallama,na kashe mata wayah danayi.
Dan takaici ba tsaya yi mata wani bayani ba nayi hanyar ɗakina,ina jinta tana biye dani har sannan bata daina ƙananan maganganu ba,jin abin zai min yawa goma da ashirin yasani dakatar da itah,tareda cewa,
"Dan allah saleema ki barni na huta tukunna koma menene sai tambayeni ,amma yanzu bakya ganin daga hanya na dawo,babu sannu da dawowa bare ruwan sanyi sai aukin ƙorafi,wai yaushe zaki sanja ne?"
Jumbura daki tayi irinna sakalai kafin tace cikin muryar shagwaba,
"Haba honnnney,yanzu hakama zaka ce dan gaka ina damuwa da kai,fisabilillahi tun yaushe ka bar garinnan,sannan tun kwana uku da suka wuce yakamata ace ka dawo,amma baka dawoba sai ma kashemin waya dakayi bayan na ƙiraka,wai meyasa kake min hakane "
"Ni babu abinda nayi miki saleemah,kawai akwai abinda yasa na tsaya ne,kuma idan kikayi haƙuri inna zauna zan sanar dake,domin kema yah shafeki"
Daga haka na juyah na wuce ɗakina ina riƙe goshina,wanda nakejij kaman zai iyah darewa a kowanne lokaci.
Wanka na shiga naji ɗan dama dama,ina fitowa na samu saleema a bakim gado tana jirana,ban yi mata magana ba sai da na shiryah kafin nazo na zauna,anan na kula ashe abinci ta taho dashi,ta wannan bangarenne kawai take burgeni,dan idan na faɗamata abu tanayi,sannan kuma bata fiye yimim musuba,barta dai a shagwaba kam har da ta siyarwa.
Jawo kwanon abincin tayi tah juba,duk raina bayaso saboda na ƴan aikine,ita kuma babu dama tah dafa abinci da kanta,wannan sam ya zama abinda tah maidashi haramun a gareta.
Kaɗan naci kafin na ajiye cokalin ina kallonta,wanda tunda nafara cin abincin ta tsura min ido tana kallona,
"Uhm ......dama saleema akwai abinda nakeson baɗamiki,kar lokaci yaƙure ban faɗamikiba kice ban kyautaba"
"Uhm ina jinka honey mai yah faru ne?"
"Da farko kinsan ni mijine ke mace sannan kuma an halattamin auren mata guda huɗu idan ina da dama koh?"
"Tsaya tsaya haka,banason jin wanann bayanin gaskiyah,dan wallahi babu kishiyar dazaka yimin ana zaune kalau,nasan ma bazaka yi ba ai,dan haka a bar wannan zancen"
"Amma yah kamata ki dunga tsayawa kina jin karshe magana,dan aure ba zancen za'ayi bane an riga anyi ne,dan yanzu haka ma amaryar jibi za tare kuma samee.............."
"Karka cigaba da faɗin abinda kunnuwana bazasu iyah ciggaba da jiba sameer,me kake nufi,aure!!!,kuma ma har an daura,nan da wasu kwanaki matar zata zo ta zauna a gidana,kuma itama tah mallakeka kaman yanda nakeyi,inaaaaaa hakan bazai taba yiyuwa ba kama canja zance amma ba wannan ba ............kasan mai kake faɗa kuwa??"
"Nasan mai nake faɗa mana salee............"
Tun kafin nagama magana ta watsamim wani kallo wanda tunda nake bansan ta dashi ba ta bar ɗakin da sauri tana bugomim ƙofar ɗakim kaman zai karye.
"Yah salam"
Shine kawai abinda na faɗa,dannasan shikaɗai zai kawo min mafita akan abinda yake shirin tunkaroni.


💎*Sameemah a madubin gani*💎




Lokacin da mai lallen ta zo ma kaman bazan tashiba,da jinake wani baƙin ciki yana taruwa a cikin kirjin lokaci zuwa lokaci,samun waje tayi tah zauna ba kin katifar sameerah ta da,tana sunkuyar da kai kaman mai tsoron haɗa ido dani,ƙoƙarin katse shirun ɗakin nayi tah hanyar cewa,
"Miye sunanki?"
"Hamiddah"
"Karki yimin mai yawa,shima dan babu yanda zanyine kawai shiyasa zanyi"
Tasowa tayi tah fara haɗa kayan yin lallen,har tah gama.
Wata shawara ce tah kawo kaina cikin ƙanƙanin lokaci,aikuwa nayi shu'umin murmushi.
Bamu daɗe da farawa ba muka gama,dan cewa nayi tayimin zanen da tasan ba'ayi a lalle kaman zanen kwari da na su ƙadangare,kallona take da mamaki kafin tah fara abinda nacemata,dayake ta iyah zane kuwa,sosai hotunan ƙwarin suka fito kaman suyi magana harda kala ta saka musu,ɗaga hannun nayi ina kallon zanen yamda yah fito raɗau a hannuna,dan duk mai tsoro ƙadangare da kuma su dandoriyah to yana gani nhannu na zai fita da gudu,daɗi ne yah isheni koba komai zuciyahta tayi ɗan sanyi danayi tsiyah.
Tana gama lallen koh nace zanen tayi shiru tareda ɗan matsawa gefe,sai kallon abinda yake hannuna da kuma ƙafata takeyi.
"Ai baki gama ba,ina so kiyimin zanen maciji ya nannaɗe wuyana,ina zaki iyah?"
"Eh zan iyah anty"
"Yawwa toh yimin yayi biƙi sosaifah"
"Toh anty"
Ina gama faɗan hakan na cire rigata nabar iyah zani ɗaurin kirji,lallen da sake haɗawa kafin ta fara zanen
Wanann sai da ya ɗaukemu lokaci domin so nake ya fito kaman na gaske,aikuwa nima kaina sai da naga kyau na macijin,rai na fari tass yayi ganim abinda nake shirin aikatawa yah fara tafiyah yanda nake so.
Kuɗin aikinta na bata ta tafi,kitso kuma shagon gyara nake son zuwa saboda kawai abinda nake son aiwatarwa.




💎*Saleema a madubin gani*💎




Tun naji furucin daya fito daga bakin sameer mai kama da dafin maciji na tashi na tsaya,ji nake duniyar tana juyamin duk illahirin jikina rawa yakeyi ga kuma wani tashin hankali da baƙin ciki da suka taru a ƙirjina,numashina har sama sama yakeyi.
Ɗakina na nufah ina haɗa hanya dan ko hanyar idanuwana basa gani sosai,babu abinda yake amsa kuwwa a cikin kai na kalmar da sameer yah faɗa ta,aure aure kishiyah kishiyah.
Da ƙyar nasamu damar sakawa Zuhra riga(mai sunan mahifiyar saleemah,hajiyah Fatima)na sunkuceta sai bakin motata,shikuwa farouq bai dawo daga makaranta ba ta isilamiyya,idan yah dawo ubannasa yasan yanda zayyi dashi.
Ikon allah ne kawai yah kaini gida,sa'a ta ɗayah babu nisa duk a cikin barikin sojojinne,saboda girmansane yasaka ni ɗaukar motar dan idan na ce zanje a ƙafa toh zam iyah yin kusan wata a ganina ban ƙarisaba.
Ina kashe motar na fitah daga motar da gudu zuwa cikin gidanmu,har na kai bakin ƙofah na tuna nabar ƴata a cikin motah,da gudu na koma na ɗaukotah kafin na shiga cikin gidan.
Akan kujerar falo na dire zuhra dan ita haushinta nakeji ubanta yah shafamata,mai aikin gidan nagani zata wuce madafar abinci.
"Ke zo ki ɗauki yarinyar nan ki kula da itah sannan ki bata madara"
Zuwa tayi tah ɗauketa ni kuma na yi ɗakim mommy da gudu har ina tuntube,babu abinda nake buri sai,wanda zan samu na faɗawa mai yake faruwa,sannan kuma da wanda zai rarrasheni.
Ina shiga na faɗa kan mommy wacca take naɗe kayan ta ƙanana akan gado,kuka na rushe dashi wanda dama na daɗe ina riƙeshi,sai yamzu yah samu damar kwacewa yah fita.cikin shshshekar kuka nafaɗamata abinda yah faru.
Tana gamajin labarin tah tureni daga jikinta tareda cewa,
"Dallah ni matsa kiban waje,dan mijinki zai ƙara aurenne kike wannan kukan kaman wata sakaryah,ke kuwa kina hankali kuwa?,kai kai wallahi alhaji yajiƙa aiki daya shagwabaki,ya maida ke bakisan kinemi abu ki rasa ba,sanann ya maidake bakisan kiyi haɗaka da wani ba akan abin duniyah,saidai yanzu alhamdulillahi gwanda da yayi auren koba komai zaki koyi darasin haɗa abu da wata,kuma zaki san duniyah ba kullum abinda kake so kake samuba koh ake yi maka ba"






Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150


Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.




💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎










*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*




💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}






💎9~10💎






Matsawa nayi daga jikinta na bar ɗakin,da wanne zanji da kishiyar da akayimin koh kuma da faɗan da takemin,idan tana wani abun saikace ba itah ta haifeniba matar ubace,nidama nasan batasona kaman yanda abba yekiyimin,kullum cikin yin faɗa take da hantarata.
Kuma wallahi ban haƙuraba daddy yana dawowa zan faɗamasa,bazan bar gidan bama anan zan zauna har sai ya saketa tukunna kaman yamda ya aureta.


Ɗakina na gidan na nufah,ina kuma danna ƙiran wayar SUHAILAH,tsuka naja ganin tana ta ringing amma bata ɗaga ba sai daga baya kafin ta ƙirani.
"Sully kina ina ne wai,ina ta kiranki baki ɗauka ba,akwai matsala fah"
"Matsala kuma wace iri,banganeba mrs major,fayyacemin naji mai ake ciki"
"Hmmm ke miyema bai faruba aikawai sai kinzo,dan zancen baxai yiyuba a waya"
"Toh shikenan gani nan zuwa,dama yamzu na dawo daga makaranta,cin abincina kenan,bari nayi wanka nazo naji mai yake faruwa"
Ajiye wayar nayi bayan nagama wayah da suhaila,nasan ana jimawa zan ganta,safa da marwa na fara a ɗakin tsakanin kujerar madubi da kuma bakin gado,duk abin duniyah yah isheni,lokaci ɗaya har na rame na fitah hayyacina,dama haka mata suke ji idan za'ayimusu kishiyah?,tabbb gaskiyah abin babu daɗi,dole ne muyitah,koh ni koh itah,duk da bansan ma wacece ba.
Sai kusan magriba kafin suhaila tazo,ita kanta nasan a lokacin uzuri takemim saboda babu laifi tasha madifa tafi cikim kwando.
Itama bata wani bani shawara gamshashshiyah bah,duk daga nayi kwalliyah,na dunga jan ajina,sai kuma kar na bari tah rainani,kallon suhaila nake lokacin da take faɗan hakan,lallai bata san me ake jiba idan akayi maka kishiyah,dan taga batada mijinne bare kuma zancen yimata kishiyah,toh yaushe ma zan zauna da itah har nafara wannan shirmen na jan aji da kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login