Showing 42001 words to 45000 words out of 53080 words
Chapter 15 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt
gabana ba kadanba.
Hangar vandakin na nufa,duk da baraxanar bugawa da zuciyata takeyi amma haka nayi biris da ita na fara alwalar,yau na dauki alwashin gwada yaki da duk abinda yake cikin jikina.
Fitowa nayi na dauki hijabi a kan gadon ummee wanda take sallah dashi na saka,kafin na shimfida sallaya.
Tun daga hawa sallayar nakejin kaman nadora kafa akan wani abu mai zafi,amma haka na jure ina runtse ido.
Kabbara na tayar wanda ina ga ban tabsyin guda uku ba tsawon rayuwata,abinda yasa ban mantaba saboda anayinta a masallatai ne kullum.
Suratul maryam bakina yakama nafara karantawa,daga iyah aya biyu na yanke nayi ruku'u,ina jin kaina yana barazanar fashewa amma ban fasa abinda nakeyi ba,lokacin danakai sujjadane naji wata murya tansmin magana cewa,
~~Hakika kin Kaimu bango a yau,kina tunanin zamu sallamar da ruhin da anriga an yi mana kyautarsa,to hakan bazai yiyuba,daga yau zamu kasance mune zamu tinga control din gangar jikinki har zuwa nan da wata uku lokacin da zamu mallakeki ki rike matsayin dayake jiranki,idan kuma ba haka ba dole mu hallakar dake,yanzu ma dolene ki karbi hukunci~~
An gama fadar hakan naji wani zafi da kuma kara ya ratsa cikin kaina,hakanne yasa nima na zunduma tawa karar danima bazan iya zure azabarba.
💎*Sameer a madubin gani*💎
Yau kwanan sameemah biyar a gidan mahaifiyar ta, ko waya bamu tabayi ba duk kewarata ta isheni,duk da ba komai ne yake shiga tsakanimu ba amma ganinta kawai a cikin gidan yakan sa naji nutsuwa a tareda ni.
Hakanne yasa na yanke shawarar dama zanje wajensu ita da farouq sannan na gaishe da hajiyah maryam.
Hanyar gidannasu na nufa har na isa gidan,a falon na samu hajiyah maryam tana aiki a system tasaka glass,Murmushi tayi da taga nine,
"Lahhh ango ya biyo sawun amarya kennan,da alama kana kewar iyalanka,ya d'aya y'ar tawa take ita da mai sunan yaya ta"
"Lafiyansu kalau hajiya"
"Mutuniyar taka tana ciki bari na kira maka ita ko"
Dan sosa keya nayi dan dama hakan nakeso naji tace.
Ta ta shi kenan da niyyar shiga ciki,mukaji karar sameemah daga cikin daki,da alama wani abune yake faruwa da ita,da sauri dukkan mu mukayi dakin da muryar take fitowa.
Akan sallaya muka sameta duk gaban hijabinta ya baci da jini gashi dama mai haskene,saurin tallafarta mukayi nida hajiyah maryam muka nufi hanyar kofar gida wajen mota.
Da sauri muka turata zuwa dakin taimakon gaggawa,inda ummee tayi saurin sanja kayanta a office dinta ta shiga wajenta.
Muna nan tsaye zuwa lokacin kowa yazo yan uwa domin labari yah isa garesu.
Ummee ce ta fito daga dakin amma babu alamar nasara a fuskarta,alhaji musa ne yayi saurin tambayar mai yake faruwa,amma cewa tace bata farfadoba cikin karamar magana.
A zaune muke dukkanmu a office dinnata,
Dagowa tayi ta kallemu fuskarta dauke da damuwar halin da y'ar ta take ciki,
"To yanzudai bamusan mai yake faruwa ba,dan duk wani gwaji munyi amma babu abinda muka gani,gashi har yanzu bata farfado ba tukunna,saidai mu tsaya mujira mai zai faru.
Wasu sun tafi gida amma ni da hajiyah Fatima da kuma ummee a anan muja zauna domin ganin mai zai kasance,baba umaru ma an aika masa suna zuwa shida inna ramatu wanda tace zata zo ta gani saboda munafurci.
Ni kadaine xaune a gefenta akan kujera na kifa kaina akan gadon,can wajen misalin karfe dayan dare naji kaman hannunta dana rike yana motsi kamar a mafarki.
Saurin bude idona nayi na ga dukkan jikinta yana jijjiga,tashi nayi na tsaya akanta,a lokacinne naga idonta ya bude wanda babu alamar farar kwayar ido bakine sidik.
Wani mungun murmushi tayimin kafin tayi saurin tashi ta kama wuyana da wani irin karfi ta mannani a jikin bangon dakin,dariya taci gaba dayi da bakinta wanda yake bakikkirin,wuyana ta saita tana niyyar cizona ,har na lumshe idona na saddakar,saboda duk karfin mutum bazai iya kwacewa da wannan rikon ba,can kuma sai naji ta tsaya cak kuma tana huramin numfashi a wuyana,kaman wanda take yaki da wani abu a cikin ranta.
Karar budewar kofa naji dama na danna alarm danaga tana jijjiga.
Ummee ce ta shigo dakin wata nurse tana biye da ita a baya,
Jefar dani tayi a kasa kamar shamfora tayi kan ummee da wani sauri wanda ba nata ba,tsaywa tayi a gaban ummee tanayi mata kallon kaman yaro yana son gane mahaifiyarsa,har ta kama ummee sai kuma ta saketa da sauri ta kama wuyan wacce suka shigo da ita ta gatsa da karfi,ihuu ta saka na azaba kafin ta durkushe akan gwiwoyinta,daga baya kuma ta fadi summamiya.
Hanyar waje tayi tana nufin fita nayi sauri na tashi da dan karfin dayayi saura ajikina naje bakin kofar na tsaya inda zata wuce,
Wani kallo takemin na ranta ya baci amma ban matsa daga kofar ba,saima wayata dana ciro a cikin aljihuna na kira alhaji musa na fada masa ya taho da malami.
Tanajin abinda nafada tayi kukan kura da sauri ta nufi inda nake da niyyar bigeni ta wuce,saurin rike kunkuminta nayi tareda yi mata magana a kunne.
"Ki tsaya sameemah ki saurareni,karki bari koma menene yayi iko dake,kiyi kokarin yin abinda ya dace,ke jarumace sameemah kiyi amfani da jarumtarki,nasan kina jina kiyi kokarin saita kanki,nasan zaki iyah,kidaina cutar da wanda basu da laifi karki zama wacce zata kasance abar tsoro a cikin mutane"
"Ni ba mutum bace ni nakasance wata halittace daban,sannan zanyi abinda irina sukeyi,kadaina kusanto inda nake,inaso idan ka ganni ka gudu saboda ni dododanniya ce abar gudu ga kowa"
"Keba dododanniya bace,ke matata ce kuma masoyiyata abar sona,bazan taba daina sonkiba,sannan idan kina son ki fita ki cutar da mutanen to ki fara taina sameemah,niya kamata ki fara hallakawa saboda nine na bar rayuwarki lokacin da kike bukatar wani a kusa dake,sannan na kasa bincikar halin da kike ciki har sai da abin yafi karfinki,dan haka ki fara ta kaina"
Duk da har yanzu yanayinta na wani abune daban amma hakan bai hana na gano alamar sararawa ba a jikinta,zuyawa tayi ta kalli ummee wanda tayi suman tsaye tana kallon nurse din ta take kwance kaman gawa jini yana fita daga wuyanta.
Dago da idonta tayi ta dorasu akan y'ar tata wanda idonta yayi baki,hakoranta sukayi tsayi har da gashinta.
Baya ta fara ja da kadan kadan tana kiran sunan allah,wanda hakan yasa sameemah yin gurnani irin na namun daji tana rike da kunnuwanta. Ganin ummee bata daina salati bane yasa sameemah tayi kanta da niyyar shaketa,saurin riketa nayi ta baya dakyar,
"Dan kinga y'ar ki tana nuna tirjiya akan karmu tabaki shine har kika samu ikon fadamana wannan kalmar?,kece sanadiyyar sakata yin abinda mukafi tsana wato sallah,shine kike cigaba yanzu ma dan kinga mun kyaleki?"
Tana cikin maganar ne mukaji alamar tahowar wani,daga bakin kofa,hankalin ta ne yayi wajen da sauri,saidai tana isa wajen ta dawo da sauri tana buya a bayana,wani malamine da hiraminsa sai kuma alhaji musa shida baba umaru.
Karatu malamin yah fara tun daga shigowarsa,wanda hakan yasa sameemah ta zube a kasa tana wani irin karaji,itama ummee zubewa tayi tareda fasa kara mai karfi.
Dukkan mu abinne ya kidima mu muka fara kallon kallo.
Cigaba yayi da karanta wasu ayoyi da kuma addu'a harna tsawon lokaci kafin sameemah tai shiru kaman ta sankame.
Cikin sauri yace a daukesu a biyoshi yanzunnan.
Nine na ciccibi sameemah yayinda wasu nurse suka fita da wacce sameemah tayiwa rauni,wasu kuma suka sauki ummee zuwa cikin mota.
A hanya alhaji musa yayiwa hajiyah fatima waya ta samemu a gidan malamin.
Muna zuwa gidan ya bude wani daki mai dogon lungu,saida mukayi tafiya kafin muka zo wani daki,shiga mukayi ina dauke da sameemah a hannuna.
Wata igiya ya dauko siririya doguwa daga cikin wata kwarya mai ruwa ya daura a hannun sameemah kafin ya daura a jikin wani karfe dayake wajen.
Ajiyeta nayi a kasan wajen ya karisa daureta a wsjen,tausayinta ne yakamani sosai,hakika taga jarabawa dayawa,yanzu kuma wannan halin zata kuma shiga. Kallon malamin nayi kafin nace.
"Malam wannan igiyar zata iya tiketa kuwa,tana da karfi fa sosai"
"Hmm nasan karfinta,amma kai baka san karfin wanna igiyar a gun shedanu ba,duk da bansan wane irin shedanu ne a jikinta na haka ma bansan iya karfinsu ba,amma nasan bazata iya tsinka igiyar nan ba,yanzu dai muje tukunna sai anyi binciken wane irine kafin a fara magani,saidai naga kaman kuruwarta bata jikinta na tsawon shekaru,da wata kuruwar daban take rayuwa,dan haka dawo da tata kuruwar zai bada matukar wuyah".
Daga haka inaji ina gani babu yadda zanyi muka tafi muka bar sameemah a wajen,wanda tayi summ kaman sankararriyar gawa.
Komawa mukayi daki inda hajiya fatima take yiwa ummee fifita,itama a kwance take kaman gawa.
Wucewa malamin yayi zuwa wani daki ya dakko wani kokon ruwa yah fesa mata,ajiyar zuciya ta sake kaman wanda aka sakawa sabuwar rayuwa.
Tashi tayi zaune kaman mai cutar mantau said kallon mu take,kokon hannunsa yah mika mata ,hannu tasa ta karba kaman mai karbar umarni tackai bakin ta,kurba biyu tayi mika masa abinsa,saboda wata atishawa da ta turnuketa.
Kallon muyayi kafin yace,
"Da alama an goge mata wani bangarene na tunanin ta a shekarun baya,kuma yana da alaka da abinda yaje jikin yarinyar"
Aikuwa bai gama rufe bakiba ummee ta fashe da kuka kafin takama rigar hajiya fatima ta tike gam tana cewa,
"Yaya fatima na tuna abinda yafaru,wallahi na tuna,yaya fatima Abdulwahab ya cuceni yah yaudareni ya zalunceni nida Y'a ta yasakamu cikin tsaka mai wuyah,bazan taba yafemasa ba har numfashi na na karshe ya fita daga jikina. Bazan yafe masaba sai anyi masa hisabi nida shi,uwa uba kuma sameemah ya cuceta fiyeda abinda baki zai yah fada yayi mata abinda ko a tarihi said an tona kafin a samu.
"Meyafaru maryam ki sanar damu,ko yamzumma baza ki iya fadaba kaman sauran lokuta a baya"
"Yanzu zan iYa fada,natunna komai duk abinda yah faru babu wanda ban tuno ba yanzu zan fadawa kowa mai yah faru,koda kuwa abinda yah fada gaskiyane cewar idan nafada abakin raina,to saidai na mutun amma sai na fada kowa yah ji.......toh fah🤭
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎41~42💎
💎*Hajiya maryam a madubin gani*💎
Auren soyayya mukayi da Abdul wahab ina sonsa yana sona,saidai abu dayane yake hadamu dashi shine kullum zancensa akam yanda zayyi kudi a dunga kwatancensa,ni kuma duk sands zai fadi haka sai na yi masa wa'azin akan yanemi zabin alkhairi,ban dauki abin amatsayin wani abuba saoboda a ganina idan har ya girma ko kuma allah ya xaunar masa da sana'arsa ta Engeneer to zai bari.
Saidai ashe abin ba haka yake ba.
Muna nan zaune yah samu nasara sa'anarsa ta bunkasa yazamana sai a tsallake manyan Engeneer azo wajensa neman wani abu ko aiki,abin yabani Mamaki da farko amma sai na dauka cewa iko ne na allah.
Kwanci tashi bayan shekarar uku da aure sai wasu kamfani suka kirashi aiki zuwa kasar india.
Da farko nayi zaton tare zamu tafi saboda naga aikin yana kawo masa kudi amma sai yace zamu koma garin bauchine da zama saboda zai saka kasuwamci ne a can.
Kasan cewar nasan aikinnasa tun daga farko sai vandamu sai nasan mai yake gudana a can kasar india ba.
Haka muka zauan yana zuwa akai akai amma daga baya sai zuwansa ya ragu.idan ban mantaba nayi barin ciki har sau biyu a can,kafin na samu cikin sameemah,amma kwata kawata bana tuna nayi barin sai yamzu,kumma dukkansu sai yazo nake barin kafin ya tafi,cikin sameemah ne har aka goyashi na haifeta bai saniba,lokacin dayazo tana da shekara kusan biyu sannan,dan har na yayeta ma.
Nayi farincikin zuwansa sannan nayi bakin cikin rashin zuwa wajena akan lokaci,koda badanni ba yakamata yazo yaga y'ar sa wadda yake da ita kwal a duniya.
Lokacin daya dawo sameemah kin amincewa tayi dashi saboda bata son mutane sosai inba wanda ta saba da suba,amma dayake yana zanta a jiki da kuma siya mata kayan wasa sai ta sake dashi a kwana uku,naji dadin hakan sosai ganin yanda yake janta ajiki kuma yake nuna mata so matuka.
A tsakanin zuwansa na sati biyu kusan kullum sai sun fita shida sameemah idan zasu dawo sai na gansu da kayan wasa ko kuma su minti da biscuit.
Abinda yasakani shiga firgici kuma bazan taba mantawa dashi ba matukar ina cikin hayyacina shine:
Wata rana muna zaune dashi sameemah na cinyata shikuma yana zaune a bakin gado muna hira,sai nace masa bari naje wajen hajara hira,tunda shi yacemin magana zayyi mai muhimmanci shida abokan business dinsa.
Daukar sameemah nayi muka fito,har munzo bakin kofar fita daga falonnawa naga tayimin fitsari duk da wayonta amma ta iya wannan tsiyar idan taso,dungerata nayi kafin na koma dakin domin dauko mata pant,abinda naji ne yasaka ni cikin firgici da tunanin anya kuwa ba mafarki nake ba ,
"Eh duk yanda muka tsara ya tafi,kuma munyi nasara jininnata yayi daidai da wadda kujerar mulkin take bukata,nidai burina shine idan kun karbeta ni kubarni na dawo kasata da zama,tunda na baku wacce zata maye gurbina,yakamata nadawo gida kar a fara zargina da aikin danakeyi,inason zaman aure kuma da matata da kuma rike kamfanina,y'ay'a ne nasan zan samu wasu nan gaba,tunda nabaku wata daga jinina wacce zata maye gurbina shikennan............eh na bata abun ta cinye na tsawon kwana ukune sannan nakaita wajen da kukace din ma,abinda ya saura shine gobe zan bawa su muhiddeen ita su taho da ita,kuma ina so ku kuyi wani abu ta yanda za'a manta da ita a rayuwa,ya zama tamkar ba a haifeta ba kwata kwata......."
Numfashina ne yake hawa sama sama har bansan lokacin dana kankame sameemah a jikina ba wacce nakejin za'a rabani da ita,rababwar da bata da maraba da kashe rayuwarta,dabara ce ta fadomin da sauri nayi hanyar dakin su hajara ina bugamusu kofa.
A lokacinne na basu sameemah halak malak kuma nace kar suyi abinda zai kawota garin baushi koda wasa.
Sunyi dani nazo mutafi saidai kuma a sanann bata rayuwata nake ba sai ta Y'a ta wacce nake da ita d'aya.
Ina Shiga dakin naji an shake wuyana da wani abu,maganar Abdulwahab nani yana cewa,
"Ina Kika kaimin Y'a ta,sannan miyasa kikaji abinda bai kamata kijiba a rayuwarki"
Fazge wuyana nayi na kalleshi cike da tsana nace,
"Natsaneka Abdulwahab,ka cutar dani sanann ka cutar da Y'a ta kwaya d'aya danan mallaka,saidai kasani burinka bazai cika akan taba,dan bazaka sake kallonta ba har abada,na kwammaci naga gawarta dana baka ita ka hallakar da ita kaman yanda kake akan hallakar"
Wata fizgowara yasake yimin,zuwa wannan lokacin yafita a cikin hayyacinsa,dan ina ganin sanda jini yake fita daga hancinsa da bakinsa,amma ko digon tausayinsa banjiba dan a lokacin babu abinda nake buri daya wuce naga gawarsa a kwance a gabana.
Shakeni yayi yana magana amma banajin abinda yake fada,da haka har jijinsa ya shika na samu na kwance,ina gani yana wani abu yana fita daga bakinsa baki marar dadin gani har ya mutu,wani irin kara naji a cikin kaina wadda tasani shiga firgici har na tsinci kaina a garinnan wajen yaya fatima bansan ya akayi ba,amma na kasa furta koda kalma daya data shafi Abdulwahab.
A tunanina na tsetar da sameemah daga sharrinsa ashe van saniba suntiga sun hada ruhinta da nasu,sun cigaba da cutar da ita a tsawon lokacinnna ba tareda sanin kowaba,allah sarki baiwar allah,sun zalunceta da yawa,allah ne kadai zai saka mata abinda ubanta yayimata............."
💎*sameer a madubin gani*💎
Kuka ummeee take kaman ranta zai fita,duk dakin babu wanda baiyi kuka ba haka ya girgiza da al'amarinba,tabbas babu abinda ya gagari allah,kuma duk mai imani yaji labatin sai ya tausayawa rayuwar sameemah.
Hajiyah Fatima ce ta jawo ummee jikinta ita ma tana share nata hawayen a kan fuskarta.
Malaminne ya numfasa kafin yace,
"To yanzu tunda munji abinda yake faruwa aikin bazai dade ba za'a fara,saidai amma zai bada matujar wahala da kuma daukar lokaci,saboda sun riga da sun cakuda da jikinta da kuma gangar jikinta na tsawon lokaci,dan haka zamu dauki lokaci kafin mu rabata da abinda yake jikinta,idan aikin yayimin karfima sai munkaita wajen malamina tukunna,amma kafin sannan zamu fara dadai kokarinmu.
Daga haka ya sallami ummee tunda ta samu lafiya,baba umaru da alhaji musa kam basuce komai ba sai jinjina lamarin da sukeyi.
Komawa gida malamin yace muyi saidai mu dunga zuwa muna kallonta,duk lokacin da muka zo sanda yake tsaka dayimata magani haka zamu dunga jiyo ihunta da kuma karar wata irin dabba da takeyi.
Yau kimanin tsawon wata biyi kenan da kulle sameemah a gidan malamin,kullum sai na je dubota amma daga waje yake bada damar hangota kawai,saboda shiga wajen hatsarine sosai,koyaushe cikin saka magani ake,saboda hana wasu shedanun shiga jikinta,dan idan abin yayi yawa bazata iya daukaba.
Duk da munsan malamin yana kokari saidai kuma kunsan dan adam dason cigaba da gwada wani salon musamman idan wannan din babu cigaba.
Yauma hanyar gidan malamin na nufa,dan hanyar ta kasance ta bina ce a kkwace rana,a bakin gidan nayi parking na shiga,sallama nayi masa amma kuma babu alamar mutum a ciki,hanyar dakin sameemah na kalla wata zuciyar tana cemin naje wata kuma tana cemin na bari sai ya dawo.
Bin ra'ayin zuciyata nayi wanda ta mato akan san ganin masoyiyarta,a hankali nake tafiya zuciyata tana bugawa kadan kadan har na wuce inda muke tsayawa idan mun zo ganinta.
Kofar na tura na sameta a daure kaman ko yaushe,kayan jikinta da aka daureta dashi har ya sanza kala,ita kanta yanayinta harda fatar jikinta ya sauya,ta fita akan halittar jikin dan adam.
Duk da haka ban yi alamar zan tsaya daga karisawa izuwa gareta ba,dan hakan shine abinda zuciyata take ra'ayi .
💎*sameemah a madubin gani*💎
Tun ranar dana gwada yin sallah na suma,dana tashi naji ni a wani yanayi daban,babu abinda zuciyata take buri sai cutar da duk wanda idona ya sauka akansa,kullum zugani ake akan na bar wajen mutane na tafi inda nafi dacewa dashi.
Lokacin da wani mutumi ya zubamin wani abu naji wani duhu ya lullubeni dan dama yaushe nasaba da kasancewa cikin duhun.
Ta shi nayi na samu jikina daure da wani abu kaman zare,amma duk yunkurin dazan yi nayi amma na kasa tsinkewa daga zaren,sai kuma na kula da yanayin siffata yana sauyawa zuwa wata kala daban irin ta mutanen danake gani a cikin mafarkina.
Duk da bansan wane lokaci nake wajenba amma nasan na dad'e a jikin wannan zaren danan tsana a rayuwata,da kuma mutumin dayake zuwa yama konamin jikina da wani ruwa.
Ina jin Karar bugawar zuciyoyi suna zuwa kusada inda nake,amma duk sanda wannan zuciyar tazo ina