Showing 3001 words to 6000 words out of 53080 words

Chapter 2 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt

05 Nov 2024

13050

dana samu nakashe wannan wutar.
A ranar na fara yimana shirye shiryen kayan ita dai hajara kallona kawai takeyi,dan nasan idan zanyi shekara ina abu indai ba faɗamata nayiba bazata tambayeni ba.
Ranar tafiyarne na kaiwa iyah kayan sameer saboda yana zuwa makaranta shi,kuma ma yayi girma a tafi dashi gashi bamusan wajen ba muma tukunna.
Mun daɗe muna tafiyah a mota sai gamu a garin bauchin yakubu,hajara kam duk tah galabaita saboda jijjigar mota ,gashi dama koba mota amai takeyi inaga ta samu dalili.
Mai adaidaitah sahu muka ɗauka zuwa anguwar rail way inda tayi mana kwatancen gidan.
Shima kansa mai adaidaitan baisha wahala ba saboda gidan ba a lungu yake ba,kan hanyane inda kowa zai gane.
Kuɗin na bashi kafin na ranƙwafo da hajara zuwa jikina muka fitah zuwa bakin gidan.
Duba takardar ta take hannuna nakeyi sannan kuma ina sake duba gidan,"anya kuwa shine?" nafaɗa a raina,dan gaskiyah giraman gidan bayyi kama da wanda za'a gayyaci kamanni cikinsaba.
Ganin ba sarki sai allah ga kuma matata tana bukatar taimako ne yasa kawai nayi shahada da tunkari kofar gidan,saboda mun riga mun zo kuma ai babu batu komawa.
Wasu inyamuraine masu kayan sojoji suka buɗe mana kofar gidan,saboda tsabar tsoro bansan lokacin dana mika masa takardar hannu na ba,saboda dama tace idan nazo nabawa ɗayah daga cikinsu,zasu barni na shiga.
Hakan kuwa akayi ina mika masa yabani hanya wuce ina mamakin toh wane irin aiki kuma zanyi,danni a iyah tunanin gadi nakawo da tace zata ban aiki a cikin gida kuka zan iyah zuwa da iyalina,toh kodai ba nan bane,dan nan kam suna da mai gadi,wanda koh kare bazai nuna masa gadin ba ,dan ga ganinsa a fuska ma zaka tantance.
Nidai ban sare ba muka cigaba da tafiya a hankali saboda yanayin tafiyar hajara da bata sauri saboda rashin karfin jiki.
A bakin wata kofah muka tsaya saidai itah karamace amma dai tafi kofar shiga ɗaki girma,da wata yarinyah muka,haɗu tah yimana iso zuwa ga matar gidan.
Shiga mukayi tareda itah bayan tah dawo tacemana mu shiga.
Tabbbb danƙari wani kayan sai amale aradu,ai ina arba da inda aka shigo damu na saddaƙar da cewa ba'a Nigeria nake ba kawai,dan wajen badai ado ba kam.
A ƙasan wajen muka samu waje muka zauna inda mai aikin tacemana mu tsaya.
Bata daɗe ba kuwa sai gata ta shigo bakaman sauran masu kuɗiba da zasu iyah barka a zaune har awa guda.
Sallama tayi mana tareda nuna mana kujera akan mu zauna,nidai duk hankalina bai kwanta da zaman kujerar ba saboda kar mu bata musu,amma kasancewar ƙasan da sanyi ga kuma yananyin jikin hajara sai muka koma kan kujerar.
Har ta gyara zama zata fara magana sai kuma tayi saurin kiran wata a cikin gidan,saida ta bayyana naga ashe wacce ta rakomu ce,
"Yawwa blessing kawo musu abin sha da abinci mana,kinga har na fara cikasu da surutu kafin na bansu wani abu(juyar da kanta zuwa ga inda muke sannan tah cigaba da cewa).
Afuwan malam umaru,naga mai ɗakinnka ma kaman batajin daɗi sainaga kaman ma ƙaruwa zamu samu,yamzudai bari na saka akaiku ɗakin dazaku zauna kuci abinci ku huta daga baya sai muyi magana koh?"
"Toh shikennan babu matsala duk yanda kika ce ranki yah daɗe"
"Kacemin madam kawai,itah kuwa tah kirani da sunana Maryam,allah bamu ikon zama na fahimatar juna"
Daga haka ta tashi tayi hanyar wan beni,itah kuwa hajara tun gaisawa da sukayi bata ce komai ba sai murmushi da take kawai,duk wanda yaganta yasan akwai alamun gajiyah a tareda itah.
Ɗakine mai matsakaicin girma amma yah ƙawatu kam matuƙa,gashi an shareshi tasss sai ƙamshi yake fitarwa mai daɗi da kuma sheƙi.
Wacce hajiyah maryam ɗin takira da blessing ce tasake dawowa ɗauke da kayam abinci,godiyah nayi mata na ɗawainiyha damu kafin tah fita a ɗakin.
Kallon hajara nayi wadda samu bakin gado tah zauna tana ɗan riƙe ciki.
"Ciwo cikin yakeyi ne"
Batayi magana ba sai jijjiga kai da tayi,nima bansake tambayarta ba nayi hanyar banɗaki domin ganin menene babu,saidai da mamakina naga komai yana inda yake gashi na zamani,dan ma allah ya taimakeni nasan yanda ake amfani da banɗakin zamani da hakan sai yaban wuyah.
Ruwan mai ɗan zafi na haɗa mata a bahon wanka,wajen cin abine dai saida aka kai ruwa rana tukunna.
Muna cikin hakanne kuwa blessing ta sake dawowa,ɗauke da magani inji hajiyah maryam na masu ciki,dayake itama cikinne da itha kuma bai girma sosai,dan zayyi wata ɗayah dana hajaran.
Ina bata maganin kuwa tah fara baccin farin ciki wanda rabonta dashi har tah manta ma.
Kwanan mu uku a gidan kafin hajiyah maryam ta nemi ganina a falon baƙi.
Gaisheta nayi tah amsa batareda dogon jawabi ba tah shaidamin cewar aikina shine bayin fulawa safe da yamma da kuma kula dasu akai akai.
Mamaki abin yabani jin ɗan karamin aikin da zanyi kuma aka bani muhalli da kuma albashi ga uwa uba abinci mai rai da lafiyah,dan kwanan mu uku har mun murmure daga ni har hajara,wanda yanzu tah koma kaman ba itab saboda. Magananin da ta ke sha da kuma samun abinci mai gina jiki.
"Nasan zakayi mamakin ganin karamin aikin dana baka,amma bakomai bane dama nayi niyyar taimaka maka,kuma bai kamata mutane masu amana da rike mutuncin alƙawari su ƙare ba,kayimin abinda bazan mantaba nima,inshaallahu dama ina da niyyar buɗe shago toh zan baka ka riƙemin nan gaba,amma a halin yanzu wannna shine kaɗai hanyar dazan tsimaka maka"
Farin cikine haɗi da jin daɗi suka kamani har na rasama da wanne irin baki zan gode mata irin kyautar da tyimin haka.
Itama ganin na diriricene yasakata saurin barin falon tana murmushi,da alamun bata son godiyar tawa kenan.
Nikuwa hakan bai wuceba dan dana koma ma na faɗawa hajara tun kafin na rufe baki tace zatayi mata godiyah tsakanin itah da itah.


Tun daga fita godiyah ba itah hajara ta,dawoba sai wajen karfe tara ba dare,abinne ya ɗauremin kai inda na tamabayeta mai yah faru,nan take cemin wai hira suke tayi irinna mata ,musammaan ma akan ciki da kuladashi,da kuma tsabtar jiki da tah muhalli.
Sannan tace mata idan cikin yakai wata biyar zasu dunga zuwa awo tare.
Tun daga lokacin daga na fita sai hajara ta tafi sashen hajiyah maryam tanan tayata ɗan ayyuka ita kuma tana koyamata abubuwa,musamman da yake karatun nursing tayi saidai bata aiki a kan hakan.
Nima bana hanata zuwa tunda ina ganin sanji a abubuwa da dama a game da zamanta da hajiyah maryam ɗin,kuma bata zama cikin kaɗaici sai ma wani haske da ta ƙara saboda kyakykyawar kulawa da take samu a wajen hajiyah maryam ɗin,matar da ba abinda zan iyah saka mata dashi sai alkhairi.
Wani muhimmin shirye shiye aka fara a gidan na tarbar dawowar mai gidan wanda yake aiki a kasar India,mukan mu ganin hajiya mairo tana murnar tarar masoyinta yasa muma muka fara tayata murnat duk da bamusan shiba bare jin labarinsa,hajara kamma a can ta yini suna ta aiki.
Can wajen la'asar misalin karfe uku ji karar shigowar motoci,tab nan fah abin yazama abun kallo,dan kuwa inaga duk girma da faɗi irinna farfajiyar gidan saida suka cika da motoci kaff,babu koh masakar tsinke.
Mudai muna tsaye daga bakin ɗakinmu wanda yake ɗan gefe da inda motocin suke fakawa ,mun zubawa sarautar allah ido.
Can bayan sun gama shigowane kuma sai dukkan sauran motocin suka baɗe suka fito.
Samarine da mata farare kall ba irin na kasar nan ba,duk da akwai masu surkin bakin fata a cikinsu,sanye suke kkwannensu da kaya baƙiƙƙirin kaman zunubi.
Dukkan layi sukayi a jikin jar motar da take tsakiyah wanda itah ce kaɗai mai banbancin kala a cikinsu,dan duk sauran baƙaƙene.
Na gaban motarne yah fito kafin yazo yah buɗe bayan motar. A ɗan jima kafin mamallakin motar yah jefo ƙafarsa waje,kafin yah fito da dukkan sauran jikinnasa.
Kyakykyawane na fitar hankali,dan koni dana ke na miji naga kyawunsa bare kuma mace,.
Kayane a jikinsa farar shadda ƙal,da kuma baƙar hula da takalmi shima baƙi siɗik, taku yake cikin kwanciyar hankali har yazo yah wuce falon hajiya mairon,yayinda sukuma sauran naga duk sun koma motarsu sun bar gidan,sai jar motarce kawai take nan da kuma wanda yah tuƙota.


Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150


Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.


💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎










*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*




💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}






💎5~6💎




Tun lokacin daya dawo aka ɗauko wasu masu aikin daban ana biyansu ,saboda abincin da'ke dorawa gidan yah fi na mutum ɗari ƙartin samari,duk kuma na sadaka ne,da farko hajara taso tashiga cikin masu girkin ta tayasu amma hajiyah maryam ta hanata,a son ranta tah huta ba'ason mace mai ciki tanayin aikin wahala mai tsanani.
Har aka shafe kwana uku da zuwan alhaji ABDULWAHAB kullum gidannan a cike yake da mutane masu neman taimako,kuma duk wanda yah shigo toh baya fita hannu rabbaan saida kayan abinci koh na sutura,gwargwadon abinda yazo nema dai.
Masu karbar abinci kuwa har dare ake kaiwa ana karbar abinci a kofar gida,dan masu rabawa da ban masu dafawa daban haka masu sakawa a cikin robobi.
Muma kanmu kayan da hajiyah maryam ta bani har kuka nayi saboda ganin yawansa.
Tunda muka kalli alhaji abdulwahab lokacin da yah zo gidan zuwan farko bamu sake sakashi a idonmu ba saboda yawan zirga zirga dayake tayi na,meeting halarta wurare da sauransu.
A kwana na huɗu kuwa yah koma inda yah fito wato ƙasar India da sassafe ma yata fi koh tashi bamuyi daga bacciba.
Shima saida rana nakejin zancen a wajen hajara ta dawo daga wajen hajiyah maryam,wai ƙiran gaggawane yah sameshi daga can akwai abinda zayyi.
Kwanci tashi har muka shafe wata guda ciff a garin bauchi gidan alhaji abdul wahab,shahararren mai kuɗi da duniyah take damawa dashi.
Zuwa sannan hajara tah daina wani laulayi saboda cikinta yayi wata biyar,duk bayan sati biyu yanzu suke zuwa awu ita da hajiyah maryam,inda direba yake kaisu yah ɗakkosu.
Kowa yah kalli hajara sayya yayi mamakin canjawarta tayi luwai da itah.
Nikuwa a cikin wata biyunnan zuwana gida uku,kuma kowanne sainayi sati guda nake dawowa,hankalin ramatu bai zo kaina ba saboda tah samu sana'a tanayi ,gashi kuɗi yana shiga mata,idan nace tazo mutafima nasan bazata biniba tunda bata san wainar da ake toyawa a canɗin ba.
Da haka rayuwa ta cigaba da garamana har watan haihuwar hajara yakama.
Naƙuda tah fara gadandan inda hajiyah maryam ta zauna a wajenta tana taimakata,amma ganin abin yana son yah fi ƙarfin saninta gashi itama da tsohon ciki,sai ta ɗakko mota domin mu tafi asibiti,musamman dana faɗamata yanda tayi a cikin fari,da kuma matsalar da mahaifarta take dashi.
Can asibitinma saida muka kwana tukunnan a washagarine tah samu damar haihuwa.
Munyi farin cikin samun kanta duk da tah galabaita amma saidai yarinyar tana jin jiki ga kuma tare ta fito duk da mahaifar gabaɗaya,wannan labarin yaui mana babu daɗi amma babu yadda zamuyi sai rungumar ƙaddara.
Kasancewar yarinyar bata da lafiyah saida muka zauna a asibitin na tsawon kwana biyu tana karbar magani,ga tsada amma hajiyha maryam tace koh godiya kar muyi mata,itace da godiyah ma zaman da muke da itah,saboda bata da kowa a garin bauchi aurene kawai yakawotah.
Ranar suna iyah yan uwan hajara ne guda dayah tazo,wanda itah ma shekararta biyune da aure dama tana da niyyar zuwa,wato inna rabi.
Yarinya taci sunan hajiyah MARYAM,ana kiranta da sunan tah,kar kuga murna a wajen hajiyah maryam kaman ta cinye yarinyar dan murna,dan ma bata da lafiyah ko yaushe tana ɗaki,ba a fiye futowa da itah ba,saboda cutar sanyi da take ɗauke da shi.
Bayan sati biyu da haihuwar hajara itama hajiyah maryam tah haihu,inda tasamu ƴa mace,saidai ita a gida ta haihu,kawai ma'ikaciyar lafiyar aka turomata domin tah taimaka mata.

Cikin koshin kafiyah kuwa suka samu kansu daga itah har y'arta ba'a samu wata matalaba,itah ce ma aka ɗan yi mata ɗinki saboda ɗan ƙaruwa da tayi.
Tun kafin suna mutane suka fara cika da mutane,mutanen arziƙi da kuma ƴan uwa wanda dama haihuwarta suke jira.
Lallai munga mutane kam kuma manyan mutane ba mutane haka ba.
Duk da haihuwa tah farko da alhaji abdul wahab yasamu amma bai zo ƙasar nigeria ba,hakan yabawa mutane da dama mamaki kan cewa wane irin aikine ya riƙeshi haka,dan tun farkon samun cikinma bai wani murna ba,saidai tambayar lafiyar uwar kawai yakeyi,ga shi shekararsu huɗu da aure sai yanzu allah yabasu arziƙin samun haihuwa.
Da sati yah zagayone yarinyah taci suna SAMEEMAH,suna kawai taci,kasancewar hajiyah maryam tanason sunan.
Biki akayi a lokacin sunan kaman na yin auren wata mace,saboda dumbin mutane da taro yah tara, banda abin duniyah a da akayi ta rabawa.
Tun daga sannan hajiyah maryam ta cigaba da rainon ƴar ta ciki kwanciyar hankali.
Maryam kuwa tun bayan haihuwarta kowane sati sai ankaita asibiti domin gwajij numfashinta,amma koda da sau ɗayah hajiyah maryam bata taba gajiyawa ba akan hakan,mukan ma har mun fara cire rai da rayuwarta,musamman ma mahaifiyarta wanda cikin dare idan na farka saina ganta tana zaune tah zuba mata ido,soyayyar ɗa da mahaifi duk sainaji nima wani iri.
Dahaka muna cikin yanayinnan har maryam tayi wata huɗu,amma kaman ƴar wata biyu haka take.
Wata ranane jikinnata yayi tsanani muka tafi asibiti kwananmu biyar acan tace ga garinku nan.
Ko mukanmu iyayenta bamu yi damuwar da hajiyah mairo tayiba,dan saida nazo ina basu baki itah da hajara.
Dawowa gida mukayi gida saboda ayi mata sallah da kuma kaita gidanta na gaskiyah,inda kowa zaman jiran nasa yake yi.
Bayan sadakar uku har mun fara manatawa da itah,dan dama itah ba lafiyayya bace.
Zuwa yanzu sameemah tayi wayo dan kullum nan muke yini da itah,saboda hajiyah mairo tah koma aikinta na asibiti,duk da alhaji Abdul wahab baya so amma haka ta lallameshi ta,koma aikinta a cewarta taimakon mutanene zai kaita ba neman kuɗiba.
Shaƙuwa sosai tah shiga tsakaninmu da sameemah,dan wani lokacin da ƙyar mamarta take ɗaukarta idan tah dawo daga aiki,dayake akwai abincinta na yara shi ake bata.
Itah ma hajara daga bayah aiki hajiyah maryam ta,sama mata a asibitin suke na shara da gogen daƙin masu jinyah,sai yazamana tare suke tafiya a motarta,idan hajiyah maryam ta shiga aiki sai hajara tah riƙeta,kusan ko yaushema tana wajen hajaran idan dai ba dutynta bane.
Haka har muka samu shekara biyu kyawawa a gidan,yamzu ansaba kowa yasan da wa yake zaune,dagani har hajara munyi sabo da mutanen wajen sosai da sosai.
Sameemah kyakykyawar yarinyahce dan kallo ɗaya mutum zai tabbatar da hakan,saidai bata da son mutane irin na uwarta,dan idan ka ɗauke mu da mahaifiyarta toh babu wanda take sakewa dashi,da farko hakan kaman abin ƙiwa ne yarinta sai kuma hakan yajuye kaman halinta ne,amma duk da haka yarinyah ce mai shiga rai da kuma farin jini a wajen mutane.
Kwatsam da tsakar rana saiga alhaji abudul wahab yadawo saidai wannan zuwam babu manyan motoci kaman na farko,ita kanta hajiyah maryam tayi mamakin rashin zuwannasa da kuma zuwan bazatan dayayyi,dan daga kallon irin kallon da take jifansa dashi mutum yasan tana jin haushin rashin zuwannasa.
Sameemah da take hannunta yah miƙo hanu zai karba,aikuwa dama badai kiwuyah ba,da sauri tah maida hannun gefe tareda juya kai.
"Kagani koh,ko ƴar ka ma tana ƙin zuwa wajenka tunda bata sanka ba"
Dariyah kawai yayi tareda karbar yarinyar duk da bata so yayi hanyar kofar tasu.
Itah binsa tayi a baya,ni ma kuma muka bar wajen har sannan muna mamakin irin zuwan bazatan da babban mutum kaman alhaji abdul wahab yayi.


Lokacin da kwana uku yah cika munyi zaton zai koma,sai muka ga har anyi sati guda bai tafiba,hakan yasa mukayi tunanin koh hutu yah samu a wajen aiki yasa yazo domin yayi su da iyalansa,kuma ya kyauta hakan,dan itah kanta hajiyah maryam taji daɗin hakan.
Sannan sameemah har ta fara sabawa dashi dan koyaushe yana tare da itah,kuma duk sanda yah fita sai yah siyo mata abin wasa da kayan ciye ciye,wani abin ma bata iyah amfani da shi,kawai siyah yake irinna iyaye masu ɗokin irin na ƴaƴan fari.
Mukuma a namu bangaren muna tah shirye shiyen tafiyah zuwa gida,saboda iyayen hajara suna so taje ganin dangi,nima kuma inason zuwa ganin yah yanayin gidan yake tafiyah. Mun yanke shawarar nan da sati ɗaya zamu tafi,kuma zamu kai wata guda bamu dawoba.
A ranar da daddare kowa yayi bacci kasancewar daren yayi sosai,ba abinda mutum yakeji sai shirun duniyah kawai,kowa yan kwance yana hutawa.
Ban daɗe da zagawa bayi ba naji bugun ƙofar ɗakinmu,saida na kalli hajara wanda take kwance kafin na isa bakin kofar ina wasiwasin na buɗe ko kuma na barta,ina cikin hakane naji muryar hajiyah maryam da alamun tashin hankali a cikin muryarta tana cewa,
"Malam umaru kabuɗe ni ce,kayi sauri banida lokaci sosai"
Cikin sauri har jikina yana rawa na zare sakatar dakin da sauri.
Haɗa ido mukayi da itah jikinta sai rawa yakeyi lokaci zuwa lokaci tana waigawa baya kozata ga wani yana biyota.
Sameemah ce a hannunta wacce take ta bacci abinta,saurin mikomin itah tayi da sauri,zuwa lokacin hajara tah tashi,sai na miƙa mata yarinyar,tun kafim na tambayeta ta fara magana cikim sauri muryar tana rawa,
"Na roƙeku dan darajar allah,ku fitah daga gidannan a yanzu basai gari yah waye ba ku bar gariannan ma idan san samu ne,bazan iya yimuku bayanim abinda yake faruwa ba,saidai inaso ku riƙemin ƴata da amana a wajen ku,duk da nasan zakuyi hakan tunda nafi kkwa sanin halinku na mutunci,sannan ku kumin alkawari zaku riƙeta a matsayin ƴar da kuka haifa a cikinku,kar wani yasan gaskiyar iyayenta,na baku itah halak malak burina kawai tasamu gata da kuma rayuwa mai kyau koda bana cikin rayuwarta,kartayi maraicina ko kuma rashina",
Tana gama faɗan hakan tah ciro wani ƙullin kuɗi a jikin rigarta ta miƙamin kafin ta cigaba da cewa,
"Ga wannan kuɗin,na aikina ne danayi na tsawon shekara kuda,wannan zai isheku hawa motah,wannan katin kuma na asusun bankine mabuɗin cirewar sunan sameemah ne,nabaku zaku iyha amfani dashi wajen inganta rayuwarta,amma idan kunga bazaku iyah amfani dashi ba saboda nasan halinku toh,ku ajiyemata idan ta girma ku bata a matsayin kyautata tace a gareta kuma ina rokonta,da tayi muku biyayya tamkar mahaifanta"
"Kuyi sauri ku fito yanzu nan kafin lokaci yah kure mana,kuma dan allah karku bari sameemah tah tako garin bauchi lo da wass"
Tana gama faɗan hakan tah fara haɗamana kayanmu da sauri,akwati ɗayah muka ɗauka ta rako mu bakin get ɗin gidan,hajara tana rungume da sameema a jikinta,duk da bamusan menene ba amma munsan abinda zai raba ɗiya da mahaifiyarta na kaɗan bane ba.
Hajara ce tayi karfin halin cewa
,"amma hajiyah maryam bazaki iyah guduwa keda itah ba ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login