Showing 30001 words to 33000 words out of 53080 words

Chapter 11 - Wasa Farin Girki Cigaban Gidan Gandu Complete Hausa Novel By.txt

05 Nov 2024

13052

zatonta alhaji bala yana Egypt wajen wani program yanda ya fada mata.
Rana tsaka ta tashi dawowa hakn ma dan sunyi waya da yusrah ne ta fadamata cewa alhaji bala yana Nigeria duk tsawon watannin nan,aikuwa kaman iska haka hajiyah mairo ta tayar,ko gama zamn batayiba ta kamo hanya ta dawo.
Muna kitchen nida sameerah muna abinci,na dawo falo kenan na zauna saboda sameerah tace na huta kawai,ina zama saiga hajiyah mairo ta shigo,idonta dama a kaina yake kaman zai fado kasa,musamman da taga abinda yake gabana wato ciki.
Tun daga cikin idonta kana ganin kalar bakin cikin da ya kunsa,dan nasan tayi datasanin zuwa neman maganin,da ta bar kafar kawai ta rube.
Kaina tayi da niyyar turmusheni akan kujerar daidai kuma da fitowar alhaji bala daga cikin dakinsa,saurin dakatar da hakiyah mairo yayi Yana cewa.
"Baki da hankaline da girmanki da komai kike kokarin cutar da ita,bayan kuma ga ciki a jikinta,idna wani yayiwa yarki haka zakiji dadine iyee,to wallahi karanaji na gani mairo,idan kuwa kika kuskura naga kin sake cutar da wannan mutanen a cikin gidamnan kaman yanda kikayi a baya,toh a bakin aurenki,ke sai kibar gidan in yaso kawai,tun da ba zaman lafiyay kike so ba"
Yana maganar cikin daga murya,daga gani ransa yah baci sosai.
Daga haka yah juya ya fita daga gidan,nikuwa kallon zakisan dawa kike nayiwa hajiyah mairo wanda dan takaici har kwalla idonta yakeyi.
"Yaushe haka ta faru,wane asirin kika yiwa mijina dan ubanki"
"Wane asirin na karya dai,babu boka ko malam sai zalllan kissa,idna kema kika cigaba zaki samu naki rabon fiyeda nawa ma tunda kin fini saninsa"
Shiru tayi kaman ta dauki magana ta sai kuma tayi dakinta da sauri kaman ana jefata,dukkuwa da kiba irin ta jikinta.
Haka zaman ya cigaba da kasancewa tsakanimmu dani da hajiyah mairo babu wanda yake shiga harkar kowa,saidai sameerah kam tana shan wahala a hannunsu,musamman da suka ga tana kula dani.
Karyah babu irin wacce hajiyah mairo batayiwa umaruje akan sameerah,a dole sai ta saka yah musguna mata.
Zancen da tayi na auren yar kawarta kuwa yana nan babu fashi sai shirye shirye sukeyi.
Duk wanda yaga sameerha sai yau tausaya mata,don ta rame ta fige kullum tana cikin tagumi,gashi wani irin so take yiwa umaruje kamar ta ci babu.
Dan yanzu karatun ta nutsu tayi sallah bata wuceta,har makarantar dare ta shiga saboda rage zama a Gidan ma Yana rage mata kewa.
Domin kusam kullum Mufeedah tana gidan wai tazo gaishe da hajiya mairo,shikuwa umaruje sai rawar kafa ta tashi,koda idon sameerah baya sa ya dauke idonsa,saidai ita ta bar musu wajen.
Takaicin hakan nake gani gashi banida ikon yin komai akai,koba komai sameerah yar uwata ce,ganinta cikin hakan yana tabani sosai zanyi,dan nima ta kaina nake,ni kadai nasan wahalar danake sha a cikinnan.


Shirye shiyen auren ake dan har an kusa saka rana biki ya fara kan kama,a zaune muke a dakina sameerah ta kawomim shayi na dare wanda yazam kaman jiki kullum sai nasha.
Kallonta nake da mamaki sanann da tausayinta ganin yamda ta tsurawa waje daya kallo ko kyaftawa batayi,danni kaina sshaida ce a irin soyayyar da take nunawa umaruje.
"Sameerah ki dunga hakuri,idan kika biye hakan zai iya kaiki yah baroki sannan kuma dolene a jarrabi bawa,amma idan kinga zaamn yana cutar dake yakamata kiyi wani abun.
Dannaga wani abun da gangam sukeyi dan suga iyay gudun ruwanki akai"
"Nasani salma nasan duk abinda yake faruwa,saidai na ma gode allaah da abin da na shuka nake girba dun daga nan duniyah,ba a barmin shi sai naje lahiraba,dan salma wallahi sai yanzu nake nadamar rayuwar danayi a baya,musamman idan malamin mu na makaranta yana fadan wani abun,sai naji ashe mu duniya kawai zuwa mukayi bamu karu da komai ba.
Inaji a jikina abinda nayine ake nunamim a gidannan,idna na tsalleke na tafi kaman na bar baya da kurane,dan haka zan cigaba da zurewa salma har zuwa inda zuciyata bazata iya daukaba,alkawari na daukawa raina bazan taba cewa umaruje ya sakeni ba saidia idna shine yaga yana bukatar hakan. Nagode salma sosai da nuna kulawarki dan a wajwnki ne kawai nake samun nuna kulawa mai kyau,dan ummah kan idan naje bata da magana sai ta na koma wajen boka a sake min aiki. Gaskiya nikuma naga ba abinda boka yake yiwa rsyuwar mutum banda kara masa wahala da kuma zefashi cikin hallaka,wanda nayi a baya ma ina neman yafiyar allah,dan haka bana bukatar sake dorawa kaina wani laifin wanda bansan iya kacin masifarsa ba"
Tana gama fada hakan ta dauki tiren shayin cikin sanyini jiki tayi hanyar kofa tareda yimin saida safe.
Lokacin data jamin kofar bansan sanda na fashe da kuka ba mai cin zuciyya,lallai munyi rayuwar dana sanj a baya kam.
Istigifari nake tsyi ina maida zuciyau har bacci ya daukeni.




Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150


Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.


💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎










*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*




💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}








💎29~30💎






💎*Sameemah a madubin gani*💎


Tun da muka yi maganar nan da yah sameer nakeji wani irin yanayi yana jiyartar cikin jikina yana taruwa a cikin kirjina,tun yana min ina iyya daurewa har yah zamo na farajin zafi a cikin kirjina,"mai hakan yake nufi?"
Shine tambayar danayi wa kaina amma banada amsar hakan. Da haka bacci yah daukeni,saidai bankai ga jina cikin duniyar baccin tsulum ba mutanena suka bayyana cikin siffa ta bacin rai.
~~~me like nu fine Wai,kina nufin zaki bar soyayya ta huda cikin zuciyarki wacce take haramun ce ga kowanne namiji yha shigeta,to hakan bazai taba yuyuwa ba dole ki tashi daha yaudararren maganar daya miki matukar kina so ki karisa guntun rayuwar da ta sauramiki a cikin su lafiya"
Kowanne lokaci cikin kwarin gwiwata nake tsayawa a gabansu,saidai yanzu ma nemi wanann kwarin gwiwar narasa shi,sai ma sunkuyar da kaina danayi kawai ina jinsu har suka gama masifarsu mai hade da gargadi suka bacewa ganina.
Tambaya daya anan shine"shin zan iya abinda suka umarceni da yi,wato cire ɗigon soyayyar yah sameer data darsu a cikin raina a daren??".


Da safe dana tashi kokari nayi na katse duk wani tunani daya shafi abinda yah faru a daren jiyan daga cikin raina,saboda halina ne banason duk abinda zai dunga tsayawa a cikin raina yah dunga yawo lokaci zuwa lokaci.
Ina Bude kofar tawa idona ya sauka akan fuskar sameer wanda ya dam jingina a jikin tasa kofar yana kallona,Murmushin dayake aikomin daga wajen dayake tsayene yasa na saduda na mika dukkan ragamar danayi niyyar rikewa daga farko,"wayyo allah yazanyi da wannan halittar da take kokarin keta rayuwata ta,shiga"
Takowa yake a hankali har yah iso inda nake tsaye,hannunsa yasaka mai laushi sosai kaman ba na namijiba yah dago fuskata izuwa ga tasa.
Kallon kallo muke yi a haka kowa yana enjoying yanda zuciyarsa take shigomasa da shauki.
"Dafatan wannan kyakykyawar kanwartawa kuma matartawa tanajin abinda nake ji a cikin raina,sannnan kuma da yanda na kwana cikin begenta da kuma son kasancewa a kusa da itah"
Har zuciyata tana kokarin sallamasa kaman yanda take da burin na barta tayi abinda take some tun lokacin dana hada idona dashi.
Saidai kuma abinda zai biyi baya nake tunanin,ni ba kowacce sauran yam adam ce mai yanci ba,kowa yana da ikon yin abinda yaga dama,amma ni bana da wannan ikon koda nayi niyyar yin hakan.
Jan numfashi nayi mai karfi kafin na sauke hannunsa dayake kan fuskata nayi saurin shigewa kitchen,nasan abinda nayi ban kyautaba kuma bazai ji dadin hakanba,saidai hakan shine yafi masa kuma yafimin,yaj kamata nayi nesa dashi tun ina da damar hakan.
Shiryawa nayi kana na shiryah farouq muka bar gidan,saleemah kuwa tun lokacin da aka dawo da ita ba wani haduwa muke sosai ba.
Duk hanyar dazan bi dan naga na gujewa haduwata da yah sameer abin yaci tura,dan koyaushe yana mkaale dani yana min murmushi ko kuma bani hakuri wanda nikaina bansan mai yayimin ba.
Yauma ina cikin aiki a office naga yah shigo yah samu kujera yah zauna,dago idona nayi na kalleshi kafin na cigaba da yin abinda yake gabana.
Gyara kwamciyarsa yayi akan kujerar dan dama bansa a raina zai fita lokacinba,har nagama aikina na tattara kayana yana zaune yana danna waya,wucewa nazoyi ta wajen dayaje zaune aikuwa karaf naji ya zawoni zuwa kan cinyarsa,zuya idona nayi zanyi magana yayi saurin nunamin bakinsa nayi shiru.
Hakan kuwa na tsinci kaina dayi wato bin umarnin daya bani.
Tashi yayi daga kwancen dayake yah hada kirjina da nasa ya rungemeni sosai,banyi kokarin raba jikinnamu ba dan bazanyi karyah ba ina tsintar kaina cikin farinciki idan hakan ta kasance.
"Meyasa sameemah kike guduna a kkda yaushe,sau nawa zan fadamiki nesanta ni da kike daga kusadani Yana cutardani,sau nawa bakina zai cigana da furtamiki cewa Yana sonki sanann Yana kaunarki,kece mahadin rayuwarsa,sameemah babu karyah a cikin maganar daake miki.
Dagoni yayi domin naga hakikanin gaskiyar a cikin idonsa wanda ko ban ganiba nasan abin hakane,cigaba yayi da furta kalmomin da suke sakani jin ina raye,ta wani bangaren kuma suke kasheni sannan suke kara nisantani daga gareshi,yaushe bakina zai iyha buduwa yah sanar dashi halin danake ciki,anyah kuwa zan iyya zure wannan rayuwar da muke ciki.
A duk lokacin dana kwanta na tashi sai shedanun sunyi kokarin mallake jikina da kuma ruhina,wanda dama hakan shine burinsu kuma sun fara samun nasara.
Hannuna na saka a bakinsa domin banason cigaba da jin wanann kalmomin da dama nariga nasan suna cikin ruhinsa,
"Yah sameer kayi shiru da fadin wannan kalmomin nasan dama Akwai su a cikin zuciyarka kuma da gaske kake duk abinda ka fada"
"Idan Har kinsan da gaskene meyasa kika kasa bani dama sameemah akan mu koma zaman da kowanne ma'aurata suke,ko baki da lafiyane,idna akwai wata matsala ki fadamin"
Saurin kallon idonsa nayi tareda jijjiga masa kai da sauri,da hankalin sa yana kaina sosai da zai gano shock din dana shiga a lokaci guda.
Ta shi nayi daga kan cinyasa nayi waje,shima dayaga hakan biyoni yayi muka tafi gida,a hanyama babu wanda yace wa kowa komai.


Magana muke jiyowa daga dakin Saleemah lokacin da muka shigo gidan,muryar ta babbar matace da alama kuma sameer yasan wacece,dan hannuna yasake da sauri ya nufi dakin saleemah din,nima nawa dakin na wuce domin canja nawa kayan.
Ina jin lokacin da Saleemah ta rako matar tana ta yimata shagwaba amma ban fitoba dan bana son shishshigi a lamurana sosai.
Can wajen magribane sameer yashigo dakinnawa yake cemin doctor maryam ce kanwar hajiyya fatima tazo,bata kasarnan taje karo karatu jiya ta dawo,zata fara aiki a sibitin cikin barrack dim,toh kawai nace masa dan yamzu yawancin lokuta yakanzo dakina yayi ta min hira koda bazan amsaba,nima har na saba da zamansa a kusadani yanzu shida farouq,idan babu daya sai na yi ta jina cikin kadaici.
Kiran sallane yasa ya tashi ya tafi masallaci,nikuwa da ba yi nake ba ina zaune ina cigaba da aikina.
Sake shigowa yayi a karo na biyu saikuma naga ya tsaya daga bakin kofar kamar mai nazari.
"Sameemah kinyi sallah kuwa fitata daga dakinnan?"
Tambayar ce tayimin wani giff a cikin kirjina har tasa nayi shiru narasa wace irin amsa zan bashi.
Shiru nayi ban ce komaiba sannan ban tashi daga inda nake zaune ba,har nabude baki zan cemasa bana sallah sai kuma naji yace,
"Shin mai yake damunki sameemah,tunda nake dake ban taba ganin kinyi sallah ba,nasan yanzuma cewa zakice bakya sallah amma kuma bahaka bane,saboda tun sanda nake zuwa office dinki ban taba ganin kin tashi kinyi sallah ba,wane irin al'ada ne zayyi wata guda yana zuba uhm?"
Gumine ya fara karyomin ta ko ina a cikin jikina,shin mai zancene ma tukunna.
"Ba wasa da sallah kike ba sameemah,kwata kwata ma batada lokacinki mai yasa haka,kuma ina kukada dake zaki saka farouq yaje masallaci amma ke bakya zuwa yij sallah,dan muyi bauta aka turomu duniyayr nan sannan wajibice akan kkwa babu wanda aka daukewa,Allah yana cewa a cikin alqur'ani :
Wama kalaqtul insi wal jinni illah .........."
"Liya'abudun"
Nayi saurin karisamasa numfashina yana cikowa,yah sameer naji kuma zanyi yanzunnan.
Kallona yake da mamaki saidai shima tasa fuskar babu alamar wasa a cikinta.
Bandaki na shiga na dauro alwala jina ke kaman na junduma ihu saboda tunowa irin azabar da zan fuskanta.
Lokacin dana fito baya cikin dakin,hakan yasa nayi ajiyar zuciya tareda komawa na cigaba da abinda nakeyi.wayata naga tana haske,ina dubawa naga sunan husband,yaushe kuma haka ta faru,kenan shine yamin saving number sa.
Ɗauka nayi na kara a kunnena domin jin mai zaice,
"Kinyi sallahr ne?"
Uhm kawai nace masa a taikace kafin ya kuma cewa,
"Kizo dakina yanzu ina son ganinki to"
Daga haka ya kashe wayar,nima ajiyewa nayi ina tunani,mai zai cemin wanda ba zai fada a dakina ba.
Kawar da tunanin hakan nayi kafin na dauki gyalena na nufi hanyar dakinnasa,dadai nazo shiga dakinnasa na hadu da saleemah saidai banda harara babu abinda ta iya yi dan shakka ta takeji ba kadan ba kuwa.
Tura kofar nayi nashiga batareda nayi sallama ba,a kan kujera naganshi yana wani rubutu.
"Zaki shigo dakin mutum amma babu sallama,sannan idan anyimiki ma bazaki amsa ba koh"
Duk da hakan halina ne amma saina tsinci kaina da jin babu dadin yanda yake fadar hakan,bakina nabude kaman wanda yake ciwo na ce,
"Salamu alaikuma"
Amsawa yauyi tareda tahowa inda nake,kama hannuna yayi ya zaunar dani a bakin gadon shikuma ya zauna a kasa na,
"Barka da zuwa dakin mijinki karon farko tun aurenki,nayi farinciki sosai da kika amsa gayyata ta seemah"
Seemah!! Shine abinda na fada a cikin raina,yau kuma lallai kam.
Kama hannuna yayi yasaka a cikin nasa kafin yace,
"Ina matukar son rayuwa tareda ke seemah amma kinki amincemin muzama abu daya cikin inuwa daya,duk da nasan kema kina da bukatar hakan,ina sonki sosai sameemah amma naga alama kinfi son ki ganni kullum cikin kewarki da son kasancewa tareda ke koh"
Maganganunsa kashemin zuciya suke ba kadan ba,ko kadan banason ganinsa cikin wanann halin,hakan yana cutar dani,musamman da nasan cewar nice silar hakan,yah aureni yah fara sona nima ina sonsa amma kuma na kasa yimasa abinda kowacce mace zatayimasa,duk da zuciyata tana kin yarda amma nasan saleemah tafini a wajensa,tunda zata iya yimasa abinda ni bazan iya yimsaba,kaitona da zamtowa wani bangare na rayuwarsa wanda zai zame masa ciwo ba maganiba wayyo allah nah!.
Rintse idona nayi tareda saurin kawar da bakina daga nasa bakin wanda yake kokarin hadawa da nawa,bazanyi wanann gangancinba ban shirya ganin gawarsa a gabana ba tukunna,ina cewa zan iya rasa komai bayan ummah tah sai yanzu nagano duk zancene,rasa wannan ruhin da baisan komai ba sai soyyayyata abune da bazan iyah zurewa na sam,dan haka bazan iya yin abinda zamyi danasani ba koda kuwa zuciyata hakan take matukar bukata.
Kamo fuskata yayi yana kallona ko akwai abinda yake damuna,saidai ko kusa naki bude idona wanda nasan zuwa yanzu sun tashi daga kalar irinna bil'adama,kamani yayi yah rungumeni a jikinsa yana magana cikin sanyin rai.
"Seemah narasa gane mai yake damunki,nace miki idan bakya da lafiya ki sanar dani bazan iya zurewa zamanmu a haka ba sameemah,ni namijine mai matukar bukata,na fadamiki idan wani abune nayi miki ki fadamin zan gyara,amma idan kika hanani kanki abin zaimin yawa seemah,bazan iya dauka ba sam,ina kaunarki sosai fiye da yanda bazan iya misaltawaba kiyimin afuwa da kuma uzuri dannima haka na tsinci kaina ciki.
Horonki yana gasanj ba kadan ba,bansan har zuwa yaushe zancigaba da jiranki ba,koda babu ke dole zan kara aure saboda bazan iyah zama da mace daya ba,amma yanzu tunda na aureki banda burin sake Lauren wata macen kece dama zabina na dade ina jin wani abu a game dake tun kina karama sameemah,nasha kuka daki ina tambayar kaina mai yasameni nake sha'awarki bayan kin kasance muharrama a gareni,saidai daga baya ganin abin ba zai wuceba yasa na yanke hukuncin nesanta ki daga inda nake tun lokacin da ummah tana da rai.
Amma yanzu ke halaliya tace sameemah karki bari wani abu a cikin ranki ya dakushemana farin cikinmu,inason yin rayuwa dake har zuwa lokacin da numfashina na karshe zai fita"
Saurin zare jikina nayi daga nasa ina matsawa can gefen gadonnasa,wani abu naji yazo ya tokaremun makogaro,ganin banida ikon yin abinda mijina yake bukata daga gareni,duk ina bukatar sallma masa kaina amma bazan iya ba domin gangar jijin ba mallakina bace,an riga an gama iko da ita.
Wani irin kuka na fashe da shi karon farko kenan bayan ummah ta ta rasu sai yamzu na samu ikon yin kuka.
Wani irin zafi da tafarfar fasa zuciyata takeyi yayinda nake jin wani zafi yana tsaga sassan jikina,duk da haka ban sareba saida na tattaro sauran kalomomin dake bakina nafara cewa,
"Kayi hakuri yah sameer! Kayi hakuri mijina ! Kayi hakuri masoyina.
Hakika da ina da ikon aikata abinda kake bukata dana aikata,koda kuwa hakanne zai kawo karshen wanann wahalelliyar rayuwartawa,banida ikon yin nesa dakai ko kuma yi maka musu saidai hakan baya cikin abinda zan iya aikatawa.
Barinka kana isowa har kusan jikina ma ka tabani ba karamin kokari nayi ba akan hakan yah sameer,inajin kunyar kaina a halin yanzu,ban taba jin banason yanayin halittata ba sai yanzu,amma babu yanda zanyi hakan shine kaddarata dama tun farko banida ikon hanawa barekuma canjawa.
Ni wata irin matace sannan kuma wata irin masoyiyace wanda bazata karu da mijinta da komai ba sai kawo masa damuwa da kuma hatsari,zan kasance mai son kai idan nace kacigaba da nuna min so ko kuma tunawa dani,dan haka kayiwa allah badanniba sai dan allah yah sameer ka koma rayuwarka da kakeyi a baya kaman kk wanne mutum mai farin ciki,ka barni nacigaba da rayuwata kaman yanda nakeyi wacce banajin tausayi banajin shauki sanann banjin dadi,ta hakane kowa zai zauna cikin farin ciki nima kuma na rayu ina kallonku kusa dani "
Shiru nayi da magana ina cigaba da rusa kuka mai tsima duk zuciyar wanda yake saurarona,kirjina na rike gam wanda yake barazanar fashewa da hannuna,shima sameer dayaga haka rarrafowa inda nake yayi idonsa yana zubar da kwallah,wamda nasan ganin halin danake cikine yah saka shi.
Rike dukkan hannayena yayi da nasa hannun kafin yace cikin karfin hali.
"Menene yake faruwa da rayuwarki sameemah,kiyimin magana naji kinji ki daina rike abu ke kadai haka"
Bude bakina nayi zance masa wani abu sai kuma naji bakina yah cika da wani abu mai dandanon gishiri,zubar dashi nayi da sauri,anan naga ashe jinin ne har da guda guda,wani tarin ne yasake sarkeni da karfi mai matsanancin ciwo.
Jinine yake ta zuba daga bakina kaman famfo wanda da kadan kadan naji jikina yana shikawa har saida yah zamo dishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login