Showing 27001 words to 30000 words out of 74994 words
Chapter 10 - MATAR OGA NA COMPLETE DOCUMENT writing by UMMY AYSHA.txt
Deedee tace'' Kai Jameel dauki wayar banza kirawo yan iskan nan masu bakin glass da matar shi tace suna zuwa ɗaukar shi cemasu yace abari zai nemosu bayajin daɗi.
To yace ya dauki babbar wayar tashi yaganta da security.
Miye possword naka yace yana kallon shi.
Adnan ya juyar dakai cikin tafasa zuciya da tinanin abinda zaimasu duk ranar daya ganshi tsaye da kafar shi.
Ganin zai batamasu lokaci yasa Jameel fizgo hannuwansa ya dangwala ta bayan wayar take ta bude ya fara shige shige last call din shi da yayi ne yabi.
Bayan an dauka ya mikama Aymah anan ta sanar dasu bayajin dadi yace subari zai nemesu.
Fatan Alkhairi suka mai ya aje wayar Aymah tace. tom tashi kabar gidan dan kaine da bari nikam dai zama daram daram sai na nemeka kazo.
Zai fara kururuwar ihu katti nan da suka hau gyara saman dakin nashi suka sakko sukai sama dashi .
Wannan Dattijon dake nuni da shine mai gadin Dr ya bisu yana nunamasu hanya.
Cen wani kauye mai bala'in nisa suka kai shi aka jingine kasan bishiya bayan sunba wanda zai dinga kula dashi 5k da ledar garin kwakin shi sukai gaba Abin su.
Ɗan sauran kudin Adnan Deedee ta dauka da yamma ta saimasu katiffai don tace ta dawo gidan saitaga abinda zai turema buzu nadi.
Dan barinsu agidan kamar sun tonama kansu asirine kuma idon mutanan shi zasu dawo kanshi wannan shawarar da suka yanke yasa Dr ba Aymah wayar tashi da suka riga suka ciremata possword gaba daya dan duk wanda zai kira ya sameta..
Da yamma Deedee taje gida tamasu bayanin abinda yafaru duka sunsha mamaki daganan sukai fatan Allah yasanya Alkhairi ta nunamasu saboda kadaici tanaso ta zauna da Aymah dan debemata kewar Iyayen ta.
Amsawa sukai baki daya dan sun aminta da shawarar Tata
Rayuwa suka fara mai daɗi Tsakanin Aymah da Deedee komi cikin jin dadi da walwala .zaman Deedee gaban Aymah ya mugun debe mata kewa da kuma dawo mata da farin cikin data rasa na rayuwa.
Adnan kau ba kasafai take tinashi ba tinda ba Alkhairi bane a rayuwarta.
Jameel kau sosai yake cikin damuwar da duk iyayen shi sunyi tambayar duniya yaki cewa dasu komi.
Da yamma yayi shirin shi tsaf yayi bala'in kyau cikin wata brown din shaddar daya dinka ga wata sallah dabai fiya sata ba ya kafa hula coffee ya fesa turaran sa mai saukin kudi wato Emergency.
Tinda ya fito Malam ke fadin masha Allah yau kuma sai ina Jameelun Deedee kamar wanda ya samomuna sirika matsala daya dai babu walwal a fuskr ka.
Dan Murmushi yayi yace zanje naga Deedee.
Murmushi kawai Inna su tayi tace dan Allah ka gaishesu da Aymah.
Tom yace kamin yakama hanya ya tafi.
Zaune suke a tsakar gidan da yanzu yazama wajen shan iskan su Deedee ta dafamasu gyada sai cin abinsu suke suna fira.
Da sallama ya shiga dukkan su suka zubamai ido bayan sun amsa.
Deedee ya gaida kamin ya dan saci kallon Aymah ya ɗan turo baki.
Itama Kallon nashi tayi kamin tayi dan murmushi tace" ina kwana Jameel.
Lfy yace yana dan hade fuska .
Deedee ta rike haɓa tace Jamalu minike gani haka wanga lamari tafa girmema?.
Pink lips dinsa ya turo yana fadin to ni ba Namiji bane .
Ido suka zaro su duka kamin Aymah tayi dariya tace "hakane kam sannu da zuwa ta tashi tayi ciki dan kawomai ruwa.
Zama yayi Deedee ta kamo hannushi tace "Dan Allah da manzon sa mike damunka Jameel, mahaifinku yace na tambayeka dan Allah minene ko son umma ne yamaka yawa?
Aa Deedee,Abu daya ne ke damuna arayuwata.
Taya zan iya samun sana'ar da zan rike ku a halin yanzu.
Deedee kayan abincin kufa yayi kasa.
Aymah maca ce Deedee tana bukatar yan Abubuwan rayuwa na mata.
Deedee tayi tagumi tace wallahi hakane da ɗan pampas din nan na zamani da suke likawa in suna haila da kuma Turaruka gata da son gayu ni nama Manta bansawo mataba danaje sayayya.
DeeDee zan koma sana'a ta ta da gaskiya bazan iya ganin Aymah ta tagayyaraba asanadina ta salwantar da dukkan abinda ke garetafa Deedee.
❤️ MATAR OGA NA ❤️
Mallaki
Ummy Aysha
Domin mallaka naki ki biya kudin ki ta account Number nah kamar haka
9064260199 Amina dahiru OPAY BANK saiki turo shedar biyan ki ta Whatsapp number nah 07038423451
Page 13
Deedee taja numfashi tace.
Hakane! shiyasa nima kaga Dukkan wani abun da zanyi na faran ta mata inayi saboda wannan yarinya Wallahi inajinta tamkar kai din nan, ina son Ummu tana da kyakyawar alaka ,tana da kuma saukin kai ,bata da kyamar talakka som.
Kai namiji ne Jameel jajirtaccen daya kamata ya tsaya da kafar sa. na baka goyon baya dari bisa dari.
Dukkan abinda kasan zakai da karfinka da gaɓɓan ka in dai aikine na halak, kai koda kwasar kashi ne kam na baka dama kaje kayi ka wadata da abinda Allah ya Hore ma..
Mahaifin ka Kuma tinda Allah yasama sana'ar shi Albarka kabar shi ya rike nashi iyalin ,kai ka zamemata garkuwa ko nace ka zamemuna, Allah ya sanya Albarka ga dukkan abinda zaka taba yamaka jagora zuwa ga neman Halaliyar ka duk inda take.
Ameen yace yanajin dadin addu'a ta.
Aymah kau dake tsaye bayan su tin sadda taji ya ambaci sunan ta ta tsaya cak.
Wasu hawaye masu bala'in zafi suka zubomata,ashe duk inda take kai farar zuciyar su Deedee da zuria ta sun wuce myan,Taya,zai wahala yazo ya kashemata? Akanta kawai.
Idon ta ta daga sama tana wani nazari.
Saidai ina lokacin bayyanuwar hakan bai ba gareta, Bayyana wannan ɓoyayyan sirrin nata kamar watsa sabuwar rayuwar da xata gina ne anan gaba .
A'hankali cikin sanyi jiki ta karasa inda suke ta ajiye masa flat din da tasamasa ruwan pure water mai sanyi dan tini suka maido fridge din Adnan palon ta na kasa.
Daya ya dauka yace Nagode kamin Deedee tace'' Aymah wai yau kodai bakyajin dadine naga idon ki ya kumbura ko zazzabi kike?.
Da sauri Jameel ya ɗago kai ya zubamata ido baya ko kyaftawa sai zujiyar sa dake tsalle tsoron shi daya kar ace wani abu ke damunta .
Cikin sanyin ta tace banajin komi kaka kawai dai hakanan naji sauyin jikina.
To ko muje Asibiti. cewar jameel yana zubamata ido cikin kulawa.
Dan murmushi tamai tace A'a bai kai nan ba.
Fuska ya ɓata ya mike ya zura takalman sa yace" Deedee bata mayafi muje Asibiti Amma Hijjob ba gyale ba.
Deedee tace kwaraiko kuje! Hijjob kuma wannan baka isaba abinda take so shixata sanya.
Ido ta zaro sadda taga ta mike cikin shagwaɓa da takema Deedee datake gani kamar uwarta tace" nifa gaskiya bazanjeba amun allura, kana bake ce kikace ya koma aikin sa na daba dan ya samomun kudi ,nikuma baki fadaman miye aikin ba ko na wahalane oho ta karasa tana turo baki da Dire kafa kamar yar 17yrs...
Sassanya Murmushi ya saki yana yin kasa da kai da sauke ajiyar zuciya jin dadi da tace ba komi ke damun taba .
A'Hankali yace "madallah da wannan halitta mai dumbin Alkhairi..
Deedee kau haba ta rike tace ƙudura sama liman da wawan zama ! Yanzu dama duk akan wannan karama matsala kika saki lokaci daya? yo nace in bai nema mikiba wazai ba?.
Murmushi tayi suka hada ido dashi ta d'agamai gira kana tace shi din nan kanena ne Deedee,Hakkina ne na tashi tsaye wajen neman nawa na kaina dan samar mishi abinda zan gina shi.
Kai wai kai mene ma matakin karatunka ta karasa tana zaro mai ido da daure fuska irin ita Babba nan.
Kai ya shafa yana murmushi dan ya lura so take ta kasheshi da salan ta kamin yace "ai mace bata girman namiji som, Yanzu haka da wani abu xai shigo gidan nan ita kanta wannan Deedee data baje anan aguje zatai ciki nine dai zakin da zan tsaya naji mike shirin farauta Iyali...datse harshen sa yayi da karfin masifa tinowa dayayi da katoɓarar da zayyi.
Deedee kau dariya tashigayi yayin da Aymah bata gane hausar tashi ba .
Deedee ta dauki ɓawon gyaɗa ta hau jefamasa yana caɓewa.
Tace Allah ka shiryaka yaron nan ..
Aymah kau murmushi kawai tayi tana wani nazari.
Anan unguwar Yayi sallah mangariba da isha kamin yaci abinci ya masu sallama ya tashi.
Washe gari ana gama Asuba bayan yagama duk kan azakar nashi yama su Baba sallama ya fita.
Kai tsaye tasha ya nufa wajen abokan sa na da.
Sun kau yi farin ciki matuka da ganin shi dan tinda ogan shi yayi accident shima yabar zuwa.
Jiki na rawa aka hau bashi key na motoci dan kowa yason shi da zafin nama gashi baya wasa da Hakkin kowa.
Motar Dutsama kawai ya karbi key dinta dan bayaso yana nisa dasu yafiso yaje garin dake kusa da nasuya dawo cikin ikon Allah.
Karfe tara akama motar lodi ya hau ta da addu'a.
Cikin kwarewa yake murza sitiyarin ya kaisu lfy ya sake yin wani lodin na katsina ya dawo .
Bayyi kasa a gwiwaba ya sake hadawa ya koma.
A takaice saida yayi tsawu ukku kamin aka raba kudin ukku akabama mota daya, shi daya , Mai mota ɗaya .
Ba laifi ya samu kudi a ƙallah dubu 8k
Koda ya dawo gida ya zubema Inna su shi sosai suka samai Albarka sukamai murna.
Yace su ɗauki nasu ya kaima su Deedee sauran.
Baba dake gefe yace A'a bazaayi hakaba gaskiya.
Ka kaimasu sai kaima ka rike wani abu ni Alhamdulillah wanda nike samu Ya ishemu .
Aa yace yana mikewa yace babu abinda zanyi nida gobema in sha Allah fita zanyi wannan ai na farko ne dan Allah ku dauko wani Abu..
Albarka suka sake samai Inna su tace to ga 5k ka kaimasu mu bari mu dauki biyu kai kuma ka dauki daya kayi kalaci.
Godiya ya masu kamin yace wai Inna mu ina wannan Halima dake zuwa gidan nan ne.
Malam ya harare shi yace sai yau ka tinota yarinya datama bauta da iyayen ka kamar zata mutu ta gaji ta koma garin su.
Baki ya dan tabe kamin ya shige dakin shi ya dakko kayan wankan shi ya dibi ruwa yayi wanka ya daura alwallah mangariba.
Bayan ya zira kananun kaya masu baylain kyau ya fesa turare kana ya dauki hanya gidan Aymah.
Da sallama ya shiga gidan bayan an'bashi izini ya shiga palon kasancewar akwai wuta firar su kawai suke wayoyin Adnan gaban Aymah tana dan lallatsawa Akai akai .
Ido ta dago tace kanena sannu da shigowa.
Wata harara ya dan ballamata yana faɗin. gaskiya zan daina zuwa kinacemun haka Deedee kimata magana.
Tom'tom sorry Yayana na daina sannu tace tana murmushi.
Yawwa lovely sst tnx u.
Deedee tace cen dai ta matsemaku kai gyambo da san girma ita kuma tana biyema taɓarar ka.
Karkacewa yayi ya zaro 5k din yace gashi ku fara sayen abinda babu dan Allah zuwa gobe.
Aymah ta zaro ido tace kai Jameel miye kayi ka samu kudi.
Sata nayi.
Ya bata amsa kai tsaye yana zubamata shanyayyun idon shi.
Ido ta zaro tare da hada hannaye tace" bance ba! Amma Dan Allah wane aikin wahala kayi yabaka wannan kudin .
.
Deedee tayi murmushi tace mota fa yafaraja yanabin garuruwa dama aishine sana'ar shi.
Sosai Aymah ta mayar da attention dinta kaf kanshi tare da zubamai fararan idanun ta da a hankali hawaye keta kwanciya ciki.
Shima din kallon ta yake amma irin kallon nan na tsoro da bazaice ga nufinta a zuciba shin kudin ta raina koko oho dai.
Tsawon lokaci kamin cikin sanyi tace" Duk akaina ka fara wannan wahala?
Deedee tayi Murmushi tana fadin' bari dai in watsa ruwa inzo mungode Allah ya tsare ka daga sharrin abin hawa.
Ameen yace yana gyara zamanshi har lokacin zuciyar shi bugawa take dan baison hukuncin Tambaya da Aymah ta masaba.
Tana ganin wucewar Deedee ta rarrafo inda yake gab da junan su kamin tace" Jameel.
Dan kallon ta yayi yace" na'am.
Miyasa ka zabi komawa abinda ka bari saboda ni?
Kafada ya daga kamin yace kawai hakanan sabida kasancewar ki marainiya ayanzu baki da gatan kowa saina Allah dani,to gani ai bazan amince ki fita nema ba,Kana karki manta saboda nine kikayi missing kaf abinda kika mallaka,So in ban tashi na nemar miki ba waye zaibaki ?.
Hawaye suka zubomata kamin tace.
Jameel dan Allah da manzon sa in dai nice ka daina ,kabani lokaci kalilan dan Allah,Kana wallahi badan kai na rasa komi ba,Yana cikin ƙaddarata,Karka manta komi a rubuce yake a kaddara bawa fatan mu dai Allah kabamu ikon cinye jarabawoyin mu...
Ameen Ameen..
Amma in'dai Hakane kinga kenan nima komawata wannan aikin yana cikin ƙaddarata so kimun Addu'a kawai.
Murmushi tayi tana dan kallon shi tace" kai ko,nizakawa wayo?.
Shima murmushin ya mata yace" A'a kawai dai inq bisa sunnar maganar kine komi kaddarane a rayuwar bawa.
Tom Allah ya mana zabin Alkhairi,amma ni yanzu nafiso koda neman zakai ka tattalawa kanka kaga ka dan fara girma kyanshi ace nan da shekara ukku zuwa biyar in aurar dakai, kana bikin ka ba irin na kowa bane dole muyi dogon tanaji..
Ido ya zaro kamin ya k'ank'ance ɗaya akanta yace Biyar?,dan bakya sona, sai nayi shekara biyar ba aure,in sha Allah nan da shekara biyar yaron mu ko yarin yamu sun kai shekara hudu.
Kaf fara'a fuskarta ta dauke jin furunci shi cikin wani alhini tace " Kenan dama kana da wacce kake so amma baka fadamana ba.
Murmushi yyi yana shafa kanshi yace" Allah mas@ni ,muna dai lalubune a duhu.
Deedee ce ta fito tana baza kamshi tace "wai har yau firar bata kareba ni inacen har nayi nazarin Abinda zai fishe mu.
Aymah tace kaka miye kika nazar ta?.
Deedee tace "bazamu zubamasa ido kullum Yaje ya nemo ya bamu muga Randuna sai dai mu girke ana zubamamu muna lashewa.
Dan haka nida yar jikallena tsaye zamu tashi wajen neman na kanmu sana'a zamu fara in sha Allah , Gobe goben nan zanje kasuwa Naga abinda ya dace nayi.
Dariya ya hauyi harda rike ciki abinda bai fiye yiba.
Sosai Aymah ta shagala da kallon baiwar kyan dake tattare da matashin bawan Allah nan mai jini ajika.
Deedee kau rai ɓace tace" ai dole kayiman dariya ka daukan mahaukaciya nadai gama ma komi tinda na kawo ubanka duniya.
Cikin danne dariyar sa yace "kema Deedee daga shiga har kinyi bacci da mafalki saiki hango abu har ya tabbata.
Takalman kafarta ta cire tana fadin tashi kabar gidan nan gwauron banza ko in'bugama aka.
Mikewa yayi yana bude hannu da fadin "ko baki koramba tafiya zanyi nan ya masu sallama yatafi.
Ajiyar zuciya AYMAH ta sauke tana lumshe ido.
Washe gari Jameel karfe takwas ya bar gida sadda ya isa tasha shine kawai ake jira .
Kamar yanda ya zama akidarsa fara addu'a kamin hawan karfe haka yayi kana ya kunna suka dauki hanya sai fatan dawowa lfy.
Deedee kau tana tashi ta damamasu kunun tsamiya da kosai suka zauna suna kalaci Aymah kau sai santi take dan ita duk bata iya wannan kayan galgajiyar ba gata da son su shiyasa in Didi nayi kamar kunnan ta ya tsinke.
Bayan sun gana tashiga gyaran palon Dede tamata sallama ta fita kai tsaye kasuwa ta nufa.
Zobo ta auna kwano biyu da aya kwano biyu da citta da kanunfari na 500.
Wajen masu fruit ta nufa suka hadamata
kwakwa
Dabino
cocumber
kankana
Kashu
Abarba
kana tayi gida zuciyarta fess.
Koda Aymah taganta da kayan itama dariya tayi tace .
miza'ayi da wannan Deedee karki manta G.R.A muke batasu ake ba kar abinki Yayi kwantai.
Cikin bama kai kwarin gwiwa Dede tace in sha Allah bazaiba na fadamiki tsaya dai kiga ta karasa tan aje mayafi ta ɗauki Ayarta ta surfa ta wanke sosai ta cire tsakuwar kana ta samata ruwa ta aje ta hau tafasa zobon dayaji citta da kanunfari da bawon abarbar data saya.
Cocumber da kankana da Kashu da sauran Abarba tasa Aymah ta mata blending nasu.
Zoɓon na tafasa ta tace tare da juye kayan fruit din ciki ta ɗauki sugar da foster dinta mai kwakwa da gwaiba ta juye aciki wani ni'imtaccen kamshi ya fara tashi kota ina.
Aymah ta ɗibi wani a roba tace" tun kamin yayi Sanyi yawuna ya tsinke tasa a fridge.
Deedee tace ja'ira kyama sake fada ta dauki markadan Ayarta da kwakwa da dabino ne kawai aciki sai citta da kanunfari tace .
Natafi kai markaɗe.
Aymah tace kawo nakaimaki tace A'a bashi dai na fita.
Da kwatance ta gane wajen mai markaɗan nan tayi tsaye ta wanke injin din tass da kusan rabin jarka ruwa.
Mai markadan natamata dumin ta karar da ruwan taa.
Shuru Deedee tayi tana kissima yanda zataimata .
Ana'mata fashi ukku tace.
Baiba saida akayi biyar kana ta dauki goma ta bata tace ungo kyasai ruwan wannan kuma darin markade ne gobe in zandawo nazo da ruwana kazamar banza.
Takaici ya kashe matar ta bita da kallo Deedee ta mata murmushi tace bye inji Anna (Arna)
Koda taje gida ƙanƙara tasamu takai biyar ta dinga fasawa tana juyewa kamim ta samu suyi ta tace ta xuba shiga tare da kulla abinta tsaf ga leda da duk ta saya tashiga sawa a fridge.
Karfe biyar na yamma komi yayi sanyi sosai.
Tayi wanka, ta shirya Tare da fesa turare ta dauki karamin boket ta zuba komi goma goma yace aymah xanje in dawo.
Ido Aymah ta zaro tace badai tallaba.
Aa haba sadaka zanyi ina zuwa.
Fita tayi ta fara shiga makwaftan dake kusa dasu duk in an'gaisa zatayi kwatancen gidan da take suyi barkwanci da masu gidan kamin tace to sana'a nike gashi a a ɗan Ɗana kamin azo asaya.
Duk kau gidan data ba sai sunsha gabanta suna santi wasu subata kudi da niyyar zasu bita su kara saye wasu kuma suce zasuzo saye ahaka dai tashiga gida goma cur kamin tadawo gidan su Yara biye da ita da zasu karɓa nan ta shiga zubama kowa abinda yake so.
Karfe shidda yayi sallama ya shigo gidan hannusa rike da leda.
Wani milk din yadine jikin sa mai saukin kudi an'mai ɗinki zamani ɗan madaidaici yamasa masifar kyau. madaidaiciyar sumar sa tasha gyara sai kamshi yake.
Sannu da zuwa sukaimai Aymah ta tashi ta kwasomai kunun Aya da zobon Deedee ta kawo da jallop din taliya da suka dafa.
Allah yasakamiki da Aljannah yace yafara Bissimillah yanaci suna dan fira da Deedee dan Aymah kau hankalinta naga wayar Adnan.
Suna zaune akaita shigowa sayen zobo kan kace mi abu yayi kasa saida Deedee tace babu kana aka kyalesu tace kai kaji gantalallu an'saba shan lemu mai karas yau anji nawa ana so azuke man koni banshaba.
Dariya yayi yace wannan ne kike Sayarwar ?
Eh mana yayi dadi Ko.
Sai magana yaga Aymah