Showing 6001 words to 9000 words out of 74994 words
Chapter 3 - MATAR OGA NA COMPLETE DOCUMENT writing by UMMY AYSHA.txt
kuma na mayar dashi kabir,Saboda na daɗe da fara littafin aka fara azumi na dakata sai yanzu naga dacewar cigaba to kuma ban samu page one nd two ba saidaga baya so kawai zamuje da sunan jameel din ne nagode ina fatan kun fahimce ni.
***
Innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un wannan yaron karfa ace ni na kasheta kason abin fada bayayin wahala wa mutane.
Jameel da yaketa kallon sashen wuyanta da yayi sawun riko alamar shaka ya dago jajayen idanun sa ya zubama mahaifiyar tashi tare da faɗin" Inna banson mizamuyimata ba, amma mafita daya akaita Asibiti kawai.
Yawwa hakan yayi akaita Asibitin ta kawai tace cikin sauri.
Halima ta kama mai kafafuwan ta suka sanyata bayan mota ya shiga mazaunin Driver Inna su ta shiga gefe yayin da sukace da kabeer ya shiga ya kula da gida suka ɗauki hanya.
Basu wani jimaba suka iso mahaifin shi malam Habu na zaune kan Benci da redio yana jim labarai ya tashi da fara'a ya buɗe get din Asibitin yana fadin" Hajiya barka da shigowa.
Jameel ne ya dan leko yace barka Baba sannu da aiki.
Cikin mamaki mahaifin nashi ya sake kallon motar da kuma kara dalla shi da fitila duk da hasken fitulun dake harabar wajen kamin cikin mamaki yace , kaine da Mota Hajiya?
Kai ya dagamai kamin ya shiga yayi parking Baban su ya rufe kofar da sauri yayo kanshi daidai sadda Baraka ta fito daga motar.
Wani irin sauri Malam Habu ya kara ganin matar tashi da gaggawa ya cimmasu yana mai sanya hannu wansa ya kama na Baraka.
Kamar jira take ta fashe da kuka tana fadin "Baban su Hajiya ce gatanan kwance babu lfy tana aman jini ai maza a kirawo ma'aikatan jinya dan Allah su duba ta.
Jin hakan yasa shi fadin" innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un. Tare da sakin Baraka da sassarfa ya fara kiran nus din cikin lokaci suka fito da whell chair dan sunson bai wuce majin yaci aka kawo ba yake neman kashe masu Dodon kunne...
Waye babu lfy malam Habu ka bude baki kanata watsamuna kira haka? Haba da Allah ka dinga daukar rayuwa da sauki.
Cewar wata Yar tsamurmura dake sanye da fararan kaya kamar sabuwar gawa sai karairaya take ala dole ita ma'aikaciya ce.
Jameel kau dake tsaye ranshi yayi matukar ɓaci cikin bala'in saurin maganar dayakeyi mai haɗe da in ina duk sadda ranshi yakai matukar baci ya nunata da yatsa yace.
Ke kikama kanki..ɗi..yar Yara ko in wanke miki fuska da mari, maza kwasheta ku shiga da ita ko in'baki mamaki Ya karasa idon shi rufe cikin muguwar tsawar data sanya jikin su ɓari.
Malam Habu ya matsa ya rikemai hannu yana faɗin Kayi shuru kaji yaron kirki,Kyaleta Allah ya tausashi zuciyar Jameelu na,Kuma Jamalun Deedee .
Shiru yayi baiko motsa ba kuma bai bude idon saba.
Ke kuma Ramatu Hajiya ce ke bata lafiya shiyasa kikaji ina kiran ki da ƙarfi amma kiyi hakuri.
Jin haka yasa da sauri suka karaso motar suka fiddota har lokacin kadan kadan jini na zubomata ta bakinta da kuma hancinta.
Shikau jameel A'Hankali ya fara bude idon shi da sukayi wani mugun ja, Duk da duhun dake saman sararin samaniya amma kana ganin yanda hasken fitulu suka tona Asirin hawayen dake kwance a cikin kyawawan idanun nashi.
Wacce aka kira da Ramatu Kallon shi tayi sadda zasu wuce da Aymah tanajin wani bala'in tsoro da shakkar shi ,ga wani kwarjini da yamata, a wani sashen kuma na zuciyar ta ya bala'in burgeta mussamman sadda yake magana nan Cikin sauri da sauri gashi in inarsa ta motsa saidai ya rufe ido kamin ya samu magana tayi daidai Ya buɗe..
Yana ganin wucewar su yayi tsaki yana kallon Baban nasu.
Malam Habu yaja hannusu su duka suka koma gefe dan yason dokar Asibiti ba A bari ka tsaya wajen majin yaci yayin da DOCTOR ke duba shi.
Bayan sun zauna nan Baraka ta shiga koramasu bayanin abinda ya faru .
Jameel na jin su baice komi ba Amma har cikin ranshi yaji mugu mugun tsanar Alh Adnan dama shi bai maiba tin farko.
Baba habu ya gilgiza kai cikin rauni da salon iya magana na Dattijon Arziki yace.
" Kai Maman su Allah ya ganar da wasu mazan,hakika wasu mazan na jahiltar zaman Aure,suna ganin duk sadda suka nemi mace suka samu aka basu ita tayi sallama ta shigo gidan su to daga ranar ta zame masu baiwa,ta zamemusu takalmi duk inda suke so zasu taka da ita,Suna ganinta kamar baiwa babu mu'amullah mai kyau da zasu iya yi da ita,nikam aganina daga sadda iyayen ka suka baka mace ka kulle kofa da ita Maman su ai angama maka komi ko? , Sannan matan mu marufin sirrin mune,duk sadda muka kasance masuyin rayuwa mai dadi da matan mu wallahi azeem sai munfijin dadin rayuwa koda ba ko sisi,Ke Baraka banason Allah yabani arzikin da zan gujewa iyalina kwara na zamana cikin rufin Asiri nafi samun lokacin da zan sauke hakkin ku dake kaina,Ta yanda zan karɓi sakamakona da hannu dama a gobe kiyama..
Hawaye Baraka ta sake sharewa tace.
" Wallahi Baban su na sani, Kuma ina mai kyautata maka zato,Bazan ce bama faɗaba saboda tsakanin halshe da hakorima ana sabawa ɓalle mutum da mutum,Amma tabbas samun ka a wannan lokacin Babba rabone saboda irin ku kunyi karan ci.
Wannan yaron dan Allah kuyi koyi da halin mahaifinku dan Allah, Duk wacce Allah zai baku kumata irin rikon da mahaifin ku kemun ,kunga dai yanda muke rayuwa dashi da daɗi ba daɗi amma babu abunda ya dakushe daga fannin kulawar da yakemun,Bana tinanin tin tashin ku kuntaɓa ganin muna faɗa dashi yace nace,To munayi.
Amma adaki,sannan ba ihu yakemun ba,Yana mun nasiha ne ta yanda zan fahimta amatsayina na mace mai karancin tinani,Ina ƙara godiya a gareka Ranka ya dade ta karasa tana haɗe hannayenta waje daya tare da sakin yalwataccen murmushin daya sasu duka darawa.
Kai kawai Jameel ya gilgiza dan yason duk Abinda ta fada gaskiyane, kuma shi kanshi baya fatan ace ya zauna da mace dan ya kuntata mata ,Yafiso ya zauna da wacce zata soshi domin Allah, yabata kulawa ta bashi, Ya tarairayeta ya bata lokacin sa itama ta bashi nashi.
Suna nan Nursing ɗin nan ta fito tana yanga tana gwatso da neman karewa tace" Dr Aymah na kiran Baraka.
Tsaki kawai Jameel yayi jin yanda ake kiran sunan mahaifiyar sa gatsau kawai dan batada kuɗi ,gashi wannan yar shilar har tasamu bakin Kiran sunan uwar su kai tsaye.
Da sauri Baraka ta tashi tace da malam habu tana zuwa ya dagamata kai yana fadin .
"Kiyi dai a sannu wajen a kwai sulɓi sosai tafi a hankali Kinji.
Murmushin gefen baki kawai Jameel yayi soyayyar iyayen nasu na tsananin burgeshi da bashi sha'awa, bakaramin taka tsantsan mahaifin su keyi da mahaifiyar suba bayaso ko ruwan sama na dukan ta( *WAYYO SOYAYYA DAƊI WLH ,ALLAH KA BARMU DA MASOYAN MU NA GASKIYA MASU GIRMAN KAI KAU DAN KAR IYALIN SU SU RAINASU ALLAH YA TSINE MUSU YAN KUTUMAR BURA'UBA*😎)
Koda ta mata jagora har dakin da take ta juya Baraka kuma ta rufe Kofar tare da ƙara sawa da sallama tace sannu Hajiya.
Aymah da hannuta ke sargafe da karin ruwa tace.
yawwa Baraka sannu,Waya kawoni nan?..
Dan Murmushi tayi tace ki gafarceni Hajiya yaro ne nasa ya kawomu da motar ki ganin ki cikin wani mawuyacin Hali.
Ido ta lumshe hawaye na zubomata tace.
" Baraka wai duk namijin da zai daga hannu ya dokeki yana sonki kuwa,Anya Adnan baya shaye shaye kuwa?..
Shuru tayi kamin cen ta nisa tace.
"Kiyi hakuri dai Hajiya aita gayama Allah, Allah zai kawo mafita.
Baki Aymah ta cije tana kallon ruwan hannun ta kamin kuma ta tashi ranta ɓace ta cizgeshi ta diro daga kan gadon.
Duk yanda Baraka ke mata magiya akan ta tsaya karta tashi amma ina zuciya ya ciyota(A kiyayi ƙure mai hakuri) .
Fitowa sukai tana ta sauri kanta hula ce kawai babu ko mayafi sai doguwar rigar data zuba data fito wanka dan ma Allah yasa dare ne ba kowa zai gane ba.
Kai tsaye motar ta ta shiga da hanzari Baraka ta buɗe gefe ta shiga kamin a karo na farko ta riko hannuwan ta tace.
*Ummu Aymanah*.
Da sauri Aymah ta kalleta dan Tinda Iyayen ta suka rassu babu wanda ya taɓa kiranta da sahihin sunanta cikakke kamar yau, batataɓama sanin tason sunan taba dan kullum Hajiya take cemata.
Kai Baraka ta gilgiza cikin dattako da girma tace .
Duk abinda hakuri baiba Aymanah rashin sa bazai ba,sannan babu abinda ke ɗorewa sai ikon Allah,fushi ba naki bane , Domin ke macace mai rauni ,Aikin mi kike da kika bar damuwa ta shiga ranki,ina Alkur'ani ki?Ina ilim ki da bazakiyi amfani da koyar wa annabi Muhammad sallalahu alaihi wassalam ba ki magance damurmwar ki,Ayma nason ban haifekiba amma kuma inajin ki kamar kanwata,Shawara daya ki kara dagewa wajen kyautata alakar ki da Allah,kana karkiyi zalinci,kina nan zaune zakiga sakayya daga mai sama,ki yawaita sadaka tana magance masifa ko wace irice,Ina mai baki hakuri da baki shawara da karki yarda kije wani wuri a halin da kike ciki yanzu kiyi hakuri ki koma ki zauna daki da safe sai ki koma kibashi hakuri, tana gama fadin haka ta bude motar ta fita tare da zagayowa ta budema Aymah ta kamota kamar jaririya haka suka koma ciki,Kai tsaye office dinta ta nufa Baraka na rike da ita ganin yanda take rangaji kamar wadda tasha giya.
Nasiha Baraka ta sakemata kamin tamata sallama tace zasuje gida.
Harta sanya hannu zata bude Aymah ta dago jajayen idanunwa ta kalleta tanajin wani girma da mutuncin matar na ratsa ta lungu da sakon ta, akaro na farko taji ya kamata ta girmamata ta daina fadin sunanta gatsau kamar yanda ta saba,Ko ba komi yau ta mata abinda iyaye ne kawai zasuma shi..
Kanta ta mayar a kasa tace nagode Baba Baraka Allah yasaka da Alkhairi,kana kicewa Baba ya rufe get din kuje tare da Asuba ya dawo.
Madallah Nagode Baraka tace tafita tanajin tausayin Aymah a ranta , Duk da batacemata ga abunda ke faruwaba amma tana tare da ita tanaganin yanda shakkar mijinta ke hanata sukuni in dai yana nan, ya riga ya samata tsoron shi cikin rai(Nikam nace gidan miji ba barikin sodoji bane Adnanu mai kan kwakwa)
Koda Baraka ta fita ta faɗama Baba gida suka wuce sunata tattauna maganar Akan Aymah da Alkawarin sata cikin addu'a su dan ta masu halacci yanzu sular tace suke samun ci dasha har so ukku arana.
Jameel dai baice komi ba dan shi dama miskiline na bugawa a jarida magana hamsin zakayi muddum baka sashi ba baya tankawa.
*Alhaji Adnan*
Tinda ya zube kasa yake ihu yanajin kamar ranshi zai fita,Ya daɗe a wannan yanayin kamin ya samu sukuni yatashi yana kokarin bude kofar amma ta rufe ta waje.
Mai gadin gidan ya kira yazo ya bude shi kamin ya samu fitowa yana sakin numfashi sama-sama.
Dakinta ya tura ya shiga wayam. Dama Yayi tinanin haka dan sama sama yaji tashin motar ta, kenan nufinta ta hallaka banza , aiko zai maganinta yason duk inda taje zata dawo tinda bata da gidan daya wuce nashi .
A daddafe yayi wanka, Bayan ya gama ya fito dakyal yake tafiya,Zaman palon ya fara yaji ya gaji ya koma daki da niyyar fara aiki amma ya kasa gaba daya ta lalatamai wannan ranar yanaji yanagani ga xafin da yakeji kamar zai hallaka shi.
Karfe goma da rabi na dare yaji kamar zai mutu ko wando bai iya sawa dole tasashi lalubo number jameel.
Saida yamai kira ukku kamin ya dauka yayi shuru.
Maza kazo dan Allah ka kaini Asibiti Alh Adnan yace cikin sanyi da murya dake nuni da yanajin jiki.
Jameel din yayi shuru kamin kuma yace" to ya ajiye wayar ya tashi ya sanya kayan shi ya fito ya iske Inna su da Baban su waje sunata firar su abin su cikin nishaɗi, gefen su gyaɗa ce Baban su na barewa yana samata a tafin hannu tanaci.
Baba Zanje in kai wannan mutumin wani wuri yace fuska ba walwala.
Allah ya tsare kawai sukecemai dan sungane wayake nufi tinda inna taba Baban su labarin aikin da aka daukai,sun son in suka cikashi da tambaya zai iya fasa fitar,Dan da alama bayason aikin kawai zayyi ne dan ya magance wata matsala ta gidan.
A ƙafa ya tafi har ya iso kai tsaye bakin motar da suka hau ɗazu ya tsaya yamai waya akan ya iso.
Kamar jira Hajji Adnanu yake sai gashi ya taho cikin jallabiya yana ware kafa jikin shi sai reto yake kamar wanda ya ɗaura laya..
Wata dariya ce taso kufcema jameel ganin yanda Alhaji ke watsa ƙafa kamar wanda ya hadu da sharrin wanzam.
Bayan motar ya buɗe bayan ya bashi key ya shiga da kyal suka dauki hanya.
Wata special hospital ya kaishi dakecen kasan su ta Aymah, Bayan an duddubashi aka bashi maganin da zai ragemai radadi kana suka taho gida .
Ko Sannu jameel baicemai ba haka yana ajeshi ya juya zuciyar shi fesa dan shi kanshi mamaki yake yanda yajisa cikin farin ciki dayaga Alhajin ma bayajin daɗi.
Aymah kau ba sallah zataiba saitayi zaune taita azkar cen ta dauki wayar ta taita chart cikin natsuwa.
Tsawon lokaci bacci ya kwasheta ta fara mafalki mai daɗi.
A furgice ta falka tana zubama waje daya ido,waye shi,kuma taya,Suwaye wayan nan yaran.
Bata da mai bata amsa hasalima saita shiga tashin hankali da kara tsinema Alh Adnan, gashinan halin daya jefata yana neman sa ta halaka har ta fara kwanciya tana mafalki da wani wanda ba halaliyar taba, Ya Allah ka warware mun ka xaɓaman abinda yake Alkhairi A rayuwata .
Washe gari da sassafe Baraka tazo ta ganta ita da Malam habu sukamata ya jiki harda dawainiyar saimata kayan fruit.
Sosai tasha hakan kuma ya masu dadi dan atare ma suka fito ta sauke Baraka ita kuma ta nufi gidan Haj Asiya.
Lokacin da ta isa wani tinani ya faɗomata hakan ya sata sauke Ajiyar zuciya ta juya motar ta ɗauki hanya.
Ido na zaro lokacin danaga Ta danna Hon Bakin get din gidan ta.
Bayan mas gadin sun buɗemata suka gaishe ta Amsawa tayi kamin ta kutsa kai ta shiga get ɗin na biyu har inda suke parking.
Cikin natsuwa ta buɗe motar ta fito daga ita sai rigar jikinta amma ta ɗora lab court akai da siririn farin mayafi.
Da sallama ɗauke a bakinta ta tura kofar palon ta shiga ..
General ne zaune ya ware ƙafafuwa tare da saita panka akan jikin shi yanata kwasar ganima iska, dagashi sai jallabiya daya ɗageta sama,gefen sa uban magunguna ne kamar za'a buɗe Chemis...
Yanajin buɗe kofa ya zabura ya tashi yayin da ko gezau idon Aymah baiba saima kallo data bishi dashi na ƙurullah kamar maison gano wani abu.
❤️ *MATAR OGA NA* ❤️
*MALLAKI*
❤️ *UMMY AYSHA* ❤️
*PAGE FIVE*
*ƘORAFI*
*MUTANE SUNATA KORAFI AKAN SUNA SO A RAGEMUSU KUDIN LITTAFI DUBA DA YANAYIN GARI DA KUMA YANDA RASHIN KUƊI YAYI ƘARANCI ,TO BA DAMUWA NA MAYAR DASHI 300 KACAL INA FATAN BAZAN SAKEJIN BAKIN KOWA BA NGD*
Ga wanda yayi shirin biya ya turo kuɗin Sa ta account number nah
*0006454115 Amina dahiru access bank*
Shedar biyan ka ta wannan layin nawa
*07038423451*
""" Matsanan cin rawa jikin shi ya ɗauka, Ranshi in'yayi dubu a ɓace yake,Gani yake duk duniya babu ɗan iska kamar Aymah, Babu kuma wanda yakaita buɗewar ido, wannan ma ya ƙara tabbatar masa da zargin sa tabbas Aymah ta son duniya , Yanzu abinda ta mai har zata iya haɗa ido dashi kuma cikin yanayi na dakewa ba tsoro ba shakka.
"Barka da safiya Yallaɓai tace cikin halin ko in kula tare da raɓashi zata wuce.
Aymah!
Ya dakamata mugun tsawar da ta sata dakatawa cak ba tare data cigaba ba.
Mikikazoyi gidana,Ashe zaki iya Neman kasheni kuma ki dawo inda nike? saboda baki da tinani kuma idonki ya gama buɗe wa ko?.
Ɗan juyowa tayi tana sakin murmushi .
Kamin ta fara tako dai-dai cikin Ƙasaita tana tura hannuwanta cikin lab court ɗinta tace.
" Adnan kenan!Mene zanji,mene zai bani shakka da tsoro A tattare dakai,Karka manta Rana ɗaya naga gawarwakin iyayena kwance gabana,Kana tinanin bayan wannan akwai abinda zai sake bani tsoro ya kuma furgita rayuwata,Noo b Ayishi ba,Kana dakaga na dawo gidan ka ai kason bana da inda ya wuce nan ko ka sakeni ne ban sani ba?Abu na karshe Anan shine.
Danmi ake koya maku training? Ba saikabani amsaba amma nason dan ku kare kankune duk sadda ka ganka a fagen yaki,Tom ni banje ba, bankuma karantaba, banma iyaba,Amma iya abinda yazo raina kenan dan in kare kaina da rayuwata nama abinda nama.
Kallafa. Tabuɗema sa wuyanta da yayi duhun kwanciyar jini.
Tace na tabbata da na sake 10mnt ina hannun ka da yanzu an kaini makwancina,Na cijeka inaganin hakan ne mafita amma baima ba saboda bak'ar zuciyar ka,Hakan danama shine dai-dai, kuma wallahi azeem ko yanzu ka sake kwatan ta kai hannun ka akaina sai nama Abinda yafi wannan, karka manta ranka anan yake,Zan jure komi bazan jure duka irin nakaba dan baizo a Shari'a islama ba ta ƙarasa tana juyawa zata tafi.
Gabaki daya jikin shi yayi sanyi duk wani kudiri nashi da yayi niyya kasawa yayi a dai-dai wannan lokacin , Wato takurawar da yake mata yakai ga tama daina tsoron sa da shakkar shi, lallai ya yarda da maganar Shekh Aminu daurawa da yake cewa duk yanda kake da mace karka ƙure Hakurin ta , Dan Mace in ta tashi so gabaki ɗaya take af'kawa, hakama in ta tashi ƙi gabaki daya take fitarwa , Ya Rahman ya Raheem yace yana komawa gefe ya zauna yana cika bakin shi da iska.
Aymah kau cikin natsuwa ta haye saman tayi wankan ta mai kyau ta sanya wasu riga da wando rigar mai hannun vest ce pink sai wandon Blue yalwataccen gashin ta tayiwa parking ɗin tsakiya tare da ɗaukar katon bnt pink ta ɗaure shi ta saki jelar , kamin tazo zata feffesa turare idonta ya sauka akan ledar Humra data saya wajen UMMY AYSHA.
Murmushin mugunta tayi tare da ɗaukar ta ta ɗan goga a hannu ta murje jikinta da bayan kunnanta .
Kamin ta sanya flat ɗin takalmanta blue ta ɗauki wayarta da headphone ta liƙa a kunne ta tura wayar Aljihu bayan ta sanya suratul Rahman cikin Qira'a Sheikh Abdullahi gwani wato majabakin Pantami.
Kaɗan kaɗan ta fara sakkowa daga step ɗin dan shiga kiching ta