Showing 18001 words to 21000 words out of 74994 words

Chapter 7 - MATAR OGA NA COMPLETE DOCUMENT writing by UMMY AYSHA.txt

08 Nov 2024

14607

kowa dan Inna su da Baban su suntafi su huta kamin tace".


Wai jamalun Deedee anya allura nan bata tabama kwalwaba,Nifa so ne nike gani cikin kwayar idon ka,Jamalu son MATAR AURE?MATAR OGAN kaface anya akwai hankali anan ta karasa tana ɗora hannu aka da Rusa ihu.


Cak ya tsaya yana kallon'ta kamin da kyal ya yunkura ya mike ya ɗan kama hannuta cikin balain sanyi kamin yace.


DeeDee nah" SO fa?
Wayace miki ?
Ni nace miki Deedee?
Deedee ya ake gane so dan Allah?




Cikim tausayi tace Jamilu wallahi azeem ka kamu da son MATAR OGA ka
Tausayinta ne yayi tasiri aranka har ya rikide ya komama SO mai zafi.
Bakai murna ka rabu da wannan uban cuta dayakai robar wanke shinkafa girmaba ,Fatan ka kawai ka ganta anan gaban ka sannan zakaji daɗi,idan ba so ba to miye?.


Cikin Karaya yace *Tausayine*
Deedee.


Murmushi tayi tace. Hmm amma dai kam akwai ƙura anan sosai.
Amma ba ason Abinda Allah yayiba wannan matar kau tabbas mituniyar kirkice,Kaf wannan kudin da akama aiki ita ta biya, silar haka kuma ta rasa duka dukiyar ta mai yawa,Nan ta shiga koramai bayani .


Batama ƙarasaba ya mike tsaye cikin tashin hankali yana neman tafiya.


Jawo shi tayi ya fasa wani uba ihu.




Cikin rawar jiki tace ka natsu Jameel wallahi wallahi ko rana ɗaya ne saina Ramama Yarinya nan Dukan da yamata .


Jameel kau bayajin ta gabaki daya idon shi ya rufe har wani jijjiga bakin sa keyi.




Cikim ihu ta kwallah ma DOCTOR kira.




Aguje kam ya shigo dan dama zaizo bashi takadda sallama.


Dakyal ya maida shi bisa gadon dan burkice mai yayi yana ihu mai gunza da faɗin saiya ganta.


Y salam Deedee tace tana dafe kanta.


Mama dan Allah bamu wuri inji DR.


Tashi tayi ta fita ya mayar da natsuwar shi akan Jameel yace" Abokina natsu ka saurare ni man.


Kallon shi Jameel yayi yana cije baki.


Murmushi yayi yace" kana sonta ne?




Ido ya dan zaro kamin yace" Aa nifa tausayi take bani ai Babba ce Kuma marainiya Bata da kowa!.


Sake murmusawa Dr nan yayi yace.
Ƙarami baya Auran Babba ne,Annabin mu ya auri Nana khadija data bashi shekaru kuma sukai Aure ,Akwai magana da zan fadama wacce zata zame ma hujja,akwai kuma taimkon da zanma duka rayukan nan biyu ma'ana kai da ita in sha Allah,Fatana dai kayi hakuri,ka kuma iya takon ka,karka bayyana Asirin zuciyar ka kai tsaye ,Saboda irin wannan abin da Mutumin nan kema baiwar Allah nan zai sanya mata ganin bakin maza ciki kuwa har dakai,Tinda a yanda naga ta damu ranar data bada kudin nayi tinanin ita zatai zaman jinyar ka,Bana da masaniyar an barta ko ba abar ta ba amma dai tabbas da saita zo sake ganin ka koda so dayana Amma shuru..


Kayi hakuri ka ida warkewa duka miya rage ?Dan'ma fa baka shan magani bakacin abinci da kwana biyune ko ukku na sallame ka.




Shuru Jameel yayi yana nazarin maganar shi ina shi ina son mace mai kudi Mai kyan Aymah,MATAR OGA NA fa kai ina ya faɗa a fili yana jujjuya kai .


Murmushi Yayi yace Ni kuma inaji ajikina kwana kusa zaka mallaketa tazama ƙarkashin kulawar ka inda rabo ta haifama yan Babys masu kama daku,Azahirin gaskiya kundace da juna Abokina...


Kunya sosai ta kama Jameel wacce saida tasa shi juya baya ya wani saki sassanya murmushi nan nasa daya daɗe Baiba ya wani lumshe ido da fadin anya,To taya?


Dariya sosai Dr yayi. har cikin ranshi yake tausayin su su duka , Amma in sha Allah mafita nata ɓullowa kota ina .
Haɗa mai komi yayi na maganin sa kamin ya kamo shi kaɗan kaɗan suna takawa suka fito .


Deedee ta zaro ido tace lfy?


Murmushi Yayi yace Zan aje Abokina gida ne Baba ki dakko kayan amfanin ku.


Baki ta washe tace.
" Kai Allah yamaka Albarka Ɗan lukuti, inaga yau zaka karya sihirin Aljanin Abokin shi,Yo miskilancin jameel yasa ko Aboki bashi dashi tin na yarinta da ya fada Rijiya ya rassu har yau baisake ba, kullum yana daki kamar mai jego,Yau kau gaka dashi abinda na dade banba Ai sai godiya.


Dariya yayi yace Miskili kafi mahaukaci ban haushi zan gyara miki shi kwana kusa.


Allahu yasha Yasha Dan lukuti.


Murmushi kawai Yayi dan in tana wani abu sai tabashi dariya yana son zama da Tsahhi yasha dariya ya kuma ƙaru da wasu labaran nada..




Yan kayan su da ba yawa ta halhaɗo ta fito dasu anata kallon su da Babban likitan da Bakowa yake kulawa ba.


Motar sa ya buɗe ya sanya Jameel gaba kana ya Buɗema Deedee Yan Kayan ya watsa su boot kamin yaja da bismillah suka dauki hanya Deedee na kwatan tamai.




Gab da gidan Aymah Jameel ya Kalle shi yace Friend Dan Daraja Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ku tsaya naganta na mata godiya karamcin ta gare ni.


Cak Dr ya tsaya yanabin gidan da kallo kamin yace DeeDee kimasa jagora ku shiga ku fito na ƙarasa daku.


A'Hankali ya fito ta kama shi yana tafiya sannu sannu.


Faɗa Deedee ta fara dataga yanda suke tafiya taki karewa kamin su iso bakin palo .


Akan kujerar robar barandar Aymah ya zauna yana sauke numfashi dan yagaji ba karya amma fatan shi yayi tozali da kyakyawar fuskar ta mai cike da karamci da Kamala.


Deedee ta kwankwasa kofar shuru tsawon 10mnt kamin taji an ɗan Budemata.


Aynah ce cikin shigar rigar atamfa hijjob dinta har kasa ga cazbaha a hannunta.


Kallon kallo sukai kamin kuma tace sannu Inna ina wuni.


Deedee dake mata kallon tausayi tace lfy klau sannu.
Ni Kaka Jamilu Baraka ce, Ni na haifi mahaifinsa to munzo Muyi godiya .


Ido Aymah ta ɗan zaro kamin ta ce sannu Kaka sannu fa shigo.


Aa ba sai na shigo Ba Allah ya miki Albarka Ya kuma yaye matsalaki ya baki mafita cikin gaggawa, Allah ya maki Albarka yajikan Magabata..


Ameen tace cikin rauni kamin tayi
Shuru Zuciyarta na bugawa dan so take ta tambayi jikin sa amma bakinta ya mata nawie ,bataso ta sake kullah alaƙa da kowane Namiji duk girman shi duk karantar shi.


Jameel kau da tin sadda ta fito yakejin wani masifaffan faduwar gaba, ga zuciyar sa sai tsinkewa yake yakuma kasa daina kallon ta..


Kallo ɗaya yamata ya gane ta bala'in rame kuma tana cikin damuwa fatan shi kawai yaji tayi tambayar inda yake dan ya lura som batagan shi ba .
Yana so yanda Ya damu da ita yaji koya ne ta damu dashi.


Deedee tace to mungode sosai Allah ya biyaki ya kuma baki lada kana ya warware Damuwar ki.


Cikin sanyi tanayin kasa da kanta tace "Ameen Kaka nagode,Dan Allah ki gaishemin da Baba Baraka sosai asake bata Hkr akan abinda ya faru Shii..m..a.. ace mai Allah ...ya .sa..wake..y..asa..anyi ...a Sa'a takarasa a rarrabe muryarta har rawa take idon ta na cika da Hawayen data kasa gane ko namiye..


Sassanya murmushi mai sauti ya saki da saida yasata dagowa da sauri idon su ya sarke dana juna.


Gabaki daya saida Zukatan su ya buga da bala'in ƙarfi, kowa ya zubama Ɗan uwan shi ido,sunama junan su kallo mai cike da kewa da kuma bege.


Aymah ce tayi saurin kawar da kanta gwfe tana dan wasa da yatsun hannuta dan wani girma ya karamata da kwarjini.


A'Hankali tace "ya jiki?


Alhamdulillah yace A'hankali Narkakkun idon sa akan ta .


Ɗan dagowa tayi suka hada ido da sauri ya kawar da kai gefe itama haka .


Kanshi ya ɗan shafa yace "Hidimar da ki kaiman Allah ya maye miki gurbinta da farin ciki na hr abada,Zan miki Addu'a allah yabaki tukwicin Aljannah,Ngd sosai nazone na miki gdy ya faɗa yana mikewa dakyal yana dan Cije baki.


Ido ta lumshe dan ba karya kalaman sa sun ratsa mata zuciya, sun kuma sanyata farin cikin Da take jin tayi bankwana dashi Abadan..


A'hankali tace Ameen tnx u.


Baice komi ba ya fara ƙoƙarin tashi da kanshi.
Da kyal ya mike ya fara tako Dan ƙafarshi tayi mugun sanyi .
Gab da ita yawani turguɗe zai faɗi.


Da Karfi ta kwallah ihu tana Rarumo shi jikin ta gabaki daya, dakuma dukkan ƙarfin ta hankali tashe.


Wani irin tsalle zukatan su keyi lokacin da suka zubama junan su ido Yana tallabe A hannuta.


Deedee kau kamar ɗiyar roba ta hau Kif-kifta ido dan gani tayi yanda yayi kwanciyar aka tallabe shi kamar wanda zaisha Mama😄




( Weyyyy Hajja Deedee nasu ba irin naku bane)


Last free page in sha Allah


❤️MATAR OGA NA❤️
Last free page


UMMY AYSHA.
PAGE 🔟






**Aymah kau cikin bala'in sanyi tace."Sannu kar ka fama raunin ka ta ƙarasa tana ɗagoshi A'Hankali.




Ido ya dan lumshe mata yana gyara zaman riga shi kamin A'Hankali yana ɗangyasawa Ya fara takawa.


Wani irin tausayin sa sosai ya dirar mata Ahankli tace.
" zaka dawo bayan ka warke?


Cak ya tsaya kamin ya juyo ya kalleta yace "kina buƙatar hakan?


Cikin wata shagwaɓaɓiyar murya da batason tana da itaba tace .
Babu kowa agidan kuma ina jin tsoro .


*Subhanallahi! A karon farko wannan magana tayi tasiri akwalwarsa har ta motsa lfyr sa ta ɗa namiji.


Ido ya lumshe mata kamin ya ɗan fara tafiya dan tsayawa kamar tonuwar Asirin sane.


DeeDee ta kalle ta cikin tausayi ta kama hannu ta tace.
Miyasa kike so ya tsaya Ummu bakya tsoron dokar mijinki yabi ta kanshi Kamar yanda yabi ta kan iyayen shi.


A'Hankali tace.


Kaka inajin tsoro sosai na zamana ni kadai agidan nan, Babu tsaro ga halin da ƙasar nan ke ciki,Kana dama yace shikadai xai bari yanamun sayayya dan Allah karkuyi fushi in ya warke ki barshi ya dawo gidan nan.


Deedee ta kama hannuta ido cikin ido tace..
Kinaso na taimakamiki ki fita kangin rayuwar da kike ciki cikin ikon Allah koko bakya so?.


Cikin rawar baki Aymah tace
Zanso haka amma Kaka na riga da nayi Alkawari wa Kaina bazanje ko ina Ba .
Saboda bana da inda yafi nan ,kana dangina duk sun gujeni bazasu karɓeni ba,Kaka Biyar dinma da zan hau mota bana da ita kibarni kawai inga iyakacin Adnan..


Murmushi Deedee tayi tana karema gidan kallo kamin tace.
Shidin banza shidin wofi.
su Makashima sunyi yayin su sun shuɗe balle shi da ko Rabin su baikai ba A hatsabiban ci ,gamawa dashi har wani abune bari dai jikana ya warke xan maki zuwan kanki kwana biyu, Yo kwana biyu Mana dan yakin bana dare ɗaya bane.


Murmushi sosai Aymah tayi tanajin soyayya kyakyawar tsohuwar har cikin ranta.


Murmushi tayi tace ngd Kaka Allah ya kiyaye.


Ameen tace cikin sauri ta cimmasa tare da kama shi suka fara tafiya.


Sadda zai Fita get din ne ya dan juyo a sanyaye yayin da sukai ido hudu da Aymah dake bin Faffaɗan bayan shi da aikin wahala yasa shi buɗewa da kallo.


Ɗan kauda kai tayi cikin aji yayin da shikuma ya ficce suka fada motar Dr suka tafi har kofar gidan su ya ajesu .


Deedee tace ya shigo yace A'a zaizo da mangariba.


Godiya sosai Jameel yama shi yana dagamai hannu suka shiga ɗan madaidaicin gidan nasu.


Da sallama suka shiga Inna su na tuka tuwo Malam Habu na daka Daddawa sai firan su suke, Yayin da Autan ta ke Wanke'wanken .
Gabaki daya sunyi farin cikin dawowar shi dan Kabeer rungume shi yayi yanata kuka dan akwaishi da karara zuciya gashi yanason Yayan nasa.


Bayan sun xauna sun natsu Deedee ta ƙanƙan ce ido tace .
Wallahi wallahi sai wannan auran ya mutu ina mai shedamaku kwana kusa , Saboda yarinyar nan akwai jini ajikinta na yarinta wannan azabar da zai'bata itace zatasa ta zama Kwarangwol kamin nan ya saketa sannan kuma ne duniya zata juyamata baya dan baka da wanda zai auri sauran mutuwa.
Kai nifa dana hango palon nan sai Naga kamar babu ko labule!koko idona ne oho.
Inaji ajikina Muzguna mata zayyi, to aiko yayi a banza wallahi dan sai yaji a jikin shi Yaseen xanta hurama cikin shege .


Gabaki daya suka sanya dariya malam yace .
A'a uwata kiyi hakuri karkimasa wannan aikin kinji,Ki barshi wallahii ki zuba ido tin duniya Allah ke sakayya yanzu.
Badai dukiyar marayaba Hmm! zai tantance hatsabibancin ta gare shi.


Hahahaha Deedee ta shiga dariya babu ko tsaitsaya wa .


Gabaki daya ido suka zaro dan tinda sukaga tana wannan kafirar dariya sunson ba karamin balai ta shiryama Adnan ba.


Ya rasulu ya manzon Allah. Dan Allah Deedee nah karkije ki tabomuna inda za'a hallakamu Kinga sai sojane.


Cak ta tsaya da dariya tace in kaga wani Abu ya faru daga Allah ne , Dan haka karka wani damu.


Adnan.


Kullum in ya fita baya sake dawowa gidan sai dare,Gidan bude yake amma ya zuba matakan tsaron da in tayi yunkurun guduwa zaisa a cafketa.


Ranar daya cika wata ukku cif yayi Shirin komawa aiki dan ya fahimci komi ya kammala dan da niyyar sa wata daya zayyi ya koma, Amma saida ya tsaya ya siyar da Asibitin Aymah da wasu filayenta kamin ya wuce...


Garin kwaki mai yawa ya ajiye mata yakai tiyya biyar da uban yaji dakakke sai manja.


Baimata sallamaba yasanya Key ya rufeta ya kama gaban shi.




Bata taba gane abinda ya shiryamata ba saida taji kwana biyu tsit din tayi yawa anan taga ko kujera dake dakin shi an ɗauketa ga Dakin yayi datti.


Tsaki tayi ta koma D'akin ta ta kwanta ƙasa tare da tada kai da jikkunan ta da sune kawai ta tsira dasu Amma ko pilo bai barmata Ba.


Yunwa taji tanaji ta tashi ta shiga kiching dan samun abinda zataci dan yanzu har ta saba da maneji .
Indomie kau har tasanya zafi ya tasomata saboda cinta da take yawanyi.
Cikin natsuwa ta fara tafasa ruwan zafi kenan gas din ya kare ya salam tace tana dawowa ta zauna palo to ta ina zata samu abunda zatai Amfani dashi.


Idonta ne ya sauka ga ledar garin Kwakin nan anan ta tashi ta buɗe tayi murmushi dan harga Allah taji daɗi, Dan sadda tana mkrt in taga an'kawoma Ƙawayenta suka Haɗashi har rokonsu take.


Manja ta diba ta kaishi ga rana tare da jefa tafarnuwa guda biyu kana ta dawo ta ɗiba ta Jiƙashi.


Ya salam tace sadda taga tana kwadashi yawunta na tsinkewa.


Sadda tagama taci ta koshi tasha ruwa kamin ta tashi tayi Alwallah ta dawo ta ɗauki Alkur'anita da yazama abokin zamanta ta fara karatu.


A haka Aymah keta rayuwa cikin kunci tin tanajin dadin abincinta na yanxu har ta dainaci dan Ta fahimci tsab ya tsanemata Ruwan jiki Sai dai shan Ruwa ,Ace Rogo ne da safe dare rana abin Yayi yawa tayi kuka har ta gode Allah ta hakura..


Jameel kau masha Allah jiki yayi sauki kullum kagan shi kwance daki yayi shuru, wani lokacin kuma yana sakin murmushi da kama pilo .
In kuma ya tino wani abun sai yaji shi cikin fargaba da Kunci.


Kwana shi Hamsin yaso komawa su Inna suka hana shi da Alkawarin sai Yayi wata biyu.


Ranar daya cika wata biyu kam da kuzari sosai yatashi yana fatan zuwa ya ganta cikim aminci.
Bayan ya gama shirin shi tsaf Deedee ta kama hannushi ta rike sosai tace.
Allah yamaka Albarka , nayi istakhara nagano muna da nasara.
Dan haka kaima kaji tsoron akkah karka cuci kowa karkuma ka keta mutuncin matar Aure ta hanyar yawaita fira da ita,in akwai rabo tsakanin ku duk wuya duk dadi zata zama taka,ka kama kanka ka iya takonka kar in'ƙara ganin wannan rawar jikin naka.




Murmushi yayi yana dan rungumeta yace ngode Kakar da babu ya ita,Nifa bance Sonta nike ba,Aa kawai ina tausayin ta ne..


Dariya tayi tace haka yake wannan karatun.
To Amma in ba so mike kawo Tausayi?.


Shuru Yayi yana ɗan sosa kai kamin ya mata Bankwana ya fito .


Gaisawa sukai da mahaifin shi dake Tsince Tattasai dan yanzu dole tasa shi kasa cefane kofar gida yana siyarwa kuma ba laifi Allah yasama abun Albarka Yana samun Na cefane,dan Basu da Matsala kayan Abinci Babu Abinda Dr nan Bai ajemasu ba.


Jameel kau bayan sunmai addu'a ya fita ya tsaya ya ɗauki wayar shi tare da kiran Alh Adnan.


A mutum ce ya ɗauka dan dama kamar jira yake.
Bayan sun'gaisa yace .
ka warke ko ?zaka iya dawowa bakin aiki dan dama inaso a duba gidan nan aga ya labarin Dabbobin dana bari.


Ido jameel ya dan zaro yana tinanin to wace Dabbba Ya aje? Kar yaje ya barshi ya shiga wajen abinda bai saba dasu ba.


No in kaje kagani karka damu yanzu turomun account number ka zan sama kudin aikin ka 50k.


Sai kuma in sama na abincin dabbobin 10k kayi manege kullum Dari biyu da Hansin zaka kashe in ka kashesu kamin wannan lokacin wallahii nidakai ne.


Tsaki Yayi yana Harara wayar kamin yace .
OGA bafa xai yiyu kanamin ihu ba karka manta jinya nayi ba sannu ba komi Sai faɗa!in baka bukatana saina tafi ka samu wani Dama ai ka kori Iyayen na ni zaman mi zanma?


Shuru yyi kamin yace ina jiran account number xan lissafama komi ya kashe wayar.


Minti biyu tsakani yaji alart.
Da kuma list din kayan abinci kamar haka.


Garin kwaki
Manja.
Barkono
Gishiri.


Dariya Jameel yayi sosai yace
mugu yanzu bayama iya sammasu abincin gidan kwara amasu Wannan Haɗin Bala'in dan shi duk tinanin shi Karnuka ne.


Bayan ya isa gidan wani mutum yayi parking da Machine kusa dashi ya buɗe gidan kamin ya Mikama Jameel din yace .
Gashi inji oga in zaka tafi wani wuri kaje dashi kaima muna biye dakai.


Cikin mamaki yace biye dani danayi mi?


Shuru mutumin yayi tare da tada Machine Yayi gaba.


Ganin ba sarki sai Allah ya buɗe gidan yashiga duk compound din yayi kura ,Gashi duk motocin Gidan Basanan.


A'Hankali yafara kalle kalle wata Zuciyar nace mai ko harda Aymah yatafi wanna karan dan baiga alamar akwai mutane agidan ba.


Karnukan ma bai gansuba ko Haushin su Baiji ba..


Aymah kau tin sadda ya bude ya shigo ta dawo bakin kofa ta bude ta fito barandarvta dan damabkofar a bude take.


Ido yajiyo jin motsin abu.
karaf kau suka hada ido.


Gabaki daya wani mugun zaro ido yayi ganin yanda tayi mugun duhu ga wata uwar rama datayi kamar ba Aymah ba dagani ba wadataccen abinci.


Hankalin shi tashe cikin sassarfa ya nufeta yace miye haka jinya kikai.


Batace komi ba ta kawar dakai.


Wata kafurar tsawa ya bugamata kamar wanda ya girmemata yace .
Ba magana nike mikiba mike damunki?...


Kuka sosai tasa dake cin ranta kamin ta fara magana cikin rawar murya


"Nagaji! Nagaji Wallahi da rayuwar nan, Ya rabbi ka ɗauki ra....




Wani uban tsalle ya daka yana matse bakin ta idon shi yayi bala'in ja cikin rawar murya yace.
Da kaddara Allah zakiyi jayayye,shin kenan bazaki gode Allah da Ni'ima dayamiki ba ta barinki da rai,Mike faruwa dake? Miyasa ba zaki godema jarabawar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login