Showing 57001 words to 60000 words out of 74994 words

Chapter 20 - MATAR OGA NA COMPLETE DOCUMENT writing by UMMY AYSHA.txt

Advertisement

08 Nov 2024

15414

zuwa.


Dariya yayi Yace'' sorry manager ne ke neman mu muje yace yana kama hannunata
Sannu sannu suka sakko idon mutanan dake palon yayi cah a kansu.


Kasa ta danyi da kanta Yayin da shikuma ya sake tamke fuska Gam, Jameel akwia dattako da kamun kai,in:kaga rawar kafarsa jikin matar shi yake.


Bayan sun sakko ya dan kallesu nan yaga su Deedee ne dasu Dr Abbah da Jannat, sai yaran su ,sai manager da wata mata da matasam samark guda ukku yam mata biyu.


Wannan ce matar Adnan din matar dake zaune tace.


Noo matar Jameel dai, a dane take matar Adnan Jameel yabata amsa idon shi kamar ya faɗo tsabar harara.


Tabɗi jan, Yanzu dama kece kika rike min miji munafuka tsawon wata ukku ba zuwa ba aike, sai Aukin karya da gaskiya da kuke shiryaman keda wannan munafukin manager, to ta Allah ba takuba abokan aikin sa sun fadaman duk munafuncin da kuka shirya dan haka yanzu kun shigo hannu shaheed ce su shigo..


Cike da rashin kunya saurayin ya tashi yana shagwaɓa da kara kwale wando kasa kasa yake faɗin wai ina Daddy nah Yake mom, kince da munzo zamu gansa kin tsaya ɓata lokacin ki akan wayan nan talakawan maciya haram.


DeeDee kam cike da masifa take lumshe idanuwan nan nata kafafunta daya akan daya ta daiki furta komi amma kai ba sai ance maka zuciyar ta tafasa take ba.


Kai dai jeka kadawo shalele matar tace.


Yana fita sai gashi da zugar sodoji sun kai mutum goma duka da bindigogi.


Aymah
Manager
Jameel
Deedee
Dr Abba
Jannat
Babu wanda fuskarshi ta bayyana wani tsoro saboda tsaro .


Ina kuka ɓoyeshi.
ɗaya daga cikin su ya fada a fusace yana ƙara bindiga akan Jameel.


Kulll wlh,Karku tabaman Miji Aymah tacw a fusace tana mikewa tsaye rai ɓace.


Kema bamu barkiba dan muna tuhumarki da rashin fadamana gaskiya da kikai saboda mugun nufi.
Kana taya zaki auri miji biyu kina mace,ko ganin wancan ya samu nakasu ne yasa kikai aure kan aure ina shi Adnan din yake.


Deedee ta dauki wayarta ta shiga lallatsawa tanayi tana kanne ido .


Sadam ne,yawwa to ku shigo da mushrikin nan,ohk tom takarasa tana kashe wayar.


Hajiya waya baki umarnin daukar waya kiyi kira bayan kina kalkashin hukuma saboda muna zarginki da zabgamana karya akan abinda kika fadama shuwagabannin mu da farko sann...


Wani wawan mari Deedee ta yankamai jikinta har rawa yake tace.
shekara 63 A duniya ba dan tsinanniyar da yaceman kaziba saikai ,nace saiki? shege da katon kirjinka kamar Allon Ƙirya,to ubankama kaje kace nace uwarsa,kai da hukuma da wanda ya kirkiro hukuma kun tile kun kwashe kan babba bura ubaku..


Sosai su AYMAH suka gilgiza da bala'in Deedee dan basu taba ganin ta cikin wannan yanayin ba ga zagi kamar wacce ta tashi tasha.


Rai ɓace yake sosa kumatin sa kamin ya dauki Bindiga yashiga nunamata tare da fadin shiga gaba.


Deedee kam a zafafe ta kwaceta ta shiga rattaɓamai ga kwalkwalinsa sai huci take,lokaci daya kuma ta cire dan kwalinta ta jefar gefe ta fara wani ihu tana kururuwa da bude hannuwa.😳


MATAR OGA NA
UMMY AYSHA
Page 28




Zanso kuga yanda hankalin kowa ya tashi a palon nan, Aymah kau kuka ta fara sosai,Jameel kau hankali tashe ya doshi Dede.
Cikin wani irin ɓari da take tare da daka mai tsawa akan karyayi kuskuran zuwa wajen ta, inba hakaba sai ta kashe kowa cikin mnt biyu.


Aguje manager ya jawoshi hankalin shi in yayi dubu a tashe.
Dr Abbah kau tsawa yashiga dakama sodojin nan cikin ɓacin rai Yace'' ga abinda kukajawo muna, kuyi takanku tin kamin tazama ajalin ku dan ba lafiyayya bace kundaiga alama.


Kunson maza da tsoron jinni cikin kurin baki daya daga cikin su Ya fara matsawa yana faɗin.
" ai'dai zamu dawo, Tinda ba haka zata dawwama ba,dole mu binciketa yakarasa yan kama hannun wanda ta kwalama Bindiga aka,.
Zanso kuga yanda kanshi yayi malolo kamar an buɗe fatar an adanamishi lemom tsami ,kusan waje goma duk ya kumbura ya tashi sai kan ya koma kamar bishiyar mangoro.


Yaran Adnan kau bayan Maman su suka lafe Jikinsu duk ɓari yake xukatan su cike da tsoro.
Ita kanta matar Adnan din shuru tayi gabanta sai bugawa yake taga wadda tafita masifa.


Mtssssa aikin banxa tsinannu haihuwar shabiyu saura kwata na rana ,yo har kun'buga dani,Sharrima in yaganni guduwa yake balle kai banxa bazara da wani tsinannan kanka kamar gidauniyar silba, zaka wulakantani ka karyatani a gaban Jikokina, bayan nason na girmi uban uwarka.


Kaiiii Yaran ɗan ta Adda. ta dakama yaran Adnan tsawa.


A gigice suke kallo ta..


Ido ta zaro masu kamar zasu faɗo tace .
Naci uban ku dukkan ku,na daka tsalle na mari uwarku,na shake uwarku tayi aman haramcin da taci,zan zabgama kowannan ku mari dari dari in baku tashi kun dawo nan kasaba,tinda kujerun bana uban ku bane, shaggu kamar yaran turwa da ganin ku babu tarbiyya,kai Dan ubanka har zakazo muna mussulmai ka zazzage wando tsagar mazaunan ka abude da shegen Ƙugi bakikirin kamar bayan tukunyar gidan gandu,to zankoyama darasi kamar yanda na koyama Wancen katon banza uban naku.


Zanso kuga yanda katon nan da akallah ya kai shekara 23 ya fara kuka yana Mama bazan karaba karki dakeni.




Duk yan palon saida dariya taso kufcemasu lallai yaron nan basu samu tarbiyya ba sun sangarce da yawa.


Manager dan Allah ka ceci ran yarana Matar Adnan tace cikin tashin hankali dan itama yanzu ta karaya Ainun.


Babu ruwana Madina tinda ke ai a ganinki Amanarki zanci,bayan munyi magana dake ta fahimta akan in Aymah ta warke zamu baki address kizo gidan nan akwai magana,amma dan ki tozartamu da uwarmu da mukejin dadin zama da ita shine kika kwaso wayan nan sukazo suka mata rashin kunya,to babu abinda zan iya,cen kuda ita...


Cikin tashin hankali ta fara rarrafawa gaban Deedee tace" dan Allah mama kiyi hkr karki tabaman lfy yarana wallahi zan sallame su yanzu,magana ta gaskiya ogan nin mijina basumason xan zonan ba,Wayan nan dai sune nasamu labarin komi a wajen su bayan nama su Alkawari kudi mai tsoka akan in sun kawoni zan basu.


Shewa Deedee ta saki tace .
To maza korasu furgada su, mnt biyar suka kara wallahi saikin sani ubanwa zasuyima barazana da bindiga,nida ubanama ke zama gabana Yana hada boma bomai( KAI HAJIYA DEEDEE 🤭)


A guje kam Madina ta ɗauki wayarta ta sata Speaker tace suje bayason aikin.
Gardama daya yaso kawomata ta faramai masifa da fadin zata tona mai asiri dole yasa ya kashe wayar suna zaune sukaji tada motar su.


Zatai magana kenan aka turo kofar aka shigo su Sadam ne dauke da Adnan da suka sakemai wanka ..


Da sauri madina ta mike tayi
Wajen shi, Yayin da yaran ma sukayo wajen shi da sauri kowa na zaro ido .


Cikin wutar kishi sosai take kallon shi kallon sama da kasa,kallon da babu tausayi balle Rahma,kallo mai cike da kiyayya da nuni da ka munafunceni..


A fusace ta faramagana.


Ba shakka,ai dayake namiji kake,maci amana,Allah na godema, Allah ya kara kassaraka ya kuma kara kwashema albarka,kullum zuciyata ƙaryatawa take akan bazaka iya hadani da kowaba kamar yanda kace, Amma gashi,jibi wacce ka rayu da ita,nikuma inacen ka barni da yara Niga wahallalla,to Wallahi azeem dukiyata kaf sai kabani abina matsiyaci,Ka manta yanda na aureka,kana cikin haki na kunci,biyar baka da ita, Adnan wane gatane ke banmaba,amma sakayya farko shine zakaman kishiya,kishiyar da bantaba ji ko labarintaba daga wajen ka,Kullum nunawa kake nice ta farko ta karshe,hmm namiji kenan..




Idonta ta mayar ga ayimah ta zubamata ido tsawon lokaci kamin cike da dogon nazaro tace kai dakata!!!.


Wannan ba itace kake ceman kayi hayar taba in zaka shiga taro tana rakaka saboda ni banajin turan ci? itace dama matar taka,lallai kacika mugun makaryaci,ina fatan kuma Allah ya ɗai-ɗaita karshen ka mugu azzalumi takarasa cikin kuka sosai.


Kuka sosai yasa yace madina karkiman haka,karki furta mugayen kalmomi akaina,Madina ke kinfi kowa sanin duk wahala da nake sabodake da yaranki,sannan wallahi babu son ta ko daya a zuciyata face ɗaukar Fansa dake cike da ruhina,madina dubi halin da nike ciki.
Maimakon ki kasanceman jagora da zata tsayaman akan a kama wayan nan mugayen Azzaluman a garkame saboda abinda sukaman,kiji yanda suka barni na dawo,jin
Bi ruwan da kafana keyi mai ɗoyi wanda ni kaina damuna suke,amma ko Chemis basu taba kai niba,ko paracitimol basu taba baniba,dan Allah ku kwatar man yancina yace cikin kuka tare da faɗin yaku nan yarana yana bude masu hannu.


A yatsine suka dinga kallon shi lokaci daya kuma suka dan fara matsawa bayan uwarsu suna noke kafada Alamar bazasu ba.


Hankali tashe yake kallon su yana fadin mikenan idona ke fadaman.


Uwakace sanye da dan buje kafara gani Deedee tace tana gilgiza kafa.


Madina kau tace.
Gaskiya yarana bazasuzo wajen ka su kwashi wannan cutar ba,sannan ai akan munafurci kayi auran baka fadaman ba to babu abinda zai sani shigema gaba,batun kuma yara karka sake cewa naka dan Wallahi wallahi bazan iya bari yarona daya ya raɓeka ba da sunan zaman jinya,Kuma takarda dole kabada,sannan gida daman ai nawa ne tinda na mahaifina ne, ko sisi na uwarka ko uban ka babu banza butulu.


Madina ki fahimceni banci amanar kiba wlh, tambayeta kuncin da nasata gatanan,Madina bantaba yarda na Bata koda Cikin tsuntsuwaba saboda banason hada iri da ita , Wallahi so biyu ma na kus...


Lafiyayyan mari Jameel ya dankaramai zuciyarshi cike da bakin cikin jin mugun kalaman da yakema matarsa.


Cikin tafasar zuciya da fitowar kwallah daga idonsa yace .
Jahili kai dama baka isa ka bata ciki ba ko ka hanata, Allah dai ya isa tsakanina da kai Adnan,kana kuntataman zuciya duk sadda ka ai'banta wahala daka ba matata,kana sani kunci,kana kasheman walwala,inajin kamar in sanya wuka in daɓama ita ga zuciya ka mutu uban kowa ya huta, Wallahi wallahi kai asararre ne jahili marar hankali.
Kuma yau yau din nan sai kabar gidan nan tinda babu ko sisin tsoho da tsohuwa.


Karka sake zagina Jamilu kajirayi fansata gareka, bazaima dadiba tinda har ka iya sanya hannu kana dukana Adnan yace cikin bacin rai.


Okh fine mu zuba nidakai shege ka fasa.




Madin kam taɓe baki tayi tace" to in kama koreshi gidan wa zaije,nidai kam nayi iya wahalata dashi bazan iyaba,Saboda na sashi inuwa ya jefani rana.


Afusace Deedee tace to ai ga yaranshi nan masu siffar rakumin gwangwani su dau kai suyi gaba Man.


Ikram ce cikin damuwa tace" mom yanzu fa akace wannan shine baban mu wallahi love bazai iya aurena ba ko waleedah.


Kuka walidah tasa tace'' wallahi Nima Nason yaseer bazai iya haɗa iri da niba ace Daddy mu ke rike da mata biyu,sannan dubar safa duk ya lalace ya zama kazami mom ya daina wanka sai wari yake, dan Allah mutashi mukoma mom banason ganin sa.


Kuka sosai Adnan yasa yana taɓa hannu da fadin" karkumin haka yarana duk abinda nike kutino domin ku nayishi,karku juyaman baya bazan iya jure rashin kuba..


Manager Yace'' taya kuka haɗu Madina.


Hawaye ta share tace Adnan macucine kuma ALLAH ina da kokonto a kansa yanzu.


"Ni dai kam haifaffar garin kaduna ce,acen natashi da iyayena mu ukku ne a wajen su,yayyena biyu maza dukkan su ba anan suke ba suna legos da matayen su kasancewar suke rike damu mahaifina ba shi da karfi sosai.
Nayi Aure na auri wani Attajirin mutum harma na haifi da namiji guda daya a wajen sa,Ban dade da haihuwar ba aka sanar dani rassuwarsa bayan anyi zaman makoki na fita iddah dole tasa nadawo gaban iyayena nida yarona Bashir da aka raba gado akabani nawa da nashi ashema ba mai tsawon rai bane
.Shekarasa biyu yayi kyanda ya koma ga mahaliccin sa.


Tsawon shekara goma 10 ban sake aure ba lokacin kuma zaman gidan ya isheni duk da ina ɗan taba kasuwancin kayan mata na atamfa lace jikkuna da sauran su.


Wata rana ina yawo cikin gari mota na ta lalace a waje mai karanci mutane.


Cikin tsoro dai na fito da in dan dudduba kamar wasa naga mutum biyu sun zagayeni fuskarsu nade da rawani,hannu suka bani akan na basu key din motar da wayoyina da kudadena.


Jikina na rawa na mikamasu key din da wayar .


Cikin tsawa sukace in cire kayana ko su zabgaman wuka.


Kuka na fara ina gamasu da Allah cikin rashin tausayi daya ya yankaman mari tare da sanya wukar hannushi ya keta riga na daka sama har kasa .


Gigitaccen ihu nasa lokacn da naga na bayyana tsirara.


Dariya suka fara ba kakkautawa kamin kuma inji sun tsaya,kaina a kasa na farajin suna bada hkr.


A gigice na dago dan ganin misuke ba hkr haka nan idona yayi gamo da matashin saurayin da ke gwara kansu,kana ganin shi kason shima dan duniyar kanshine dukda na tabbata na girme masa nesa ba kusaba , zabgegiya bindiga naga ya zaro yana fadin zai kashesu.


Hkr suka hau bashi amma Saida ya masu dukan mutuwa kamin ya ansheman komi yabani ya juya zai tafi ba tare da ko kallona yayi ba.


Bawan Allah nace jikina na bari ina kankange jikina.


Kallona yayi sama da kasa kamin yace wani abu.


Dama gdy zanma dan Allah ka taimaka ka ajeni gida karsu dawo su iskeni na fada ina mikamai key din motar




Kamar bazai an'saba kuma ya karba cikin ikon Allah ya dan jajjagula motar ta tashi muka tafi.


Har gaban iyayena ya ajeni yama su bayanin abinda ya faru suka masa gdy Sosai.


Nikam farat daya naji na natsu dashi Saboda inason jarumin Namiji a rayuwata da kaina naimasa tayin kaina bayan nabashi lbr mijina daya rasu da harkokin da nike yaceman zayyi shawara.


A takaice wannan haduwa da mukai da adnan kamar wasa ya zama gaske har yanazoman fira..


Ganin haka yasa Abbah na cemasa ya turo iyayen sa.


Anan yake fadaman shi bashi da iyaye ɗan Nijer ne wanda ke rike dashimane ya koreshi shine yazo kaduna neman aiki Har muka hadu.


Sosai muka tausaya mai babu wanda yayi dogon bincike aka sanya ranar auran mu .
gida hadadde na saya nabashi ba tare da sanin kowaba har iyayena saboda son da nike mai.


Bayan bikin ne nikuma saboda son da nikemai da Tausayi na samar mishi Form din aikin soja.


Ranar yayi farin ciki sosai ya saman albarka tare da rantsuwa da Alkur'ani akan bazai tabaman kishiyaba saboda halaccin da namasa.
Naji dadi sosai kam dan ina son sa banaso ya hadani da wata.


bayan ya cike ni nayi duk hada hadar da zanyi wadda ta zama wajibin da..
Ankai shekara goma da fara aiki sannan ya samu babban mukami yayin da nikuma nike da yara biyar maza ukku mata biyu .
wata rana yake shedaman zaije yayima mai gidan sa daya koreshi Alkhairi ya nunamai yanda duniya tahi dashi.


Naji dadi nama sa fatan nasara .
To bayan ya dawo kuma yake shedaman sun daidaita harma ya bashi wani kwangila aiki da zai kawo mahaukatan kudi amma zasuyi shekaru.


Sosai na bashi goyon baya dan ina son cigaban sa.


Cikin damuwa yake shedaman bayason yin nisa dani na kwana ɗaya balle shekaru.
Sake nunamasa nayi ba komi ko karshen wata ne yazoman .
Haka dai ya dawo katsina da wannan zama yaceman yana aiki da brek ɗinsu .
Nama murna sosai akan shima ya bani Shawara da mizai hana in'bashi dukiyata ya jefata cikin kasuwan ci ya juyaman ta hanyar shigo da motoci daga kwatano zuwa kano,Na amince naji dadi na bashi duk abinda na mallaka,yacigaba da juyawa duk wata in zaizo yana bani kudi mai tsoka hakan yasa na sake sakankancewa da bashi dukkan yarda.


Wata rana yake ceman First love anaso a dinga turani manyan wuri da zamu tafi da iyalan mu dan tattaunawa da manyan mu amma ke bakyajin turanci.


Shuru nayi gabana na bugawa,Raina ya bani ko dai Aure zayyi dan yaga gaba da baya tsufa ya tasoman haikan.


Murmushi yayi yace karki taba tinanin zan hadaki da wata saidai bansaniba ko zaki amince na dauki hayar wata mata duk in haka ya kama muje da ita.


Da sauri na amince ina sauke ajiyar zuciya .


Bayan dawowar shi yan gidan mu sukazo ganina.
Yah Hashim
Da Yah Lawal


Bayan mun gaisa suke sanar dani sun samu labarin ashe gidan da muke ciki ni nasaya to bazasu hanani kyautatama.mijinaba amma dai yazama dole in basu dukkan dukiyar da nike da ita.


Nan fa rigima ta kaule tsakanin dasu aganina dan su kuntatama mijina ne suka ɓullo tanan.
Wannan rikici dai har Adnan yaji inda ya basu hkr da cewa su bashi wata daya ya ida sayar da kayan da aka Sawo zai kawomasu da kanshi.


Nan suka tafi rai ɓace ko sallama nikam ban masu ba.
Washe gari Adnan yaman sallama alan zaije ya hado koda kudin nane ya basu dan mu.zauna lfy.


Kwana ukku da maganar nan aka sanar dani kamawar da gidan mu yyi da wuta cikin dare wacce ba ason miya assasataba,Gabaki daya iyayena da Yayyena da sukazo tacinyesu.


Fadara tashin Hankali bazai faduba.
Amma Adnan ya taka rawar gani Sosai wajen dawo da walwalata fan kiri kiri hawan jini ya nemi kayar dani Allah ya tadani har naji sauki kamin ya dawo.


A takaice dai Saida akai shekaru kamin ya koma cen da zama sai yayi watanni kuma kamin yaceman zaizo ganin kasuwancin shi na nan .


Wannan shi ne tarihin mu amma a yanzu inada shakku akan ka Adnan,ina tinanin kai ka kasheman iyaye hakane??.


Kan shi ya dago idon shi jage jage da hawaye.


Gaskiya magana Ba...


Ya isa Adnan fadamata Gaskiya da bakin ka, a wannan palon ba'a karya Manager yace fuskar shi ba walwala idonshi sunyi jawur .
MATAR OGA NA
UMMY AYSHA
Page 29




Cikin matsanancin kuka yace.
Tabbas Madina ina sonki amma nafison kudi da kowa a duniya,Kuma nayi alkawarin duk wanda zai Saɓaman akansu sainaga bayan shi,ba karya kikaiba nine nan nasa aka ma gidan ku wuta, domin danace miki na tafi babu inda naje hasalima ni nayi aikin da hannuna.
Zahirin gaskiya tinda na tashi nidai kam banyi wayon sanin dadin iyaye ba saboda mugun takaucin su,duk a titi nayi rayuwa dan ganin na samu kudi amma bansamu ba, banson kowaba sai kyarar al'umma,shiyasa ban tashi da tausayi ko wani imani ba saboda inajin zafin masu kudin da ke shagali mukuma muna masu wahala, Bala'in takaucine yasa Babana guduwa yabar mama mu data kasance makauniya.
Bata wani jin dadina dan bana mata biyayya saboda natashi da zafin zuciya takaicin haka dai yasa itama tayi lahira nikuma naci gaba da gararin rayuwata dan babu dan ginsu dake sona,A hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login