Showing 15001 words to 18000 words out of 74994 words

Chapter 6 - MATAR OGA NA COMPLETE DOCUMENT writing by UMMY AYSHA.txt

08 Nov 2024

14609

tafi farin ciki fal zuciyar sa tsuntsu daga sama gasa she


❤️ *MATAR OGA NA*❤️
*MALLAKI*


❤️ *UMMY AYSHA*❤️


*PAGE* 8️⃣


""" A bakin get suka iske Baraka da Malam Habu datama waya ta faɗama halin da suke ciki ya zo,sunyi tagumi daganin su suna cikim damuwa.


Daidai wajen su yayi parking dan ya gane Baraka.


Malam Habu ya taso da sauri yace.


Ranka ya daɗe barka dai! anyini lfy? Dan Allah ya jikin Yaro nah?.


Adnan


Bazan iya gane halin da yake ciki ba saboda bamu shiga ba, amma dai albishir ɗaya da zan'maku anan shine matata ta bayar da kaf dukiyar ta wajen yimai aiki,An fidda kudin sa sauran sun zama nawa.


Baraka da Tinda suka fara magana batace komi ba ta ɗago kai cikin matukar razana, Dan ta fahimci in'da kalaman shi suka dosa .


Arikice tace minene kace Alh?


Adnan yayi murmushi yana bude mota ya fito Aymah kau sake kwantar da kanta tayi tanajin su sama sama dan wani uban zazzabi ke kawomata farmaki, hakoran ta har datsewa suke.


Adnan kau tiryan tiryan ya masu bayani. yakuma sake da cewa kai Malam na dakatar dakai daga aiki,Haka kema,saboda dama bani ke biyan kuba, Ɗan ku kuma shi akwai aikin da zaiman da shama na mayar maku da kayan ku,Dan haka dan Allah daga yau kar wanda ya sake takoman gida ko Asibiti nah, ina fatan kun fahimce ni?




Gabaki d'ayan su saida zuciyar su ta buga ba kuma korara su da yayi bane tashin hankalin su a'a sai wannan mugun zalinci da yama Aymah na kwashemata kaf dukiya ,yanaso ta tagayyara kenan a rayuwa, in sha Allah burin shi bazai taba cika ba har abada Baraka tace a zuci.


Baraka kau inda Aymah take ta zagaya ta bude tare da kamo hannunta.


Aymah da take layi kamar tasha wiwi ta kalleta tana lumshe kumburarrun idon ta.


Miyasa kikai man haka Ummu Aymah dan Allah Baraka tace hawaye na zubomata..




Dan murmushin karfin hali ta saki idonta na neman rufewa kamin ta hada hannayenta duka biyun ta dan kalli gefen Baraka alamar ban hakuri.


Kimin magana manah Aymah. Baraka tace da ƙarfi kuka na kufcema ta.


Karr,.. ki..daa..muu yana..cikin kaddara rayuwata abinda ya faru tace a rarrabe cikin mawuyacin hali.


Baraka zata sake magana Adnan ya dakamata tsawa da fadin ta kwashe duk abinda tason natane ta fita tabashi waje .




Basai ta d'aukaba,Anan ta samai anan kuma zatabar ma kayan ka,Kana ka sani duk abinda zakai akwai Allah,kana karkayi tinanin kaci bulus ko kuma ka dauki hakkinta Allah ya barka ina,ina mai tsananin tausayama wallahii, amma Allah ya shiryaka malam Habu ya karasa yanajan hannun Baraka dake kuka sosai suka tafi...


Adnan kau da harara ya bishi kamin ya zagaya ya budemata ya kamota keyy kamar jaka ya fito da ita tare da rufe motar.


Da sauri sauri yake janta har zuwa palo ya ajeta akan kujera yayi wucewar shi d'aki.


Koda ya shiga gudar wayar shi ya dauka ya fara latsawa inda yaga kiran matar shi da yaron sa.


Bayan ya kirata suka shiga yin waya zakuyi Mamakin Yanda yake sakin kalamai da kuma sassauta murya a maganar tasu,Bayan sun aje yabi yaran ya kira yana wasa da dariya dasu kamin ya aje wayar ya fara aikin gaban shi, Bai damu da ko sallah azahar da la'asar din data kawo kai yayi ba fatan shi ya kammala hada komi kana..


Saida yaji cikin shi na ihun kuka kamin ya mike ya fito cikin masu gadin yasanya suka sawomai abinci ya dawo nan kusa da Aymah dake nishi sama sama ya zauna ya ɓararrake yaci ya koshi yabuga gyatsa kamin ya tashi ya haɗe salloli yayi, yana gamawa ya jawo Computer shi yacigaba da aiki baya ko kallom inda take dan shi yanzu amfanin ta ya kare mai tagama ci tagama sha daga dukiyar sa masu gadin sama sallamar su zayyi dan yason yanzu bata da wani amfani a Rayuwa,Dan biyar bazai bata ba balle ta nemi guduwa..


Aymah


Duk iya sonta data tashi tayi wanka ta gyara jikin ta abin ya gagara som, bata da karfin aikata ma kanta komi , inda ta gode Allah ba sallah zataiba shiyasa taita kwanciya bazaka taba gane ai'nafin abinda take ciki ba .




Jameel.


Daga sadda suka kai shi aka hana shi cin komi,zuwa la'asar ya bude idonshi dan yaji dan ƙarfin jikin shi.


"Ina take miya faru da ita ,Ya fara tambayar kanshi amma ba amsa,Hawaye suka shiga zubomai yana faɗin.


" Kiyi Hakuri duk yan da naso na tare miki lfy tamin karanci,banson wane jahilin mutum kika hadu dashi ba, banson mi kikaimai ba dayake dukan ki, Dan Allah ki gudu kibar shi zan kasance tare dake matsayin bawanka har abada, Dan Allah ki kashe Auran,ki barshi,kizo gare ni ya ƙarasa cikin ihun kuka yana neman faɗowa daga kan gado saboda fizge fizgen daya dingayi na Alluran da ake bankami cikin ƙarin ruwa.




Nursings ɗin dake wajen aguje sukaje suka Rikeshi wasu kuma suka kira Dr daya duba shi.


Dakyal ya samu yayi control din Abinda jameel din keyi ya samu ya lalla sheshi kamin ya danna mai Allura bacci yayi gaba dashi.


Bai jima da kwanciya ba Baraka da Malam Habu suka shigo dakin bisa ga jagoran wata ma'aikaciya mai share share.


Likitan dake tsaye kanshi ne ya basu waje tare da gaidasu a mutunce kamin ya musu bayanin ciwon nashi.


Amsawa sukai suna sake mai gdy da fatan nasara kamin ya fita.


Malam Habu ya buga tagumi yace.


Baraka kinga wata kaddara Allah kuma? Wai akan Jamilu ta bayar da komi nata,Baraka wannan mutumin fa azzalumine kannan mugune taya dukiyar wani zata zama naka? Dukiyar ma ta marainiya Allah.


Shuru tayi kamin ta nisa ta share hawaye tace lamarin su Hajiya na bala'in bani mamaki,Har yau nikaina bazance ga irin zaman da sukeba ,Amma inaji ajikina kamar dama auran manufa yayi da ita.akwai abinda yakeso bana tinanin yanason matar nan dan zaman da suke som babu kulawa balle ayi batun soyayya.




Shuru yayi kamin yace Allah ka warwarr muna baki daya.


Ameen Ameen tace .


Wayar shi ce ta fara Ring ya ɗauka da sallama cikin mutunci yace.
Barka da dawowa Deedee nah fatan kin dawo lfy.


Alhamdulillah


Muna asibiti yace cikin ladabi.


Ido ya dan lumshe kamin yace.


Jameelu'n ki.


Kwatance ya mata ya kashe wayar tare da cewa tofa Deedee ta dawo Baraka, Nason zatayi fada sosai mussamman in taji Abinda ya faru.


Baraka tace A'a gaskiya zamu fadamata kawai, ai uwace muna buƙatar Addu'a ta.


Kimanin 20mnt suka farajin hayaniya Malam Habu ya leko da sauri dan yana da tabbacin mahaifiyar tasa ce dan batabarin sai ta kwana.


Da sauri ya isa wajen masu gadin da suka hanata shiga sai zazzaga masu bala'i take hannuta rike da buta.


Yace Deedee nah Lfy?


Afusace tace barni da yan iska da sukayi kama da masu gadin ɗakin macizzai,yo macizzai mana sai wani juye juye suke suna kaɗa kawuna kamar jikokin an'gulu,Yo ya za'ayi suce bazan shigaba ganin jikana,Jikana a kwance ace bazanje na ganshi ba,Wai sunce ko.l wani abu na kawo Nace a'a.
sunce yanzu wanda zai shiga sai dai mai kai abinci to tinda bani da abinci na ɗakko buta masallaci in kaima jikana yayi Alwallah ya gaida mahaliccin sa akwai abinda yafi wannan Fa'ida? Amma dayake kafuraine na farko wai basu yarda ba narantse da Allah saina shiga ko duk in'fasamaku kawuna ku kwanta jinya asamu masu hana har iyayen ku zuwa munafukai Yo daɗi ke kawo bawa Asibiti ta karasa tana ɗakko katon dutsi da gayya ta jefoshi gefem mai gadi daya aguje kau ya Ruga yana rike kanshi.


Ta sake ɗakkowa zata jefo shima dayan ya ruga ta sanya hannu ta turo kofar tana murmushi tare da cema zugar dake bayanta ku shishigo kuga dangin ku kunji ko sai nima kuma jikana addu'a.Ai nayi aikin Allah na sadaku da yan uwanku marasa Lfy nason zan'samu Lada.


Aiko kamar jira suke mata da maza haka sukaita turawa kowa yashiga kamin ta karasa wajen Malam Habu daya rike kanshi yana murmushi da kallon ikon Allah.


Tace kai kuma miye ko jikin jamalun ɗin ne yasaka murmushi in ce ya warke..




Murmushi Yayi yace.


Ina kallon jarumar uwata datafi ta kowan.Jameel ɗin ki da sauki,Fatana dai Allah ya kara miki lfy Deedee tah.


Ameen tace tana Ganin masu gadin da ransu ke ɓace suna surfamata harara.


Dan murmushi tayi tace .
Kuyi hakurin Dan uwayen ku kunji ko,Kunson rikicin tsufa! eh nace kunson rikicin Tsufa, Dan Allah kuzo ku garkame get din kar akawomuna farmaki tinda na shiga kuci gaba da aikin ku ta karasa tana wucewa Malam Habu biye da ita yana Murmushi.




Tunda ta shigo dakin ake Nunata ana cewa itace tasa aka shigo .
Nan fa akaita gaida Deedee tana hura hanci da amsawa cikin isa kamin ta farabin mutane tanamasu sannu har suka shiga ɗakin da Jameel yake..


Ganin yanda yake yasata fashewa da kuka tace shikenan jamalun Deedee,Abu yakai ka kass,gashi an'ki sayen gonar wallahi yanda naje abanza haka na dawo a wofi.
Kowa na korafin yanda aka matsama gonar nan da sace sacen mutane shiyasa kowa gani yake jalli joga zai saima kanshi.


Baraka tamata bayanin an'biya kudin aiki.


Haɓa ta rike tace wannan wane dan aljanna ne ya biyasu ?


Nan fa Baraka ta karkace tana kuka tana fadamata abinda ta sani game da Aymah.




Koda ta gama Gabaki daya saitaga Deedee tayi shuru tsawon dogon lokaci kamin tace inane gidan nasu?


Nan baraka ta bata.kwatancen wajen.


Deedee tace karki damu Allah na tare da ita, kuma nima zanje har inda take in'sha Allah, Allah yasanya wannan taimakon datamana yazams silar warwarewar damuwar ta,Kukuma Allah ya maku zaɓin Alkhairi.


Ameen suka amsa Baraka ta tashi tayi gida dan samo masu abinda zasuci duk da babu kudi sosai hannunta ta riga tayi sayayya kayan abinci .


Ana gama sallah mangariba tayi Asibitin inda ta iske jameel ya tashi amma ko zama baya iyayi sai gadon da aka ɗan dago masa.


Kallonta yayi ta kalle shi tare da mai ya jiki.


A'Hankali ya amaa yace "tana ina?


Gabaki ɗaya suka kalle shi Deedee tace'' wa?


Ita
Yace yana cije baki.


Deedee tace'' Subhanallahi har anzo nan wajajen jamalu,Yaushe aljana ta aure ka da kake jajenta bamu saniba ?kodai zafin ciwo ne ?.


Kallon ta yayi yana cije baki kamin ya dan harareta ya kawar da kanshi yana lumshe ido ,gaba ki daya tinaninta ya addabi zuciyar sa,wannan ciwon ya mugun kwafsamai ,Bayan shi wallahi azeem da sai ya gwadama Alh Adnan sabon jini ke yawo a jikin shi dan sai yamai mugun dukan da bazai iya numfashi ba.
Amma ko gobe ya ɗauki Alkawari sai ya rama mata dan ko ta yafe shi bazai yafe ba.




Hajiya Aymah kake tambaya ne Inna su tamai magana tana zubamai ido.


Da sauri ya dagamata kai yana zubamata ido.


Tana.nan Lfy bata jima da tfy ba.


Kai k awai ya d'aga yana furta Alhamdulillah a ranshi.


Fira suka danyi banda shi daya lumshe ido.


sai karfe tara Deedee da Inna su suka tafi aka barshi da.mahaifin sa kawai.


Aymah.


Zata iya cewa tinda take bata taba ganin mugun mutum ba kamar Adnan, Dan duk halin da take ciki ko alama bai tankamata ba, har aka yi Sallah mangariba akayi isha yana zaune sai wajen tara ya mike yayo Alwallah ya hadesu kamar yanda ya tashi ya sanya key a palon ya dawo ya kwanta .


Aymah Ma a haka bacci ya tafiya da ita sai wajen karfe ukku ta falka Tare da yun kurawa ta tashi cikin ikon Allah taji daɗin jikinta sosai.


Wanka tayi da ruwan zafi sosai ta gasa fuskar ta kamin ta dawo bisa gado ta kwanta ta lumshe ido tana tunanin juyin rayuwa.


Washe gari


Jameel


Karfe Shidda aka shiga dashi theater room sai mumafasa fatan fitowa Lfy.




Aymah kau wata fitinanniyar yunwa ce ta tayar da ita .
Dakyal tayi wanka ta sake gasa jikin ta ta dan fito palo dan samar wa cikinta abinda zataci.


A'Hankali take tafiya har ta iso palo.


Ido da ido suka hada ya kawar da kanshi gefe yana amsa waya da sake tsuke fuska..


Ina kwana tace cikin sanyi.


Baiko am'saba ya juya kai.


Bayan tashiga kiching din ta hada tea na ruwan sanyi dan bazata iya dafawaba tasha abinta.


Tana cikin wanke cup din ne taji shigowar katuwar motar tanka har inda daga shi sai ita ke shigowa .


Glass ta dan zuge taga katti na fitowa daga ciki ,su dukan su da shigar banza.


Gabaki daya suka Dumfaro palon.


Hakan yasata watsar da cup din ta fito da sauri daidai lokacin da suka banko Kofar suka shigo...




Hajiyoyin kamshi akwaifa UMSAD INCENSE na nan tana muki sabon shirin turarukn ta msu kyau da dadi kun san komi basai na fada.ba
.❤️ *MATAR OGA NA* ❤️
*MALLAKI*
*UMMY AYSH*
*PAGE* 9️⃣




* Sosai jikin ta ya ɗauki ɓari ganin duk jikin su a murɗe.


Adnan ya ɗago ido yana kallon su kamin ya mayar akan wayar shi yace" kun kyauta da kukazo kan lokaci ku fara dana sama tass kamin ku sakko nan ko ku rabasu biyu.


Da" to" suka amsa wasu suka haura dakin shi wasu sukayi nata duka biyun suka fara kwance kayan'ta suna sakkowa dasu.


Daga lokacin data fahimci ya san su sai hankalinta ya kwanta ta ɗauki Hijjob ta sanya tare da lafewa gefe tana kallon yanda Saketa kwashe mata kayan daki .


Saida suka cika motar gam kana sauran suka fitar dasu waje suka fara zuwa kai wasu su dawo.


Tana nan zaune shima yana saman kujera suka gama kwashewa tass suka zo zasu fara kwashe kayan palon.


Tass nan ma suka kwashe har labule basu bari ba .


Ido suka haɗa da Adnan ya saki murmushi ita dai batace komi ba.


Duka saida suka gama suka tafi bayan ya sallame su.


Lokaci ɗaya komi na gidan ya dawo wani iri kamar kango.


Masu gadin yama waya yace suzo.


Bayan sunzo nan yace ya dakatar dasu su koma Bariki zasuyi waya.


Gabaki ɗayan su Amsawa sukai suka tafi suka kwashe kayan su sukai tafiyan su ya rage dagashi sai ita.




Dan kallon ta yayi yana wani lumshe ido da sakin murmushi yace.
*Aymah Abdulkarim Mai Dala*.


Tom yau ina Abdul kareem din ina kuma kudin ina uwar ina uban ina kuma izzar mahaifin naki? ina dukiyar daya wulakantani kanta yakimin alfarma Ya barta yana taramiki?
Tom yau gashi an wayi gari bana tinanin abun biyar kina dashi a gidan nan.


Ko akwai?


Kai Kawai ta d'agamai tana sake bude idonta akan shi.


Murmushi yayi yace.
gabaki d'aya na canzamiki tsarin gidan nan da kuma rayuwar ki,Inaso kiji yanda naji,Kana ki ƙare a haka har abada,Ke ba mai Aure ba ke ba zawara ba.
Aymah zan baki umarni kai tsaye wallahi wallahi kika tsallake saina kasheki.


Ido ta zaro da karfi tana kallon shi.


Yess zan kashe ki kamar kiyashi ba ubanda ya sani,Ba kowa gidan nan dagani sai ke.
In kuma kikayi yunkurun guduwa ..Hmm ya fada yana murmushi da faɗin aka kamoman ke wallhi saikin sani domin nasamaki matakan tsaron da bazaki taɓa ganin suba sai sai su Su ganki..


Kana wannan yaron shine kawai zai dinga zama gidan nan shima Akwai dabbobon da zan aje wanda shine ya cancanta ya kula da su dake da abincin da zakici ,Dan daga sadda zai samu sauki Ya dawo bakin Aiki kin gama girki sai sai A siyomiko na bakin Hanya da yaran talakawa keci..


Murmushi tayi tace.
Adnan bazan gudu ba,ko baka aje kowa ba bazan gudu ba,Saboda nason daraja Alkawari karka manta alkawari nayi,Mudddum bakai ka koreni ba bazan bar gidan kaba,So wajen wama zani in nabar Nan.


Yace Kimma kanki taimako ya ƙarasa yana mikewa ya shiga dakin shi da ba ko gdo sai doguwar kujera. wanka yayi ya shirya ya zauna ya fara nazari rayuwar shi ta baya da Mahaifin Aymah da duk Duniya Yafi kowa tsanar shi,Dole ya fanshe bakin cikin sa akan Yarsa.


**
Alhamdulillah Jameel anyi aiki cikin nasara sai fatan Allah yasa karshen wahala kenan.


Deedee tayi murna tayi kukan farin ciki lokacin da akacemata aiki yayi kyau Masha Allah.


,**


A'Hankali sauyin rayuwa ya fara kawoma Aymah farmaki inda ta koma kamar wacce ta samu matsala kwalwa gabaki daya ta daina magana.
To dawama zatai. Saita kwana batace komi ba,Iyaka zakaga tana sallah tana addu'a sosai,Adnan baya gabanta dan loi kayan kamshin data saya gabaki daya ta mayar da abinta jikka ta ajiye dan tagama tusa kanta inda ba kwarjini ,Duk abinda zata faranta mai yanzu bata son sa.
Adnan ya mata abinda ko shine autan maza dole ta barshi yanda yake da manufa wulakanci akanta ,bazatace ga abinda tamai ba Hakama iyayen ta.
Amma ta son ya fito yanzu ya gwadamata kiyayya zahiri kana kamar yanda tayi alkawari muddum baibata takaddaba bazataje ko ina ba daj bazata fita da dakon igiyar sa dake kanta ba.


Gabaki ɗaya ya fiddamata kaunar Namiji cikin rayuwarta saboda tana ganin kamar duk wanda zata samu abinda yamata shima haka zai mata.


Adane take da burin ta fita gidan shi ta sake aure amma ayanzu kam som Babu wannan tunanin cikin ranta.


Jameel.


Tinda akai mai aikin nan ya susuce ya dawo so silent,Kullum tinaninta yake abin har tsoro yake bashi ,kullum zuba ido yake yaga ko zatazo kamar yanda Maman shi tace amma ina har ya fidda rai gashi har an'kwana biyar .
Kullum nazari yake akata,da Tinanin mitake? wani lokacin ma zuciyar sa takan bashi amsa da kilan tanacen ana dukan ta ,In kau ya tino haka burkicewa yake yace sai ya tashi ya koma gida ya warke.
sai sunyi da gaske yake komawa ya kwanta yana huci.


Yauma data kama sati daya damai aiki kuma yau ake shirin sallamar shi.
Kwance yake akam gado daga shi sai gajeron wando da farar vest.
Fatar nan tashi tayi lumi tayi kyau na maji yaci.
Hancinshi ya kara wani tsawo hakama pink lips dinshi sunyi yarrr dasu alamar jinya yake.


Kanshi a sama ya zubama silin ido.
Bai an'kareba ya farajin saukar hawaye .


DeeDee dake kusa dashi ta fasa kuka tace.
" Kai jama'a jamalu nah ka daina kuka ko baka warke ba?.


A'hankali ya karkato da kan shi akanta zuciyar sa na zugi da bala'in zafi yace "Deedee nah inaso na ganta wallahi,inajin zafi,inaso nasata idona, Deedee minai mata da bata sake waiwayana ba, DeeDee ko fushi tayi tana ganin da gangan na barsa yana dukan ta Bankwace taba?Ki faɗamata zan rama mata wallahi azeem zan rama mata Deedee nah. Dan Allah kice tazo yanzu ya ƙarasa hawaye sosai na ambaliya akan kyakyawar fuskar shi.


Deedee ta sake kallon gefe da gefe dan kara tabbatar ma da ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login