Showing 42001 words to 45000 words out of 74994 words

Chapter 15 - MATAR OGA NA COMPLETE DOCUMENT writing by UMMY AYSHA.txt

Advertisement

08 Nov 2024

15427

suka ɗauki hanya suna isa motar manager na tsayawa .
Gabaki daya suka fito motar shida Jameel inda manager kuma ya bude motar shi shima ya fito idonshi cikin na Jameel.


Wani mugun tsuma jikin Jameel ya fara dan rass ya gane shi.
Ranshi ɓace yake nuna shi da hannu yace" ubanmi kazo yimata anan? Ko ina dukiyar matata take munafuki yayi kanshi gadan gadan.


Dakyal Babb Ali ya iya buɗe gaban motar ya fito Yana daga sandarshi yace" Kayi hakuri yaro komi zai tafi daidia wannan ba macuci bane kamar yanda kayi zato kaji...


Cak Jameel ya tsaya yayin da manager da jikinshi ya dauki rawa yace "Wallahi babu niyyar cutar Aymah a Rayuwata, gatanan ka tambayeta ya faɗa yana bude bayan motar.
Nan ta bayyana kwance tana sauke numfashi kadan kadan da alama Athma ta ce ta tashi dan sai haki take.


Cikin wata tafiya ta mazajen zakuna Jameel din yayi bayan motar inda yaganta cikin wannan hali.


Ya subhanallahi, faɗar tashin hankali da yaron nan yashiga a dai-dai wannan lokacin ɓata lokaci ne...


Domin kuwa idon shi ganemai yaadingayi kamar bata numfashi.


Wani irin ihun kuka yasa yayi kanta gadan-gadan ya cakumota yana fadin.
Aymah dan girma Allah da manzon sa kitashi ki faɗaman misu kai maki,karkiman haka kar ki tozartani, karki yaudari zuciyar data ɗauka so da amana ta baki , Allah ne gatana sai iyayena ayanzu bani da gatan kowa sai naki, Wallahi rasaki a rayuwata tamkar rasa rainane, karkiman haka kibamu dama mu mallaki juna mu haifi yara inma tafiyarce sai mutafi dan Allah, kibari murayu a kalkashin inuwar aure, Aymah nah dan Allah yafada jikin shi ko ina na rawa zufa na ketomai hawaye kam kamar an bude pampo..


Dr Abbah ne yaja shi yace.
ka dubafa tana numfashi Jameel bafa mutuwa tayi ba ,a halin yanzu ma taimako take nema jibi yanda numfashinta ke barazana barin jikinta ko dai tana da Athma ne?.


Baba Ali yace.
Tabbas tana da ita dan ba shakka ta gadeta ne wajen mahaifin ta, ba abin mamaki bane ace itama bazata rasata ba.


Kagani ko maza dakkota muje Asibiti Jameel kukuma kushiga ciki Deedee na nan yace da manager.


Baba Ali yace.
A'a bazamu shigaba zamubiku munason sanin halin da take ciki..


Jameel kau tinda yaji tana da rai bai sake bin takan kowa ba ,aguje ya saɓeta kamar baby sukayi cikin mota Dr Abbah ya rifamasu baya. Kai tsaye FMC suka nufa Emergency ganin su da Babban Dr babu wanda ya tsaya neman katin su.


Likitoci ukku ne akanta dan ƙoƙarin ceto numfashinta, Yayin da Jameel kuma keta safa da marwa yana Addu'a,, Gefe kuma tinanin miyatasomata da wannan ciwon yake , kana miye alakar ta da wannan manager Abokin mijinta nefa maci amana ,abu na karshe waye Wannan Dattijon, kana ina sukaje haka sukadai da wannan ranar?..


Dr Abbah ne ya dafashi yana goge zufar fuskar sa yace.
Gaskiya akwai matsala Jameel,Banson wace irin damuwa Aymah tashiga ba wacce ta fara neman taɓa lafiyar zuciyar ta,A yanzu haka maganar da nikema ba Athma da muke tinani bace ta tashi kumburine zuciyarta yayi abin babu dadin ji.
Mafita daya shine ayi gaggawa yimata aiki..


Ya Salam.
Jameel yace.


Ya rabbi ka rabamu da shiga tsaka mai wuya yace yana dararashewa kasa.


Yau garana dukiya,da yana da ita babu wata fargaba da zayyi ,koda kai zasuce zasu fita wata kasa amma ahalin yanzu ko maradi akace yaje bashi da wannan halin.


Manager da suke jinshi ya taso yakara neman bayani Dr Abba ya masa yace babu Damuwa A fara shiri kawai.


Dr Abbah yace. Tom Babu damuwa,Sana gaskiya inaga Deedee bazata iya da wannan jinyar ba dan abune mai wahala.


Jameel dai shuru yayi yana binsu da ido dan bashi da ta cewa.


Manager ya kalli Jameel ya kalli Dr Abbah ya dan ja hannusa zuwa gefe nan suka shiga tattaunawa na wani lokaci kamim su dawo inda yake yayi tagumi zufa sai ketomai take.


Jameel in sha Allah yanzu da an'fito Sallah azahar zamu daura maku aure kaida Aymah ,Kana Aikin ta gobe da asuba ne Allah ya bata lfy zamuje wajen Baban ka yanzu.


Ido kawai Jameel ya zubamai dan bashi da abin fada a daidai wannan lokacin.
Ganin halin dayake ciki yasa Dr Abbah kamashi suka zauna akan kujera ya hau lallashin sa da nusar dashi mahimmancin aikin da za'amata , ba wani abu bane mai wahala, ai an maka kagani ko?


Kai kawai ya shiga ɗagamai, Tare da mikewa yaje inda window wajen yake yayi tsaye amma baya ganin ta.


Ganin haka Dr Abbah ya kama shi suka shiga Ciki inda take kwance tayi wani kyau tayi fresh gashinta duk a balbaje ga na'urar shakar iska makale a hancinta.


Gefen da take ya matsa yayi shuru, inama ace tana zaune da kafarta akamai albishir din wanna auran da kullum yake fata.


Dr Abba kau Hannu shi yaja suka fito tare da neman excuse suka sake hawa motoci sukayi gidan Deedee inda suka isketa zaune ta buga tagumi ga Uban zobo data gama hadawa amma batasa fridge ba.


Suna shiga ta taso tana binsu da kallo da leka bayansu ta kece da kuka tace" Dan Allah ku nemoman yar marainiyata wallahi tin safe ta fita banson inda ta tafi ba...


*Babu editing bana da charge*


❤️MATAR OGA NA ❤️
MALLAKI
UMMY AYSHA


PAID BOOK NE .
Page 20




""Dr Abba yace .
kwantar da Hankalin ki Deedee Aymah na tare damu , Yanzu haka akan maganarta muka zo miki..


Zama tayi tana zubamasu ido ta kasa cewa komi.


Cikin natsuwa ya shiga koramata bayanin ciwon Aymah da aikin da suke so amata.


Ya salam ! Deedee kamar ta shiɗe tsabar masifar kuka..
Dakyal tayi shiru tashiga kwararo Addu'a neman dace wa Aymah akan aikin da za'amata.
Suna cikin magana ne sukaji sallama baƙin kofa.
Dr Abba ne kawai ya fita yaga iyayen Jameel ne da kuma Baba Ali sai manager.


Sannu da zuwa Deedee ta masu tana sake matsamasu da carpet gefenta.
Yayin da Inna su Jameel kuma ta dawo kusa da ita ta zauna.


Bayan an gagggaisa nan ta kalli su manager tana fadin" ban wayeku ba?.


Bayan sun gaisa nan ya fara bata labarin rayuwar da sukai da Adnan, da Baba Ali, kamin ya kara da cewa .. Mama wallahi nayi nadama mafarin kenan sadda Adnan yajeman da batun son sa Aymah ta rattaɓa hannu akan takardun kaddarata na bata wasu takaddun na bogi dayake ba Allah a ransa som baima gane ba.
Ita kanta saida ta kalle ni a lokacin tsawa na dakamata akan ta sanya.
Alakata da Aymah ta farane sadda Adnan ya kwanta wannan jinyar, a binciken da take a wayar sa ne take gano wasu abubun dayake nufatar ta dasu da irin magana da yakeman nason yanda ya tsara kassara dukiyar ta ina kara ɗora shi akan hanyar da yakeso.
Anan ita kumaa ta ɗauki number nah taman magana akan son sanin manufar da Nike da ita akanta,Taya zan bama mijinta shawarar akanta sannan kuma naki yarda na bata Original ɗin takaddun kaddarata yah haka miye nufina akanta? .


Saida na gamsu da itace. Nan na koramata bayani asace da son taman Alkawari babu wanda zaiji har sai a fara bincike akan wasu abubuwan da har yanzu bamu gane ba..
.
To Wannan dalilin ne yasa nayi tsayuwar daka wajen gano wasu ɓoyayyin sirrikan nashi har muka gano video da yasanya akaje akamasa lokacin da mota kebin takan iyayen Aymah.


Dukkan su saida suka share hawaye Jameel kau bakin shi karkarwa yake sosai.
Kai dole Aymah tayi jinya masifar nan ta isa ace mijinka, Wanda kuke kwana tare ku tashi, shike da manufar sharri akan ka Da iyayen ka .


Baba Ali ya numfasa yace" Adnan Akwai Hakkin al'umma sosai akansa ,sai dai fatan in mai shiryuwane Allah ya shirya shi.


"Ba Ameen ba Dattijo... Deedee tace a fusace tana fadin "kai dole matsiyacin nan yaji hukuncin duniya kamin na lahira.


Murmushi Baba Ali yayi yace "A'a Hajiya ya daifi abar shi da mahaliccinsa,Kamar yanda yayi ba tare da sanin kowaba haka ya kamata abar shi ya koma wajen mai sama zaima kowa sakayya dai dai da hakkin sa...


Malam Habu yace" haka ne Deedee dan Allah kiyi hakuri.


Kwafa kawai tayi amma ranta ya ɓaci..
Manager yace .
Yanzu Deedee wannan jinyar ta Aymah akwai bukatar adinga kulawa da ita, kana dukkan mu babu wani makusancin daya dace ace an'barta dashi,shine muka yanke hukunci hada auran su da Jamilu tinda ya tabbatar ma Dr Abba da amincewarta a daran jiya.


Kuzo kuga washe baki kamar ba ita ke kuka ba.
Hannu ta taɓaa tace.
Shikenan na amince Allah subhanahu wa ta'ala ya tabbatar da Alkhairi.
Nan ta tashi tashiga daki sai gata da kudi ta aje gaban Malam Habu tace'' Abada sadakin Jameel, da wannan 50k din Allah ya tabbatar muna da Alkhairi.


Godiya sosai suka shiga yimata nan suka mike da niyyar zuwa suyi shiri su wuce Sallah Juma'a daganan za'a daura auran kamin su dawo dan akwai bukatar zama da Adnan.


Fatan Alkhairi tama su suka fita suna tafiya manager ya bayar aka kawo kaji da cefane da kananun kayan abinci akan Ayi girki dan rabama Muta ne .


Nan da DeeDee da Inna su Jameel dake ta murmushi jin daɗi da Almajiran Deedee aka zage suka shiga aiki bakama hannun yaro, wannan zoɓon datayi dama batayi kunun Ayaba aka saka a fridge aka hau bashi wuta.


Dr Abba kau waya yayi ya shedama su Yaya nura Auran gaggawa daya taso ma Jameel,.


Ya shedami zuwan su in sha Allah cikin lokaci..


Daganan yaja shi suka tafi wani katafaran shago ya sawo mai wata farar shadda mai masifar kyau mai tsada da hula da takalma da agwogo ya biya wajen masu aski aka gyarama Jameel din fuska..


Duk da fuska tashi ba walwala amma zanso kuga yanda baiwar kyau ta bayyana ga bawan Allah nan.


Kai tsaye gidan Dr Abba sukaje anan dakin saukar da baki yabama Jameel din umarnin ya shirya shima bari yashiga ciki ya kimtsa..


Ba kuzari amma haka ya shiga ya watsa ruwa ya haɗi da Alwallah ya fito, mai kawai ya ɗan murza yayi zaune ya zubama mirro ido..


Shifa ba Auran ne ya dameshi ba , Ya ga ta tashi zaune da mazaunan ta shine fatan shi,zuciyar shi namai sakar abubuwa marasa daɗi dakesa gaban shi
Bugawa.


Guntun hawayen daya zubo mai ya ɗauke A'hankali yace.
" My wife zakiyi farin ciki da ni in sha Allah,da yardar Allah sai na gusar da dukkan damuwar ki,na maye miki gurbin bakin cikin da kika tsinci kanki da farin ciki,Nayi Alkawari da sanina bazan taɓa saɓamaki ba,Zan bada farin cikina domin naki,banason komi naki kawai ke nikeso,farin cikin da kika rasa daga yau zaki fara samun sa in sha Allah,I love you so much Sweetheart.


Dr Abba ne ya Turo kofar ya shigo cikin wata dakekiyar shadda Milk sai zuba kamshi yake...
Turus yaja ya tsaya ganin Jameel nata sambatu.


Kai ya gilgiza cike da tausayinsa kamin ya matsa wajen shi ya hau lallashi da nusar dashi mahimmancin ɗaukar ƙaddarata aduk sadda tazoma.


Sosai kam hakan yayi tasiri a zuciyar Jameel din ba kadan ba ya samu saukin raɗaɗin da yakeji nan ya tashi ya shirya shape shape.


Ya subhanallahi.
Wallahi ba kadyan ba kayan nan suka karɓi fatar shi, sun mai mahaukacin kyau ga wani fresh da yayi ,ya fito Angon sa sak.


Turare Dr Abba ya dauka ya shiga fesamai ko ina kamin ya gama suka fito suka shiga Sabuwar motar Dr suka dauki hanya Yana ta sake ƙoda kyan da Jameel ɗin yayi...




"Hmm Wai yau zan mallaki Aymah matsayin mata yace yana lumshe ido.


Murmushi kawai Dr Yayi yace.
Al'amarin Allah ai ba abun wasa bane, kana kaima ayanzu zakai amfani da damarka ta fannin ƙaryata tinani da take na ganin ka yaro ,Ka nunamata Yaron ma namiji ne...


Akaro na farko ya saki murmushi yana dan cije lips ɗinsa da taune na k'asan da karfi ya daga gira guda sama yana ɗan turo halshe kamar zayyi fito.


Dr Abbah ya juyo karaf suka hada ido gabaki daya kuma suka sanya dariya .


Hmm wallahi kardai ka manta ni likita ne, babu abinda bazan karantaba daga fuskar ka Yaro, A dayyi A'Hankali, Dan kayi jinya muka baka badan kashe ƙishin kaba tsohon tazuru.


Ido Jameel ya zaro kamin kuma ya jawo haɓar rigarsa ya lulluɓe fuskar shi ganin ya gano manufar sa.


Dariya sosai Dr yayi a haka suka shiga Masallacin dake cike da al'umma dan dama babban masllacine gashi kuma ranar ta kama Juma'a.


Bayan gama gabatar da huɗu ba aka hau sallah, ana idarwa su manager dama sun sanar da Ɗaurin auran, nan limamin ya tsayar da mutane .
Bayan an daura Auran akan sadaki mafi ƙanƙanta dan samun Albarka aure.
Nan manager ya zage ya dinga ɓarin kuɗi da Su Sweet ,goro, da dai sauran su.


Fatan Alkhairi sosai aka shiga yima su Jameel wasuma duk baison suba yaƙe kawai yake masu.
Yah Nura ne da zugar yan uwa da abokan su suka zo suka tsokane shi tare da tayashi murna, daganan suka hau motocin su suka dauki hanya gidan Aymah.


Ido nazaro ganin yanda aka kawata harabar gidan da wasu manyan runfuna da kujeru ko wanne ɗauke da table da mutum hudu zai iya zama akai.
Ga abinci nan mai rai da lfy kai kace an shiryama bikin dama.


Cikin gidan na fada nan idona yayi tozali da Hajiya Deedee cikin wani mahaukacin farin lace mai tsada,sai sheki take ta zuba murjanan ta.
Ga wani coge data buka illahirin farin gashi ta na fulanin usuli ya sakko mata.
Kamshi kau kai kace Daga Dubai tazo..


Lokacin da motocin suka tsaitsaya nan fa mutane Harda yan gulma aka hau shigowa ciki dan samu a cika teɓa da abinci da kuma gulma, dan sun tabbata mai gidan ce zatai aure kuma anson mijin na nan to amma miye dalili? Amsar nan kowa so yake ya same ta.


Jameel ne hannushi cikin na Dr suka shiga har katon palon da aka kawata da babban carpet.
Bakowa ciki sai Deedee da kawarta Hajiya murja Dan batayi gayyaba..
Tana ganin shi ta hau guɗa sosai tana farin ciki da jero addu'a zaman lfy Ana amsawa da Ameen. Daga karshe suka shiga photina dan tarihi.


Akunan ta yace Ina Inna mu bazata shigo ba?


Cikin raɗa tace kai ta tafi kunya takeji.


Murmushi kawai yamata yana kauda kai.




Sai da aka gama tashiga daki ta dakko powder da kwalli ta aje gaban ta kamin ta nebo ruwa a yar madaidaiciyar roba ta gyara zamanta kamin ta kece da kuka.


Attention din mutanan wajen duka ya dawo kanta .
Saida tayi dan kanta ta gaji kamin ta wanke fuska da wannan ruwan ta dauki powder da kwallin ta shafa ,kamun ta dago tana murmushi tace ah toh ubanwa zaice nayi kuka?


Gabaki daya kau suka fashe da dariya dan da yawansu sunyi tinanin wani abu akai mata.


Jameel ne kawai da Dr da sukason hali basu damuba.


Kai ta gilgiza tace" Kukan farin cikine, Fatana Allah ya tadoman da Amanata lfy.
Kunson Allah banajin dadi duk da abin farin ciki ya samemu amma abun baiba da cittaba akan ace idonta Bude cikin koshin lfy.


Dr yace in sha Allah komi zai tafi yanda akeso kumata Addu'a.


Nan suka tashi suka fita suka ci suka sha masu tafiya suka fara tafiya, sai bayan la'asar kowa ya watse kamin Suka haɗa motoci dan zuwa dubo Aymah.


Lokacin da suka shiga da bibiyu suka shiga suka ganta har lokacin bacci take cikim natsuwa ba wani fargaba.


Dr Abbah ne yayi murmushi yace Alhamdulillah haka muke so ta samu relief zamu iya tafiya gidan Deedee dan gabatar da abinda ke gaban mu kamin ta tashi.
Ina Baba Ali?.


Manager dake cikin shirin Babba riga yasha uban kyau yace .
Yana cen bamuzo dashi ba, shima saida nasa aka dan karamasa ruwa baima samu halarta daurin auran ba ,amma na tabbata zuwa yanzu ya dan dawo daidai zamu iya iske shi gida..


Fatan samun lfy suka mai suka dauki hanya .


Abakin dakin da Baba Ali yake sukai sallama suka shiga, lokacin Sadam nata bashi abinci yana jeramai sannu cikin tausayi da jin kai.


Koda suka shiga idon shi ya dago ya bisu da ido kamun ya danyi murmushi yace .
Masha Allah. Alhamdulillah, wannan ganin dana maku ya tabbatar mun da kun bada auran Amamatu nah wajen mutumin kirki, Allah ya hada kawunan su ya kawar da fitina ,Allah kasa karshen wahalar baiwar Allah nan ne yazo.


Kowa da Ameen ya amsa kamin suka shiga mai sannu da tambayar abinda yake bukata ?
Yace Babu komi gatan da akai mai ma da lfyr sa baya da tace wa.


"Baba zaka iya tashi muje dakin wancen Yaron ko ko? Cewar manager.


Ɗan shuru yayi kamin yace "tom yaro nah,ba matsala muje ya yunkura da hannusa daya zai tashi da sauri Sadam dake hawayen tausayin dattijon ya kamashi ya rike suka fito su duka harda DeeDee sukayi dakin Adnan.




A kwance suka iskeshi yana kallon sama da alama wani abu yake tinani.


Baba ne yabishi da Kallo na tsoro da kuma fargaba gami da tausayi, kamin cikin rawar murya yace" Black Driver Haka rayuwa tayi dakai dama?.


Ya salam.


Zanso kuga irin zaburar da Adnan yayi ya na mayar da ganin shi kansu, ido ya zubamasu.


.
Murmushi Baba yayi mai ciwo tare da bude hannun shi dake cure yace" in d@i har ka manta da wannan fuskar wanna hannun daka Yar a ƙasa bana tinanin ka manta, sai dai in dama ba shine na farkon wanda ka fara yankewaba ya karasa cikin kuka mai cin rai kamar sannan abun ya faru.


Cikin Wani tashin hankali mabayyani Adnan yace..


Ali Mai Gadi dama kaine..
Deedee
Sadan
Dr abba
Bash.
Jameel.
Manager


Duka ido suka zaro jin yayi magana babu ko alamar karaya halshe.


Wani irin gilgiza ya fara na son muke wa zaune yana faɗin.


"Wallahi saina kashe ka koda hakan zaizama sanadin Rayuwata......


*Aman uzuri gobe biki gareni na Sst nah*..


❤️MATAR OGA NA ❤️
PAGE 21
Paid book


...Dukkan su da kallon mamaki suka bishi.
lamarin nashi ya daina basu mamaki sai dai tsoro,Ace kai arayuwar ka som Babu nadama bale ka fara tuba wa mahaliccin ka.


Kukan kuran da Yayi ne da niyyar tashi a fusace Jameel ya sanya tafin k'afar sa ya daki kirjinsa, nan ya silale yana gunjin ihu kamar mayunwacin zaki.


Cikin Rawar da jikin shi keyi in ranshi ya ɓaci ya duka tare da masa wata kafurar shakar data sanya Adnan din ɗauke wuta yayi gum.


Cikin sauri mai haɗe da in ina yake masa magana


Kaji.. kunya,kakumayi asara duniya kayi ta lahira jahili marar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login