Showing 51001 words to 54000 words out of 74994 words
Chapter 18 - MATAR OGA NA COMPLETE DOCUMENT writing by UMMY AYSHA.txt
som ban yarda ba,Babu wanda ya isa ya taɓan lfyn ka ya zauna kalau,Zan yi yaki da dukkan wanda zai taɓa rayuwata tace cikin shagwaɓa tana turo baki.
Ya salama saida Jameel yaji kalmar Tata har cikin kwalwar sa.
Akasalance shima yace. To naji Sweety nah Nagode kadan kadan zanmiki,banaso jikin ki ya miki nawie ba..
Shuru tayi tare da lumshe ido.
Ahankali ya yaye zanan dake rufe jikinta ba komi kam kamar yanda Yayi tinani , tsaye yayi yana zubama halittar ta ido mai tsananin kyau da ruɗa lafiyayyan mutum,tsawon lokaci kamin ya sauke ajiyar zuciya ya fara jika towel din cikin ruwan dumin yana gogeta tass, a dubarance kuma yana yamutsa ta duk abinda yake tana jinshi amma ta kasa bude ido dan wata irin kunya takeji kai aure akwai sirri acikin sa.
Shikam saida yagama kana ya ɗauki sabon zanan gadon dake gefe na Asibiti ya rufamata.
Gefe ya koma ya jingina da kofa A'hankali yace" Sweetheart.
Shuru tamai sai idonta daketa kyaftawa alamar batai bacci ba.
Dan Allah kibuɗe idonki inaso naga kwayar idonki.
Uhm uhm ni kunya nikeji tace tana turo baki.
Munfa zama daya Aymah haka zamuje gidan mh kinamun,kina so na kalli wata awaje,kinaso ki tauyeni ne har nafarajin sha'awar mutanan waje,Ki zage kimin abin sa nike so shi zai sa babu wata ya macen da zata burgeni ko kinaso namiki kishiya?.
Da sauri ta buɗe idon ta ta watsamai harara tace.
gaskiya karka sake cewa zaka kalli wasu ashe zaka iya haɗa sona dana wata ? Zaka iya shearing dina da wata da har kake tinanin min kishiya Baby?
Dariya yayi kadan ya matsa wajen ta yace" bagashiba nasa kin bude kinyi kyau sosai ,Ina mai miki Alkawari da yar dar Allah kece kawai a birnin zuciyana,Koda Allah ya tsaraman zanyi fiye da ɗoya to namiki Alkawari bazata kaiki ba balle ma bana da wannan ƙarfin na rike mace har biyu..
Ido ta lumshe tana murmushi tace Allah yasa da gaske, Allah kuma ya dorar da son da kakeman har abada.
Nayi missing Deedee nah sosai fa ina kewar ta .
Ameen sweetheart.
Hmm kibar Tsohuwar nan nikam babu kewarta danayi dan yanzu Deedee tana ta samun rikicin tsufa,nan yashiga bata labarin abunda tamai jiya.
Murmushi sosai ta dingayi wanda da tana da lfy sai tasha dariya.
DeeDee nah kenan Allah ya karamata lfy da nisan kwana..
Ameen Sweetheart mizakici?mikuma kike so na miki.
Mifa zan bukata ina tare da kai,duk wani abun da nike so kamin,bana buƙatar komi Baby.
Tom naje nayi wanka kin yarda?
Kai ta jinjinamai tace kaje saika fito.
Kiss ya mannama ta a goshi yace *zaki rama wanda nake miki in kika warke fa ki sani bashi ne kike ci,in so goma na miki in har kinji sauki tom sai kin min so goma kin yarda?.
Ido ta rufe cike da kunya shikuma yayi murmushi kamin ya mike yashiga toilet din.
Sadda ya fito tayi bacci hakan yasa shi bude kofar ya fito dan son zuwa gida ya ɗakko mata abinda take so.
Ahanya suka hadu da Dr Abba da da matar shi sai yaron su guda biyu ɗaya namiji sai mace hannusu rike da basket.
Ango ango yashiga zaulayar sa tare da faɗin.
munbarku ba komi Sorry fah madam ce ba lfy sosai shiyasama muka fito yanzu..
Bkm Dr barka da kwana ya fada yana mikamai hannu,Baya sun gaisa ya juya suka gaisa da matar .
Ango ya mai jiki? .
Alhamdulillah da sauki sosai yafada yana bama yaron hannu suka gaisa.
Ya sunan ka ya tambayi Yaron.
Sunana Abul khairi,
Nikuma sunana
Ummul khiri inji macen tana turo baki.
Dariya yasa cike da sha'awar yaran yace khairi, kin san ni?
Aa ban s@n kaba Daddy ne yace muzo muga Friend nasa da Aunty bata lfy.
Cike da son yaron har cikin ranshi yace hakane to muje sai kuga Aunty kumata ya jiki ba.
Da to suka amsa yamasu jagora suka shiga har dakin Aymah.
Bayan ya ɗan duba wasu magungunan nata yace .
Jannat ki zauna da ita zan dan ganshi muna zuwa Dr Abba yace.
Ohk my Love sai ka dawo ta fada tana aje ledar hannuta kusa da gadon.
Hannun Jameel ya kama suka fita kai tsaye office din shi suka nufa suka mayar suka rufe.
Kula ya jawo ya shiga zuba masu felfesun yan ciki daketa tashin kamshi kana ya aje ledar Bread kusa da su ya tsiyayamasu Black tea mai kayan kamshi.
Abokina muci wannan na tabbata baka ci komi ba.
Murmushi Jameel yayi yace naci mana.
Tom naji wannan na daban ne.
Nan suka wanke hannu sukaci suka koshi bayan sungama yaba Jameel katuwar ledar daya sawomashi kaya sunkai kala goma yace" ga gudun muwa ta nan bayawa,sauran na wajen tela.
Baki Jameel din ya sak kamin a raunace kuma yace wai miyasa kakeman hidima haka ne,jibi fa abinda kamana dan Allah,.
Kafi karfin komi Jameel awajena bakason yanda na daukeka bane, Jameel an yaudareni anci amanata abokin dana yarda dashi ya rusa rayuwata,shi nike ba sirrina yayin da ya daukan sakarai daga karshe ya nemi lalata da matata Jameel daga lokacin na kasa samun Aboki ko guda saboda na tsorata,kai kam na yaba da halaccinka na yaba da kirkinka da rike takonka Jameel, som baka da rawar kan matasan zamani,nakara sonka ne tun sadda naji Deedee nama faɗa akan baka tarayya da kowa shiyasa na kutsa kaina awaje ka har nasamu ka aminta dani,Dan hala nike da gdy ,ga matana nan Jameel ina so ka hadasu zumunci da matarka ina fatan Allah ya dorar da zumuncin mu har abada,albishir da zanma anan shine yau an'hadama motarka in sha Allah, da Daddare zasu fita gobe su dawo Allah muke roko yasanya albarka da buɗi acikin kasuwar nan.
Cikin farin ciki yabrungume shi yace* wallahi ni nai sa'a, kuma in sha Allah zaka sameni mai amana Abbah zan ruke iyalin ka tamkar nawa ngd sosai Allah yabamu Sa'a rayuwa da mutuwa.
Nan yashiga duba kayan yaga kananun kaya ne masu shegen kyau da tsada na yan gayu , sai jallabiya guda biyu da vest da gajeran wanduna masu yawa a takaice lefe ya hadama Jameel.
Gdy yamas asosai kana ya fada Toilet ya sake zabga sabon wanka ya fito ya shirya zanso kuga mahaukacin kyan da yayi ga sajen nan nashi dake kara kawata kyakyawar fuskar sa.
Da hannu Dr Abba ya nunamai wata kujera yace hau kayi bacci in ta tashi zanma magana.
Ido ya zaro yace bacci kuma? Ina jinyar matar nawa?.
Yeah bacci naga bakayiba som kar kaima na kwantar dakai oya maza yakara yana ɗaure fuska..
Murmushi yayi dan Baya da ta cewa hakan yasa shi cire rigar ya hau kujera dan danan kau bacci ya kama shi.
Acen daki kau yaran ne suka natsu akan wani karamin gado suka hau game da wayar Abul khairi.
Jannat ma wayar ta hau latsawa suna zaune sukaji an'turo kofar ana faɗin" Aymah nah i milisu ( miss u) yau som banyi bacci ba ,wai dan uban sheɗan saida yaga asuba tayi dan dai yaja Allah yakamani ya lallaɓo ya dingaman kalamai masu sanyi sai gashi najini Bangaladash sai tara na tashi shegen yayi nasara ayau amma In sha Allah bazai sake ciba har abada, Sannu .
Murmushi Jannat tayi tace" Deedee ina kwana?.
Laaa wacece ke mutum ko jinnu? a ina kika sanni baiwar Allah Deedee tace hankali tashe idon ta kamar zai faɗo akan Jannat.
Murmushi Jannat ɗin tayi tace" Dr na bani labarin ki sosai muna nishaɗi,shiyasa kina magana na gane kece.
Washe baki Deedee tayi tace laa wai ke matar Dr Abba ce , Allah sarki,nan idonta ya kai kan yaran tace kwaraiko ga macen nan Tuleliya kam tayi kama dashi,yoke maimakon kibar Namijin ya biyo ubansa saike kika gadosa.
Dariya yaran suka hau yi aguje kuma suka yo kanta suna faɗin yau munriga Daddy ganin Deedee shi.
Haɗa su tayi tace wannn haka yake Yar lukutar dadi nidai kam ga miji na nan ke kam kishi yace tafada tana ba Abulkhairi hannu suka kashe.
Kuka khairi zatasa Deedee ta jawota tana murmushi tace ke wasa nike duk kan ku I lobilu wallahi ..
Gabaki daya suka sanya dariya kana ta juyo wajen Aymah nan taga ta tashi ta bude ido sai murmushi take.
Da sassarfa ta ƙarasa wajen ta tace sannu Aymah na sannu,jiya kinbi layin tinkiyoyin likita kinsh wuka, Allah yabaki lfy sannu kinji.
Yawwa Deedee nah nayi kewar ki,ina zoɓo ina kunun aya?
Haba Aymah nayi su yanzu ai nacika yal'bura uba,bari nayi inga lafiyan ki kana,kajin kwai ma zan saya asaka ɗakin Adnan.
Murmushi tayi tace Allah ya samiki Albarka.
Ameen ta amsa kamin ta juya ga Jannat daketa murmushi ta bata hannu tace sannu Mrs Abbah.
Cikin kulawa Sosai Jannat din ta bata nata tace sannu Mrs Jameel kuna lfy ya karfin jiki Allah yasa an'maki a Sa'a.
Alhamdulillah Ameen ya rabbi sannu ku ta fad tana kirawo su Abul khairi nan suka gaidata cikin ladabi.
Cikw da aon yran da kaunr su ta hau amsawa tana dan tamhayar su abinda ya shfi karatun su sun bata amsa.
Deedee tace kai ammafa naji dadi wallahi jikin yayi kyau Aymah,jiya kau yanda kikason zaa maidaki yar mafiya haka aka dora maki karafuna a kirji da kai kai munga masifa Allah ya kara lfy
Ameen Deedee nah kowane bawa da nashi kaddara.
Eh ina fatan wannan yazama nah shine silar farin cikin kin Rayuwar ki har abada.
In sha Allah tace tare da waigawa ganin bataga Jameel bah.
Duk da kallo suka bita Deedee tace .
wai Aymah ina Jameel na dauka bayan gida ya zagaya amma har yanzu shuru ko haihuwa zaiyi ai sai haka?
Yafita shida Dr Jannat ta basu amsa tana bude kulolin ta shiga zuzzuba masu abinci , Yayin da ta hadama Aymah mai ruwa ruwa ta bata tanaci suna fira saida taga ta koshi kamin ta zauna taci .
Suna haka Aka turo kofar Jameel ya shigo.
Sanye yake cikin kananun kayanshi sai baza kamshi yake kana ganin fuskar shi kason bacci yayi.
Ido suka hada da Aymah ta kawar da kanta tana turo baki alamar tayi fushi.
Kanshi ya shafa yana fadin kiyi hakuri sweetheart laifin Dr ne shine yasani kwanciya.
Murmushi tayi tace"Au nakau godemasa cikon tekun maliya tinda har yasa ka huta Allah yabiyaka da Aljannah ka cancanta wallahi.
Ameen yace yana karasa wajen ta ya zauna gefe gadon tare da dan shashafa fuskar ta ya gyara zanan jikin nata A'hankali yace" zamu kara wankan yanzu ko sai Anjima?.
Laaa haula wala kuwati illah billa,yanzu Aymah dama lfyn ki klau har wanka kukayi tare amma kika naɗe kafa kika koma gurguwar ƙarfi da yaji kai jama'a ni Deedee shekaru na sun tashi a iska dana kasa tantance wayon ku.
Jannat ce dake dariya harda hawaye tace kai Deedee kefa kin ganema idon ki Daddy yabani labarin har suma kikai kika kasa magana , shine zakice karyane,kinson ba wanka zatayi ba so akwai bukatar ana kula da jikin nata dan taji daɗi ko kuwa?
Oho yanzu naji zance kinson su sun'waye yanzu bama tani suke ba tace afusace.
Deedee wallahi zaki fita waje kina ma matana ihu Jameel yace yana zubamata harara.
Uwaka Jameel tashi bar dakin na raba auran ku ni zanyi abinda kakeyi...
MATAR OGA NA
UMMY AYSHA
PAGE 26
Dariya sosai yasa yace. "Wannan kuma baki da hurumin sa.
Atakaice haka suka zauna cikin nishaɗi da farin ciki mamaye a zukatan su.
Bayan azahar Manager yazo shida Baba Ali suka ganta da jiki suka aje masu kayan dubiya kana suka tafi..
Adnan
Wani mugun azaba sadam ke gana mai wacce tin yana da kudirin daukar fansa har ya fara sanyi yana so kawai ya samu mai taimakon sa ya dauke shi daga gidan tin kamin sadam ya kashe shi.
Fitsari kam kullum sai ya bashi so daya arana ya taushe shi dole yasha.
Wannan hali da yake ciki yasa Adnan din fara son kuntatama sadam din ta hanyar kwantar da hankali ya tiƙa uban kashi dan yaba su Sadam din aiki.
Shikam Sadam ganin haka yasa yace to ai hikenan tinda ni zakaba aiki kwara ahutar da kowa zaka rayu in da ya dace dakai..
Katon buhu suka samo suka dora Adnan din akai suka dinga jan shi har zuwa toilet din dake cikin get ɗin.
Akan shadda dake wajen suka ɗorashi babu ko wando yace to kaitayi in ka gaji ka sake wani dan buhun ubanka munafuki mu bamu fika Hatsabiban ciba.
Yasha kuka ya gaji gashi ko gusawa baya iya yi, ga masifar sauro da kwarin Toilet dake dallamai cizo tinda babu Kulawa,Sosai yashiga nadama abinda ya shirya gashi ya gina Ramun mugunta abin kuma ya rufta dashi..
Abinci kam a cikin leda suke kawo mai da ruwa guda su jefa su kama gaban su.
Wannan rashin kular ba karamin matsala tajaza mai ba, dan cikin lokaci jikin shi ya fara wani irin wari marar fasali,kafarshi kam da bata da lfy har wani ruwa ruwa take masu masifar Ɗoyi.
Awannan lokacin ne ya fara kuka da hawayen shi akan halin da yake ciki.
Ta ɓangaran Aymah kau Abin sai son barka ,Dr Abbah da matar shi sun shayar dasu mamaki ta hanyar bada dukkan kulawarsu ga Wannan ahli, Jameel ya sake tabbatar da haduwar su da Dr ba karamin Alkhairi bace,Aymah kau in'ka gansu da Jannat zaka yi tinanin dama tare suka tashi dan shakuwa.
Ta bangaran Manager kam abin sai son barka Hidima sosai yakemasu bakin rai bakin fama .
Bayan sati daya
Ya kama kwana takwas kenan da aikin Aymah..
Turo dakin yayi ya isketa zaune tana ƙoƙarin mikewa tsaye alamar ta fara samuwa.
Cike da farin ciki ya buɗe hannu yace oyoyo matana ta kusa dawowa hannun Babyn ta tarama masa wankan da yake mata.
Cike da shagwaɓa data kware da ita yanzu tace.
Nifa gaskiya A'a kai zakaitamun Bazan iyaba wash Baby kirjina zai faɗo ta fada tana dafe wajen da akai aikin.
Da sauri ya kamata yana fadin ki daina tashi ba,kinga gashi an sallamemu Jannat zatana kula dake gida tinda itama Nursing ce,Ga hutu mijinta ya bata saboda ke Har sai kin warke.
Cikin mamaki tace da gaske?
Yeah da gaske nike bara na dakko whell chair na tura yar gurguwata mu wuce ko, gasucen duka gidan ki ke kawai ake jira..
Murmushi tayi tace good dana zama gurguwar taka ba ta kowa ba.
Gida kuma ada ne yake nawa,a yanzu ni Aymah na baka wannan gidan halak malak,Banso kace komi in ba haka ba zamuyi fada bazan sake yarda kanamun wannan abunba ta faɗa tana juya kai cike da kunya...
Dariya sosai yashiga yi kamin ya sake rungumeta yace dan Allah sake faɗa naji, akwai dad'i dama kina so?..
Aa banaso tace murya ƙasa -ƙasa.
Ban yarda ba yace yana huramata iska a kunne tsawon 5mnt kuma ya daina.
Jin yayi shuru yasata dago idonta da sukayi jawur har ruwa ruwa ke kwanciya aciki ta zubamai su alamar yadai..
A kasalance shima ya zuba nashi cikin nata yace.
kikace bakyaso ga idonki nan ya fallasa sirrin zuciyar ki,Allah ya karabaki lfy Aymah, na fara kosawafa sosai wallahi yanzu burina ɗaya naji nayi ajiya a wannan wajen ya fada yana shafa cikin ta.
Cikin kasalalliyar murya datafi tashi yin low tace.
Ka manta bana haihuwa,Shekara 16 da aure fa ko ɓatan wata banba ,kai sai kasanya rai zan haihu a gidan ka?.
Sosai ya dinga sakin murmushi da kalaman ta har saida ta kai aya ya juyo ya fuskanceta tare da rike kafaɗar ta yace.
Matana ba juya bace som,Kema kin son haka,da kuma kikaga kin kai wannan lokacin karki manta wani baya Haihuwar ɗan wani,Sannan dama tin farko Allah ya rubuta zan ba Adnan aron'kine kamin na girma na bunƙasa na iya rikeki na kuma iyautata zaman takewar mu,yanzu kuwa bagashi an maidoman abata ba, Gashi duniya ta sheda zan iya Rikeki a halin yanzu,kuma kema kin sheda hakan,jinyar nan taki itace tazama shamaki a tsakanin mu,amma ni ina da tabbacin In sha Allah duk ranar da Mukai wasan dambe dake aranar zan jefa kwallo a raga in Allah yaso ya yarda ki rubuta ki aje nikaina na yarda da kaina , ko zakiga zahirine?
Da sauri ta ɓoye kanta a kafaɗar shi tana kai masa k'ananun duka akafaɗa tace.
Som yanzu bakaji,ada ba haka kake ba,ada ustaz ne kai,amma ayanzu idonka ya buɗe why?.
Masha Allah da kikason da ni ustaz ne, Ustaz fa dukkan abinda yason halaliyar sane to bazaki samai dajin nawie a wajen nan ba,in kuma abu ya zamto na saɓama Shari'a musuluncine zaki samai mai kaffa kaffa da abin saboda bin umarnin Allah,Karkiyi mamaki dan Yanzu na waye akan wasu abin nawinki fa ya hau kaina kana idona ya sake budewa da kallon Kyakyawar surar ki,ke in'ma baccin abinki Aymah waye zayyi ido huɗu da kyakyawar mace kamar ki bai gane cewa shi lfyayye bane, wallahi tin washe garin zamanki Asibiti na kara tabbatar da lfy nah,kai Alhamdulillah Allah kulli halin ya karasa yana bata wani lafiyayyan kiss a goshi. .
Zatai magana yace ina zuwa ma idata agidan ki, akan gadon mu,kanki a cinyana,hannuna a br....
Bakin shi ta daɗe da sauri dan kar ya ƙarasa.
Shikam dariya yayi ya mike da sauri yafita tare da cewa matsoraciya.
Naji! tace tana gyara zamanta Murmushi kwance a fuskarta,Kai Auran wanda keda rufin Asiri Duniya ne,yanzu ta tabbata da Adnan ne sai dai ta rub'e ta lalace bazai iya bata koda awa daya Acikin a wannin saba, gaskiya da mata zasubi shawarar ta su daina cewa sai mai manya kuɗi,su samu mai rufin asirin da zai basu lokacin su ya basu kulawa,amma wallahi mai dukiya bashi da cikakken lokacin kowa saina dukiyar sa da tinanin mi zai shiga ya fito,miye in yayi zai bada riba ba faduwa ba,kullum tinanin shi yanda zai sake yalwata canjin sa,ciwo in yakama matar shi bazai iya sashi zuwa ganinta ba sai dai ya turo kudi dan yana ganin sune maganin matsala komi ,baison kaga mutum kusa da kaiba ma kawai arzikine Babba,kai taga banbanci dari bisa dari.
Ahankali tace" gashi yaro jagab,kuruciya bai'baye dashi,ga kamala,ga iya soyayya,ga iya sarrafa mace,iya sarrafa halshe yayin furta zance,wow Jameel kayi sosai, Allah kabama wanda suka daura mana auran nan tukuici da gidan Aljannah.
Jameel kau Dr Abbas yaje ya kira ya sake dubata kana ya sallame ta ya fito da ita cike da kulawa da tarairaya mutane sai kallon su suke, yayin da wasu suke tinanin Yan uwan junane, wasu kuma suna tinanin miji da matane duba da irin tarairaya dayake bata.
Bayan sunje gaban