Showing 39001 words to 42000 words out of 74994 words
Chapter 14 - MATAR OGA NA COMPLETE DOCUMENT writing by UMMY AYSHA.txt
kayiman bayani yanda zan gane miya faru wane sharri ke tsakanin Adnan da mahaifina da har ya iya sanya masu Babba mota bin takansu?
Hawaye ya share yace.
Aymah kinson dai ni Amintaccen mai gadin mahaifinki ne tsawon shekaru, kinson harkar mahaifinki harkace ta bukatar taimakon al'umma dan mutum daya bazai iyaba kinson harkar fito dai.
Mahaifinki na da dribobi da dama da suke masa tukin mota in sun dawo zaima kowa sallama ta kirki wanna dalilin ne ya karama shi farin jini kowa nason yayi aiki a kalkashin sa.
Yanada wani aboki Alh Hamza ɗan sanata babban aminin sane kuma duka harka ɗaya suke saidai an'fison kayam mahaifinki sosai saboda ragowar farashin da yake dashi...
Hamza baya Kaunar mahaifinki ko kadan amma bai taba yarda ya bayyanaba ko afuska hasalima kullum goyan baya yake samu daga mahaifin naki.
Wata rana muna zaune gidan dawakan mahaifinki saiga Alh Hamza da wani yaro kaca kaca yaron yasha wahala Daganin shi a tagayyare yake ashekaru baifi 25 ba.
Bayan sun gaisa yakecewa da mahaifinki Alh ga yaro nan na kawo kason ni yanzu harkata ta farayin ƙasa bama da empty motar da zanbashi ka taimakamasa yana bukatar taimako saboda ya kula da mahaifiyar shi.
Abban ki mutum mai tausayi cikin lokaci yaji yaron ya bashi tausayi .
In takaicemaki aranar ya bashi sabuwar motar gwarama dakuma kayan abinci yace yakaima iyayensa.
Yaron na har kuka saida yayi daganan fa shima ya dage ya rike amana yazo ya sharce dukkan sauran dribobi kokari gashi kaifi daya kuma baya zalinci da wasu keyi sana duk abinda akai zai kawoma mahaifinki bayacin ko sisin sa, ke ko mota ta lalace baya faɗa sai dai yasa kudin sa ya gyara wannan fa shine yakarama mahaifinki soyayyar yaron nan mai suna Adnan da Dribobi yan uwan sa ke cemai Black driver ya jawoshi jiki ke saida ya mayar dashi tamkar ƙanan sa wanda suke uwa daya uba daya babu inda zaishiga bakiga Adnan a bayansa ba,Uwa uba inda ya ida saye Baban ki wajen son da yake maki da baki kulawa duk inda yaje yadawo tsarabar ki daban...
Sun samu shekara takai biyar suna cikin wannan jin dadin rayuwar kwatsam wata rana Adnan din yazoma mahaifinki da son Ya aramishi kuɗi tsabar 100ml.
Mahaifini kuma lokacin ya kwashe yawancin kudadansa wajen turomasa da wasu sabbin kayan da basu riga sukayi magana da Adnan dinba ya bashi hakuri da nunamai ya Bari sai komi ya kammala zai bashi Yanzu ga ƙudirin sa.
Wannan abufa yama Adnan zafi ganin lokacin da suka ɗauka amma ya kasamai Alfarma kawai yasha alwashi sai yabar aiki kalkashin sa tinda amfani kana tare da mutum ya taimakama ranar da kake da buƙata.
Bayan kwana biyu yazo da kanshi muna zaune bakin get din gidanku ya cillama mahaifinki key tare da mai munana kalamai ta hanyar nunamai shiɗin mutum ne mai masifar son abin duniya uzirin sa kawai yasani baison na kowa ba Allah ya hada kowa da rabon sa.
Iya wuya mahaifinki yashiga tashin Hankali yin duniya Adnan ya tsaya yaji uzurinsa amma yaki daga baya ya nuna mai shi ya hakura da nashi uzirin yazo yabashi amma yaron nan ya shure kafa ya tafi cikin zafin zuciya dan dama bakar zuciyane dashi som Abokan aikin suma basu son shi gashi dama Mahaifinki yafi sonsa dasu akwai wannan kishin A ransu.
Amamatu wallahii Alh Abdulkarim kuka yasa sosai yana faɗin" Dan Allah kuce yazo wallahi zanbashi banaso wannan abun yashiga tsakanina da yaron nan Baba Ali banaso kowa yaga baƙina kar Adnan ya daukeni maison kai kamar yanda yace.
Ban'cemai komiba illah tashi dana yi cikin sassarfa nabi bayan as
Adnan dan in samo in lallaso shi ..
Daga nesa nike hangosa banyi tinanin kwala mai kiraba illah binshi danacigaba dayi har muka fara shiga cikin gona ki inda cak ya tsaya kalkashin wata bishiya tare da zaro sigari yasa a bakin shi ya ɗauki waya ya fara latsawa.
Koda aka dakko wayar cikin muryar sa ta yan daba da bamuson yana da itaba yace" Yahajj komi yazo kwana ɗan iskanan fa yashiga tashin hankali ya kake gani akarɓa koko abar shi da Alhini,aini dama wallahi ba wani sonsa nikeba nutum ana tare dakai muke wahala amma arziki nakane kullum jinike kamar in karshe shi wallahi shida ɗiyar nan tasa mai ciman kudi har cikin raina in nasaimata Abun biyar shikam yayita washe baki dan ubansa yanajin dadi zasuzo Hannu ai...
Jikina ɓari ya kama tashin hankali mabayyani ya bayyana agare ni da jin furucin wanda banyi tsammaniba .
Jin yacigaba da waya yasani dade bakina nayi kasa cikin ciyayi inajin yana fadin.
Yo dayason halacci ko Billion nace zai bani ai zai girmama bukatuna amma ba komi nayi alƙawarin Sai naga bayan shi ,sai nayi gutsun gutsun da naman jikin shi ,wanna Yar tashi kuwa sai na lalata rayuwarta badai ita yakema wannan ɓata lokacin ba, Wallahi wallahi yau ko gobe saina watsamata rayuwa nayi mata daga daga na keta mutuncin ta shikuma bazai sake sani idoba sai bayan shekaru zanzomai ta sigar da baitaɓa tinaniba.
Kuka ya kufceman da karfi wanda yasa shi juyowa a razane nan mukai ido hudu dashi jikina ya fara bari na fara ja da baya yana biyoni da fadi" kai Ali tsohon banza dama laɓe kakeman aiko daga kaina ka gama yasa hannu ya zaro wata katuwar wuka yayo kaina .
Dan ceton rayuwata na juya na fara gudu yana bina sai dai sabon jini da tsohon jini sunsha banban ganin zanbashi wahala yasa shi jefoman wannan Wukar takau saman anan ya gwadamasu wajen wuyan shi kamin yace ganin nafaɗi ciki jini ya biyoni ya haye ruwan cikina yace tinda kaji sirrina nida Hamza sai kabar duniya ,Zan kuma datse hannuka guda saboda kaida ɓarawo hukuncinku ɗaya dan kayi satar maganata. kara cakaman wukar A ciki Yayi yakuma sata ya datseman Wannan hannu ya karasa yana gwadamasu guntun hannusa dake cikin riga..
Kuka Sosai Aymah keyi yayin da manager ke share hawaye Anya Adnan mutum ne kuwa..
Yacigaba da fadin..ganina cikin Wannan halin ya tabbatar mai da bazan sake rayuwaba nan ya jani har gab da gidan gonar Mahaifinki ya ajiyeni kamin ya kama gabansa tafiyar da yayi mai dogon zango.
Ni dai kam a labarin da naji nan wasu manoma suka tsinceni aka fadama mahaifinki nan aka zo aka kawoni Asibiti Cikin garin katsina. Babu wamd yabani ran tashi sai gashi cikin hukunci rabbi Allah yasa ina da tsawon kwana a gaba..wani zuwa da mahaifinki yayi ganina naita gamashi da Allah akan banaso Abokin sa yasan ina raye..
Yaso yaji dalili na fadamai dai ba komi in lokaci yayi zan fadamai.
Amamatu kinson bashi da matsala son jin abinda bakai niyya faɗamai ba.
Bai matsaman ba hakama bai faɗamasu ba, koda na warke gidan shi aka mayar dani ya sanya masu kula dani ana gadina.
Bayan naji sauki sosai mahaifinki yasa aka dawo dani cikin iyalaina saidai hankalina a tashe yake ina tinanin taya zan iya sanar dashi manufar wayan nan azzaluman akansa.
Wani lokaci nayi shiri asace nabi dare dan zuwa in samu mahaifin ki Muyi magana aka shedaman bakwa kasar naji zafi sosai dan sabon mai gadin nasama dakeman kallon kamar mugu abinda yaceman bazaku sake dawowaba sai nan da shekara goma.
Nakauji dadi nakumaji na natsu da hakan na dawo cikin iyalina na cigaba da aikin gonata nida yan uwana hankalina akwance dan nason bakwanan ko Adnan ya dawo bazai iskeku ba.
Bayan shekara biyar wani wanda nike ɗan samun labarin gidan mahaifin ki yakeceman wai an ɗaura Auran ki da Adnan kana kina shekara 20 Amamatu nayi kuka nashiga tashin hankali nayi jinya duk akan wannan Auran naki da bantaɓa tinaniba.
A binciken da nayi na gano cewa Ashe saida Adnan yayo Babban shiri ya tun kari mahaifinki .
Shikam Baban ki a sannan Babban burin shi kar ya sake ɓatama Adnan shiyasa duk abinda ya nema yake mai jiki na ɓari har auranvki duk mahaifinki baya hayyacin sa, ke karshema rabashi yayi da danginsa baki daya sai shi kawai, Alh hamzama watsar dashi sukai baƙi daya basu sake bi takan shiba.
Saida ya tabbatar ya ginu da dukiyar mahaifin ki kana ya fara tinanin kawar dashi dan ya ida mallake komi.
Sadda kika kammala karatunki mahaifinki ya fara shelar son kowa yaje mishi Walimar buɗe Asibitin ki, bayan naji labari nabi dare dan zuwa wajen shi sai dai banson wake lura dani ba wasu suka kamani suka kulle tsawon kwana biyu baci ba sha ajikin bishiya.
Da yammacin da nike niyyar kwana na farajin ihu dana saurara da kyau naji kuka Yarana ne biyu da Allah yabani mace da namiji sai mahaifiyar su nan aka kawosu gabana aka yar, Adnan ya bayyana da zafgegiyar wuka yana murmushi yace" Ali kenan babu abinda bansaniba agame da binciken da kake domin ni , Sai dai awannan karon bazan ma ko kwarzaneba bakin ciki zai sanya zuciyar ka bugawa suma wayanda kakeyi dominsu gobe war haka ana shirin kaisu kushewa koma an binne su.
Gama wannan maganar keda wuya ya sanya wuka yama matata yankan rago da yarana biyu yasa aka binnesu ko wanka ba amasu ba.
Aiko maganar shi tayi tasiri dan nima nan wutata ta ɗauke sawon lokaci ashe har taɓin hankali ya sameni dana dawo hayyacina ake faɗaman mutuwar Iyayen ki Aymah nayi kuka nashiga tashin hankali.
Ganin ba sarki sai Allah na dawo nan dajin ina rayuwa ba wanda na sani babu wanda ya sanni.
Kayan itace sune abincina.
Wani lokacin kuma in hakura in kwanta gabaki daya duniya ta juyaman baya Aymah Allah ya sakamana dan Adnan ya mana tabon da bazai goge ba...
Wani irin kuka Aymah keyi jikinta kau wane na Jameel ya riga da yayi zafi.
Manager ma kuka yake Sosai yace Baba naji dadi da taji daga bakinka ada tana ganin wani abun bazai yiyu Adnan ya mataba.
Dukiyar tama tace wai ta barmashi dan kawai tayi Alkawari yanzu irin wannan mutanan za'a barwa ƙaruwa?.
Murmushi Yayi yace wane shi Amamatu.
Manager ya kalla yace waya faɗama inda nike???
Kuka sosai Manager yayi kamin yace Baba nayi kuskure a baya amma a yanzu ina son gyara laifina watakil ku yafeman kai ko baka yafeman ba nima zankai kaina court ..
Nine wanda.....
❤️ *MATAR OGA NA* ❤️
UMMY AYSHA
PAID BOOK
PAGE 19
""Nine wanda ya dakkoma Adnan iyalin ka har inda aka daure ka, amma wallahi azeem bai faɗaman kashe su zaiba, ya dai sanar dani cewa Aima barazana dasu wacce zatasaka guduwa daga garin baki ɗaya..Baba ni yaron sane babu abinda ban saniba na Adnan, amma daga lokacin dayama wannan zalincin naji na tsane shi ina neman kuma hanyar da zanbi in gyra kuskurena,nasha wahala sosai kamin in samo inda kake dakyal wani mutun Almajirine yanzu daya kasance Aminin ka a lokacin shike baka labarin rayuwar gidan su Aymah ya bani wannan address din naka,Shima yace a nemamasa gafarar ka domin kuwa Rashin kudi ya kamashi ya zagaye yaci amanarka wajen sanar da Adnan bibiyarsa da kake Har abinda ya faru ya faru dakai..
Murmushi sosai Baba Ali yayi kamin yace" ba komi Allah ya yafemana ,kai kuma na yafema suma kuma dasuka rigamu gidan gaskiya Allah ya gafartama su ya yafemasu kura kuran su. Amma tabbas Aymah yau ba gobe ba sai dukiyar ki ta dawo hannu ki dan gumin mahaifin kine,Hakki kuma naki ne bana Adnan ba..
Dakyal ta iya ɗago idonta dan kanta da kirjinta masifar ciwo yake ta zubamasu ta kasa cewa komi.
Ganin haka yasa hankalin su tashi manager ya tashi yana faɗin ta taso sutafi amma jikinta yayi bala'in sanyin da ko yatsanta bata iya mikewa.
Addu'a sosai baba Ali yashiga yimata kamin A'hankali ta fara sauke ajiyar zuciya.
Cikin maganar ta da bata fita sosai tace" Baba dan Allah kabini muje gida ina so mu ida magana ne acen Banajin daɗi.
Sosai ya nuna rashin amincewar sa saida tasamasa kuka tare da bashi labarin su Deedee tace''.
ina so kai ka zameman uba inaso ka gyara Alaƙar dake tsakanina da yan uwan Baba na,har yanzu zaune tsaye bata kareba tsakanina da Adnan, ga matar sa dake shirin shigowa danma manager na dakatar da ita banaso ta fara zargin wani abu ayanzu kaine hujjana na karshe Baba dan Allah ta karasa tana rike kirjinta Sosai dake barazana rabewa..
Cikin gamsuwa da kalamanta ya mike zai dauki kayan sa kala guda wayanda biyune dama yake rayuwa dasu ,yau in yasa wannn gobe ya wankesu da ƙafa tinda ba hannu ya shanya.
Hanashi tayi da faɗin muje kawai Baba.
Dakyal suka fito daga Wannan jejin، sadda suka kawo bakin mota Aymah ko gani sosai batayi saboda bala'in jirin datakeji daga jiya zuwa yai taji abinda yafi ƙarfin tinaninta shiyasa duka yanayin ta ya sauya.
Hanya suka ɗauka tafiya kamar ba gobe Baban kanshi saida ya gaji.
***
Jameel kau farin ciki hana shi bacci yayi Asubar fari ya samu Mahaifinsa da maganar, Sosai kuwa yaji daɗi da fadin ta wannan hanyar kawai zaka sakama Aymah dan Allah ka rikeman ita a mana Jameel kaga yanda ta sadaukar da farin cikin ta akan naku.. .
In sha Allah yace yana dukar da kanshi.
Inna su ce tafito daga ɗaki.
Da sauri ya tashi ya koma daki tabishi da kallo dan duk taji abinda suka tattauna Murmushi kawai tayi ta zauna tace" yanzu Baban su kana ganin taya zai iya Auran Hajiya Aymah? mace yar gayu data tashi gidan hutu Jameel ko gidan da zasu zauna babu ,gashi babu abinda zai mata koda lefe ..
Shuru Malam Habu yayi yace .
Duka abin Aure na Allah ne , Insha Allah kuma nima gobe zanje nasamu Deedee muyi magana,in yaso gonar nan inje kauye da kaina asake sata kasuwa muga abinda Allah zayyi.
Amince mai tayi da addu'a Allah ya zaɓamasu Alkhairi...
Duk abinda suke faɗa akan kunnan Jameel sosai yaji dadi haka kuma sun bashi tausayi shawarar Dr Abba ta fadomai .
Nan ya ɗauki wayar shi ya kirashi akan yanaso su hadu su tattauna akan batun kasuwancin da yace...
Sosai kam Abbah yayi farin ciki inda yabashi izinin ya iskeshi officer dinsa yanzu.
Ba ɓata lokaci yayi wanka ya shirya ya kira Abokan sa ya shedamasu bazai samu damar zuwaba sai washe gari.
Fatan Alkhairi suka mai shikuma ya sallami iyayensa ya doshi hanya Asibiti.
Bayan sun gaisa yake sheda mai Amincewar sa akan bukatar da yataɓa zomai da ita dan yanaso da kanshi yayi hidimarsa ba tare da ya dorama iyayen sa nawie ba.
Yaji dadi sosai nan ya kira dan uwansa yashedamai harkar da Jameel keso ya fara amma bayaso abashi driver kai tsaye yake so ya tsundumashi cikin Harkar, ga 500k ya bashi gudumuwarsa halak malak Allah yasa masu Albarka.
Faɗamaku halin farin cikin da Jameel ya shiga awannan gaɓar ɓata lokacine domin kuwa har hawayen farin ciki yayi kyautar irin wannan zazzafan kudi lokaci daya ba dangin iya bare na Baba.
Dr Abbah kau lallashin sa kawai yake yana nunamasa muhimmancin taimakama wanda bashi dashi.
Tare sukaje gidan ɗan uwan Dr Abbah nan suka zauna suka fara gaisawa kamin ya fara masu magana.
"kaga yanzu man petur muke kaiwa Nijer sukuma su bamu gas.
Dr Abbah yace to kamar ya ake harkar Yaya Nura?
Gyara zama Ya Nura yayi ya fuskance su sosai yace a ƙallah million biyu zata iyamaka wannan harkar.
Na farko dai sai kasai mota ka kuma sai jarkoki uwa uba zaka sai man petur din ..
Misali
Duk jarka biyu in kabasu zasu baka jarka guda ta gas kai kuma in kazo nan Najeriya ka saidata zaka iya samun ribar 5k duk ga wannan jarkar,to saika lissafaman in ka kai jarka dari nawa zaka samu riba.?
Sosai kam suka gigice dajin wannan uwar riba dake shigowa.
Murmushi yayi yace. Amma fa akwai kalubale, saidai kamin ya afkama zaka iya mayar da dukkan kudin da ka kashe cikin sati biyu zuwa ukku mussamman in'ka samu Driver Arziki ɗan amana da bashi da wasa.
kalubale kuma shine kamawa da Costume keyi.
In suka kamafa shikenan sai dai hakuri da fatan Allah ya mayar da Arziki.
Cikin gamsuwa da bayanin sa Dr Abba yace" Amma dai yaya ai ba kullum zasu kamaba ko?
Murmushi yayi yace haba Alh ai da kaima saika binciko aikin ka, in'kau akace kullum muma da bamuyi ba.
Cikin farin ciki sosai yace.
Yayah munji zan bashi aron Million daya da rabi ya fara ,Kaga dana yana da 500 a wajena in yaso sai a fara masa ko zuwa sati mai zuwane.
Murmushi yayi yace Babu damuwa Abbah duk yanda kuke so kuma nima in sha Allah zan dubamasa cikin amintattun drebobina in bashi wanda zasuyi harka tare..
Jameel yace "Yallabai ko ni zan iya wallahi.
Da sauri Dr Abbah yace" A'a kai dai abar shi hakan sune masana harkar tashi muje iyaka kai komi yayana zai maka ka ganshi nan yafini ilimi nesa ba kusaba amma kuma baya da ra'ayin aikin gomnati sai wannan harkar amma fa wlh shine Attajirin family namu kaima haka nike fata kaxama kaf Family naka.
Rungume shi Jameel yayi Yanajin wani mugun kaunar shi har cikin ranshi.
Mikewa Yaya Nura yayi yana dariya ya haɗasu ya rungume cikin wayewa yace.
kai dai munbari kai tama mutane Allura, mukuma munfison kullum Bugun Abuja suyita shigo wa.
Kai kuma kanena Allah yasanya ka fara asa'a,Ka gabatar da istakhara kamin farawa, kana ka yawaita Addu'a ka dinga sadaka zakaga haske in sha Allah,...
Godiya sosai suka mai suka tafi suka shiga motar Dr Abbah.
Jameel ya fara mishi godiya ya tsaidashi yace.
Jameel harkar sirri zamuyi dakai.
Saida gaban Jameel ya buga jin wannna magana cikin mamaki yace bangane ba?.
Dan murmushi Dr Abbah yayi yace" Jameel inaso karka bari Aymah ta sani,inaso ka aure tane kana cikin wannan yanayin naka na Driver mota,Ina so yazamana iyayenka kawai zaka sanarmawa a sirrance dan su sama Albarka, kana in kuka yi auran ko haya ka kama muku ku zauna.
Agefe ribar da kake samu kaje ka samu katon gida Lafiyayye ka gina kai atsayema in dai kanaso zaka iya samu.
Cikin Amincewa da bukatar shi Jameel ya rungumes hi tsamtsam yace" nagano manufarka Allah yasaka da Alkhairi, in sha Allah haka za'ayi ita kuma Aymah inaso nan da watanni kalilan amana Aure, ko bata tareba wallahi inaso najita ƙalƙashin inuwar aure na.
Wannan mai saukine yace yana tada mota.
Cikin jin daɗi yace" muje gidan ta inaso na ganta.
Motar ya tada yana zaulayarsa nan