Showing 30001 words to 33000 words out of 74994 words
Chapter 11 - MATAR OGA NA COMPLETE DOCUMENT writing by UMMY AYSHA.txt
tayi maza ta mike tare da daukar Hijjob din Deedee sauri sauri tace ina zuwa Kaka ta fita da sauri...
Kallon juna sukai Kamin Deedee tace "lfy kuwa? to ina zata waye ta sani .
Kamar tunamai tayi da sauri ya mike ya mara mata Baya.
Yana fita get din ya hango wani mai Machine ya juya baya ita kuma tayo ciki tana ɓoye abu.
Waye shi yace idon shi na sauyawa zuciyar sa namai mugun zafi kamar zata fasa kirji ta fito.
❤️MATAR OGA NA ❤️
MALLAKI
UMMY AYSHA
LITTAFINAN NA KUDI NE KIBIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI HAJIYA
ACCOUNT NUMBER 9064260199 AMINA DAHIRU OPAY BANK
SHEDAR BIYANKI TA WANNAN LAYIN 07038423451
Page 14
"Kallon shi tayi na lokaci kamin ta ɗaure fuska gam babu alamar fara'a ko wani wasa a tattare da ita ta nemi raɓashi zata wuce batare data bashi Amsa tambayar sa ba.
Aymah maganafa Nike miki Jameel yace yana bin bayanta.
Juyowa tayi itama idonta sunyi jawur tace.
Kaga Jameel bai'dace kanamun haka ba dan kaga na baka fuska,Kana da Babban matsayi a Rayuwata kaida iyalinka amma wannan bashine zaisa nabaka fuska kana tuhumata kamar yar cikin kaba,karka manta a shekarun da nike dashi zan iya tantance gyara zan kuma iya tantance b'arna,karka matsama Rayuwarka da tuhumata akan Duk abinda kaga nayi,kazuba ido kayi kallo,kana karkacika matsaman da son jin abinda bani na buɗe baki na fadama ba,in har mukatafi akan haka sai kafi kowa jin dadin zama dani ina fatan ka fahimceni ta karasa tana juyawa tayi tafiyar ta .
Jameel kau da kallo yabita.
kallo mai cike da mamaki da maɗaukakin tashin Hankali.
Yanzu har akwai abinda zai iya zama sirrinta wanda bazata fadamaiba,shine take kallo take fadama wannan bakar magana akan kawai yanaso karemata mutunci!
Aiko saiya gwadamata namijin duniyane shi, kana shekarun shi bazai zama Hujjar da zata iya rainshi ba.
Wannan dalilin ya ɓatamai rai sosai ko sallama bayyi da DeeDee ba yayi tafiyar shi gida ranshi na suya.
Aymah kau tana shiga ta Haura sama kamin ta dawo kasa ta cire Hijjob ta aje.
DeeDee ta bita da ido ganin ba walwala fuskarta sai batacemata komaiba illah ruwa datace taje tasha.
Ruwan kau ta ɗauka tasha sosai kamin ta ajiye tayi sama da kanta ta fara nazari.
"Son Jameel yamata shigar bazata A zuciyar ta bayan tasanya makullin kiyayyar Ɗa namiji ta rufe, Amma Dole soyayyar da takemai tasa ta karfin tsiya ta bude ta bashi babban matsayi a zuciyarta.
Ita kanta har mamaki take yanda lokaci ɗaya son yaro ƙarami yayi ma zuciyarta shigar farmaki haka cikin sauki.
Tana da burin Alkhairi wa Jameel da Family nasa amma kuma lokaci baiba da zata bayyana amatsayi hasken rayuwar sa.
Tana kyautata mishi zaton Alkhairi amma kuma bazata bashi damar Sanin abinda batai niyya ba ayanzu.
Cikin rauni tace''
Am so sorry My Jameel karkayi Fushi kaji. .
Jameel kau kamin ya isa gida wani zazzafan zazzaɓi ya saukar mai dan shi halittar shi muddum aka ɓatamai rai ko bakar magana sai ya kwanta ciwo tamkar mace.
Da sallama yashiga gidan nasu yana Layi.
Inna su ta kamashi tana fadin "Kai lfy?.
Kaina ke ciwo yace dakyal yana sauke numfashi.
Sannu tamai tare da rakashi daki ta kira kabeer akan yaje ya taimakamasa ya cire rigar.
Kamin ma ya shiga ya iske ya cire kayan daga shi sai vest da wando yayi kwance ya lumshe ido.
Ganin hakan yasa Kabeer din fita dan bashi waje yayi bccin sa.
Yana ganin fitar sa ya gyara kwanciyar sa kanshi na kallon kwanon ɗakin.
Wasu hawaye masu masifar zafi suka zubomai.
Ya Yadda son Aymah A jinin shi yake.
Ya yarda da kaunar ta aka halicce shi,Baitaɓa tinanin soyayya A rayuwar sa ba.
Yana ganin ɓata lokacine da shirme,amma yau ɗaya Ta ɓatamasa rai akan wani gantalallan tsamurmurin saurayin da tayi wanda ko yayi rantsuwa bazai kaffaraba babu abinda zai kaishi.
Shine Dan'yayi kishinta zatamai faɗa,koko tana ganin dan yayi zama kalkashin su bai cancanci ya tsaurara tsaronshi akanta ba bayan amanar shi yake ganinta ahalin yanzu Tinda yana da Babban buri akanta.
Cikin rawar murya ya fara magana.
"Aymah ina son ki ,ina kuma matukar Kaunar ki wlh, Duk da ina tsoron bayyanamiki hakan dan nima nason bandace da keba Gaba da baya kinfi karfina,,To Amma shi so ba ruwan sa.
Karkiyi amfani da girman shekarun da kika fini ki'ki bin umarnina hakan zai iya jefani tashin Hankali da bashi da magani,Dan Allah AYMAH ki fahimceni,ba nufina nayi takura wake ba,Inaso ne dai na kare maki mutuncinki,aganina ayanzu baki da dan uwan dayafini , bai'dace ace akwai abinda kike ɓoyeman ba nazama ke kinzama ni in abun Alkhairi ne zan baki goyon baya, wanda naga zai cutamiki zan nisantaki dashi haba man Aymah ya karasa haƙoran shi na haɗewa dana juna tsabar masifar zazzabi .
Malam ne ya shigo yana fadin sannu jamilun Deedee ashe bakaji daɗe ba Allah yabaka Lfy ga Paracitimol na siyoma.
Mikewa yayi ya karɓar yasha ya koma ya kwanta.
Cikin lokaci bacci yayi gaba dashi .
*Kauyen Abukur*.
Tsintsiyar kwakwace Hannun Wata mata tana shara ranta ɓace ta juyo ta fallama mutumin da kan shi ke ƙasa mari.
Cikin fushi tace.
"Jakin inane kai akan ana bamu 5k na kula dakai shikenan saika zauna kai tamana kazanta yanzufa na gyara wajen nan sai kuma ka sake ɓatawa dan ubanla.
Bance in kana da buƙata kayimana Haushi akira Malam ya kaika ba tinda baka magana,Katon banzakai ka sake ka gani yanda zanma.
Kanshi ya ɗago anan nima na zaro ido ganin yanda lokaci kankane yanda halittar Adnan ta juye yayi wani masifaffan baki idon shi duk sunyi zuru zuru alamar yunwa ta faramai illah.
Kai yashiga d'agawa dan ko magana baya iyayi.
Kunnen shi ta rike sosai tana murɗawa tace zaka sake.
Da sauri yashiga jujjuyamata kai Hawaye na sakkomai bana komiba sai na bakin ciki.
Kanshi ta dungure tace Ɗan wahala kawai kimanin wata daya amma jibi yanda siffarka ta dawo kamar ta ifritu mina jinni, in sake ganin yaman kazanta wajen turken awakina yaga yanda zan yimai sabuwar kaciya ta karasa tana xaro wuka da zaro mai ido...
Sosai kau ya furgita dan zaman da yayi da Ladidi ya fahimci duk abinda tace zatai mai yimai take dan batada tausayi balle imani ko kaɗan a ranta.
Aranshi kau Ya ɗauki Alwashin yanda zai samu kakkafar wukar da zayyi mitsi mitsi da naman jikinta Duk ranar daya ganshi tsaye da kafarsa.
Hmm akwai daba ,Dole ya haɗa kogo guda na jinin makiyansa na fili dana ɓoye..
Washe gari.
Aymah ce waya akunnan ta cikin tashin Hankali tace" Dr ga Yan wajen aikin sanan zuwa yanzu gidan nan Duba shi ina cikin matsala ya zamuyi?
Deedee ce ta dawo daga kasuwa bayan tayo sayayya kayan kununta da zoɓo.
Dan Asuba fark kuɗaɗan mutane sukazo hannuta tace.
Lafiya kike Safa da marwa Aymah?.
Hawaye ta sharce tace Deedee "
Mutanan wajen aikin sune zasuzo duba shi gashi nacemasu yana gida yanzu haka suna hanya na kira Dr yace bari yazo.
Tsaki Deedee tayi tace dallah nasama wani abune.
"Kice basai yazo nan ba yasanya a dakko Adnan din inda aka kaishi akawo nan.
maza azo da wayan nan mazajen da suka kaishi suma.
Ihu Aymah ta fasa tana rungume Deedee da sumbatar goshinta kamin ta ɗauki waya ta kira Dr ta shedamai.
Shima rikicewar da Yayi baisa wannan tinanin yazomai ba saida ta faɗamai.
Cikin farin ciki ya juya akalar motar sa kuwa zuwa gidan bulo din daya dakko matasan.
Ganin motarsa yasa suka taso suna ihu.
Bai tsaya komi ba yace su shiga kawai.
Kai tsaye suk faɗa ya fara kwasar gudu kamar zasu tashi sama.
Cikin lokaci suka isa kauyen .
Inda yake suka isa suka iske ba'a dade damai wanka ba dan ya tika kashin safe.
Basu tsaya komiba yace su kwaso shi aka sanya mota yana ta harara Su.
Bayan sun shigo Cikin gari suka kaishi akai mai Aski tass aka gyara mai fuska kana sukayo gida.
Umarni ya basu akan su sake mai wanka.
Wanka sukamai mai kyau .
Deedee tace su samai Harda malum malum saiga Adnan kamar ƙadangare cikin Babba riga duk yayi wani iri.
Shinkafa da miya da Nama Deedee ta zubo ta aje kusa dashi sai zaro ido yake.
Murmushi Deedee tayi tace Noo inji turawa wannan duk cikin basajane irin wadda kake ma mutane.
Hon suka fara ji kamar za'a fasa gidan ashigi hakan yasanya Deedee aguje matsawa kusa dashi ta fara bashi abincin yanaci da sauri sauri.
Matasan nan suka fita suka budemasu get din tare da zama cen wajen, Yayin da Dr ya kara gyara zaman glass din sa da abin aune aunen dake sargafe wuyan sa .
Aymah ce cikin shiga ta kamala Hijjob har kasa ta fita ta masu jagora harda manyan shi suka shigo palon da ko kujeru Babu.
Wulcum shanaye inji Deedee tana murmushi.
Ɗaya daga cikin su ne yayi dariya da alama yajita yace Mama shanaye kuma.
Tace to ai naji tana ta cemaku wulcum sir nikuma ai ƙara inyi jimla karwani yaji zafin bancemai ba .
Sannu ku dai mala'ikun Duniya ga Abokin kunan Bakaken aljannu sun shanyemai Dukkan gaɓɓai yanzu haka bamu da komi agidan duk ta sayar wajen neman masa magani...
❤️ MATAR OGA NA ❤️
Mallaki
Ummy Aysha
Domin mallaka naki ki biya kudin ki ta account Number nah kamar haka
9064260199 Amina dahiru OPAY BANK saiki turo shedar biyan ki ta Whatsapp number nah 07038423451
Page 15
"Wani da ya hakimce tsaye Saboda rashin mazauni da alama ogan su ne ya kalli Dede ya gaidata cikin hausar shi data ke zau ta sakota wa yace "Mama ya mai jiki.
Deedee ta karkace saiga hawaye tace" Kabari kawai Yallabai abun babu sauki ciwon anne (Arne).
Lami lafiya fa yazo daga wajen aiki nima nazo ganin yar kanwata wato matar sa.
Yaji anata dukan kofa kason soja da fusata ya fita yaga wata mata tace ya sammata abinci batada abinda zataci.
Maimakon ya bata hakuri Aa saiya hau tsulamata mari dai yanda Wani makwabcin su ke faɗaman dayake yana wajen Abun ya faru.
Tom yana cikin dukan natane ta ɓacce shima ya faɗi nan Yana Rawar Banjo .
Haka dai Aka kawomana shi nan ciki muna kuka da tinanin ko pamalise ce Inji yan boko wato dai shanyewar Ɓaran jiki ya samai.
Wannan likitan shine nan Babba Asibiti yake aiki wato Asibitin kwarari .
Duk aune aune dai da Akai basu nunamana komi ba yadaice afitar dashi waje.
Yanzu haka yau kwanan mu biyu da dawowa dan gajiya sukayi suka koromu ko silifas bamu saba suka furgaɗomu.
Gashi ko magana Bayayi ma yanzu gabaki ɗaya kwara da Yana Haniniya irin Ta Doki,To yanzu ko Haniniyar sauro Bayyi hakadai Yake tamkar butum butumi na India.
Tom Yanzu dai sana'a na fara da zansamu murafawa kai Asiri aita nema masa Magani kaga sheda cen yanzu nadawo kasuwa Ah toh maula zanyi kwara inyi da karfina..
Dukkan su saida tausayin Dattijuwar ya tsargasu Dan sun hango mugun alhini a fuskarta gata da shiga rai.
Adnan kau soi rarraba ido yake yanajin kafurar karya da Wacce baison ko wace ba take keto mai.
Ya rabbi ka budeman koda bakina ne in karyata tsohuwar nan yace aranshi yanajin kamar ya fashe da kuka,Shida ko Chemis basu kaishiba amma Ance yaje kasar waje Yah Allah.
Ɗaya daga cikin sune ya kallai yace "Kuma kamar yanason yace wani abu Mama.
Deedee data dakko kayan sana'a ta tace" Yo ai haka yake wata rana ma gani zakai Yana zillo Kamar tsohuwar motar dataci Cikusoba.
To dai Ina ganin Aljanar ce kemai Cakulkulo..
Gashi fa Nan gani yake duk kun'mai tsaye kamar masu gadin jahannama yaganku Cikin kaya masu Ruwan ganye.
Yanzu bala'in tsoron mutane yake balle ku da zai ganku da yawa.
Kuma ina laifin ku shigo da dai-dai amma kamar zaku Rakiyar kansilan kauye ku shigo daki duka sai kace an'tadaku daga Asambali.
Dadama daga cikin su dariya suka hauyi dan akwai hausawa Sosai wayan da Basajin Hausar kaɗan ne.
Nan dai sukaita Alhini suna kuma jerama Dr tambaya yana basu amsa cikin natsuwa.
Babban ogan sune yace da DeeDee" Mama ko kina ganin mu maidashi Bariki cen kalkashin kulawar mu.?.
Haɓa ta rike zatai magana Adnan ya zabura yana gur'nani.
Deedee ta taɓa hannu tace "Alhamdulillah! Da da bakina nace wani abu saiku karyata to kungani da mazajen idanun ku.
Som Som Aljannun Basuson matsawa daga ko ina, Sunfison zaman nan din dai kamar kabari .
Ina mai tabbatar maku da cewa kuka kaishi cen saiya ida haukacemaku baki daya Ƙarshe ma ya gudu.
Abarshi nan inta kula dashi ainima d'ana yake balle ni daban taɓa haihuwaba sai najisu kamar sun Ketani sun kutso ta Jiki Na.
Aymah ta danyi murmushi lallai ta yarda duk wanda yaja da Deedee ruwa yake tsullugudum,Yau da Babu ita da Batason ya zatayi.ba ..
Addu'a suka hau jeramai ogan nasu yace yanzu dai zamu tafi zamu iya barmaki masu kula dashi ko mutum biyar haka,irin wannan ciwon wahala garai dole saida majiya ƙarfi.
Hawaye ta share tace" Kai ina! Ka ganni nan Arayuwata ina tausayin yaran da basa gaban iyayensu da iyalin su Saboda nayi Maraici banji Daɗin saba ..
Ga matasanan bakin get dake nan kusa damu sune muke neman Alfarma suna kulamana dashi gakuma ita matar tashi Da take Maharramasa..
Indai taimakon zakumana kwara ku dinga sallamar su kun'rageman nawie ,su kuma wayan nan abarsu
Su koma ga iyalan su Lami Lafiya..
Dukkan su am'sawa sukai Cikin gamsuwa.
Dayawa daga cikin su kuma sunkara sonta dan kowa ya farajin faduwar gaban barin shi da za'ayi jinyar mai laluri irin ta Adnan.
Nan fa zaratan maza suka buɗe bakin Aljihu suka fara fiddo kudi sunawa Deedee Alkhairi tana kauda kai da fadin kai duk ku kwashe abunku ni kulawarma da kukai da jikana kawai ta wadatar.
Hakuri suka shiga bata kamin su mike ogan su yace Mama zamu dauki Nawin ku na tsawon lokacin da zai warke in sha Allah.
Duk wata zamu baki 250k ina ganin zata isheki kiyi manege.
Yanzu ga motar kayan Abinci nan zansa akawomaki Allah yaba shi lfy sukuma masu kulawar dahi Ace dasu zamu basu 50k duk wata Allah yabiyaku da Aljannah.
Ameen ta amsa tana murmushi da samasu Albarka.
Harya fara tafiya ya dawo ga Aymah ya kara kallonta kallo na tsanaki kamin yace "banji ɗuriyar yaran nashi ba?
Dam gaban Deedee ya faɗi dana aymah da sauri Kuma DeeDee tace'' Deedee tace ai kason su biyune ita waccen ta nemi saki tin zuwan farko da tayi yaran kuma sunyi hankali suna wajen dangin Uwar tasu sun ruke kayan su.
Cikin gamsuwa da kalamanta ya daga kafaɗa tare da fadin" Taiwa kanta kukuma Allah yabaku ladar jinya.
Ameen Deedee tace tana masu Rakiya suka shishiga suka dauki hanya tana rakasu da Addu'a.
***
Jameel kau da Asuba ya tashi lfy klau jikin ya sauka amma fuskar shi babu walwala.
Kamar yanda yasaba shiri yayi yama iyayen:sa bankwana ya fito da kudin da jiya baiba su Aymah ba.
Ya dauki hanyar Gidan su kenan aka mai waya motar ya cika dole ya tafi ya dauki hanya zuciya ba dadi.
Deedee kam tana shiga ciki ta Ɗanɗara guda tace Adnanu kagani ko?.
Kai kayi nufin Alkhairi wa zuciyar ka kaga in komi bai warwarema ba Dan Butar ubanka.
Yanzu gashi gabanka Alkhairin Allah ya saukar muna shashasha mahaukaci, Allah kadai yason abinda ka shuka shiyasa ya nannaɗeka Haka Kamar fanke waje guda,Ka tuba kaga in Haske bai Ratsa Rayuwar kaba.
Abincin ta turamai gaban shi tana harar shi kamin tace da Aymah tisamun kudin Nan.
Ta kalli Dr tace wai nikam Ina Jamilu ne Tinjiya ko Bankwana?
Yace tindazu nike kiranshi baya ɗauka Allah yasa dai lfy.
Deedee tace tom Ameen dai.
Zai tashi ya tafi ta tsaidashi da faɗin ya raba kudin ya ɗauka..
Dariya yayi ya A'a Deedee in banbaki ba bana karɓa ba baccin kokorin Naki ne.
Wannan Hakkin kine wallahi daɗi sukaji suka baki babu kudin kowa anan .
Dariya tayi tace hakane likita wai kai ya sunan ka ne.
Murmushi yayi yace tsawon wata hudu sai yau ake tambaya to Dr Abba sunana.
Dariya tayi tace'' To Abba mungode da dawainiya Allah ya sakamaka da Alkhairi ya biya dukkan bukata na Alkhairi.
Allah kasanya kagama tsire mazaunan kowa lfy, Allah kasa kar hannun ka ya karkace ka caki wani inda cutar shan inna zata kamshi.
Dariya sosai ya hauyi AYMAH na tayashi daidai lokacin da Jameel ya turo kofar da sallama yashigo .
Ƙasa tsayawa sukai da dariya yayin da kallo daya yamasu ya ɗauke kai ya zauna kusa da Deedee ya gaidata.
Amsawa tayi tana fadin" lfy kakecin magani muna cikin hali na farin Ciki.
Ɗan yake yayi yace ba komi dama nadawone nace bari inkawomaki kudin cefane xan koma.
Aymha ce ta dakata da dariya tana binshi da ido kamin tace'' Ya aiki.
Kamar ya kyaleta kuma ya juya yace Alhamdulillah tare da mikewa yaba Dr hannu yace zai wuce.
Sosai taji ba daɗi tason kuma abinda tamai ne yasa shi kasa sakin jiki dasu yau Allah dai yasa ba wani abu ya zarga game da itaba.
Shikam Dr Abbah mikewa yayi yakama hannun Jameel din suka fito Abakin Get sukaga Su Sadam Yaran da suke kula da Adnan.
Nan ya faɗamasu bukatar zaman da akeso suyi da shi dan bazasu sake maidasu Kauye ba.
amma su maido shi Dakin Baki .
Godiya da murna suka shigayi Kamin suce zasuje su dawo.
Abincin da ka kawo masu yace su fara shiga dashi ciki kamin su wuce.
To sukace suka fara Jilarshi shikuma suka ƙarasa bakin motar Jameel din suka tsaya ya dan kama kyauran motar Jameel din kamin ya shiga zayyano mai abinda ya faru da faɗin. kai bakama lura dashiba naga Yamafara bacci..
Murmshi Jameel din yayi yace Som idona baigan shiba.
Lamarin Didi sai Addu'a .Allah dai yasakamaka kaima da mafificin Alkhairi muna godiya.
Ameen yace tare da sake rike hannun Jameel din yace.
Ya maganar soyayyar ka da Aymah kana sonta ko ka janye danni banga wani abu ba?.
Ɗan murmushi Jameel din yayi da yafi kuka ciwo yace" Tom mundai barwa Allah zaɓi kawai.
Amma ina ganin kamar nike haukan banza na ita som batani take ba hasalima daukar yaronta takeman ka kauga ba'a aure haka kwara in kyaleta .
Murmushin Dr yayi yace lallai kai sabon shigane a soyayya.
Ba'aima soyayya gadara, ba'amata fushi, komi sai sa sai da ake binsa saikaga an'cimma nasara.
Karka manta isa da gadara da banzatarwa yakai Aymah da mijinta wannan matsayin da suke Jameel.
Kaikuma yanzu kobakace AYMAH i love you ba akwai hanyoyi da dama da zaka isar da sakon ka, kana dole ka iya kawar da ido akan duk kan abinda zakagani..
Na maganar nata bakomi saika magantaba karkasanya tayimana jimla