Showing 27001 words to 30000 words out of 45829 words
Chapter 10 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt
zauna tare da shan kunu, ta kula yaran basu samu tarbiyyar daya ishe su ba dan haka dole ne ta ɗauki matakin da kar raini ya shiga tsakaninsu, ba zata ɗauki wannan shashancin ba dole ne ta seta su kuwa, yaran kuma tunda tayi musu faɗa suke cin magani sai wani turo baki suke yi bata bi ta kansu ba har zuwa la'asar, a lokacin ne Ilham ta ɗauki jakarta tana cewa Aslam suje ƙofar ɗaki su jira Mamansu daga nan suyi wasa, kanzil Safna bata ce musu ba suka fice ta mayar da ƙofa ta rufe, sai da ta gabatar da sallah kafin ta shiga kitchen ta ɗaura wake dan tana son cin shinkafa dawake da mai da yaji ne, ta dawo ta kunna data ta soma chart, anan ne taga Zayyad online sai ta tura masa da saƙo kamar haka.
Farin Masoyi ina cike da tsantsar kewarka ya sanda mai ruwa, ya fama da mutane Allah yasa albarka a cikin nemanka.
Ta tura masa, Zayyad ya yi murmushi lokacin daya karanta sai ya bata reply kamar haka.
Sanda mai ruwa gashi nan ya cika taf yana niman inda zai yi ban ruwa, na tabbatar Ƙaunata a kullun tana maraba da shi dan haka ki yi masa tanadin gaggawa dan yana gabda....
Hahaha gabda me? Ƙaunarka tanadin gobe ko jibi take yi maka.
Kinma isa ai wlh sai dai in banyi niyya ba, ko so kike yi na samu wata 'yar fara a waje ina rage zafi.
A'a wlh ban yarda da wannan mugun wasan ba.
Ta tura masa tare da imoji mai hoton hawaye ɗaya, Zayyad yayi dariya dan yasan ya tabo inda bata so, yasan Safna akwai kishi sai dai yadda take burgeshi bata nuna kishinta akan matarsa ko ta nuna jin haushinta, wani sa'ilin har tare mata take yi.
Ruhin Zayyad kema kinsan ni ɗin wa ku biyu ne kawai In Sha Allah, yanzu me kike dafa mana dan nasan kin ɗaura sanwa baki wasa sa kammala girki da wuri.
Nan ta sanar dashi abincin da zata yi, yaji daɗi domin ya kwana biyu bai ci ba, dan haka yace sai siyo musu latas suci dashi sannan ta dafa musu kwai, to tace masa kana suka cigaba da hirarsu na sakin layi wanda tun aurensu ya fara koya mata, tun tana jin kunya har take biye masa suna yi dan gwara yayi da ita da ace da wata can manza 'yar kwalta suke yi.
***
Rashida sai gabda magrib ta dawo gidan ta tadda yara a tsakar gida suna buga kwallo, suka yi mata oyoyo Ilham tayi kwaɓa kwaɓa da fuska tana cewa.
Anty ta yi mana masifa sai faɗa take yi mana har da cewa wai bamu da tarbiyya, ni bazan sake zuwa gurinta ba.
Nima bazan je ba, gwara kice mu shiga gidan maman Walida mu jiraki.
Cewar Aslam, Rashida maganar yaran yazo mata wuya wato Safna zaginsu tayi da faɗa, saboda son kai bata tambayi yaran me suka yi mata ba har tayi musu faɗa, sai ta yanke mata hukunci akan bata son su ne, tayi ƙofa ta jasu suka wuce ƙofar ɗaki ta buɗe suka shiga, a sannan ne taga ɗakin ba yadda yake, to bata yi komai ba ta fita, a lokacin ne kuma Zayyad ya dawo dan ranar Lahadi baya fita da wuri kuma yana dawowa gida da wuri, sai duk ta daburce ta rasa ina zata fara gyarawa.
METAFORCE
Tsari ne mai matukar kyau daya zo mana a saukake, dan samun kudin shiga ta hanyar amfani da wayar hannunka. Kana kwance a gadonka zaka tare 'yan daloli bisa jajircewarka.
MENENE METAFORCE ⁉️
Kasuwanci ne na network marketing da ake gudanar dashi da wayar hannu, kasuwanci ne wanda kowani reshe ka ta6a kudi ne, kasuwanci ne wanda yake biya 💯percent, kasuwanci ne wanda kowa ma zai iya yinsa, kasuwanci ne da yake da tsaro da kuma tsari wanda yake akan blockchain technology. Project ne me zaman kansa saboda decentralized ne, babu Wanda ze iya HACKING, DELETING KO EDITING. Wani abu daga kasuwancin koda kuwa founder na METAFORCE ne wato Mr.lado saboda an riga an tsara shi Kuma a haka zai ci gaba da tafiya💯 Alhamdulillahi
Alhamdulillah metarforce ana samun arziki da shi sosai. Duk wanda ya shirya dm 09034940106
[17/09, 7:53 pm] null: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C2K7oAG7DtwAX8OnKUpxns
*AMARYAR ZAYYAD*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 12.
Rashida da sauri ta ɗauki tsintsiya ta fara sharar falo a lokacin Zayyad ya shigo da sallama, ta amsa tana ɗan sakin murmushi domin mamansu sosai ta yi mata huɗuba fushin da tayi da shi, shiyasa ta ɗauki aniyar sauyawa domin ta sauya salo, tayi masa sannu da zuwa ya amsa tare da yin hanyar kitchen dan ya saka ruwan wanka saboda yasan bata saka masa a flaks ba, yana shiga yaga yadda ya barshi ɗazun haka ya same shi hakan ya tabbatar masa da Rashida bata daɗe da dawowa ba kuma bata gyaran gidan ba kafin ta fita, hakan ya ƙona masa rai amma in da sabo ya saba, dan haka juyawa yayi ya wuce zai fita ta dakatar dashi da sauri.
Ina kuma zaka je? Me zan dafa mana ne.?
Zayyad ya juyo yana dubanta da kyau.
Rashida bana buƙatar komai kuma ki daina yi mini tambayar ina zani tunda ni ba ɗanki bane.
Amma ai naga yanzu ka dawo kuma nice da girki.
Ashe ma kin san ke ce sa girki shine zaki je kiyi zamanki baki dawo da wuri ba, sannan kin fita baki gyara gidanki ba wannan wace irin rayuwa ce.
To ai yanzu zan gama komai In Sha Allah, bari na saka maka ruwan wanka a kettle.
Ki barshi kawai dan kinsan bana son jira, kuma yanzu ba ke kaɗai bace ina da damar da zanje inda zan samu farin ciki. Aslam zo muje ɗakin antynku.
Ya ƙare maganar dasu Aslam, Rashida tayi saurin dakatar dasu.
Ba inda zasu je, Matarka bata son yaranka dan cewa suka yi tayi musu faɗa har tana ce musu ba su da tarbiyya.
Safnar ce zata ce haka me suka yi mata? Ilham me kuka yi mata har tayi muku faɗa.
Wai daga Aslam yaga abinci a center table ya fara ci, sai kuma muka shiga bedroom muka ɗiba cincin, shine wai ba mu da tarbiyya har take mana faɗa meyasa zamu ci bada izininta ba.
Eh mana Abba faɗa tayi mana shine mu kuma muka yi fushi muka bar mata ɗakinta, dama mamanmu tace duk abinda tayi mana in ta dawo mu faɗa mata shine...
To faɗi ba a tambayeka ba, fara rattafo zance rarara kamar wanda ya haɗiyi radio.
Cewar Rashida data katse shi cikin faɗa, Zayyad ya gyara tsayuwa yana ƙara haɗa maganganun yaran a kansa ya tabbatar tunda Aslam ya faɗi haka to Rashida zata aikata.
Kin kyauta kin ji, da kanki kike son ɓata tarbiyyarsu, na tabbatar baki ji ba'asin faɗar data yi musu ba kike niman yanke mata hukunci.
Ato yara da gidan ubansu sannan ta san kana da yara ta aureka dole ne tayi musu uzuri matsayinsu na yara.
To amma tarbiyya ce kice musu duk abinda tayi musu su faɗa miki, wannan ai sakarci ne kina so ki ɗaura raya a turban da bai da kyau, Rashida ban san me yasa kika sauya ba wlh, da farko kin nuna kina tare da Safna amma tunda tazo gidan nan kike ta abu daban daban masu cike da mamaki, ban taɓa zaton haka daga gareki ba, dan haka ki sauya hali in ba haka ba ke ce zaki wahala.
Dama ai komai nayi laifi ne yara ne kuma In Sha Allah ba zasu ƙara zama a gunta ba in yaso sa riƙa jirana a maƙota, itama zata haihu ai zata san zafinsu, tarbiyya dai dai gwargwado ina basu Allah ya sani ai.
Ban da lokacinki, Ilham zamu je gurin antynku ku bata haƙuri.
Ba in da zasu maza ku wuce kuje ɗaki ku cire uniform.
Sum-sum yaran suka wuce Zayyad ya girgiza kai ya fice. Da Safna ta buɗe masa da farararta tace.
Sannu da zuwa farin masoyi yau ka dawo da wuri Allah yasa dai lafiya.
Alhamdulillah dama duk sunday ina shigowa da wuri, kina da ruwan zafi.?
Eh akwai a flaks sannan akwai wani a kettle.
To juye mini zanyi wanka.
To tace masa ta wuce ɗakinsa ta ɗauko bokiti daga bayinsa ta isa kitchen ta juye ruwan kana ta fito ta kawo masa gabansa, da kallo ya bita yana cewa.
Ki kai mini bayi anan zanyi.
Ai na ɗauka zaka je can kayi dan naga ba nan kake ba.
Safna ki wuce dashi ki sirka mini.
A'a Abban Ilham kaje dai dashi ka yi acan tunda ta dawo, da dai bata nan ne sai kayi anan.
Ɗaure fuska yayi ya miƙe yana cewa.
Ki bar ruwan bana so.
Afwan mijin so wlh ba korarka nake yi ba, haƙƙi ne bana son shiga.
To daga yanzu karki ƙara yi mini musu inna saka ki kiyi mini abu.
Yana kaiwa nan ya ɗauki ruwan ya fita. Rashida tana kitchen amma data ji ya shigo ta ganshi da bokiti da ido ta bishi ya isa ɗakinsa ya buɗe ya shiga yayi wankansa kana ya shirya cikin jallabiya ya fito da bokitin Safna falo akan in zai je masallaci zai mayar mata, sai dai kuma da aka kira ya manta da shi ya tafi masallaci tare da kama hannun Aslam, Rashida tana ganin fitarta ta ɗauki bokitin da fita tsakar gida tayi wurgi dashi, Allah yasa robar mai kwari ce da ya fashe, Safna tana bedroom ɗinta taji ƙarar robar jikinta ya bata bokitin ta ne sai ta fito da sauri, tana zuwa tsakar gida a side ɗinta nan taga bokiti anyi jifa dashi, guntun murmushi tayi dan tasan za ayi haka ganin yadda Rashida take bayyana zafin kishinta, ta ɗauka ta koma ɗaki bakinta alaikum.
Zayyad bayan sun dawo Aslam ya wuce ɗakinsu shi kuma ya nufi ɗakin Safna ya zauna a falo yana cewa.
Kinga nayi mantuwar latas ɗin nan, zuba mini abincin ki yanka albasa da tumatur yunwa nake ji.
To tace masa taje ta zuba masa abincin ta haɗo komai a babban tire ta kawo masa kan center table ta ajiye, nan ya aje wayarsa ya soma cin abincin dan sosai yake jin yunwa, can ba jimawa sai ga Ilham ta zo tana buga ƙofa Safna taje ta buɗe ta shigo tana cewa.
Abba Mamanmu tana kiranka.
Ki ce ina zuwa.
Ya bata amsa sai ta fice zuwa sashinsu ta samu Rashida a kitchen tana fere doya zata yi musu faten doya.
Mama naga Abba yana cin abinci a ɗakin Anty.
Abinci ko?
Ilham tace eh, sai ta saki abinda take yi ta fito ta nufi sashin Safna, dama fitar ilham basu rufe ƙofar ba aiko haka ta murɗa handle ta samu a buɗe nan ta tsaya a bakin ƙofa tana yi musu kallon uku saura kwata.
Wlh Zayyad bazan taɓa yafe wannan ba taya ranar girkina zaka zo ka zauna kana cin abinci anan, ke kuma shafaffiya da mai kin kyauta Allah saiya saka mini.
Safna mukus tayi bata ce komai ba, Zayyad ya miƙe yana nunata da yatsa.
Ki ɓace mini daga nan tun kafin raina ya gama ɓaci.
Zaka zo har ɗaki ka same ni.
Ta faɗa a fusace ta juya ta wuce ranta in yayi dubu to ya ɓaci, Zayyad yayi ƙofa ya koma ya zauna ya cigaba da cin abincinsa, Safna ko bata ce kala ba dan ita lamarin ya fara isar ta, da zai taimaka mata ya daina ci a gunta daya fi mata dan bata son rigima. Sai da ya kammala cin abincinsa tsaf kafin ya miƙe yace mata yana zuwa ya fita. Safna ta miƙe ta rufe ƙofar tana jin ba daɗi a cikin ranta bata so ace ita ce sanadin rikicinsu.
Zayyad yana shiga sashin Rashida ta miƙe a fusace ta fara zazzaga masa masifa, wannan karan bai yi shuru shima ya fara mayar mata, wanda har sashin Safna tana jin wannan faɗar da suka yi, ga yara suma suna kallonsu sai dai suka kame a kujera ko wanne ya natsu, Rashida garin masifa ta zageshi Zayyad ya yo kanta ya zabga mata mari ta fashe da ihun kuka tana Allah ya isa tare da zaginsa, ganin ya ƙara yo kanta ta ruga ɗaki a guje ta rufe dan yadda ransa ya ɓaci to fa zai iya rufeta da duka, ya koma ya zauna zuciyarsa sai tafasa yake yi, daga bisani fitowa yayi ya shiga mota ya bar gidan. Sai a lokacin Rashida ta fito daga ɗakinta ta kira wayar Mamansu, koda ta ɗauka tana rusa kuka ta faɗa mata komai, ran maman ya ɓaci ta shiga zazzaga masifa, daga bisani ta bata haƙuri tace zata yi magana da babansu dan abin ya fara yawa, bayan sun gama waya ta kuma kiran ƙawarta Kubura itama ta bata labari.
Karki ji komai cikin satin nan zan dawo In Sha Allah matsalarki tamkar anyi miki maganinta.
Dan Allah da kin shigo gari ki sanar dani, har gida zan zo dan wlh sai nayi maganinsu.
Cewar Rashida tana hucci, haka suka jima suna maganar daga bisani suka yi sallama ta koma kitchen ta gama haɗa musu sanwar abinci.
Zayyad sai dare kusan goma da rabi ya dawo gidan, ya fara zuwa sashin Safna ya zauna a falo babu wani hira da suke yi domin har lokacin fuskar Zayyad ba walwala, ganin haka yasa Safna kame bakinta ta cigaba da kallo, bayan kamar minti goma da shigowarsa ya kira sunanta ta amsa tana kallonsa.
Daga yau duk abinda su Ilham suka yi miki karki ƙara yi musu faɗa ki sanar dani ni zan ɗauki mataki, sannan banji daɗin yadda kika yi musu ba a matsayinsu na yara har kina ambaton ba suda tarbiyya, to yarana suna da tarbiyya kawai dai akasi aka samu duba da suna yi miki kallo kamar mamansu ne shiyasa suka yi miki abinda suka aikata, dan haka ko me suka yi miki karki ƙara yi musu hukunci ki sanar dani.
Kenan kana nufin ban isa na tayaku tarbiyyarsu ba, ina ce nima ina da haƙƙin kula da tarbiyyarsu matsayina na matarka kuma wacce take zaune a cikin gudanka, duk abinda naga sunyi ba daidai ba kar nayi musu faɗa kenan? sannan ni ban kira su marasa tarbiyya ba sai dai in juya maganar aka yi Allah shine shaidata. Kuma In Sha Allah daga yau bazan sake shi lamarinsu ba tunda hakan ya zama damuwa.
Safna ni kike faɗawa magana haka?
Haba Zayyad ya kake so nace maka, ni abinda naga yaran nan sunyi har nayi magana ganin bai dace su riƙa ɗaukar abinda suka san ba nasu bane gudun kar suje wani guri suyi, amma tunda ya zama laifi bazan sake saka baki a lamarinsu ba.
Tana kaiwa nan taja bakinta tayi shuru, nan Zayyad ya shiga yi mata faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, wato duk haushin Rashida sai ya gama saukewa akanta, da yake ita tasan darajarsa bata kuma cewa komai ba har ya gama faɗarsa kafin tace.
Allah ya huci zuciyarka kayi haƙuri zan gyara da yardan Allah.
Bai ce mata komai ba ya miƙe yana ce mata sai da safe, amma har cikin ransa yaji daɗin yadda ta bashi girmansa, ko anan yaga akwai babbancin tarbiyya tsakaninta da Rashida, yana fita Safna ta rufe ɗaki ta dawo ta zauna a cushing tare da tallafe kuncinta.
Allah kasa naci jarabawarka, domin na samu kaina a cikin wani irin ƙaddara mai wuyar misali, duk yadda nake hangen gisan Zayyad zai zame mini farin ciki ba haka na samu ba, sai tarin matsaloli da suke kunno kai Allah ka ƙara mini juriya.
Ta ambata tana jin wani rauni a zuciyarta dan har hawaye ya cika mata ido, haka ta shanye shi ta miƙe ta kashe kayan kallo da wutar falon ta wuce ɗakinta, ta yi shirin barci ta kwanta.
****
Tun daga wannan ranar zama yaki daɗi tsakanin Zayyad da Rashida, Safna tana iya ƙoƙarinta wajen kyautatawa Zayyad duk da barazanar da take gani a cikin idanun Rashida, dan ko ta gaisheta bata amsawa sai mugun kallo da harara, haka 'yan uwanta in sun zo wani lokacin a ƙofar sashinsa suke yada zango suci hira suna yada mata habaici, haka take maƙalewa a ɗaki ta rufe kanta bata sakewa har sai in Zayyad ya dawo. Sannan batun buga ƙofa da safe har abin ya fara bin jikinta, duk da in anbuga yana sakata faɗuwar gaba, akan abin Naira ashirin Rashida takan buga musu ƙofa ko ta aiko yara su buga, da safe ko da daddare duk kuma a cikin girkin Safna take yin haka muddun In Zayyad yana cikin gidan, yayi faɗar amma duk a banza dan da alama tayi mugun raina shi bata shakkarsa. Safna bata taɓa faɗawa wani matsalar da take fuskanta ba a gidan, dan ko 'yan uwanta da iyayenta in sun kirata suka tambaya komai lafiya to lafiya lau take ce musu, haka ma ɓangaren 'yan uwan Zayyad ko sun tambaye ta lafiya take ce musu, domin tana yawan magana dasu a online, Amminsu kuwa suna waya kota kirata ko ita Safna ta kirata, haka rayuwa ya cigaba da gudana a cikin gidan Zayyad har aka ɗauki wata guda da sati ɗaya wanda ya kama kwanakin Safna a gidan wata ɗaya da sati biyu.
Akwai ƙura kam Allah yasa mu dace. Ina godiya da addu'ar ku da kuma comments dinku Allah ya saka da alkhairi Ameen.
[19/09, 11:52 pm] null: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C2K7oAG7DtwAX8OnKUpxns
*AMARYAR ZAYYAD*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 13.
Safna tana kwance a cushing a falo ita kaɗai, Zayyad a sashin Rashida ya kwana shiyasa bata damu da haɗa abin karin safe ba sakamakon ta wayi gari da ciwon kunne duka biyun, ita kaɗai tasan irin azabar da take ji dan gane da kuɗar da yake yi mata, dama tana da history akan ciwon kunne shara uku da suka wuce tayi fama da shi sai da suka dage da magani sosai daga na asibiti har na islamic kafin ta samu lafiya, abinda ya fi damunta a yanzu shine yadda kunnenta na hagu ya toshe bata ji sosai da shi har ya sakar mata da ciwon kai. Sallamar da Zayyad yayi daga ƙofarta shine yasa ta miƙe jiki ba kwari ta isa ta buɗe masa sai ta juya ta dawo ta zauna a cushing, da ido Zayyad ya bita ganin ba ta da walwala da kuzari, ya tura ƙofar ba tare da