Showing 21001 words to 24000 words out of 45829 words

Chapter 8 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

hijab ta saka ta fito, ta samesu a kofar ɗakin suna jiranta ta rufe ƙofa suka wuce gaba tana binsu a baya. Da sallama suka shiga falon sun tadda Rashida ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kai ba ɗankwali ko hula tayi parking gashi, kallo ɗaya Safna tayi mata ta kawar da kai ta samawa kanta gurin zama shi kuma Zayyad ya zauna kusa da Rashida yana cewa yara suje ɗakinsu suka wuce.


Ina yini maman Ilham.


Lafiya lau antynsu Ilham ya baƙunta da rashin sabo.


Alhamdulillah.


Safna ta bata amsa a taƙaice, sai Zayyad ya ɗaura da nashi bayanin, nasiha yayi musu sosai da kuma irin yadda yake so su haɗa kansu, ya ɗaura da cewa.


Rashida kece babba idan Safna tayi miki ba daidai ba ki sameni ki faɗa mini In Sha Allah zan tsawatar, haka kema Safna ki yiwa Rashida biyayya saboda ta girme miki sannan itace uwargida kafin ke, matsayi ne da Allah ya bata nasan kuma zaki bada haɗin kai. Batun girki ko wacce zata riƙa girkinta wacce keda miji tayi da shi wacce kuma ba ita ce da miji ba ta girka abinda zata ci, cefane da abinci duk ko wanne da shi nasan wannan In Sha Allah zai kawo zaman lafiya, sannan na yanke kwana biyu biyu zan riƙa yi a kowani ɗaki, da fatan wannan tsarin yayi muku, in da mai tambaya ko magana sai yayi.


Ni dai ba abinda zance domin tsarin yayi, Allah ya bamu zaman lafiya.


Suka amsa da Amin Zayyad yace.


Bari muje sai zuwa anjima zan sake shigowa.


Ya ƙare maganar yana miƙewa Safna ma ta miƙe suka wuce, da dogon harara Rashida ta bisu dan bata amsa saida safen da Safna tayi mata ba, suna fita ta ja tsaki tana cewa.


Munafukan banza kawai.


Ta miƙe ta mufi ɗakin yara dan ta faɗawa su Anisa yadda suka yi. Koda ta basu labari maganganunsu suka yi suna cewa ta tashi tsaye karta ɗauki raini, daga bisani Zuliha tace.


Anty kin aika musu da abincin kuwa?


Ohhh kinga na manta bari na haɗa sai ki kai musu.


Tana faɗa ta isa kitchen ta haɗa kulolin abinci guda biyu shinkafa da miya sai kosilo a ƙaramin faranti ta fito dashi falo tana kwalawa Zuliha kira, ta fito ta amsa tiren ta wuce ta fita zuwa sashin amarya.


Safna kuma suna shiga Zayyad yace ta kawo musu abinci, ba musu taje kitchen ta haɗo komai a babban tire tazo da dire a carpet nan suka zauna suka ci abinci tare da Zayyad yana zuba mata santi, suna tsaka da ci ne suka ji bugun ƙofa wanda duk in aka buga sai ƙirjin Safna ya faɗi, Zayyad ya miƙe ya isa ƙofar ya buɗe ganin Zaliha da tire niƙi niƙi da abinci yasa shi mamaki kafin yayi magana tace.


Anty Rashida ne tace na kawo muku.


Ikon Allah ai yau amarya ta fara girki yanzu haka abincin muke ci ki mayar mata dashi, dana san zata yi ma dana ce ta bari.


To Zaliha tace cike da talaici ta juya, shi kuma ya rufe ƙofa ya koma ciki yana mamakin wai Rashida ta yi musu girki, matar da sai ya dawo daga shago bata ɗaura komai ba sai a lokacin ne zata ce masa me zata dafa, girgiza kai yayi bai cewa Safna komai ba dan yasan taji maganarsu suka cigaba da cin abinci. Bayan sun kammala Safna ta mayar da kayan kitchen ta gyara gurin kana ta juye masa ruwan wanka ta kai masa bayin ɗakinsa, ya bita a baya ya shiga yayi wanka ita kuma tana zaune a gefen gadonsa, ya fito ya shafa mai ya saka jallabiyar data ciro masa ya saka yana cewa.


Nan ɗakin ya zama nawa ni kaɗai kenan?


Namu dai amma kuma komai naka yana nan, in ba ni bace da girki zan kwana a ɗakina, in kuma na amsa zamu kwana tare.


Na ɗauka tunda ya zama nawa ni kaɗai zan kwana a ɗakin.


Uhum ni dai ba haka na tsara zan rayu a gida sirrin ruhina ba, in dai yana tare dani to tabbas numfashina da nashi zasu riƙa gauraya guri guda.


Ashe ni ɗan lelenki ne.


Ya faɗa yana tsayawa a gabanta ya kamo hannunta ta miƙe suna fuskantar juma, yadda yake jifanta da wani kallo yasa ta sunne kai ƙasa tana ɗan murmushi.


Da alama wannan kunyar sai na kakkaɓe sauran daya rage, dan naga zai riƙa kawo mini cikas.


Ni dai kaje ka dawo dan ina buƙatarka kusa dani a irin wannan lokacin.


Ta faɗa tana cire hannunta a nashi, murmushi Zayyad ya saki sai ya wuce ya fice kwakwalwarsa yana maimaita masa maganganunta da suka yi tasiri a zuciyarsa, sosai yaji daɗinsu tare da hango tabbas farin cikinsa yana tare da Safna. Yana shiga falon Rashida ya samu ba kowa sai ya wuce ɗakinta ya tura ƙofa yaga tana zaune a gefen gado tana tsare hawaye, da sauri ya isa gareta yana tambayarta ba'asi, banza tayi masa tana ƙara haɗe girar sama da ƙasa.


Rashida saboda kin san zubar hawayenki yana ɗaga mini hankali shiyasa kike hukuntani dasu ko.


Zayyad tun ba aje ko ina ba kana niman wulaƙantani, yanzu fisabilillah ya dace in aika muku da abinci kasa a dawo mini sash, wannan ai cin fuska ne.


Zayyad ko da ta kai aya a maganarta kallonta yake yi yana mamakinta, ta ɗaura da cewa.


A gaban amaryarka kasa a dawo mini da abinci ai wannan raini kawai kake son jawo mini, koda ba zaku ci ba ai yaci ace ka amsa kun saka albarka in yaso sai ka dawo mini da sauran, kaga ka mutuntani a gunta.


Hmmmm dana san zaki aiko da abinci zan ce ki barshi domin na riga na sata ta yi mini girki, kuma cikin ikon Allah koda na dawo ta kammala tana jirana, tayi wanka ta tsaɓa ado jikinta da ɗakinta ko ina yana ƙamshi, wannan ya tabbatar mini da na samu mai sharen hawaye na, kuma in da ace naso kiyi mana girki ai zan kiraki nace ki girka, dan haka banga abin kuka ko jin haushi ba dan nace a dawo miki da abincinki ba, in kinyi dan ki burgeni ne to wlh ba kiyi ba, tuntuni haka na so ki riƙa yi amm ba kiyi, kin nuna ke ga yadda kike so shiyasa na rabu dake ban takuraki ba, ɗan haka ki sani ni yanzu babu abinda sa kiyi ya bani haushi dan ina da wacce zata faranta mini.


Abinda zaka ce ma kenan? Zayyad duk son da kake ikirarin kana yi mini ashe daɗin baki ne, ba aje ko ina ba kana son nunawa banda sauran amfani a gunka.


Ta ƙare maganar tana dubansa idanunta suna zubar da kwallar baƙin ciki, Zayyad ya taɓe baki yana ɗage kafaɗa.


Kece dai kika yiwa maganata fassara amma ai gaskiya na faɗa, dama ce nake baki domin ki gyara kuma da bana sonki bazan kawo iyanzu ina zaman aure dake ba, soyayyar yasa nake ta haƙuri da matsalolinki, kuma ko yanzu auren da nayi ba zai sa na juya miki baya ba kina nan a matsayinki a zuciyata.


Hmmm kawai ta iya cewa ta cigaba da matsar kwalla, Zayyad jin tayi shiru yasa shi shima yin shuru sai ma ya ciro wayarsa ya shiga facebook yana duba pages ɗin mutane, shi dai yasan gaskiya ya faɗa mata in taso ta gyara in taƙi karta gyara shidai yanzu ya samu wacce zata faranta masa, ganin ya kai kusan minti ashirin a ɗakin ya sashi miƙewa.


Ni zan je na kwanta sai da safe, in kuma da abinda kuke buƙata ki faɗa mini dan bana son buga ƙofa da sassafe.


Yanzu kena duk uzurin daya taso mini ban isa in zo in tashe ku ba sai na jira ka fito, wato haka amaryar taka ta tsara maka kenan.


Kina so ki tsuro da halin da ban taɓa tunan kina dashi ba, meyasa ina yabonki sallah amma zaki kasa alwala.


Ni ban sauya ba kaine dai amarya ta soma sauyaka, da alama bani da ta cewa sai abinda ta tsara maka, Allah dai yana ganin komai.


Ta ƙare maganar cikin kuka, wannan karan tsaki Zayyad yaja ya juya ya fita dan in ya biye mata ɓata masa rai zata yi, ya kula lallaɓata da yake yi ne yasa take niman wuce gona da iri, duk da baya jin daɗin ganin tana kuka amma ya zama dole ya rabu da ita dan ba zata caja masa kai ba cikin daren nan.


METAFORCE
Tsari ne mai matukar kyau daya zo mana a saukake, dan samun kudin shiga ta hanyar amfani da wayar hannunka. Kana kwance a gadonka zaka tare 'yan daloli bisa jajircewarka.


MENENE METAFORCE ⁉️
Kasuwanci ne na network marketing da ake gudanar dashi da wayar hannu, kasuwanci ne wanda kowani reshe ka ta6a kudi ne, kasuwanci ne wanda yake biya 💯percent, kasuwanci ne wanda kowa ma zai iya yinsa, kasuwanci ne da yake da tsaro da kuma tsari wanda yake akan blockchain technology. Project ne me zaman kansa saboda decentralized ne, babu Wanda ze iya HACKING, DELETING KO EDITING. Wani abu daga kasuwancin koda kuwa founder na METAFORCE ne wato Mr.lado saboda an riga an tsara shi Kuma a haka zai ci gaba da tafiya💯 Alhamdulillahi
Alhamdulillah metarforce ana samun arziki da shi sosai. Duk wanda ya shirya dm 09034940106
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels






Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
[15/09, 7:29 pm] null: *AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 10.




Rashida da kyar barci ya ɗauketa a wannan ranar sosai ta kuma ƙullatar Safna da zayyad ɗin, hakan yasa ta yi fushi dashi bata kula shi iya gaisuwa kawai ke shiga tsakaninsu, har Safna ta gama kwana bakwai na amarcinta, a ranar Safna da kyar ta bari Zayyad ya fita aiki dan sosai ta langwaɓe masa akan kewarsa da zata yi, koda ya fito sai ya wuce side ɗin Rashida ya samesu a falo, ya zauna yana amsa gaisuwar su Zaliha suka miƙe suna cewa in zai wuce ya rage musu hanya zasu wuce gida, yace to kana suka wuce ɗakin yara dan fito da jakar kayansu. Zayyad ya kalli Rashida fuskarsa sake.


Uwargida har yanzu fushin ake da Zayyad ne? Ya kamata a sausauta masa haka tunda yau kece da shi, da fatan zai samu kyakkyawar tarba.


Kai da kace duk abinda nayi ba burgeka zanyi ba ai babu wata tarba da zaka samu.


Nifa ba haka nake nufi ba, meyasa kike da nacin magana ne da yawan ƙorafi, to kiyi haƙuri komai ya wuce, ki rubuta mini abinda babu ta text anjima zan aiko Jamilu ya kawo miki.


To adawo lafiya dama naso zan je gida kafin yamma na dawo.


A'a ba zaki ko ina ba ki bari sai wani satin.


Dan Allah ka barni na tafi kusan wata kenan ban leƙa ba, bazan jima ba zan dawo.


Amma ki rasa ranar da zaki fita sai ranar girkinki, meyasa haka ne? sannan yara in sun dawo fa.


To baga antynsu ba sai su zauna a gunta kan na dawo.


Hmmmm ba zaki je yau ba, ki yiwa su Zaliha magana su fito mu wuce.


Ya ƙare maganar yana miƙewa ya fice zuwa waje, Rashida cike da takaici ta kwalawa Anisa kira suka fito sai ta rakasu har mota tana cewa.


In Sha Allah ina nan zuwa gobe in Allah ya kaimu ku gaida su mama.


Suka amsa da to kana Zayyad ta tayar da mota ya wuce. Ta koma ɗaki ta zauna tana jin ba daɗi saboda ba kowa sai ita kaɗai, su Ilham sun tafi hadda sai wajen biyu na rana zasu dawo ga duk baƙinta sun tafi, a wannan lokacin ne taji sha'awar son ta ƙara wani haihuwa, dan tun bayan data haifi Aslam ta saka implant na shekara biyar, to gashi Zayyad ya ƙara aure ya kamata ace ta cigaba da haihuwa kafin amarya tazo ta fara nata, burinta ace tafita yawan yara, dan haka tunanin ya tsaya mata a rai da nufin dole ma taje gida gobe daga nan ta wuce asibiti a cire mata implant ba tare da ta sanar da Zayyad ba, dan tasan in ta sanar dashi bazai bari ta cire ba tunda ba son haihuwar yake sosai ba, in kuma ta biye masa itace zata kwan ciki har amarya tazo ta fita haihuwa gwara ace nata yaran sun fi yawa, da wannan tunanin ta miƙe ta nufi ɗakinta ta zauna ta ɗauki waya ta kira ƙawarta Kubura, koda ta ɗauka suka gaisa take ce mata.


Nayi baƙin cikin bikin nan bana nan, amma da zarar na diro gari zaki ganni, wai Rashida kina miye ne har kika bari auren nan ya tabbata?


Ya zanyi to Kubura ƙaddara ta riga fata, gashi ba aje ko ina ba Zayyad yana son nuna mini halinsu na maza saboda yaji sabon guri.


Hmmm ai wlh kece kika yarda amma kin ganni babu wata ɗiya da zan bari ta shigo mini gida wai sunan kishiya, ga Aliyu nan yasha gwada yin auren da magana ta taso za kiji ta kwaranye to an gaya miki zama zanyi, ai ba zan bari ma magana tai kwari ba balle ayi aure, kema tuntuni naga kinyi sakwa sakwa ne amma ko yanzu bata ɓaci ba.


Ni gwara dai ki dawo muji ta ina zamu ɗaura, dan wlh inna cigaba da ganin Zayyad da wata za'a wayi gari aji nayi mushe zuciyata tayi bunga.


Hmmm kisha kuruminki, akwai wani magani ɓata gaban kishiya zan haɗo miki su ki tsuma kanki, ta yadda idan ya kusanceki wlh ita da shi sai rabo in ya tsaga, sannan batun sauran mallakan suma zan sa yayana ya haɗa miki, kin san mu gidanmu yayi ƙaurin suna da malinta.


Kamar nawa zan turo miki? dan ina buƙatar maganin matan nan sosai, da dai bana sha amma yanzu kuwa ba sanya.


Zan je gidan innata itace ke sayarwa duk yadda muka yi anjima zan faɗa miki, har da mallakan da zan amsan miki guri yayana.


Rashida cike da farin ciki ta soma zuba mata godiya tana cewa in ma bata kira ba ita zata kirata tunda itace ke buƙata, haka suka yi sallama tana sauke numfashi cike da tsantsar farin ciki, dan kam a yanzu bata ga zama ba burinta ace ko Zayyad bai saki Safna ba amma ta zama hoto a gurinsa ta yadda ko dabba sai ta fita daraja.


*****


Bayan sallar isha'i.


Safna ta fito wanka duk jikinta ba kwari duba da yau ita kaɗai zata kwana sai duk take jin kewar 'yan gidansu, kamar ta buɗe ido ta ganta a cikin gidansu tare dasu yaya Mudan suna tsakusawa. Zama tayi a gaban madubi tana sanye ta siket underwear ta daga shi sama zuwa ƙirjinta da yake yana da ɗan tsayi ya kai mata rabin cinya, kuma shi kaɗai ne a jikinta ba pant ba bra, ta shafa mai ɗinta mai kyau wanda yake ƙaramata laushin fata, data gama ta ɗauki turaten humra tana bin fatar jikinta tana shafawa tare da duk wani joint na jikinta hatta bayan kunne ta shafa, kana ta miƙe ta ɗauki body spray ta fesa a hammatarta bayan ta saka asalin turaren hammata wanda yake ɗauke gumin zufa, sai ta tuna da indimie ɗinta data ɗaura a gas a low heat, da sauri ta fita kitchen ta duba taga da sauran ruwa sai ta ƙara gas ɗin ta fito falo, a lokacin mbc max sun saka wani action film daya ɗauki hankalinta, sai ta zauna hannun kujera tana kallo dan dama taso taje ɗaki ne ta saka kayan barcinta. A lokacin taji dirar motar Zayyad tasan ba ita ke da girki ba shiyasa bata damu ba ta cigaba da kallo, bayan kamar minti goma ta miƙe ta isa kitchen ta juye indimie ɗinta da dafaffe kwai guda biyu data ɗora a sama ga kuma naman kaza data saka a ciki guda daya, ta fito falo ta aje a center table dan ya sha iska ta ci.


...


Zayyad yana shiga falo ya tadda yara suna kwance kamar marasa lafiya babu wani karsashi a jikinsu, ko dan oyoyo da suka saba yi masa bai gani ba, ya zauna yana cewa.


Mamana me yake damunku na ganku haka, Abbana yaya lafiya kuwa?


Ya faɗa yana dubansu, kafin su bashi amsa sai ga Rashida ta fito daga kitchen tana cewa.


Yunwa suke ji shine ka gansu kamar anyi musu mutuwa.


Meyasa baki basu abinci ba gashi har takwas ta wuce.


Kasan wake wahalar dahuwa yake mini, har yanzu yana kan wuta ban ma saka shinkafar ba.


Da kallo Zayyad ya bita har ta ƙaraso ta zauna a cushing cike da takaici.


Kina nufin baki gama kirgin ba? Tun yaushe kika ɗaura? Ko gas ya ƙare ne?


Akwai gas miya na ɗaura anan itama ta kusa yi, waken yana kan electric.


Da yaushe kika ɗaura girkin nan Rashida?


Wlh barci ne ya shammace ni da yamma sai bayan magrib na samu damar shiga kitchen, yanzu ma nake shirin yin sallar isha'i.


Zayyad shuru yayi ya mike yana duban yaran.


Ilham ga kankana da lemu ku fara sha kafin ta gama muku abincin, ina zuwa.


Ina kuma zaka je?


Zan kaiwa Safna nata kankanar.


Ya bata amsa a takaice, Rashida ta miƙe tana cewa.


Ka aika Ilham ta kai mata mana, ko ka bari anjima in zaka shiga gabaɗaya ka bata.


Saboda ke haka nake yi miki ko, inna shigo da abu yara nake kira su kai miki ko kuma in zan zo na ganku gabaɗaya shine zan kawo miki. To baki isa ki tsara mini yadda zanyi a gidana ba.


To ba sai ka bari in kaci abinci ka shiga ba.


Hmmm kawai ya ce ya fice riƙe da ledar fruit ɗin Safna, yana isa ƙofar ya buga mata tare da yin sallama da sauri ta aje cokalin data fara cin abinci ta isa ƙofar ta buɗe masa, ta ɗauka miƙa mata saƙo zai yi dan tasan haka yake yiwa Rashida amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login