Showing 15001 words to 18000 words out of 45829 words

Chapter 6 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

kayi haƙuri da abinda ya faru jiya In Sha Allah zan kiyaye hakan ba zai sake faruwa.


Idan kika yi haka zanfi kowa farin ciki, sannan ki daina zubda hawayenki dan yanzu nine zan maye gurbin su Umma. Safna sonda nake yi miki babu wasa a cikinsa dan Allah ki zauna lafiya da Rashida ki mutuntata dan itama tana sonki.


Ya faɗa yana jawota zuwa jikinsa, Safna bata iya yin magana ba sai ajiyar zuciya da take saki, nan ya kama kanta ya koro addu'ar da duk wani ango ake so ya yiwa Amaryarsa a ranar farko da suka kebe, bayan ya gama ya ɗagata daga jikinsa ya miƙe tare da ɗaukarta cak ya isa da ira kan gado ya kwantar, ya koma ya naɗe daddumar ya kashe wutar ɗakin yaje ya kwanta a gefenta tare da cire mata hijab ɗinta, a hankali Zayyad yaji duk wani haushin daya kwana dashi jiya ya tafi, sai ya shiga yi mata hirar walimar da yayi da abokansa, tare da taɓa sassan jikinta yana shafa fatarta da yake da santsi da laushi, Safna dai ta kasa sake jiki saurarensa take yi kawai amma har lokacin zuciyarta a cunkushe yake, ba tada lafiya ga yunwa da yake damunta wanda rabonta da abinci tun jiya da rana shima ba a nutse taci ba, ganin da gaske yake yi zai rabata da kayan jikinta, sai ta kasa jurewa ta kama hannunsa tana marairaice fuska akan yayi haƙuri ya bari anjima, shima kallonta yayi da rinannun idonsa da suka sauya launi zuwa wata duniya.


Yanzu zamu gama sai ki koma barci nasan akwai gajiya a jikinki.


Shuru tayi bata ce komai dan ba tada wani zaɓi, jikinta rawa kawai yake yi ga fargaba ga kuma rashin kuzari, tana mamakinsa na yadda yaƙi tausaya mata a halin da take ciki tunda ko bata faɗa ba yasan bata jin daɗin jikinta dan har wata rama tayi daga jiya zuwa yau. Haka Zayyad ya biya buƙatarsa ba tare da wani ɓata lokaci ba, babu dogon wasa ko wani abu da zaisa ta samu gamsuwa shi dai nasa ya sani, Allah yasa kayan gyaran data sha ya taimaka mata wajen fitar da lubricant wanda yasa ya samu sauƙin samun hanya, kuka kawai take yi saboda azabar da take ji daga jikinta, gani take yi kamar ma ba wani soyayyarta a zuciyarsa saina matarsa tunda bata ga wani tausayinta a idonsa ba, haka ya miƙe ya fita falo ya shiga kitchen da niyyar ya saka ruwa a kettle na wanka sai ya tadda akwai ruwan zafi har butar ta kashe kanta, haka ya dawo ya ɗauki bokiti ya koma ya juye ruwan ya mayar da wani. Yayi wanka ya gyara jikinsa kana ya koma ya juye mata nata ruwan ya mayar da wani ya kawo mata bayi ya aje ya fito.


Ki tashi kiyi wanka zaki samu ƙarfin jikinki, in kin fito sai mu kwanta zuwa ƙarfe tara saimu karya na fita. Dan nasan 'yan uwanki ƙila suzo da wuri.


Gyaɗa kai tayi tana cije leɓe ta tashi ta zauna da kyar ta ɗaura zanin kayanta ta sauko tana tafiya da kyar jikinta har ciccira yake yi tsabar zafin da take ji a ƙasanta, haka ta shiga toilet ɗin ta tsuguna da kyar fitsari ya fito mata wanda nan take taga ya gauraye da jini, hawaye ya zuba a kuncinta tasan kuma ta rasa wannan duburcin da ta jima tana tattalinsa, sai dai zuciyarta ta shiga tararradi da kokwanton mutumin data mallak masa shi kamar bai dace daya mallake shi ba, haka ta sirka ruwan da zafi sosai ta gasa HQ ɗinta sosai kusan ruwan anan ya ƙare, Alhamdulillahi taji sauƙin raraɗin da take ji, ta miƙe ta mayar da zanin ta fito akan taje ta dafa wani ruwan na tsarki.


Ina zaki je?


Zayyad ya tareta yana duba wayarsa da alama chart yake yi.


Ruwan ya ƙare zan saka wani ruwan zafin ne nayi wanka.


Ok kawo bokitin na juye miki dama na mayar da wani.


Ya faɗa yana aje wayar a bedside drower ya miƙe ya amsa, ba jimawa ya dawo mata da ruwan ya miƙa mata yana murmushi.


Ki saka ruwan da zafi sosai ki watsa za kiji ƙarfi kinji.


Hummm tace ta karɓa ta koma ciki ta yi wankan, ba jimawa ta fito ta shirya cikin doguwar rigar shadda purpul wanda yasha aiki tun daga sama har ƙasa, ta shafa mai ta saka kwalli ta koma gado ta kwanta, anan ne ya kashe datarsa ya mirgina zuwa inda take kwance ya rungumeta ta baya.


Kiyi haƙuri da duk abinda ya faru jiya wlh raina ne ya ɓaci,vbanso daren farkonmu ya kasance haka ba amma In Sha Allah nayi miki alƙawarin tsawon kwana shida da zamuyi sai ya zame miki daren farko a ko wace rana, saboda tanadin dana yi miki na soyayya ba zai tafi hakanan ba, nagode da kika adana min kanki na sameki cikakkiyar mace, Allah yayi miki albarka yasa a zuwan farkon nan nayi kyakkyawar a jiya wanda zai zame mana sanyin idaniyarmu. Ina matuƙar ƙaunarki Safna ina jinki a can ƙasar zuciya wanda ba zan iya misalta miki yadda nake ji ba, Allah yasa albarka a cikin zamanmu ya kauda dukkan fitina.


Ameen ya rabbi, nima kayi haƙuri da abinda nayi jiyan ban zaci zai zama laifi ba, duba da a wannan lokacin kai kaɗai nake tsumayen jira nayi tozali da annurin fuskarka, shiyasa ban buɗe musu ƙofar ba ganin dare yayi, amma bazan sake hakan ba nayi maka wannan alƙawarin, duk abinda kake so shi zanyi koda raina baya so matsawar bai saɓawa addini ba.


Allah yayi miki albarka Amaryata ya saka miki da gidan aljanna maɗaukakiya, na yarda dake nasan ba zaki zama silar damuwa ta ba. Mu kwanta muyi barci kafin anjima na haɗa mana breakfast.


Kai kuma?


Eh mana, ai tun yau aikina na kula dake zai fara sai na tabbatar miki da gidan Zayyad ne farin cikinki na duk duniya.


Murmushi mai sauti Safna tayi dan sosai kalamansa suka yi tasiri a zuciyarta nan take taji duk wata damuwa ya yaye a ciki ranta, ta kuma yi masa uzuri bisa abinda yayi mata jiya, yadda taji ya ƙara rungumeta yasa ta lumshe ido tana sauke numfashi a hankali, shi kuma a wannan yanayin jinsa yake a wani sabon duniya da bazai iya fasaltashi ba, wani irin so da ƙaunarta ke fuzgarta kamar zai haɗiyeta, haushin kansa yaji akan yadda ya tarbeta jiya da faɗa, sai yake ganin da yayi mata uzuri matsayinta na baƙuwa kuma abar sonsa, daya bi abin asannu to ba zasu kwana jiya kamar wasu abokan gaba ba, a haka barci ya ɗauke shi da tunaninta, itama barcin ya ɗauketa cike da samun natsuwa.


****


Rashida.


Wajen ƙarfe shida ta tashi tayi sallah ta zauna jugum bisa sallaya tana tunanin ko ya Zayyad suka kwana jiya, Zaliha ce ta shigo ɗakin tana cewa.


Anty alale za muyi ko ƙosai?


Ƙosai dai zaifi daɗi da kunu.


To ai mangyaɗa ya ƙare wanda ya rage ba zai ishemu suya ba.


Ok a wanke waken akai niƙa sai na bada kuɗi ku siyo man.


To tace mata sai ta fice ta miƙe ta naɗe sallayar ta adana, kana ta cire hijab ta fito tsakar gida inda suke surfen wake, Wasila ce ta matso kusa da ita tana yi mata rasa.


Yanzun nan naje ɗauko dutsen da zamu haɗa wuta dake can gefen naji ana yin wanka daga sashin Amarya, da alama komai ya kankama abinda kika haɗa bai yi aiki ba.


Wani irin zullo zuciyar Rashida yayi tare da bugawa da ƙarfi har sai da ta dafe bangon da ke kusa da ita, kana ta tsuguna ta zauna a dakalin dake ƙofar ɗakinta ta shiga mayar da numfashi cikin haki kamar wacce tayi gudu, hankalin Wasila ya tashi ta dafa kafaɗarta tana cewa.


Dan Allah ki sausautawa zuciyarki karki yiwa kanki illa, gwara ma kici maganin zama da su dan wlh Namiji ɗan akuya ne ba zai ga sabuwar mace fil a leda ya kasa taɓawa ba gwara ki daina yaudarar kanki, dan aikin gama ya gama tunda an ɗaura, kamata yayi ki zauna ki yiwa kanki linzamin da zai ja ragamar girmanki a cikin gidan nan.


Rashida dai ta kasa magana da kyar ta haɗiye miyau kana ta ɗago kai tana duban Anty Wasila tace a hankali.


Da alama Safna tafi ƙarfina bazan samu yin galaba akan ta ba.


Kama hannunta Wasila tayi ta miƙe sai ta jata suka shiga can uwar ɗaka ta rufe ƙofar da key tana cewa.


Babu gaggawa fa Rashida komai sai a hankali zai tafi, kamar yadda na faɗa miki in wannan bai yi ba to wani zaiyi aiki kar dai ki sare.


Nan ta cigaba da ɗaurata akan mummunar makirci da shawarwari marasa amfani, Rashida sai da ta hau sosai kafin ta ɗan ji hankalinta ya kwanta, sai suka ƙara fitowa waje ta nufi sashin Safna, ta tsaya a ƙofar ta shiga bugawa da ƙarfi kamar wacce tazo amsar bashi. Safna da Zayyad barci bai jima da ɗaukar su ba buga ƙofar da aka shiga yi yasasu suka farka a razane, Safna kam nan take kanta ya rasa mata zuciyarta yana wani irin buguwa cike da tsoro dan har Aljanunta sun motsa, cikin ɓacin Rai Zayyad ya fito falo yazo ya buɗe ƙofar ya fito, bai taɓa zaton ganin Rashida bace, kallon kallon suka yi fuskarta cike da mirmushi.


Ango ango kasha ƙamshi.


Rashida wannan wani irin abu ne da zaki zo ki buga mana ƙofa kamar tarar aradu, barci fa muke yi sannan duk uzurinki ba zaki bari anjima ba in na fito.


Rashida ta marairaice fuska tana cewa.


Wayyo Allah ban zaci barci kuke yi ba ganin ba a jima da asubahi ba, dama mai ne ya ƙare da sugar shine nazo ka bada kuɗin, sannan naji me kuke buƙata a yi muku na karin safe.


Ta gama bayaninta Zayyad yana kallonta fuska haɗe.


Shine ba zaki iya kirana a waya ba zaki zo kina buga ƙofa haka, kin san ai bana kashe wayata in kuma ina da buƙatar kiyi mana wani abu zan kiraki ai. Kuma da kuɗi a hannunki da zaki iya amfani dashi na tabbatar wanda na baki jiya basu ƙare ba, in ma babu saiki ranta a gurin 'yan uwanki inna fito kya amsa ki basu.


Zayyad har nayi lalacewar da zaka tsaya kana gindaya mini sharaɗin da zan yi magana da kai saboda kayi amarya kaji sabon guri ko, tun ba aje ko ina ba zaka fara sauya mini, babu komai Allah yana gani ni bada wani manufa nazo ba, kayi haƙuri tunda ranka ya ɓaci saboda na tayar da shalelenka.


Ta faɗa tana matsar kwalla tare da juyawa ta wuce, Zayyad baiji daɗin yadda ta fassara shi ba kuma duk maganar daya gaya mata shine dai dai, amma ganin hawayanta ya karya masa guiwa sai ya bi bayanta ya tadda 'yan uwanta suna hada hadan haɗa abin kari nan suka shiga gaisawa, ya amsa fuska sake sai ya bi bayanta zuwa ɗakinta, ya sameta gefen gado tana matsar kwalla, Zayyad ya zauna tana dubanta.


Rashida na faɗa miki kina da matsayin da babu macen da zata saka na wulaƙantaki, ni banji daɗin yadda zaki je kina buga ƙofar mu da kanki ba, domin ina duba miki kar ki zubar da girmanki ne, dan in da Sadfna ce ta buɗe ƙofar bansan da wani irin kallo zata yi miki ba, kinga girmanki zai zube a idonta.


Sai dai in kaine zaka bata damar ta raina ni, amma daga zuwa in yi magana da kai shine zai zama laifi da zubda girma, tun ba aje ko ina ba kana nuna mini iyakata da kai bayan tare ta zo ta ganmu.


To shikenan kiyi haƙuri ni bana son ganin wannan damuwar akan fuskarki, yanzu bari naje na ɗauko kuɗin saiki aika a siyo miki duk abinda babu. Haba uwargidan Zayyad ai babu macen da zata kaiki matsayi a zuciyata.


Hmmm Allah yasa.


Ta faɗa tana miƙewa shima miƙewa yayi sai ya kamo ta ya rungume ta tare da manna mata kiss a goshi sai ya saketa ya fice. Yana isa ɗakin Safna ya sameta jingine da filo tana duban ƙofa, murmushi ya sakar mata yana cewa.


Kiyi haƙuri an tasheki a barci yara ne suka zo suna bugawa wai an aiko su su amsa kuɗi za a siya man suya.


Zayyad ya samu kansa da zabga mata ƙarya, bayan lokacin daya fita ta isa windonta na uwar ɗaka taji duk maganarsu da Rashida, murmushin yaƙe tayi masa tana cewa.


Ba komai dama kaina ke mini ciwo kuma buga ƙofar ya razanani, amma ina da sauran panadol zan haɗa tea nasha sai na sha maganin.


To kiyi haƙuri kuma na tsawar musu, bari nayi sauri na fita na haɗo mana kayan tea danni na riga na tashi kenan bazan iya komawa barcin ba.


To sai ka dawo.


Tace, Zayyad ya isa inda ya aje kayansa daya cire jiya ya ɗauki kuɗi ya fice daga ɗakin, da kallo ta bishi tana mamakin yadda yake rawar ƙafa akan Rashida, da alama duk wannan soyayyar da ta nuna mata ashe shigo shigo ba zurfi tayi mata, dan makircin data haɗa mata jiya da kuma abinda ya faru yanzu ya tabbatar mata da wuya suyi zaman lafiya, da akwai mugun nufi a zuciyarta ba soyayyar gaskiya take yi mata ba, haka ta runtse ido tana fatan ko yaya barcin ya ɗauketa amma ina, hirar da 'yan uwan Rashida suke yi a waje ya hanata dan hira suke yi sosai da shewa kamar ba safiya ba.


Haka zayyad ya dawo ya shiga kitchen ɗinta, da kansa ya haɗa musu abin kari, ya haɗa musu tea ya soya kwai tare da gasa biredi da butter a toaster kana ya aje musu a falo, ya je ya kira Safna ta fito suka karya, dama da yunwa a cikinta bata yi wasa ba ta ci sosai, ya kalleta yana cewa.


Kinga kazarki baki ci ba, na manta dana sarrafa miki kin ci shi amma karki damu anjima zan siyo miki wata.


Wai in tambayeka mana.


Ta faɗa tana murmushi, ya kalleta da kyau yana 'yar dariya.


Ina jinki Amaryar Zayyad.


A ina ka koyi girki ne?


A gurin Amminmu, dan lokacin da muke matasa ba abinda ban iya ba da aikin gida, kin san ita duk wadatar Abbanmu bai sa ta yarda da masu aiki ba muke yin komai a gidan.


Yanzu kace har Mukhtar shima ya iya aikin gida?


Sosai kuwa sai dai in hakan bai taso ba.


Nima In Sha Allahu haka zanyi training yaranmu.


Ta ƙare maganar tana rufe fuska cike da jin kunya, Murmushi Zayyad yayi yana girgiza kai ba tare da yace komai ba, haka suka gama karyawa cikin nishaɗi kafin suka miƙe zuwa Bedroom, Zayyad ya shirya cikin manyan kaya yasa hula tare da feshe jikinsa da turare ya juyo yana dubanta.


Na haɗu kuwa.?


Irin soaai ɗin nan kayi, sai dai kar 'yan matan waje su gama kalle mini kai.


Ko sun kalla kwalelensu, ni wa Rashida da Safna ne aka halicceni kaɗai.


Murmushi tayi masa tana jin kishin ambaton sunan Rashida da yayi, ya ɗauki key mota da waya.


Anjima zan aiko da cefane ina so na fara cin girkin Amaryar Zayyad, kiyi tuwon semo miyar kuɓewa ɗanya.


An gama Sirrin Ruhu.


Ta ambata tana murmushi, shima dariya yayi tare da wucewa ta bishi a baya har zuwa ƙofar ɗaki, ya wuce ta rufe ƙofar da key ta ciki ta koma dan ta gyara inda suka karya da turare ɗakin kafin 'yan uwanta su ƙaraso. Tana jin fitar motarsa wanda baifi da minti biyar ba taji an zo ana buga mata ƙofa da ƙarfi, wanda ya sanyata faɗuwar gaba har kofin dake hannunta ya faɗi ƙasa dan razana.


*Akwai ƙura a wannan tafiyar*
[13/09, 8:53 pm] null: https://chat.whatsapp.com/D5ISXoMOGGR9PPoswkybsj


ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .

Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.


MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .


UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari 🤗🤗🤗


*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 8.


Safna daidaita natsuwar tayi da addu'a kafin ta isa ƙofar ta buɗe saboda karta ƙara yin wani laifi, tana buɗewa taga mata kusan su biyar kuma babu wacce ta sani daga ciki sannan ba mai mayafi, hakan ya tabbatar mata daga sashin Rashida suke, matsa musu tayi suka shiga sai ta koma ciki ta zauna a one seater tana cewa.


Sannunku da zuwa.


Yauwa Amarya ina kwana ya baƙunta, kiyi haƙuri mun sake dawowa Allah yasa bamu dameki ba, kin san amarya farin jini take da shi mun ƙosa mu ganki shiyasa tun jiya muka zo sai kuma baki buɗe ƙofar ba.


Cewar Anisa da ta nace sai ta ga Amarya, Zaliha ta matsa kusa da center table ɗinta ta buɗe sauran kunshin naman kazar jiya da Zayyad ya bari a gurin.


Anty Anisa ga mutumiyar fa, da alama mune za muci sauran kazar amarya, Amarya sai dai kiyi haƙuri damu dan gaskiya bama ganin Dajaja bamu sanya mata albarka ba.


Ta faɗa tana yago tsoka ta saka a baki.


Kuma wlh bata yi komai ba da yake a rufe aka aje shi.


Ta ƙare maganar tana taunar kazar kamar mayya, nan fa sauran suka taso duk suka saka hannu amma banda Anisa da ita wajen da suka karya ta nufa, ta zauna tana shan sauran tea data gani a kofi ga kwai da suka rage shima, nan ta gyara zama ta yaga biredi ta soma ci hankalita kwance, Safna tsabar gubar mamakin da ya bugar da ita rungume hannu tayi a ƙirji ta tsaya kallon ikon Allah, hankalinsu kwance suke ci suna hira tamkar dama sun daɗe da saninta, bata iya cewa komai ba banda ido data zuba musu har suka gama cinye komai tas dan hatta biredin saida ko wacce ya yagi rabonsa ba subar komai ba, Anisa ta miƙe tana guntun gyatsa.


Aiko ysnzu na rage hanya dama da guntuwar yunwata na tashi, idan an soma suyar ƙosai na ƙara cika ƙuiɓa ƙuiɓa na da shi. Amarya kiyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login