Showing 3001 words to 6000 words out of 45829 words
Chapter 2 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt
Rashida ce zata shigo amma data ji yana waya sai ta tsaya tare da jin wani ƙululun baƙin kishi ya tokare mata maƙoshi, amma sai ta shanye shi bayan ta haɗiye miyau mai ɗaci ta turo ƙofar ta shigo, kallon kallo suka yiwa juna fuskar ko wanne ba yabo ba fallasa, ta ƙaraso kusa da shi tana cewa.
Sannu da zuwa Abban Ilham ka shigo ɗazun ina bayi dana fito kuma na sha'afa muka shiga hira.
Ai dole ki manta dani tunda yanzu na zama mara amfani a gurinki kin daina sona.
Ya faɗa yana tsuke fuska, Rashida ta saki wani lallausar murmushi mai cike da ma'anoni da yawa.
Ni ɗin banza na da zan daina sonka, kaima kasanni da yawan mantuwa.
Eh hakane, amma Rashida meyasa kullun sai na tuna miki ki riƙa duba flaks ɗina in ba ruwa a ciki ki saka saboda inna dawo bana son jiran ruwan wanka.
Mantawa nayi kayi haƙuri.
To shi kuma singilet da ƙananun wanduna na da suka taru a bayi nace ki wanke su meya hana ki wankewa? Ke kullun sai an tuna miki abu, haka fa kwanaki sai da na rasa wanda zan saka a jikina ƙarshe fita nayi na siya wasu, bafa wanke kayana na tilasta miki ba bayarwa nakeyi a wanke, waɗannan ganin ƙananu ne basu dace a bayar wanki ba na ce ki riƙa wanke su amma abu ya faskara.
Kaima kasan aikin gidan nan yayi mini yawa sannan nayi niyyar wankewa yau, zuwan Anty Wasila ya sa namanta amma gobe In Sha Allah zan wanke.
Allah ya kyauta.
Ya ammata ransa a dagule, Rashida ta yi shuru ta kasa magana tana sosa ƙeya, Zayyad ya ɗago kansa yana dubanta.
Ehen ki daɗi abinda ke ranki.
Dama hmmm me zan dafa maka ne? mu taliya muka dafa na manta ban kira na tambayi me zaka ci ba.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Kullun na dawo sai kin tare ni da abinda sai ya ɓata mini rai, yanzu fisabillahi sai na dawo daga aiki ne za a riƙa ɗaura tukunyar abincin da zanci a gidana, duk yunwar dana kwaso saina jiraki kin dafa, wannan matsalar tun kina amarya har yanzu kin kasa gyarawa, duk tsananin son da nake yi miki amma a hankali kinata rage ƙimarki a idona Rashida.
Dan Allah kayi haƙuri yanzu zan dafa ka faɗi me kake so.
Ta faɗa cikin muryan tausayi kamar zata yi kuka. Miƙewa Zayyad yayi ransa ba daɗi dan har idonsa ya sauya zuwa yin ja.
Tabbas ba zaki sauya ba saboda tsawon shekara takwas kenan da aurenmu amma lamarin bai sauya zani ba, Allah ya shirye ki. Amma ina buƙatar wacce zata kula da rayuwata ba dan bana sonki ba, ina fatan zuwan Safna gidan nan ya sauya mini ke.
To ai nima ina maraba da zuwanta Allah ya bamu zaman lafiya Alh. Zayyad.
Ta ambata cikin miskilin murmushi wanda kuma zuciyarta cike yake da zazzafar ƙuna, jikin Zayyad yayi sanyi yana dubanta tare da cewa.
Allah ya gani ina iya ƙoƙarina da haƙuri dake amma naga duk a banza baki gani, kuma ni auro Safna da zanyi ba zai taɓa sanyawa na sauya miki ba domin kece tauraruwata, ina sonki har gobe.
Sauke ajiyar zuciya Rashida tayi sai ta juya ta fice daga ɗakin dan ji take yi kamar ta kurma ihu, zuciyarta a karye yake zata iya yin kuka kota faɗa masa maganar da zai iya dagula musu lissafi, kuma bata so ya gano logonta, Zayyad ya bita da tsantsar tausayawa banda yana matuƙar kaunar Safna da zai iya fasa aurenta, amma bazai iya ba domin Safna wani ɓangare ne na rayuwarsa, yana matuƙar mamakin ma yadda a 'yan kwanakin nan yake jin son Rashida yana niman dagula masa lissafi sai dai ya bayar da tausayinta da yake ji ne saboda yadda ta nuna dangana da danne kishinta tare da juriyarta akan auren. Falo ya fito ya samu Anisa da su Ilham suna kallo ya wuce Kitchen ya juye ruwan butan da yayi zafi kana ya mayar da wani ruwan ya ɗauki wanda ya juye a bokitin fenti ƙarami ya wuce ɗakinsa. Toilet ya shiga yayi wanka sauri sauri ya fito ya shirya cikin baƙar jallabiya da wando jins ya feshe jikinsa da turare tare da gyara sumarsa na kai dana gemu, sai ya ɗauki flaks da robar fentin ya koma kitchen ya tadda ruwan yayi zafi sai ya juye a flaks ya ɗauka ya mayar ɗakinsa ya ɗauki key, dama wayarsa yana aljihunsa ya fito ya rufe ɗakin da key ya fice abinsa Anisa tana yi masa tsiyar tasan zance zai je ya gaishe da antinsu. Yana fita sai ga Rashida ta fito falon ita da Anty Wasika sun zauna tana kumbure kumbure, Anisa tace.
Ke ya barki da ƙunan zuciya yayi ficewarsa zuwa ga Amaryarsa, wlh ki watsar da shi ki cigaba da lamarinki, shi namiji in kika saka shi a rai sai ya ɗaura miki hawan jini a banza.
Gaya mata dai Anisa, ke gashi baki yi aure ba amma kinsan wannan balle ita, ki cigaba da danne kishinki harta zo a goga ai naji daɗin da zai haɗaki gida ɗaya, kinga sai kuyi zaman kowa ta iya allonta ta wanke, karki yarda wata banza can tazo ta kwace miki miji kina ji kina gani ki zama 'yar kallo.
Anty ya zanyi? Ƙorafin Zayyad yayi yawa duk ƙoƙarin da nake yi akansa baya gani dan kawai ban yi masa girki ba, shi komai a gunsa ƙorafi ne baya min izuri.
Ki rabu da shi Allah ya nuna mana auren lafiya muga amayar da wacce zata zo.
Nan suka cigaba da hirarsu wanda gabaɗaya ɗebewa maza albarka suke tayi, dama a nan zasu kwana da yawan 'yan uwanta in sun zo daga wani gari tofa sukan yi kwanaki a gidanta saboda suna samun kayan daɗi da abinci waja waja. Ita Anty Wasila goɗai goɗai da ita gata yaya ce amma haka take shafe kwanaki a gidan in tazo garin, shiyasa Zayyad har ya fara rainawa 'yan uwanta saboda yadda suke nuna kwaɗayinsu a fili, ƙarin haushinsa muddun in suka zo haka Rashida take banzatar da lamarinsa ta mayar da hankalinta kacokan kansu bata damuwa da buƙatunsa.
Mahaifinsu Zayyad mai suna Ahmad ya rasu sai Hajiyarsu Halima wacce 'yarsa ilham taci sunanta, Aslam kuma yaci sunan babansu Ahmad, yana da yaya mace Bilkisu suna zaune a Abuja da mijinta Kamaluddeen yaransu huɗu, sai Zayyad sannan Asiya wacce itama tana aure a malali yaranta biyu, sai Mukhtar da yake karatu a KASU.
Ɓangaren Rashida kuma ita ce ta biyu a gidansu, tana da wa Salis, sai Rashida, sannan Haruna sai Anisa sannan Zaliha, ita Wasila yarinyar yayan babansu ce amma a gurin mahaifiyarsu Rashida ta tashi shiyasa suka taso tamkar uwa ɗaya uba ɗaya.
Zayyad da Rashida auren soyayya suka yi kuma Alhamdulillahi a wancen lokacin sun samu fahimtar juna, yaransu biyu Halima (Ilham) 'yar shekara bakwai sai Ahmad (Aslam) ɗan shekara Huɗu. Babban saɓanin da suka fara samu shine yadda Rashida take da mugun kuiya musamman a gurin yin girki, ta mayar da Zayyad tamkar gauro mara mata kullun abincinsa yana waje, dan sai yafi sati bai ci abincin gidansa ba saboda sakacinta, musamman in ya dawo bata gama ba zai fice yaje rastuarant ko yaje gidan mahaifiyarsa yaci saboda baya ƙaunar jira dan ba yi da juriyar yunwa. Idan kuma aka ce watan azumi ya kama to dama baida abun buɗe baki a gidansa, saboda kwata kwata Rashida bata mayar da hankali ta fara aiki da wuri balle a samu ta gama aci akan lokaci, hatta yaranta tana horar dasu da yunwa tsabar kuiya da yayi mata yawa, ga rashin bawa shinfidarsa muhimmamci saboda shegen saurin barci gareta duk inda aka ce goma tayi to tana nan ta hangame baki ta soma barci, sai ya dawo daga inda yaje bata san ya shigo ba, haka yake yawan azumin litinin da alhamis yana ragewa kansa zafi saboda marabarshi da mara mata abu kaɗan ne. Tarin matsalolinta ya sashi soma kule kulen mata a waje musamman waɗanda suka haɗu a shafin sada zumunta na facebook da Instagram, badan yana sha'awar ƙara aure ba sai dan kawai ya riƙa samun in da sai rage lokaci kafin dare yayi ya shigo guda, ko kuma in ya dawo haka zai ɓata lokaci yana chart da 'yan mata kala kala tun baya kauce hanya har ya fara biyewa suna irin hirar nan na batsa, duk da shi mutum ne mai matuƙar tsantseni da aikata zina, sharholiyarsa a iya waya yake yi shima bai yarda da tura hotunan tsiraici ba sai dai zantukan batsa dan ragewa kansa zafi. Hakan yasa ya haɗu da wasu natattun 'yan mata su biyu Zubee da Seema, da yake su yan hannu ne babban burinsu shine su samu damar da Zayyad zai kwanta dasu, duk da suna kawaye amma basu damu ba ko kishin junansu ba tunda rayuwa ce ta bariki.
Matsalolin Rashida sune suka jawo rashin jituwa a tsakaninta da 'yan uwan Zayyad, tun yana ɓoye damuwarsa har sai da Hajiyarsa tazo ta sani, ita da kanta tasha zuwa tana bawa Rashida shawarwari akan zamantakewa dan ta gyara, saboda tana son Rashida kuma ita irin surukan nan ne masu sauƙin kai da hali sam ba tada takurawa matar ɗanta, amma baisa Rashida ta karɓi gyara ba sai tayi biris da shi taga kamar ma takura mata take son yi, gata sam ba tada kunya bata tauna magana kafin ta yi shi wannan yasa zamansu ya koma zaman haƙuri duk kuwa da irin son da Zayyad yake yi mata bai taɓa tunanin ƙara aure ba a ganinsa har da ƙuruciya zata gyara.
Sai dai kuma tun sa'ilin da yayi tozali da Safna ya kamu da zazzafar soyayyarta yaji yana buƙatarta a cikin rayuwarsa, shiyasa ya yi ƙoƙarin samun zuciyarta har suka kawo gaɓar yin aure, hakan yasa shi ya ja baya da 'yan matan da yake kulawa a shafin sada zumunta ya mayar da hankalinsa kan Safna kawai. Batun gidansa kuwa dama tuntuni yaƙi mayar da hankali ya gyara side ɗin dake cikin gidansa, wanda a da niyyyarsa zai saka 'yan haya in kuma ƙaninsa Muktar ya kawo munzalin aure ya tayar da 'yan haya ya aje matar a ciki, sai gashi ashe da rabon Amaryarsa ce zata tare a ciki, shiyasa ya mayar da hankali har sai da ya kammala gyaran.
Lokacin daya nunawa Rashida zai ƙara aure sam bata ɗauki lamarin da gaske ba, dan tasan yana matuƙar son ta saboda da zai yi mata kishiya da tuntuni yayi irin yadda mutane ke zugashi, amma data ga da gaske ne sai ta kwantar da kanta bata ɗaga masa hankali ba dan tasan tunda yayi niyya sai yayi, kawai dai fargabanta kar ya auro wacce zata kwace mata shi, shiyasa tayi yadda zata yi ta shigewa Safna a jiki dan tasan wacce irin mace Zayyad zai auro mata, tayi sa'a Safna tana da sauƙin kai tana matuƙar girmamata, suna yin waya da chart a tsakaninsu, wannan yasa sosai Zayyad yake ganin zasu samar masa da zaman lafiya a gidansa kuma ba ƙaramin farin ciki yake yi da haka ba, shiyasa yake ƙara kyautatawa Rashida duk abinda tace tana so sai yayi mata domin ya sata farin ciki, amma kuma duk a banza dan har yau ba sauya halinta tayi ba tana cigaba da yi masa riƙon sakainar kashi wanda hakan ke ƙara tunzurashi da ya auro Safna.
***
Gidansu Safnah.
Zayyad yana isa gidan yayi parking yana fitowa sai ga Yaya Mudan ya fito zai je siyo abu, ya isa gabansa suka gaisa kana yace ya shiga cikin gida bari ya kira masa ita, Zayyad yayi masa godiya tare da bin bayan Mudan daya nufi cikin gida, sai da ya fara ɗauko masa tabarma ya shimfiɗa a simintin tsakar gida daga gefe, kana ya shiga kwalawa Safna kira ta amsa daga cikin falo.
To ki fito ga mijinki ya zo, gashinan a tsakar gida.
To tace masa kana ya fice ya nufi inda zashi, ba jimawa Safna ta fito cikin dogon Hijab riƙe da tire a hannunta da jug da kofi biyu akai sai gorar ruwan swan da kuma plate an rufe shi da ɗan uwansa plate.
Rahma Ce.
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, ban hanaku ɗaura labarina ba amma a barmin sunana tare da barin rubutuna yadda yake, da fatan za a kiyaye_
[05/09, 7:12 pm] null: https://chat.whatsapp.com/D5ISXoMOGGR9PPoswkybsj
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .
Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.
MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .
UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari 🤗🤗🤗
*AMARYAR ZAYYAD*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 3
Safna ta aje tiren a gabansa kana ta zauna nesa kaɗan da shi tana cewa.
Amincin Allah ya tabbata a gareka Sirrin Zainab.
Ameen Wa Iyyaki. Ya mutanen gidan.
Alhamdulillah duk kalau suke.
Masha Allah! Amma kafin mu kai ga hira, ki fara gabatar mini da abinda kika tanadar mini cikina ya ɗauka tukuna.
Murmushi tayi wanda yasa kumatunta lotsawa dimple, tare da matsawa gabansa ta buɗe plate ɗin Samosa data soya shi ɗazun, Zayyad tun kafin tace masa gashi yayi saurin zura hannu a ciki ya ɗauka ya kai bakinsa ya fara ci, yana irin santin nan da mirgina kai dan yayi masa matuƙar daɗi, Safna dai murmushi kawai take zuba masa kana ta ɗauki kofi ɗaya ta shiga tsiyaya masa kunun madara, Zayyad ya yi saurin katse ta da cewa.
Meye wannan kuma ko yoghurt ne?
Sha dai kaji?
Ta faɗa tana miƙa masa, Zayyad ya amsa tare da kai kofin bakinsa ya kurɓa, wani irin garɗin daɗi ne ya shammaci maƙogoronsa bai san sanda ya kafa kofin a bakinsa ba ya shiga kwankwaɗa, sai da ya shanye kafin ya cire kofin yana sauke ajiyar zuciya mai ɗumi, ya kalli Safna cike da tsantsar ƙauna.
Allah yayi miki albarka, yadda kika faranta mini ubangiji ya faranta miki sannan ya cika miki burinki na mallakar Zayyad.
Wannan karan dariya ne ya kubce mata ta shiga yinsa a hankali sautin yana fita.
Ya baki ce Amin ba kina min dariya.
To ai gani nayi kamar sai an sanya maka waigi, wannan irin santi kamar ance maka ga Safna a cikin gidanka an baka halak malak.
To me ya rage nan da wasu 'yan kwanaki ƙalilan ne komai zai tabbata har abada. Amma batun gaskiya ko miye wannan abun ya mini zallar faɗi, na dai san an saka madara dan ƙamshinsa ke dukan hancina, amma me kyau ki faɗa mini me kika bani ne haka mai daɗi?
Wannan shi ake kira da kunun madara, kuma shi kasha.
Wow amma gaskiya ya kayatar da ni, ban taɓa shansa ba amma ki tabbatar in kinje gidana zaki cikani da salo salon girkinki Ruhieee.
Ya yi maganar yana jan ƙarshen tare da lumshe ido yana saka hannu a gefen zuciyarsa, sosai Safna ta saki dariya, nan dai suka cigaba da hirarsu gwanin sha'awa har misalin ƙarfe tara da rabi kafin suka yi sallama, amma fa saida Safna ta kakkaɓe masa duk wani damuwar da yazo dashi kafin suka rabu ya nufi gidansa cike da bege da ƙosawar son kasancewa da ita.
Ko da Zayyad ya isa gida ya tadda kayan kallo a kunne kitchen a buɗe amma ba kowa a falon, ga plate ɗin abinci da suka ci suka barshi a falon banda ƙamshin taliyar manja babu ƙamshin dake tashi, haka ya kashe soket ya jawo ƙofar kitchen kana ya wuce ɗakinsa, ya cire jallabiyar ya rage ƙananun kaya ke jikinsa ya kwanta tare da jan bargo ya rufe ƙafafunsa, Safna ta riga ta cika masa ciki baida buƙatar abinci, kuma da yake yasan halin matarsa bata girka masa komai ba, da zai kirata ya tambayeta zata ce ta manta, guntun tsaki yaja ya kunna data ya fara duba WhatsApp domin ganin saƙonninsa, dama time ɗin chart ɗinsa kenan dan inya fita aiki ba yida lokacin waya saboda hidima da mutane, nan saƙon Safna ya shigo tana cewa.
Allah yasa mijina ya sauka gida lafiya.
Sai da ya saki murmushi kafin ya bata amsa da lafiya lau sai dai yaga bata online, nan ya fito ya shiga duba saƙonni nan ya samu Seema tana online, sai suka fara chart daga nan kuma suka cigaba da hirarsu na sakin layi, haka ya shagala har kusan sha ɗaya da rabi, ya ce mata zai sauka barci zai yi suka yi sallama tana yi masa mitar itafa ta gaji da ja mata rai da yake yi ya kamata yazo su haɗu su jiyar da juna farin ciki, bai bata amsa ba ya sauka dan yasan ba zata taɓa samun wannan damar ba yana matuƙar kyamar aikata zina, wannana chart ɗin da suke yi shima so yake ya yakice shi ya huta tunda Safna tana gabda shigowa gidansa, Zayyad barci yake ji amma kuma cike yake da buƙatar mace a wannan lokacin musamman yadda yasha kunun madara ya tada masa da maitarsa, dan shi da zarar yasha madara da dare ko yogot to tabbas sai ya motsa masa buƙatarsa, ya duba agogon wayarsa sha biyu saura nan ya shiga wajen kira ya lalubo number ɗin Rashida ya soma kiranta sai dai kash tasa wayar a silent ta saka a jikin chargy a wuta, sannan ma barcinta take yi hankalinta kwance dan tuni tayi nisa dan koda ya dawo tayi barci Anisa ce keta danne danne a waya tana chart, Zayyad sauke ajiyar zuciya yayi mai ɗumi ga mace har mace amma sam hoto ce bata damu da buƙatarsa ba sai nata, dan in abin ya motsa mata tasan ta jira shi ya dawo duk inda yaje, kota dinga kiransa a